Share this page
sending kudaden wasu kuma suka tura, abinda be isa ba za'a cika a asusun kungiya. Compound din building din tuni ya cika da kayayyaki, kayan masarufi, kayan amfanin mata kama daga kan sabulai da turarukan wanka, kayan sawa, mayukan gyaran fata da gyaran gashi, takalma, kai abubuwa dai da yawa da mace zata bukata na gyara daga wajen mijin ya, ba mutum daya ne ya kawo ba, kowannen su kan zo da abinda Allah ya hore mishi ne in aka hada se a raba, suna yin hakan ne dan ragewa mata takaicin namiji da wani baze iya bada kudin gyaran jiki ko wani gyaran gashi ba, musamman ma masu irin matsalar su da mata ke kallon basu kudin gyara ko wani abu as a waste of resource. Kowanne ka kalla fuska cike da farin ciki ana wasa ana dariya suka rabu, Falmata cikin ranta bata ji dadin yadda abun ya zo mata cikin rashin kuɗi ba sai dai taji dadin yadda yar uwar ta kuma aminiyar ta Farida ta rufa mata asiri domin kuwa ashe kayan masarufi ne cike damkan a bayan motar ta bayar da sunan Falmata. Gida ta mai da ta bayan sun zagaya gari duk saboda tayi lightening mood din Falmata wadda duk abinda Farida ke yi ta na ankare haka kuma zuciyar ta cike take da matukar godiya ga Allah bisa kyautar wannan rai mafi tsananin so, kulawa hadi da tausayi gare ta, bata san me yasa ba se take jin wani matsananciyar kewar Faridan tare da ita duk da gata a gefen ta suna tare. Har bedroom Farida ta rakata, duk yadda take fada mata ita fa lafiyar ta lau bata bar ta ba se da tayi wanka ta canja kaya gaban ta ta ci abinci sannan ta kwanta kana hankalin Farida ya kwanta har ta iya ta mata sallama ta tafi nata gidan. Kallon Hassana tayi dake zazzage karamar akwatin yan kunnen ta, wani babban saiti ta dauka me hade da awarwaro, zobe, sarkar kafa da kuma zobe, jujjuya su tayi kana ta dauka ta sa a handbag din ta dake gefen ta kana ta umarce ta ta maida ragowar, cike da dimbin mamaki Hussaina ke kallon ta wanda duk Farida na hankalce amma se ta nuna kamar bata gani ba ta mike tare da nufar bedroom din ta tana umartar Hussaina da ta bi bayan yar uwar ta su kwanta se kuma gobe, haka dole ba dan taso ba Hussaina ta yi dakin su ranta cike fa mamakin me maman ta zata yi da babbar sarkar auren ta, sarkar da iya rayuwar ta zata iya fadar so nawa ta sa ta saboda son da take mata. Washegari tana tashi Falmata ta fara kira, jin ta garau yasa hankalin Farida kwanciya sannan ta gabatar da ibada ta koma baccin da bata samu yi da wuri ba saboda tunani. ★★★ A hankali na kashe datan waya ta fuska ta dauke da madaukakin farin ciki, a duk lokacin d nake kallon mutanen nan ta cikin waya ji nake kamar na budi ido na ganni cikin su, wata irin kaunar su nake ji kamar irin yan uwa na ne na kusa kusa, na san ba komai ke sa min wannan feeling din ba se dan ya kasance matsalar mu iri daya ce dasu, damuwar mu iri daya ce sedai wata tana fin wata samun kwanciyar hankali. A duk sanda nake kallon su wani irin kwanciyar hankali nake samu da nutsuwa sanin ba ni kadai Allah ya jarraba da wannan ƙaddarar ba muna da yawa haka kuma ina karuwa da shawarwari da nasihar da ake yi a karshen meeting din. A kalla shekara goma sha daya kenan da nayi joining kungiyar NATIONAL ASSOCIATION OF INFERTILE WOMENS, yaya Salima ce ta ga sunan kungiyar a facebook lokacin bata bunkasa haka ba se kuwa ta fada min tana yabon yadda suke gudanar da tsare tsaren su, aikuwa ban yi