Share this page
3 / 6
tararrabin wa zata ce. Wasa wasa sai da tayi sati a asibitin. Duk iyaye da lallami da rarrashi anyi anyi taki magana sai kuka. Ga ciwo yana neman dawowa sabo. Inno abin duk ya ishe ta kullum ita da kausar suna aikin bata shawara tace ita bata yafe ba ma duk wanda ya fada a cikinsu. Tahir dama bai taba nuna mata ya sani ba. Sai da ta tabbatar babu kowa a bakin motar sai shi kadai yana jiran dreban sa ya idar da sallah Inno taje bakin motar ta durkusa har kasa. Baba Aliyu yace haba haba don Allah tashi yana magana yana waige waige. Ya zaki durkusa min haka bayan ko ba'a fada ba nasan kin girmeni ko so kike babban Malam ya fara min waazi? ya kare zancen da murmushi. Inno ta mike ta sunkuyar da kai kasa. Ranka ya dade akan maganar ummalhairu ne. Ina jinki Inno ya fada hankalinsa na gareta. Alhaji tun yarinyar nan bata san kanta ba take son shi har girmanta. Saboda shi wallahi bata fita fira da wasu mazan gashi bai ma san tana yi ba tana fadin haka sai kuka. Baba yace bangane ba waye shi din. Ta face hanci yallabai Amadu nake nufi na wurinka. Wani irin farinciki ne ya saukar masa a zuciya har fuskarsa ta nuna. Ahmad kika ce fa? Kin tabbata? Alhaji wallahi bazan maka karya ba. Bandir din 'yan dari biyu ya dauko daga aljihunsa ya bata. Murmushi tayi irin nasu na tsofaffi Alhaji bani da burin da ya wuce naga auren Ummalhairu da Amadu shine kawai abinda zaka bani tukwici. Bai taba zata haka abin zai kasance ba. Sai dai yayi murna mara misaltuwa. Alhaji Aliyu yana son kannensa sosai. A dalilin su ya hakura da jami'a a shekararsa ta biyu don kudin da yake samu bazai isa ya ciyar da gidansu kuma duka suje makaranta ba. Dr Abdallah 'ya daya gareshi idan dansa ya aura yasan ya gama hada kan 'ya'yansu tunda Hashim lalura tasa ko auren baiyi ba. Karshe sai ya yanke shawarar bazai fadawa kowa ba sai ya sami hanyar bullowa lamarin. ****************** Ahmad zaune a dakin mahaifinsa ya sunkuyar da kai kasa ga mahaifiyarsa a gefe. Kalon agogo yake yi domin kuwa yabar khairi jikin babu dadi sauri yake ya koma. Baba yayi gyaran murya yace Ahmad idan na baka umarni za ka bi? Baba bana fatan Allah Ya nuna min ranar da zan ketare maganarka. Alhamdulillah yace sannan ya dubi Haj Karima duk abinda muka zanta da Inno ke kadai na fadawa saboda na aminta da cewa kema bazaki bijire min ba, Ahmad ko kasan cewa kanwarka ciwon nan da take yi dalilinka ne. Da sauri ya dago kansa...ni kuma Baba ya fada cikin rudewa. Eh Ahmad kai. Dazu Inno tayi min gamsashen bayani ashe ka taba cewa kaine mijinta tun tana karama. To tasa abin a ranta ta kuma girma da sonka. Ikon Allah haka kawai yake fada a ransa. Ko shiyasa ya zama restless akan lamarinta? Lallai kuwa idan haka ne zai share mata hawaye domin ko ba komai a cikin kannensa daban khairi take. Baba ya katse masa tunani da cewa ina son kayi min alkawarin zaka aure ta kuma bazaka taba wulakanta min 'ya ba. Kafin ya bada amsa Hajiya tace Alhaji ina ganin abinda yafi shine kace kai ka hada auren kawai kasan mu mata da gutsiri tsoma ko da wasa wata zata iya fada mata magana nan gaba. Ahmad ya kalli mahaifiyarsa Hajiya akwai tunani. Baba ma yaji dadin shawararta..yace kaga jiya Abdullahi ya tafi madina taron malamai na sati uku daga nan zaiyi umra kafin ya dawo. nasan shima ciwon yarinyar