Share this page
iyayen ta batare da ni ta kalle ni ba, ban damu da hakan ba na sake daidaita zaman mayafi na tare da ɗaukan handbag dina na kalli Salees "Ni na tafi se na dawo". "No ki tsaya ki sauke baby a school yau ba zan fita da wuri ba". Ya katse ni da sauri daga nufar falo da nayi, dole na ja na tsaya cike da damuwa dan na makara na kuma san se na kara wata a kan wadda nayi saboda sanin halin Ilham wanda uwar ta ta gama poisoning mind din ta a Kai na "Yi sauri kiyi breakfast ku tafi baby, yau Aunty ce zata kaiki". "To Daddy". Tace tare da zama ta shiga tsakuran abincin gaban ta kamar ba zata ci ba, ni kam daga tsayen da nake mamakin Salees ne ya cika min rai ganin yadda be damu da rashin gaishe ni da Ilham tayi ba, na jijjiga kai kawai tare da kallon wristwatch dina me tsada dake daure kan tsintsiyar hannu na kana na maida kan Ilham da se lokacin take yin spoon na uku a abincin. "Eat fast pls Baby, am already late". Ba wanda ya tanka min cikin su ukun haka kuma ba ta fasa cin abincin yadda ta ga dama ba, nikam tuni raina ya ɓaci dan nasan da hujja take yi dan ta bata min lokaci saboda i overheard them once tana fada wa uwar bata san tafiya dani saboda ni nake kai ta wataran kamar dai irin yau in baze fita da wuri ba, budar bakin uwar ta bata shawarar dinga bata lokaci in tare zamu tafi, a cewar ta har na gaji na tafiya ta kafin ta gama shininnikin ta. "Ina ganin zan wuce fa Abban Ilham dan na makara tuni gashi kuma naga ita bata gama ba". Ban jira amincewar sa ba bare umarnin tafiya na shiga takawa zuwa waje dan da kyar ma na lallashi kaina na yi maganar dan kar yaga laifi na sedai ashe ban tsira ba "Wai meke damun ki ne a kwanakin nan Khadijah, ina fa lure dake duk sanda nace ki sauke baby a school se kin kawo uzuri, makara, ba zaki fita da wuri ba and many more, me kike nufi ne?". Seda na lumshe ido jin wata sabuwar fitinar kuma da sanyin safiya kafin silently na juyo Ina tausar Kai na "Babu abinda nake nufi fa Abban Amir, kalli agogo it's already past eight kasan Kuma ka'idan aikina thirty minutes past seven ne na makara". "Ba matsala, zaki iya tafiya zan kai ta da kaina Allah yasa uban ta na da motar". Ɗan jim nayi kamar na tafi sai dai zuciyar neman zaman lafiya ta rinjayi me tunzura ni se kawai na koma cikin falon na zauna tare da rufe ido, daga haka nake jiyo maganar Mariya murya kwance cike da tsantsar kissa da yaudara "Haba baban yara, me ye na fusata haka, ai kaga tana da uzuri me ƙarfi, ko rannan ma ta tafi ta bar baby ne saboda tana da meeting, se kana mata hakuri fa, kasan bata saba da hidimar yara ba". Abin dariya wai Salees se ya dubi mariya "Abin da Khadijah ke min a gidan nan ya fara isa ta, amma ba komai ta cigaba". Se kawai fuuu yayi sama, "Dan Allah Auntyn yara ki dinga kiyaye abinda ze sa Abban Amir ya dinga miki faɗa haka, wallahi bana jin dadi". Ban iya cewa komai ba saboda kullutun da ya tare min makogaro, da na buɗe baki nasan ba me daɗi zan fadawa Mariya ba wanda da nayi hakan nasan wani tashin hankalin ze Kuma zama so se kawai na zabi yin shiru, ina jin ta tashi ta bi mijin ta sama ta bar ni nan zaune na kasa motsi cike da ɓacin ran da ta jagoranci zama silar sa, seda siririyar muryar Ilham yet cike da rashin kunya ta ratsa kunne na "Ni kin ga Malama in