Share this page
2 / 6
ta dubi Khairi tace 'yar uwa wata shawara zan baki game da maganar Uncle don na lura har yau baki da nutsuwa. Kina istikhara kuwa? Ji wata irin tambaya khairi ta fada to ke yanzu idan nace bana yi ai anyi asarar kudin tara. Kausar tayi murmushi ai nasan kina yi amma da wuya idan ba kina yi ne kawai don samin abinda kike so ba ba domin neman zabin Allah ba tunda kin dade da yankewa kanki wanda kike so. Shiru tayi alamar tunani sannan tace gaskiya ne Kausar amma daga yau zan canza niyya. Banda niyya ina ganin shima Uncle ki koyi dena shiga sabgarsa da yawa kamar wayar da kuke yi kullum da yawan fara'a kamar gonar auduga idan kin ganshi. Khairi tace tohh wani sirrin ne kuma da hakan. Eh ta bata amsa sannan ki dan bawa Captain chance kiga ikon Allah. Ta karbi shawarar kausar yanzu ba ta kiran Uncle a waya kamar da idan ya kira ma sai taki dauka. Amma hakan ba karamin punishment ta dauke shi ba. Shi kanshi Uncle Ahmad abin ya fara isarsa. Ko haduwa suka yi ta dena rawar kan da take yi. Tana zaune da Tahir a waje saboda zafi gashi injin gidan yaki kamawa. Yauma ta kasa sakin jiki sosai amma dai tana amsa shi idan yayi magana. Wayarta ya dauka wadda ke kan wani karamin table da ta ajiye masa lemo. Amma dai kasan daukan kayan mutane ba da izini ba babu kyau ko? Eh ya bata amsa tare da cigaba da kokarin kiran wayarsa da tata domin ya sami number dinta. To ai sai ka ajiye min tunda ka sani wannan karon cikin fushi take maganar. Karkari dai ki kirani barawo kuma ba kaina farau ba. Murmushin da yake yi ne ya bata haushi tace me kake nufi? Hmmm Khairi kenan i love your eyes idan kika kalli mutum sai yaji kamar ya gudu dake. Ganin yana neman canja topic din ta tashi zata koma ciki yace barauniya....cak ta tsaya sai kuma ta waigo kafin tayi magana yayi yar dariya barauniyar zuciyata ina zaki ba sallama. Bata iya yin fadan data yi niyya ba sai ta shige gida. Yana tashi shima gidan ya nufa sai dai a hanya wayarsa tayi ta ringing. Yana parking a cikin gidansu ya duba yana da 13 missed calls. Kira yayi don bai gane nunber din ba. Hello yaji an fada ana daga wayar.. ko cikin bacci dole ya gane muryar nan duk da ya shekara biyu bai ji ta ba. Katse wayar yayi tare da dafe kirji. Meye dalilin da yasa Jalilah take kiransa a yanzu? Batul MammanπŸ’– πŸ’• MEYE DALILINKA πŸ’ž 7 Yau kuma me ya faru kika shigo da fushi 'yata? Khairi ta kalli Inno idanunta cike da hawaye tace Inno ko sau daya Uncle bai taba kallo na da wata manufa ba bayan kanwarsa da ya daukeni. Kada ki manta na fada miki ki bin iyaye wajibi ne idan kika bi su zaki ga amfanin yin hakan 'yata. Ki daure ki bawa Tahir din dama kiga abinda Allah Ya tsara miki. Share hawaye tayi da dankwalinta Inno in Allah Ya yarda zanyi kokari na cire Uncle a raina. Zan koyawa zuciyata son zabin Malam. Ni dai ki taya ni addua. Yana shirin kwanciya ya sake jin waya ta shigo ko da ya duba number din da Jalilah ta kira shi da ita ce dazu. Wannan karon ya dauka yayi sallama. Tahir nice Jalilah. Ta fada cikin siririyar muryar jan hankali. Lafiya kike kirana