An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://thausanovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.thausanovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
*RUFAFFEN SIRRI*
*NA SADNAF*
*ADABI WRITERS ASSOCIATION*
*BISMILLAHI RAHAMANIR RAHEEM*
*PAGE 1*
"Ba abinda na tsana sama da abinda zai Shiga tsakanina da baccina,kamar na kurma ihun
bakin ciki haka nake ji a lokacin da naji Abban Nusrah na ta shafani wanda nasan mai hakan
ke nufi,tun kafin nayi bacci bai neme ni ba sai yanzu,ban motsa ba dan har ga Allah bazai samu
abinda ya keso har ya gamsu ba,sai dai shi kadai yayi kidan sa yayi rawar sa duk da ba abinda
ya shafe shi ko baccin nake idan yayi ra'ayi ko ban bashi hadin kai ba zai juyo dani ne ya samu
biyan bukatarsa.
Ina Jin lokacin da ya rabani da zanin dana dora a saman t shirt din dake jikina,a madadin ya
juyo dani sai naji ya rungumeni ta baya,ya fara k'ok'arin neman hanya da jikinsa dan tsawon
zamana dashi ban wani san dan aike ba balle har wai a motsa min sha'awa,shi dai burin sa
kawai ya shafani sama sama ya samawa kansa nutsuwa,inda naji Yana k'ok'arin yi yasa nayi
saurin janye jikina,sai a lokacin na motsa na juyo Ina kallon sa cikin mamaki,shi kuwa idonsa a
kankance ya kara jawoni,sai na juyo a rigingine dan ya samu abinda yake so dan Ina tunanin
dan ta gefe yasa yayi hanyar da ba haka ba,sai dai a madadin ya hau kaina sai naga ya Kara
juyar dani ya kankameni da hannu daya ya sa hannu daya ya Kara danna jikinsa wajen da yasa
na Kara janye jikina da bala'in sauri na Mik'e zaune cikin mamaki Ina kallonsa.
K'ok'arin jawoni yake na janye jikina Ina "Lafiya kuwa Abban Nusrah mai haka"?
"Wane irin tambaya ne wanan Sajeeda bangane mai haka ba ki matso na samu nutsuwa ki
koma baccin ki"
"To ai kai din ne bangane ba Kai ma kasan ba wajen nutsuwar ka nufa ba bayana naji kana
k'ok'arin shiga"
Tsaki yayi ya Kara jawoni da k'arfi Yana "Ta bayan yafi dadi bari kigani"
Da karfi naga Yana Neman tura jikinsa bayana
Da k'ok'awa na fusge jikina cikin tashin hankali da mamaki na sauka daga gadon na nufi wajen
haske na kunna na zuba masa ido kamar yanda shi ma ya zubo min ido, tamkar an like min
baki haka naji dan tsabar mamaki na ma kasa magana,shekarar mu Ashirin da biyu da Aure
bana Jin da gani har shi bakine a wanan fagen balle ince sani ne bai yi ba shi yasa yake
k'ok'arin nema na ta baya har Yana cevmin yafi Dadi.
"Abban Nusrah anya a hayyacin ka kake kuwa"?
Mik'ewa yayi ya nufo wajen da nake tsaye yayi kasa da muryarsa yana "Sajeeda a hayyacina
nake nasan zaki ji wani iri amma ki taimaka ki ba ni hadin kai ina so na gwada ta bayan nan
ance yafi dadi"
"Allah ya kiyaye Kabiru Allah ya kiyaye ni zaka nema ta baya ta Inda ake kashi,kabiru Anya
Kaine kuwa?waye yace ma ka nemi matar ka ta baya, idan Wanda ya baka shawara bashi da
ilimi kai ina ka Kai naka ilimin bayan kasan haramun ne, bazan iya ba Kai ma da ka yi tunanin
kayi gwajin ka fara istigifari"
Kasa ya Kara yi da murya cikin rarrashi ya matsoni Yana "Sajeeda yanzu baza ki iya taimaka
min ba ki bari nayi sau d'aya sai muyi istigifari an dade ana kwadai ta min ta bayan nan haba
matata"
Ya fara k'ok'arin rungumoni na ture shi da iya karfina dan zuwa yanzu ma sai naji tsoron uban
yayana ya kamani,gani nake kamar bashi ba
"Kabiru Ina ga ba'a hayyacin ka kake ba a tsawon lokacin da nake tare da Kai nasan baka
shaye shaye ballantana nace ba'a hayyacin ka kake ba,a iya sani na ka na da ilimin ka daidai
gwargwado ka san abinda ya ke daidai da wanda yake haramun, bazan tab'a maka biyayya na
Sabawa Mahallicina ba Ina mai rokon ka idan a hayyacinka ka ke wani ne ya baka shawara ka
zo ka neme ni ta baya,ka gaggauta rabuwa da koma waye dan so ya ke ya Kai ka halaka"
Daga haka na nufi Kan gado na na dauki zanina na daura nayi hanyar fita daga d'akin ya hau
kwalla min kira Yana
"Sajeeda Sajeeda karki sake ki bar d'akin Nan
Ko juyawa ban yi ba har na bar d'akin har lokacin ban daina mamakin sa ba.
Koda na fito dan karamin palon namu fitila na kunna idona ya sauka akan agogo naga karfe uku
na dare na zauna akan kujera tare da dafe kaina jikina har rawa yake bansan tunanin ma da ya
Kamata nayi ba.
Na kasa yarda da abinda ya faru yanzu a daki,na kasa yarda mijina uban yayana da shekarar
mu Ashirin da biyu da aure da arzikin Yara biyar har mun aurar da Yar mu ta fari Nusrah shi ne
yau dare daya zai nemeni ta baya wai ya dade yana san yayi gwaji an ce Masa yafi dadi har
waye zai ce wa Kabiru ya gwada abinda Allah ya haramta.
Sosai na zurfafa a tunani bansan tsawon lokacin da na d'auka Ina saka da warwara ba,sai Kiran
sallah ne ya katse min tunanin da na tafi.
Mik'ewa nayi na koma d'akin.
A kwance na ganshi Yana dan girgiza kafarsa da alama ba Bacci yake ba idonsa biyu.
Bandaki na shige na daura alwala na fito har lokacin Yana kwance bai motsa ba,nasan fushi
yayi,da ace wani abin na Masa da har zai yi fushi dani da sai na bashi hakuri,amma ni nasan ba
laifin da na masa bazan tab'a masa biyayya a sabon Allah ba ba muyi haka tun kuruciya ba sai
yanzu da muka Manyan ta,tsawon zamana dashi ban tab'a hana shi hakkin sa ba Koda kuwa
fada mu ke amma dai yau na bijire masa dan bazan iya Sabawa Allah ba,
tsigar jikina har tashi yake idan Ina hararo yanda wai zai sadu dani ta baya.
Sallah nake amma na kasa yin sa a nutse sabida tunanin da ya dankare min zuciya.
Har na sallame Yana kwance zuwa yanzu sai naji kamar canzo kabiru aka yi bashi bane dan iya
sani na baya Wasa da Sallah fushi dani bazai saka wai yak'i fita massallaci sallah ba.
Kasa hakuri nayi da carbina a hannu na Mik'e na zagaya ta wajen da ya kwanta Ina "Abban
Nusrah "Abban Nusrah yau ba zaka yi sallah bane"?
"Dama can ke kike saka ni nayi Sallah"?
"Bani nake saka ka kayi sallah ba amma dai bai dace idon ka biyu kana Jin ana sallah ka k'i
tashi kayi akan lokaci ba"
Tsaki yayi ya juya min baya.
Zuwa yanzu bazan iya fadan kalar mamakin da nake na sauyawar halin mijina dare daya ba,ga
nemana ta baya ga k'in sallah.
Bai tashi ba sai da gari yayi haske ya shige bandaki ya dauro alwala yazo ya tada sallah Yana
sallamewa ya fice daga d'akin.
A ranar sukuku na wuni na rasa mai ke damuna dan tunda Abban Nusrah ya fice daga gidan
bai Kara dawowa ba.
Har karfe hud'u na yamma Ina zaune zuciyata fal da tunanin muryar Yasmeen ya katse min
tunanin da na tafi "Umma ko dai magani zan d'auko miki ki sha"?
Girgiza kaina nayi na aro murmushi na yafa a fuskata sam bana so ta fahimci Ina cikin
damuwa,dan nasan sai ta fini ma shiga cikin damuwar, kallonta da nake fuskar kanwata nake
gani a fuskarta Margayiya Nuratu damuwar da nake ciki yasa naji hawaye na zubo min.
"Umma kuka kike"?
Share hawayena nayi Ina "ba kuka nake ba Yesmeen na tuna kanwata ne kawai Allah ya
gafartawa Nuratu"
"Bata amsa ba illa idon ta da naga ya ciko da kwalla shekara goma kenan da rasuwar kanwata
da ta kasance mahaifiyar Yesmeen.
