Share this page
ganina a matsayin wanda ya gaza wajan baku tarbiyya? Jibi abinda Rabi ta aikata itama fa. Kinci sa'a ke uwatace wallahi da sai na dakaki a cikin ɗakinnan tunda baki da hankali. Ke baki rasa ci ba, baki rasa sha ba, baki rasa suturaba da an taɓo ku ku dawo mana gida, alhalin iyayenki duk sun rasa abinda ke baki rasa ba a naki gidan mijin. Matar Bahaushe kenan, ire_irenku ke sa adadin yawan zawarawa yake sake hauhawa a ƙasar Hausa, da gangan ake ɗaura mana laifin kacokam, ai in ɓera da sata daddawa da warinta. in zaki bi mijinki ki bi mijinki, kin ganni nan aure zan ƙaro ni kaina nan da sati biyu masu zuwa, kuma yarinyace bata shige sa'arki ba. Yaushe za'aita zama da tsofaffin guzuma bayan Allah ya bamu damar da zamu more rayuwarmu." Ta inda mahaifin Hajiyayye ya shiga ba ta nan yake shiga ba. Shi ba kuɗi ba, sana'ar tashi ba wata ta kawo makudan kuɗi ba amman yana maganar cikace mata ta huɗu. Matanshi uku, yara kuwa sunfi ashirin, shagon siyar da gwanjo na yara yake dashi a kasuwar gwanjo dake katako. Yanayin sana'ar tasu hawa da sauka ne. Haka su Hajiyayye suka taso babu yabo babu fallasa, abincin da zasu ci wani sa'in sau biyu kacal yake iya ciyar da iyalanshi, na ukun sai dai iyayen su yi buga bugarsu a ƙuƙuta aci. Ko makaranta yaran da dama iyayensu mata su suka ɗau ɗawainiyar makarantar yaran nasu. Matsalolin yau daban na gobe daban. Amman a hakan yake neman yayo ƙarin Aure da ƙaramar yarinya sa'ar Hajiyayye. Mahaifin Hajiyayye yana ɗaya daga cikin mazan ƙabilar Hausa masu cisgunawa matansu da yaransu. Dalilina kuwa shine, ƙarfin samunshi bai wuce na mata ɗaya da ɗan yara ƙalilan ba. Kuma shima yasan da haka, amman dake babu sunnar da Hausawa suka fi ɗabbakawa sama data ƙarin aure a hayayyafa dan manzon Allah yai alfahari dasu ranar ƙiyama. Fahimtarsu ce ba dai_dai ba. Domin babu a inda akace a haifi yaran iska, a kasa basu tarbiyyar islama kuma ayi tunanin wai wannan yaron zai zama abun alfahiri ranar ƙiyama. Ai ko ku da kuke iyayenshi ba za kuy aifahari dashi ba. Sannan babu a inda akace sai an auri mata biyu, uku, huɗu dole, akwai mazan da auren ma ya sauka a kansu baki ɗayanshi. In kana da halin ɗaukar nauyin lalurorin mata huɗu da yaransu, kuma kana da lafiyar jiki da zaka dinga iya biyan buƙatunsu, kana da dukiyar da zaka ɗauki nauyin karatu da tarbiyyar yaranka, zaka kwatanta adalci a tsakaninsu. Alh ai baka da matsala sai kayi mata huɗu abinka. Gargadi muddin kasan baka da wannan halin to maganin kar ayi kar a soma, ko dan gudun haifar ƴaƴan iska masu addabar anguwa da sace_sace da harkar daba, fyaɗe, da sauran gurɓatattun abubbuwa. In kunne ya ji jikinmu ya tsira. Haka mahaifin Hajiyayye yay mata tas, sai kukan baƙin ciki take yi. Tafiya su kay suka barta a cikin damuwa da tashin hankali. Rana zafi inuwa ƙuna. Gida ba daɗi, iyayenta haƙuri