Share this page
da tabarau fari mai kyau, sai ƙamshin turaren 212 yake yi. Kaila ƙyalli kenan ƙyalli shine inkiyar shi, wanka kam akwaishi a wajan Kaila ga iya direshi, in ya ci wanka babu mai cewa yana da aure ma balle a yi tunanin yaranshi sun kai Bakwai" "Yanzu Shanono yarannan a haka kika turasu masallaci ɗazu? Kinga kayan jikinsu kuwa, in banda zarni babu abunda suke yi. Wannan ai wulaƙanta ni kika son yi Shanono" Ɗan Murmushin dole na ƙwaƙwulo nace. Kayi haƙuri kayan nasu masu daman ka gansu a shanya basu bushe bane shi yasa, amman baza'a sake ba. Rago muka samu? To Allah ya ba da lada" "Ameen Shanono" Yana faɗar haka suka tafi suka barni a tsaye, hannunshi riƙe da ƙugun Hajiyayye suka nufi turakarshi. Hannuna na wanke na koma ɗaki, bayan nayi sallah na shigo mana da katifinmu ciki. Sannan muka shige ƙurya ni da matan. Lalle na soma yi musu, kafin ma in gama musu duk sun yi bacci. Kwanciyar na gyara musu. Sannan na shiga jera seletab a ƙafata, bani na kammmala lallennan ba sai wajen sha biyu da rabi na dare. Ina zaune a gefen katifa tunani yai mun yawa, kaina sai aikin saramun yake yi. Ni bansan lokacin da bacci yayi awon gaba dani ba, sai kiraye_kirayen sallar asuba ne ya farkar dani. Lalle na na cire yako yi shar dashi. Gishirin lalle na kwaɓa da toka na shafa, yaranma na kwashe musu lallen na sa musu gishirin lallen. Cikin minti goma yayi baƙiƙƙirin gwanin sha'awa. Nan fa yara duk suka tashi muka shiga yin alwala. Muna tsakar gida na jiyo ƙamshin turaren Kaila ta bayana, wucewa yaxo yayi da sauri yana saye da farar jallabiya mai ɗaukar idanu. Hajiyayye kuma ta fito riƙe da ƙatuwar buta a hannunta tana waƙe_waƙen data saba yi in dai Kaila yayi mu'amalar aure da'ita. Ɗaki muka shige da yara mu kai Sallah. Na fito na hura wuta na ɗaura ruwan wanka. Kafin shidan safe tsakar gidan ya kacame da ƙamshin girkin Hajiyayye da Hindatu, mu kuma sai wanka muke yi. Nice karshen shiga wankan. Ina fitowa naga Hajiyayye da wani lafiyayyen leshi mai taushi ɗinkin doguwar riga, tasha ɗan kunne da sarƙa da zobe da awarwaro harda agogo tayi kyau sosai. Samira kuma tana cikin wasu riga da wando na kanti sababbi fil, kanta yasha bit itama ba laifi tana da gashi. Fati da Zulaihat da Tasi'u yaran Hindatu matar ƙanin Kaila suma suka fito cikin ankon shadda mai ruwan ƙasa su da uwarsu kowa yayi kyau. Gaisawa na tsaya mu ka yi dasu kafin na wuce, yara suna jira in fito in basu kayan da zasu saka. Kowa ya shafa mai. Wata bulu ɗin yadi na zaro ma Sulaiman da Shafi'i da Sani, Inno aka ba sadakarshi ta kawo mun, basu taɓa sawa ba, kuma sabone fil. Su kuma su Balaraba atampa na ciro musu wacce na dinga musu da ƙaramar sallah atampa roba, kowa yasa kayanshi, na basu sababbin hijabansu duk suka sa harda Hauwa, su kuma su Sulaiman suka saka baƙar hularsu ( gobe da mandiri) wacce na siya musu a kasuwar mai shafi da azumi ɗari bibbiyu. Ficewa su ka yi tsakar gida suma suka shige cikin ƴan uwansu. Ni kuma na shiga ciki na zaro wata abaya irin ƴan italiyannan itama Inno ce ta kawo mun ita tare da kayan su