dan yana cikin maza masu naci kan abinda yake so, sedai na kudire ko yafi antaru taurin kai da naci wallahi baze sami komai daga gare ni ba.
Da sauri na mirgina jin hannun sa ta cikin riga ta, tunkurkur na zauna tare da zuba masa idanu na da mayen son sa suka sa yayi ja lokaci guda ina bata rai matuka, cike da basarwa irin tasa ya nuna kamar be gani ba ya matso tare da son sake shige min sedai tuni nayi baya da sauri Ina turo baki
"Bana son irin abinda kake min wallahi, baka na dawo nan bane, ya kamata ka gane hutawa nake son yi".
Dan tsai yayi yana duba na da mamaki dan zan iya cewa ban taba yi masa gardama ga bukatar sa ba cikin rayuwar da muka yi ya tsawon shekaru goma sha shida, na san dole abin ya dake shi gashi kuma nayi fuska abina tare da komawa na kwanta na bashi baya.
Sosai jikin Salees yayi sanyi sedai he's the type that doesn't give up easily so se ya Kuma matsowa tare da sa hannu ya juyo dani ta karfi, be kuma jira komai ba ya danne ni cikin son se ya hade bakin mu guri daya, aikuwa kamar me haka na shiga fighting din shi na kuma ki bashi duk damar da yake so, ya zata abin wasa ne ya shiga kokarin kashe min jiki sedai ya ga ko kadan ban da niyyar saduda asali ma na kara kai mi ne wajen kokawa dashi dole ya hakura ya daga ni tare da tsura min jajayen idanun sa da ke cike da neman magana ga kuma bacin ran da na tusa masa, yana daga ni na tashi ina gyara riga ta na mike tsaye tare da kakkabe jikina nayi hanyar barin garden din ina karkada masa jiki, ko banza na san shima na bata masa kamar yadda yake bata min.
★★SALEES★★
Duk yadda yake tunanin iskancin khadeejah ya wuce wajen, kalli yanzu abin da tayi masa kamar wani kwarto alhalin yana matsayin mijin ta shugaban ta, a yanzu kam dari bisa dari ya yarda raini ne tsagwaron sa tsakanin sa da Khadijah, ta raina shi ne take masa haka, ai da datake ganin girma da kimar sa musu wannan ze iya kirga so nawa ta masa, lallai se ya dau kwakkwaran mataki kan ta, ba dai jikin ta bane take masa wulakanci dan ya bukata?, To ta rike abin ta ta jika tasha dan alkawari ne baze kuma neman ta ba, in kuwa ta kawo kan ta lokacin zata san ita bata iya wulakanci ba dan se ya nuna mata shima tantiri ne kamar ta, yana ji da fiye da duk abinda take ji.
Ya dade zaune a wajen kafin ya iya mikewa ya koma gida, fita ya so yi ko yaji sauƙin bacin ran sa sedai baze iya ba, a yadda marar sa ke damun sa cikin ma da kyar yake taka kafa.
Ganin yadda ya wuce su rai bace fuska hade yasa Mariya tashi ta bi bayan sa da sauri, sedai ko kafin ta kai gare shi tuni ya shige tare da datse kofar, turus ta tsaya tana kallon kofar dan this is unlike him, bugawa ta shiga yi hankali tashe sedai duk iya bugun ta yayi mata banza ko uhm bece ba haka ne bude kofar ba har ta gaji ta juya jiki a mace ta sauka kasa.
Shi kam Salees duk bugun da take yi yana ji kuma yana sane yayi mata banza, abinda bata sani ba dan ita ya rufe kofar dan ya san se ta zo takura masa shi kuma baya bukatar takurar ta dan ba abinda zata iya yi masa, khadeejah ce kawai maganin sa ita kuma ya fahimci hayaki kan ta keyi amma yayi alƙawarin sauke mata duk ma uban dake kan.
Haka ya cigaba da juyi dafe da marar sa se uban gumi yake haɗawa kafin wani wahalallen bacci yayi gaba dashi me cike da mafarkin Khadijah kala kala.