sanya ba bayan tafiyar ta nayi searching sunan kungiyar na kuma gan ta, ban gushe ba se da nayi wa daya daga cikin admins din magana privately ita ce ta fada min dukkan procedure din da zan bi wajen yin register haka kuma nayi. Takaici na daya da ya zama kungiyar tana garin Bakwarni ne ni kuma ina garin Darma ne so ba ta yadda zan dinga attending meetings din su, lokacin da aka kawo shawarar yin live vedio yayin meeting din ba karami dadi naji ba, tun daga lokacin kuma ban taba missing ko daya daga cikin meetings din ba, haka kuma sanadiyar watsapp group da kungiyar ke da mata da yawa sun kulla zumunta tsakanin su, nima akwai wata Zuhra da muke so close da ita saboda yanayin yadda naji Kaddarar ta kamar tawa har kuwa irin dangin miji da surukar da Allah ya bamu. Numfashi na sauke tare da tashi zuwa kitchen bayan nayi offing data na, yau girki na ne gashi kuma me gidan yayi tafiya se yau ze dawo shiyasa zan shiga kitchen da wuri dan sama masa abin tarba. Kusan wuni nayi cikin wajen ina aiki, dishes kala kala na hada wanda nasan miji na na so kuma ze yi farin ciki in ya gani, seda na jera komai a dining tare da yin decorating sannan na tafi daki dan yin wanka. Staright gown na saka na wani dark purple material da ya sha wani azababben dinki, ko ta ina jikin rigar stones ne sune shining suna daukan ido, yadda rigar ta kamani kam yasa na tabbatar eh nayi kiba fa dan last sawar da nayi mata bata kama ni haka ba. Light purple head nayi anfani dashi na kafa a kai na ta yadda ya zauna sosai kai kace a haka yake tun ainahi, turare kuwa kamar wadda nayi wanka dan bana iya kirga adadin turaren da nayi wa kaina feshin, kawai duk wanda naji kanshin sa ya min dadi ɗorawa nake kan na baya. Falo na dawo na zauna ina dan girgiza kafa ta tare da taunan cingum a hankali, duk wannan kwalliyan fa ba komai a face na ban da powder da kohl se mascara kawai, ba dadewa kuwa naji shigowar motar da driver ya je dauko shi, cike da madaukakin farin cikin da na kasa boyewa na tashi zuwa bakin kofa na tsaya dan na kasa tsayawa jiran sa, kwana ukun da yayi baya gida se naji tamkar mun shekara uku ne bamu ga juna ba, ni kai na wannan zumudin nawa akan Salees na bani mamaki, sedai na fi dangan ta hakan da yadda muke zaune lafiya kalau cikin kwanciyar hankali tun bayan alkawarin da yayi min wanda kusan two month kenan yanzu baya, daga Salees dai ban kuma ganin wani abin bacin rai na azo a gani ba se wanda ba'a rasa ba na yau da gobe wanda shima mostly akan ya'yan sa ne dan Allah ya jarraba Salees da mugun so da gudun zuciyar ya'ya wanda nake jiye masa wataranan da idanun su shida mahaifiyar yaran ya rufe basa hango ta. Daga wajen Hajiya Iya da yan uwan sa ne kan nake Fuskantar Matsala dan sun matsa min a kwanan nan, har gidan nan suke zuwa su ci min mutunci yadda suka so, ba yadda zan yi haka nake shanye wa nake kuma hana kai na damuwa tun da dai muna zaune lafiya dashi. Maybe ku ga rashin zuciya ta akan nacewa zaman gidan Salees sedai ba naci bane, sanin ciwon kai ne da kuma biyayyar iyaye domin a kullum Ummi na na fada min babu suturar da ta kai ta aure wajen ya mace, gidan miji shine bigire mafi daraja a wajen mace haka kuma shi mijin shine rai mafi girman biyayya, taya kuke tunanin zan biye wa zafin zuciya da bacin rai wajen yin fatali da nasihar uwar da na tabbatar tafi kowa so min kwanciyar hankali da zaman lafiya.....?. Rundunar