su ke yi da Babansu. Gidan Auren ma babu daɗi Kaila ya ƙaro samfurin rashin mutunci. Tana zaune dirshan a tsakiyar ɗakinta ta jiyo dirin shigowar lifan ɗin Kaila. Da harara tabishi ta labule ba dan tana ganinshi ba. A cikin kunnuwanta take jiyo oyoyon da Kaila ke ma Bilkisa, itama tana mishi oyoyon cikin muryar kirsa irin tamu ta mata. Yatsa Hajiyayye ta ciza. Tana ta jiran shigowar Kaila yau zai shigo, gobe ne, ko jibi. Har bayan isha bata jiyoshi ba. Ba shiri ta miƙe da cikinta a gaba ta nufi turakar Kaila. Kaila: Shi kuma Kaila a dai_dai wannan lokacin yana zaune Bilkisa na bashi abinci a baki. Sai washe mata baki yake yi. Yana shigowa gidan ta jashi bayan gidan ɗakinshi, dama tasa Shamwila ta haɗa mai ruwan wanka. Yana fitowa ya wuce masallaci, bai shigo ba sai da akayi isha. "Amman Ɗanyan gwal yarinyar ta iya abinci babu laifi. Ni tunda nake ban ma taɓa cin soyayyar taliya ba, ga kazar ta ɗau maggi da tafarnuwa." Murmushi kawai tayi mishi tace. "Nima da na ci abincin na yaba mata. Kaga bani da wata fargaba ko ran girgikina in na samu aikin kwana, Shamwila zata yi maka duk abinda ya dace, ba tare da na shiga hakkin abokan zamana na ɗaura musu hakkin da ba nasu ba." Dariya yayi yace. " Ƙwarai ma da gaske, Shamwila za tai mun komai da komai daya dace. Da kike maganar ɗaura hakki, ai Shanono ce kaɗai zata iya yarda tayi wannan aiki ko ba ranar kwananta ba. Hajiyayye ai baza ta taɓa yarda ma tayi ba. Wannan da kike ganinta ƙwayar boris ce zafi gareta fa sosai." "E babu shakka an zauna ana kwance mun zani a gaban kishiya. Tur da kai Kaila wallahi . " Suka jiyo saukar muryar Hajiyayye a kansu, sai jijjiga take faman yi, basu ji shigowar tata ba ma. Kaila yace "Zaki fita a ɗakinnan ko sai na turaki gidan tsoho kin je kin ɗan ja koriyar miya ne? Nifa shi yasa naso a barki a gida, ko nima na huta amman mahaifinki ya dinga mun magiya darajarshi na duba har kika ganki a tsaye a kanmu" Hajiyayye tsabar kunya sai taji kamar ƙasa ta tsage ta faɗa. Masu iya magana na cewa, in baki yasan me zai furta, bai san me za'a mayar mishi ba. Jibi yanda Kaila ya tsinkata a gaban kishiya yana jifanta da kalaman da zasu zubar mata da mutuncinta. Cikin borin kunya ta ɗaura hannunta a bakinta ta shiga yi mishi ele. "Woooo woooo wooo kaji kunya Kaila kaji kunya. Yarinyar da na yi imani sai da ka gama zakuɗa hannunka cikin ramar kayi kwaɗo kafin ka kawota cikin gidan kamar yadda nima kayi mi...." A mugun fusace Kaila ya dakatar da'ita da cewa. "Ƙarashe kalmar da kike son fesarwa dai_dai yake da saki Hajiyayye. Baki da hankali ne, ni zaki ci ma mutunci a gaban iyalina?"........✍🏻 NA FADO DAGA BENE.... NA ZARCE RIJIYA HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU 8 _*AMMA ARAB!AMMA ARAB!!AMMA ARAB!!!