nan ya tsorata shi fada ne kawai baya yi. Idan ya dawo zamu yanke lokacin aurenku da su Kawu Hadi. ****************** Kausar da Inno sun sami Umma a barandar asibitin sunyi mata bayanin komai. Suna haka Baba ya kira yayi mata zancen tare da sanar da ita cewa kada ta fadawa Malam wannan aikinsa ne idan ya dawo. Ya sanar da ita ne domin yana son a samin kan Khairi kafin ya dawo. ita Hajiya tace bama zata nuna tasan komai ba kada Umman taji babu dadi shiyasa ita bata kira ba.Kaji manya masu tunani. Batul Mamman💖 💕 MEYE DALILINKA 💞 14 Uncle Ahmad gida ya wuce ya tarar yaransa sunyi bacci a falo ya dauke su ya kai daki. Mufida wai meyasa kike son barin yaran nan a falo su kadai? Gashi har sunyi bacci. A fusace ta juyu zata bashi sai taji tsoron kada ranshi ya baci yaki kwana da ita ta sake asarar maganin mallakar da Mai Dafa'i ya bata ta shafa a kirji da mara. Abban Iman nasan kanwarka tana kwance a asibiti amma hakan ba yana nufin ka dena dawowa da wuri ba ko ka dena cin abinci. Rungumota yayi amma hankalinsa yana wurin khairi. fuskarta ya shafa yi hakuri Mufida kinsan dole hankalina ya tashi ita kadai Malam ya mallaka kuma idan zaki tuna ko kafin aurenmu mun shaku sosai. Itama sakin fuska tayi tana kokarin su hada ido yayi arba da kwallin data sa. Sai dai hakan bata samu ba domin sakinta yayi tare da bata hakuri. Mufida wanka zanyi na koma asibiti jikin khairi babu dadi na barta dazu. Kai wannan yarinya ko jaraba tana asibitin ma ta hana ruwa gudu.. gara a aurar da ita kowa ya huta. Bakin wando da maroon din shirt ya saka sunyi masa kyau sosai. Sai turare yana fesawa yana dan humming din wata waka. Mufida ta harare shi ni wannan abin da kake yi sai na zata zance zaka ba wurin patient ba. Dariya yayi don baya so suyi fada kada ta bata masa lokaci. Daren yau na Khairina ne ya fada a ransa. Yana tuki cike da farinciki kamar wani sabon shigar soyayya. Shima abin mamaki yake bashi. Fada suke da Inno akan cin abinci Uncle Ahmad yayi sallama sai da suka masa izini ya shiga. Tare da wata nurse suka shigo dakin ta gaishe shi kanta yana kallon plate din abincin. Inno allura zan mata har biyu ina fata taci abinci. Yana maganar ne cikin zolaya inno tace bata ci ba ai rigimar da muke yi kenan kafin ka shigo. Nurse din ya sallama dama yana sane wurin yin rounds dinsa yabar dakinta ya zama na karshe. Kujerar gaban gadon ya jawo kusa da kafafunta ya zauna sannan ya kalli inno nifa zance nazo Inno gaskiya ki bamu wuri. Eyye dan nan lallai yaran zamani ba kunya. Ita kanta khairi ji tayi kamar gadon ya tsage ta shige. Lafiyar Uncle kuwa? Inno na fita ya dauke plate din daga cinyart. Bude bakin in baki a baki kinji khairina. Kallonsa take galala ikon Allah. Dan zare mata ido yayi da gaske nake fa. Ni zan iya ci da kaina....shima kwaikwayon muryarta yayi ya maimaita abin da ta ce har tayi dariya gaskiya Uncle da kai mace ne saboda muryarka zaka rasa miji. Wai!!! Garmaho kenan. Ganin yadda har ta sake tana dariya ya sanyaya zuciyar Ahmad. Khairi will never sieze to amaze him. Matso da fuskarsa yayi kusa da tata. Tell me something khairina.. ina jinka ta bashi amsa sai dai cikinta har kadawa yake don tsoro. Gaba daya nauyinsa yake ji bare ya matso kusa da ita gani take ya kara girma. Katse mata tunani yayi bakya son muryar tawa ne? Ina so