daga baya su kai ta rarrashina. Inno kuwa wanka tayo ta shirya tsab, tana rabon tsaraba tana sake jaddada musu labarun da in haddace sun riga da sun daɗe da haddacewa. Yadda suke ji, da irin halin da suke shiga, da irin tsangwamar duk da suke shiga in ina gabansu ina zawarci. Wai me yasa iyaye da jama'ar gari basa yi ma BAZAWARA uzirine? Har ta gama rabon tsarabar batai shiru ba.
"To ni kam zan wuce gidan bikinnan. Ke Tani Karime ta raka ki ku je ku dubo Dauda. In yaso kwa same ni a can gidan bikin zamu tafi da su Use. In shi Naranin ya amince muku sai ku ɗauko Daudan ya ɗan zauna dake kafin mu tafi. In bai amince ba ku bar mishi abunshi" Ajjiyar zuchiya na sauke, naji sanyi a raina sosai. Tare da adda'ar Allah yasa Narani ya amince ya ɗan bar mun Daudan mu ɗan zanta" Da haka muka shirya. Na cire tsarabar da nayo ma Dauda na kwancen kaya da takalmi na riƙe. Muka kama hanyar Unguwar Marabutawa. Muna kusantar gidan ina hangoni a lokacin danai fitowar ƙarshe babu ko mayafi balle kallabi. Ina kuka, ina ambaton Ɗana kar ka raba ni da gudan jinina Narani" Abubbuwa da yawa suka shiga yi mun yawo. Bansan sanda na yar da ledar hannuna na wuya ba. Ji nayi na fasa shiga cikin wannan gidan mai ɗumbin tarihi, gidan da anan matsalata ta soma. Gidan dana zama ɗanya ina wari sabida wanka da ruwan sanyi da ɗanyan jego. Gidan da na kusan rasa hankalina tsabar damuwar ɗa namiji."
Kuka nake yi mai ciwo, irin kukan wacce ta fama wani babban gyanbon daya daɗe yana ruruwa a ƙasan zuchiyarta. Yaya Karime ce ta dafa ni.
"Haba Tani wai ke dan Allah ba kya mantuwane? Duk abunda ya faru ai ya riga da ya faru. Yanzu yaro muka zo gani, Narani bai isa ya koro mu ba, bai kuma isa hana ki ganawa ko keɓewa da ɗanki ba. Ki cije mu shiga gidannan ki ga ɗanki. Ki sani shima yana da hakki a kanki, ba kya tsoron shi yaron ya girma ya dinga tunanin kamar kin watsar dashi ne?" Numfashi naja, tabbas shima yana da hakki a kaina. Hawayena na share zuchiyata da hantar cikina nata kaɗawa haka muka shiga gidan a bisa jagorancin Yaya Karime. Sai na tuno sanda aka kawoni gidan a matsayin Amarya, su Baba marka na cewa in shiga da bismillah kuma da ƙafar dama. Duk wani taku dai dai yake da bugawar zuchiyata. Sallamar Yaya Karime ce tasa hankulan matan gidan ya karkato izuwa garemu. Na san da dama, da dama ban sansu ba, basu sanni ba. Sai dai nayi imani ba zasu gaza samun labarina ba.
"Sannun ku, mun same ku lafiya?" Cewar Yaya Karime. Kallon ƙuda muke yi ni da Ta Maulidi. Tana ganina ta datse annurin dake shimfiɗe a kan fuskarta, tsaki taja taci gaba da dakan masarar yin tuwo, wanda ya zama ta'adar gidan. Fiddausi da Ɗausiyya matan ƙannan Narani ne suka ce.
"Tani ashe rai kan ga rai, umman Dauda ashe baki mance da mu ba?" Ɗan murmushi na ƙaƙaro cike da ƙarfin hali da juriya nace."
Ba gashi yau rai ya ga rai ba. Ɗausiyya na same ku lafiya ya bayan rabuwa?"
"Sai Alkhairi Tani. Ku ƙaraso daga ciki Iya mai Fura tana ciki" Naga mun gaggaisa da kowa cikin fara'a banda Ta Maulidi wacce take ta waƙa tana shilla taɓarya tana cafewa"
"Ina wuni Ta Maulidi, na same ku lafiya?" Harara Yaya Karime ta zuga mun tace.
