Share this page
8 / 9
yi babu shakka ban isa ba, ba ni kuma da mutunci ko ka'dan a idonka". "To shike nan na ha'kura saboda kai, ba zan yi magana ba Baba! Yanzu yaushe zan zo ka kai ni wajen Yayar Kwalli na ba ta ha'kuri?" Baba ya dan yi tari kadan ya ce, ,"To mu bar shi zuwa Juma'a daga Masallaci sai mu wuce. Sannan ina jan hankalinka ka sasanta da 'yan uwanka Al'amin da Sakina". Ya dinga godiya sosai, har ya mi'ke ya sake komawa ya gurfana. Ya kalli irin yadda ya sake gurfana tamkar zai kwanta masa. A ransa ya san wani al'amarin zai sake barowa. Ilai kuwa sai jin sa ya yi yana cewa, "Ka daure Baba ka je ka yi wa Guduyo nasiha yanzu fa gaba'daya ta bijire mini, yau dai kwanaki hudu ke nan da dawowarta amma har yanzu ba maganar arziki a tsakanin mu balle a je ga maganar gyara mini 'dakina". "Kunya ta kama Baban cike da nauyi ya ce, "Je ka zan kira ta a waya". Yana jin haka ya mike da azama yana cewa, "Na tafi to, ka kira fa kafin na isa, so nake ina shiga na gane ka yi magana". Da ido kawai ya bi bayansa yana ta faman yi masa addu'a a zuciyarsa. Domin ya gane akwai abubuwan da ba zai ta'ba dainawa ba. Bai zame ko ina ba sai bangarensu ya tarar da dukkan sisters dinsa suna nan, sun saka Umma a tsakiya a nata dabdala. Ya tsallake ya ratsa tsakiyarsu ya zauna jikin uwarsa. Cike da shagwa'ba ya ce, "Umma shi ne ake wannan dinner din babu ni?" Ba walwala ta ce, "To na sani ko za ta bar ka ka zo, tunda dai na gane ta yi galaba a kanka ta fi karfinka, sun kwace mini kai". Ta fa'da cike da rauni sosai. Cikin tarin soyayya ya ce, "Mai kwace Gudale a hannu Umma ai sai mutuwa, ba dai biladama ba. So nake yanzu ki yafe mini, ki kuma sanya Guduyo cikin jerin 'ya'yanki, matata ce kuma ita ce uwar su Amnah da Aman, ta ci albarkacinmu". Ta nisa ta ce, "To amma da sharadin za ka sake yin aure, har yau Fauziyya tana son ka". Gabansa ya yanke ya fa'di, ya zabura ya tashi a jikinta ya zauna sosai ya ce, "Gaskiya Umma ki yi ha'kuri ba zan sake jawo wa kaina masifa ba, waccan ma da na yi yaya na kwashe ne? Ki yi ha'kuri, a bar wannan maganar kawai don Allah". Sakina da take gefe ta kyalkyale da dariyar iyashege, yayin da su Antin Zaria suke fa'din yaro ya gane Jahar Borno a Arewacin 'kasarmu take". Ya hassalo musamman dariyar da Sakina take faman tintsirawa. Ya ce, "Umma ki ja wa Sakinatu kunne ta fita a harkata! Ba don ina gudun bacin ranki ba da tuni na saka an sakaye mini ita". Ai ko Umma ta hauta da fa'da tana cewa, "Yo Sakina za ta girma ne, tana gudun bacin rai na ne? Kai dai da ka damu da damuwata 'kara ha'kuri da ita kawai, idan ka hadu da dan-uwa mai wuyar zama ai sai dai ka yi ta ha'kuri kawai". Ya mi'ke ya saka hannuwa biyu ya dagata ya ce muje daki akwai abin da zan fa'da miki Umma! Ai kuwa ta bi shi suka bar su a falo. Sai da ya zaunar da ita a bakin gado, sannan ya tsugunna jikin kafafuwanta ya ce, "Na ro'ke ki Umma ki yi ha'kuri, ki sassautawa 'kaddarata! Ki yi hakuri ki karbi Guduyo a matsayin surakarki, ki yi mini alfarmar hakan Umma". Ta fara goge idanuwanta cikin kuka ta ce, "Na yarda zan sassauta mata, amma ka sani idan ka fifita ta a kaina zan