Share this page
albarka". Murya ta na rawa na amsa da Ameen dan ba abinda ya fado min rai se shekarun baya da muka wanzar da tsantsan so da kauna a zaman mu, haka Salees ke min wannan godiyar duk lokacin da ya samu nutsuwa dani. "Na san ni me laifi ne, na san ina bata miki sedai wallahi kin ji na rantse khadeejah ban san me nake yi da yake bata ran ki ba, jiki na ne kawai yake fada min nayi laifi, dan Allah ki fada min kuskure na I promise to repent insha Allah". Shiru nayi cikin harhado laifukan Salees gare ni na shiga analysing wanne zan fada wanne zan bari dan wallahi ba zasu fadi duka ba saboda yawan su. Jin yadda yake hura min iska a kunne yasa a hankali na bude baki na "A kullum fatana da buri na be wuce karasa rayuwa ta da kai ba Salees, ban taba hasko rayuwa da wani da namijin ba bayan kai, kai na fara so kuma har yanzu kai nake so sedai abubuwa da yawa na dakatar dani a kan ka. Allah be bani haihuwa ba Salees, da siyar wa ake yi wallahi bana jin da ko shekara zan kai a gidan ka batare da da ba, da kwatowa ake yi shima ko da zan rasa raina zan fita nayi gwagwarmaya na kwato, haka kuma da soyayya ke bada haihuwa nasan da tun farkon auren mu ka bani, sedai Allah ne me badawa ga wanda yaso ya zaba ba kuma dan mu da ya hana baya san mu ba amma mutane basa fahimtar hakan, ba damuwa nayi da wasu se sun fahimta ba in har Kai da nake tare da kai ka fahimta, sedai abin da ke tayar min da hankali kai ma din kallon mara amfani kake min, kai ma din ka gaza fahimtar ba kasawa ta bace, so da yawa se in ga kamar jira na kake abu ya hada mu kayi min gorin rashin haihuwa, wannan shine babbar matsala ta a gidan nan se kuma na matar ka ya biyo baya, amma a kan ta ba zan ce maka komai ba dan duk abinda take yi Allah yana kallon ta kuma i do believe yasan yadda ze yi da ita". Shiru dakin ya dada yi na tsawon lokaci kafin Salees yayi breaking silence din "Am sorry for all my mistakes, am sorry na saki bacin ran da nayi times without number, am sorry for everything khadeejah, dan Allah kiyi hakuri and am ready to change, for good and for you khadeejah, ki fada min me kike so nayi wallahi i promise you zan yi". Abin mamaki kawai yake ban dan rabon da mu sami mutual agreement kamar haka wallahi ba zan ce ga yawan shekarun ba, abin da na rike kawai its too long, an dade sosai. "Ka ringa bincike kafin yanke hukunci, ka dinga sauraren both side kafin zaban me gaskiya, ba abinda nake bukata a wajen ka face adalci, kulawa da kuma tausaya wa, this is all I need from you Salees, dan Allah". Na hade hannaye na alamun roko hawaye na zuba a ido na, da sauri ya dora nasa kan nawa ya jimke kana cikin taushin murya ya amsa min "I promise you love, care and justice daga yanzu har zuwa ranar da numfashi ze bar gangar jiki na, insha Allah ba zan kuma yanke hukunci batare da bincike ba, insha Allah zan zama me adalci gare ku baki daya, ke kuma abu biyu nake so wajen ki dan Allah, uzuri da soyayyar ki, ina barar wannan abubuwna khadeejah". "And i promise you also". Ba muyi bacci ba seda muka cimma matsaya wa rayuwar mu, wannan daren ya shiga cikin tarihin rayuwa ta domin dai tun da muka shiga daki da shi tun dawowa ta karfe hudu da rabi Salees be sake fita ba se washegari dan hatta