"In ma ba lafiya kika same su ba, meye naki?" Ai Yaya Karime na faɗar haka Tamaulidi ta soma tafi tana dukan cinya. Habaici da gori dai mun shashi, ƴaƴan mabarata. Da kyar na jaye Yaya Karime muka shiga ciki. Iya mai Fura tana zaune tana cura fura muka shiga da sallama. Idanunta ƙifi_ƙifi duk ya dame irin na tsofaffin fulani. Amman ras Iya mai Fura ta gane mu fes. Bayan mun gaisa Iya mai Fura tace.
"Tani ni na ɗauka kin haƙura da Dauda ne ai. Kin tafi babu ko waiwaye, kuma ke iyayenki fulanin tashi ne, ballantana mu mu neme ku mu kai muku shi yayi ziyara. Inno dai tana zuwa ganinshi duk randa ta shigo Shanono. Kuma ana kawo mishi saƙo, kuma ana faɗa mishi daga wajan gyatumarshi ne. Wacce Fatsumar ce a bayanki?" Yaya Karime tayi dariya tace.
"Wannan Hauwa ce ba Fatsume ba?" Baki ta turo tayi zunɗe harda kashe ido tace.
"Duk shegiyar ɗarin ce, itama tsohuwarce ita ta haifi gyatumina" Dariya muka yi dukkan mu. Tace.
"Tamaulidi ta nuna muku Daudan ne? Yanzu ma ya gama bacci a tsakar gidan fa"
A'a bamu ganshi ba" Tashi tayi tasa ƴan uwanshi nemoshi a waje. Fura ta dama ta bamu."
"Ai yana ko almajirci a can wani ƙauye mai nisa, yanzu haka ma sun kusan tafiya. Dan sauran ƴan uwan nashi ma har sun yi gaba. Sun ɗan jima a Shanono wannan karon, tun fa damuna suke, an ƙare noma abinci ya dawo gida, sai azamar komawa bakin karatu" ƙirjina naji ya doka da ƙarfi data ambaci almajirci, yanzu Daudan ne yake ɗaukar nauyin cin shi da shan shi da lafiyarshi? Bakina na rawa nace.
Ai na ɗauka yana zuwa makarantar boko, ta allon na ɗauka makarantar malam babba zai yi ai Iya?"
"E hakane, hakanne ya dace kuma. Da har ya shiga makarantar yana aji uku a firamare, sai uban yace bazai iya ba ya cireshi, sakamakon faɗuwa jarabawa da yake yi. Kinji yadda akayi, ko a ta allon fa bai da ƙoƙari ƙannenshi ma sun wuce shi, amman shi shekara guda yana wai Abasa wata wallah. An sashi a garejin ma, ogan ya hana shi zuwa baya gane komai sai shegen wasa da niman tsokana a cikin Dauda. Ga yawo" Tana cikin faɗar haka wani ɗan yaro ya shigo da yagaggun kaya, yayi futu_futu, sai jan ƙafarashi yake yi. Ga sumar kanshi daka gani kasan fulanine, amman kora ta cinye fatar kan."
"Tani kin ganshi nan ja'iri. Ga uwarka tazo dubaka" Ƙura mishi idanu nayi, ina jin motsin sonshi a dukkan jikina, wani irin so nake yi ma Dauda so irin na yaran fari, so irin na uwar data soma haihuwar ɗanta ta buɗe idanu ta ganshi a matsayin mallakinta fid duniya wal akira. Shima ni yake kallo tamfar ya sanni. Fuskarshi ta yaiwatu da fara'ar data kusan karya kuzarin dana aro na yafa. Sai nake ji kamar bazan iya tafiya in bar Dauda a cikin garin Shanono ba. Hannu na miƙa mishi.
Tawo gun ummanka Dauda" Dariya yayi har wawalonshi ya bayyana, da halama famfara ya soma. Cikin ɗingishi da yanayi na azabar ciwo ya iso gareni. Riƙe mishi hannu nayi dam. Siraran hawayene suka gangaro a idanuna. Ji nake sake rabani da Dauda a karo na biyu tamkar zare mun munfashine, ma'ana nabar doron duniya. A halin yanzu hankalina ya dawo kan Dauda, kuma inason in da so samu ne yaci gaba da rayuwa a gabana, in sashi a boko, wala Allah ko su sa samu damar cika mun burina, tunda ni aure, da yawan yara ya danne burina."