janye sassaucin wallahi" Ya ru'ko hannunta ya ce, "Har abada ba ni da kamar ki, ba wata halitta da zan fifita sama da ke, ina ro'kon Ubangiji ya mini tsari da yin hakan". Cikin rarrashi ya ce zan kawo ta gabanki ta baki ha'kuri Umma! Na kuma jaddada mata cewar za ta iya bata mini rai na ha'kura, amma ta'ba ki na nufin fishina mai gigitarwa. Ke kuma sai ki saka mana albarka ki fa'da mata kin amince da zamanmu tare kina farinciki da hakan". Ta ce, "Sharadin haka ta sanya maka?" Da sauri zuciyarsa ta buga, ya aka yi ta harbo jirginsa da sauri? "A a Umma so nake dai kawai a yi afuwa a sassauta ko zuciyoyinmu sa nutsu, nan duniya ke ce cikon farincikina. Idan babu kyakkawar alaka tsakaninki da ita wallahi zan dauwama cikin kaico da nadama." Ya fa'di hakan cikin matsananciyar damuwa saosi. Karon farko da ta yarda za ta yi ha'kuri da Halimatu a matsayin surakarta ba don tana so ba, sai don hakan Gudalenta yake so. Ta nisa ta ce, "To shike nan na amince, amma ka sani yayarku ta ce ta ri'ke su Saudatu! Idan har na ji kun yi magana akan hakan, na san ita ce tunda kowa ya san yadda ta ma'kala su a ranta. Wallahi idan hakan ta faru har kai ma ba za ka ji da'dina ba, bare kuma ita". Da sauri ya ce, "Haba Umma ta isa ma ta fara wannan katobarar? Ke dai Allah ya kara miki lafiya na gode sosai Ubangiji ya shaida na yi godiya sosai Umman Saddi'ku". Suka dawo falo ya kalle su ya ce, "Kowacce ta tashi ta tafi gidanta kun zauna har takwas ta yi." Ya juya ya fice yana jiyo irin carin da suke yi masa. Ya dawo ya tarar da ni a falo ina kallon M.B.C 3 saboda yadda na saba da kallon Cartoons a dalilin su Amnah. Na amsa sallamar da ya yi na ci gaba da kallo na. Ya zauna kusa da ni ya ce, "Baba bai miki waya ba ke nan?" Ban kalle shi ba na ce, "Ya yi mini mana". Ya shige yana cewa, "Ki zo ki same ni, ina son mu tattauna wata muhimimiyar magana". Na tabe baki ina jin a raina kuma na san ba dai na taka dakinsa ba kam". Ina ganin ya shige na tashi na kashe komai na shige nawa dakin na rufe da mukulli. Ina jin sa ba irin sintirin da bai yi ba, ba kalar bugun kofar da bai yi ba, amma fir na ki. Waya kuwa kashe ta na yi. Washegari ya tarar da ni a Study Room! Fuskar nan a daure tam ya ce, "Kin kyauta da kike wulakanta mijin aurenki, ina bin ki ne saboda na san na yi miki laifi amma ke sam kin kafe, kin ci laya. To ki sani wallahi ba zan yarda ba, dole sai kin zo dakina wallahi". Na dago na watsa masa harara na ce, "Sai na ga dolen ai". Ya ce, "Kin gama abin karyawar ko kuwa?" Kai tsaye na ce, "Ba zan yi ba". Ya jijjiga kai ya koma." Ba a jima ba ya dawo cikin Shirin fita, Aman na hannunsa shi ma ya yi masa wanka, sun yi fes da su, kammaninsu guda har rashin jikin. Sai da suka fita sannan na gyra gidan na yi wanka. Ina zauane sai kawai na tsinci kaina da son ci gaba da hararo ba'dakalar da na shiga a baya. *LAIFIN DADI KAREWA* *Karshen Free pages ke nan na wannan kayataccen littafi mai suna _SABO DA KAZA..._ Zan dakatar da yin posting na dan lokaci ka'dan, da zarar kun karbi labarin ta hanyar sayan littafin zan ci gaba da sakar muku shi a Paid Group dina. Ku karanta cikin lumana da salama. Wanda ya yi noma dai ya huta da awo.