Ruk'onta ya dawo hannuna Ina balain kaunar yesmeen tamkar yanda nake kaunar yayan cikina,
Yesmeen ta Kara siye zuciyata ne daga lokacin da rukon ta ya dawo hannuna,tana da bala'in
biyayya da hankali duk wani abu data san ina so bata Wasa dashi bata da burin daya wuce taga
ta faranta min ko Yaya ta gani a cikin damuwa itama tayi ta damuwa kenan.
Ko yanzu ma nasan ba lailai taci abinci ba sabida ta gani a cikin damuwa.
"Jeki d'auko mana abinci mu ci dan nasan baki ci abinci ba.
Tura abincin kawai nake ba wai dan Ina gane dandanon sa ba,na daure na hadiye damuwar da
nake ciki dan Kar na Kara dagawa Yesmeen hankali.
Koda muka gama cin abincin daki na shige na cewa Yesmeen zan dan kwanta dan itace take
yin aikace aikacen gidan Kamar yanda ta Saba kafin Nusrah tayi Aure tare suke aikace aikacen
gidan,dan su biyu ne kawai Mata kannen Nusrah duka maza ne,Saifullahi Fahad Hamza da
Annur.
Sosai na tsinci kaina a cikin damuwa dan tunda nake da Abban Nusrah bai tab'a fita Yana fushi
dani ba dan muna samun sabani zamu shirya,duk da Yana da zuciya nasan hanyar da nake bi
na shawo kansa,amma jiya abinda ya b'ullo min dashi ya girmama tunanina bazan tab'a iya
barin sa ya neme ni ta baya ba sai kace wasu jahilai.
Karfe goma Sha daya ya shigo gidan fuskarsa a bala'in hade ina zaune a palo Ina jiran
dawowar sa dan har yara duk sun yi Bacci.
Ko sallama bai yi ba ballantana ya kalli Inda nake, d'aki ya shige batare da ya amsa sannu da
zuwan da nake masa ba.
Da ido na bi bayan sa Ina Kara mamakin fushin da ya ke dani na rashin gaskiya har ga Allah
mamaki da al ajabi nake ,mik'ewa nayi na d'auko farantin da na jera abincinsa na bi shi d'akin.
Ko da na shiga a gefen gado na gan sa a zaune yana duba wani abu kamar a takarda ban dai
san mai yake dubawa ba"
Na ajiye farantin a gefen teburin dake gefen gadon Ina
"Abban Nusrah Sannu da dawowa"
Bai dago ba ya cigaba da duba takardar Hannun sa
"Abban Nusrah mai na maka kake fushi dani?a iya sanina ba abinda na maka Abban Nusrah
wani bak'on al amari ka zo min dashi wanda ni nasan kasan haramun ne,dagani har Kai ba yara
bane,ga ta hanyar da Allah ya hallata ma ka neme ni ka samu nutsuwa dani,amma dare daya
Abban Nusrah kace zaka neme ni ta baya ta Inda Allah ya haramta kaga dan na k'i bin umarnin
ka bai Kamata kayi fushi dani ba dan babu biyayya a sabawa Allah,bansan waye ya baka
wanan gurguwar shawarar ba,iya sanina duk wayanda kake mu'ammalla dasu ba mutanen
banza bane bansan waye ya ce ma ka gwada ta baya zaka ji dadi ba,taya wajen da ake kashi
yayi dadi Ni dai kayi hakuri zan iya k'ok'arina dan na gamsar da Kai amma ban da ta baya"
Sai a lokacin ya dago ya kalleni ya ajiye takarda a gefen pillo Yana "Sajeeda duk abinda nake yi
Ina sane tsawon zamana dake Ina ga baki tab'a ganin na neme ki ta baya ba,gwaji ne kawai
nake so nayi naji abinda ake ji ba wani abu ba,amma tunda kin nuna bakya so shikenan ba zan
Kara nema ba,na dauka duk abinda nake so matsawar bai fi karfin ki ba Zaki iya min"
"Wanan yafi karfina ne Kabiru shi yasa bazan iya ba abinda akace haramun ne ban ga dalilin da
zai saka kace zaka gwada ba mu fa ba Yara bane idan muna raye ma wani shekara zaka gan
mu da jika"
"Ya isa haka Sajeeda Kinga na Kara neman naki ne yanzu"!?
Shiru nayi Ina kallon sa yaja siririn tsaki ya kwanta ya juya min baya.