Baka da lafiya ne Dauda, na ga ka kasa zama?" Runtse idanu yayi yana ta ƙoƙarin son zama, amman ya kasa. Cikin nutsuwa na miƙar dashi tsaye na juya bayanshi, na ga jini a bayan rigarshi. Gabana ne ya yanke ya faɗi ras. Hannuna na rawa na ɗaga mishi rigar, wandonshi ma da jinin a jiki. Zuchiyata na tsalle na sa hannu zan zame wandon nashi, cike da tsoro Dauda ya riƙe mun hannuna.
"Innata da zafi karki cire mun. Kema irin abinda Alh Zangina yake yi mun zaki mun? Ciwo nake ji" Rugujewa zuchiyata take shirin yi. Cikin fitar hayyaci nace.
Ba irin abinda yake ma zan yi ma ba, gani zanyi, naga jini a wandonka" Iya mai Fura tace.
"Kaji mun ɗan baɗo, zaka cika mata hannu ko sai na buge hannun da sanda?" A firgice ya cikan hannuna. Jikina a mace na zare mai wandon ina jawo numfashi daga cikin huhuna da ƙyar. Abunda na gani ya gigitamun lissafina. Tunanina ya gurɓace. Fata_fata takashin Dauda take, ga wani irin mugun wari, ga ɗiwa, harda tsirarin tsutsotsi in ba dai haukacewa nayi ba.
Innalillahiwainnailaihilrajiun innalillahiwainnailaihilrajiun kawai nake ta faman ambato. Yaya Karime ta fashe da kuka. Ni a wannan lokacin wallahi kukan ma ƙin zuwar mun yayi.
"Tashi Tani maza mu tafi asibiti kar yaronnan ya mutu. Iya ku kuna ina wannan al'amari ya faru, ɗan mutum ya ruɓe ba ruwanku. A ruɗe Iya tana kuka tace"
"Wallahi bansan komai ba Karime Tani. Bari matar Shehulle ta fito kuje" Ba wanda ya bi ta kansu. Yaya Karime ta goya Dauda a bayanta. Ina biye dasu ina haki, ga ciki ga goyo, ga numfashina na fita da nauyi. babban Asibitin gwamnati na Shanono muka shiga. Ganin yadda Yaya Karime ta ruɗe da kuka. Ba shiri ma'aikatan jinya suka amshi Dauda suka shige dashi wani ɗaku. Mu kuma akace mu jira a waje"
MRS BUKHARI✍🏻
[10/8, 18:33] Badiat Ibrahim: NA FAƊO DAGA BENE...
NA ZARCE RIJIYA
HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI
GAWURTATTU UKU 10
*INA MIƘA DUMBIN GODIYA GA DUK ƊAUKACIN MASOYA WANNAN LITTAFIN. HAKIƘA SAƘONNINKU SUNA ZUWA GARENI. KUMA INA GANIN WAYOYINKU DAGA GARI_GARI ƘASA_ƘASA. WAƊANDA BAN SAMU DAMAR ƊAUKAR WAYOYINSU BA, SUIMUN UZIRI ABINNE DA YAWA. WAƊANDA BAN SAMU DAMAR BASU AMSOSHIN WASIƘUNSU BA, SUIMUN AFUWA SUMA DAN ALLAH. ZAN AJJIYE LINK ƊIN GROUP ƊIN LITTAFIN NA FAƊO DAGA BENE NA ZARCE RIJIYA, MAI SON KASANCEWA TARE DANI SAI YA SHIGA. KU SANI INASONKU MASOYANA A DUK INDA KUKE.*
Kaila:
wani irin farin ciki Kaila yake ciki marar musaltuwa. Tun dawowarshi da asuba, ya dawo ya samu Balkisa ta fesa ado da wata jar atampa ɗinkin riga da siket. Kayannan sun zauna mata ɗas a jikinta, kirjinta ya bayyana sosai, sai wannan hasken Amarcin irin na amaren kwana ɗaya tare da miji take yi. Kaila na ganin Bilkisa a cikin wannan ado, tuni ya mance da takaicin ganin Tani da yayi a tsakar gida. Dan bayan ya gama magana da Tani, fata yayi a ranshi dama ace Tani kar ta dawo in ta fita ta fita kenan, ko kuma ya ji labarin motarsu tayi dungure babu wanda yayi rai. Da wannan mummunan tunanin ya shigo, ganin Balkisa ya yaye mishi dukkannin cunkushewar zuchiyarshi. Tuni ya washe bakinshi tare da ware ma Bilkisa hannunshi. Da shagwaɓa ta faɗa jikin Kaila, shima ƙamshin yake zubawa kafin ya fita Masallaci sai da yayi wankan soso bayan wankan Sallah. Kan gadon suka faɗa suna dariya. Cikin so Kaila yace.