* *Labarin Guduyo labari ne mai ta'ba zuciya, labarine da dole sai kin ci karo da irin kalar taki matsalar ko kaddarar. Ubangiji ya kara mana ha'kuri da juriya* *Duk wannan bayanin sharar fage ne. Ina tabbatar muku ba za ku yi nadamar saya ba, lallai kwalliya za ta biya kudin sabulu.* *Na san da yawa cikin masoyaba su ya kamata su fadi ba ni ba, to amma kasancewar an ce 'waka a bakin mai ita ta fi dadi.' Sannan kuma akwai sabbin masoya da ba su san littafina mai suna _HALIN YAU_ ba. Don haka ku hanzarta sayen wannan littafi don jin yadda aka haihu a ragaya!* *Bissalam! Sai na ji ku*. # Team Gudale. # Team Guduyo. # Surayya Dee. # One Love Ana Tare!🤝 *Wannan littafin na ku'di ne, ki tura 500 ku'din karatu ta wannan asusun* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank.* *Ki tura shaidar biya ta wannan lambar* *08032773332*. *SDK21&22.* *GODIYA* *Na gode da yadda kuka nuna mini alhinininku na rasuwar mijin 'yar-uwata.* *Masu bugo waya takanas da wandanda suka yi ta'aaziya ta zauren WhatsApp duk na gode muku Allah ya bada lada*. *JAN KUNNE* *Laifi ne babba karanta wannan labarin a kowacce irin sadarwa ba tare da izinin mai hakkin mallaka ba* *TUNASARWA* *FITAR DA LABARIN NAN LAIFI NE DA YAKE DAI-DAI DA SATAR DUKIYA* Ban baro gidan Sakina ba sai washagari da yamma. Da kanta ta kawo ni gida. Muka tarar da Abba da Baba! Zaune a cikin 'yar bukkar zamani da take can gefen harabar gidan. Da azama muka isa gare su, cike da ladabi muka tsugunna, muna 'kwasar gaisuwa. Baba ya mi'ka hannu ya karbi Haydar 'din Sakina da yake kafa'data yana shirin yin barci. Abba ya kalle ta ya ce, "Me kuke tattaunawa ne da 'kanwar taki? Ta fa'da miki wancan yaron da ta turo ba mu amince da shi ba?" Da mamaki ta ce, "A a ko ka'dan ba mu yi maganarsa ba". Ya nisa ya ce, "Ki dinga nusar da ita, al'amarin samari yanzu sai an yi taka tsantsan". Da sauri ta ce, "Ina yi mata Abba! Kawai dai ita din ce na ga tamkar ba ta fahimce ni ba, shi yasa na ce zan zuba mata ido". "A'a Sakina yaushe kuwa kika ta'ba ganin babban da ya san me yake yi ya bar na 'kasansa da dabararsa? Sai dai idan babban kwabo ne, domin kuwa dole sai an yi ha'kuri, an yi juriya sannan a samu kyakkawan sakamako. Don haka ci gaba da nusar da ita, ina tabbatar miki wataran za ta fahimce ki, za ta gane ke din mai girma ce a cikin rayuwarta, ku sata a cikinku Sakina! Bana son a samu 'kofar da za ta gane ita din dabance a cikin ku, ba na son ta ji cewar ba ta da yan'uwa mata". Dukkan mu har Baba jikinmu ya yi laushi da kalaman Abba. A hankali Sakina ta ce, "In sha Allah Abba! Ina tabbatar maka ban taba jin tana da bambanci da su Anti Ramla ba, asalima na fi jin nisha'di idan ina tare da ita a kansu, amma kwanaki na yi mata fa'da, ta kalle ni ta gaya mini maganar da take nufin ita din bare ce a cikinmu". Sai lokacin Baba ya saka baki ya ce, "Ai lamarin Sadiya sai addu'a domin idan ranta ya baci, ko idan tana son abu ba ta iya sassauci ba, yanzu nan sai ta fàdi maganar da za ta janyo mata wahala. Babbar matsalarta ke nan, kafiya da kuma furzar da maganar da ba