mana, tana fada taji kunya sai tayi saurin rufe fuskarta. Shi kanshi dadi yaji a ransa bude fuskar ki ci abinci akwai allura da zan miki. A ina ta tambaya a tsorace. Yau ba tsoron allurar bane kadai harda tsoron wanda zaiyi domin kullum nurse ke yi mata. Indai kin cinye duka zan kira Sister Shukriya tayi miki. Ai kuwa tana da kirki Uncle zan cinye. Tana ci suna hira abin gwanin shaawa shine nima har nayi addua Allah Ya kara mana so, kauna, tausayi, mutuntawa, da girmamawa tare da dunbin romanciyya tsakanin mu da mazan mu. Amin ta cinye abincin tas sannan Uncle Ahmad yace to Khairina sai da safe na korar miki inno ko. Ai nasan zan sha mita. Sai da safe kanwata ya fada yana bude kofa...sai da safe Uncle dina. Yaushe rabon da ta kira shi da wannan sunan? Yana fita Inno ta shigo da nurse yau khairi ko ihun allura bata yi ba. Bayan ta fita ne Khairi cike da nishadi tace Inno yau Uncle Ahmad ya canja min sosai. Ai naga kina ta faraa kamar kin tsinci hakori amma tuntuni baki kula bane haka yake miki tunda kika fara ciwon nan har kuka fa yayi. Da gaske? Zan miki wasa ne 'yata. Ki cigaba da addua kila bukatar ki ce zata biya. Dama ta samu an cire mata drip saboda haka alwala ta dauro ta yi nafila tare da kara addua indai akwai alkhairi Ya Allah Kasa Uncle Ahmad ya zama mijina. Batul Mamman💖 💕 MEYE DALILINKA 💞 15 Tun daga lokacin da Uncle Ahmad ya fara nuna kulawarsa ga Khairi. Kulawa irin ta soyayya sauki ya fara samuwa sosai dama ciwon nasa ne. Umman khairi dai farincikinta baya misaltuwa domin tilon yarta ta sami lafiya. Alh Aliyu duk da ya hana a sanar da Malam halin da ake ciki amma har gida yaje ya sami Alh Mahe akan maganar Tahir. Hakika duk mutum mai halin kirki ya kan dace da abokin kwarai. Alh Mahe yace kada ka damu Alhaji kafin yayi magana da Ahmad din ma sai da ya sanar dani halin da ake ciki. Idan Malam ya dawo shima nasan zai fahimta. Allah Ya yi mana jagora. Tun safe suke baki kasancewar yau asabar babu aiki masu zuwa dubiya sun karu. Ganin har wurin takwas na dare da baki Uncle Ahmad yazo da kanshi ya sallami kowa domin a cewarsa Khairi na bukatar hutu sosai. Umma da Indo ne karshen tafiya yaje rakasu mota. Yana dawowa ya tarar khairi tayi bacci. Abin ya daure masa kai. Inno ba yanzu na fita tana hira ba ya kika bari tayi bacci bata sha magani ba. Kasan dai bata son maganin nan na dare kullum ta sha sai tayi kakarin amai, wai wari yake yi. Murmushi yayi don yasan sarai idonta biyu. To tunda bata so ai akwai allurarsa sai nayi mata. Yana fita ta mike ta gyara kwanciya harda rufa har kanta duk da zafin da akeyi saboda hadarin da ke haduwa. Inno dai dariya take yi. Ko da ya dawo ta fara gumi a karkashin bargo yace kinga ban sami karamin syringe ba sai wannan babban shi kuma allurarsa akwai girma. Kallonta yake yi yana magana don sai mutsu mutsu take daga cikin bargon....hmmm yarinya zafi zai koro ki ya fada a ransa. Inno sai kin dan danne min ita fa don allurar nan idan aka yiwa mutum yana dadewa bai motsa ba. Jin hannun Inno yasa ta bude kanta ba shiri shi kuwa ya dage sai yayi. Kuka ta sa masa da rokon yayi hakuri zata sha. Komai na khairi shaawa yake bashi. Har yanzu dai zancen soyayya bai hada su ba amma kana ganinsu tare zaka gane akwai wata a kasa. Malam yayi matukar farinciki yadda yake jin muryar khairi