Nace masa ga abincin sa yace bazai ci ba.
Wasa Wasa mijina ya fara fushi dani dan naki bari ya nemeni ta baya Wanda zuwa yanzu
lamarin nasa ya fara bani tsoro ko Yaya na shawo kansa asan na faranta Masa rai, a madadin
yayi ta hanya da ya dace sai naga Yana neman tura jikinsa bayana.
Halin nan daya bijiro min dashi ya matukar daga min hankali dan kullum cikin fada mu ke.
Gashi mu ba Yara ba ballantana nace wani Zan nemi shawarar sa Wanda ni nasan mu ya
Kamata ma mu ringa hana wasu ba dai mu ba.
Ko a yanzu da ido nake bin sa har ya gama shiryawa bai ce min komai ba ya fice daga dakin
na sauke ajiyar zuciya ina tunanin mafita Kiran Nusrah daya shigo wayata ya katse min tunanin
da nake.
Ina dagawa muka gaisa kamar yanda muka saba Inda take sanar min zuwan ta anjima na ajiye
mata dambu na saki murmushi Ina sai ta zo.
Na Mik'e nayi waje dan na fadawa Yesmeen zuwan Nusrah duk da nasan kila ma sun yi waya.
Ina fitowa naga Abban Nusrah a zaune a doguwar kujera duk a tunanina Yama fita ashe fitowa
yayi ya zauna a palon.
Yesmeen kuma na tsugunne a gabansa tana hada mi shi shayi.
Fitowa ta yasa ta dago tana "Umma Ina kwana"
Zama nayi a gefen shi fuskata d'auke da faraa na hau amsa gaisuwar ta ko kad'an bana so
yarana su fahimci wani abu.
Tana gama hada masa ta mike tana bari ta d'auko kofi ta hado min shayin na girgiza mata kai
akan ta bar shi sai anjima.
KABIR
Da ido ya bi Yesmeen din har ta shige d'aki ya d'auki shayin ya fara kurba a hankali har ya
shanye Yana Jin idon Sajeeda a kansa.
Yana dire kofin ya mik'e yayi waje batare da ya tsaya Jin mai Sajeeda ke cewa ba.
Yana fita ya haye machine din sa bai zame ko'ina ba sai wani hadadden gida da fadar haduwar
sa bata Baki ne.
Mai gadi ya riga da ya gane shi hakane yasa ya bude masa ya shige da machine dinsa kansa
tsaye ya nufi d'akin saukar baki dake farfajiyar gidan.
Kamar yanda yayi tsamani a zaune ya tarar da Alhaji Rabiu a cikin dakakiyar shaddarsa dake ta
kyalli kamar madubi.
Sai da Kabiru ya sama wa kansa wajen zama.
Alhaji Rabiu yace "An dace kuwa"?
Sai da Kabiru ya sauke ajiyar zuciya yace "wlh ba'a dace ba duk ta inda kake tunanin zan biyo
mata na biyo mata wlh tak'i bani hadin kai"
Murmushi Alhaji Rabiu ya saki Yana "Na fa san irin su haka suke da balain taurin kai Amma
idan tasan wata ai bata San wata ba ka tashi muje wajen shugaba mu masa bayani"
Ya mik'e Yana k'ok'arin yin hanyar waje.
Kabiru yayi saurin dakatar dashi yana "Rabiu Ina kaunar matata tunda na yarda zan yi harkar
nan zuciyata take cike da fargaba da tsoro ko bacci bana iya yi dan Allah muje wajen shugaba
ka fada masa ya duba min ko zan iya yi da wata na samu biyan bukatata ba sai Sajeeda ba.
"Ikon Allah toh wa zaka samo"?
"Akwai yar kanwarta da nake rike da ita da ita nake so na samu biyan bukatar tawa"
"Bani da ta cewa muje daga can muji ko zai yu......
Hmmm
*RUFAFFEN SIRRI*
*NA SADNAF*
*ADABI WRITERS ASSOCIATION*
*Page 2*
Kabiru har suka je Suka dawo bai iya magana ba sabida kasan zuciyarsa cike take da
tsoro,ji yake Kamar ba zai iya ba dokokin da Abubuwan da akace yayi sun masa yawa da
tsauri,a hankali ya Kai dubansa wajen Alhaji Rabiu da ya kasance abokinsa tun primary da a
lokacin ya fi shi k'ok'ari nesa ba kusa ba dan shi yake zuwa na karshe ma a ajinsu da kuwa
suka gama primary bai Kara saka shi a idonsa ba,bai Kara jin labarin sa ba sai a shekara biyu
da suka wuce ya had'u dashi,sai da yayi da gaske ya gane shi sabida yanda ya dawo fari kal
sabida yadda hutu da Jin dadi suka zauna masa tashin farko,kyautar dubu dari ya Masa,ya
hada da bashi lambarsa,duk kalar rayuwar da yaso tun Yana karami na rayuwar Jin dadi shi
yake gani a wajen Rabiu.