*_ _kai daga jin sunan kasan sunan ya amsa sunansa,AMMA ARAB ta kawo muku wani supplement na gyaran jiki mai sanya daɗi da ƙamshi AMMA ARAB gidan ƙamshi_ *MUSUK* *MADARAR TURARE* *KAJIJI* *ROT* *SANDAL* *HUMFUR* *SANDAL FLASK* *SANDAL WUD* *AALUT* *GAF-GAF* *JANNAMI* *ƘWALAKCA* *MAHAHABSUFYAN* *WANNAN SHINE GRP ƊINA NA WHATSAPP,KI ANTAYO SABODA KADA AYI BABU KE* 👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 https://chat.whatsapp.com/BrUXmBHnDN6KUJYnkBDT7S *ADDRESS👇🏻👇🏻👇🏻* Zaria road kwankwasiyya sabon gari dangwauro house number 224 *AƘWAI WANI SUPPLEMENTA NA GYARAN JIKI DA TAZO MUKU DASHI KE DA KANKI IDAN KIKA YI ZAKISAN EH LALLAI ZAKI GIGITA ME GIDA,KINSAN MAZA SAI DA ƘAMSHI DUK MATAR DA BATA SAYI WANNAN SUPPLEMENT ƊIN BA TO AN BARTA A BAYA* *AƘWAI BABBAN MAGANI NA INFECTION,WANDA ZAI DAWO MIKI DA MARTABARKI NA ƳA MACE,ZAI CIKO MIKI DA NI'IMARKI KI KOMA ƳAR GATAN MEGIDA* *AƘWAI BABBAR KAMBASA,TA TURARA KAYA HAJIYA KI BUƊE BAKIN ALJIHU KI JIƘO DA ƘAMSHI,KINA ZAMA AN SAN KIN ISA MACE HAJIYA DON AMMA ARAB TA SHARA SOSAI WAJEN KAWO MUKU KAYAN GYARA NA MATA* *AƘWAI SABULAN GYARAN JIKI SUNE KAMAR* *MULATO SOAP* *FACE CREAM* *FACE SOAP* *MULATO WHITENING LOTION* *HAIR GROW OIL* *HAIR GROW CREAM* *KAR-KAR OIL* *MINT LEAVE OIL* *ANTI PIMPUS SOAP* *AƘWAI SABULUN NANKARWA* sannan ina harkar👇🏻👇🏻👇🏻👇🏻 *ABIN BUKI* *ABINCIN OFFICE* *SNACK* KAMARSU👇🏻👇🏻 *WAINAR MASA* *SINASIR* *MEAT PIE* *CINCIN ƊAN LAUSHI* *CUP CAKE* DA DAI SAURANSU. AMMA ARAB GIDAN GYARAN AURE😄👏🏻 Hatta inifom mijin Sabira ne ya ɗinga musu, da basa zuwa ko ina sai gararamba a unguwa. Haka zalika shi ya sanyasu a islamiyya irin ta cikin anguwa, duk sati suna tafiya da nera hamsin, shima wannan ko da Kaila yaga suna zuwa bai ce dani komai ba, nima ban tanka mishi ba. Ajjiyar zuchiya na sauke na dubi Sabira a karo na barkatai nace. To zan bar miki su, zan haɗo inifom ɗinsu Sani zai kawo miki. Zaki sha bari_bari kenan bakin ki sai yayi tsini ashe kafin in dawo. Dariya tayi tace. "Su Mustapha da Umar fa da kike ganinsu wallahi sun fi Shafi'i da Sulaiman rigima, Sani shi bai da yawan ƙiriniya magana ma bata isheshi ba. Kullum a cikin raba dambe nake." Hmm suma ko da yaushe aikin Kenan." Mun jima muna tattaunawa kafin muka fita domun ɗora girkin rana. Ƴan Wudil kam har sun fito tsab zasu koma, ƴan Akwanga suma ina ji suna cewa da sun yi azahar zasu tafi. Sallama nayi ma ƴan Wudil, muka shiga hidimar abincin rana. Girkin dangin Amarya daban Sabira tayi shi. Tuwon shinkafa miyar ganye tayi musu da kaji. Ita tayi komai da komai, kuma ta ɗauka ta kai musu. Bata jima ba ta fito. Ƴan Akwanga suna cin abinci suma suka kama gabansu, harda Baba Rammai dan an bogo waya an yi musu haihuwa. Sabira da Hindatu ne suka yi wanke wanke da gyaran gidan. Fes suka wanke tsakar gidan yayi kyau sosai. Misalin huɗun yamma muna tsakar gidan ina ɗaura sanwar miyar dare. Sai ga dangin Amarya su biyu, sun sa Amarya a tsakiya. Suna