Share this page
5 / 9
na gane son Gudale ne yake hana ni kallon duk wani namiji balle har ya burge ni. A daddafe na yi sati ban nemi Yaya Sadik ba, shi ma kuma ya yi 'diban karan mahaukaciya da ni. Kan dole na gaji da fishinsa na dinga bibiyar sa har na samu ya huce yake kula ni. Bayan ya mini jidali iri-iri, wai don yana shiga shirgina ne yasa na raina shi, har nake ganin zan yi gaba da shi haka siddan. Na dinga mamakin yadda ya fusata, ashe ya san raini ne ka dauki gaba da mutum daga maganar fatar baki? Amma shi yake yi da duk wadda ya shiga gonarsa, ko da kuwa kuskure aka hango yana yi aka yi gyara masa. Da a ce Antin Zaria ba ta kammala sakandire aka yi mata aure ba, da ta haifi wanda ya fi shi, amma ba ya jin nauyin yi mata cin mutunci ko ya gan ta ido cikin ido ya dauke kansa. Haka anti Maimuna, ko 'dar ba ya ji wurin keta ta. Bare kuma Juwairiya da yake ganin tamkar ba 'yar gidansu ba ce a dalilin tun kafin a haife shi aka bawa Yayar Kwalli ita. Shi har ya fi mutuntata 'kananun yayyensa Ramla da Sakina. Duk da dai ba yadda za a yi su hadu da Sakina ba su yi fa'da ba, har yau fa'dan sa'ko da sa'ko ba su bar shi ba. A cikin fa'dan nasu za ka fahimci wani irin so suke yi wa juna mai wahalar samuwa a yau. Ni shaida ce ba 'karamar 'kauna Sakina take yi wa Gudale ba, kai dukkan sisters 'dinsa ma kawai wulakancinsa ne yasa suke kaffa-kaffa da shi. Kwana biyu a tsakani ya huce gaba'daya, ya yarda na shiga motarsa, muna dawowa a hanya ya ce, "Na samo lambar Nusy da kika 'ki samo mini". Zuciyata ta buga da tsananin gaske. Na ce "Na taya ka murna". "Ke ba kya murna na samo miki sister in-law?" Na yi ya'ke na ce "Na yi mana". Ya murmusa ya ce, "Muryarta me za'ki tamkar ta ki, kin san Ubangiji ya hore miki amo mai da'di, idan aka ji muryarki ta waya ba za a yi tunanin tu'ke'kiyar halitta aka bawa wannan muryar ba." Idona ya ciko da hawaye, wai har haka 'kibata ta munanta ne ko kuwa a idon Yaya Sadik ne ta 'kazanta? Na hakaito Nusaiba, siririya ce ta sosai tamkar Rahma Sadau a farkon shigowarta wasan kwaikwaiyo. Na dinga tunanin ni kuma da wacce jarumar zan kwatanta kaina? A lokacin na dan fi jarumar Izzar so da ka'dan musamman daga 'kasa, amma yanayin farinmu 'daya hatta idanuwanmu, haka tsayinmu zai zo 'daya, kawai dai jiki zan 'dan nuna mata, a dalilin na zarta ta cikar 'kirji, da fadin 'kugu. Sai dai ita ma daga baya ta zo tana kibar sosai. A fili na ce, "Hala dai kana mini kallon giwa saboda girma?" Ya ja gemunsa ya ce mini, "Nan kusa kafin a samu me jikinki ai za a jima, shekarunki ashirin fa kike da wannan jikin, idan kika kai shekaru talatin kuma ai sai addu'a". Wata irin karaya ta dinga shiga ta, hawaye ya goce mini, ina dauke su cikin dabara. Har muka isa gida ban sake magana ba. Na shiga ban'daki na ci kuka na koshi, kishin Nusaiba ya fi maganganunsa ciwo a zuciyata. Kwana biyu ban yarda mun tafi tare ba, na yi sa a ma tafiya ta same shi zuwa Enugu akan wani darasi. *Kina bu'katar canja kayan dakinki?