Be tashi ba se after Six, a gurguje yayi wanka ya fita Masallaci jikin sa duk ba kwari, sallar ma ranar cikin wasi wasi yayi ta dan gaba daya hankalin sa na kan Khadijah, tunane tunane kawai yake yi a kan ya, wata zuciyar na fada masa ya sake gwada ta ko zai dace wata kuwa na bashi shawarar fita harkar ta har ta gane kuren ta, be bar masallacin ba se da yayi isha kana ya nufo gidan cike da karbar shawarar zuciyar shi ta sake bata dama.
★★★★
Fadawa nayi kan bed fuska ta cike da murmushi me fadi wanda na manta rabo na da irin shi, wato yau da naga Salees cikin irin yanayin da na kan shiga a dalilin da se naji raina yayi sanyi, sanyi fa sosai dan ba karya naji dadi wallahi.
Juyi nayi tayi ni kadai ina sake shirya yadda zan cigaba da zama da kowa na gidan da halin sa, na daina daukar cin kashin kowa tun da ina hakuri amma ba'a san ina yi ba, da ace duk abinda ke faruwa Salees na bin bayana in Ina da gaskiya da maybe ban sare ba haka, amma babu ruwan sa dani, babu ruwan sa da zan damu ko zuba cutu, shi dai duk abinda aka tsara masa shi yake hawa, duk abinda aka fada masa a kaina se ya yadda, nayi ban yi ba duk ba ze bin cika ba, kamar ba shine a baya yake fada min ba wanda ya kai shi sani na ba, ba wanda ya kai shi sanin hali na, ba wanda ya kai shi sanin abin da zan aikata ko ba zan aikata ba, duk ya manta wannan, duk ya zubar da komai ya watsar da komai, baya kallo na a komai face Khadijah, matar da yake aure wadda bata haihu ba, ba'a ma maganar soyayya, dan yanzu ina tantama in akwai so na a ran sa, dan abinda yake min masoyin gaskiya baze yi shi ba.
Kiran sallah ya sa na mike tare da shiga toilet na dauro alwala na tada sallah, ina idar wa na yi azkhars dina kana na cire hijab din na fita zuwa kitchen dan yunwa nake ji, noodles na dafa na zauna na ci acan kana na wanke plate din na aje na koma daki, system na jawo na shiga aiki na dan yanzu na sake maida hankali dan bana san abin d zesa suna na ya fita daga cikin masu samun promotion din nan, na saka rai sosai ina kuma fatan Allah ya sa na dace.
Karfe tara na tattara komai na aje na shiga wanka, sleeping dress na saka kana na feshe jiki na da turarukana masu sanyin dadi wanda ko ba zan je dakin Salees ba bana fashin sa su, se da nayi addu'a sannan na kwanta bayan na kulle kofa ta.
Har bacci ya fara dauka ta na ji kamar an bude dakin an shigo, a tsorace na mika hannu na kunna wuta dan switch din na daga saman kai na ne, a boye na sauke ajiyar zuciya ganin Salees sedai a fili se na bata fuska in bin shi da kallon mamaki da kuma gajiya da ganin sa, maida kofan yayi ya rufe tare da takowa ya zauna bakin gado yana kallo na nikuwa na kau da kai gefe ina bata rai.
"Tashi zaune muyi magana".
Kamar ba zan tashi ba se kuma na fara tashin a hankali kamar me ciwon laka wanda ina sane nayi dan na bata masa dan tuni na dade da sanin baya san jira a rayuwar sa, kusan minti biyu kafin na zauna sosai sannan na kai kai gefe.
"Bana san tashin hankali Khadijah, ki fuskance ni mu sami fahimtar juna".
Juyo da kaina nayi na zuba masa ido kamar yadda ya bukata, seda ya dan yi shiru alamun yana tunanin ta ina ze fara kafin ya riko hannaye na, na kalli hannun sannan na maida duba na kan sa
"Bana san irin wannan zaman da muke yi Khadijah, ban taba tsara hakan tsakani na dake ba, in laifi nayi miki ki fada min na baki hakuri a wuce wajen amma bana san gaba da fushi".
