Share this page
soma aikin bayan gidan sai ki yi amfani da nawa na cikin turakata, ni kaɗai nake amfani dashi dama, zan yi gaggawar ƙarashe sabon gida, wannan da muke ciki ma inaga a kasuwa zan sa shi, kuɗin sai in ƙundume a sabon gidan, wannan sabon gidan dama dake ya dace, da ace tun farko na tuno da batun sai da wannan tsohon gidan, da yanzu ma muna sabon gida." Jin za'a tayar da salla ne yasa Kaila ya miƙe cikin kasala. "Ɗanyan gwal bari in je sallah kinji har za'a shiga Masallaci. Ga keyn turaka zaki iya komawarki can, waɗannan ledojin ki tafi dasu" Yana gama faɗar haka ya ajjiye mata keyn turaka ya fice. Da Hajiyayye yaci karo a tsakar gida, bangazarta yayi, yayi ficewarshi yana faɗin. "Aikin banza aikik wofi duk jarabarki ke baki isa kin hanani shan man Amarya ba" Nan ya barta a tsaye tana cizon yatsanta, dan data ganshi hanya ta tare mishi. Bayan sallar magriba ta kafa ta tsare tana jiran shigowar Kaila domun ta mayar mishi da martanin cizon yatsan da yasa tayi. Shinkafa da miya da nama da latas take ci. Sai taji haf door ɗin ɗakin Amarya yayi kara, juyawar da tayi tayi tazali da Bilkisa cikin wasu fararen riga da wando masu shegen kyau, kanta babu ko kallabi fuskarta sai sheƙi take faman yi. Take numfashin Hajiyayye ya nemi dakatawa, yuu daga ita har Hindatu suka bita da kallon mamaki. Far tayi da idanunta tace. "Barkan ku dai da gida" Ba ta yi maganar domun lallai sai sun bata amsaba, duba da yanayin sigar ta tayi maganar, kuma tana yi ta nufi turakar Kaila. Ɗan mabuɗi tasa ta buɗe ɗakin ta shiga. Hajiyayye bata dawo daga cikin duniyar mamaki da ruɗu ba Amaryar Kaila ta sake fitowa daga turaka ta nufi ɗakinta. "Lallai da gani wannan amarya bata da kunya, har tsakar gida bako kallabi, ace amarya daga kawoki har kin soma nuna isa da turakar miji." Ƙuta Hajiyayye tayi. Bilkisa ta sake fitowa daga ɗakinta da ƙaramin akwatinta ja na aure. Tasa kwaɗo ta datse ɗakin nata tayi shigewarta turaka. Abincin da Hajiyayye ta kasa ƙarashe ci kenan. Ajjiye kwanon tayi ta shige ɗakinta. Hajiyayye: Tunda ta shiga ta kasa zaune ta kasa tsaye. Kishi kawai ke ɗawainiya da zuchiyarta. Bata san sanda ta fashe da kukan baƙin ciki ba. Bata taɓa tunanin Kaila zai ji marmarin yin wani aure nan kusa ba. Domin a tunaninta da kuma abinda Kaila ya faɗa mata a yayin da yake kan karagar sonta cewa yayi. Tani bata iya gamsar da sha'awarshi in ya shigeta baya ko jin alama, sabida yawan haihuwa ta zama fanko maras amfani a gado. Shi yasa yake son yayi auren kece raini, kuma yana sha'awar mace wayayya wacce zata latatashi a shinfiɗa so yake a dinga lasarshi kamar alawa, kuma mai jin turanci da iya gaye yake so. Hajiyayye tayi tunanin itace mace mafi soyuwa a zuchiyar Kaila, ganin tayi dai_dai da irin macen da Kaila ke ra'ayi. Duk da cewar ita iyakarta sakandare ne kawai, amman tana ɗan jin turanci kuma tana iya mayarwa babu laifi, kana ta iya rubutun turanci, kuma tana karance_karancen littafin Hausa. Tun tana gidansu take bama Kaila dukkan kulawar da yake buƙata. Sau biyu Kaila na kwanciya da'ita a wani shagon abokinshi. Ya kuma nuna mata babu wata mace a zata iya kere mata a matsayi. Sai gashi