* *Kina bu'katar abaya ta zamani?* *Kina bu'katar kayan kicin na alfarma?* *Kina bu'katar siyan ginannen gida?* *Kina bukatar samu gidan haya mai cike da tsaro?* *Kina bu'katar siyan filin da ba zaki shiga matsala ba?* *Tuntu'bi AMYAS NEW & FAIRLY USED* *CIKIN AMINCI DA SAUKAKKAN FARASHI* 08083909947. Bai dawo ba sai da ya shafe sati guda. Sosai na yi kewarsa, na dinga murnar dawowarsa na manta da komai. Ranar wata litinin tana cikin jerin ranakun da ba na mantawa da su saboda irin tozarci da na sha a wajen Gudale. Sanyin safiya muna tafiya zuwa B. U.K. mun zo daidai 'Danagundi danja ta tsayar da mu. Na zuba masa ido ina masa kallon tsaf! Wani irin al'amari ya dinga keta dukkan sassan jikina, kwalliyar da ya yi cikin tsadaddun kananun kaya sun matu'kar yi masa kyau, 'kuruciya sosai a tare da shi. A lokacin bai jima da yin birthday dinsa na shekaru 28 ba. Ya juyo muka hada ido, na waske na dauke kai. Bai yi magana ba, ganin ya daina kallona yasa na ci gaba da 'kare masa kallo ina tasbihi ga Ubangijin da ya kyautata halittar Yaya Sadik. Ban sani ba ko matsanancin son da nake yi masa yana da ala'ka da kyansa da nake gani sosai. Dan tsurut da shi sai 'daukar hankalin 'yammata musamman ma ni. Yanayinsa a wancan lokacin ya fi kama da Ramadan Both din shekarun baya. Kafin ya yi 'kiba. Mun zo daidai 'Kofar Famfo danja ta sake tsayar da mu. Na ci gaba da kallonsa, ba zato ya ce "Oh ni Guduyo saboda Allah wane irin kallo kike bi na da shi haka? Ba na so, ni gaskiya ki daina tsorata ni haka". Na nisa cikin borin kunya na ce, "Wane irin kallon ka kuma? Shin kai din tauraro ne ko me?" A kufule ya ce, "Ban son rainin wayo! Ina ce sau uku ina kama ki kin kafe ni da ido?" Cikin shau'ki da subutar baki na ce, "Kai mai kyau ne fiye da farin wata, bakinka ya dace da gemun nan da ka tsayar, ka iya zaben turare mai nutsar da zuciyar mai bege, komai naka cif tamkar kai ka za'ba". Ina rufe baki na ji ya dauki salati, idonsa ya canja sosai, saboda bacin rai ya ce, "Ashe ke 'din lalatacciya ce Guduyo? A gabana kike yabon kyaun halittar namiji? Kaicon ki! Zan fa'da miki da babbar murya, ni Saddi'ku 'kwalelenki, ba kya cikin jerin matan da zan nuna wa duniya su, asalima kunya zan ji a ce ke 'din matata ce. Amma zan fa'da wa su Abba gaskiya su yi gaggawar mi'ka ki 'dakin aure kafin a wayi gari a ga kinfi haka fitsara, Dan l ji tsoro ma Kika bani, Dan kuwa zaki iya shammatata ki danne ni". # Team Gudale # Team Guduyo # Surayya Dee # Ana tare🤝 🌺 *SABO DA KAZA* 🌺 *NA* *SURAYYA DAHIRU* ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *Masu son karanta cikakken labarin babu yankewa ku biya 500 kudin karatu ta wannan asusun* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank.* *Sai a tura shaidar biya ta wannan lambar 08032773332*. *Tunasarwa* *Ina Jin koarafin cewar typing yana yin ka'dan.* *Ina bin umarnin kungiya ne na kada shafi ya wuce yawan allon comfuter biyu. A hakan kuma ina yi muku yawan allon comfuter uku ne.