An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://thausanovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.thausanovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
Ouummey 01 {4/28/2023 }
😭 *RASHIN HAIHUWA*?
_(Ƙaddarar wasu matan)_
Na
💝💖* Ouummey* 💞💕
Wattpad @ouummey
Godiya
Da sunan Allah me Rahma me jin kai, dukkan Godiya ta tabbata ga Allah SWT Ubangijin talikai, me kowa me komai da ya bani ikon fara rubuta wannan littafi me suna a sama cikin koshin lafiya, ina addu'ar Allah ya bani ikon gama shi kamar yadda na faro ya sa mu amfana da duk wani darisin cikin sa, kuskuren cikin sa kuma Allah ya yafe min.
*Jan hankali*.
This book is a total work of fiction, suna, gari kasa ko wani abu daga cikin labarin in aka yi rashin Sa'a yayi daidai da naki to fa arashi ne, ban rubuta wannan littafi dan cin mutunci ko wulakanta wani ba face dan ganin yada ce in fito da virtues din matan da rashin haihuwa yasa ake yi wa kallon kaskantattu, wulakantattu ko marasa amfani, a guji yanke wani abu ko juya min labarin ta kowace siga dan tabbatar da zaman lafiya, kamar yadda na faɗa wannan labarin ƙirƙirarre ne bisa fasaha da baiwar da Allah ya bani tare da yin duba ga rayuwar mu da abubuwan dake faruwa cikin wasu gidajen auren.
*Dedication*
*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sai dan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*.
______________________________________
______________________________________
_Free Chapter One_
Tun daga kasa har sama nake karewa kaina kallo ta cikin tafkeken madubin da ke girke a dakin baccin nawa, babu ta inda na hango wata makusa ko kasawa a tattare da ni, hakan be wadatar da ni ba sai da na sake ɗagowa na sake sako duban tun daga kan yalwataccen gashin kai na bakikirin dake kwance kan kafadu na, a hankali na sauke duba na kan matashiyar fuska ta dake cike da tashen kuruciya, ba wai na budurtaka ba a'a na shekarun tashe ga iri na da muke kan wannan mataki, zagayayyar fuskar ta ɗauke take da wadatattun idanun da Allah ya ƙawata ta dasu, farare tas masu haske da matukar daukar hankali, ban tsawaita ba na sauko kan dogon karan hanci na da ya dada wa fuskar kyau bayan idon, hanci na ba siriri bane zut ɗin nan yana da dan fadi kadan da yasa ya zauna das kan fuskar, kyakkyawan ƙaramin baki na me ɗauke da madaidaitan lips da basu cika karanta ba haka kuma ba manya bane, a hankali kuma na lumshe idona na buɗe tare da sakin kyakkyawan murmushin da ya bayyana jerarrun haƙora na da basu kasance farare ba sedai milk ne masu kyau da suke samun kula a ko yaushe.
Cikin wani irin yanayi na girgiza kai na wani abu na tsirga min cikin raina na sunkuyar dashi kafin cikin karfin halin da na saba yi na bude na cigaba da surveying jikina, a kan cikakken wuya na idanuna suka sauka wanda ke dauke da wasu layi haka ko guru guru zance, cikar kirjina dake fisgar hankali na maida kaina farin ciki na ratsa ni, shafaffen ciki na da bashi da alamar ɗagawa balle in aje tumbin da wasu daga cikin sa'anni na ke korafi dashi suke kuma sha'awar lafewar cikin nawa sai dai gare ni hakan shine ciwo mafi girma ga rayuwa ta dan babban burin na a wannan duniyar be wuce in farka in ga cikina ya tasa kamar kowace mace da Allah ya albarkace ta da arzikin haihuwa ba.
Da kyar na haɗiye wani mugun miyau ina janye duba na daga wajen na maida kan faffaɗa kuma cikakken kugu na wanda shine abu mafi daukar hankali a jikina gaba ɗaya, nikaina yana daya daga cikin halitta na da nake alfahari dashi dan shine kadai abu ɗaya da ya rage min da ya riƙe ni a gidan aure na ya kuma sa nake da yar ragowar kima a idanun mijina wato surar da Allah ya min, ban tsawaita ba na karasa kan kafafuna dake wadace da jan lalle wanda bana rabo shi, lallen ya zauna daras kamar a kai a aka ƙirƙire shi, yadda ya haska farar fata ta kuwa abin ba'a ce wa komai.