a daren nan? Lafiyar kenan my one and only. Shiru tayi tana jiran amsar shi. Yaushe rabon da yaji muryarta balle ma ta ambace shi da wannan sunan. Disconnecting din call din yayi ya kashe wayar gaba daya. Me Jalilah ke nema tare dashi bayan irin cin fuskar da suka yi masa? ******************** Gidan Baba Aliyu Umma da Khairi suka nufa kafin azahar bayan Hajiya ta kira su bayan asuba ta sanar dasu haihuwar Rahma. Yakumbo ta gani tana yiwa baby wanka tace to yar tsohuwa ki wanke ta da kyau dai kuma kada ki fesa mata goro. Hajiya dake ta fama da Rahma taci abinci tace to yar nema daga shigowarki zaki fara ko. Da kin kyale ni da ita Karimatu in gama da 'yar ta ta in buge bakin. Wa zai buge miki baki khairi taji ana fada daga bakin kofa. Tana juyawa suka hada ido bata bashi amsa ba sai ta gaishe shi ta mike zata fita. Au yau bakya son na tare miki fadan ne? Ya tambayeta sai dai bata bashi amsa ba tace bari naje wurin Baba Hashim mu gaisa. Kallonta kawai yayi gaba daya Khairi ta canja masa ya rasa dalili amma ko kadan abin baya masa dadi. Dariya suke ita da Umaima suna zaune gaban wheel chair din Baba Hashim yana basu labari. Duk basu kula da tsayuwarsa a wurin ba sai da ya danyi knocking kofar yace Baba Hashim wane labari kake basu ne ba'a hada damu ba? Shigo Ahmad ya fada yana murmushi. Labarin kiriniyar ka nake basu. Ai mun sami na tsokana ko Khairi? Umaima ta tambayeta ita kuwa kokarin tashi take tace ina zuwa zanyi waya ne. Idan wasa ne ya soma yin yawa. Uncle Ahmad ya fara gajiya da yadda Khairi take share shi. ko a waya amsar maganarsa bata wuce eh ko a'a wanda ko kadan ba haka suka saba ba. ****************** Toilet ta shiga tayi kuka mai isarta sannan tayi alwala ta diga maganin ciwon ido mai sa ido yayi haske. Ba tun yau take amfani dashi ba indai tayi kukan Uncle sai ta diga. Khairi kenan Rashin kula shi ba karamin damunta yake ba sai dai tasan hakuri ya zame mata dole. Kamar ba ita ba ta fito ta shiga dakin Momi tayi sallah. ****************** Shi kan shi bai sani ba amma bayan mintuna kadan yake dauko waya ya duba ko text dinta ya shigo. Sau uku kenan yana mata text yau na tsokana ta share. Wai ni wayar wa kake jira ne Abban Iman? Tun dazu kake abu daya. Abu daya kamar me fa Mufida. Kallon ka raina min hankali tayi mishi kafin ta bashi amsa kallon wayarka mana. Its nothing to worry about bani ruwa mai sanyi dai. Ita tasan akwai abinda ke damunsa amma idan bazai fada ba zata jira. Batul Mamman πŸ’– πŸ’• MEYE DALILINKA πŸ’ž 8 Sati biyu kenan da khairi ta fara ja da baya da Uncle Ahmad kuma ta daure tana kula Captain sai dai ta rasa sukuni da walwala kamar yadda ta saba. Wannan abu kuwa babu wanda baya damu a gidansu. Babbar matsalarta yanzu bata wuce zafi da kirjinta yake yawan yi sai taji kamar zuciyarta zata cika mata kirji. Babu wanda ta iya sanarwa wannan hali da take ciki iyaka ta dage da yawan addua. Ba irin wayar da Jalilah bata yiwa Tahir amma yaki saurararta daga karshe tayi masa text wanda a ciki take ta sanar dashi aurenta ya mutu tana so su dawo da soyayyarsu. Ji rainin