a waya. Umma ta fada masa an kusa sallamarta ma. ****************** Dakinta yasha gyara don yau Umma da kanta ta gyara shi ta fitar da kayan wanki sannan ta gyara mata wardrobe. Gida yana ta kamshi kamar wata amarya zata tare. Gidan Baba aka fara kaita ta gaishe da yakumbo da baba Hashim wanda ya damu kwarai da ciwonta sai dai sau biyu aka kaishi dubuta. Daga nan kuwa gida suka wuce Umma baki har kunne. Ashe dai tana ji da khairin ta ta. Wanka tayi tasa wata dogowar rigar atampa tayi kwalliya kausar tace khairi irin wannan ado kamar ba daga gadon asibiti kika taso ba. Dariya sukayi harda tafawa sai wayar khairi tayi ringing tana dauka ya fara fada. Ina kika shiga ina ta waya baki dauka ba? Duk kin daga min hankali. Yi hakuri Uncle dina ta bashi amsa a sanyaye. Na shiga wanka ne kuma dana fito ban duba wayar ba. Jin yanayin maganarta yasa baiji dadi ba ko ya bata mata rai. Khairina ba fada nake miki ba kinji ko. Naji tsoro ne ko wani abu ya same ki. Murmushi tayi har yaji sautinsa wanda hakan yayi masa dadi. I am already missing you here. Na saba ganinki kullum kwanakin nan. Shiru tayi tana sauraronsa. Khairin Ahmad kina ji na? Wayyo dadi har wani juyi tayi a kan gado. Kausar tana gefe tana kallon ikon Allah. Ina jinka Uncle dina ta bashi amsa. Ki shirya yau zanzo zance na gaske after magrib. Zance kuma Uncle? Eh ko zaki hanani ganin mata ta ne? Wace matar ta tambayeshi cike da murna. Ummulkhair Abdallah Saraki Batul Mamman💖 💕 MEYE DALILINKA💞 16 Tana ajiye wayar ta rungumo kausar nagode da adduarki yar uwa. Allah Ya saka da alkhairi. Ture ta tayi tace duk nasan saboda uncle Ahmad ne kike wani tarairaya ta. Dariya tayi kafin ta zauna bakin gado. Ki fada min gaskiya tsakani da Allah baki da hannu a lamarin nan? Ni Allah Ya isan ma da nayi idan kika fada na yafe fa. Yadda take magana yasa kausar yin murmushi sannan ta fada mata duk yadda sukayi da Tahir da Uncle din nata. Karshe tace mata Allah Khairi shima yana sonki don baki ga fuskarsa ba lokacin da Captain yace masa kina da wanda kike so. Da kina ganiyar ciwonki kuwa ai yadda ya rinka yi ko Umma albarka. Ke dai mu dage da addua a kodayaushe. Khairi dai bata tsaya jin karshen maganar kausar ba ta daga gira daya wato Captain ta wani ja sunan yadda kausar tayi. Lah wallahi kada ki fassara ni. Me kika ji nace har kin tsargu kamar mara gaskiya. Khairi ki kiyaye ni fa. Ganin kausar ta yo kanta yasa ta mike itama zata gudu idan naki fa... Umma tana daga falo tana jin hayaniyarsu. Zuciyarta fes ta Inno Allah Ya biyaki. Ji yau kadai da khairi ta dawo gidan nan har ta cika min kunne. Ai Hajiya idan da rabo sai kiga ta cika miki gida da yara nan gaba. ****************** Uncle Ahmad ya cika alkawari domin kuwa a masallacin kusa da gidansu khairi yayi sallar Isha sannan ya kira ta a waya. Ya sanar da ita zuwansa. A falo ta makale saboda Umma tana kallon news. Yana ta kira tana rejecting calls din. Umma kuwa tana lura da ita idan bazaki tashi ba nima bazan baki wuri ki sami damar fita ba zan ga karshen gulma. Gajiya yayi ya shigo falon bayan an amsa masa sallama. Gaban Umma yaje ya zauna. Anti Munnira barka da yamma. Mun wuni lafiya Ahmad? Ya zirga zirgar ku, Allah Ya kara zumunci Ya saka da alkhairi. Amin ya bata amsa. Khairi ko kallonsa taki yi duk yadda yaso su hada ido. Umma