da Salees yayi min ce ta dawo dani hayyaci na, ban yi wata wata ba nima na bude hannaye na na zagaye shi dasu cike da tsananin farin ciki da jin dadi, se kuma nayi saurin yin baya jin sautin yaran na fadin "Oyoyo Daddy, oyoyo". Se lokacin na kula tare suke da maman su, yo Ina na kula, ganin miji na ya mantar da ni kowa, daya bayan daya ya daga ya'yan suna dariya yana amsa musu sannun da suke mishi, daga karshe ya karbi Amir a hannun Mariya muka taka cikin falon gaba daya muka yi masauki kan kujerun wajen. Sannu da zuwa muka shiga sake yi masa yana amsa wa cike da walwala haka kuma muka dora da hira gaba daya wadda sa'i da lokaci Mariya ke kokarin zare ni cikin su sedai yaki bayar da kofar hakan, ko akan yan uwan ta tayi magana se ya sako ni nima kuma bana gwale shi zagawa nake na amsa shi, na kula hakan ba karamin batawa Mariya yayi ba, wanda dama tun da taga yadda muka dinke da Salees yake gudun bacin rai na kamar farkon shigowar ta cikin mu shikenan ta rasa walwala. Yanzu ma tashi tayi ta tafi daki ta kwanta wai bata jin dadi kan ta na ciwo haka kuma tana ganin jiri, sannu duk muka yi mata yaran suka bi bayan ta nikuma na wuce dakin Salees ya biyo ni dan yin wanka da kuma samun hutu. Duk yadda nake son kwalliya ta seda Salees ya bata min dan dagewa yayi tare zamu yi wanka, haka ba yadda na iya na biye masa, muna fitowa na wuce dining na kwaso abinci na kawo masa saboda yadda yake ta kiran yunwa yake ji, ashe fitowar da nayi Mariya ta gan ni, zuciyar ta ta kuma cunkushewa da bacin rai na gani na da towel kai na a jike, ita a tunanin ta wani abu ne na daban niku wa ba da gangan nayi ba kaya na ne ya jika min wajen wanka gashi kuma ya ruda ni da kiran yunwa shiyasa ba shiri na dauro towel na fito. Cikin annashuwa nake kallon sa yana cin abinci a nutse, irin yadda nake farin cikin zaman lafiyar mu wallahi ba zan iya kwatanta wa ba, ganin yadda na tsare shi da ido yasa ya dago kai ya kalle ni tare da dage min gira daya "Ya dai yan mata, irin wannan kallon haka kamar za'a cinye ni?". Murmushi nayi me fadi da yasa haƙora na bayyana "Kawai inq tunani ne". "Tunanin me kunq bayan gani a gaban ki". "Tunanin rayuwa zuma na, irin yadda muka samu kwanciyar hankali se nake jin ba abinda ya kai hakan dadi". Seda yayi dariya kafin ya kashe min ido cikin tsokana "Ke dai fadi gaskiya, kina tunanin rayuwa babu ni ne, uhm fada min". Nima dariyar nayi "To meze raba mu balle har in yi tunanin rayuwa ba kai?". "In ba rabuwa fa akwai mutuwa Khadijah, kin san wannan?". "Na sani sosai Salees sedai ina fatan Allah ya dauke ni kafin kai dan i can't imagine a life without you, beside haka kana da wasu rayukan da kai ne jigon su ba kamar ni ba da ban aje komai ba, rabuwa kuma, hmm bana zaton akwai wannan kaddarar a tsakanin mu". Aje spoon din hannun sa yayi ya zuba min ido har na gama magana kafin cikin serious tone yace "Rabuwa tsakanin mu itace zata zama mafi munin kaddara da bana fatan kasancewar ta a gaske, dan Allah kar ki kuma kawo wannan maganar a ran ki ko da kuwa a mafarki ne". Kallon sa kawai nake zuciya ta na bugawa saboda tuno wani incident da ya faru shekaru tara da suka wuce, wani irin faduwa gaba na yayi kamar a lokacin abin ya faru, irin yadda na runtse ido tare da dafe kirji yasa Salees saurin riko hannu na a rikice "Lafiya kuwa Deejah, me ya same ki?". Seda nayi dan sakwanni kafin na bude