Sulaiman harda takalmi mai kyau ta haɗomun dashi duk da dai takalmin ya yi mun yawa kaɗan. Bayan na shafa mai na zura rigarnan doguwa mai kyau, na saka dan kunne da awarwarona, sai jar hoda Zainab dana ɗan barbaɗa akan tsumma na shafa, na bi farin idona da kwalli. Hijabina baƙi na ɗakko na maka na daƙko baƙin takalmina na saka abuna. "Shanono shanono ki fito mana in kina zuwa, in kuma bakya zuwa mu tafi" Kaila ne yake mun magana murya a sama. Ba shiri na fito da ƴar posa ta baƙa a hannuna, ɗakin na kulle na samesu a ƙofar gida. Kaila yaci ado da wata farar shadda mai kyau, ya kafa hula da sabon takalmi fil, idanunshi saye da tabarau baƙi. Motar Abokinshi Isa na gani a ƙofar gidan. Shiga nayi kamar yadda naga Hindatu a ciki, mandiya hamshaƙiyar kuma tana gaban mota da ƴarta ta sa wani mayafi shara_shara. A bayan mun matsu sosai sabida yara amman a haka dai muka tafi zuwa masallacin idi. Yaya kuka ji wannan salon tafiyar kuma? Tafiyace mai tsayin gaske, labarine mai tsawon gaske, ku bini a sannu sannu domin ganin yadda zata kaya. Ƙofa a buɗe take ga masu son magana dani. Wannan littafin zai soma zuwa muku 20 ga wannan watan in sha Allah. GAWURTATTU UKU 👠👠👠 1 _KWAI A BAKA_ *(UMMU AFFAN)* 2 _ZULFA_ *(UMMU MAHEER MISS GREEN)* 3 _NA FAƊO DAGA BENE..._ _NA ZARCE RIJIYA_ *(BADIAT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI)* MRS BUKHARI CE https://chat.whatsapp.com/Dqaioj0tydVHQGo5zoG0lm [10/8, 18:30] Badiat Ibrahim: NA FADO DAGA BENE...... NA ZARCE RIJIYA hakkin mallakar Badi'at Ibrahim Mrs Bukhari b4b gidan ƙamshi. Gawurtattu uku *ASSALAMU ALAIKUM MASOYAN GAWURTATTU UKU, MASOYAN BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI. GAMU MUN FITO DA ZAFINMU A BISA ROƘO DA ƘORAFIN MASOYA DA MUKA SAURARA AYI KARATU LAFIYA. NA SOMA DA SUNAN ALLAH MAI RAHAMA MAI JIN ƘAI. GODIYA DA TABBATA GA MAMALLAKIN RAINA, WANDA YAI MUN HANCI DAN SHAN ISKA. SAƘON GODIYA. INA MIƘA SAƘON GODIYATA GA ƊAUKACIN MASOYAN RUBUTUNA. HAƘIƘA NAGA ƘAUNA. SHAFI ƊAYA NA WALLAFA NA LITTAFINA, AMMAN A RANAR NA SAMU WAYAYO DA SAƘONNIN MASOYA BILA ADADIN. HAƘIƘA WANNAN LITTAFIN YAZO DA WANI IRIN FARIN JINI NA MUSAMMAN. SHANONO TACE IN MIƘA MATA GAISUWA GA MASOYAN LABARINTA. SADAUKARWA: NA SADAUKAR DA WANNAN LITTAFIN GA KO WACCE BAZAWARA TA ƘASAR HAUSA. NA SAKE SADAUKAR DA WANI KASO DA MATAN AURE IYAYE. GAWURTATTU UKU UMMU AFFAN (ƘWAI A BAKA) UMMU MAHEER MISS GREEN ( ZULFA) MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI ( NA FAƊO DAGA BENE NA ZARCE RIJIYA) Lamba ta 2 A filin masallacin idi mu ka yi sallar idinmu, zukatan al'ummar musulmi cike yake da farin cikin wannan rana. Yara da manya kowa ka kalla a cikin ado da kwalliya yake. Inata kallon yara ƴan gata yara sa'annin Balaraba da Amina da jaka da agogo harda tabarau na yara duk an sai musu, kansu cike da bit kamar ba da kuɗi ake siye ba. Kaila ne ya iso inda muke muna jiranshi shi da Abokinshi Isa. Gaggaisawa akayi, nan Isa ya bi ko wanne yaro da goron salla na sababbin ɗari biyar_biyar, mu kuma ya bamu dubu ɗaɗɗaya. An gode Baban Nana Allah ya saka