har ta fara jin kunya ganin haka ta tashi ta tafi daki. To ai sai ki tashi tunda nayi miki hanya ko a nan zamu yi hirar? Kunya ce ta kamata. Yanzu sai ta bishi falon baki...anya zata iya kuwa. Ganin bata da niyyar tashi yasa ya miki 5mins na baki idan baki zo ba zan tafi. A hankali ta shiga falon kamar wadda zaa kama. Yana daga zaune yana dariya ashe dai kina son mijinki. Mayafin jikinta tasa ta rufe fuska a haka taje ta zauna. Kin dena magana ne khairi na. A'a ta bashi amsa cike da kunya. bazan hanaki jin kunya ba yanzu khairi amma very soon zanyi maganinta. Janye mayafin tayi ayi maganinta fa kace Uncle? Babu inda za ta. Hmm..... akwai ranar da zan kashe bakin nan. Mu kashe na juna dai ...tana fada kuma sai ta tuna da wa take magana ba shiri ta mike Uncle sai da safe.. Shima tashin yayi ina zaki kike wani sauri? Sai kin fada min yadda zamu kashe bakin juna. Da gudu ta fice zuciyarta tana bugawa da sauri. Shima Ahmad ta barshi cikin wani irin yanayi mara misaltuwa. Gidan su Khairi yau an tashi da gyara da girke girke Malam yana hanya. Kwananta uku da dawowa daga asibiti. Cike da doki ya shigo gidan Khairi ta kankame shi tana ta murna. Yayi mata addua tare da bata guzurin zamzam da yayi mata. Da murna ta shiga daki ta kira Uncle tana sanar dashi dawowar Malam. Ita kuwa Umma tsabar murna bayan ya gama cin abinci tace Malam albishirinka. Goro fari Munnira yana magana cike da nishadi. Ba dole ba khairinsu ta warke. Tace to bani tukwici don nasan sai ka fi Alhaji murnar abinda zan sanar da kai. Allah Yayi miki albarka uwargidana. Amin ta amsa sannan ta bashi labarin khairi da Uncle Ahmad. Tunda ta fara gabansa ke faduwa ai kuwa abinda yake tsoron ji ta fada. Ummulkhair da Ahmad. Tana gama bayani ya mike a sanyaye Munnira...naam Malam ta amsa masa cikin jindadi. Mikewa yayi idanunsa fal da hawaye yace kiyi hakuri amma ko na mutu kiyi min alkawarin Ahmad ba zai taba auren Ummulkhair ba. Batul Mamman💖 💕 MEYE DALILINKA 💞 17 A tsorace ta miki har wayar da ke kan cinyarta ta fadi ta tarwatse. Malam meye dalilinka na fadar wannan maganar. Bai iya bata amsa ba don bashi da bakin magana. Dakinsa ya shiga ya rufo kofar. Haj Munnira ta shiga tashin hankali saboda sabanin reaction din da tayi tsammani ta gani a tare da shi. Ko dai Ahmad yana da wani mugun hali ne da basu sani ba? Shi kuwa Dr Abdallah ko da ya shiga daki alwala ya dauro yazo ya fara nafila wadda bai san adadinta ba. Yana yi yana kuka tare da tsananta addua ga Allah SWT kada ya nuna masa wannan bakar rana da Ahmad zai auri Khairi. Ita kuwa khairi da bata san abinda ke faruwa ba baccinta tayi mai dadi domin kuwa sun dade sun hira da uncle Ahmad a waya. A nasa bangaren bayan yaje gida ya tarar Mufida tana wanka. Cire kayansa yayi daga shi sai singlet da gajeren wando ya zauna a kan gadon yana jira ta fito shima yayi. Tunawa yayi wani abokinsa ya bashi gift din pack din necktie bai sami damar dubawa ba sai ya tashi ya bude wardrobe dinsa yana nema bai san inda Mufida ta ajiye ba. Garin dube dubensa yaga wata bakar leda a bangaren kayanta. yana budewa wata takarda ta fado sai ga wasu kananan kwalabe da kulle kulle a leda. Tattatawa yayi zai mayar mata don ya zata irin kayan matan nan ne da take sha ya dai yi mata fadan ta tabbatar ta san me take sha saboda lafiyarta ma. Haka nan ya bude takaddar ya fara karantawa domin rubutunta ne a jiki yana yar dariya... 