* *Amma in sha Allah za'a duba korafinku. Zuwa gaba* *Na gode sosai da yabawarku, da soyayyarku*🤝 *Page 13&14* Hawaye ya 'balle mini, wani irin takaicinsa ya mamaye mini 'kalbi. Cikin murya marar amo na ce, "Ni ka jefa da wannan 'kazaman kalmomi irin haka?" "A to 'kazafi na yi miki? Ban da lalata har kin san siffofin maza? Amma na gane ba ki da laifi, sakacina ne da nake bibiyarki nake zama sakarai a gabanki". Na kasa bu'de baki na ce masa uffan a dalilin bacin ran da yake raina mai girma ne. Har muka isa makaranta ya tsaya a inda ya saba ajiye motar ban ankara ba. Shirun da na ji ya yi yawa ne, ya sanya na 'dago fuskata jage-jage da hawaye amma na kasa furta kalma ko guda. Na yun'kura na 'dauki jakata na bu'de kofar amma na ji ta a rufe, na juya na kalle shi ya ha'de girar sama da ta 'kasa. Na san nufinsa, tunda ya sanya mini dokar da ta zame mini ka'ida kullum muka zo sai na yi masa godiya da fatan alheri don na gane shi ba direbana ba ne. Tun ina yi cikin iyashege da mamakin son girma irin nasa, har na dawo ina yi cikin farin-mciki da shagwa'ba. Amma a wannan ranar sai na ji sai dai komai zai faru ya faru din, amma ba zan gode masa ba, bayan ya gama tozarta ni. Fiye da shudewar awa guda muna zaune cikin motar, dukkanmu mun rasa darasin wannan lokacin. Ya hassalo sosai ya dube ni ya ce, "Ke ba na son iskanci kin ji! Za ki yi abin da ya kamace ki ko kuwa?" Yana rufe baki na ce "Ba zan yi ba". Ya sake harzuka ya ce, "Guduyo ki shiga hankalinki, bar ganin ki haka zan yi miki duka, zan karairaya ki na watsar da 'kasusuwanki a ruwan 'Bagwai". Na share shi ina jin yau dai kam bai isa na bi shi ba. Ya bu'de murya ya ce, "Idan na 'kirga uku ba ki yi dalilin da kika fitar mini daga mota na daina kallon ki ba, za ki yi mamakin abin da zai same ki". Ban san lokacin da tsaki ya subuce mini ba. Na ce "Allah yasa gadar Zurmi za ka kai 'kasusuwan nawa ka zubar. Ba na tsoron mutuwa, Ubangijin da ya 'kagi mutuwa ka'dai nake jin tsoro". Ya yi matu'kar ka'duwa ya kalle ni ya ce, "Ni Abubakar Sadik kika yi wa hakan?" Na dauke kaina ba tare da na tanka masa ba. Ya nisa ya ce, "Wallahi matu'kar ba ki yi godiya ba, za ki 'dan'dana kudarki a hannuna, sai hakan ya zame miki sanadin kuka mai yawa, don kuwa zai zama dalilin da ba zan sake yi miki sassauci ba. Kaf gidanmu ke ka'dai kike shiga hancina na dauke miki kai, amma tunda na gane ke din tabbatacciya ce zan gwada miki 'karshen tsageranci! Kumbusar banza kawai. Na fa'da miki da babbar murya duk jarabarki wallahi ni dai kam 'kwalelenki". Na daure na hadiye kukan da ya zo mini na ce, "Ko ina danne maza ai ka san dai kai sai dai na matse ka, domin ka yi mini ka'dan, yo ni maza irinku ma marasa zati mene ne abin burgewa a tare da ku ne?" Ya kuwa zabura ya dam'ke gashin kaina da ya sha dauri da ribbons da 'karfin gaske. Sosai na ji zafi amma na 'ki nunawa bare na karaya. Ya ce, "Ko a hanya kika nuna kin san ni sai na ci kazar ubanki. ya bugi 'kirjinsa ya ce, "Ni ne ba ni da zati ko Guduyo? Na