da Alkhairi " Idanu Kaila ya ƙuramun cikin kallonshi na yaudara, nayi saurin kawar da kaina, yaran duk suka mimmiƙo mun kuɗin hannunsu. Muna tafe zamu je inda muka ajjiye mota Balaraba tace. "Umma siya mana askirin" Dariya nayi mata, Hindatu ta shiga yi mata tsiya. Ɗari biyar na zaro na ba Sani nace. Yaya maza siyo muku dukkanku na duka." Jikinshi har rawa yake yi ya karɓi kuɗin ya zura da gudu ya siyo musu. Mota muka shiga muka koma gida. Muna isa Hajiyayye ta shiga rabon abinci. "Umma! umman Samira tace ki kawo kular abincinki, da kwanon da zata zuba miki nama da cincin" Cewar Shafi'i. Yana gama faɗa ya fice a guje. Mayafin doguwar rigar jikina na yafa na fito a lokacin Kaila na kiciniyar fita da rago. Yaran kuma ashe Hundatu ce ta zuba musu shinkafa da miya a katon trai suna ta ci, harda zoɓo mai sanyi. Kula na shiga kitchen na ɗakko da kwanon nama na kai bakin ƙofar ɗakin Hajiyayye. Tana fitowa data ganni da doguwar rigarnan sai tayi wani turus ta kasa ɓoye mamakinta dan rigace mai kyau da gani kuma zata yi tsada. Kafata ta kalla sai ta haɗe ranta tace. "Hmmmm" Ni dai ina tsaye ta zuba mun fried rice ɗinnan da koslow a kwano. Sai naman kaza da cincin, da meat pie. Cike da mamaki na dubeta ganin nama da kayan fulawar data zuba mun kamar ni kaɗaice a ɗakina banda yara. Hajiyayye ki ɗan karamun naman da kayan fulawar kinsan muna da yawa" "Dan kuna da yawa? Ai ba dan ku nayi ba, nayi ne sabida Baby da abokanshi ba sabida ke da yaranki nayi ba, mtwss" Taja tsaki. Ban tanka ta ba na ɗauki kwanon naman na ɗaura a saman kular abincin, na sa kwanon koslow ɗin akan kwanon naman na ɗauka. Sai ga Shafi'i ya biyo ni da lemon kwalba 7up guda huɗu. Ajjiyewa yayi na dubeshi nace. Maza kuci abincin kuzo ku tafi ku kai ma su Inno abincin Sallah maza. Nan Shafi'i ya shiga murna a guje ya kirawosu, sai gasu har suna rige_rigen shigowa. Ƙatuwar samira ta kasan na cika ma Inno da abinci dam, samirar tsakiyan kuma nasa mata nama da meat pie. Na samu ɗankwali mai ɗawisu na kulle musu samirun dashi, na samu leda ɓaka mai ƙarfi na zura samirun a ciki, na ɗakko 7up guda biyu na zuba. Ragowar meat pie da lemun kwalbar nace musu su ci kafin su tafi, dan in sun tafi sai an gama bikin sallah ranar da naje wunin sallah na gida nake tarkatosu mu dawo tare. Suna gama ci su kai mun sallama suka fice. Hauwa kuma sai bacci take yi. Zama nayi na zuba abinci a plate na soma ci, gaskiya abincin yayi daɗi sosai, Hajiyayye ta fini iya girki nesa ba kusa ba. Bayan na gama cin abincin saina ɗan shingiɗa a bakin katifa har bacci ya soma ɗibata na jiyo muryar Kaila a tsakiyar kaina. "Shanono ki taso ki gasa mun hanta ga kayan ciki nan na shigo dashi ki soma aiki. Kallonshi nayi nace Kaila ai girkina sai zuwa bayan la'asar zai shiga Hajiyayye ce da kai har yanzu" "Ke dai babu dama ayi magana ki ce to. To Hajiyayye tana can tana zuba ma abokaina abinci, kuma ta gaji ita tai ta yin hidima jiya, in zaki taso ki taso ni dallah sai shegen sa'insa mata ba dama ace mata abu ɗaya. Allah yana gani ni nayi nadamar auroki da