"Jina nake kamar nafi sauran maza sa'a. In ana cin ɓaure ba'a tona cikinshi Ɗanyan gwal, amman abunda zance miki shine kin sabunta mun jinina, kin sake mayar dani fresh. Dan ƙazantar su Shanono saura ƙiris ta shafe ni, ke kika ceceni. Matane gasu dai a gida, daga mai warin dauɗa da kuɗin cizo, sai mai warin baki. In Hajiyayye ta yi magana bakinta kamar shadda fa. Ke kuwa naji har yawunki ƙamshi yake yi" Dariya Bilkisa tayi na farin ciki. Ko wacce mace ta fi son mijinta a kalleta a matsayin TA FI SU, shi yasa da yawan mata basa iya takama maza burki in sun kwaso gulmar kishiya sun kawo musu. Sai dai tai ta zura miji shi kuma yana sakin layi. To ki sani yin hakan tamkar cikin ki ki ka daɓa ma wuƙa, yau ga wani gobe gareka, musamman sha'anin maza.
"Gwanda amman dai bakwa sumbatar juna in kun zo mu'amular Aure ko? Kyama har ta kama ni, ji nake uwa in yi amai" Dariyar yaudara Kaila yayi, ya gyara mata kwanciyar tata, tare da faɗin.
"Ai komai baya yiwuwa kamar yadda na faɗa miki tun kafin kizo. Ni fa duk wani soyayya da tarairayar miji a gado ban sanshi ba. Ke baki ga hakan a haɗuwarmu ta jiya ba? So fa kika yi ki buɗe mun kai" Dariya tayi mishi tace.
"Tarairaya Gwanda ai baka ga ma komai ba. Ni dai fatana shine kaci gaba da sona har izuwa ƙarshen rayuwata. Ni kuma zan baka duk wata kulawa." Nan suka shiga musayar kalaman ƙauna masu zafi, tamkar zasu koma ruwa, amman ina cikinsu na kiran ciroma, ba shiri Kaila ya miƙe dan bashi da juriyar yunwar ciki da yunwar mace.
"Bari in shiga gidan in samo mana abinda zamu ci ko?" Baki ta taɓe tace.
"To Allah yasa dai in iya ci Gwanda" Fita yayi daga ɗakin. Akan idon Hajiyayye Kaila ke ta faman jan rigarshi a ƙoƙarinshi na san dai_daita kanshi daga fitinar dake cin ƙasan ranshi. Wandon shi da yayi tudu tabi da idanunta. In da Hindatu take zaune tana wanki tabi da kallo, itama Kaila take kallo harda riƙe haɓa. Wani ƙaton malolon baƙin kishi ne ya tokare mata maƙoshi. Bata dawo daga duniyar takaici da zafin zuchiya ba, taji saukar sautin Kaila yana faɗin.
"Ina abincin karin Amarya Hajiyayye na ɗauka sassafe za'a shigar mata dashi, kinsan dole da yinwa ake wayar gari" Ji tayi muryarta ta dashe, ashar tayi niyyar lailayowa da ƙyar ta danne, taci gaba da wankin da ta tashi dashi yau.
"Ba dake nake ba Hajiyayye dan rashin son albarka shine kina jina ki kai mun kunnen uwar shegu, ko an faɗa miki ni sa'an wasanki ne?"
"Abinci dai banyi ba, kuma in sai Bilkisa taci abincina zata rayu sai dai ta mutu. Kayi haƙuri Kaila bana son ka taɓo ni in fa ba haka ba zaka ga jajjagen rashin mutunci, alo tsiya alo......." Tas ya wanketa ta wawan tafi. Da sauri ta dafe kuncinta tana mamaki, miƙewa tsaye tsaye tayi dafe da kunci. Shi kuma ya haɗe rai ya kumbura jiran ƙiris yake ya fashe.