rantse miki ba zan yarda ba, tunda na zo duniya ba wanda ya ci mini fuska irin ki". Cikin rashin tsoro na ce, "Ina fuskar da zan ci 'din? Ai idan na ce zan ci fuskarka ba za ta ragu ba, domin 'yar masayau ce ba afki". Ai kuwa ya dinga kawo mini duka ina karewa, ina sake cewa, "Wallahi yau na gane kai din mace ce da rigar maza! Domin duk namiji mai gwada 'kwanjinsa akan mace wallahi sakarai ne". Ina rufe baki ya sakar mini gashi, ya kifa kansa a jikin sitiyarin mota, tsawon lokaci sannan ya dago da fuskarsa da ta hade da zufa da hawaye duk da sanyin AC da ya cika motar. Yasa hannu ya zaro tissue a cikin kwalinta da take tsakanin kujerunmu. Ya dinga goge hawayen takaicina. Na sa ci kallon sa na ga gaba'daya ya birkice. Jijiyar kansa ta fito rada-rada idonsa ya yi jawur tabbacin ya kai 'koluluwar fusata. A raina ban ji 'dar ba, domin ya riga da ya kai ni 'karshe da bakaken maganganunsa, idan ma ni lalatacciyar ce ai shi ne ya lalata ni, domin duk wani abu na iskanci cikin dabara shi yake fara nuna mini shi. Na tuna da wayona da komai, ba a wani jima ba ma ya 'kankame ni ya mini tunbudin da ban san yadda ake yin sa ba sai a ranar. Soyayya ta hana ni ganin laifinsa, bare na nuna masa cin zarafi ya yi mini. Na sake tuno lokacin da ban yi hankali sosai ba, amma na fara girma yake jana dakinsu yasa ni rawa, ko ya zaunar da ni akan cinyarsa da nufin ganin hotuna a wayarsa. Na yi tsaki a fili, a zuciyata kuma na ce wai mai wannan ta'asar ne yake jifan wani da lalata. Amma laifina ne da na amince ban ta'ba nuna masa ba na so ba. Dole ya ce mini komai. Ba zato na ji ya danna mabudi, ni ma a gaggauce na bu'de motar na fice ina jin da na sake shiga motar nan gara na jingine karatun ga'badaya. Ina da hakuri akan komai amma na tsani a ta'ba mini mutunci. Zagayawa na yi na samu inda ba kowa na zauna a gefe na ci kuka sosai domin ba karamin dafa ni kalmominsa suka yi ba. Na tuna wai ni ce abin kunya a gare shi, ni ce ba zai iya nuna wa duniya ba a matsayin matarsa. Sannan kuma ni ce zan yi masa fyade. Duk yadda haushinsa yake nukurkusa ta ban ji na daina son sa ba, bai fita a raina na can ba. Sai dai kuma wata irin jarumta ta shige ni da nake jin zan iya auren Munir. Don haka ban 'bata lokaci ba, na zaro wayata karon farko da na 'kira Munir da kaina. Ya katse ya 'kira ni. Na dauka na yi masa sallama, ya amsa cike da zumudi mai yawa. "Ranki ya da'de! Ina fatan dai ba kuskuren kira na kika yi ba?" Na saki yar dariyar da babu nisha'di a cikinta na ce, "Ba kuskure ba ne kai din Ustaz na yi niyyar kira, ba kuma kiran kawai ba, zan sanar maka ka samu lokaci ka je wajen Abba". "Who am I today?" Ya fa'da cikin yanayi na farinciki. Na yi shiru ina sauraron maganganunsa na murna. Na katse shi ta hanyar fa'din "Zan shiga lakca". Na katse wayar ina jin dole na tattara na bar wa Gudale filin gidan tun bai tuso ni a gaba da bala'insa ba. Hawayen da ya yi ba zai zuba a banza ba, na sani akwai abin da zai shirya mini a gaba. Na kuma sani da gaske ni kawai yake 'dagawa kafa, amma ko antin Zaria ma ba ta tsira ba. Wannan karon kuwa na sani ba zancen sassaci tunda ya fa'da da bakinsa. *Kina neman kwararriya tela*? *Kina bu'katar kyawawan takalma da jaka irin na manyan Mata?