nayi" Ficewa yayi fuu. Babu shiri na biyo bayanshi, har sun gama aikin ragon, yana jikin bangon ɗakin Hajiyayye a banƙare. Wuta na haɗa a korfo, na shiga cakuɗa hanta da maggi da yaji da kayan ƙamshi, nan na shiga gashi. Ina jiyo shewar Kaila a ɗakin Hajiyayye da abokanshi, harda shewar Hajiyayye Babu kowa a tsakar gidan sai ni, Hindatu tana ɗaki da mijinta suna kallon wakokin ado gwanja. Haka na gasa hantarnan tas nayi sallama a ƙofar ɗakin Hajiyayye. Fitowa tayi ta karɓi plate ɗin ta shige ciki. Nan na duƙufa gyaran kayan ciki, nazo na yayyanka bayan na gama na zuba a tukunya na aza bisa wuta, na zuzzuba duk abinda ya dace, na koma ɗaki ina nishin gajiya, na tarar Hauwa ta farka sai kuka take yi. Ɗaukarta nayi na zura mata nono a baki, nan ta shiga tsotso tana sauke ajjiyar zuchiya. Nima ajjiyar zuchiyar nake saukewa zuchiyata cike da tunanin shin haka mazan ƙabilar Hausawa da yawansu suka lalace wai, so suke ƙarfi da yaji su mayar da mata baya can zamanin jahiliyyah. Kuma abun takaicin shine ba ga masu sanin ba, ba ga jahilan ba. Tunda ni na auri malami na gani, jahilin ma na aure shi shima naga kalar tashi rawar, ga tsaka tsaki shima na aura naga irin tashi rawar da yake takawa. Wai mu mata ina zamu tsulma ranmu ne muji sanyi, haba maza iyayenmu ya kuke son mu yi da ranmu ne? Gashi in ƙaddara ta samu mace tayi aure ɗaya zuwa biyu ta fito, sai ƙabilar Hausa su sa mata jakar tsaba, wasu su kirata da maras tarbiyya, wasu suce mata mai ruwan ido, wasu su kirata da kwaɗayayya. A gidanku ma baka huta ba a wajan iyaye da ƙanne, tsangwama daga ko wanne ɓangare babu daɗi. Wannan dalilin shike tilastama wasu mata zaman dole wanda ka iya zama ajalinsu, ko silar shigarsu wuta. Ni kaina a wannan auren nawa karo na biyar na ɗau alƙawarin duk rintsi duk wuya zan zauna ko da wuya da ciwon zuchiya za sui ajalina. Tuno mazajena na baya na yi da dalilan mutuwar Aurarrakina. Numfashi naja mai ƙarfi dana tuno da yanda akayi na haɗu da Kaila a hanyar kasuwar taminus wajan da Baffa yake zaman Bara a masallacin ƴan taya. Wasu zafafan hawayene suka gangaro kumatuna. Ƙauri na soma jiyowa da sauri na fita na sauke tafashen kayan cikin. Man gyaɗa na gani kwalba biyu a kofar ɗakina an ajjiye mun a wulaƙance. Ɗaukowa nayi na juye a bojuwar suya na soma suyan kayan ciki. Hindatu itama tana tsakar gidan tana suyar hanji wanda Kaila ya dibar musu. Wani kurfo na dakko ƙarami na zuba gawayi da gaushi a kai. Ina suyar nan na tsai da sanwar miyar tuwon dare, na ɗebi tafashasshen kayan cikinnan na zuba a cikin ruwan miyar da ruwan tafashen. Zuwa bayan la'asar na kammala suya tas na juye a roba mai murfi bayan ya huce. Assalamu alaikum Hajiyayye dan Allah ɗan miƙo mun key ɗin turaka zan ajjiye namannan ne" Naji shiru dama a rufe naga ƙofar amman dake na saba ganin hakan a wajen Hajiyayye sai ta saka Kaila a ɗaki ta rufe shi da ranar Allah gida fal yara bata ko jin nauyi. Hindatu ce ta fito daga bayan gida take ce mun. "Ai basu daɗe da fita ba, ɗazu da kika shiga ɗaki ɗakko robar da kika juye kayan ciki tai mun sallama