baki shirya tafiya ba ki bari in faɗawa uba na ya kai ni, atoh tun da ina da iyayen da suka haife ni su ba juya bane". Wal haka na ware idanuna na sauke kan fuskar yarinyar me cike da kuruciya hadi da yarin ta da a lokacin take shekara na sha uku, fuskar nan irin ta mahaifin ta a yamutse ta turo baki gaba cike da tsiwa yayinda madaidaitan idanun ta ke wulkitawa da hararar da take min. Cike da wani kudiri a raina na mike tare da fita daga falon ina dan karkada mukullin mota na har na karasa tare da budewa, farar mota ce me kyau tasha wanki tana ta ƙyalli, da addu'a na bude mazauni na na shiga tare da rufewa kana nayi unlocking sabida ta shiga dan ina hango ta biye da bayana, murmushi nayi jin shigar ta bayan motar wato ta mai da ni driver Kamar yadda ta saba in tafiya ta haɗa mu tun da ta fara wayo. Sai da muka hau titi sosai bayan na bawa me gadi ihsanin da na saba na cigaba da tuki na cike da nutsuwa, ba wata tafiye me nisa muka yi ba dan bamu gama fita daga unguwar ba na tsayar da mota tare da bude murfin na fita, door ɗin da Ilham ke zaune na bude tare da finciko ta a fusace har seda ta tsorata, na bude gaba na sakata bayan na watsa mata wani shegen kallo me cike da gargadi hakan yasa bata yi yunkurin komawa bayan ba har na shiga mazauni na. Kyakkyawan mari me kyau nayi wa bakin ta da ya gama zuba min rashin kunya ta yadda seda ta sa ihu tana rike bakin ga ba halin guduwa na rufe motar, kunnen ta na kama na riƙe da kyau ta yadda na san gargadi na ze shige ta na fiddo kyawawan ido na waje na haske ta dasu ina zare su "Duk sanda kika kuma yi min rashin kunya, kallon banza ko harara se na ci uban ki tun da baki da kirki, kina zuwa school kina haduwa da marasa tarbiyyan yara kina koya ko?". Da sauri ta girgiza kai jikin ta na rawa dan yadda na mata ba ƙaramin tsorata tayi ba ga bakin ta dake zafi dan har lips din sun fashe "Ni ba sa'ar ki bace balle ki kawo min iskanci, duk rashin mutuncin da ke kan ki se na sauke miki shi dan duk kika kuma min ɗaya daga abin da na faɗa se na kulle ki a daki na zane ki ciki da bai ko kuwa in wullo ki daga sama ki fado ki mutu kowa ya huta, zaki kara?". Yanzu ma da sauri ta girgiza kai na kuwa sake haɗe rai tare da zare mata ido "Baki da bakin magana ne kike min knodding?". Yadda nayi maganan a tsawace yasa bakin ta na rawa ta furta "A'a...a'a...ba zan kuma ba...". A firgice, haka na mata warning me kyau kafin na sake ta bayan nasa ta gyara kan ta na tashi mota muka cigaba da tafiya ina bin karatun Alkur'ani da nasa suratul Noor cikin raina kuwa cike fal da tunanin yadda zamu kaya da boss dina wajen aiki saboda nayi makara fiye da ka'ida a tsukin. Har cikin school premises din na kai ta tare da kara mata kudin break ta karba tare da barin wajen da sauri, na bi bayan ta da kallo ina tariyo tsoro na da na hango cikin idan ta sannan na fita, se kuma tunanin yadda zamu kwashe da Salees in ta faɗa masa ya fado min, dogon tsaki na ja ina jin na shiryawa duk ma me ze faru, abu ɗaya na sani ba zan dau raini daga uwar ya in Kuma na dau yarinyar ba, yar da da na sami haihuwa da tuni ina da sama da ita sosai, kai baze sabu ba wannan karon nima na shiryawa duk abinda Salees ya taka. Da wannan tunanin na karasa wajen aiki na inda nake aiki da ma'aikatar haraji wato