"Ni ka mara Kaila sabida ƴar iskar Amaryarka?"
"In kika kuma kiranta ƴar iska sai na saki a cikin dana sani wallahi "
"An faɗa ƴar iska, an kuma ƴar iska" Cikin ɗaga murya da hargagi yace.
"Kije gidanku na sake ki. Tunda ke bakya ji, baki isa ki hanani sakewa da matata ba. Ki je gida kawai" Kuka Hajiyayye ta ruguje dashi. Wannan kukan sakin ya zame ma mata dole. Ko da mace ita ta nemi sakin, da zaran miji ya furta kalmar sai zuchiya tayi rawa gami da raunata. Amman dake Hajiyayye itama A ce, kuma ita tayi dai_dai da Kaila. Bai yi aune ba ta juye mai ruwan wankin da take yi a ka. Ta jiƙashi sharaf. Bilkisa da Amadudu tare suka fito a guje tsakar gidan, a sakamakon hargagin Kaila da Hajiyayye. Da mugun gudu yabi Hajiyayye jikinshi har yana ɓari. A guje ta fella bako mayafi daga ita sai doguwar riga. Kaila bai bar binta da gudu suna ratsa mutanen anguwa ba. Sai da Hajiyayye ta faɗa cikin wani gida jikinta na rawa. Yanda taga ɓacin rai a fuskar Kaila bata san me zai yi mata ba daya kamata. A ƙofar gidan ya tsaya yana cizon yatsanshi. Amadudu ne ya iso da sauri wajan, dashi da Baban Mustapha mijin Sabira, da wani dattijo maƙocinsu. Wannan dattijon ne yace.
"Haba Baban Sani, ya zaka take ka biyo mace da tsohon ciki waje, kana gudu tana gudu ko mayafi babu. Ai koma meye tayi maka bai dace ku fito titi ku fallashi kan ku ba. Ka duba yadda anguwa ta cika da mata, jibi can mata ne daga katanga suke leƙe fa" Kallon katangar da dattijon ya nuna musu suka yi. Mata uku suka gani sai leƙe suke yi. Anguwar ts soma cika da mutane. Dan da dama sun jiyo sautin muryar Kaila a lokacin da ya furta ma Hajiyayye saki. Haka dai wannan Dattijo ya taushi Kaila ba dan haka ranshi yaso ba ya bar ƙofar gidan yana ƙuta. Yana shiga gidan bai zarce ko ina ba sai banɗakinshi, dan takaicin bai gurje bakin Hajiyayye ba da ruwan sanyi yayo wanka. Yana fitowa ya kintsa, Bilkisa dai tana zaune tana kallonshi, so take ta bashi haƙuri amman tana jin tsoro. Ita yawan fara'ar Kaila da kashasshiyar muryarshi ta yaudara kawai ta sani. Sai gashi yau taji muryar cikakkun maza tattare dashi" Kai tsaye Kaila wajan mai indommie ya je. Kwai yasa aka toya mishi guda huɗu, ya sai kayan tea da ƙaton biredi ya dawo gida. A inda ya fita ya bar Bilkisa anan ya sameta a harɗe, jira yake ta amshi ledar hannunshi amman yaga ko gezau batai ba. Ba ta mishi ko sannu da zuwa ba. Amman dake amarya ance bata laifi ko ta kashe ɗan masu gida, haka ya barta.
"Ga kayan tea na siyo, ki dafa ruwa ko a kettle ne ki haɗa mana tea, akwai soyayyen ƙwai a ciki sai mu haɗa da kazar jiya" A yangance ta ɗauki ledar ta fita zuwa kitchen ɗinta na langa langa. Bata jima ba sai gata da trai a hannunta ta sako komai a kai, harda kaza mai turiri da halama ta dumamata a oven ne ko microwave, dan an danƙara mata kayan wuta iri_iri. Suna zaune suna karyawa babu mai cewa da kowa komai, sai da suka kusan kammalawa Bilkisa tace.
"Gwanda kayi haƙuri da Hajiyayye ka dawo da'ita ɗakinta, ga ciki kuma naga ƴarta ƙaramace, ɗazu ma daka fita ina jiyo kukanta a tsakar gida. In ka rabu da'ita waye zai riƙe mata yaranta" Ƙur Kaila ya mata da mayaudaran idanunshi yace.