*? *Kina bukatar samun zababbun suturu?* *Kawai tuntu'bi Umm Muhd collection* *Ina tabbatar miki zaki huce takaici* Washegari kuwa Munir da yamma ya je wajen Abba suka tattauna. Kwanaki uku a tsakani na je gai da shi da sassafe kafin na tafi makaranta. Har na mi'ke da nufin tafiya ya tsayar da ni. Ya ce, "Na yi binciken sirri akan wannan yaron domin na san ubansa duk da dai ba mua'amala muke yi ba. Sai dai bayanan da samu a kansa ba mai da'di ba ne. Ni ya ce mini ya ta'ba aure matar ce ta rasu tun ba su yi shekara guda ba. Yanzu kuma na sami bayanan da suke nuna mini tamkar shi din mai yin auren mutu'a ne. Tunda an tabbatar mini sau uku yana auren yana saki, duk aurarrakin nan kuma akwai rabo a tsakaninsu ma'ana yaransa uku daga uwaye mabanbanta." Na dinga jin wani irin tashin hankali na ratsa ni ashe Ustaz kura ne da fatar akuya! Ni zai yaudara? Kafin na ce wani abin Abba ya ce, "Don haka ina sanar da ke ki rabu da shi ba mijin aure ba ne, makaryaci ne mai auri saki". Ki nutsu sosai Ubangiji zai kawo miki wanda ya fi shi alheri tunda dai kin kafe ba kya son yaron kirki irin Anas". Na sunkuyar da kaina 'kasa ina jin wata irin damuwa na rasta ni ba don komai ba, sai don yadda babban mutum da ya kai shekaru talatin da biyar a duniya amma zai iya karkace baki ya shirga 'karya don kawai ya cim ma burinsa. Kaicon wannan halayyar tamu, kaicon son zuciyarmu da a kullum suke zama sandin shigar mu cikin 'kunci. Ko mene ne ribar da za ka samu idan ka yi 'karya don ka zalunci wani? Babu sai damalmalewar al'amura. "Tashi ki je, ki ci gaba d addu'a ni ma zan taya ki, amma ina jan hankalinki ki cire shi a ranki ba shi da nagartar da zamu ba shi aure. Ubangiji ya yi miki albarka, ya ba ki na gari". Na amsa da ameen tare da yin godiya da kuma yi masa fatan inganci a lafiyarsa. Na fita jikina babu 'kwari. Ina fita na hango Gudale yana shirin shiga motarsa na dauke kai, ina jin ko ya ce na zo na shiga ba zan shiga ba, bare na san shi ma ba zai dauke ni ba. Haka kwanaki suka shu'de ba tare da mun sake haduwa da Gudale ba, tsakaninmu sai daga nesa shi ma ba kasafai ba. A hankali sai na fara hucewa, kewarsa ta fara shiga ta, har na fara tunanin yadda za'a yi mu shirya. Ran nan sai ga Sakina ta zo gida, daga asibiti ma take. Muka yini cikin walwala a dalilin Umma ta je Yola. Matu'kar kuwa tana nan ba na samun fuskar da zan shiga cikinsu a yi hira da nishadi. Muna zaune a falon Umman muna cin shinkafa da wake da salak. Gudale ya shigo ba sallama, yana gani na ya hade fuska tamkar ya ga gawa. Ya zauna kusa da Sakina sosai ya jingina rabin jikinsa a jikinta, fuskarsa na kan kafadarta. Wani irin al'amari ya kama ni, shaukin kaunar su na diba na tamkar irin haka Yaya Al'amin yake so na. Kamarsu guda shi da Sakina, duk da kyan Gudale na tabbatar Sakina ta fi shi kyau. 