Shiru nayi kawai, lallai namiji bai da kunya, wai ni Salees ke tambaya in laifi yayi min saboda yanzu tashi ta kawo shi, duk abinda ke faruwa be ga ni ba, duk abinda yake min ba laifi bane, aikuwa ze ga rainin hankali in dai nice dan nq shirya masa
"Kiyi magana, ki fada min laifi na and we'll sort things out komai ya wuce".
"Baka yi min komai ba zuma na".
Zuba min ido yayi na tsayin mintina kafin ya sake matsowa kusa na har nunfashin sa na sauka kan fuska ta
"No nayi miki, Ina ji a jikina nayi miki laifi, in haka ne meyasa da baki min haka ba se yanzu?, pls ki fada min me nayi miki dan iya tunani na na kasa ganowa".
Murmushi nayi jin wai ya kasa gano laifin sa
"Ka kwantar da hankalin ka pls, baka min komai ba ni hutu kawai nake bukata, pls ko zaka iya komawa wajen Mariya har zuwa wani dan lokaci?".
Izuwa yanzu ina iya hango bacin ran d Salees ke ta kokarin boyewa sedai ko gezau ban ji komai ba a raina akasin da da ban so ko kadan in ga fushi ko damuwa tattare dashi
"To kuwa baze yiwu ba, na biki na lallaba ki, na kwantar da kai na sanyayar da murya duk dan mu zauna lafiya amma kin ki bani hadin kai, zama da nine kika gaji ko kuwa wani salon wulakanci ne?".
Zare hannyeye na nayi daga nasa na koma na kwanta ina bashi amsa
"Babu ko daya cikin biyu kawai dai kamar yadda na fada maka ne ina bukatar hutu, Allah ya bamu alkhairi, pls in zaka fita ka kashe min wutar ka kuma rufe min dakin".
Daga haka na ja bargo na lullube ƙafafuwa na tare da kulle ido na, tabdi bala'i ni kaina na san na tsokana masifa sedai sanin na shirya mata yasa nayi banza da duk bala'in da Salees ke yi
"Kar ki maida ni wani shashasha mana, bar ganin ina bin ki ina lallaba ki amfada miki tsoranki nake ji, ko kuwa kin fi karfi na ne, to wallahi kyale ki nake yi kawai darajar su Abba, amma ban da haka ke in ance kiyiwa Salees iskanci ba zaki fara ba, wacece ke da za'a dinga bin ki kina wani daukan kai, ban da ma kin kasance butulu duk rufin asirin da nayi kiki baki gani ba, duk suturar da nayi miki amma nine zan zama abin wulakancin ki, to bar ganin ana wani cewa kin raina ni kin mallake ni, wannan duk karya ne dan ba macen da ta isa ta raina ni, ba'a haife ta ba wallahi dan kuwa se ta koma gidan gyatumi tun da babu abinda ya zama dole, kuma wallahi tun muna shaida juna maza ki koma hayyacin ki kafin mu kai ga yin batacciya dan akan haka wallahi komai ze iya faruwa, in nace komai ina nufin komai".
Ya sa kai ya fice tare da banging min door din, duk da cikin fadan nasa akwai kalaman da suka zafafa min amma se ban bari sun yi tasiri a raina ba, mafi aala shine na bata masa rai wanda shine aiming dina kuma na ci riba dan haka se na tashi na maida kofa ta na rufe tare da kashe wuta na koma na kwanta tare da rufe ido bayan nayi addu'a, aikuwa ba jimawa bacci yayi awon gaba dani.
Washegari tun bakwai saura na fice dan bani ce da girki ba bana kuma bukatar abin karin su, a office na hada tea da heater na dan ina da komai na bukata, na karya a nutse hankali kwance sannan na shiga aiki na raina fes.