hankali..tamkar ta aikawa dutse haka ya share zancen. Iyaye sun gama magana an yanke shawarar yin bikin khairi bayan babbar sallah lokacin Tahir zai dauki hutunsa na shekara. Yana jindadin yadda khairi take bashi hadin kai suyi hira wadda bata wuce zancen makaranta, kausar da uncle Ahmad. Bai taba kawo komai a ransa ba sai dai ya fahimci kamar tana cikin damuwa wadda bata so a sani. ***************** Ina kuma zaka je daga dawowarka Abban Iman? Wani kallo yayi mata bai amsa ba ya cigaba da saka safa a kafarsa. Abban Iman magana fa nake yi maka 'yan kwanakin nan na kasa gane kanka idan anyi magana kace ba komai. Tashi yayi ya dauki keys dinsa ya fita ya barta tsaye saroro. Shirun nasa shi yafi bata tsoro don a yadda take da Ahmad bata magana biyu baiyi abinda take so ba. Idan ma wata yar isakar ke neman daga mata hankali to wallahi tayi kadan. Dole ta koma wurin Mai Dafai ya bata wani sirrin malakar. Ahmad baya cikin mazan da mace zata sameshi taso rabuwa dashi. A hanya yana ta sake sake a zuciyarsa. Damuwarsa bata wuce ta Khairi da yadda ta canza masa lokaci guda. Khairi ki fada min gaskiya ko baki son aurena ne? Wani murmushi tayi wanda ya kara haska kyawunta wa ya fada maka Captain? Kefa kin saba amsa tambaya da wata tambayar. To ai kaine kamar wani lauya ka cika tambaya baka san ance wala ta jassasu ba. Tana magana tana yar dariya sai dai Tahir ba yaro bane yasan dariya kuma ya san yake. Lemo ta zuba a cup zata mika masa Indo da Uncle Ahmad suka shigo falon. Sakin cup din tayi ba shiri da jin muryarsa yana sallama. Duk su ukun kanta suka yi suna tambayar ko bata ji ciwo ba don ya tarwatse ko ta ina. Allah Captain babu abinda ya same ni ta duka tana matse kasan skirt dinta. Abin ya bawa Ahmad mamaki kamar bata ganshi ba taki amsawa yana magana. Tahir ya lura da abinda tayi sai ya mika masa hannu suka gaisa. Mikewa tayi bari na gyara jikina na dawo. No ba sai kin dawo ba Ummulkhairi zan tafi kinga tara tayi. Wani murmushin tayi to kana tsoron dare ne? Gidan uncle fa yafi naku nisa amma kaga yanzu yazo. Ahmad kaji kanwarka ko wato gidanmu ne banda ita. Ganin yadda suke wasa yasa yaji ransa ya kara baci. Da shi kadai khairi ya kamata tayi wasa irin haka. Kuji karfin hali. Wato ko kunyata ba kwa ji ko. Tahir yana dariya yace tuba muke yi Uncle. Sai da safe Khairi. Yana fita ta kama hanya zata fita daidai lokacin da Indo ta dawo da tsintsiya da tsumma zata gyara wurin da khairi tayi bari. Ke ina zaki ya tambaya fuskarsa babu fara'a. Da yasan yadda ta kidime da ganinsa da bai tsayar da ita ba. Batul Mamman πŸ’– πŸ’• MEYE DALIINKA πŸ’ž 9 Yanayin da taga fuskarsa ya bata tsoro don da gani ransa a bace yake. Indo ya jira ta gama sharar da take bayan ta fita a hankali ya rinka tafiya ita kuwa yana matsowa tana kara tsorata. Sai da yazo daf da ita sannan ya tsaya yace Khairi wai menene matsalarki ne these days i dont understand you. Bakinta na rawa ba...ba kkkomai Uncle. Sami wuri ki zauna, ba musu ta koma ta zauna. Kada ki bata lokacinki wurin yi min karya irin yadda kike min kwanakin nan nasan akwai wani abu. Kanta a kasa don ba zata jure kallon da yake mata ba. Babu komai da gaske kawai yanzu ina dan jin kunyarka ne. Kin manta nine ma sirikinki Alh Mahe, malama ki saurare ni da kyau Allah idan na sake kiranki kika ki dauka ranki sai ya baci...kuma the next time kika yi pretending baki ganni ba..hmmm kada ki sake kawai. Yana gama magana ya fice ba ko sallama. Da gudu ta tafi dakinta tana shiga tayi jifa da hijab da dankwalinta ta kwanta tana kuka. Yanzu haka Uncle Ahmad zai rinka yin abinda zai kara daukan hankalinta amma yana nuna halin ko in kula a kanta. Wani irin tari ne ya sarke ta tana cikin kukan tasa dankwalinta ta rufe baki sai dai tana cirewa ba karamin razana tayi ba domin kuwa jini ta gani a jikin dankwalin. ******************* Mufida zaune a gaban Mal Mai Dafa'i ta fada masa duk matsalolinta da mijinta yace kada ki damu ga wannan kwalli da hodar da zarar kin yi amfani dasu kun hada ido to an gama magana. Tana ta washe baki ta mika hannu zata karba ya noke tare da mika mata daya hannun nasa. Haba ranki ya dade ai sai naji kafin alkalami a tukunna. Da sauri ta bashi kudin ta mike , a ranta kuwa tayi kwafa tace dani kake zancen Ahmad. Yaya Kausar wai ki zo inji wani Tahir. Tahir kuma ta maimaita cike da mamaki. Ni yace ka kirawo Hassan? Eh ya gyada kai. To kace ina zuwa kuma ka gaishe da mamanku. Neman izini tayi a wurin mahaifiyarta sannan tace ya shigo. A farfajiyar gidan ta ajiye musu kujeru yazo ya zauna. Nasan zaki yi mamakin ganina duk da bamu taba haduwa ba ko. Haka ne ta amsa da 'yar fara'arta. Yanayinsa ya nuna alamun damuwa yace Kausar nine Tahir din da zai auri kawarki Allah baiyi mun hadu ba sai yau. Nan da nan ta mike Allah sarki ai ban gane ba...ina fata lafiya dai ko? Lafiya kalau in sha Allah. Ya nuna mata kujera dawo ki zauna magana nazo muyi akan Khairi. Jin haka ta dan sha jinin jikinta, ita kanta ta san khairi ta canja yan kwanakin da suka gabata. Canjin da Uncle Ahmad yace yana son gani daga gareta ya gagara domin kuwa Khairi yanzu yawncin kullum bata jindadi daga zazzabi sai ciwon kai. Malam ya shiga damuwa kwarai itama Umman khairi abin ya isheta domin gidan ya zama shiru ba hayaniyarta. Suna zaune a falo zasu yi karatun asuba da Malam ya turo glasses dinsa gaba sai dai sabanin yadda ta saba yau Khairi kwantar da kanta tayi a jikin kujera bata da niyyar tashi. Malam da Umma sai kallon kallo. Batul Mamman πŸ’– πŸ’• MEYE DALILINKA πŸ’ž 10 Kasa karatun tayi ta tashi ta koma daki. Ba komai take gudu ba face tarin da ya taho mata kada su ga jini su tsorata. Ita kadai tasan yadda take ji a jikinta. Su Malam da ta baro a falo kuwa hankalinsu ya tashi. Gari na karasa wayewa Malam ya kira yayansa ya sanar dashi halin da ake ciki. Uncle Ahmad yana ta sauri ya shirya saboda yana son fara biyawa ta sabon asbitin hadin gwiwa da suke shirin budewa shi da abokinsa wayarsa tayi kara. Momi ce ta sanar dashi Baba yana nemansa idan har bashi da patient da safe yazo yanzu. Yana ajiye wayar ya fita da sauri ko breakfast baiyi ba. Mufida tasha takaici domin maganin dubu ashirin zuba masa a abincin. ******************** Mamakin ganin Malam yayi a gidan da safe haka sai Baba Hashim da Yakumbo. Malam ya zayyana musu halin da Khairi ke ciki hankalin Uncle ba karamin tashi yayi ba. Kowa a wurin yana fadin irin canjin da ya gani a tare da ita. Baba ya dubi Ahmad yace to kaine babba wanda idan babu mu dole kasa ido kan kannenka kuma gaka likita dole kayi wani abu a kai. Kansa a kasa yace in Allah Ya yarda zanyi iya kokarina. Kuma tunda kun shaku sosai kayi kokarin sanin ko wata matsala gareta inji Yakumbo. 'Ya'yan Alh Mahe ne suka zo duba Khairi domin Tahir ya sanar dasu bata jindadi. Wata kanwarsa tace antinmu anya ba ciwon tafiyar yaya kike yi ba. Duk suka yi dariya cikin karfin hali tace ai duk inda yake tare muke banda abinki. Haka suka tafi suna ta yabonta. Daga wurin aiki gidan Malam uncle Ahmad ya wuce. Ya gaisa da Umma da take kitchen tace masa Khairi tana falo. Kamshinsa mai dadi ne ya fara dokan hancinta ta yunkura ta tashi zaune Uncle dina sannu da zuwa. Yauwa kanwata ya amsa mata a sanyaye. Khairi kin rame ji idanunki a loko. To kada dai kace min mujiya don ita ce mai ido a loko. Yana dariya yace ai fa ke din nan da bakinki. Ko ciwon karya kike yi ne duk kin wani tayar mana da hankali. Tsayuwar da yayi a gabanta yasa duk jikinta yayi sanyi shi kuwa wani irin kallo yake yi mata. Yadda yake ji game da kanwar tasa yau daban ne,yana tausayinta sanan yana tsoron rabuwa da ita. Rashin kula shi da take yi yasa ya kara sanin cewa Khairi is an important part of his life. Uncle ka zauna mana ta fada kanta a sunkuye.kujerar da ke kallonta ya zauna. Khairi kafin ayi zancen asibiti don Allah ki fada min abinda ke damunki. Hawaye taji yana taruwa a idanunta sai ta kasa bashi amsa. Kinsan yadda muka damu da ke gaba daya amma cikin kankanin lokaci kin canja ga rama kamar ana tsotse ki. Murmushin da tayi sai da yasa zuciyar Ahmad bugawa da karfi...God Khairi is so beautiful. A zahiri kuwa cewa yayi ko aure ne baki so ko Tahir din? Babu ko daya Uncle malaria ce ta sani a gaba. Duk kin zama makaryaciya ya fada yana kallon ta ido cikin ido tana kokarin kawar da kanta yace Khairi...wani iri taji har tafin kafarta. Ki kalle ni da kyau ki rantse baki da matsala... Kafin ta bashi amsa tari ya sarke ta ga hawayen da take kokarin mayarwa. Uncle Ahmad tashi yayi da sauri ya dauko mata tissue yana cewa wanke ni zaki yi da virus din mura ko? Yana mika mata tissue din tayi wani tari mai karfi sai jini ya watso masa a gaban riga. Ita kuwa Khairi faduwa kasa tayi a sume. Innalillahi wa inna ilaihi rajiun shine abinda ya fada da karfi har Umma, Inno da Indo suka shigo falon da sauri. Batul MammanπŸ’– πŸ’• MEYE DALILINKA πŸ’ž 11 Ganin halin da Khairi ke ciki Umma ta soma kuka ina zan sa kaina ni Munnira ta koma ga Uncle Ahmad don Allah kayi wani abu ita kadai gareni. Yadda suke ta kuka yasa shima ya dada rudewa. Daukarta yayi ya fita Indo tayi saurin bude masa mota yasa ta a ciki. Umma ta shiga gaba kan Khairi a cinyar inno suka nufi asibiti. Tun kafin su isa ya kira wani abokinsa ya kwatanta