zuwa in da muke suka tsaya. "Bayin Allah muna neman ɗakin uwar gidan gidanne, zamu kai amarya bisa doron al'ada." Sabira ce tayi musu jagora zuwa ɗakina ta nuna musu taburma. Ni kuma na kirawo Hajiyayye da Hindatu, tare muka shiga ɗakin, na shiga na same su sai yamutse fuska suke yi, ba shakka zarni ne ya ishesu. Bayan an yi ƴan gaishe_gaishe wata farar mata tace. "Wacece uwar gidanne a cikinku?" Hindatu ce ta nuna ni tana dariyar ƙeta, ta nuna Hajiyayye a matsayin ta tsakiya. Baki suka sake su kansu, ƙila sun yi tunanin mai aikin gidan Kaila ce ni, dan sun gagganni face_face ina shan uban aiki kamar jakka tun zuwansu." "To uwar gida kece babba ga Bilkisa mun kawota domun ku gana, ba Domin mun kawo muku amanarta ba, amanarta na hannun wanda ya rabota da garinta da ahalinta. Bilkisa ki buɗe fuskarki abokan zamanki su ganki ki gansu" Bilkisa tana saye da wata lafaya mai adon duwatsu faca_faca hannu tasa tayi baya da mayafin. Wallahi bani ba hatta Hajiyayye da take jin ita shahararriyace sai da ta ƙware. Bilkisa gaskiya tana cikin sahun kyawawan matan hausa fulani, uwa uba gata da haske sosai, ga iya kwalliya da zabin kalar daya dace da launin fatarta. "Ina yininku Anty da Anty?" Wani ƙwallon kishi na haɗiye nace. Lafiya lau Amarya Bilkisa ya baƙunta?" Murmushi kawai tayi mun bata ce komai ba. Iyakar abinda ya faru kenan, sai shaida mana cewar yanzu zasu tafi da suka yi. Fatan sauka lafiya nayi musu Hajiyayye dai in kun tanka ku masu karatu to itama ta tanka, tunda Bilkisa ta buɗe fuskarta Hajiyayye ta daskare a zaune. Ana cikin haka Kaila yayo sallama ya shigo, sai faman dariya yake yi, yana doro. "Anty Zinaru baku wuce ba ashe?" Sai wani dariya yake yi harda wani sin_sin da kai. Ita wacce ya kira da Zinaru tace. "Munkaila yanzu zamu tafi, ka kula da Bilkisa sosai kar ka manta da sharaɗin da Mahaifinta ya gindayama tun kafin ma tafiyarku ma tayi nisa. Bayan kwana bakwai zata ci gaba da zuwa aikinta, an yi magana an gama mata komai aikin kawai zata soma zuwa." Dariya yayi yace. "Babu ai komai Anty Zinaru ni dama ƴar bokon naso shi yasa na biyota kuma na aminta da komai. Zuwanta cikin rayuwata aikhairine mai girma, gidan zai ɗau saiti sosai, nifa yanzu ne na san nayi auren kece raini. Ina godiya sosai da karramawa" Nan su kai mana sallama suka fice, ni maza sun dena bani mamaki tuni. Hajiyayye ce tayi kasaƙe tana kwasar ruwan mamakin Kaila. Fitar Amarya da ƴan uwanta ke da wuya Hajiyayye ta miƙe tsaye tace. "Aikin banza aikin wofi ni Kaila zai wulaƙanta sabida ya auro ƴar boko, wallahi zaman lafiyar Kaila da kilakin daya auro ya ƙare. Fuuu ta fice kamar kububuwa, Hindatu ta bi bayanta tana faɗin. "Allah ya kyauta, wannan cin fuska dame yai kama ne ni ƴasu?" Sabira ta dubeni, nima ita nake kallo, murmushi nayi mata kawai muka koma bakin aikin mu, amman zuchiyata a cushe