sallah tare muka dinga gabatarwa a daki. Tun daga wannan lokacin zance alhamdillah domin kuwa Salees ya tabbatar da alkawarin sa ko ince yana kan tabbatar wa dan haka har wata kiba nayi ta kwanciyar hankali da samun nutsuwar zuciya. ★★★FALMATA★★★ Yau ma zaune take a falon ta, sedai tun da gari ya waye take jin ta ba daidai ba, cikin ta wani irin ciwo yake mata da ya hanata zama guri daya, tun tana daurewa a daki har ta kasa ta janyo wayar ta ta shiga kiran me gidan, wayar na ringing amma ba'a dauka ba, azaba ta sa itama ta kasa daina kiran wanda a kalla ta masa miscall kusan ashirin amma no answer. Azabar ciwo da radadi yasa ta wurgar da wayar ta shiga malelekuwa kan carpet din kasan gadon, gaba daya ta fita hayyacin ta , a haka Allah ya jefo daya daga cikin masu aikin ta, cikin tashin hankali ta fice a guje dan zuwa sanar da mutan gidan halin da uwardakin ta ke ciki, sedai bata sami Alhaji ba dan baya gida, ita kuwa Hauwa da ta fada mata Allah ya sawwaka kawai tace ta dauke kai. Dole harira me aiki ta kuma kwasowa a guje ta dawo, ita ta zauna da ita sedai ta rasa me zata mata, cikin ikon Allah ta hango wayar Hajiya Falmata ta dauka hannun ta na rawa, dake tayi makaranta har zuwa secondary se ta lalubo number Hajiya Farida ta kira, shine fa ta zo, ashe maganin ta ne ya kare ga ba kudi hannun ta, dole Hajiya Farida ta tafi siyowa ita kuma harira ta taimaka wa uwardakin nata zuwa falo kafin Hajiya Faridan ta dawo.......................... Ouummey 📚✍️. Ouummey 09 {5/7/2023 } 😭 *RASHIN HAIHUWA*😭 _(Ƙaddarar wasu matan)_ Na 💝💖* Ouummey* 💞💕 Wattpad @ouummey *Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ____________________________________________________________________________ _Free Chapter Nine_ Babu dadewa Hajiya Farida ta dawo rike da maganin, kusa da yar uwar ta ta zauna tana mata sannu ganin yadda ta damke cikin tana runtse idanu, da sauri ta balla maganin harira ta miko bottle water ta haɗa ta kamo falmatan ta sa mata maganin a baki kana ruwan, da sauri ta hadiye tana dan jujjuya kai na ciwo. Babu dadewa ciwon ya lafa dan maganin babban magani ne haka kuma fast action shiyasa yake da tsada sosai, seda ta dawo hayyacin ta harira ta zuba mata abinci bisa umarnin Hajiya Farida ta karba ta dan ci ta aje ragowa. Ganin yadda hankalin ta ya dawo sosai yasa Farida kasa iya cigaba da rike abinda ke cikin ta "Wai haka zaki yi ta zama da ciwo a ciki sai dai ki sha magani ki kwantar dashi?, Wait taya ma aka yi yau maganin ya yanke miji?". Dan murmushin takaici Falmata tayi "To y azan yi Farida, tun da kaddara ta kenan?, D ana sake wa Alhaji magana yace wai in jira next month yanzu kam dai babu kudi wajen sa, magani kuma yace na bawa Adam kwalin ya siyo, to tun da na bashi ban ma kuma ganin sa ba". Kankance ido Farida tayi cike da mugun mamaki "In ji shi Alhajin yace ki cigaba da zama da ciwo har zuwa karshen wata?, Lallai mutumin nan ya wuce duk yadda nake zato, ke dama kin sa ran ya kawo muku maganin, wannan tambadadden dan da uwar sa ta riga ta gama poisoning mind finishing, ai na fada miki kin ki yadda, wallahi hau da za'a ce kin mutu dukkan su murna zasu yi domin dadadden burin su ne ya cika". "Kuma fa cewa nayi ko a asibitin nan ne ya biya ayi min