revenue nake kuma da office na bakwai mafi girma a wajen, sai da na kai uzurin rashin lafiya wa me gidana kan na koma office ɗina Ina istigfar na karyar da Salees yasa nayi. Aikina nayi cikin nutsuwa duk da sa'i da lokaci wasu abubuwan na daga rayuwa ta kan fado min cikin rai sai dai bana bari ya zauna balle ya hana ni aiki na ke ture shi gefe. Waya ta ce ta dauki soft ringtone me daɗi wanda na sawa duk family na, ina dubawa na ga Ummi na ce, take naji wani sanyi ya shiga sauka cikin raina na dau call din cike da farin cikin jin muryar mahaifiya ta "Ummii naa" "Dijeehh naaah". Itama ta amsa min cike da so da kauna ta wanda suka fallasa kan su sanadin rashin haihuwa da Allah ya jarrabe ni dashi "I miss You Ummi naa, hope kina lafiya ba abinda ke damar min mamana". Sai da tayi yar dariya sannan ta amsa min "Ina lafiya Khadijah, ina fatan kema haka kuma babu wani matsala ko?". "Alhamdulillah, Allah ya kara muku lafiya ke da Abba na, matsala kam babu Ummi sai dai duk da haka muna bukatar addu'ar ku". "Wannan kam a kullum ba'a fashi Khadijah, kullum addu'a ta da fatana shine Allah ya azurta ki da rabo me albarka, Allah ya kare min ku ya tsare ku daga dukkan wani sharri ya albarkace ku ya kuma hada min kan ku". "Amin Ummi na, Allah ya saka da alkhairi ya kara girma tare da nisan kwana me albarka". "Amin, ki kwantar da hankalin ki ki cigaba da rayuwar ki cike da tawakkali tare da godiya ga Allah, har kullum ina faɗa miki be manta dake ba ba kuma baya son ki bane ya jarrabe ki, ki rike addu'a ki tsarkake zuciyar ki ki kuma zauna da abokiyar zaman ki Lafiya, dan Allah Khadijah kar ki bari sheɗan ya zuga ki a kan ƴaƴan ta ko ita, in da kara da mutuntaka ya'yan mijin ki naki ne, ki gyara musu ina suka kuskure amma ban da cutar wa dan Allah". Wani irin rauni ne ya lulluɓe ni kamar yadda ya kasance yana faruwa duk Ummi take min nasiha "Insha da Ummi na, ina iya kokari na ki cigaba da taya ni da addu'a, ina autan ki ne ban ji shi ba kwana biyu?". "Allah ya shige mana gaba, auta yana can ya fita neman maganar da ya saba, ai ni dai wannan da se Allah ya shirya min amma jin magana kam ba'a cewa komai". Da haka muka bar waccan maganar muka koma hirar mu har lokacin da muka yi sallama na aje wayar ina sauke numfashi.......................! Ouummey 📚✍🏻. Ouummey 03 {4/29/2023 } 😭 *RASHIN HAIHUWA*😭 _(Ƙaddarar wasu matan)_ Na 💝💖* Ouummey* 💞💕 Wattpad @ouummey Ouummey 003 *Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*. ____________________________________________________________________________                _Free Chapter Three_ Hankali a kwance na tashi aiki tare da tattaro kaya na na fito, tsayawa nayi ina gaisawa da abokiyar aiki na me suna A'isha "Yau ba zaki jira oga ba kenan?". "Ai bana tunanin oga ya shigo yau dan a gida na bar shi". Na bata amsa, akan Salees take magana dan wajen aikin mu daya da shi sai dai ya fi ni matsayi da office uku, mataki na uku yake a ma'aikatar ni ina na bakwai "Eh na manta fa, kin san zasu je meeting a main branch so yau zasu tafi". Da yake na amsa mata dan na manta da batun haka kuma da zan fito be min sallama ze tafi ba, da haka muka rabu na wuce wajen mota na na shiga tare da barin ma'aikatar. Sannu a hankali nake driving zuciya ta cike da tunanika barkatai, wato dai