Share this page
7 / 9
har na tsargu. Ta nisa ta ce mini "A kar'bar sakon ne har da sake gyara fuskarki?" Ta ja mayafinta tana cewa, "Mu je na raka ki". Gabana ya yanke ya fa'di na diririce. Hakan da ta gani yasa ta gane komai ta ce wato "Namoriki akwai fitinannen mutum". Kan dole muka fita! Yana zaune cikin motarsa ta alfarma. Ganin mu tare ya sanya ya sauke gilashin motar ya ce, "Na shiga uku ni Saddi'ku". Sakina ta daure fuska ta ce, "Duk tsiyarka ba inda za ta tafi, kuma wallahi sai na fa'da wa Abba wannan bibikon da kake yi, sam-sam ban yarda da kai ba". "A wulakance ya ce, "Yadda na shaida Allah daya ne haka na shaida ke din masharranciya ce, dadin abin ma abin da ya ha'da ki da Guduyo shi ya hada ni da ita bare ki nuna mini kin fi ni kusa da ita, mai shisshigi da cusa kai". "Ka kiyaye ni Namoriki" Sakina ta fa'da tana nuna masa yatsa. A kausashe ya ce, "Ai tun jiya na kiyaye ki Sakina! Tunda na gane jarumin namiji irin Yunus amma a hannunki yake ai dole a nemi tsari da tsiya mai wasali irin taki". Ta kalle ni ta ce, "Shige mu tafi munafukar banza marar kunya". Na shige na bar ta a tsaye. Na labe a jikin gate din. Na ji yo tana cewa, "Wallahi sai na yi maganin wannan girman kan naka, ba za ka ta'ba samun sassauci a wajena ba har sai ka fito a mutum, ka bayyana kyakkawar manufa akan Halimatu. Idan ba hakan ba kuwa, wallahi ka rubuta ka ajiye ba ka ga komai a irin tsiya da makircin da kake danganta mini su ba. Da ikon Ubangiji sai na kai ka 'kasa Namoriki". *Kina neman jakadiyar oriflame ta kwarai?* *Kina son mayuka da zasu face da launin fatarki a wannan lokacin na sanyi?* *Kina son 'kamshin na alfarma?* *Albishirinki indai harkar kayan kwalliya ne ma kece raini. Kina bu'katar ki zama Iya Basiru dawisu sarkim ado?* *Kawai tuntu'bi Aisha lame* *A wannan lambar 07036662633* A zafafe ya ce, "Da gaskiyar Umma da take fa'din an canja mata ke a asibiti, nononta da kika sha ne ya sanya kika rikide kika samu kammaninmu, amma kyakkawar siffar da aka yi miki, aka kuma yi miki mummunar zuciya irin ta kafiran Turawa masu ra'ayin ri'ko ya isa ya tabbatar mini ke din dangin su Ifiriti Minal Jinni ce amma ba jinin Malam Habu da Saude ba". Dariya ta kwace mini, na yi maza na rufe bakin nawa. Tsakin da Sakina ta ja mai 'karfi ne ya taimaka dariyar ta tsaya mini cak. Ta ce, "Komai za ka fa'da bai dame ni ba. All I know Halimatu ba za ta tafi ba sai gobe, kuma rashin kunyar da ka mini ba za ta ta fi a banza ba, sai ka gane ni ba su Antin Zaria ba ce". Da sauri na ruga na yi cikin gidan saboda na jiyo takunta. Yayin da haushinta ya mamaye zuciyarsa domin so ya yi ya ba'de ta da 'kurar tayar mota. Sai kuma ta riga shi barin wajen, abin da ya fi tsana ke nan ana cikin magana a tafi a bar shi. *AMYAS NEW & FAIRLY ITEMS* *komai da ruwanka ne su* *Ina amare yan kwalisa?* *Ina matan da suke son su yi canjin kayan daki?* *Ina matan da suke son kayan daki na hannu masu aminci?