aikin duk da akwai risk me girma amma na gaji da wahalar da nake sha Farida, wataran har na kan gwammace mutuwa saboda radadi da azabar da ni kadai na san me nake going through, ki dena ce musu tambadaddu, Allah ya shirye su su gane gaskiya ". "Uhm". Kawai Hajiya Farida tace cikin takaicin yar uwar Tata, kalli dai wahala ta gama sha ta sanadin Alhaji da ƴaƴan sa amma wai a daina ce musu tambadaddu, ita ta rasa wace irin zuciya Allah yayi wa Falmata amma komai ya kusa zuwa karshe dan ita ba zata zuba ido ba, dole ta dauki mataki ko dq da ba da sanin Falmata bane. Yin wannan tunanin yasa ta saki ranta ta shiga kwantar wa da yar uwar ta hankali kana ta tashi ta gyaggyara mata daku na inda masu aiki basa shiga mata, se daf da magriba ta yi shirin tafiya bayan ta jaddada wa Falmata cewan ko yaya taji wani ciwo ta kira ta haka kuma ta tambayi Alhaji suje su ga yan uwan su. Da toh Hajiya Falmata ta amsa mata kana suka yi sallama Farida ta wuce. Bedroom din ta ta koma ta yi wanka ta fito ta tsaya gaban mirror dan yin shirin ta sedai se ta bige da kallon kanta cikin madubin. Gaba daya tayi baki ta rame kamar ba ita ba, farar fatar ta me sheki duk ta yi duhu, kyakkyawar fuskar nan duk ta mokade saboda rama, baka ganin komai a fuskar se dogo siririn yancin ta da ya kara tsayi se kuma kodaddun idanun ta da kallo daya zaka musu ka hango rashin lafiya, damuwa, rashin nutsuwa da rashin kwanciyar hankali cikin su. Hannu tasa ta shafo wuyan ta inda kasusuwa suka bayyana kan su a wajen, ta dade ta na shafa wajen cikin tunanin tana hawaye batare da ta san tana yi ba, tsayin lokaci kafin ta farga ta share fuskan ta kana ta karasa gaban bed da ta aje kayan da zata sa ta dauka ta maida wardrobe, a yadda tayi wannan ramar sam ba zata sa kayan mu na al'ada ba dan ba kadan ba zasu bayyana ramar ta kasancewar duk an dinka su ne lokacin da take falmatan ta ba yanzu da se sunan kawai ba. Doguwar riga ta sa kirar Oman kana ta aje dankwalin a gefe ta shiga gyara kan ta wanda shima se d aya samu tangarda saboda halin da take ciki, seda ta tufke jelan sannan ta daura dankwalin kan ta, ba karamin kyau tayi ba duk da kuwa fuskar ta babu komai face kwalli da ta sawa idan ta dan ya rage kodewar da yayi. Kai daga yadda ta daura dankwalin abayar zaka san lallai a da an zuba gayu an kuma kafa dauruka ba kadan ba, ita kan ta murmushi tayi da ta kalli kanta sannan ta kwashi wayoyin ta ta fita falo. Tare da harira suka zauna dan duk cikin masu aikin ta tan matukar kaunar harira haka kuma ba matsayin me aiki take kallon ta ba, kallon yar uwa kuma karamar kanwa take mata dan ta girmewa hariran nesa ba kusa ba, hirar su suke yi suna kallo sama sama abinda yasa zuciyar Falmata dan samun nutsuwa daga tunane tunane. Yadda hankalin su ya dauku yasa har basu ji sallaman Alhajin ba balle shigowar sa seda yayi gyaran murya, da sauri harira ta tashi tayi waje ta kofar baya bayan ta gaida shi, kusa da Hajiya Falmata ya karasa ya zauna inda ita kuma ta tashi zuwa kitchen domin kawo masa ruwa. Kan karamin tray ta dauro bottle water da juice na kwali me dan sanyi kana ta hado da glass cups ta kawo gaban sa ta aje kana ta zuba ruwan ta mika masa ya karba ta kuma shiga zuba juice din. Seda ya karewa juice