"Tunda fa na sanar musu da batun aurenki, bata taɓa barina nayi bacci mai kyau ba. Dama fa fitinar Hajiyayye yawa ce da'ita. Ki barta kawai ta je gidan. Ala bashi in iyayenta su ka yi tunanin dawo da'ita ɗakinta shikenan." Kai Bilkisa ta gyaɗa tace.
"To shikenan ba damuwa. Abu na gaba kuma ya batun mai aiki da kayi mun alƙawarin zaka ɗauka mun washe garin ranar dana tare, kaga yau kenan. Dan gaskiya bazan iya haɗa tarairayarka da shiga kitchen ba, ga aiki in na soma zuwa. Bani ma da wannan lokacin gaskiya" Murmushi Kaila yayi yace.
"Yanzu bari in kammala karyawa sai in fita, in sha Allah da ƴar aiki zan dawo cikin gidannan. Ai ba wuya suke yi ba masu aikin. Gaskiya Ɗanyan gwal kina ji dani fa, sabida tsabar tarairayata da kike son yine kika ji girkin ma ba zaki iya yi ba." Nan dai su kak ta faman tattaunawa, daga ƙarshe Kaila ya fita, Bilkisa kuma ta koma ɗakinta. Babu abinda ta taɓa a ɗakin, kayan da su ka yi kari suna wajan, kayan da Kaila ya cire suna zube a kan gadon. Kafin azahar sai ga Kaila da ƴar aiki ya kawo ma Bilkisa. Tana harɗe a falonta tana kallo suka shigo.
"Ɗanyan gwal, wannan sabunta kwalliya haka, kai gaskiya ina morewa idona. To yanzu dai ga ƴar aiki nan na samo miki ita, sai ki faɗa mata aiyukan da zata dinga miki, da kuɗin da za'a biyata ko?" Bilkisa ta murmusa tace.
"Godiya nake ɗan maraƙin jimina gagara ɗaukar shawo. Ke me sunanki" Yarinyar tace.
"Sunana Shamwila Hajiya"
"Okey Shamwila, aikinki shine, girki duk ran girkina, wanke wanke, wankin kayana da kayan mijina duk randa yake ɗakina. Sai gyaran ɗakina da turakar mijina, sai aika haka in ya kama zan dinga yi miki. Ina ga shikenan iya aikin. Zamu dinga biyanki duk wata nera dubu bakwai. Amman fa bana son fashi in ce dai gidanku babu nisa da nan ɗin ko?" Kaila ya shiga ruɗu da mamakin yanda yaji Bilkisa ta lissafo harda gyaran turakarshi da wankin kayanshi ranar girkinta, ya soma tantamar tana da hankali kuwa? Ta ya zata sakar ma ƴar aiki girkin mijinta, da gyaran turakarshi, harma da wanki? Yarinya matashiya, mai jini a jika, kuma kyakkyawa irin haka. Shiru yayi ya ƙudurce zai taka mata burkine. Muryar Shamwila ce ta dawo dashi daga taɗin zuchin da yake ta faman yi da zuchiyarshi.
"Gaskiya ina da nisa Anty. Kuma dole sai dai in dinga tawowa da ƙafa, dan in nace kullum zan cire kuɗin abun hawa kuɗin zai ƙare, kuma ni ke kula da mahaifana da ƙannena" Shiru Bilkisa tayi tana nazari. Kaila yace.
"A wacce unguwa kike haka, sannan mahaifinki bashi da rai ne da yarinya ƙarama dake nauyin iyayenki da ƙannenki yake wuyanki?" Shamwila sai ta saka fuskar tausayi tace.
"Mahaifina yana kwance ba lafiya shekaru biyar kenan. Kuma mu masu ƙaramin ƙarfine sosai. mahaifiyata girma ya kamata. Shine nake buga _buga ina ciyar damu, danginmu dukka suna Niger mu Sadaka yalla ne, waɗanda ake mana laƙabi da muna bara muna karuwa. A layin ƴan ƙarya muke da zama can kusa da babtis." Kaila ya girgiza kan shi kawai. Balikisa tace.