tun kafin aje ko ina ya nuna mata kalarshi. Zama tayi a kujera tana tuno ranar da Kaila ya fara ribatarta ya jata zuwa shagon abokinshi, ranar daya rabata da darajarta kenan. Irin kalaman soyayya da irin alƙawarurrukan da Kaila yai mata a wannan ranar abun ba'a cewa komai. Kuka ta sake fashewa dashi tace. "Kaila ka cuceni. Amman wallahi bazan barka kaci amarcinnan lafiya ba, saina ja maka masifa" Wata zuchiyar tai mata gargadi da cewar. "A'a Hajiyayye kar garin kishi kije zuchiya tasa ki aikata abunda zaki zo kina ɗan daka ce baki aikata ba." Shiru tayi tana nazari. " "Tani ko tana ɗakinta kamar bata ma gidan. To wai wacce iriyar zuchiyace a ƙirjin Tani, ita bata san ciwon kanta bane ko yaya? Na tatama Tani rashin mutunci da cushen baƙin ciki iri_iri. Amman a tsakanina da'ita sai dai tayi mun murmushi kawai. Tana cikin wannan sambatun Kaila ya ɗaga labulen ɗakin nata, ya zuba mata mayaudaran idanunshi yana nazartar yanayinta. "Ni zan shiga daga ciki Hajiyayye babu wata matsala dai ko?" Ai Hajiyayye dama kamar jiranshi take ya dasa aya ta miƙe." "Ai ba sai ka zo kayi mun sallama bane zansan cewar zaka kwana da mace ba. Wanne darene jemage bai gani ba, ƙila itama ka gama shan romon amarcin nata tun daga zauren gidansu, ba girin_girin ba dai tayi mai" Idanun Kaila har ƙanƙancewa su ka yi dan ɓacin rai, ita kanta Hajiyayye data kalleshi sai da tasha jinin jikinta. Amman a zuchiyarta kuma taji sanyi sosai da taga ɓacin rai a shinfiɗe a fuskarshi. Harararshi tayi ta ƙule ƙuryar ɗakinta ta barshi riƙe da labule yana mata kallon mamaki." Dariyar mugunta yayi, bai bi ta kanta ba ya ƙule turaka wajan amaryarshi. A wannan daren Kaila ya tsunduma wata duniya iriyar duniyar da bai taɓa tsintar kanshi a ciki ba. Me yasa? Sabida wannan shine karon farko daya ɓare matarshi ta sunna dal a leda. Hajiyayye ba wai bai sameta a cikakkiyar budurwa bane, ko ɗaya. Sai dai kawai sun gudunar da kwanciyarne babu nutsuwa da kwanciyar hankali a tattare dasu. Kuma kasancewar tasu bata zama mai armashiba domun sun kauce ma shari'a( Ƙalubale a gareku ƴan mata masu miƙa ma saurayi kai tun kafin a shiga daga ciki) Duk wata hadda dake kan Kaila a wannan daren sai da Ɗanyan gwal ta kankare mishi Tani: Bayan nayi sallar isha, sai na shiga tunanin yanda zaman gidannan zai sake yi mun zafi. Amman inason da zaran Allah ya saukeni lafiya in tashi tsaye domun cikar burina. Duk da nasan fitowar burina ka iya haifar da matsaloli masu tarin yawan da ni kaina bansan su ba. Amman gani nake yi muddin naci gaba da rayuwa a haka haƙiƙa baƙin ciki da damuwar gidan Kaila ce zata zame mun ajalina. Kaila ya mayar dani tamkar wata jakkar gidansu. Dangin Baba Rammai babu mai ganina da kima, Hajiyayye wanne irin baƙin cikine bata cusa mun ba, ga Amarya kuma bansan ita da wanne salon tazo ba. Ni duk wannan fafutukar inayi ne domin yarana, bana fatan abinda zai sa in tsallake in barsu, nasan babu mai iya kularmun dasu, ƙarshe gararamba zasu ci gaba dayi a anguwa kawai. Wayata ce tayi ƙara ta katsemun tunanina. Yaya Use ke kirana, nayi mamakin kiran duk da dai dare bai yi sosai ba, goman dare ne. Assalamu alaikum Yaya Use kece