yanzu ban da sauran matsayi a wajen Salees, da ni da banza kwance kusan ɗaya muke, to in ba haka ba ai ya cancanta ya min sallamar ze tafi ko. Wai a duk cikin yanayin da nake sai da wani bangare na zuciya ta ya dinga tursasani yiwa Salees uzuri, ban ja ba na yi masa ta hanyar yin tunanin maybe dan yasan na san zancen ne tun a office. Seda na tsaya a mall nayi siyayyan kaya shafa na da suka yi kasa tare kuma da undies dina da naga kaman sun ɗan yi sanyi, ban fito ba se da na siyowa baby wato Ilham wata gown me kyau da ta burge ni Amir kuma wani takalmi me kyau, wannan sabo na ne bana yin siyayya ban musu tsaraba ba har Salees, Mariya ce dai ban taɓa ɗorawa kaina yin wannan karyar ba dan ba zan iya ba, shima Salees ɗin daga baya aje wa nayi ganin ba sannu bare na gode. Sai da na adana motar inda ya kamata sannan na kwashi ledoji na zuwa main falon mu, da sallama a baki na na shiga , yuuuu haka Mariya da ƙawayen ta suka zuba min ido kamar sun ga wata sabuwar halitta lamarin da yasa naji na tsargu dan kafin na shigo kaya kaya haka nake jin surutun su. Kadaran kadahan na musu sannu da gida na wuce daki na ina tafe ina jin kaifin idanun su da suka min rakiya da shi, zube ledojin nayi kan bed tare da zama ina aje numfashi, seda na huta sannan na cire kaya tare da shiga toilet na yi wanka. Jakar shopping ɗin su Amir na ɗauka na fita bayan na shirya cikin atamfa ta purple color ɗinkin riga da skirt da suka zauna a jikina suka kuma kama ni wanda yawancin dinkuna na duka haka suke, duk tsadar kaya bana bakin cikin kacaccala shi wajen yin dinkin da nasan zasu zauna a jikina in birge me gida. "Sannun ku fa, maman Ilham ga wannan nasu Amir ne". Na faɗa ina aje mata ledar a gaban ta kana na juya zuwa kitchen dan yin girki "Oh mace har mace amma bata da wani amfani, to meye amfanin juya da bata haihuwa?". Kalaman daya daga cikin su da na jiyo dan dama a yadda ta daga sauti take magana ta faɗa ne dan naji "Haba ke kuwa Asmah, bana san neman magana, ya muna zaune ƙalau da yar uwa ta kina min irin wannan kalaman?, Gaskiya bana so". Mariya ta fada da murya me kaman tana dariya ne ko kuwa, nidai ban tsaya ba na shige kitchen din na Kai jingine jikin Island da sauri ina sauke numfashi a jere a jere kamar wadda tayi tseren gudu, makogaro na ya bushe kamar wadda ta shekara bata sha ruwa ba, da kyar na iya lakato wani yawu me daci na haɗiye ina lumshe ido, a kuma lokacin ruwan hawaye ya fara zarya kan kunci na, halin da na shiga a lokacin ba me bayyanuwa bane. Sanin suna falon yasa na daure zuciya ta na lallashi kaina na hada fruit salad maimakon noodles da na shigo da niyyar yi, juice na ɗauka me sanyi tare da bowl dina na fita cike da fatan kar wata ta kwata faɗa min irin maganganun nan dan a yadda nake ji zan iya biye musu muyi duk wadda ta kama. "Auntyn yara angode fa". Yatsu biyu na daga mata batare da nace komai ba na shige ɗaki, da kyar da sidin goshi na sha salad din nan dan wani daci naji yana min a baki. Kuskure baki nayi bayan na gama na ture plates din gefe tare da ɗaukan waya ta ina dubawa wai ko zanga missed call din Salees, sedai ga mamaki na ko text babu balle kira, murmushin takaici nayi tare da kiran shi ni, ta dade tana ringing be dauka ba har ta katse na sake kira shima be ɗauka ba, seda na