din kallo kafin yayi bismilla da karfi sannan yasha, ita dai tana kule dashi sedai bata bashi wani muhimmanci ba har ya shanye lemon ya aje. "Wanka zaka fara yi ko abinci zan kawo?". Da sauri kamar wanda tace zata kawowa mugun abu ya shiga kada kai "A'a, a'a ai ba zan ci abincin nan ba, na riga naci abinci a waje cikina a cike yake". Dan tsai tayi tana kare masa kallo kafin kuma ta girgiza kai tana dan murmushin da kan kallo zaka san ba na jin dadi bane "To shikenan, wankan fa?". "Yanzu zan je can part di na nayi, dama dai nace ba wata damuwa ko?" Seda ta dan hadiye miyau kan ta bashi amsa "Maganin da na bawa Adam ne dai har yanzu be kawo ba". "Se fa kina yi wa yaran nan uzuri, yana da harkoki da yawa ne, yanzu haka ya ma tafi can kudu kan kayayyakin mu da ze shigo dasu, amma kiyi min texting sunan maganin se na taho dashi". "Ko kawai ka bawa Bala ya siyo min?". Ta fada sanin in dai shi ze siyo maganin to kuwa har ta mutu be kawo ba. "Shikenan zan bashi kudin ya siyo kawai, shikenan ko?". "Maganar aikin nan alha......". Tun kafin ta karasa ya katse ta yana mikewa tsaye daga zaman da yayi "Ai tuni muka gama magana akan wannan, na fada Miki babu kudi a hannu na yanzu amma watan gaba insha Allah se ayi aikin ko a nan asibitin Shehu ne dan gaskiya fita wata ƙasa ze ci miliyoyin kudade kuma kin ga yadda yanzu harkokin suke se a hankali". Tun d aya fara maganar take kallon shi har ya kai karshe "Allah ya kara budi, gobe ina so inje gida". "Gida kuma, wane gidan kenan?". Ya fada yana bata rai kamar wadda tace masa zata je gidan karuwai ". "Gidan marayu mana, muna da wani gidan da yafi nan ne?". "Ba zaki je ba". Ya fada yana kade babbar rigar sa ya nufi fita waje "A'a Usman ka bar ni kawai dan wallahi goben nan se naje". Ta fada da rawar murya, shima Alhaji tsayawa yayi kana ya juyo cike da mamakin yau Falmata ke ja da hukuncin sa, anya be fara kure hakurin baiwar Allahn nan ba kuwa. "Shikenan kije Allah ya tsare, ki gaida su". Bata amsa masa ba ta zauna tana kallon tv sedai hawaye ke zuba a idanun ta, yana fita itama ta tashi zuwa daki da sauri, kan gadon ta ta fada tana kuka me shiga jiki, wani kuka me tafe da sheshshekar dake fitowa daga can karkashin zuciya, a hankali nunfashin ta ya fara seizing kadan kadan kafin kuma tari ya turnike ta , da sauri ta tashi daga kwancen da take tare d da finciko tissue dake aje kan mirror din ta tasa a bakin ta zuwa hancin ta dan ta ana abinda ze faru gaba. Seda tarin ya tsaya mata da kyar sannan ta zare tissuen dake kan hancin ta ta aje haka ma na bakin ta, gaba dayan su sun ɓaci da jini, wani irin bakin jini me kauri, ganin bata firgita ba yasa nasan ta dade yana ganin hakan kenan. Wata tissuen ta sa ta goge bakin ta sosai kana sa ruwa ta kuskure bakin, ta dauko wani ma ta goge hancin, take fuskan ta yayi tas kamar ba ita ta shiga yanayin ba. Kora tissues din tayi cikin closet ta karawa toilet din spray sannan ga fito, bedside drawer ta bude ta ciro wani tablet guda biyu manya ta sa a baki tare da korawa da ruwa, Wani ta dauko different from the first shima ta sha biyu sannan ta cire doguwar rigan jikin ta tasa na bacci yayi light off tare da kwanciya bayan tayi addu'a. Kashegari da wuri ta shirya, tayi matukar kyau