sun fita." Dawowa nayi da robar naman a hannuna, basu tasarma fita ba sai da suka ga kwanana ya shiga. Roba na samu na cika ma Hindatu da kayan ciki duk da nasan an bata ɗanye. Kunyace tasa ina dawowa ta biyo ni da cincin da soyayyen naman kaza harda zoɓo mai ɗan karen sanyi. Godiya nayi mata na ajjiye a ɗaki. Sallar la'asar nayi na jawo wayata inga ko an kirani, ai kuwa miss call ɗin Yaya Use na gani. Ina jiyo muryar Zulaihat a tsakar gida na fita da nera ta ɗari. Zulaihat zo ki siyo mun katin glo a shagon mahi" Da gudu tazo ta karɓa taje siyo mun. Ni kuma na shiga yin talgen tuwo. Ina zaune a dokin ƙofata ina cin kayan ciki da zoɓo sassanya Zulaihat ta dawo daga siyo katin, na ganta da alkaki cike da baƙar leda tace mun. "Maman Zuhura ce tace in kawo miki wai zata shigo inta gama tuwo. Kuncewa nayi na bata guda uku nace ta kaima ummanta. Sai da na tuƙa tuwo na kwashe a leda na mayar da ruwan wanka sannan na saka katin a wayata, na ɗan sake share falona sama_sama. Ban zauna yin wayarnan ba sai da na fito wanka na kintsa tsab. Sanye nake da riga da skirt na gwanjo da azumi na siya a wajan tafsir ɗin mai shafi. Ni dama ba kananun kaya nake sawa ba, na ga kananun kaya sunfi burge Kaila ne shiyasa ma na cire ɗari ukuna na siya." Danna kiran layin Yaya Use nayi, bayan ta ɗaga nayi mata barka da Sallah mu ka ɗan taɓa hira na kashe wayata. Layin Inno na kira nayi musu barka da Sallah, daga ƙarshe na kira Yaya Karima itama mu ka yi gaisuwar sallah. Har zuwa bayan magriba ba su Kaila babu dalilinsu. whatApp na ɗan leƙa da bonus na data da glo ta bani, dan in ɗan ɗebema kaina kewa, group ɗin ƴar aljanna na leƙa mata sai turo hotunan sallansu suke su da yaransu, wasu a irin tabka_tabkan falukannan na gani a faɗe, wasu kuma a tsakar gida ma suka ɗauka, wasu a filin idi. Gasu nan dai birjik, wasu na buɗe na kashe ƙwarƙwatar idona, wasu kuma wucesu nayi. Wasu matan harda mazajensu a cikin hotunan. fita nayi a group ɗin baki ɗaya sabida naji anata kiran sallar isha. Har nayi Sallah ni dai banji motsin shigowar su Kaila ba. whatApp ɗin na koma ina hawa na ganni a cikin wani sabon group mai suna ( FGGC BAUCHI) dariya da mamaki na soma yi lokaci guda. Ina shiga na soma ganin sunayen ƴan ajinmu. Mariya Habibi, Habiba Bala, Fatima Bello, Aisha Aliyu musa Biu da dai sauransu, sauran ban sansu ba dake jiniyo kaɗai nayi daga zuwa huto aka cireni a makarantar nan komawar da ban sake yi ba kenan. Ni mamakina ma ina suka samu number wayata, duk mutanenannan ya akayi aka tattarosu" Daga farko na soma bin hirarrakinsu Habiba Bala ce ta buɗe gidan. Wani dogon voice note tayi, jikina yana rawa na danna, muryarta ce wallahi tana nan yadda nasan muryar. Nan ta faɗi manufofin buɗe group ɗin domun zumunci da ƙarfafa juna, ta bada labarin yanda akayi ta haɗo numbobinmu da dama a cikinmu, Fatima Sunusi ce ta bata number na. Mun taɓa haɗuwa da'ita ta shigo jos, lokacin ina aure a wani gidan ba gidan Kaila ba har ta ziyarceni. Haka na dinga bin saƙonnin mutane wasu a rubuce wasu voice har sai da na gaji, dan sunyi