'Ya'yan Umma kyawawan gaske ne matu'ka sai dai kyan Sakina ya zarce kwatance, tafi kowa kyau na ban mamaki. Duk iyashegensa 'kaunar da yake yi wa Sakina ba ta boyuwa, ita ce kawai za ta zage shi kanta tsaye bai rama ba. Sai dai ya gama hargagainsa amma ba zai zage ta ba, haka nan ita ce zai daina yi wa magana ya dawo ya fara yi mata ko ba ta neme shi ba. Da sauri ta ce, "Na Moriki jikinka zafi fa". A shagwabe ya ce, "Umma! Idan na shigo ban gan ta ba, sai na ji tamkar na yi ta rusa ihu, sai na je wajen Mama nake 'dan samun nutsuwa. Gaskiya zan hana ta tafiyar da ta wuce kwanaki biyu". Dariya ta yi ta ce, "Sai ka ce mai shan nono? To me za ta yi maka ne wadda ba za ka iya yi wa kanka ba, komai kake so Mama na yi maka, ga su Dala mai aikin abincin Umma, sannan ni ma komai ka ce kana so yi maka zan yi". Da wata irin murya mai rauni tamkar ba Gudale ba ya ce, "A'a Sakina ko ba za ta yi mini komai ba, na fi jin nutsuwa na shigo na gan ta a gidan nan, ina jin dadi idan ta gan ni ta bar komai ta tarairaye ni". Sakina ta murmusa ta ce, "Haka ne! To ka dinga jin maganarta ka daina sa ta bacin rai". Yana jikinta ya ce, "Ban son irin haka Sakina kin sani! Wai duka wata nawa kika ba ni ne?" Dariya ta yi ta ce, "Ai kai ne babba da shekaru sifili ka girme mini". Ta bu'de jakar hannunta ta mi'ko mini mukullin motarta ta ce, "Halimatu dauko mini wata farar leda ina zaton akwai maganin malaria a ciki". Na amsa na fice. Ban wani jima ba, na dawo dauke da ledar. Na mi'ka mata, ta bu'de ta duba ta fito da wanda ya kamata ya sha, sai da ta 'ballo masa, ta saka ni na 'bude ruwan roba na zuba masa a glass cup. Amma fir ya 'ki sha ya kafe lafiyarsa 'kalau kewar Umma ce kawai ta ke damunsa. Tsawon lokaci yana jingine jikinta, kafin ya yun'kura ya mi'ke, yana 'dan tangadi. Ina tsaye ya zo wucewa ta kusa da ni, na sassauta murya na ce "Sannu Yaya Gudale". Ba zato na ji saukar wan irin marin da ya katse mini ji da gani na wucin gadi. Na durkushe saboda ki'dima, na fashe da kuka sosai. A hanzarce Sakina ta iso kusa da mu tana tambayarsa ba'asin wannan uban marin da ya zabga mini. Bai kulata ba, illa ya bu'de murya yana fa'din "Ashe ba ki ji kashedin da na yi miki na kar ki sake nunawa kin san ni ba?" Ya yi hucin 'bacin rai, ya nisa! Ya ce "Bilhillazi idan kika sake yi mini magana sai kin ga tashin hankali! Na tsane ki, na tsani ko da jin muryar ki ne". Da 'kyar cikin rawar muryar kuka na ce "Na yi nadamar abin da na yi maka plz kar ka yanke zumunci da ni Yaya Gudale". "Tun ranar da kika ci mutuncina, kika tozarta ni, tun lokacin na tsane ki. Ina gargadin ki ki fita harkata if not you will be in trouble". Sakina ta yi sukuri tana nazartar mu, ta kalle ni ta ga na yi la'kwas hawaye na bin fuskata, na fahimci ta fi ni jin zafin marin da ya yi mini. Ta mayar da kallon ta gare shi ta ce, "Namoriki akan me za ka mare ta? Kasan haramun ne duka a fuska musamman ma ta mace baliga". Ya 