"To a gida za'a barki ki dawo nan da kwana, in yaso ranakun asabar da lahadi kya dinga komawa gida? Sabida yanayin nisa, duba da cewar kuna cikin wani hali, zan baki nera dubu goma duk wata, amman zaki samu ƙarin aiki" Shamwila ta zube tana ta faman godiya. Kaila shi kuma aka barshi da mamaki.
"A ina zata dinga kwana kenan to?"
Balkisa da take magana a gadarance tace.
"A ɗakina ga falo wadatacce, Gwanda sai ta dinga kwananta a kujera ai, tunda kai kana da turaka" Kai ya jinjina yana tunanin taya kyakkyawar budurwa haka za'a turota aiki harda kwana a gidan aiki? Tsabar haushi a wajan ya fice ya barsu. Shamwila kuma ta kama aikinta ka'in da na'in. Dan a wannan rana ita ta gyare ɗakin Kaila tai ma ɗakin turaren wuta, ta wanke toilet, da kayan da suka cire. Tayi sharar tsakar gidan da wanke_wanke fes. Hindatu sai kallon ikon Allah kawai take yi. Bayan ta kammala ta tsugunna a gaban Bilkisa da take kwance tana charting da Kaila tana tambayarshi wai ina ya tafi ne tun safe?.
"Anty inaso zanje in kwaso kayana kuma in faɗa ma Ummata."
"Yauwa Shamwila dama inason zan miki aike kasuwa. Kaza nake son ki siya mun, da kayan miya, sai kayan lambu" Bilkisa ta lissafama ma Shamwila duk abinda take buƙata, ta bata kuɗin mota ɗari biyar. Ba'afi awa biyu ba, sai ga Shamwila niƙi_niƙi da boron kayanta gari guda, da ledar cefane. Bilkisa ta nuna mata bayan lungun show glass ɗinta tace sai dai ta ajjiye a nan.
"Inason ki dafa mun jallof ɗin soyayyar taliya da pepper chicken. Akwai kayan zoɓo a kitchen ki mun zoɓo mai daɗi" Nan Bilkisa ta tusa Shamwila a gaba suka shiga kitchen ta nunnuna mata abinda ya dace ta nuna mata. Anan ta bar Shamwila tana mamakin yanda aka narkama kitchen ɗin langa_langa dukiya haka, da tunane_tunane, da burika fal ranta ta shiga aikinta ka'in da na'in. Cikin ƙanƙanin lokacin gida ya soma tashin ƙamshin albasa da tafarnuwa."
SHANONO:
TANI:
Allah kawai nake ambato, naƙuda ma nake ji kamar inayi. Matan ƙannen Narani ne suka Iso, Shehulle na biye dasu faram_faram, ga Iya mai Fura itama tana tafe. Ni kuwa zuchiyata sai tsalle kawai take yi.
"Ina Daudan yake, a wanne halin yake?" Cewar Shehulle kenan cikin ɗaga murya. Yaya Karime ce ta mishi bayani, tare da nuna mishi inda aka shiga da Daudan. Ni ko hawaye kawai nake fitarwa bana ko iya ganin gabana, kaina naji yayi wani gingiringin. Wata ma'aikaciyar jinyace ta fito daga cikin ɗakin da aka shiga da Dauda. Ina gani duk suka rufu kanta, ni ko ina zaune ina haki, dishi_dishi ma nake ganinta.
"Wannan yaron bashi da iyayene, ko dai tsintarshi kuka yi. Ya yaro kamar wannan za'a bari ta kashinshi ta zazzage har ta lalace haka? Ina mahaifiyarshi take?" Take Shehulle ya nuno ni. Wani kallon tsana wannan ma'aikaciyar jinya tai mun tace.
"Ke kuwa baiwar Allah kiji tsoron Allah. Shin a matsayinki na uwa, har kin mance da rainon ciki da lauwaye_laulayanshi, shin bakiyi ƙwannafi da amai bane, ina kika mance da zafin fitar kan yaro daga jikin uwa, ina kika bar buɗuwar da kwankwaso yakeyi yaro ya faɗo. Ga raino, ga shayarwa? Kina ma yaronnan wanka ace har baki san halin da yake ciki ba, har sai da ya soma tsutsa da ɗiwa tukunna? Anya kece kika haifeshi kuwa?"
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 9 Chapter of 17