ganin ki da Sadik".
Ba kunya na ce "Ai kuwa Abba ba wani abin damuwa, domin kirkinsa yawa ne da shi, kawai son girmansa ne ya baci.
Da kuma shi ka za'ba mini da sai na ce gara shi din akan su Yaya Ashir, ba kuma zan ce komai ba".
Ya yi shiru yana nazarina, tsawon lokaci ya kasa magana.
Ya sauke nannauyar ajiyar zuciya ya ce, "Halimatu! Sadik fa da kike ganinsa ba shi da hakuri, sannan ba shi da abin yi kamar su Abbas. Sau biyu ina samo masa abin yi yana rainawa.
Na karshen nan tare na samo musu da Al'amin amma ya bijire akan albashin ya yi masa ka'dan, bayan har nan ya zo ya ro'ke ni na samo masa aikin yi. Na samo din, kuma ya ce shi a Federal yake so ba zai karbi aiki a State ya dinga hana idonsa barci akan albashin da ba zai iya saya masa turare da takalmin da yake sanyawa ba.
Ke shaida ce akan iyashegensa sai wanda kika manta.
Shin idan na dauke ki na ba shi aurenki a irin wannan halin da yake ciki ai na so kaina da yawa, domin da wani ne a waje na gano hakan yake ba zan ba shi aure ba".
Na yi 'kasa da kai na ce "Ni kuwa dai gara shi da su wallahi".
Tausayina ya kama shi, ya fahimci bilhakki nake son tilon dansa, tunda har na iya wannan tsaurin idon cikin dabara.
A sanyaye yake kallona, yayin da na yi kasa da kaina sosai.
Ya nisa ya ce, "Idan na za'ba miki shi fa ba maganar ki ce ni ne na tirsasa ki, ba da ni za ki yi kuka ba, sannan babu maganar kawo 'kara tunda ke kika ce kin ji kin gani?"
Na 'daga kai alamun na amince.
Mamakina ya yi matu'kar daskarar da Abba a zaune.
Yayin da kunyar abin da na yi ta hana ni sukuni, don haka na mi'ke da sauri na fice.
Ina murnar zan samu cikar burina, ashe kara da kiyashi na dauko wa kaina.
*Kinsan komai da ruwanka?*
*Umm Muhd collection kenan*
*Tela ce ta gaske*
*Tana ha'da lefe*
*Tana ha'da kayan haihuwa*
*Tana adashe*
*Tana saida dukkan nau'in sutura*
*Tana saida shoes and bags latest*
*Nema ta a wannan lambar dan 'karin bayani*
*08063358662*.
A ran Abba ya ji da'di, Sai dai da yake yana cikin 'kalilan din mutanen da Ubangiji ya cika zuciyarsu da alheri, ba su da son kai ko son zuciya. Sannan suke dai-daito a tsakanin 'ya'yan cikinsu da na 'yanuwansu.
Ya jinjina wannan 'kaddarar da take shirin 'kulluwa a tsakaninmu domin shi din shaida ne Sadik bai cancanci a bashi aurena ba. Na farko ba shi ya zo gabansa ya ce yana sona ba.
Na biyu ba shi da sana'ar da zai ri'ke mace tunda har yanzu shi ma hidima ake yi da shi tunda ya'ki yin aikin balle ya rage wata dawainiyar.
Na uku kuma a bau'de yake, dabi'unsa masu tsauri da wuyar zama ne.
Sannan kuma matsalar Umma da ta kafe ba zata yi mua'amala cikakkiya da mu ba sai akan dole ba yadda za ta yi, tunda yafi 'karfinta.
Amma tunda har na iya ajiye kunya na nuna masa ina son tilon 'dansa to kuwa magana ta 'kare. Zai tabbatar da wannan soyayyar ya kuma bi bayanta da addu'a da fatan alheri.
Kwanaki uku kacal wannan maganar Abba ya sanya aka nemo masa 'kwararren mai zanen gida(Architecture).
Suka je 'katon kongo nan da yake jikin gidan aka yanki rabinsa, aka zana wani irin hadadden gini sama da kasa na alfarma.
Sai da aka fara aikin sannan Umma ta fahimci gini za'a yi a wajen da alamu suka nuna da wuri zai kammalu saboda yadda aka kawo kayan aiki tamkar Wanda aka shekara ana tanadinsu.
Ranta ya baci matu'ka da gaske, sai yaushe ne Abba zai dinga fa'da mata al'amari kafin ya zartar da shi.
A ce zai yi gini ba zai iya bude baki ya fa'da mata ba sai dai ta ga ana aiki. Wato ita da members din guda duk sammakal?
Sati uku kacal aka dauka aka gama gini, aka fara maganar rufin sama, da plasta.
Umma sai kokawa take yi da zuciyarta, akan ta ci gaba da zuba ido ta ga iya gudun ruwan dattijon.
Amma da aka yi wata da fara aikin zahirin kyaun gidan ya bayyana a dalilin an sanya tagogin alfarma ha'di da kofafi, sai aikin saka tayals da kayayyakin bandaki ake kan yi.
Hakurinta ya fara gazawa domin a cikin wasi-wasinta har hasashen ko aure zai yi a shekarun tsufan nan da ya yi?
Ta ayyana to yanzu wanne aure kuma zai yi? Sai ta bawa kanta amsa da cewa namiji yana tsufa ne, ko yanzu ya auri yarinyar mace haihuwa zai yi.
Gabanta ya fa'di da tsananin gaske! A fili ta ce "Ai kuwa da iyakacin cuta an cuce ni.
Mussaman ace tana zuwa ta jerawa Gudalenta 'kanne maza.😆
Washegari Yaya Sadik ya dawo, ya tarar da hadadden ginin da ake 'kwankwatsawa.
Umma da maganar ginin ta marabce shi, har ya fahimci 'kidimar da take ciki.
A zatona tunda an kwashi lokaci baya 'kasar ai waccan gabar da yake yi da mu ta wuce. Amma ga mamakina da na yi masa magana ko amsawa bai yi ba.
Da na sake maimatawa sai sababi ya biyo baya, tare da cewa yana nan akan bakansa na babu shi, babu mu. Na je na yi zumunci da Sakina kawai.
Da fargaba mai yawa ta tunkari mijin nata da maganar ginin da yake yi, ta ce "Tunda har yanzu bani da 'kimar da zan dinga sanin me kake ciki. Bari na kada billena na tambaya. Na ga kana gini?"
Cikin rashin damuwa ya ce, "Na Sadik ne! Aure zan yi masa nan ba da jimawa ba in sha Allah".
# Team Gudale.
# Team Guduyo.
# Surayya Dee.
# Ana tare🤝.
*Wannan littafin na ku'di ne, biya 500 ku'din karatu ta wannan asusun*
*2384876855*
*Surayya Ibrahim*
*Zenith Bank.*
*A tura shaidar biya ta wannan lambar*
*08032773332*.
An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://thausanovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.thausanovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels