Share this page
6 / 6
son muje iyayenta su san abinda take yi ne domin suyi mata fada. Idan aka kyale ta zata cigaba da shirka ne. Ni fa shiyasa naji na ma gaji da zama da ita Malam. Tunda har take iya zuwa wurin bokaye ko yan tsibbu. Ai tasan hakan ba karamin sabo bane. Eh lallai zaka ce haka mana tunda ka kwashi budurwa. Kunya ce ta kama shi jin malam ya fadi haka. Suna shiga motar Ahmad, malam yace ban aminci ko Yaya yasan maganar nan ba balle Ummulkhair. Shi rike sirri yana da kyau kuma rufin asirin matarka rufin asirinka ne. Hotoro suka nufa gidansu Mufida. Mahaifinta ne zaune da Uncle Ahmad da Dr Abdallah. Sun gaisa cikin girmama juna sannan suka fara abinda ya kawo su. Mufida aka kirawo tare da mahaifiyarta wadda ta shigo ne don ta gaisa da Malam. Tana shirin fita yace ai gara ta zauna. Malam yace me akayi miki kika dawo gida Mufida? Rainin wayo tace a ranta kamar ba yar cikinsa ya turo mata suyi sharing miji ba. A zahiri kuwa cewa tayi babu komai. Ashe baki san cewa duk matar da take fita ba tare da izinin mijinta ba duk taku daya a wuta take yinsa ba. (To yan uwana mata masu tambayar fita daya suyi biye biye ko ayi satar unguwa. Don Allah mu kiyaye domin haramun ne). Da bata bada amsa ba sai ya fiddo ledar da Uncle ya kawo mishi. Tana gani ta razana sosai Malam ya hade fuska yana mata magana a matsayinsa na malami ba uban miji ba. Kuka ta fara yi iyayenta basu gane me yake faruwa ba sai da uncle yayi musu bayani. Kuma ta fara amfani dasu ne kafin ma zancen aurensa ya tashi. Mahaifiyarta ce ta rinka dukanta yanzu zubar min da mutumci zaki yi mufida? Ashe ban miki tarbiyar arziki ba. Tana magana tana kuka. Babanta duk kunya ta kamashi. Shi dai Ahmad baice komai ba. Babanta ya dago kai Mufida wa ya koya miki zuwa gidan boka? Baki san sallarki ta kwanaki arbain bazasu karbu ba banda shirka ta yadda da su. Cikin kuka tace wallahi Baba ba boka bane. Malami ne shima sunansa Mai Dafa'i. Sunansa mai uwarki dai inji mamanta. Malam yace haba hajiya ya zaki zage ta. Huci kawai take yi don takaici so tayi a barta ta jibgi yar banza. Cikin kuka ta kwatanta gidansa a wata unguwa. Dabara ta fadowa malam yace ai kawarki da kuke zuwa tare ce ta tona miki asiri. Ta kalle shi tana sharar hawaye kuma fa wallahi malam ita ce ta dage sai munje. Lallai Laraba ta cuceni. Yace to ya kamata kusani akwai bambanci tsakanin boka da malam. Duk wanda zai zauna yana bugun kasa ko a baki dogon carbi ace ki kama daya duk ba hanyar Allah bace. Yanzu an baki hoda da kwalli ki mallake miji to daga mallakar sai me. Karshe bazaki taba jin dadin zaman ba tunda kinsan ba don Allah yake miki ba kuma tun daga kabari a fara azabtar da mutum kafin aje lahira. Suna amfani ne da son duniyarku sai su kira kansu malamai a wurin irinku masu sauran imanin da basa son zuwa wurin boka. Mufida tayi shiru maganar ta shigeta ta bawa iyayenta da mijinta hakuri. Malam yace ta shirya yaranta ta koma gida tunda ba sakinta mijinta yayi ba. Tana fita Malam yace da Ahmad ka nemi laraban nan ko wace kayi mata nasiha idan bata ji ba ka hanata shiga gidanka. Baban Mufida yace au baka santa ba dama. Wayo kawai nayi mata nasan dole kaita aka yi. Tunda ta koma gidan Uncle Ahmad ake zaman lafiya. Rayuwarsu abin shaawa. Lokacin da khairi ta sami ciki Uncle Ahmad ya ga shagwaba iri iri. Mufida tana biye mata suna tsula tsiya son ransu. Tun safe take jin ciwo kadan kadan tana daurewa. Suna falo Mufida tace anya Khairi ko abin yazo ne. Khairi tace a'a saura sati uku fa. Cikin dare kuwa ciwo yasa ta farka daga bacci ta dumawa Uncle dundu ya tashi ba shiri. Kai khairina me ya faru. Jin tana numfashi da kyar yayi saurin tashi ya kunna fitila. Cikinta ta nuna masa yace yana zuwa ya tafi ya dauko handgloves zai dubata sai mamaki ya kamashi ganin har kai ya fara fitowa. A daki su kadai ya taimaka mata ta haifo masa santaleliyar budurwa. Sai da ya yanke cibi ya jira mahaifa ta fito sannan yaje ya taso mufida. Tana ganin jini jikinta ya fara rawa na shiga uku Abban Iman meye wannan? Wani kuka taji baby tana sanar da zuwanta. Ai bata tsaya daukan baby ba ta tafi neman ruwan zafi. Ta wanke baby tas tasa mata kaya. Itama khairi tayi wanka mufida ta hada mata tea mai zafi tasha. Sai da asuba suka rinka buga waya Umma da kyar ta jira takwas na safe tayi. Malam yana ta mata tsiya yar fari ce fa. Tace ai yau duk mai iyawa ya kirani mara kunya amma sai na je. Khairi na kwance a daki ya shiga. Khairin Uncle a zama mama. Tayi dariya dama jira nake kazo. To gani wani cikin zan miki ne...an gaya maka ina tsoro ne ....yanzu dai kaga banyi raki ba kyauta zaka bani. Kin manta naci dundu a baya. Kinsa ina tafiya kamar tare mukayi nakudar. Rungume matarsa yayi Allah Yayi miki albarka. I love you...love you too uncle dina. Nan suka yi shawarar sunan baby da zaa sawa baby. Suna ta boye boye sai ranar suna kowa yaji sunan yarinya Hawwa amma zasu kirata Jiddah saboda sunan Yakumbo ne. Ita kam Yakumbo har kuka tayi yaran da taso bata tsakanin iyayensu ne suka yi mata wannan karar. Jiddah na bacci Uncle ya fara mintsinin khairi tana juyuwa yace Khairina tashi ayi sabon baby please. Yadda yayi maganar yasa tayi dariya yana fara kissing dinta Jiddah ta tsala ihu. Duk suka juyo suna lalubenta don har an kashe fitila..... To daga nan zamuyi sallama da iyalan Dr Ahmad Aliyu Saraki. Sai muce Allah Ya bawa kowace mace mijin kwarai Ya zaunar damu lfy da mazanmu Ya bamu zuria dayyiba. Taku Batul Mamman💖 An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://thausanovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.thausanovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 6 of 6