masa miss call biyar sannan ya turo min short text "Busy". That's all he said, Ina gani na aje wayar jiki a sanyaye, saboda gudun tunanin da ka iya rufe ni na janyo tablet dina na hada mata keyboard na shiga ayyuka a ciki, duk wanda ya ganni kallo ɗaya ze min yasan ina aikin ne kawai amma ba dan jin dadi ba. Dake Allah Alhakeem ne se gashi tashi ɗaya ya aiko min da sanadin farin ciki madaukaki, ba komai bane face karin matsayi da ake shirin yi a ma'aikatar mu, cikin rahamar Ubangiji kuma har da suna na cikin wanda za'a yi reviewing Wanda muna sa rai in mun tsallake review shikenan promotion ya tabbata. Ban yi farin cikin ni kaɗai ba na kira Ummi na na faɗa mata tare da fatan a taya mu da addu'a ta amsa, yayata Salima na kira itama na sanar da ita, ba tun yau ba na fahimci kunya da nauyi na ta take ji ba sedai ni a raina wani irin girman ta nake gani domin tai min abinda ba kowa ze iya ko kwatanta wa ba. Ta taya ni murna tare da fatan dacewa, tana neman kashe wayar na tare ta da sauri "Ina yaro na?, Shiru baya neman mommy?". "Ba haka bane ba maman Haidar, kin san baban makarantar wuni ya kai shi saboda yaki maida hankali a waccan". "Ayya, dan Allah yaya a kula min da shi sosai, kar a bar min shi da yunwa da damuwa". Daga cikin wayar na jiyo faffaɗan murmushin da tayi tare da amsa min mukai sallama na kashe wayar sabon zafi na sake hudowa daga kirji na sedai tuni na dakatar dashi saboda bana san abinda ze dinga tuno min da baya, duk da present din ma ba dadi ne dashi ba amma bayan nan akwai ciwo me matukar raɗaɗi. Seda na tabbatar ƙawayen Mariya sun tafi dan gidan yayi shiru ba hayaniyar su kana na dau bowl din da nayi amfani dashi na fita zuwa kitchen. Zama nayi a kujera tare da kunna Tv na shiga kallon wata drama da ake yi a mbc Bollywood, cike da zallar nishadi na kalli abina har aka gama na tashi zuwa daki dan It's evening, akwai bukatar in kwance kai na dan sati na biyu yake ciki. Seda nayi Asr sannan na fara tsifar a falo ina yi ina sauraren wani hirar classmates dina a group da sukai ta hanyar voicenote, a lokacin ne kuma baby ta shigo dan se five ake tashin su, da karfin gwiwar ta ta shigo murya a sama tana ihun kiran sunan uwar ta ita kuma tana saukowa daga sama tana amsawa sedai tashi ɗaya taji dif yarinyar tayi shiru. Wai ashe ni da ta tarar cikin falon ne yasa ta ɗauke wuta jikin ta ya shiga rawa, sam ban ma lura ba ni hankali na na kan abinda nake ji seda naji babar na tambayar ta "Me haka, lafiya na ga jikin ki na rawa?, Me ya faru?". Da mamaki na daga kai ina kallon su, yarinyar ta maza ta faɗa jikin mamanta tana zare ido, ko da na gane abinda ke faruwa se kawai na dauke kai na cigaba da abinda nake yi ita kuma taja ta daki tana tambayar ta. Ban san me ta fada wa uwar ba se ganin Mariya nayi a gabana a tsaye kamar wata bishiya "Wane irin rashin imani ne yasa kika yi wa Ilham wannan marin, kin kuwa ga yadda bakin ta ya kumbura?". Kamar kar in tanka se kuma na tanƙwasa kai na sanin shi bayani yana da dadi kuma rigima sam ba abar so bace musamman gare ni da ba hali na bace, zama da Mariya ne yasa har ban san yaushe na canja ba. "Ilham rashin kunya take koyowa Mariya, wai kamar ni zata kalla ta zaga, imagine fa". "Ban gane zagi ba, kin ga tun kafin raina ya ida ɓaci ki min bayani