masa halin da take ciki domin a tanadi kayan da ake bukata kafin su iso. Umma a gefe daya ta kira Malam sai da taji shiru bai dauka ba ta tuna yau alhamis yana yin karatu a masallacin Mus'ab ibn Umair a nan unguwarsu. Driver dinsa ta kira Lado ta sanar dashi idan Malam ya fito ya fada masa. Ko da isarsu asibitin sake daukarta yayi abokan aikinsa suka yi masa jagora zuwa dakin da zai kaita. Yana dora ta akan gado sai ta fara aman jini idan tayi yunkurin aman sai kirjinta ya amsa. Haka Uncle ya rirrike ta tana amai tana hawaye duk kayansa sun baci sai dai ba ta su yake. Yana daga zaune bakin gadon ya rike ta yana bada command kamar wani soja. Daya ga kamar ta fara fita hayyacinta sai ya fara marin fuskarta da sauri Khairi stay with me, wani gumi ke karyo masa hasbunallahu wa ni'imal wakil open your eyes please. Karshen maganar dai da kuka ya kare ta. Dr Maina ne yaja hannunsa da kyar ya fitar dashi daga dakin. Tamkar karamin yaro haka ya zauna a kofar dakin yana kuka. Umma na ganin haka ta fadi a sume. Ana kokarin dauke ta Malam da iyalan gidan Baba Aliyu suka shigo. ******************** Innalillahi wa inna ilaihi raji'un shine kawai ake fada. Inno ce ta iya yi musu bayanin abinda ya faru domin Uncle Ahmad kai kawai ya rike yana zubar da hawaye saboda baya tunanin Khairi zata tashi. Bayan an sami kanta Umma ma ta farfado Malam da Baba suka tafi office din Dr Maina. A can suka tarar da Ahmad fuskarsa duk ta nuna alamun damuwa. Baba ya sake kallon likitan cikin fushi wai nufinka karamar yarinya kamar Ummulkhairi ita ce da hawan jini da ciwon zuciya? Dr Maina ya dubi Uncle yace Dr Saraki ai na nuna maka dukkan binciken da mukayi. Malam yace to ni ba wannan ba ku fada min meye abin yi. Ina ganin ina maganin da aka bata ya sake ta sai mu tambayeta menene problem dinta. Me ta sa a ranta har ta kamu da wannan ciwon cewar Baba. Uncle Ahmad yace zan tambayeta Malam. Ku daure ku tafi gida a kawo abubuwan da zata bukata da mai kwana daya. Nima ba tafiya zanyi ba. Batul Mamman πŸ’– πŸ’• MEYE DALILINKA πŸ’ž 12 sai da ta kwana uku ta dan fara dawowa hayyacinta. Duk yadda ake ta rarrashinta ta fadi matsalarta abu yaci tura domin kuwa cewa take babu komai. Ai da kunya tace tana son wani da namiji da bakinta. Musamman Uncle wanda bata taba ganin alamun zai mata son aure ba. Kausar suna ta fada da mai adaidaitan da ya kawo ta asibiti saboda bata da chanji sai ta hango shi yana fitowa daga mota. Kaf idanunsu suka hadu sai kallon kallo. Ko me ta tuna tayi saurin dauki ido tare da cewa a'uzubillah. Tun kafin karaso kamshinsa yayi masa iso yana zuwa dubu daya ya mikawa mai dan sahun yace mata muje ko. Ko sauraron godiyar mai dan sahun baiyi ba. Itama dai godiyar tayi masa tare da gaishe shi. Kafin su shiga wayarsa tayi ringing ya dauka yana magana da kyar. A ranta kausar tace idan namiji yasan ya hadu wulakancinsa karuwa yake. Jalilah na fada miki ki dena kirana kuma idan kika sake zuwa gidanmu zan sa kannena suyi miki duka. Kausar dai dariya ma take yi. Yana gamawa ya harareta ku mata kun iya rainin wayo. Khairi