take ainun. Zuwa yamma gidan babu kowa sai mu mazauna gidan, yara suna gidan Sabira ta haɗe kansu dasu Mustapha sun tafi, Hauwa tana bayana. Ina kan yin shanyar kayan Hauwa dana ɗan ɗauraye sai ga Kaila ya shigo gidan, kici_kici da manyan ledoji yana shirin wucewa ɗakin Amarya. Sannu da shigowa *Ango* Jin na kirayeshi da Ango yasa ya washe mun bakinshi har kunne. "Sannu Shanono da hidima da jama'a fa" Murmushi nayi mishi, Hajiyayye tace. "Inason yin magana da kai Kaila kafin ka shiga ɗakin Baturiya" Dubanta yayi yana nazartarta kafin yayi wani malalacin murmushi wanda ni nasan na muguntace. "To yau dai kwanan Amaryane baki da hurumin da zaki ce dole sai kin yi magana dani." Yana kaiwa nan ya burma ɗakin Amarya ya rufo ƙofa garam. Numfashi kawai naja, ina gama abunda nake yi na yi alwalar magriba nayi shigewata ɗaki na danna sakata." KAILA: Yana shiga ya tarar da Amarya a harɗe a kan kujera tana kallon tashar Mbc action, ana wani film na soyayya. Baki ya buɗe yana dariya. Itama juyowa tayi ta yi mai murmushi mai burgewa. "Amarya bakya laifi ko kin kashe ɗan masu gida. Ni na ɗauka zan zo in tarar dake akan gado a harɗe kin rufa da mayafi kina jiran in sai bakin ki?" Dariya tayi mai tace. "Siyan baki kuma? Sai kace wadda bata waye ba. Ai ni na ɗauki wannan abun a matsayin ƙauyanci, Shekara guda muna soyayya sai yau kawai in rufe maka fuskata haba mana Ƙyalli " Murmushi yayi haƙiƙa Kaila sai ya ji Bilkisa ta sake burgeshi, irin macen daya jima yana nema kenan. Amma a baya bashi da damar mallakar irinsu, duba da yanayin rashi da yake ciki. Amman a yanzu sai hamdala, sana'arshi dai shine gashin kajin gidan gona, kuma wajan gashin nashi babbane, a rana ya kan siyar da kaji guda ashirin ko sama da haka, banda masu siyan pat_pat irin su cinya, ƙirji, kai da ƙafa da sauransu. Kuma shike kiwata kajin a gidan gonarshi da kanshi, ga kashin kajin da yake siyarwa buhu_buhu. Zama yayi a kusa da'ita yasa hannu ya jawota jikinshi tare da lumshe idandunanshi. Itama idan nata a rufe yake, taushin fatarta da irin ɗumin jikinta yayi daban da na matanshi baki ɗaya. Iya hakan ya fitar dashi daga hayyacinshi sosai. Bilkisa ba tai aune ba taji Kaila yai ma bakinta riƙon alawar yara. Abunka da wayayyar mace tuni itama ta fara mayar mishi da nata martanin, cikin wani irin salo mai gigitarwa. Kaila kusan suman zaune ya kusan yi yanda yaji Bilkisa na wasa da harshenta a cikin bakinshi. Kota ina a jikinta ƙamshine har bakinta, hatta numfashi in ta fitar ƙamshi yake korowa. Wannan masoya sun jima suna shaƙar ɗumin juna, dana bisani Kaila ya zare bakinshi a nata ya zuba mata idanunshi da suka narke dan jaraba irin tasu ta maza musamman ma sabon ango. "Ɗanyan gwal. Barka da shigowa cikin rayuwata da fatan zaki kula dani fiye da irin kulawar da kika bani a baya? Ki ɗaukeni tamkar jariri sabuwar haihuwa