Karfe tara daidai na kwaso takardu zuwa cikin hall din da zamu yi meeting din ma'aikata gaba daya, a nan naga Salees sedai kallo daya yamin ya dauke kai ni ma kuma ban kuma kallon sa ba muka shiga abin da ya kawo mu, muna gamawa na koma office dina, karfe biyu nayi na tashi aiki, yau kam ban iya dauke ido daga hanyar gidan mu ba duk da zuciya ta na fada min kar nayi amma wata bangaren na tunzura ni kan naje dan ko na tambayi Salees baze bari ni ba, tun bayan auren Mariya ya dauki wata banzar akidar kulle ya ɗorawa kan sa, har gwara ma ni ina zuwa aiki ita Mariya ba inda take zuwa se ta rufe watanni shida bata fita a gida ba, sauƙin ta yana kai wa iyayen ta ya'yan ita ce dai se sanda ya so sannan ze kai ta da dare, nima haka se dare yake bari na zuwa gida ko ya kai ni, daga baya ne nake takura masa in wuce daga wajen aiki shima ba ko yaushe yake yadda ba.
Ajiyar zuciya na sauke bayan na gama daidaita parking a compound din gidan mu kana cike da matsanancin kewa nake bin ko ina da ido ganin an sake gyara shi yayi kyau fiye da da, gwanin sha'awa ko ina ya sha sabon paint ga kuma shuke shuke masu daukan hankali, ba karamin kokari su yayan mu ke yi ba akan gidan mu shiyasa kullum cikin sa albarkar Abba da Ummi suke, gidan mu babban gida ne tun a da dan Abban mu na cikin masu kudin unguwar mu, compound din gidan mu babbane dan yana daukar motoci sama da biyar, a takaice dai ze dauki mota bakwai ko takwas batare da takura ba, sassa uku ne a gidan mu, bangaren samari wanda yanzu duk sun yi aure, bangaren Abban mu se part din Ummin mu inda a nan muka rayu ni da yayata salima.
A hankali na bude kofa na fito me gadi ya washe baki yana min sannu da zuwa haka ma sauran ma'aikatan mu, na amsa a mutumce muka gaisa kana na nufi main falo din mu.......................
Ouummey 📚✍️
Ouummey 08 {5/6/2023 }
😭 *RASHIN HAIHUWA*😭
_(Ƙaddarar wasu matan)_
Na
💝💖* Ouummey* 💞💕
Wattpad @ouummey
Ouummey 08
*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*.
____________________________________________________________________________
_Free Chapter Eight _
A hankali na tura kofar na shiga baki na dauke da sallama, Muryar Ummi da ta amsa min yasa na san tana zaune a falon so ina cire takalmi na na shige gaba daya na cike da dokin ganin ta, aikuwa da gudu na karasa na fada kan ta ina dariya
"Kai kai kai, kayar dani kike son yi Khadijah, irin wannan fadowa ai se ki karya ni, wai ke bama ki san kin girma bane?"
Ummi ta fada cikin dariya itama tana rike ni a jikin ta, gyarawa nayi na zauna kusa da ita kamar zan koma cikin ta na kwantar da kaina kan kafadar ta ina fadin
"Nayi kewar ki ne sosai Ummi na, wata uku fa rabon da nazo naga Ummi na ai nayi kokari".
"Ba wani kokari, mu da ada mace se tayi shekara bata je gida ba in ba wani abun ne ya faru ba".
Zaro ido nayi, shekara, lallai
"Tab wallahi ba zan iya shekara banzo gida ba, waiiii".
Hararata Ummi tayi
"To in ba'a barki ba ya zaki yi ai dole ki zauna".
"Ai ko daga wajen aiki ne se na biyo, yanzu haka fa Salees be san zan zo nan ba, kawai na kasa daurewa ne na biyo".
Ban san abinda ya kaini da shegen surutu na na fadi haka gaban Ummi ba bayan na san halin ta, aikuwa ture kai na tayi da sauri daga jikin ta lamarin da yasa gaba na ya fadi ga kuma amon muryar ta cikin ban umarnin in juyo gare ta cikin tune me shaida sam babu wasa a tattare da ita.