cikin Abayan da tasa kirar Dubai, sosai ramar ta ta buya se wadda ba'a rasa gani ba, sallama tayi da su harira sannan ta fita cikin motar ta wadda bata wata me kyau bace can amma kuma ba wai ba ta da kyau bane. A compound din gidan Hajiya Farida tayi parking ta fito tana sakin murmushi, Farida ce kawai kawar ta ita ce kuma kadai yar uwar ta haka kuma aminiyar ta, gurbin da Farida ta cike mata ba kadan bane haka kuma halaccin ta gare ta me yawa ne duk da dai ita ce ta fara yiwa Faridan amma ba kowa ke iya rama alkhairi ba. Da sallama ya shiga falon, ihu Hassana ta saki tare da tashi ta nufo ta a guje, duk kai kai kai din da Hajiya Farida keyi be sa ta fasa ba se da ta fada jikin falmatan har da wani dan tsalle kafin ta kankame ta, ita ma sa hannu tayi ta sake riƙe ta a jikin ta suna dariya Farida kuwa ta soma fada "Ke dai wallahi ban san yaushe zaki yi hankali ba Hassana, ban da rashin mutunci kayar min da ita zaki yi da zaki dane min ita haka bayan kin san ba wani lafiya ne ya ishe ta ba salan ki cuce ni, to Allah ki ka kuma se ran ki ya baci, bana son shashanci, yarinya ga uwar nauyi kaman buhun shinkafa kawai ki nemi illata min yar uwa". Bata fuska Falmata tayi ganin yadda Hassana tayi rau rau da idanu, "Gaskiya ni dai Farida kina min abinda bana so, kawai shikenan se ba zata zo ga uwar ta ba saboda bani da lafiya, ko kuwa ke kadai ce me yar uwa da zaki ce haka, dan ma kin samu ana yin yar uwar ta ki, to ni dai kiji ma ya'ya na are above anyone, maza matso ki sake yi min oyoyo sweetheart ". Ta fada tana sake buɗe mata hannu bayan ta matsa nesa da ita daidai lokacin da Hussaina ta fito daga bedroom suka kuwa kwaso da gudu su duka biyun suka fada kan ta gaba daya suka zube kan kujera suna dariya, ita kam Farida bata kuma bi takan su ba ta cigaba da abinda take yi a kitchen jin yadda Falmata ta gwale ta sedai tana jiyo kyakyacin dariyar su daga nan wadda ta manta rabon da taji dariyar Falmata har haka. Wani irin tausayin ta ne ya sake kama Farida tuno yadda Falmata ke masifar son yara tun suna kanana se gashi Allah ya jarraba ta da rashin haihuwan kuma ta bata mamaki dan bata taɓa zaton Falmata zata iya karbar wannan kaddarar ba. Seda ta gama aikin ta sannan ta fito ya same su kamar wasu kawaye "Oya aje a fito da komai a shirya kan dining bari nayi wanka nima". Da haka suka tashi zuwa aikin da aka sa su ita kuma ta wuce wanka aikuwa itama Hajiya Falmata ta tashi ta shiga taya su jera abincin, tare suka yi gaba daya sannan suka wuce wanka suma ita kuma ta zauna kallon wata hira da ake yi da wani mawaki a TV. A shirye suka fito dan tare zasu tafi dukan su zuwa gidan marayu wanda nan ne gidan su Farida da Falmata kasancewar marayun da suka tashi suka budi ido a gidan batare da sanin su waye iyayen su ba, hakan yasa suka riki gidan marayun gida duk kuma wanda ke cikin gidan suka dauke su yan uwa kuma dangi, Hajiya Farida bata taɓa kunyar nuna wa ya'yan ta gidan matsayin nasu gidan iyayen ba, a kullum tana alfahari da gidan dan acewar ta ba'a yi musu rikon wulakanci ba. Seda suka karya gaba daya har Falmata sannan suka dungu ma zuwa compound suka shiga motar Hajiya Farida leaving behind motar Falmata a gidan. A motar na hirar su suke yi ita da Farida dake