kinga kuwa yana buƙatar kulawa mai yawan gaske. Ɗan wannan zaman da nayi dake a yanzu ya sake dulmiyani cikin soyayyarki. Mata ma suna suka tara ashe?, bari in fito fili in fyeɗe miki biri har wutsiya. Tunda nake ban taɓa shan yawu mai ɗanɗanon naki ba, haka ban taɓa jin fata mai nagartar taki ba, ga ɗumi, madallah da samun ki a matsayin abokiyar rayuwata." Murmushi Bilkisa tayi tace. "Amman Gwanda ni gaskiya bazan iya shiga bayan gidan tsakar gida ba, ni tunda nake ban taɓa amfani da bayan gidan gargajiya ba. Kuma kamar ni Gwanda sai kawai a ganni na fito zan je wanka? Ina gaskiya bazan iyaba wallahi, su Anty Zinaru ma sunyi magana, ni ina ganin zan yima Dady magana kawai ya kama mun haya kusa da asibiti kawai, daman hakan yaso, amman ganin ka fi sha'awar haɗe mu waje gudane yasa na tausheshi har ya haƙura" Zama Kaila ya gyara yace. "Kin fi ƙarfin wannan bayan gidan ai Ɗanyan gwal. Ki kwantar da hankalinki zan sa a yanka miki banɗaki a cikin uwar ɗakin ki, sai dai bazai kasance babba ba sai kiyi haƙuri kafin in ƙarashe ginina, ke zan fara kaiwa gidan ki zaɓi in da yayi miki. Amman kafin azo a soma aikin bayan gidan sai ki yi amfani da nawa na cikin turakata, ni kaɗai nake amfani dashi dama, zan yi gaggawar ƙarashe sabon gida, wannan da muke ciki ma inaga a kasuwa zan sa shi, kuɗin sai in ƙundume a sabon gidan, wannan sabon gidan dama dake ya dace, da ace tun farko na tuno da batun sai da wannan tsohon gidan, da yanzu ma muna sabon gida." Jin za'a tayar da salla ne yasa Kaila ya miƙe cikin kasala. "Ɗanyan gwal bari in je sallah kinji har za'a shiga Masallaci. Ga keyn turaka zaki iya komawarki can, waɗannan ledojin ki tafi dasu" Yana gama faɗar haka ya ajjiye mata keyn turaka ya fice. Da Hajiyayye yaci karo a tsakar gida, bangazarta yayi, yayi ficewarshi yana faɗin. "Aikin banza aikik wofi duk jarabarki ke baki isa kin hanani shan man Amarya ba" Nan ya barta a tsaye tana cizon yatsanta, dan data ganshi hanya ta tare mishi. Bayan sallar magriba ta kafa ta tsare tana jiran shigowar Kaila domun ta mayar mishi da martanin cizon yatsan da yasa tayi. Shinkafa da miya da nama da latas take ci. Sai taji haf door ɗin ɗakin Amarya yayi kara, juyawar da tayi tayi tazali da Bilkisa cikin wasu fararen riga da wando masu shegen kyau, kanta babu ko kallabi fuskarta sai sheƙi take faman yi. Take numfashin Hajiyayye ya nemi dakatawa, yuu daga ita har Hindatu suka bita da kallon mamaki. Far tayi da idanunta tace. "Barkan ku dai da gida" Ba ta yi maganar domun lallai sai sun bata amsaba, duba da yanayin sigar ta tayi maganar, kuma tana yi ta nufi turakar Kaila. Ɗan mabuɗi tasa ta buɗe ɗakin ta shiga. Hajiyayye bata dawo daga cikin duniyar mamaki da ruɗu ba Amaryar Kaila ta sake fitowa daga turaka ta nufi ɗakinta. "Lallai da gani wannan amarya bata da kunya, har tsakar gida bako kallabi, ace