'kan'kace manyan idanuwansa ya ce, "To ki fa'da mata ta kiyaye ni, na riga na cire ta a sahun 'yan-uwana! Matu'kar kuwa za ta mini magana wallahi sai na yi mata 'barin makauniya. Tunda na gane ba ta da kunya kuma ba ta da mutunci. Wai ni za ta kalli tsabar idona ta ce mini ba ni da zatin da cikakken namiji yake da shi, hakan bai ishe ta ba ta sake danganta ni da sakarai". Sakina ta nisa ta ce, "Namoriki tsakani da Allah bai kamata ka tsananta wannan maganar har haka ba. Ko ni ba zan iya lissafa adadin yadda kake kushe Halimatu ba, za ta yi maka abin arziki ma amma sai ka gwasale ta. Hatta Guduyon da kake kiran ta da shi, ta amsa har yau din nan ba wanda ya san ma'anarsa. Kai ne ke ce mata kumbusa, Sadi bon bon, 'Katuwa, Tu'ke'kiya, Ra'kuma da sauran sunaye na iyashege. Duk da hakan kuma jikinta na rawa take kyautata maka, ni na san ba haka kawai za ta fa'da maka abin da ka ce ta fa'da din ba". A tunzure ya ce, "Duk ina fa'da mata. Shin ni ban girme ta ba? Sannan duk sunayen dana ke fa'da din, fa'da mini guda 'daya wanda ba ta siffantu da shi ba". # Team Gudale # Team Gudiyo # Ana tare 🤝 # Surayya Dee ✍️. 🌺 *SABO DA KAZA* 🌺 *NA* *SURAYYA DAHIRU* ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *Fatan alheri ga wadanan group din, mussaman wadanda suka bani support wajen sayan wannan littafin* *Takorites* *Janaftys* *Khaleesat palace* *Gwaram discussions* *High class women* *Da sauran groups daban daban*. *Na gode madallah Ubangiji ya albarkaci kasuwancinku da 'ya'yanku* *Gudale na jinjina muku, yana bu'katar addu'ar ku*😄 *Son so*🤝 *Ku'din karatu 500 ne. Biya ki karanta cikin nutsuwa da aminci* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank.* *Ki tura shaidar biya ta wannan lambar* *08032773332*. *Page 15-16* Sakina ta ce, "To ka sani ko ka siffantu da abin da ta ce 'din da gaske?" Ya kuwa sake hasala ya ce, "Haba ai ko makaho ya shafa zai san Ubangiji ya kyautata halittata. Baya ga hakan ta ina na zama sakarai?" Sakina ta dubi idonsa ta ce, "Ko ba sakarai ba ne kai, kana yin 'dabi'un sakarkaru domin kuwa babu shakka sakarai ne mai 'dabi'ar 'daga wa mace hannu. Ai namijin duniya ba a ganin 'kwanjinsa da sunan duka sai akan 'kato 'dan-uwansa amma ba mace mai rauni ba". Ya yi shiru a dalilin maganar Sakina ta yi kunnen doki da tawa maganar da na fa'da ta tunzura shi har da kukansa. Jin ya yi shiru, cikin muryar kuka na ce, "Dukana ya yi a ranar shi yasa na fa'da masa hakan, kuma Anti tunda na ba shi ha'kuri ai sai magana ta wuce. Zalina ya ci amma tuni na yafe masa, har ina yi masa magana saboda nasan illar gaba a shari'a". Tausayina ya yi matu'kar kama Sakina ta sunkuyar da kanta 'kasa saboda yadda idanuwanta suka ciko, a dalilin ta riga ta yi amannar na fa'da komar Gudale. Ta gane na gama mutuwa a kansa, irin son da ba jan kunnen da zai yi tasiri. Ta fahimci duk wulakancin da yake mini zuciyata ba ta 'kullatar sa na tsawon lokaci mai yawa. Ta nisa ta ce, "Tunda ta ba ka hakuri

Chapter 5 of 9