Matsawa nayi daga kusa da ita da dan sauri kadan dan Ummin mu na da saurin hannu wataran duk da bata fiye yi min ba amma ina shakkar bacin ran ta
"Kika ce ba da sanin mijin ki kika zo nan ba?".
Yadda nake raba ido a wajen zaka dauka kisan kai nayi dan Ummin mu bata wasa da yaro akan gaskiya, duk shirin da kuke da son da take nuna maka baze hana ta rikide ba a take.
"Uhm ko na tambaye shi baze bar ni bane Ummi".
"Okay se hakan ya zama excuse din da zakiyi satar fita?, Saboda kina takamar kina aiki ko?, Ita yar uwar ki ba haka take zaune ba, ko kuwa kin fita iya son gida da iyaye ne?".
Da sauri na girgiza kai alamun a'a kana murya na rawa na shiga bata hakuri, aikuwa na sha fada kafin ta hakuran sannan ta ɗora da nasiha kan biyayya da hakuri cikin zamantakewar aure.
"Ummi wallahi na gaji da zaman gidan nan, jiya zuwa yau ne fa kawai nayi farin ciki amma kusan kullum cikin damuwa da bacin rai nake".
Shiru Ummi tayi bata ce komai ba se tsura min ido da tayi, ban so na fada mata ba dan nasan zata damu amma waye nake dashi bayan ita, uwa tafi kowa fahimta da kuma sauraren ya'yan ta haka kuma cikin hikima da basira zata kwantar musu da hankali, duk da mun yi magana da Abba har naji sauki sedai ba kamar Ummi ba dan Abba da yace ze kira ni da safe be kira ba, nasan kuma ba komai yake gudu ba face ji na cikin tashin hankali, sedai nasan da Ummi ce wallahi se ta kira ni, ba kira ba kiraye kiraye ma dan uwa daban ce, ina son iyaye na duka amma matsalar mace a gidan aure yar uwar ta mace ce kawai zata fahimta.
"Akwai abinda ke faruwa wanda ya kamata na sani ne Dijeh?"
Seda na sauke ajiyar zuciya kafin na shiga bayyana mata halin da nake ciki, sedai dole na boye wasu abubuwan dan nasan ze sa Ummi taji haushin Salees sosai wanda maybe har mu shirya ita tana kallon shi da abin, ba kuma wai Ummi bace kadai haka duka iyaye suke so pls yan uwa mu dinga sanin iya abinda zamu fada a gidan iyayen mu.
"Ki kara hakuri khadeejah, ina da tabbacin Allah baze bar rayuwar ki haka ba insha Allah, ki cigaba da kau da kai akan shi da matar shi da ƴaƴan shi, ban da daukar hudubar banza duk da nasan ba kawaye ke gare ki ba, amma zuciya ma na iya kai mutum ta baro, ki rike addu'a da karatun Kur'ani, komai yayi zafi maganin sa Allah, nima ina ta taya ki kullum, insha Allah Allah zai dube ki da duk ma masu iri matsalar ki".
"Ameen Ummi na Nagode sosai".
"Se kuma batun gudun mijin ki, kar in kuma jin wannan shashancin a wajen ki, ban sani ba ko sakarcin autanci ke damun ki, wataran in kika yi wani abin kamar in zane ki, nasan kin sani amma bari na tuna miki duk randa kika bijirewa bukatar mijin ki zaki kwana ne Mala'iku na tsine miki in har baki roki gafarar sa ba, dan haka umarni ne na baki in kin koma kije ki bashi hakuri kuma ban yarda ki bar shi ba har se kin tabbatar ya hakura, ban da wautar ki khadeejah ai ita mace zata iya kwatowa kan ta daraja cikin ruwan sanyi batare da tashin hankali ta hanyar irin haukan da kika yi ba, ga kuma kishiya a kusa dake da take jiran kowace dama dan sake karbe miki miji amma baki lura ba".