* *Kina son saida wayar hannunki, ko kuwa siya kike son yi?* *Kina neman electronics tuwaris, ko kuma ke ce zaki fitar da na ki?* *Kawai ki tuntu'be su ina tabbatar miki zaki samu komai daidai da bu'katar ki cikin rahusa* *08083909947.* Wannan al'amarin yana cikin abin da ba na mantawa domin a ranar yini muka yi Sakina na mini gorin rashin aji, tana habaicin mazan yanzu ma sun sha wahala kafin su aure ka amma suke wulakanci son ransu, ina kuma ga wanda ya gane son sa ake tamkar rai, alhalin shi bai ta'ba furta kalmar so ba? Na sani sarai da ni take, sai na yi sukuri, na kasa cewa komai. Iyaka dai na gane so take yi na ba ta ha'din kai, na daina nuna zakuwata akan lamarin Gudale. Na kuma gaskatata cewar bai fi ni a wajenta ba, domin kishina take yi muraran, so take yi na yi daraja a wajensa. Har yau din nan da nake ganin ta yi mini laifi na sani, ita din wata irin mace ce mai kyautata zumunci, ba abin da ba ta yi mini ba, duk wani kukan da na yi tare muke yin sa. Na tabbatar mahaifana biyu ne kawai suka mini abubuwan alheri da ya zarce wanda Sakina da mahaifinsu suka mini. Madalla da Abbahl! Madalla da Sakina! *** Na nisa na kalli agogo a dalilin na ji har an fara kiran sallar Maghrib, ashe na shafe lokaci ina tunanin rayuwata? Duk da dai har yanzu sharar fage ne, ban shiga cikin gundarin labarina ba, labarin rayuwar aurena, sunan wani littafin 'kanwata *(Ayusher Muhd)*. Rayuwa mai tarin kalubale, mai rikita-rikita da tashin hankali. Na mi'ke ina cewa, "Sai na sake samun zama zan ci gaba da yin waiwaye domin na auna kalubalen da na fuskanta, na sake jinjinawa kaina ba don komai ba sai don na san ni da kaina na yi jarumta, na jure al'amura masu nauyi, ta yadda za'a dinga ganin wauta da rashin kamun kaina. Ba kowa zai fahimci ne ba, ba kowa zai mini uzziri ba, haka nan ba kowa ne zai mini adalci ba. Sai masu fahimta, sai kuma matan da suka shiga irin al'amarin da na shiga. Sai an ji irin *Halin Yau* din da na fuskanta. Za'a gaskata azancin nan na *SABO DA KAZA* ba ya hana a yanka ta. Allah ya 'karawa mata ha'kuri da juriya a gidajen aurensu. Allah ya taimaki duk namijin da yake kyautata wa matansa, yake kokarin yin adalci, yake kuma sauke dukkan nauyin da yake kansa babu 'kwange, babu gajiya. Madalla da mazan da ba sa muzanta matan aurensu! Madalla da mazan da ba sa zaben jinsin da suke son a haifa musu. Madallah da maza masu sassauci da tausayin mace. *Ku hanzarta biyan ku'dinku dan kada a katse muku Jin wannan dambarwar* 🥰 # Team Gudale! # Team Guduyo! # Surayya Dee! # One love 🤝. 🌺 *SABO DA KAZA* 🌺 *NA* *SURAYYA DAHIRU* ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://www.facebook.com/profile.php?id=100069755834980 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *Assalamu alaikum sister's! Hakika na gode wa Ubangiji! Na kuma gode muku! Masu bibiyar wannan littafin ga'ba daya, mussaman wandada Suka saya da masu Shirin saya.