ido na kalli Salees murya ta na rawa "Shekaru tara da suka wuce, salees anya......". Da sauri ya rufe min baki yana girgiza kai kamar shima ya rude "Kar ki karasa, a wancan lokacin na sharrin zuciya ne da kuma zuga, bayin kai na bane ba Deejah, dan Allah ki daina tuna min da mafi girman kuskure na". A hankali na cire hannun sa daga baki na ina gyada masa kai alamar toh. Gaba dayan mu jikin mu yayi sanyi amma muna kokarin ganin mun danne komai mun nuna ya wuce sedai har lokacin bugun zuciya ta ya kasa sasssaitawa balle ya daidaita. ★★★ *BURAIMA QUARTERS, BAKWARNI STATE* Plate din da ta gama cin abinci dashi ta dauko zata kai kitchen, tsaya wa tayi ganin yadda yake sanda zai fice kamar wani barawo, takawa ta shiga yi har ta kai bayan sa daf sannan ta tsaya kana ta ambaci sunan sa cike da mamaki "Dada". A firgice ya juyo yana kallon ta ido waje se kuma ya sauke ajiyar zuciya tare da sa hannu a bakin sa ya mata alamar tayi shiru, seda ya kalli babban falon ya ga babu kowa sannan yaja hannun ta da sauri suka shige kitchen din ya bude kofar suka fita compound ta cikin kitchen din. Ajiyar zuciya ya sauke kana ya sake mata kyakkyawan murmushin da bacin ya'yan sa da iyayen sa ba wanda yake samun alfarmar ganin sa balle ace shi a ka yi wa. "Dada lafiya kuwa?". "Where's pretty". Ya fada da dakakkiyar muryar sa yet kuma me taushi "Tana shirya wa ne Dada, wani abu ya faru ne?". "Wa ita nake wannan sandan, bana so ta ganni dan kin san rigimar kanwar ki, da kyar tayi bacci da dare wai ita a kai ta Maamah". Ya karasa sunan in a bitter tone haka itama matashiyar take yanayin fuskar ta ya canja daga mamaki zuwa alhini da damuwa...................... Ouummey 📚✍️. Ouummey 11 { 5/10/2023 } 😭 *RASHIN HAIHUWA*😭 _(Ƙaddarar wasu matan)_ Na 💝💖* Ouummey* 💞💕 Wattpad @ouummey *Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ____________________________________________________________________________ _Free Chapter Eleven_ "Kaje Dada zan kula da ita, insha Allah ba zata yi rigima ba". Gyada mata kai yayi tare da pecking goshin ta ya juya ze cigaba da tafiya "Dada". Ta tsaida shi, da sauri ta karasa gare shi tare da shan gaban sa ta shiga bin shi da kallo "Baka yi bacci ba jiya ko?". Kau da kan sa yayi daga kan ta yana hadiye wani daci a ran sa jin yadda tayi magana da wani sassanyan sauti me cike da tausayawa "Dan Allah kar ka fita Dada, kaje ka sami bacci, i promise to look after Meerah and Meemah". Wani murmushin ya sake yi mata kana ya riko hannayen ta yana mata magana a hankali ransa cike da so da kaunar wannan yarinyar tasa me matukar nutsuwa, wayo, hankali da kuma fahimta "Bana tare da bacci Haanah, idanu na ne na tashi suna ciwo, take a look here". Ya fada yana zira hannu cikin aljihu ya fiddo da maganin ciwon ido, a hankali ta sauke ajiyar zuciya kana ta sake masa kyakkyawan murmushin da ya haska matashiyar fuskar ta me cike da kuruciya "Oh Dada, har hankali na ya tashi fa na zata bacci ne baka samu ba, shikenan a dawo lafiya Dada na". "Allah yasa Haanahn Dada, pls do take care of your little ones, I won't take long insha Allah ". Gyada masa kai tayi har lokacin murmushin ta na nan, da sauri yayi gaba jin wayar sa na daukan ringing, da kallo ta bi bayan baban nata me cike da tsananin tausayi hadi da kauna me yawa kafin ta juya zuwa cikin falo ta same hanyar da suka fito. A falo ta tadda Meemah da Meerah