Babbar ajiyar zuciya na sauke dana gama karewa kai na kallo kafin cikin sanyin jiki na dauki kwalbar turaren da tuntuni shi ne zan shafa amma na tsaya kallon kaina kamar bakuwar kan nawa, zazzagwa nayi a hannu na na shiga shafe lallausar fata ta dashi lungu da saƙo sannan na aje, wata na kuma ɗauka itama na murza a hannun na shige shafe wasu wurare masu mahimmanci a jikina, ina yi ina yan tunane tunanen da suka zame min jiki a duk lokuta irin wannan.
Ringing din wayata dake aje kan bedside drawer yasa na dawo hankali na sosai na shiga shiri da sauri dan nasan ba kowa ke kiran ba se oga, na dade da sanin ya tsani jira musamman daga gare ni kamar yadda yake faɗa min times without number sai too ifdai nikuma ya riga ya zame min jiki musamman a kwana kin nan.
Kayan bacci na ciro masu kyau, laushi hadi da daukar hankali na zura ina tattare gashi na waje ɗaya na kama shi cikin ribbon, duk da na shafa wasu turaren kafin sa kaya ba hakan ya hanani sake fesa wasu ba wanda suka sa take dakin ya cika da sassanyan kanshi na me ratsa zuciya wanda nake amfani dashi kadai lokacin da zan je ga oga.
Waya ta na ɗauka na kashe batare da duba komai ba dan bani da lokacin hakan me ni na can na jira na kuma san tuni ya cika yayi fam se nayi rarrashi.
Seda na sawa kofa ta key dan gudun matsala da jan magana sannan na wuce upstairs inda nan ne turakar me gidan take, seda nayi Knocking tare da dan dakatawa sannan na tura ƙofar a hankali ina me yin sallama cikin daga murya dan ankarar da na cikin dakin cewa gani nan fa tafe.
Nasan zaku yi mamakin wai na tsaya knocking ni da dakin mijina da addini ya bawa damar shiga wajen sa duk sanda naso haka kuma ganin sa cikin kowane yanayi halak ne gare ni, to ba komai yasa nayi hakan ba face gujewa haduwa da ɓacin rai, a irin wannan yanayin na kan ci karo da mabanbanta takaicin da kan hanani bacci wasu lokutan yayinda wasu lokutan kuwa nake hana zuciya ta damuwa ko da kuwa taso yin hakan.
Ajiyar zuciya nayi hango shi zaune ken bed Yana danna waya, cikin tafiya ta me daukar hankali da kuma karin wasu salo dan sace zuciyar oga na kai gefen mirror ɗin sa na aje yar jakar kayan hannu na sannan na karasa gare sa wanda tun shigowa ta da yayi min kallo ɗaya be sake yi ba.
Cikin jikin sa na shige ina manne masa kamar wata cingum na sanyaya murya dan nasan nayi laifi haka kuma na shagwaɓe fuska cikin fatan samun lagon sa
"Am sorry zuma naaa, na tsaya shirya maka kaina ne ta yadda zaka mori daren ka cike da annashuwa da farin ciki, ayi min afuwar dadewar da nayi plsss".
Na karasa ina kai hannuna cikin ƙirjin sa ina masa waiwayi cikin salon da nasan baze iya jurewa ba, kamar yadda na sani kuwa lumshe idon sa yayi tare da rike hannun da ke yawo jikin nasa kana ya bude su ya zuba kan fuska ta
"Kullum se kince ayi miki hakuri kuma ba haka ze Hana gobe ma ki sake ba, na kasa gane meye matsalar ki Khadijah, ke ba da ba ba jikan da zaki fake da kula da shi ba amma ko mariya dake goyo ba zata faɗa miki kawo uzuri ba, Allah ya sani kin fara kaini bango dan na fara gajiya da uzurorin ki marasa kan gado da bakya rasa na bayar wa kullum".
Daga jikin nasa da nake kwance na lumshe ido zuciya ta na motsawa, ba se Salees ya tuna min da cewa ban taɓa haihuwa ba, ba se Salees ya tunatar da ni bani da tsuntsu bani ga tarko ba dan hakan abu ne da bana taɓa mantawa ko da kuwa acikin mafarki ne.