da daddarennan haka, Allah yasa dai lafiya?" Dariya Yaya Use tayi daga ɓangarenta tace. "Babu komai. Inno ce tace in sanar miki gobe zamu tafi ashe ba jibin ba. Tace kizo da sassafe, mun samu mota har gida. Lauwali maƙocinmu direban bektira ɗinnan motarshi zamu bi har Shanono in sha Allah. Yayi mana sauƙi sosai, sai ki soma shiri tun yanzu sai da safe" Sallama tayi mun ta datse wayarta babu shiri na miƙe na shiga zaƙulo kaya. Kayan da Habiba Bala ta bani na ciri kala uku na saka a jaka. Sai lokacin na jawo ledar data rarraba mana a wajan taron. Sabulan wanki dana wanka ne a ciki, sai omon wanki, da turaren wuta, da humra, harda turaren ɗaki na fesawa da ƙaton basilin. Murmushi nayi na jinjina kaina lallai Habiba Bala akwaita da kirki. Kayana dana Hauwa na haɗa tsab, na ware mana wanda zamu saka in zamu tafi, a lokacin wani bacci mai nauyi yayi gaba dani, bani na farka ba sai asuba. Fitowa nayi ina hamma gefe_gefen bakina duk yawun bacci, idanuna kuwa cike da kwantsa bana ko iya buɗe idon sosai. Banɗaki na faɗa na kama ruwa na fito. Ina tsakar gida ina alwala Kaila ya fito da sauri ya fita zuwa Masallaci. Ina gama alwalar na shige ɗaki nayi sallah, na fito na hura wuta dan in ɗaura ruwan wanka. Hindatu ma ta fito tana bakin rijiya tana jan ruwa. Kaila ne ya shigo gidan, boll yayi da butar da nayi alwala na barta a kan hanya. Taje ta haɗu da garu ta fashe, da ido nabi butar, sannan na dawo da kallona wajan Kaila Wanda shima ni yake kallo rai a ɗaure, ni kuwa ko a jikina. Ina kwana Kaila, an tashi lafiya, ya kwanan baƙuwa?" Jin na ambaci kwanan baƙuwane yasa Kaila ɗan sakin fuska har ya iya tsayawa muka gaisa. Dama inason in roƙi alfarma, amman ban samu ganinka irin haka ba sai yau" Sai nayi shiru. "Ina jinki mana Shanono ki faɗi abunda kikeson faɗa, na bar ƴar mutane ita kaɗai a ɗaki" Shanono dama zamu je dasu Inno biki. Kuma yau zamu tafi shine nake neman izininka" "Ba Shanono zaku ba, ko bangon duniya zaku je shanono ƙofa a buɗe take, duk inda kike son zuwa ba sai kin tambayeni ba kije abunki" Yana kaiwa nan ya wuce ya barni da sakakken baki. To me Kaila yake nufi dani ne, duk inda nake son zuwa in yi tafiyata ba sai na tambaya ba, sai kace wacce take zaman kanta?" Kai na gyaɗa kawai na juye ruwan wankana a bokiti, a gurguje na ɗan diddirza jikina na watsa ruwa na fito. Hauwa nayi ma wanka na shiryata tsab. Har Yaya Use ta soma kiran wayata. A gurguje na saka kaya na fito da jakar kayana da jakar mata ta zuwa anguwa. Ɗakina na rufe na shiga cikin gidan nai ma Hindatu sallama, na bata sallahun faɗama Hajiyayye in ta fito. Gidan Sabira ma a tsaitsaye na shiga nayi sallama da yaran, na ba Sabira key ɗin ɗakina na nufi gida. Na isa gida na samu har sun shisshiga mota, Baffa yana daga ƙofar shiga gaba dafe da Habu sai faɗa yake yi. "In dai Tani ce kun santa da shauni, Inno shi yasa nace muku aba Lauwali haƙuri ya kaimu gidan nata mu ɗakkota acan." Inno tace. "To Baffa faɗan ya ƙare ga Tanin nan ta iso sai mu tafi, kai kuma Lauwali kayi haƙuri kasan sha'anin lafiya da mata" Shiga motar nayi, Baffa ma ya shiga gidan gaba shi da Habu. Sai da mota ta soma tafiya sannan muka