both decently dressed cikin islamiyya uniform din su, dage musu gira tayi while tana sake musu tattausan murmushi kana ta bude hannayen ta, da gudu suka karaso suka bata a huge sisterly hug ta sa hannu ta sake kai su jikin ta sosai, kusan minti biyu kafin ta sake su tana bin su da kallo inda tayi branching kan fuskar Meemah dake yatsuna fuska tana wani tura baki. Tun kafin ta kai ga tambayar ta meye Meemah ta fara magana cikin zazzakar muryar ta me cike da tsiwa "Kai gaskiya kadai ya Meerah baki iya hug ba, jibi yanda kika matse ni kamar zaki da kayan ciki na su fito ta baki na, da kyar fa nake numfashi, tabdi". Meerah da abinda Meemah ta fada ya kular tayi kan ta zata kai mata duka hakan yasa Haanah yin intervening da sauri "Me ye haka kuke yi?". "Jibi yadda take min rashin kunya Adda bayan ke da Dada kun hana ta". Wani kallo Haanah tayi wa Meemah da yasa ba shiri ta kalli Meerah "Koyi hakuri Adda Meerah ba zan sake ba amma kema ki daina matse ni gaskiya". Meerah zata sake magana Haanah ta daga mata hannu kana ta tashi tana pointing musu hanya "Oya let's have our breakfast, we're almost late". Ba musu suka yi gaba ta bi bayan su har kan dining din su dake shaƙe da kayan kari wanda a kalla mutum goma zasu ci a wadace, babban plate Haanah ta dauka ta zuba musu gaba daya chips din wajen ta aje musu gaban su ita da Meerah sannan ta haɗawa kowa tea a cup, ita kuwa Meemah farfesun hanta ta sa mata a karamin bowl ta bata bread da Egg. A nutse suka karya cikin nutsuwa babu me yin magana har suka gama kowa ya zari tissue ya goge bakin sa da hannu kana suka wanke a wash hand basin dake dining area din. "Ku dauko jakan ku muje na san Lawan na can na jira". Da toh suka amsa mata suka yi yadda tace, a tare suka fita daga falon tayi locking din sa suka wuce parking space inda suka tadda Lawan na jiran su kamar yadda tayi zato, Meerah da Haanah suka shiga baya Meerah kuma gaba, har ya tada motar zasu fita ta wani zaro ido tana fadin "Lalalala, tabdi malam Lawan tsaya tsaya". Tsayar da motar yayi yana kallon ta haka ma su Adda Haanah jira suke suji tace tayi mantuwa se suka ji tana fadi "Ban yi wa Dada sallama ba Adda, bari in maza in je". Da sauri Haanah ta dakatar da ita da fadin "Ba kya ganin mun yi late ne, ki bari mu dawo dan Dadan ma baya nan, Malam Lawan muje ko". Turo baki tayi gaba ta gyara zaman ta dan dole dan yadda taga Addan ta hade rai ta san ba ta isa ta kawo wargi ba. Har bakin kofar class ya kai su Meemah da Meerah inda Haanah ta sauka a ajin su Meemah kasancewar ta malamar su shi kuma ya juya ya tafi. Karfe biyu suka tashi daga makarantar, Meerah tazo ajin su Meemah dan a nan suke haduwa su tafi bakin makarantar inda Lawan ke tsayawa, sedai ga mamakin su yau Lawan yayi late xan kuwa be zo daukan su ba. Zama suka yi suna yan hirar su tare da kallon yaran dake fitowa daga makarantar har suka ji horn din motar da yasa su juya wa dukan su a tare dan ko a mafar ki suna iya banbance sound din wannan horn din daga na kowace mota. "Wallahi Dada ne, Dada na ne yeeeeehhh". Meemah ta fada tana kokarin rugawa da gudu zuwa wajen motar dake parke gaban su kadan "Kar ki fara yi mana gudu a nan, ki jira muje tare me rawar kan kawai". Meerah ta fada tana hararar ta, tsayawar ta yi bisa dole sedai bakin nan a tale kamar wadda zata yaga shi, jira take kawai su shiga mota ta haɗa Adda Meerah d Dada dan ta