* *Cikin yardar Allah free pages ya kammala a yau, bisa goyon bayanku da kuma horewar Mahallicinmu*. *Zan dakatar da posting na dan lokaci kalilan ina fatan zaku taimakawa kasuwa cina ta hanyar rufe kofar fitar mini da paid pages*. *Na gode sosai Ubangiji ya sanya na cika al'kawari, Allah ya sanya na gama muku lafiya, ina muku fatan a yi karatun lafiya cikin nisha'di.* *Gudale ya ce za'a yi fashin posting sau daya a sati. A da sau biyu za'a yi fashin, Amma soayyar da kuka nuna mini sai na 'Kara muku daya. Ina addu'ar Allah ya albarkace mu gaba'daya*🥰 *Biya 500 kudin karatu ta wannan asusun* *2384876855* *Surayya Ibrahim* *Zenith Bank.* *Sai a turo shaidar biya ta wannan lambar* *08032773332*. *Last free page* *Page 19&20* present. Na idar da sallah ina zaune a kan sallayar ina tunanin anya kuwa zan iya ha'kuri na yafe wa Gudale tamkar yadda ake so? Hawaye mai zafi ya 'balle mini. Tsakani da Allah ba abin da nake so irin ya fita a cikin rayuwata tun bai 'karasa kassara ni da ba'kin-cikinsa ba. A hakan ya shigo ya tarar da ni yana sa'be da Aman! A sanyaye ya zauna akan gado. Aman sai zillo yake na dauke shi amma na yi kememe na yi kamar ban gan shi ba. A sanyaye ya ce, "Halah! Kin ji Antin Zaria wai ba za ta ba mu su Amnah ba. Ta ri'ke su ke nan, ba za ta bayar ba sai idan ke ce kika ce sai ta ba ki 'ya'yanki! Don Allah ki daure ki tashi mu je ki nuna mata kina bu'katar su a tare da ke". Na dago idanuwana da suka kumbura na zuba masa. Na ce, "Akan me zan ce ta ba ni su alhalin na san a can ne za su samu gata da kulawa? Akan me zan dawo da su inda ake kallon su a marasa amfani? Har abada ba zan ta'ba iya wannan butulcin ba". Ya yi shiru, jikinsa ya sake yin sanyi. Tsawon lokaci dakin ya dauki ka'daici Sautin magana, sai motsin Aman da yake ta gwalantun da ba a fahimtar komai domin watansa goma sha biyar kacal. Cikin karfin hali ya ce, "Bari na watsa ruwa ki raka ni unguwa, don Allah ki shirya kafin na fito." Ya fa'da tare da miko mini Aman. Na yi funfurunfus na ki karbarsa. Ya sassauta murya ya ce, "Please my dear Halah! Wannan halayyar ba dabi'arki ba ce". Na galla masa harara na ce, "Akan me zan karbe shi alhalin ba ni ya kamata na zama uwarsa ba?" Ya yi turus yana kallona. Ya saki ajiyar zuciya ya ce, "Na sani ni mai laifi ne Guduyo! Amma na ce ki yi ha'kuri, ya kamata ki mini afuwa". Zuciya 'daya na ce, "Ka sawwake mini, domin idan ina kallon ka ba zan yafe maka ba". Amma da zarar ka sahale mini wannan kadaddararren zaman da babu komai a cikinsa sai ba'kin ciki, to kawai ka ji a ranka na yafe maka" . Ya hassalo ya ce, "Na rantse da Ubangiji sai na ci mutuncin Sakina, hatsabibiya marar mutunci! Na sani ita ce kanwa uwar ha'din wannan tashin hankalin da nake fuskanta, wato ba za ta daina tsoma mini baki a gidana ba?" A dake na ce, "Ahaf da ma na san kana nan da halinka, nan da kwanaki biyu za ka ci gaba da wula'kanta ni yadda ka saba. Akan idona kake zagin Sakina? Ina ce an riga an raba yar'uwata ce ba taka ba, kana cin mutuncin dangina, kuma kake