ta taunawa kafin ta furta". Na yi shiru domin na sani ina da wannan siffar duk da dai kafin na mayar da magana sai an 'kure ni. Amma kafiya kan abin da nake so ko abin da ya yi daidai da ra'ayina ba shakka ba ni da sassauci a nan. Abba ya nisa ya ce, "Ke ce babba Sakina, 'kara yin ha'kuri da ita, ki kuma yi mata adalci a cikin zumuncinku". A sanyaye ta ce "To Abba". Muka mi'ke zuwa shashin Umma. Muka tarar da ita tare da Gudale yana yi mata tausa a dalilin jiya ta dawo kafafuwanta na yi mata ciwo saboda zaman mota. Ba wani karkasashi ta amsa gaisuwarmu. Yayin da Gudale ko kallo ba mu ishe shi ba. Saboda fishi yake da mu sosai. Jimawa ka'dan na mi'ke ina cewa, "bari na je na dawo". Sakina ta mi'ke, ta ce, "mu je na gaida Mama". Girmama mahaifiyata da Sakina take yi yana matu'kar faranta mini, domin kuwa ba yadda za a yi ta zo ta gidan ba ta je ta gai da Mama ba. Haka Antin Zaria sosai take girmama ta. Ba su dauki zugar Ummansu ba, masu taya ta fa'dan Anti Maimuna ce da Juwairiya, musaman Juwairiya da ba ta bar Halin uwarta ba, sa'ar da aka yi ma ba a hannunta ta girma ba. Anti Ramla ce ba'a cika gane alkiblarta ba, domin dai ita a tsaka tsaki take ma'ana ba ta tsananta ba, ba kuma ta yayewa Ummansu zani. Gudale kuwa kusan a hannun Maman ya taso, sannan ba ya yarda da irin wannan gutsuri tsomar na mata. Da zarar Umma ta fara kushe Mama ko fa'din wasu al'amura marasa da'di game da ita. Nan da nan zai ce ki hutar da kanki haka Umma, mene ne Ubangiji bai yi miki ba? Kullum sai na ji kin yi wa kanki 'kirari da cewar uwar 'yaya mata ba ta wofinta, domin sai ka haife ta, ita kuma ta yi maka sanadin zama surukar Gwamna ko Sarki, shin Attajiran suraikai nawa kika tara a dakinki ne? Shikenan sai ya yi tafiyarsa ya barta, tana bin bayansa tana addu'ar Allah ya tsare mata shi da sharrin hatsabiban bayinsa masu yin 'kulunboto don a lalata mutum ya kasa amfana wa kansa bare waninsa ya amfane shi. Domin a cikin sharrin da take bin Mamah da shi, tana zargin ita take yiwa Yaya Sadik asirin da zai sake kangarewa ya zama mara marar amfani, bare ya gane gaskiya ya ture Yaya Abdallah akan dukiyar Abbansa. Ta manta itace kan gaba wajen bada gudumawa a tarin iyashegensa. Domin a gabansa take cewa ya yi duk abin da yake so a gidan, domin Abbansu ne yake ri'ke da komai, duk kuma shigegen da aka yi musu shine magajinsa tilo. Sannan duk cin mutuncin da zai yiwa yayyensa a gabanta, ba tabce masa komai sai dai su yayyen nasa ta danne su ta hanyar cewa "me yasa zaku biyo shi ne? Ku ji tausayinsa mana, ku yi masa ha'kuri watarana shine garkuwarku". Ire iren wadannan kalaman nata da ya taso ya ji tana fa'dan su tamkar karatu, ya taka muhimmiyar rawa a cikin tunanin Yaya Sadik, domin sai yake ganin tamkar 'yaya mata basu da wani alfanu, wahala ake da su a karshe wani ya zo a sama ya daukesu. Hakanan duk yawansu sun zama yiyiwu tunda dai ba sune magadan gida ba, zasu tafi ne su gina rayuwarsu a wani waje daban. Duk hidimar karatunsu da ka aka yi ta yi karshe dai mijintane zai yi kane kane akanta da dukiyarta. Shiyasa yake jin kansa tamkar shine bango a cikin Yan uwan nasa, yake