tuki yayinda Hassana da Hussaina ke baya suma suna tasu har suka kai gidan, kayayyakin alkhairin da suka saba bayarwa na kayan abinci duk suka dire haka kuma suka dinga zagaye gidan bangare bangare suna gaisawa da jama'a, da suka tashi tafiya wannan karon Hajiya Farida ce kawai ta bada kudi kamar yadda suka saba dan ita Falmata babu kudi hannun ta. Haka suka yi sallama da jama'a suka koma gidan Farida suka sauke yan biyu su kuma suka sake fita domin tafiya meeting din kungiyar su wadda Farida ta shiga ne kawai saboda Falmata dan kungiyar purpose din ta babu irin su Farida ciki. *NATIONAL ASSOCIATION OF INFERTILE WOMENS* Babbar kungiya ce da ta cika ta tunbatsa da Manyan mata iri iri, kungiya ce da aka kafa ta solely dan matan da basa haihuwa, zaka yi mamaki in ka ga dimbin mutanen dake ƙarƙashin kungiyar domin ta haɗa mata kala kala, manyan masu kudi masu rufin asiri kai har ma d talakawa. An kafa wannan babbar ne domin kwantar wa d matan da basa haihuwa hankali, samar musu da aikin yi da kuma kwatar musu yancin su a inda ya dace, haka kuma domin taimaka su a gurin da suke buƙatar taimako. Suna yin meeting din wannan ƙungiya ne annually ma'ana duk shekara, a nan za'a zauna a ji koken juna, me bukatar taimako ayi mata, sababbin members kuma ayi masu rigister tare da councelling kan abubuwan dake jawo rashin haihuwa, in abin me magantuwa ne suna tsayawa kai da fata har se sun ga an ci nasara da izinin Ubangiji batare da duba da ko nawa za'a kashe ba while the treatment........... Ouummey 📚✍️. Ouummey 10 {5/9/2023 } 😭 *RASHIN HAIHUWA*😭 _(Ƙaddarar wasu matan)_ Na 💝💖* Ouummey* 💞💕 Wattpad @ouummey                        Ouummey 10 *Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ____________________________________________________________________________                   _Free Chapter Ten_ Hajiya Falmata da Hajiya Farida sanannu ne a kungiyar saboda irin gudunmawar da suke badawa, ba wai sun fi kowa taimako d kudi bane, a'a irin matsalar da Falmata ke ciki da yadda take da jarumta da juriyar mai da komai ba komai ba yasa ka bata mukami dan na kasa suyi duba izuwa ga rayuwar ta su kuma yi koyi da tawakkali hadi da karfin zuciya irin nata. Kamar ko da yaushe yau ma cikin nasara aka gama gabatar da meeting din, inda yau taimakon nasu ya karkata ne kan wata mata da ke da matsalar karin mahaifa da ya hana ta haihuwa gashi kuma mijin da iyayen ta ba masu karfi bane hakan yasa jin labarin kungiyar da irin taimakon da ake yi a cikin ta yasa ta kawo kanta haka kuma aka saurare ta duk da bata kasance wata hamshakiyar me kudi ba, ba kuma wata celebrity ba haka kuma ba wata kusar gwamnati ba, motto din kungiyar shine mu'amala da kowa with equality, babu ruwan su da mai kudi ko talaka, abinda suka sani shine they all are one family and have almost similar problem so they'll come together in finding a solution. Miliyan uku da rabi ake bukata domin aikin dan abin yayi worsting ta yarda har ya fara neman lalata mahaifar hakan yasa ake bukatar aikin urgently, wani abin burgewa shine a wannan zaman da suka yi da kowa be san za'a iya kawo matsala ba se gashi tashi daya har an hada miliyan biyu da rabi, inda wasu suka karbi bank account na kungiya domin

Chapter 6 of 12