Haka Ummi tayi ta min nasiha tare da karin tips din kula da miji iri iri, kar kuyi mamaki dan dama ni bani da kawaye, Ummi ce kawata ita da salima haka kuma itace uwata, wajen shawara ta bani wajen gyara tayi min wajen fada ma duka haka.
Kayan gyara masu kyau da inganci ta hado min na karba cike da godiya dan Ummi tsohuwar likita ce, komai zata yi tana yin wanda tasan baze zama illa ga lafiya ba, shiyasa tun muna gida ta ɗora mu kan akidar fruit dan tace babu abinda ya kai shi amfani jikin ya mace shiyasa har yanzu ya bi jikina kullum se na sha shi kafin na kwanta.
A sanyaye na ke tuki dan fa Ummi bata bar ni na wani zauna ba, kwata kwata ko minti talatin ban rufa ba ta kore ni da tsattsauran gargadi, kalaman ta nake tariyowa lokacin da ta rako ni compound
"Ita mace nasarar rayuwar ta shine gidan miji Khadijah, nasan bakya jin dadin zaman sedai hakuri zaki yi dan bake kadai ke irin wannan situation din ba, bar ganin taki Kaddarar wallahi da za kiji ta wata se kin ji taki shafar mai ne, se kin ji ke taki ba komai bane compared to ta wata, so ki godewa Allah da niimar da yayi miki ki rike ta hannu bibbiyu ki cigaba da hakuri, masu irin Kaddarar ki da yawan su wasu na gidan iyayen su, ba dan komai ba se dan sun kasa hakuri, ko kuwa an kasa hakuri dasu, ke kuwa kin yi hakuri wanda shine ya zaunar dake har yanzu, haka shima Salees ya yi hakurin da ba kowane namiji ze iya ba saboda abin yayi masa yawa, ga iyayen sa da yan uwan sa basa son ki, ga Kaddarar ki sannan kuma kema se ki basu gudunmawa wajen kai shi bango har se an zo an yi batacciya Khadijah?, Ko kuwa kin daina san Salisun kin ne?".
Nayi dariya tuno yadda ta karasa cikin zolaya, na sauke numfashi ina yin alkawarin cigaba da hakuri da kau da kai insha Allah ko dan Ummi na, na lura bata san duk abinda ze raba ni da aurena, a ganin ta maybe ba wanda ze yarda ya aure ni bayan yasan bana haihuwa shiyasa take ta kara min kwarin gwiwa da tausa ta dan na rayu gidan Salees.
Da wannan tunanin na karasa gida na kashe motar tare da fita zuwa gida, a falo na same su gaba daya Salees har ya dawo, cikin murmushi na masa barka da gida na wuce ban kalli Mariya ba.
Ina shiga shima ya shiga dakin, ban kalle shi ba na shiga cire kayan jiki na har na gama na daura towel, ta bayan sa na zagaya na rufe kofar da ya bar mana a buɗe sannan na karasa gaban sa na zuba masa narkakkun idona wanda na shanye shi ina langwabar da kai gefe, lamarin da yasa Salees kasa cewa komai ya shiga kallo na kawai
"Wanka zumaaa naaaa".
Na fada a narke cikin wani salon murya, ban yi wata wata ba na ja hannun sa zuwa bathroom dina, tare mukai wankan ina bada hakuri a aikace, ko da muka fito tuni na ruda Salees ta yarda ya kasa jurewa bare daure alkawarin sa ya shiga min wani salo ne rikita ƙwaƙwalwa nima kuma ban yi kasa a gwiwa ba na taya shi yadda yake so har ma fiye, bayan mun sake wanka kan gado na fada dan na gaji matuka gaya, shima bed din ya biyo ni tare da daga ni gaba daya ya dora kan chest din shi ya na shafa gashi na dana busar, duk shiru muka yi se sautin bugun zuciyar juna da muke ji kafin a hankali na ji muryar Salees di na
"Nagode sosai khadeejah, Nagode matata, Allah yayi miki
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 5 Chapter of 12