kuma fatan ya haifi 'ya'ya maza fiye da mata. Dan su zame masa garkuwa, ba tare da ya fahimci cewar 'yanu-wansa mata sun fi shi zama alfanu a gidansu ba. Tunda a yau Antin Zaria ta kai 'kololuwar darakta a ma'aikatar E.F.C.C. Aunti Maimuna da ba ta yi karatu sosai ba iyakacinta sakandire, mijinta 'dan majalisar wakilai ne mai ci, daga ita sai yaranta, bata da kishiya shiyasa izzatar ta shahara. Anti Juwairiya kuwa mijinta mai rufin asiri ne, amma ita din lakcara ce a Sa'adatu Rimi College of Education. Anti Ramla mijinta matashin Attajirin 'dan canji ne. Sannan ita din ma'akaciya ce a hukumar rarraba wutar lantarki(KEDCO). Ga kuma 'karamarsu Sakina babbar nurse ce a 'bangaren yara mai mu'kamin metron. Hakanan mjinta attajirin 'dan kasuwa ne 'da a wajen hamshakin attaajiri, domin kuwa aminin Abba ne mahaifinsa. Duk wannan alfarmomin da 'yaya matan nata suke da ita a gidan da suka kere 'ya'ya mazan Maman da suka tsaya mata a rai baisa Umma ta fahimci cewar kowanne 'da da arzikinsa yake zuwa duniya ba. Fatan da za'a yi kawai a samu mai albarka kowanne irin jinsi aka samu a zama cikin godiya kawai. Sannan namijin da ta yi imanin shine bango kuma garkuwa har yau din nan baya ta'buka komai na tallafin gida, sai dai ya tsoma biyar ya wanke goma. Ba abin da yafi 'kwarewa sai ya hau mota mai tsada, ya sanya sutura mai tsada, ya kuma ri'ke waya tsaleliya. Dole kuma ayi masa hakan domin idan Abba bai yi masa ba. A fili Umma take cewa 'ya'yanta duk mai son ya faranta mata to ya kyautatawa Gudalenta. Ita ta yafe musu yi mata komai. Kawai su yi wa Gudale bai kamata a ce duk yawansu da damar da suke da ita a ce sun bar shi ya koka ba, ai watarana shi ne majibancinsu dan haka dole su cicciba shi ya tsaya.Tunda an yi sa'a ya yarda ya yi karatun to ita ta gode masa. Ko sai yaushe zai tsaya din? *AMYAS NEW & FAIRLY ITEMS* *Muna siyan kayan katako na hannu* *Muna siyan kayan electronics. Dangin fridge da talabijin na hannu* *Muna kuma sayarwa mai bukatar kaya second masu kyau.* *Haka nan muna saida atamfofi da lesina zababbu, cikin farashi mai rahusa* *Tuntu'be mu a wannan lambar dan ki sayar mana ko mu siyar miki da kaya cikin aminci da rangwame*. *08083909947*. Wannan gatan da yake da shi shi yasa ya zarta Al'amin da Abbas daukar ido da jin kai. Sai dai kuma duk da hakan tare suke yin komai bashi da kuma da wanda suka fisu duk da yana da abokansa na yaran masu kudi daban. Amma Al'amin na daban ne, duk kuwa da yadda suke tashi sama su fa'do a kullum. Dan ma Yaya Al'amin mai ha'kuri ne, sannan ba shi da riko, kawai Yaya Gudalen ne wuyar zamansa ta kai 'kurewa. Tun zuwan da ya yi gidan Sakina ban yarda na biyo shi ba har karo biyu, shike nan ya dauki zafi da ni sosai. Bare kuma Sakina da ya jefa ta sahun masu nuna masa iyaka alhalin ba ta isa ba. * Bayan Sati biyu * Har zuwa wannan lokacin bai karbi tuban da nake ta bibiyarsa ina yi ba. Gaba'daya ya fititikke tamkar wanda na zagi Ummansa akan idonsa. Ya ce, "Har abada ya yafe zumuncin da yake tsakaninsa da ni, tunda na nuna Sakina ce mutum dan tana da ku'di, mijinta ma ya tara dukiya. Shi yasa bini-bini ina gindinta