surutu fin dubu ɗaya da wani abun. Sai cigiyata ƴan ɗakinmu suke yi. Voice nayi nima na soma da gaisuwa tare da nuna farin cikina a bisa wannan gida da Habiba Bala ta zama silar assasashi, nayi musu alƙawarin in sha Allah zan halarci taron da aka haɗa domun tattaunawa na ido da ido, wanda suka tsaida rana ran huɗun Sallah,za'ayi taron a zaranda hotel. Ina turawa da saƙo duk suka fito nan muka ɓalle da hirar yaushe gamo, muna ta tuno abubbuwan dariya da suka shuɗe a lokacin baya. Ina cikin haka na jiyo muryar Hajiyayye a tsakar gidan. Sallama nayi musu kuma na miƙe. Abincinta na zuba mata na fita. Duk da nasan abune mai matuƙar wahalar gaske taci abincinnan. Ba kasafai ta fiye cin abincina ba. Nayi sallamar duniya a ƙofar ɗakin nata ba'a amsa mun ba. Ta kasan labule na tura hannuna na ajjiye mata abincin na komo ɗaki. Abincin Kaila dake jere a tire mai murtala duk tsatsa na ɗauka na fito. Da sallama na tura ɗakin Kaila na shiga. Take ƙafafuwana suka shiga rawa, ƙirjina na dokawa. Tunda nake ko a waya ban taɓa ganin tsaraici ba face na mazajen dana aura , sai gashi nayi tozali da Hajiyayye tsirara haihuwar uwarta da ubanta a saman Kaila, shi kuma sai sambatu yake yi idanunshi a kulle. Ƙaran faɗiwar tiran hannunane ya dawo dasu cikin Haiyacinsu. Da sauri na fita ina haki sai Allah kawai nake ambato, tsigar jikina sai tashi take yi. A guje na faɗa ɗakina na danna sakata ina haki. Jiyo bugun ƙofar Kaila nayi daga bayana. Ina jingine da jikin ƙofar ina tsiyayar hawaye, hoton tsaraicin Hajiyayye ƙam a idona. "Shanono ki buɗe ƙofar nan nace miki, bakya ji nane Shanono, kinga buɗe kiji" Da ƙyar na rarrafa na shige uwar ɗaki na kwanta a katifa na rushe da kuka ina tambayar kaina wai ni mai nayi ma maza ne suke ƙoƙarin ganin sun rabani da rayuwata ne?" Nayi kuka a wannan daren wanda bansan iyakarshi ba, bansan sanda baccin wahala yayi sama da faɗi dani ba. Na dai farka da asuba idandunana sunyi luɓu_luɓu. Ina fitowa tsakar gida da buta a hannu naci karo da Kaila, sai wani kallona a ido a ido yake yi. Ni kuwa nayi biris tamkar ban ma ganshi ba. Waƙe_ waƙen Hajiyayye na jiyo daga bayana, ina juyowa nayi tozali da'ita ta fito daga turakar Kaila daga ita sai rigar bacci iya cinya, bata ko jin kunyar bayyanar tsaraicinta. Wani ƙududune ya tokare mun maƙoshina. Bayan gida na shiga nayo fitsari na fito. Kwanukan tuwona dana kai ɗakin Kaila na gani a dokin ƙofata da tuwon da miyar duk an zube mun su a cikin tiran. Shigarwa ciki nayi na ta da Sallah. Ina sallah ina tsiyayar hawaye. Ruwan tea na haɗa shi kaɗai na iya sha da alkakin da ƙawata ta aiko mun dashi jiya. Ina jiyo ƙwaramniyar matan gida, ni dai ban bi takan kowa ba, kuma da har nayi niyyar hana Kaila abinci tunda bani na kwana dashi ba. Sai kuma na zuba ruwan tea da alkaki da naman kaza a tire na fita na kai mishi harda robar kayan ciki dana soya. Na sameshi yana waya ƙasa_ƙasa yana ganina ya sauke wayar a kunnenshi. "Shanono ai nayi tunanin ba zaki kawo mun kayan karyawa bane, dan naga kin ƙaro wulaƙanci. Dan kuturun wulaƙanci kina fa