gaggaisa, Baffa yace. "Abokan nawa suna gida, na ɗauka zaki riƙo hannun Inno ƙarama a tafi da'ita." Dariya nayi nace. Suna gida Baffa na barsu, ita kanta Hauwa dan dai babu mai riƙe mun ita ne da har da ita zan bari." Muna tafe munata taɓa hirar ta zumunci. Hakan ya tuno mun lokacin da muka yo ƙaura daga garin kogi zuwa Ibadan, a lokacin mabaratan koji basu fiye samun kuɗi ba, manyan mabarata daga cikinsu suka zauna domun neman mafita irin su Baffa dan Baffa na ɗaya daga cikin manyan mabarata masu ƙarfin iko. Kasancewar daɗewarshi a bara da gogayya da yarika iri_iri. Allah sarki rayuwa, mun sha yawo gari_gari yawon bara, hakanne yasa babu wacce a cikin mu tayi ilimin addini, mun dai samu na sallah a wata makarantar almajirai, muna jin yaruka da dama, domin duk garin da muka je da irin harshensu muke bara, ko da dai ba zamu iya doguwar hira da yaren ba, zamu iya roƙonsu. Kuma waɗanda ba musulmai ba sun fi ƙoƙari wajan bada manyan kuɗi ma mabarata fiye da Musulmai. Sai kaga Alh ya tsaya a ƙatuwar motarshi, mabarata sun rufeshi ana mai bara. Amman bazai wuce ya raba sababbin nera ashirin_ashirin ba, masu ƙoƙarin ciki suke raba hamsin_hamsin. Haka ƙwaƙwalwata tai ta yawo dani a cikin labarina, wani abun inna tuno in yi ƙwal_ƙwal, wani abun inna tuno na yi murmushi, wani kuma babu yabo babu fallasa. Motarmu tai ta lulawa, misalin sha biyun rana muka ɗan dakata a wani ƙauyen da bansan sunanshi ba. Baffa ya sai mana abinci. Shinkafa garau_garau ce ya siya mana akan wani ɗan tallah. An yi mata zubin ɗari_ɗari, kowa ya ɗauki ƙwano ɗaya. Wata rumfa muka nufa anan muka yi zaman dirshan. Hauwa na sakko daga baya, sai da ta ƙoshi sannan na ci abincin na bi da ruwan leda guda ɗaya. Inno tace. "Baffa ni kam zan kama ruwa, kaga Shanono daga nan da tafiya sosai, gara in rage marata, Indo muje ki rakani mu nemi wajan ciyayi haka sai in yi." Ai Inno na faɗin haka duk muka miƙe ko wacce da guntun fitsarinta ga mararta. Wani gida muka samu daga bayan wasu rumfuna, a gidan muka kama ruwan, sannan muka shiga mota, bamu tsaya a ko inaba sai a Shanono. Idanu na lumshe na shiga tuno irin rayuwar auren dana gudanar a shanono, duk su ka dinga dawomin. Tuno da Dauda ɗana ne yasa na ɗan saki ajjiyar zuchiya. Baffa ne ya katse mun tunanina da cewa. "Inno acan gida zamu sauka, jiya ina wajan bara Jafaru ya kirani, nace ya buɗe ɗaki ya ƙyara mana. In yaso ko zuwa yamma ai sai ku kintsa kuje gidan Deluwan ko?" Inno tace. "Tunda ka yanke hukunci ai shikenan Baffa. Amman ni kam ai so samuna daga nan sai gidan Deluwa, ana can anata sha'anin biki ka sani. Tun shekaran jiya ya kamata ace na iso garinnan fa haba Baffa" Da ihu_ihu Baffa yake magana kamar faɗa irin na makafi, sake ƙwalla muryar tashi yayi yace. "Da wannan tulin tsarabar kike son ki je gidan biki, shingin duk abi a sace, bazai yiwu ba. Use nuna mishi hanya kinji mu je unguwar Shakogi." Yaya Use tace. "To Baffa. Lauwali kwana zaka yi, ka miƙe har gaba da ceɗiyar can. Kana yin kwana gidan kenan"........ Mrs Bukhari ce Sai Allah ya sadamu ni da ku ranar Monday. Bana posting ranar asabar da lahadi [10/8, 18:33] Badiat Ibrahim: NA FAƊO DAGA BENE.... NA ZARCE RIJIYA HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU 9 Asalin garin Shanono. Fulanine na usil waɗanda sukai fice ta ɓangaren noma da kiwo. Suna da mata kyawawa ga gashi sosai, kuma ba ƙauye bane irin ƙayau ɗinnan ba, dan suna da kwalta, akwai ruwan, suna da lantarki, asibitoci, kana suna da makarantu masu dama, kuma yara suna zuwa makaranta ba kamar sauran ƙauyuka da muka ji su a baya ba. (Ƙaramar hukumar shanono) an kafa garin shanono zuwa ga sanannun ƴan uwa biyu. Jaukere da shanu, waɗannan ƴan uwa biyun. Suna zuwa ƙasar domin yin kiwo, ana kuma kyautata zaton sun fito ne daga garin Hadejiya dake jihar jigawan dutse a yanzu. Ganin cewa ƙasar tana da tile kuma tana da kyau ga dabbobinsu suna kiwo manyansu sun zauna a wurin a ƙalla shekara ɗaya kafin su ci gaba, amma da lura da yanayin yankin daya dace, sai suka yanke shawarar ci gaba da zama a wurin tare da dabbobin nasu. Bayan samun wurin da ya fi dacewa sai SHANU ya yanke shawarar komawa baya kaɗan don gabatar da garin Shanono ya bar JAULERE ɗan uwansa a wurin. (JAULERE TA YANZU) ya zo ya kafa aikin sa (riga) a garin shanono na yanzu har zuwa yanzu Rijiyar taushe a shanono. Garin a halin yanzu ana ganinsa a zahiri. Ga jerin mutane da sarakunan da su ka milki Shanono. Kabiru isyaku ( ɗan shanono na yanzu dakaci shanono) akwai Hakimi. Tun da Shanono ta zama ƙaramar hukuma suka fita daga ƙaramar hukumar Gwarzo a 1989 sunansa Alhaji Bello Abubakar kambun bunun Kano daga 2004 zuwa yanzu. Shanono na da yanki na 697 km2 da yawan jama'a ² a ƙidayar 2006. Lambar gidan waya na yankin ita ce 704(1) manyan mutanen garin sun haɗa da marigayi Alhaji Ibrahim aka Ibrahim ( ɗan kasuwa) Marigayi Alhaji Barau (Ɗan kasuwa) Marigayi Alhaji Haruna Muhammad Shanono. Mariga Alhaji Bawa Mashin (Man0mi) marigayi Ɗan Anni ( Ɗan siyasa) marigayi Alhaji Haruna Naganga ( cocas chairman) marigayi Alhaji Shehu Shanono. Farfesa Nura ( masan kwamfuta) dandalin matasa na shanono ( ƙungiyar ci gaba) da dai sauran fitattu a Shanono da lokaci bazai bani damar jero su ba. Shanono: A daidai ƙofar gidan su Baffa Lauwali ya tsaida motarshi. Ai kuwa Baffa Jafaru, da Baffa Yusuf suna gano mu suka miƙe daga kan kututturen da suke zaune, suna shan iska a kasan bishiyar durumi. Rana ake kwanɗawa sosai da sosai, matasa gasu nan daba_daba sunata afkin fira, kasancewar da rani ne, babu noma sai kiwo." " Naroro, Inno kune da tsakar rana haka, maraba da baƙin birrni. Use, Karime, Tani, Habu, Indo. Sannunku da hanya. Babban direba sannu" Da murmushi a fuskata nace. Barka da gida Baffa Jafaru da Baffa Yusuf." Baffa yace. "Kuna gida baku je aikin hatsi ba Jafaru, ko su Tanimu kuka tura?" Inno tace. "Lauwali mu je ciki kaci abinci, in kayi sallah Allah bashi sai ka kama hanya. Jafaru muna da kaya a mota ku shigo mana dashi ku da su Use." Inno tayi shigewarta ciki, tana ta cogala ƙafarta. Tausayi ta bani dan ƙasar da zafi sosai, gashi ko takalmi babu a ƙafar Inno. Allah ya hore mini in sai ma Inno keke ta huta da zafin rana, ko sanda." Da tulin kaya muka shiga babban gidan mai yalwar filin tsakar gida da yalwar matan gida da yaran gida. Dan Baffa su rai