tunanin zan yarda ka canja?" "Na ba ki hakuri dai, saboda na san ban kyautata miki ba. Amma tunda kin yarda da keken 'beran da take 'dora ki a kai ai shike nan. Sanin kowa ne Sakina ba ta nufina da alheri! Babban burinta ta kashe mini aure, ta 'dai'daita mini zaman lafiya a gidana, ta raba ni da kwanciyar hankali, ita dai ta gan ni a cikin tasku shi ne burinta". Ya fa'da yana haki saboda tsananin bacin rai. Na kalle shi ina mamakin da bai fahimci irin 'kaunar da Sakina take yi masa kwatankwacin irin son da take yi mini ne. Domin ni kaina ban yi zaton tana son sa har hakan ba, sai a yanzu da ta dawo da ni gidansa. Tunda nake da ita a wannan karon na ga laifinta har zuciyata. Saboda zarginta da son kai da ta nuna a tsakaninmu. Duk da dai zuciya ce da ba ta da 'kashi ta sa na yi wannan hasashen, domin ba abin da Sakina ba ta yi mini na alheri ba. Ta dauki ba'kin jini a cikin yan'uwanta, hatta mahaifiyarta sai da ta kusan sallama ta saboda ni. Amma hakan bai saka ta juya mini baya ba, ta tsaya mini, ta yi fito na fito da duk wanda yake son shatale ni. Take na ji kunyar yadda na nemi manta tarin alhairan da ta wanzu tana yi mini tun ina tsumman goyo. Har yau su Amnah ba su san cewa yayar Babansu ba ce, sun dauka yayata ce. Saboda tsananin kirkinta gare ni. Na kalle shi na ce, "Ba inda za ni, ina jin nauyin na fita da kai, a ce kai mijina ne, gaba'daya nawa kake da za ka zame mini miji?" Ba'kin cikin maganar da na yi ta kama shi. Ya tunzura ainun ya fice tare da buga kofar dakin da 'karfin gaske. Mintina ka'dan ya fito sanye cikin yadi mai tsada kalar shudin samaniya, ya 'dora hula shudiya sosai, ma'ana shudin ya ciza. Har yanzu da muka yi shekaru bakwai da aure, yana nan ba jiki, sai dai ya 'dan murje ka'dan, irin dai murjewar da Ramadan Both ya yi a yanzu. Ya yi kyau sosai! Sai 'kamshin tsadadden turaren maza na Cris Adam's yake tashi tamkar a dakin ya fesa. Ya sassauta murya sosai ya ce "Har na shirya amma kina zaune?" Na yi shiru na ki tankawa bare na ba shi amsa. Ya nisa ya ce "Wajen Baba zan je na yi tuba da neman afuwa, so nake mu je ki raka ni, ya gan mu tare don ya fahimci mun shirya kanmu". Yana rufe baki na ce, "Indai sai ya gan mu tare ne, zai gane mun shirya to kuwa ba zai taba ganewa ba". Ya tsaya cak, kallo mai tsanani yake yi mini. Na yi kamar ban ga yana kallona ba, na sake cewa "Kai yanzu sai ka iya zuwa gaban Baba da nufin gaisuwa ko wata magana?" Ba fargaba ya ce, "To ba Babana ba ne?" Ido cikin ido na ce, "Babana da Al'amin dai". "Tunda dai ya sanya an dawo mini da ke kam ai Babana ne, amma da ya ci gaba da zuba ido ana mini rashin mutunci da iko a gidana tabbas zan yi fiye abin da na yi din". Cikin 'daga murya na ce, "Ai na sani mrashin arzikinka ya kere tunanina. Ban da rashin kunya har ka iya zuwa gabansa, bayan duk cin zarafin da ka yi masa?" Ya fesar da zazzafar iskar bacin rai. Ya ce, "Ubangiji ka shaida na yafe wa Halah! Kar a kamata da laifin 'daga harshenta