amarya daga kawoki har kin soma nuna isa da turakar miji." Ƙuta Hajiyayye tayi. Bilkisa ta sake fitowa daga ɗakinta da ƙaramin akwatinta ja na aure. Tasa kwaɗo ta datse ɗakin nata tayi shigewarta turaka. Abincin da Hajiyayye ta kasa ƙarashe ci kenan. Ajjiye kwanon tayi ta shige ɗakinta. Hajiyayye: Tunda ta shiga ta kasa zaune ta kasa tsaye. Kishi kawai ke ɗawainiya da zuchiyarta. Bata san sanda ta fashe da kukan baƙin ciki ba. Bata taɓa tunanin Kaila zai ji marmarin yin wani aure nan kusa ba. Domin a tunaninta da kuma abinda Kaila ya faɗa mata a yayin da yake kan karagar sonta cewa yayi. Tani bata iya gamsar da sha'awarshi in ya shigeta baya ko jin alama, sabida yawan haihuwa ta zama fanko maras amfani a gado. Shi yasa yake son yayi auren kece raini, kuma yana sha'awar mace wayayya wacce zata latatashi a shinfiɗa so yake a dinga lasarshi kamar alawa, kuma mai jin turanci da iya gaye yake so. Hajiyayye tayi tunanin itace mace mafi soyuwa a zuchiyar Kaila, ganin tayi dai_dai da irin macen da Kaila ke ra'ayi. Duk da cewar ita iyakarta sakandare ne kawai, amman tana ɗan jin turanci kuma tana iya mayarwa babu laifi, kana ta iya rubutun turanci, kuma tana karance_karancen littafin Hausa. Tun tana gidansu take bama Kaila dukkan kulawar da yake buƙata. Sau biyu Kaila na kwanciya da'ita a wani shagon abokinshi. Ya kuma nuna mata babu wata mace a zata iya kere mata a matsayi. Sai gashi tun kafin aje ko ina ya nuna mata kalarshi. Zama tayi a kujera tana tuno ranar da Kaila ya fara ribatarta ya jata zuwa shagon abokinshi, ranar daya rabata da darajarta kenan. Irin kalaman soyayya da irin alƙawarurrukan da Kaila yai mata a wannan ranar abun ba'a cewa komai. Kuka ta sake fashewa dashi tace. "Kaila ka cuceni. Amman wallahi bazan barka kaci amarcinnan lafiya ba, saina ja maka masifa" Wata zuchiyar tai mata gargadi da cewar. "A'a Hajiyayye kar garin kishi kije zuchiya tasa ki aikata abunda zaki zo kina ɗan daka ce baki aikata ba." Shiru tayi tana nazari. " "Tani ko tana ɗakinta kamar bata ma gidan. To wai wacce iriyar zuchiyace a ƙirjin Tani, ita bata san ciwon kanta bane ko yaya? Na tatama Tani rashin mutunci da cushen baƙin ciki iri_iri. Amman a tsakanina da'ita sai dai tayi mun murmushi kawai. Tana cikin wannan sambatun Kaila ya ɗaga labulen ɗakin nata, ya zuba mata mayaudaran idanunshi yana nazartar yanayinta. "Ni zan shiga daga ciki Hajiyayye babu wata matsala dai ko?" Ai Hajiyayye dama kamar jiranshi take ya dasa aya ta miƙe." "Ai ba sai ka zo kayi mun sallama bane zansan cewar zaka kwana da mace ba. Wanne darene jemage bai gani ba, ƙila itama ka gama shan romon amarcin nata tun daga zauren gidansu, ba girin_girin ba dai tayi mai" Idanun Kaila har ƙanƙancewa su ka yi dan ɓacin rai, ita kanta Hajiyayye data kalleshi sai da tasha jinin jikinta. Amman a zuchiyarta kuma taji