Sanin shiru na wata matsalar ze jawo yasa na daure rashin daɗi na na bar shi iya cikin raina yayinda a zahiri na ɗago na sumbaci bakin sa ina tabbatar masa insha Allah ba zan kara ba wanda hakan yayi tasiri gare shi dama kuma be fiya riko ba, cikin zakuwa da natsuwa ya shiga birkita nutsuwa ta da salon sa masu tafiya da ruhi na suke kuma karamin kaunar sa a ko da yaushe inda nima tuni na biye masa muka fada cikin wata duniya me wuyar bayyanuwa, seda duk muka sami nutsuwar da ta dace kafin muka shiga wanka dan yin shirin kwanciya.
Ko a cikin toilet din ma be bar ni haka ba dan se da yayi neman maganar sa san rai kafin muka wanko jiki muka fito, cikin sanyin jikin gajiyar da ya tara min na maida kayana tare da hayewa kan gado na lafe ina sauke numfashi yayin da gefe ɗaya nake mamakin rashin faruwar lamarin da ya zame mana jiki cikin watanni ɗaya zuwa biyu da suka wuce.
Ban kai ƙarshen mamakin ba sautin kukan yaro ya fara ratsa kunne na, tun ina jiyo wa kasa kasa har ya fara ƙarfi alamun ana nufo dakin ne, cike da takaici na tsurawa kofar dakin ido cikin jiran faruwar sabon mu, dukan kofar aka shiga yi kamar a filin yaki wai kuma hakan da sunan knocking ne fa ake yi, daga kwancen da nake ban motsa ba naga tashin sa daga kokarin kwanciyar da yake yi kusa da ni ya bude dakin yana ɗan haɗe rai.
"Ka gan shi nan yaki yin shiru, nayi nayi wallahi se kuka yake har na rasa yadda zan masa, ni yadda yake yi ne ma yafi bani tsoro kalli kaga se wani miƙewa yake kamar ze shide".
Ai oga se ya nemi haɗe ran da ya ɗan yi ya rasa ya kai hannu cike da hanzari ya karbi dan ya shiga riritawa, kamar abin shiri yaro maimakon yayi bacci ko yayi shiru ba se ma karawa kukan sa karfi da yayi hakan kuma ya sake dugunzuma hankalin uban duk yabi ya tashi dan Allah ya zuba mishi so da kawa zucin yaya, ko dan ya dade kafin ya same su ne?.
Iya shaka na shaka domin dai a yau na gaza yiwa mariya da Salees uzuri, ba dan komai ba sedan saboda ba yau hakan ya fara faruwa ba, abin kamar ya zame mata sabon da take jin dadin sa ni kuma ya zama sabon da ke taɓa zuciya ta da sani cikin ɓacin rai.
"Amma dai kasan wannan shiga hakki ne ko, yaya muna kwance kawai zaka bude wa wata daki hakan kuma duk be yi ba se an hana ni bacci, shin shima hutun nawa ya zama abin bakin ciki da hassada ne ko kuwa me?.
Wani kallon Salees ya shiga yi min me kama da na mamaki ko kuwa na zallar takaici ne, kafin kuma yayi magana tayi caraf ta riga shi
"Kiyi haƙuri Khadijah, Amir ne ban san me ke damun sa ba kwana biyu, ko kuwa har ya gane uban sa ne oho, kinga har mun kwanta amma yaron yace be san zance ba kuka har na rasa yadda zanyi dashi shi yasa na kawo masa ko ze yi shiru dan mama tace yawan barin yaro yana kuka ba lallashi na jawo masa matsalar ƙwaƙwalwa da kuma ciwon zuciya".
"Kinga dan Allah dakata ba dake nayi magana ba ki bari shi da nake dashi ya amsa min, zuma naaa da kai fa nake magana".
A irin fusacen da Salees ya kalle ni abin seda ya girgiza ni dan kallo ne me shaida Allah ya soki bana kusa da ke
"A sani na dai ke ba kurma bace kin ji me tace ko?".
A yadda nakai geji nima hakuri na ya kare dan haka na bashi tawa amsar da fusatacciyar murya kamar yadda ya min
"Shine nace ina buƙatar sanin me kake nufi da ni ne dan wallahi sedai ko ta fita da yaron daga dakin nan ko ni na fita dan ba za'a dinga hanani bacci ana samun ciwo a banza ba".