tamkar alakar da take tsakanina da ita ba ita ce alakar da ta hada ni da su ba. Dan haka ko zaki kukan jini na kunce da ke". Na yi shiru ina jin maganganunsa. Ba tare da na tanka masa ba. Washari kuma ya tafi Niger yin wani reserch akan wani darasin inda zasu 'dan kwana biyu. Ranar lahadin da ta yi dai dai da ashirin da biyar ga watan Satumba, tana cikin jerin ranakun da ba na mantawa da su, ba don komai ba sai a wannan ranar na yi wa kaina kasssabar da ta zame mini *Baya ba Zani* *(FADILA LAMI'DO)* Da hantsi na isa falon Abba don na gaishe shi bisa al'adarsa. Idan ya karya karfe goma, sai ya zauna har zuwa sha biyu don ya gaisa da dukkan ahalin gidan, haka nan duk mai son ganin sa yana sauararon kowa a irin wannan lokacin ne. Na zauna kusa da kujerar da yake kai daga kasa. Cikin rarrashi da nuna kulawa ya ce, "Da a ce zan yi miki zabi ki karba Sadiya da na zaba miki mijin da ba za ki koka ba. Na matsu kwarai a yi aurenki! Ba na son na yi miki dole a dalilin ba wacce na yi wa dole a cikin 'yan-uwanki. Hakkin uba ne ya zaba wa budurwa miji, amma saboda a samu kwanciyar hankali ake ba ku damar ku zaba da kanku. Shin idan na ce na yi miki miji za ki dauke ni a mai son kai?" Da sauri na ce, "Har abada Abba ba ka da son zuciya, ba kuma za ka fara a kaina ba. Zan amince in sha Allah don na san ba za ka kai ni inda zan yi kaico ba". Na fa'da zuciyata tana bugawa domin kuwa ban san wanda zai ce ba, sai dai kam ba zan karbi Anas ba, sannan ya zan yi ne da son autan Umma da ya mini shigar sauri? Kamar a sama na jiyo muryar Abba yana sanya mini albarka saboda da'din lafazina da ya ji. Ya nisa ya ce "Abbas na za'ba miki Halimatu." Nan da nan na ce "Abba Yaya Abbas yana da wacce yake so fa". Kai tsaye ya ce "Tunda bai kawo maganar gabana ba to kuwa babu ita a wajena". Tashin hankali ya bayyana a jikina da rawar murya na ce "Yar kanwar mahaifiyata yake so har sun fara magana Abba! Ina rokon ka canja mini da waninsa saboda gujewa fitinar da zata biyo baya a zumuncin iyayen mu". Ya yi shiru da alamun maganar ta shige shi ainun. Ya yi gyaran murya ya ce, "To shike nan na canja miki shi da Ashir domin shi ma yaron akwai nutsuwa sannan akwai zuciyar neman na kai jarumi ne kwarai da gaske" . Ban san ya aka yi ba sai kawai na fashe da kuka ina cewa "Na fi shi tsayi fa Abba". A sanyaye Abban ya ce, "Na dai lura amincewa ne da zabina ba za ki yi ba saboda ba kya son auren kin fi son ki zauna ku yi ta shiririta da Sadik, lokacinki yana ta tafiya a banza. Banda kema kin baci da iyashege ta ina kika fi Ashir tsayi? Kina so ki ce mini kin fi Sadik tsayi ne? Sai dai ku yi taya, tunda tsayinsu daya da Sadik din". Ya yi shiru sai kuma ya ce "mu kaddara ma kinfi shi tsayin, shin a goshi zaki makala shi ne?" Na kasa magana saboda kuka nake yi sosai. A raunane ya ce mini, "Bar kukan haka, tashi ki yi tafiyarki na janye". Na kasa tafiya tsawon lokaci kafin na ce, "Don Allah Abba ka yi ha'kuri ba abin da ka yi zato ba ne". Ya nisa ya ce, "Idan ban yi ha'kuri ba me zan yi ne Halima? Ba za ki gane fargabar da nake ciki ba ne akan al'amarinki. Musamman idan ina

Chapter 8 of 9