yadda zan fahimta, Ilham ta zage ki tace miki me ?". "Kin san dai ko ke baki isa in miki karya ba balle ƙaramar yarinya kamar ta, ce min tayi wai Allah yasa tana da iyayen da suka haife ta tun da ba juya bane su". Ƙanƙance ido tayi cikin rashin mamaki balle damuwa "To ai ba karya tayi ba tana da iyaye, shima juyan ai ba sharri tayi ba tunda da juya ne su da basu haife ta ba, shine kawai dan wannan yar maganar zaki nemi lahantata, to wallahi bari uban ta ya dawo dan ba zan yarda ba". Iya maƙura raina ya kai wajen ɓaci dan haka na mike tsaye nima kamar yada take "In Kika yarda ma ba sunan ki Mariya ba, haka kuma in Kika fasa fadawa Salees ba ki haifu ba, maza faɗa masa yazo yayi wa khadeeja tuf ta mutu kin ji, shashasha mara tunani, a faɗa miki yarki tayi wannan rashin mutuncin amma ki goyi bayan ta saboda rashin sanin ciwon kai, to ai karki fasa, dan yau dai ba ayi masa haka in zaki gyara ki gyara". "Naki na gyara, nace naki na gyara ɗin, yar ki ko yawa, aikin banza da zaki zo kina wani kinibibi ai se ki bari se kin haifa se karki goyi bayan naki, ko da yake macen da ta shekara sha shida da aure bata taɓa ko bari ba ta ina zata haihu, wai wanda be san ciwon da bane zece ga yadda za'a masa tarbiyya, mtsww juya kawai mara amfani". Wannan kalma ta juya itace kalma mafi ciwo a duk cikin kalaman Mariya, sanin babban weakness dina gorin rashin haihuwa ne yasa Mariya daura damarar cewa se ta ga karshe na, gashi ni kuma bana iya daurewa wannan gorin, ko nayi kokarin haka se fuska ta ta bayyana halin da nake ciki, idanuna da suka yi jajir na kalli mariya dasu se kuma na juya na shige ɗaki da sauri ita kuma ta raka bayan da harara. Cikin son karfafawa kaina gwiwa na dinga tausar kai na dan na gaji da kukan da nake yiwa mariya, na gaji da bata hawayena kan ta, na gaji da komai ma na ta. Haka na wuni a daki saboda bana san fita balle shaidan ya raya min wani abu na biye mata balle kuma azo ace laifi na ne kamar yadda ake ɗora alhakin komai dake faruwa a kaina, saboda ita ɗin kirsasshiyar mace ce da gane halinta na gaskiya se wanda Allah ya ciyar kamar dai iri na da zama ya haɗa ni kishi da ita na zama victim. Washegari ban taya jiran wata Ilham ba na tafiya ta aiki, ko da na gama na dawo a nan na tadda me gidan ya dawo dan ina shiga falon idanun mu suka sarƙe cikin na juna, wani kallo me zafi na watsa masa cike da jin haushin sa, tun da mutumin nan ya tafi be kira ni ba balle text, ni nakira shi ya turo min kalmar "busy", daga ita kuma be kuma cewa komai ba haka kuma be neme ni ba, wanda in rayuwa da adalci kamata yayi ko da ace busy din ne in yayi free ya Kira ni yaji ya nake, ya bani haƙurin tafiya batare da ya sanar dani ba tun da ina da hakki amma duk be yi haka ba se dawo wa nayi na tadda shi a dararraje cikin iyalin sa suna hira cikin farin ciki da alamar rayuwa ta gama yi musu daɗi. Ko da nayi sallama ban lura da sun amsa ko ba su amsa ba nasa kai ciki, kamar in wuce batare da na kula shi ba se kuma zuciya ta tuna min da zaman kishiya a tsakanin mu wato Mariya, haka na daure cikin son nuna babu wata matsala tsakanin mu na tafi gare shi da niyyar yi masa side hug amma se ya goce yana watsa min zazzafar harara lamarin da yasa na ɗan yi turus cike da kunyar yarfa nin da yayi a

Chapter 2 of 12