"Aikuwa sedai ke ki fita dan da dai dakin uban sa ne cikin gidan uban sa, kinga kuwa maganar a fitar dashi ma ai bata taso ba".
Kuriii na masa da ido ina kallon sa yadda ya fadi abinda ya faɗa hankali kwance, ban san me yasa murmushi ya zabi wanzuwa a fuska ta ba a lokacin duk kuwa da tsananin ɓacin da rai na yayi
"Amma dai kasan nima ina da gidan uba ba daga sama na fado ba ko Salees, so ba daga daki ba ko gidan kace in fice ma yanzu se in tafi ai".
"Mtsww, Ni dai ban ce ki fita daga gida ba sedai in Kuma ke kika so, daki dai nace ki fita dan yaro na ba inda zeje, ke ban da ma rashin imani kina kallon irin kukan da yaron yake yi ko tausayin sa ba kiji ba balle mahaifiyar sa da duk hankalin ta ke tashe se wani soki burutsu kike yi, ko da yake ai baki san ya rainon da yake ba tun da baki taɓa yi ba dole ki ga kamar karya ne".
A wannan gaɓar kam tuni idanu na suka tara ruwan bakin ciki, ɓacin rai da kuma wani irin rauni dake tasowa tun daga can karkashin zuciya ta, ban kuma cewa komai ba na sauko daga gadon tare da ƙarasawa inda na aje jakata na ɗauka ina nufar hanyar fita daga dakin dauke da alwashi me girma cikin raina.
Kan bed na faɗa ina sakin kukan da nayi dauriyar riƙewa, wani irin kuka me fitar da sauti sosai jikina na rawa, kallo ɗaya me imani da tausayi ze min yaji zuciyar sa ta motsa, Allah ya sani na dade da gajiya da zaman auren Salees, ba dan na daina son sa saba, ba dan bana son cigaba da rayuwa dashi ba, sai dan in aka cigaba da tafiya a haka lallai zuciya ta na gab da bugawa, in Kuma haka be faru ba na tabbata jinina se yayi yawan da saukowar sa se Allah, yanzu haka ina mamakin yadda ko yaushe nayi gwajin bp nake samun negative result dan a irin damuwar da nake ciki hawan jini shine cuta mafi kankanta da ɓacin ran gidan Salees ka iya haifar min...................!.
_*Ba zan gaji da fada muku ba haka ba zan gaji da tabbatar muku da ba gazawa ce ta sa Allah ya kaddare ku da rashin haihuwa ba face jarraba irin tasa da yake yi dan gwada karfin imanin duk wanda yace yayi imani, da zafi, da ciwo, da damuwa, da rauni amma in akaa daure tabbas rabon me girma ne kamar yadda Allah da kan sa yace yana kunyar matan da basu taɓa haihuwa ba, Allah ya bada masu albarka inda rabo, in Kuma babu Allah ya azurta ku da dauriya da karfin iya jure wannan ƙaddara*_.
Comment, share and follow.
Ouummey 📚✍🏻.
Ouummey 02 {4/28/2023 }
😭 *RASHIN HAIHUWA*😭
_(Ƙaddarar wasu matan)_
Na
💝💖* Ouummey* 💞💕
Wattpad @ouummey
*Wannan littafi nawa gaba ki dayan sa sadaukarwa ne ga duk macen da Allah ya jarraba da ƙaddarar RASHIN HAIHUWA, ina me addu'ar Allah ya baku ikon cinye jarrabawar ku ya tabbatar muku da rabon ku ranar gobe kiyama, ina fatan Allah ya hakurtar da zuciyoyin ku ya baku babban rabo a aljanna, Allah ya albarkaci dukkan mata, wanda suka haihu da ma wanda Allah be basu ba, ba dan sun gaza ko baya san su ba sedan ya gwada imanin su, ina muku fatan rabauta da rabo me girma, tabbas mace uwa ce, kuma abar girmamawa ce da mutuntawa!*.
____________________________________________________________________________
_Free Chapter two_
Haka na kwana cike da kunci da ɓacin rai, kwata kwata dama ban sa ran Salees ya biyo ni wani rarrashi ba dan nasan ba yi zeyi ba, so da yawa na kan yi mamaki yadda tashi ɗaya rayuwar aure na ta juye daga happy married life cike da so da kauna zuwa wani yanayi da ba zan iya faɗa ba.