yaya jikin naki? Dan murmushi tayi sai idanu da suka fada ga rama. Kausar tace ai baka ganta ba lokacin da bata gane waye a kanta. To dadin abin dai banyi surutai irin naki ba...ina jinki kina cewa khairi kada ki mutu ki barni wayyo yar uwata. Lallai kin warke amma ba don kina gadon asibiti ba dundu zan miki. Ai dama ki saba min mugunta. Shi dai Tahir abin dariya ya bashi to ko zaku kara ne nayi refree. Uncle Ahmad ne shigo dakin da sallamarsa. Yayi mata kyau sosai har taji zafi a zuciyarta sai tayi shiru ta dena magana shi kuwa ido ya zuba mata kamar ya manta da mutane a dakin. Tahir da Kausar suka hada ido irin kallon you see what I told you din nan. Sun dan taba hira wadda Khairi tayi shiru. Tahir yace doctor ina son ganinka idan ka gama. Khairi wadda tun dazu bata kula kowa ba tace gulma zaku fara? Sai a lokacin Uncle yayi murmushi fuskarsa ta kara yin kyau. Khairina ta fara dawowa kenan. Ya maida dubansa ga Tahir muje ko Captain. ******************** Kafin Dr Ahmad ya rufe kofar office din Kausar ta shigo ya kalleta da mamaki a fuskarsa Tahir yace ai maganar da ita zaayi. Bayan duk sun zauna Ahmad yace kun barni a suspense fa don Allah me ya faru. Tahir ne ya soma magana tare da fada masa irin yanayin dayake ganin khairi tun farkon zuwansa ya lura tana da damuwa. Dalilin haka yasa ya nemi kausar wadda da kyar ya shawo kanta ta fada masa matsalar khairin. A takaice dai doctor Khairi is in love with someone else. What??? Kausar da gaske kike yi. Eh Uncle ta bashi amsa. Wannan abu tun muna yara ya fara har yanzu kuma mutumin bai ma sani ba. Ko kadan zancen bai masa dadi ba. Yanzu khairi wani take so....to waye ma wannan mutumin karshe dai wani kishi mai tsanani yaji ya turnuke shi ya kasa magana. Tahir wanda yake lura da abinda yake yi yayi murmushi ashe dai Khairi ba son maso wani takeyi ba. Yace kada ka damu dan uwa ai sanin irin matsalar tata zai kawo saukin lamarin. Sai ka dage wurin jin ko waye take so din. Kausar kallon shi tayi da mamaki don a yadda sukayi shawara zasu fada masa ko waye. Ni dai zan sami Alhajinmu nayi masa bayani na janye daga maganar auren. A waje yace kausar kinga na canja plan ko? Na kula kamar yana sonta ne shima gara mu bari suyi resolving din issue din da kansu. Mungode sosai Captain domin badon kayi hakan ba bazamu taba iya fada ba. Ba komai Kausar sai dai tunda kin hanani kawarki sai ki nemo min wata matar. Ahmad ya rike kansa wanda ke masa matsanancin ciwo. Waye yasa khairi wannan ciwon, ina ma dai ace.....Khairi bazan iya jure rashinki ba ya fada a sarari Batul MammanπŸ’– πŸ’• MEYE DALILINKA πŸ’ž 13 Bayani Ahmad yayi musu game da abinda Tahir ya fada musu. Malam yayi matukar mamaki domin ko da wasa bai taba ganin alama ba, uwa uba kuma shi a yadda ya santa ko saurar samari bata yi. Baba dai cewa yayi a bita a hankali kuma su fara tambayarta kafin a yanke hukunci. Babban yaya aka barwa aikin tambayar kanwar tasa sai dai abin yaci tura domin kuwa kuka take saka masa idan ya tambayeta. Shi dai yana son ta sami lafiya amma tsakani da Allah yana

Chapter 2 of 6