akan nawa". Ya fita da sanyin jiki. Har ya kai 'kofar fita daga falo, sai kuma ya dawo ya ce, "Na bar Aman yana barci a 'daki ki taimake ni, ki kula da shi". Yana rufe baki na ce, "Ba zan kula da shi din ba, domin ni ban siffantu da rainon yara maza ba". Ya sassauta murya sosai ya ce, "Abba ne fa". Na sunkuyar da kai kasa domin dai kam ban dauki lamarin duk abin da ya shafi Abba da sau'ki ba. Ni shaida ce ta yadda ya shafe rayuwarsa yana tiritiri da zumunci musamman ma alhalin gidanmu. Abba haifar mahaifinmu ne kawai bai yi ba, amma ba abin da da bai yi masa ba. Dukkan haihuwar da mahaifinmu ya yi, bai ta'ba sayan ragon suna ba. Bai ta'ba biyan ku'din makarantarmu ba, ko kayan abinci Babanmu bai san ya saya ba, domin tare Abba yake sauke musu da na gidansa, ko ashana katon guda za a kawo. Bai kuma ta'ba gajiya ko ya nuna alamun mulkin mallaka ga Babanmu ba, haka nan wani mahalu'kin bai ta'ba ji a bakinsa shi yake hidima da iyalin 'dan uwansa ba. Sannan nan Umma mai 'dakinsa za ta yi komai ta kwashe 'kalau, amma matu'kar za ta ta'ba ahalin mahaifinmu a nan take ganin taskunsa. Har igiyar aurenta guda ta ta'ba tsinkewa saboda izgilin da take yawan yi wa Mama. Hakan ya sake kambama kiyayyar da take yi mana. Ta kuma kafe akan asiri mahaifiyarmu take yi. Wadannan halayen girma na Abba da kyautatawarsa ya sanya nake girmama shi da dukkan zuciyata, ko mai irin sunansa na gani a hanya sai na girmama shi, ta hanyar cewa Babana. Idan kuma na ga mutumin mabukaci ne, sai na tallafa masa ko da idan na bayar din zan takura. A sanyaye na ce, "To zan duba maka shi kafin ka dawo". Ya marairaice ya ce, "So nake ki kula da shi muddin rai, ki kula da shi tamkar su Afrah". Da sauri na dinga girgiza kaina tabbacin ban amince ba. Na dora da cewa, "Ai ba 'daya suke ba, don haka ba za su samu kulawa iri 'daya ba, domin kai ma shaida ne ba su samu kulawarka, irin yadda ya samu ba". Ya rasa bakin magana, ya buge da cewa, "Shike nan hakan ma na gode" Ya juya ya fice. Kai tsaye cikin gida ya nufa, ya zarce shashinmu! Ya shiga ya gaisa da Mama a dakinta, ya wuce falon Baba. Sai da ya je gaban Baba sosai sannan ya durkusa, ya fara gaishe shi. Ya amsa ba yabo, ba fallasa. Tsawon lokaci yana gurfane, ya kasa magana domin sai da ya zo gaban Baban ya gane girman rashin mutuncin da ya yi masa. A sanyaye ya ce, "Baba ka dubi Allah ka yi mini ha'kuri. Ni kaina na san na yi maka ba daidai ba, wallahi tsananin tashin hankali da fargabar kar na rasa aurena ne ya sanya na yi abin da na yi din. Amma na yi nadama, don Allah ka yi hakuri ka yafe mini". Tsawon lokaci bai ji amsa ba, ya sani laifukansa sun tsananta, masu wahalar a yi afuwa cikin sau'ki ne. Ya sake sunkuyar da kai kasa yana cewa, "Baba daurewa zaka yi, ka karbi tubana indai ba so kake hakkinka ya sake damalmala mini lamaruna ba". Sai a lokacin Baban ya saki ajiyar zuciya mai nauyi ya ce "Idan ban yi ha'kuri ba na yi ya ya da kai? Ai duk abin da ka fa'da ko