Sai dai ba abin mamaki bane in akayi duba da irin nakasun da mutane ke gani tattare da ni, ba wai tawayar halitta ba, bana hali ba face na wani arziki da Allah ke bawa bayin sa da yaso ba dan kuma dan ya tsane mu mu da be bawa ba, a'a sai dai dan ya jarraba karfin imanin mu, wanda in ba ya shiga cikin lamarin ire ire na ba cin wannan jarrabawar tana yin wuya domin abun ba sauki, lamarin babu dadi sam haka yanayin me matukar taɓa zuciya ne.
Da safe ko da na tashi ban fasa yin abin kari ba sanin nike da girki, sharp sharp na hada breakfast tare da zubewa kan table kana na ɗora na Ilham da zata tafi dashi school sannan na koma ɗaki dan shirya wa zuwa wajen aiki, a hanzarce nake komai dan na makara saboda rashin samun bacci da wuri sanadin ɓacin ran Salees da mariya.
Sai da na tabbatar da zaman gyalen jiki na sannan na fesa turare kasa ƙasa wanda ba'a jin ƙamshin sa se an matse min waje sosai sannan na fito, kan table na tadda su zaune cikin farin ciki suna hira abin su, da ka gan su kaga wasu ma'aurata da rayuwa kewa dadi sabanin ni da rayuwar aure na ke cike da bakin ciki, ɓacin rai tare da takaicin da namiji iri iri.
Kau da damuwa ta nayi na shanye ta cikin ciki na na karasa tare da jan kujera na zauna
"Good morning zuma na, fatan ka tashi cikin koshin lafiya".
Na faɗa ina kissing lips din sa kana goshin sa sannan na juya ga mariya
"Barka da safiya maman Ilham, fatan kun tashi lafiya".
Duk da naga sanda yanayin ta ya canja lokacin da na sumbaci Salees amma tuni ta ture tare da maye gurbin matsewar fuskar ta da wadataccen murmushi tana amsa min har da yar dariyar ta
"Lafiya lau Auntyn yara, fatan kema haka".
"Alhamdulillah kam".
"Ehm nace dan Allah kiyi haƙuri da abinda ya faru jiya, sha'ani na yara ne me sa mutum ya rude amma ba da wata manufa nake kawo Amir ba, kin san al'amarin raino in ba wanda ya taɓa yi ko yake cikin yi wani abin ba yarda zaka yi in an fada ba, ni kaina da Umma ke faɗa min akwai yara masu kukan dare ban yarda ba seda na haihu, amma karki damu kema soon zaki fahimta in Kika haifa".
Duk wannan surutun da take yi ni tuni nayi nisa da zuba abincin da zan karya dan Ina zama na zubawa Salees, ban ɗago ba duk da naji me tace ban kuma yi mamakin maganar da ta fa min a wayance ba dan indai ita ce nasan zata yi fiye da haka dan tuni na dade da gane da kuma fahimtar inda ta dosa.
Wahalallen murmushi na kakaro na ɗorawa fuska ta na ɗago ina duban ta
"Haba ai ba wani abu bane maman Ilham karki damu".
Haka muka fara cin abinci tana ta zungurin Salees da hirar Amir da ta Ilham shi kuma ya biye mata dan a bayyane yake yana mugun son ƴaƴan sa tare da kulawa da duk abinda ya shafe su, gane hakan ne kuma yasa mariya ta samu damar kuntata min kamar yadda ta dauri niyyar yi tun haihuwar Ilham zuwa yanzu kan Amir.
Tissue nasa na goge baki na ina miƙewa daidai fitowar Ilham daga dakin mamanta goye da skul bag ɗin ta na tafiya makaranta, tun da yarinyar ta fito na kalle ta na kau da kai batare da na sake duban ta ba duk kuwa da yadda nake son yin hakan.
Allah ya sani ina matuƙar kaunar Ilham saboda yadda ta dauko kamaninn Salees kamar yayi kaki, yanayin ta na surutu da sakewa yasa take da farin jinin jama'a ciki kuwa har da ni sedai dole nake koyar dannewa tun wani incident da ya taɓa faruwa.
"Good morning Daddy, good morning Mommy".
Ilham ta gaida
All Chapters
Font Size
16px
Background
Progress
Chapter 1 Chapter of 12