ashirin cib mahaifinsu ya haifa malam Jauro Ja'e. Kuma a cikin ƴaƴa ashirin ɗinnan macen su ɗaya ce itace Goggo Ige. ( Hausawa na kiran sunan Ige ne ga macen da ta biyo maza zuryan) "Ah Inno maraba lale kune da rana haka, an tawo biki ko? Tani ashe ƙafafuwanki zasu sake taka ƙasar garin Shanono idanunki kenan?" Inji Baba mai riga matar Baffa Jafaru, mace mai faram_faram da son zumunci kenan. Dan duk da yawan yawonmu baisa ta dena ziyartarmu a duk garin da muka ya da zango ba. Ɗakinta ma ta ja mu baki ɗayanmu. Baffa kuma su Baffa Jafaru suka janyeshi shi da Lauwali. Bayan mun zauna mun sha ruwa. Nan fa ɗakin Baba mai riga ya cika maƙil da matan ƙannen Baffa, da sabbin idandunan da ban sansu ba, da yara rututu. Gaisuwa da taɗin yaushe gamo yaƙi ƙarewa. Da ƙyar muka yakice mu ka rama sallah. Baba mai riga ta saukemu da kwaɗon ganyen dimkin yaji albasa da ƙuli. Baba Marka ta kawo mana damammiyar fura da nono wacce ta ji zuma. Kowa ya bar gida gida ya barshi. Haƙiƙa garin Shanono garine mai tsaiwa a rai sosai. Suna da son zumunci, da son taimako. Kuma bugu da ƙari kusan kowa ɗan uwan kowane a Shanono. Inno tace. "Oh Marka ni ko banga matar Katagi ba, shi kanshi Katagin ban ganshi ba" Ɗan dariya Baba marka tayi tace. "Wannan yaron ai yana legas da iyalin nashi, ya samu aiki a wani babban gidan abinci. Shekararshi guda da tafiya, wallahi dawowarshi gida na uku, sai Baffansu ya bashi shawarar ya tafi da ita iyalin nashi." Kasancewarshi Ɗan fari a wajanta yasa tai mishi alkunya da wannan yaron, kamar yadda yazo a al'adar malam bahaushe. Hausawan zamanin da an sansu da yakana da kunya, haɗe da kawaici da kara. Amman kwaikwayon al'adun wasu ne yasa tamu al'adun suka samu tawaya, daga wannan lokacin mace macen aure yayi yawa a ƙasar Hausa. Gabana ya yanke ya faɗi da jin an ambaci Katagi. Katagi ya nuna kwaɗayin aurena a fili, ni kuma Allah yana gani tsanar da naima Narani ce ta shafi Katagi, da tuno da Kaila da nayi, da irin kulawar da Kaila yake bani a dai_dai wannan lokacin muna matsayin saurayi da budurwa kuma a lokacin soyayyarmu da Kaila tayi zurfin da bazan iya juya mishi baya ba, kuma ina jin maganarshi fiye da maganar kowa a duniyata. Allah yayi Kaila mutum ne shi mai daɗin baki da iya tsara zance. Daga baya ne na gane ashe tantirin gogaggen mayaudarine. Gashi da iya ɗaukar wanka aljihu babu ko sisi. ( Wannan kuma ɗabi'ace ta samarin Jos. Allah yayi da dama a cikinsu mayaudara masu iya layancewa. Bugu da ƙari akwai iya wanka ba ko tasi a aljihu. A jos ne zaku ga gaye iya gaye, yayi wanka iya wanka, amman yana kan titin salisu Adamu yana tafe ɗai_ɗai kamar bazai taka ƙasa ba. Jasawa ayi haƙuri nima ƴar Jos ce na rayu a Jos sama da shekaru ashirin, nasan komai ). Muryar Baba mai riga ce ta katseni. "Uhm Inno ai Katagi ya zama babban mutum, gonakin shi a shanono ai sunyi goma. Kuma duk nomesu yake yi tsab, irin wannan yanayi na rani yake fitar da abincinshi cikin garin Kano. Yananan yana ɗanɗasa gida a gaba dasu Tabawa kaɗan. Kuma yaron gashi da zuchiyar yi, in ya tashi yo aikennan baki gani ba, baya mancewa da kab iyayen nashi. Yama kusan ƙarin aure, mai Anguwar anguwar gabanmu