Gashi ya girma zai iya cewa ya d'auko tsufa tunda Yana dab da aurar da 'yar cikin sa duk bai
samu cikar burin nasa ba.
Tuni yaji ya kwadaitu da san yayi kudin fiye ma da da hakane yasa ya makalewa Alhaji Rabiu ko
zai taimaka Masa ya sama mi shi aiki irin nashi da shi ma zai samu kudin.
A haka Alhaji Rabiu ya ringa masa yawo da hankali Yana kasuwanci yake yi sai da yayi
dagaske Rabiu ya fito ya nuna masa ta hanyar da ya samu kudin sa,idan har yaga zai iya.
Tsayuwar motar Alhaji Rabiu a wani tamfatsatsen gidansa da matarsa ta uku take ciki ya katse
tunanin da Kabiru ya tafi.
Yayi horn Mai gadi ya bud'e masa.
Tun da suka shiga gidan Kabiru ya saki baki da hanci Yana kallon Aljannar duniya,maganar
shugaba na dawo Masa a kunne,"zaka yi kudi, idan nace ma kudi,Ina nufin kazamin kudin da
zai saka duniya ta san ka zaka ji dadin rayuwar ka zaka bar wa yayanka tarin dukiya ka tabbata
baka tsallake duk sharuddan da aka gindaya ma ba daga yanzu kafin wata ukun zaka fara
dandana arziki amma ka iya takun ka"
"Sauko mu Shiga daga ciki ka gaisa da Aseeya"
Muryar Alhaji Rabiu ya katse Masa tunanin da yake.
"Rabiu anya zan iya wlh bansan mai yasa nake Jin bazan iya ba gani nake za'a iya gano ni da
wuri bazan iya yiwa Sajeeda haka ba"
Murmushi Alhaji Rabiu ya saki Yana "Tunda na iya yiwa Sakeena Yar uwata haka Kai ma zaka
iya bafa kasheta zaka yi ba,a cikin kankanin lokaci Kai ma zaka zama kamar ni,kayi amfani da
abinda kake dashi ka samu cikar burin ka,kar ka karaya abokina muje dai daga ciki indai Muka
bi komai a yanda Muka tsara wlh baza'a samu matsala ba"
Kabiru gyada Kai yayi duk da a kasan zuciyarsa gani yake bazai iya ba.
Yabi bayan Alhaji Rabiu yana karewa gidan kallo,hararo kansa kawai yake a matsayin Rabiun
ya mallaki irin wanan gidan,ya ginawa su Saifullahi manya manyan gida daidai da Nusrah ma
sai ya mallaka Mata gida da mota, tuni yaji ya Kara kwadaituwa da ya samu kudin,a lokacin da
suka Shiga palon da Kamar a kasar waje suke da suka shiga.
A lokacin kuwa daya zauna kalle kalle ya cigaba da yi Alhaji Rabiu ya haye Sama minti biyar a
tsakani sai gashi ya sauko ya zauna.
Kafin kace me masu aiki sun cika gabansu da kayan ciye ciye.
Alhaji Rabiu kuwa sai murmushi yake dayaga yanda Kabiru ke hadiyar yawu.
Takun takalmin Aseeya matar Alhaji Rabiu dake saukowa daga saman benen yasa Kabiru
maida hankalin sa wajen benen.
Yarinya ce bata fi saar Nusrah Yar sa ba ko zata girmi Nusrah bazai fi da shekara biyu
ba,kyakyawa ce ta ajin karshe tamkar ita tayi kanta fuskarta d'auke da murmushi,har ta karaso
gefen Alhaji Rabiu ta zauna ta fara gaida Kabiru da ya hau washe baki kasan ransa Yana ta
mamakin yanda yarinya karama ta yarda ta auri sa'an mahaifinta.
Bayan sun gama gaisawa ta mik'e ta koma sama,
"Rabiu yanzu Wanan Yar yarinyar ka Aura"?