ka yi mini ai gaskiyar lamarin ke nan". Cikin nauyi sosai Gudale ya ce, "Ni dai Baba ka yi mini afuwa. Na yi tuba, a mini sassauci don Àllah". Ya nisa ya ce "Sadik ba abin da za ka yi mini a duniya da zai saka na fita daga al'amarinka! Kawai abu daya ne matu'kar ba ka yi ba, ni kuma ba ka isa na yi maka ba. Ba komai ba ne illa gaisuwa, indai har za ka gan ni ka dauke kai to ni kuwa ba ka isa na gaishe ka ba. Inka dauke wannan komai iyashegenka ai dole na yi hakuri tunda Ubangiji ne ya ba ni kai, kuma kamar yadda ka fa'da mini cewa mahaifinka ba abin da bai yi mini ba, tabbas haka ne ba na inkarin hakan, ban kuma ji zafin furucinka ba, domin ko mahaifinmu kawai ya haife ni ne, amma Alhaji shi ne komai nawa". Kunyar duniya ta kama Sadik yana tuno lokacin da ya tsaya a gaban 'kanin mahaifin nasa yana zazzaga masa dibar albarka. Ya dinga jin tamkar 'kasa ta tsage ya shige, tunda ba zai yiwu ya dawo da baya ya goge waccan ta'asar ba. "Ni dai ka yi ha'kuri Baba! Na sani ni mai laifi ne". Ya fa'di hakan cikin matsananciyar kunya. Ya zuba wa Sadik din da yake gurfane ido, yana jin tarin 'kaunarsa, yana sake jin alhinin rashin 'dan uwansa, ya tuna maganganun Abba da ya yi ta yi masa mafi yawa akan Sadik ne. Tabbas da a ce kowanne 'da halin mahaifinsa yake yi da ya bugi kirji ya ce Sadik sai ya fi kowa more kyawawan dabi'u. Sai dai kash, muna cikin wani irin zamanin da yara suke zama masu dabi'u irin na albasa. Ya nisa ya ce, "Tun tuni na yafe maka Sadik! Idan na ce ban ji zafin abin da ka yi ba na yi 'karya, idan na ce hankalina bai tashi ba, nan na yi munafunci. Sai dai na koma na auna maganganunka sai nake tuhumar kaina ko dai da gaske na yi son kai din? Na gaskata ka, tabbas da Alhaji ne ba zai daga ido ya yi magana akan ka ba, bare ya nuna an zalunce ka saboda tsananin kara da inganta zumunci." Daidai lokacin hawaye ya 'balle masa ya janyo tissue ya hau gogewa. Da rawar murya ya ce, "Har cikin zuciyata na yafe maka, ina fatan Ubangiji ya bude maka zuciya ka fahimci gaskiya, babbar damuwata da fargabar da nake ciki akan lamarinka guda 'daya ne. Yanzu Ubangiji ma ba zavka kiyayi ta'ba shi ba ? Ya maka baiwa kala-kala, ya ba ka rai, ya yi ka a Musulmi, ya ba ka lafiyar ji da gani. Sannan ya ba ka lafiyar cin duk nau'in abincin da kake so, ya ba ka damar zuwa bandaki da kanka ka yi lalurarka salin alin. Bugu da 'kari ya ba ka mace ta gari da take yi maka wani irin so da ko a wasan kwaikwaiyo yana wahalar samuwa. Ya azurta ka da lafiyayyen abin hawa, ya backa yalwataccen gida. Haka nan ya ba ka iyaye da dangi da kowa hankalinsa a kanka yake. Sannan ya ba ka haihuwa da wasu kullum a cikin kukan rashinta suke, wasu suna can, suna kashe ma'kudan kudade don neman maganin da zasu samu haihuwar". Ya yi shiru saboda yadda kuka ya sake zuwa masa. Tsawon lokaci Baban yana share hawaye, yayin da Uban gayyar idonsa ya cika taf da 'kwalla, jikinsa ya mutu murus, nadama ta sake kama shi. Da rawar murya