gaji da yadda take mata fada da abubuwa. Seat din gaba Haanah ta budewa Meerah ita kuma da Meemah suka shiga baya "How's the school babies". "Alhamdillah Dada". Suka fada a tare har Haanah da ta fara girma dan in a gaban Dadan ta ne jin ta take yi kamar wata yar baby. "Yauwa Dada, malamin mu yau ya fada mana ba kyau karya shiyasa zan fada maka abinda Adda Meerah tayi dazu". Da sauri Meerah ta zaro ido jin iya shegen da Meemah zata mata dan kawai ta hana ta gudu, "Kai Meemah kiji tsoron Allah ni kuwa me nayi da zaki fada in ba kalin sharri ba". Dariya Meemah tayi ganin yadda Addan tata ta firgita "Ki bari kawai na fadawa Dada da Adda Haanah kin sha ruwan sanyi immediately after you wake up". Rau rau da ido Meerah tayi tana kallon Haanah wadda itama ke kallon ta jin abinda tayi bayan likita ya hana ta kuma ta sani "Why, meyasa kike yin haka Ameerah?". Sharrr hawaye suka zubo mata dan suna bala'in tsoron baban su dan duk yadda yake wasa dasu yake son su baya hana ya hukunta mutum in yayi ba daidai ba "Am sorry Dada Allah ba zan kuma ba". Shiru yayi mata hakan yasa ta kara volume din kukan ta tana bashi hakuri "Will you pls keep shut, ko baki ga tuki yake ba?". Kamar an yi ruwa an dauke haka ta hadiye kukan ta bayan Haanah ta mata magana, ba wanda ya kuma magana se Meemah dake wasan ta ita kadai har suka kai gida, kowa ya dauki bag din sa suka yi falo. A tsakiyar falon ya tsaya ya zuba wa Meerah ido cikin hukuntata dasu wanda duk yayi musu irin haka suke gwammace wa yayi fada ko ma duka akan wannan silent punishment din. "Ciki na ne naji yana zafi Dada shine nasha amma ba zan kuma ba, am so sorry pls Dada". Kallon Haanah yayi se ta langwabar masa da kai alamun itama tana bashi hakuri, dauke kai yayi ya kalli me kawo gulmar Hajiya Meemah, wai dan gulma itama yarinyar nan se ta karyar da kai gefe wai itama hakurin take bashi, wannan dabi'a tasu na matukar burge shi tare da faranta masa rai. Gashi dai basu yi laifi ba Ameerah ce kadai tayi, amma yanzu da zai nemi hukuntata se duk hankalin su ya tashi ba kuma zasu koma daidai ba har se ya hakura kamar dai yanzu. Girgiza kai kawai yayi ya wuce bedroom din sa leaving them behind Wanda Haanah ta fahimci ya hakura ne dan haka ta ce "Se ki tashi ai babar marasa jin magana,ban da wulakanci so nawa kike so in nanata miki ki daina shan ruwan sanyi da safe after kin fi kowa samun you're not fine Amma shine bakya ji, to go ahead and kill yourself se mu zauna mu uku, kinga se mu dinga lissafin ke da Maamah bakwa tare da mu". Yadda muryar ta ta shiga rawa bayan ta kai karshen zancen ze tabbatar maka tana cike da kewa da alhinin wadda ta kira ga Maamah a ran ta, fashewa da kuka Meemah tayi tana kiran Maamah, ita wallahi Maamahn ta yasa hankalin su tashi. Shaf Haanah ta manta da cewa tan wajen ya sa ta ambaci sunan Maamahn ashe rabon ta jawo musu jidali ne . Fitowar Dada da sauri daga dakin yazo ya dauki Meemah tare da ɗorawa a kafada ya shiga aikin lallashin ta, wannan yanayin ya karyawa Haanah zuciya ta shiga hawaye da shessheka abinda yasa itama Meerah fashewa da kuka. Gaba daya se ya rude ya rasa ya ze yi, waye ze lallasa ma ya rasa se kawai ya juya ya zuba musu idanun sa da suka kada sukai jajir, hada idon da suka yi da Haanah da yadda taga jan da idon sa yayi yasa ta san lallai sun tayar masa da hankali, hakan yasa tayi saurin dakatar da

Chapter 7 of 12