Murmushi Alhaji Rabiu ya saki ya zuba Lemo a kofi sai da ya kurba ya ajiye ya kalli Kabiru
Yana "Shekara uku kenan da Auren mu Kuma ta wajen nan da matarka ta hana ka ta wajen
nake neman ta"
Ido Kabiru ya zaro waje Yana "Kuma sai ta yarda"?
"Kwarai kuwa ba Ina da kudi ba,a yanzu da kake ganin ta bama tasan Inda zata Kai kudi ba
kaga kuwa ko dan su dole ta yarda da bukatata dan sai da na tabbata Iyayenta irin talakawan
nan ne sosai,dan a garin talla ma na hadu da ita,na cikata da kudi na cika Iyayenta da kudi,
basu da gidan kansu kafin na aureta yanzu kuwa har yayyenta maza ba Wanda ban siyawa
gida ba tana morata a zahiri Ina morarta a badini"
Sai yayi kasa da murya
"Tana samun ciki take b'ari na riga na bada mahaifarta"
Ni kuwa Ina nan da yayana bakwai suna jin dadin su a waje"
Kabiru mamaki ya sa ya kasa ma magana dan sai a yanzu ya gane da rabon amaryar kudin sa
ke Kara hab'aka uwar yayan sa kuma ta masa silar kudin.
"Rabiu dama nima na auri wata ta zama silar kudin bana so na tab'a uwar Yayana da mu ka
Sha wahala tare da ya Kamata ace a yanzu taji dadina shugaba ya bani wata uku ya bani
Abubuwan da zanyi har zuwa matakin karshe,tunda Muka baro wajensa wlh jikina a sanyaye
yake gani nake bazan iya ba"
Wani irin mugun kallo Rabiu yabi Kabiru da shi yana "Ka ga idan baza ka iya ba ka tashi ka bar
min gida ka Kuma dawomin da kudadena da na baka,kudin nan idan kayi ni zaka bawa ko me
ana ta nuna ma hanyar arziki kana baudewa,duk uban wahalar nan da ka ringa bani dama baka
tsayar da zuciyar ka ba abu kad'an sai kace baza ka iya ba dalla tashi ka bar min gida kasan
Kuma baa yiwa kungiya haka indai ka fasa wlh sai an tab'a ka"
"Ba abinda nake nufi ba kenan Rabiu ba fasawa zanyi ba sharrudan yanzu sunfi bani tsoro ina
tsoron na kuskure a samu matsala"
"Ka kwantar da hankalin ka kasa a ran ka zaka iya Sajeeda da kake ta fadi ba fa kasheta zaka
yi ba balle,dadin ma da ita za'aji gefe guda Kuma idan an kwana biyu zaka iya auren Mata uku
kayi ta more rayuwar ka abokina kana Jin dadi,yayanka ka gan su fes,ni kasan gabad'aya
yarana suna kasar waje,shawara daya dai Zan baka duk yanda muka tsara ka bi zaka Sha
mamaki kila.ma.ka fini himma wajen bada abin arziki kudi suyi ta hauhauwa ai ba dawwama
zamu yi muna yi ba zamu Yi iya yin mu kudin ya Kai mana yadda muke so sai mu tuba muyi ta
istigifari Allah Mai yawan afuwa da gafara ne zai yafe mana duk shekara muna d'akin sa muna
neman yafiya fa wanan ba wani abu bane"
"Hmmmm toh shikenan Allah yasa duk Kar na samu matsala Ina Addu'a Allah yasa Kar Sajeeda
ta tab'a rafkoni dan tana da balain wayo da san tabi kwakwafi"
Da haka suka cigaba da hirarsu wajen laasar Alhaji Rabiu ya Kara tsara masa duk yanda za'a yi
ya d'auko kudi ya bashi mai yawa ya raka shi ya tafi.
Sajeeda
Idan naga yarana gabad'aya a gabana ji nake kamar banida wani matsala a rayuwata,
zuwan Nusrah yasa na manta da damuwa da hawan jinin da Abban Nusrah ke neman saka
min,Ina zaune a tsakiyar su duk mun baje a tabarma ana ta hira, wayarta ya hau ringing tak'i
d'auka ganin Kiran ya Kara shigowa nace "Wai ba za ki dauki wayar ki ba ko ba kiran ki ake
ba"?
"Umma Ahmad ne fa na san cewa zai yi na dawo ni Kuma na fi so na gaisa da Abba kafin na
tafi na ga kowa ban dashi bazan ji dadi ba idan ban gan shi ba"
"Sai ki Kira shi a waya ku gaisa maza tashi ki