Baba ya ce, "Sadik fa'da mini da bakinka me ya kamata ka yi wa Ubangijinka bisa wannan tarin falalar da ya yi maka? Don ya san kai bawa ne mai godiya". Cikin rauni sosai ya ce, "Kamata ya yi na kasance mai yawan godiya da tuba izuwa gare shi, sannan na kiyaye ka'idojin shari'a na girmama dokokin da aka gindaya, bayan haka na karbi duk abin da ya yi mini da hannu biyu ko da kuwa ba hakan nake so na ga ni ba". Baba ya ji dadi ya ce, "To mene ne ya hau kanka da kake yi wa Ubangijinka izgilin ba 'ya'ya mata kake so ba? Mene ne ya yi maka da'di wajen musgunawa matarka don kawai ta haifi mata, tunda na san kana son ta". Da sauri Sadik ya ce, "Alhamdulillah! Ubangijina yana mutunta ni Baba! Na gode masa da ya fahimtar da kai ina son Gudidina tamkar rai. Amma Sakina da Al'amin sun shigo mini cikin gida sun yi mini kane-kane sun hana ni damata ta mai gida. Da.ma bayan tuban da zan yi a gabanka, har da 'kararsu na kawo, ka fa'da musu su fita a harkar gidana idan kuwa ba haka ba Billahillazi kotu ce za ta raba ni da duk wanda ya sake shigar mini gida a cikinsu, munafukai azzalaumai yan ta'adda masu zuwa lahi..." Tsawar da Baba ya buga masa ce ta saka ya katse maganar ba don ya kammala ba. "Kai! Saurare ni mashiriricin banza marar kunyar wofi! A gabana kake wannan kalaman bayan ka ce tuba ka zo yi. Wanne irin tuba ne? Amma dai tuban muzuru ko?" Ya yi shiru ya kasa ba shi amsa. "Yanzu ashe ba duka ka ajiye makaman naka ba Sadik? Ina cikin fa'da maka irin rashin da'ar da ka yi wa Mahallicinka, sai ka katse ni ta hanyar kawo wata magana da babu komai a cikinta sai shiririta da rashin fahimta. Kasan irin son da Al'amin da Sakina suke maka kuwa?" Da sauri ya ce, "Na rantse Baba duk duniya su ne makiyana, ba su da buri irin su gan ni ina cikin ragaita da tagayyara. Na riga na shata jan layi da su. Ni kuwa mai za su mini a duniya? Wai su ne za su dauke mini mata, su boye ta, su koya mata yi mini tijara sannan a ce su masoyana ne? Ai kuwa Allah wadaran wannan son da suke yi mini da babu komai a cikinsa sai zalunci". "To yanzu dai na daina yi maka nasihar tunda ba shiga take yi ba ko?" Baba ya tambaye shi a raunane. "Ci gaba Baba ina jin ka! Ai tuni na yi wa Allah kuka a cikin sujjadda, na ro'ki shi gafara. Sannan ai na daina, da ma namijin nake kulafacin samu to an same shi, me ya rage ban da a yi godiya? Kuma Wallahi Baba nake fa'da maka, ba 'karamin son su Amna nake yi ba ashe? Ban fahimci hakan ba sai da waccan ta Zarian ta kwashe su, yanzu kuma don mulkin mallaka wai ba za ta dawo da su ba. Shin an ta'ba yin haka ne Baba? Ni ba yarda zan yi ba, kawai jira nake mu gama shiryota da Gudidina. Wallahi sai an ba ni 'ya'yana tunda ta ce ba za ta bayar ba sai ta ji a bakin uwarsu". Mamaki ya cika zuciyar Baba ya ce, "Waton da zarar ta huce za ka saka ta yi rashin mutunci kamar yadda ka saba ko? To na rantse maka da Allah umarni na ba ka kar ka kuskura ka yi wannan maganar idan kuwa ka

Chapter 7 of 9