jina ina buga ƙofa kikai biris dani sai kace wacce tazo ta kama ni ina zina da karuwa. Kai ku mata kishinku dai yayi yawa." Kallonshi kawai nayi yana gamawa nasa kai zan fice abuna. Sai yace. "Ki same ni a ɗakin Hajiyayye yanzu inason zan yi muhimmiyar magana daku dukka kuma yanzu. Danni fita zanyi, wannan kayan karin naki ki koma dashi Hajiyayye ta kawo mun tea da biredi da ƙwoyi. Ɗaukan turan nayi na fita ba tare da nace dashi ci kan ka ba. Ina jiyo takun tafiyarshi daga bayana. Ko dana shiga ɗaki sai da na yi kuka sosai kafin na goya Hauwa a bayana na fita zuwa ɗakin Hajiyayye. Da sallama na shiga ɗakin. Suna zaune akan 3sitter na same su suna hirarsu faram_faram. A kan 1 aitter na zauna a rakuɓe bance musu komai ba, vidiyon tsaraicin Hajiyayye sai yawo yake yi a kaina, gata dai da kaya a jikinta amman ni tsirara nake kallonta. Ɗakinnan a gyare tsab sai ƙamshi yake yi. Ga kujerunta masu taushi, ga kayan kallo ga kafet mai taushe malala a ƙasa, harda buna ta turaren wuta na ƴan gayu sosai mai wuta, an juna turaren wuta yana ta buso kamshi. Gyaran murya naji Kaila yayi. Wata leda viva ya miƙo mun yace. "Ungo nan Shanono kafin in yi muku bayani" Hannu nasa na karɓi ledar daga hannunshi kaina na ƙasa, dan mugun kunyarsu nake ji. "Baby riƙe naki kema ko?" Ya miƙama Hajiyayye ledarnan irin tawa. Zama ya gyara ya tattaro dukkan nutsuwarshi garemu, sai wani wauware idanu yake yi kamar wanda ya wanke makanta........✍🏻 *Akwai set na kayan ƙamshi, musamman domin masoyan wannan littafin. Zaku same su cikin rahusa da izinin Allah* ga masu buƙata sai su tuntuɓeni. Amman iyaka masoyan wannan littafi kaɗai zan siyarma, garaɓasar taku ce, promo nayi muku domin in faranta ranku kwatankwacin yanda kuka faranta nawa ran [10/8, 18:30] Badiat Ibrahim: NA FAƊO DAGA BENE..... NA ZARCE RIJIYA HAKKIN MALLAKAR BADI'AT IBRAHIM MRS BUKHARI B4B GIDAN ƘAMSHI GAWURTATTU UKU LAMBA TA 3. *ASSALAMU ALAIKUM BARKAN MU DA SAFIYAR LITININ. HAƘIƘA BANSAN DA WACCE SIGA ZAN MIƘO SAƘON GODIYATA A GAREKI BA HAJIYA SUMAYYA. KE ƊIN MASOYIYACE TA HAƘIƘA CIKAKKIYA. SAƘON DA KIKA TURO MIN DASHI, NA KARƁA YA ISO GARENI, BANSAN WACCE IRIN GODIYA ZAN MIƘA MIKI BA, SAI DAI ADDA'AR KHAIRIRO. ALLAH YA BARMU TARE YA ƘARA MANA SOYAYYAR JUNA* *HAƘIƘA WANNAN LITTAFIN YA KAINI WANI MATSAYI DA BAN TAƁA MAFARKIN RISKAR KAINA A KAI BA. BABU ABINDA ZANCE DA ALLAH SAI GODIYA. BABU ABINDA ZANCE DA MASOYANA SILAR MURMUSHINA, SAI FATAN ALKHAIRI* Bayan ya gyara zama yace. "Waɗannan ledojin kayane a ciki. Atampa guda ɗaya , sai mayafi, da takalmi, harda ɗan kunne da sarƙa, da nera dubu da ɗari biyar_biyar kuɗin ɗinki. Fasali ya ja kafin ya ɗaura da cewa. "Dalilin wannan kaya kuwa shine. Aure zan ƙara nan da sati biyu masu zuwannan in Allah ya nufa. Kayane na faɗar kishiya ake ce musu ko me oho dai? Ɗanyan gwal Bilkisa ce ma na bata kuɗin ta siyo muku dan ta bala'in sanin kaya da kala." "Kanbu Kaila Aure fa kace zaka yo a cikin gidannan, ni za kai ma kishiya Kaila? Wallahi in ka isa me nake, kinji fa umman Sulaiman baki ce komai

Chapter 2 of 17