ya bashi babbar ƴarshi." Ni dai nayi tsumu_tsumu dani. Su kai ta rabtako zancen Katagi da irin samunshi. Baba Marka ce tace. "Tani ai ko Dauda yana yawan zuwa gidannan. Su Tasi'u ne abokan wasan nashi. Kinsan Narani ya sashi a gareji, to garejin nasu yana nan anguwar. Amman an kwana biyu baya zuwa wallahi. In ce dai zaki daure ki mance da duk abinda ya faru kije ki ga ɗanki ko shima zaiji daɗi? Tani rayuwar haƙuri akeyi, wallahi duk wacce kike ganinta a cikin ɗakin aure. Imma babba ko yarinyar mace, zaman bazai yiwu mata ba madamar batai haƙuri ba. Yara_yaran cikin gidannan da suka ɗaɗɗauko mata. Kusan rabinsu da kwata du sun yi saki, sakin fa a cikin ƙabilar Hausawa ya zame ma mazan kamar wani ado. Face maza na gari da suka kasance sun san abinda suke yi. Kuma ba rashin addini ba, ba rashin kyawawan al'aduba, face watsi da mu kai da koyarwar Arrasul Sallallahu alaihi Wasallama, mu kasa ƙafa muka shure al'adunmu, muke hanyen turawa da mutanen kudu waɗanda addini da al'adarmu suka banbanta. Mu da ƙabilar Hausawa bamu san wani yawan mutuwar aure ba. Sai kiga mace sama da shekaru saba'in tana tare da mijinta na lalle. Ta ba gamu ba mun doshi shekaru sittin a ɗakin aure, ɗuwawu duk ya dame da kashi, amman anata bugawa dai. Ke mu fa a al'adar malam bahaushen da, ko anguwa bama fita da rana. Da asussuba muke fita, sai dare ya rufa muke dawowa. Ko kuma mu fita da daddare. Sabida kunya, da killace mace irin na malam bahaushen da, ba irin na yanzu ba." Take kawaye ya soma shatata a kumatuna. Sufa duk a ganinsu, nice nake ƙure duk mazajen da nake aure har take kaimu ga macewar Auren. Da an magana suce mace tayi haƙuri. Sai hawan jini ko ciwon zuchiya ya rabketa ta mutu suce Allah yayi, kwananta ne ya ƙare. Alhalin baƙin ciki ne yai sanadin katse mata numfashinta. Wani sa'in macen ma nason ta zauna a gidan nata duk rintsi duk wuya, amman mazajen basaso, duk hakkinta daya gama ɗauka, da gallaza mata daya dinga yi, bazai isheshiba hakan, sai yayi mata tukuicin saki, wata ma harda tagonashin duka, ko karɓe yaro, irin yadda Narani yayi mun akan Dauda. Inno tace." "Kune iyayen nata ku dai sake faɗa mata. Dan ubanta ya lashi takobi a wannan karon in ta kaso aurenta, to ba dai gidanshi ba, ba dai Shanono ba. Kuma ita tasan waye Baffa, shi a makafin ma kafiyarshi irin ta kutarece, ga mitar tsiya. Dan a yanzu haka nasan Tani bata ƙi wannan auren ya kuma turguɗewa ba. Kullum tazo gida da abinda zata ƙirƙiro ta faɗa. Sai da uban wata rana data tawo raɓe_raɓe da ciki da goyo wai tayo yaji. Wallahi dukan da Baffa yayi mata ban zaci yarinyarnan gata ba zata haihu a take a wajan ba dan tsabar duka. To da taji fa babu daɗine shine ta dena ƙorafi shekara uku kenan. Sai dai kullum a rame kamar ita ake yanka ana miya" Kuka nake rerawa mai fitar da amon muzanta da tozarta. Jina nake wata ta daban a cikin ƴan uwana mata. Dangi duk sun bugamun hatimin rashin zaman aure. Wasu ma suna kirana da mai auren sha'awa. Wasu suce mun mai ruwan ido. Sunaye maras daɗi dai. Akuyata ta riga da tayi kuka a cikin dangi. Nina kafe tarihin aure biyar, bana fatan wata ta kafa irin tarihina." Baba Marka

Chapter 8 of 17