sanyi sosai da taga ɓacin rai a shinfiɗe a fuskarshi. Harararshi tayi ta ƙule ƙuryar ɗakinta ta barshi riƙe da labule yana mata kallon mamaki." Dariyar mugunta yayi, bai bi ta kanta ba ya ƙule turaka wajan amaryarshi. A wannan daren Kaila ya tsunduma wata duniya iriyar duniyar da bai taɓa tsintar kanshi a ciki ba. Me yasa? Sabida wannan shine karon farko daya ɓare matarshi ta sunna dal a leda. Hajiyayye ba wai bai sameta a cikakkiyar budurwa bane, ko ɗaya. Sai dai kawai sun gudunar da kwanciyarne babu nutsuwa da kwanciyar hankali a tattare dasu. Kuma kasancewar tasu bata zama mai armashiba domun sun kauce ma shari'a( Ƙalubale a gareku ƴan mata masu miƙa ma saurayi kai tun kafin a shiga daga ciki) Duk wata hadda dake kan Kaila a wannan daren sai da Ɗanyan gwal ta kankare mishi Tani: Bayan nayi sallar isha, sai na shiga tunanin yanda zaman gidannan zai sake yi mun zafi. Amman inason da zaran Allah ya saukeni lafiya in tashi tsaye domun cikar burina. Duk da nasan fitowar burina ka iya haifar da matsaloli masu tarin yawan da ni kaina bansan su ba. Amman gani nake yi muddin naci gaba da rayuwa a haka haƙiƙa baƙin ciki da damuwar gidan Kaila ce zata zame mun ajalina. Kaila ya mayar dani tamkar wata jakkar gidansu. Dangin Baba Rammai babu mai ganina da kima, Hajiyayye wanne irin baƙin cikine bata cusa mun ba, ga Amarya kuma bansan ita da wanne salon tazo ba. Ni duk wannan fafutukar inayi ne domin yarana, bana fatan abinda zai sa in tsallake in barsu, nasan babu mai iya kularmun dasu, ƙarshe gararamba zasu ci gaba dayi a anguwa kawai. Wayata ce tayi ƙara ta katsemun tunanina. Yaya Use ke kirana, nayi mamakin kiran duk da dai dare bai yi sosai ba, goman dare ne. Assalamu alaikum Yaya Use kece da daddarennan haka, Allah yasa dai lafiya?" Dariya Yaya Use tayi daga ɓangarenta tace. "Babu komai. Inno ce tace in sanar miki gobe zamu tafi ashe ba jibin ba. Tace kizo da sassafe, mun samu mota har gida. Lauwali maƙocinmu direban bektira ɗinnan motarshi zamu bi har Shanono in sha Allah. Yayi mana sauƙi sosai, sai ki soma shiri tun yanzu sai da safe" Sallama tayi mun ta datse wayarta babu shiri na miƙe na shiga zaƙulo kaya. Kayan da Habiba Bala ta bani na ciri kala uku na saka a jaka. Sai lokacin na jawo ledar data rarraba mana a wajan taron. Sabulan wanki dana wanka ne a ciki, sai omon wanki, da turaren wuta, da humra, harda turaren ɗaki na fesawa da ƙaton basilin. Murmushi nayi na jinjina kaina lallai Habiba Bala akwaita da kirki. Kayana dana Hauwa na haɗa tsab, na ware mana wanda zamu saka in zamu tafi, a lokacin wani bacci mai nauyi yayi gaba dani, bani na farka ba sai asuba. Fitowa nayi ina hamma gefe_gefen bakina duk yawun bacci, idanuna kuwa cike da kwantsa bana ko iya buɗe idon sosai. Banɗaki na faɗa na kama ruwa na fito. Ina tsakar gida ina alwala Kaila ya fito

Chapter 11 of 17