1. Farin kulli hodar fuska idan miji ya gani komai kika tambaya zaki samu 2. Kwalba mai jan ruwa na shafawa a goshi, mara da kirji miji yaji tsoronki 3. Kwallin mallaka a saka lokacin kwanciya bacci Dama ga zafin gari amma wani gumi ta fara yi. Ita kuwa mufida me na rage ta dashi take neman fadawa shirka. Ko da ta fito bai nuna ya gani ba yaje yayi wanka ko mai bai shafa ba yaji ta rungume shi harda riko fuskarsa da hannayenta don su hada ido. Shi kuwa sai nokewa yake yana karanta Ayatul kursiyy. Ranar dai bai yadda anyi abinda take so ba don yana tsoron wanda ake shafawa mara kada ya hadu dashi ya fara tsoronta. Baccin karya yayi kafin na gasken ya zo tare da yanke shawarar fadawa Malam don ya bashi shawarar abinda ya kamata yayi. ****************** Malam bai sami kansa ba sai bayan isha ya tafi gidan yayansa. Alhaji Aliyu yace ai nasan kana samun labari zaka zo. Baba Hashim da yake gefe yace ai yaran nan sun gama mana komai. Allah Ya tabbatar da alkhairi. Amin, amin Baba ya amsa. Malam ya tattaro courage dinsa yace amma Yaya ka manta da maganar yaron wurin Alh Mahe? Yar dariya yayi nasan zaka ce ana neman aure cikin neman wani ko? To kwantar da hankalinka har gida naje na sameshi kai shima Tahir din da kansa yace ya janye. Ba haka Malam yaso ji ba amma yasan idan ya bari aka yi auren nan Allah bazai barshi ba. Saboda haka ya dake yace Yaya ni dai gaskiya kayi hakuri kuma na baka damar nemawa khairi miji amma banda Ahmad. Yayi kusan minti biyar a bakin kofar yana sallama basu amsa ba shiyasa bai shiga ba amma maganar Malam wadda ba karamin razana shi tayi ba yasa ya saki kwalaben asirin mufida har suka waigo suka ganshi. Batul Mamman💖 💕 MEYE DALILINKA💞 18 Yayi yayi amma ya rasa me zai ce karshe dai shigowa yayi ya zauna. Baba yace Abdullahi fada min me yake faruwa. Ahmad yayi maka laifi ne ko akwai halinsa na sabon Allah da bamu sani ba. Fuskar Ahmad kawai yake kallo a ransa yana cewa ka yafe min Ahmad. Ganin yayi shiru abin ya fara batawa Baba rai yace muna sauraronka kayi shiru. Baba Hashim yace Ahmad tun kafin abu yayi nisa ka fada mana gaskiya domin naga baban naka baya son yin magana kada ya fadi sirrinka. Kana kallon shi kasan a rude yake. Wallahi baba Hashim bansan me nayi ba. Malam yayi ajiyar zuciya babu abinda kayi kada ma ka zaigi kanka auren ne kawai bana son ayi na zumunci. Allah Ya baku wasu ku aura. Baba ya dago kai cikin bacin rai yace Ahmad bamu wuri. A sanyaye ya fita ya koma dakin mahaifiyarsa. Tana ganin yanayinsa tasan ba lafiya ta fita ta kira Momi da yakumbo suka shiga falon tare. Ni Ahmad baiyi min komai ba amma Yaya kayi hakuri auren nan wallahi baza ayi shi ba. Yana fadin haka ya fita. Yauma rufe kansa yayi a daki Umma ta rasa yadda zata yi gashi bata so khairi tasan abinda ke faruwa. Waya ya dauko ya kira Baba malam mahaifin Umma yana magana yana kuka ya sanar dashi halin da ake ciki. Ka taimaka kasa baki kada muyi abinda Allah zaiyi fushi damu amma kafi kowa sanin dalilin da yasa bazan bari ayi auren nan ba. Baba Malam yace ka kwantar da hankalinka ranar juma'a in sha Allah zan zo kanon. Amma kafin nan kada ka bari ayi auren kaji ko Abdallah. To Malam ya amsa masa cikin kuka. Haj Karima da su Yakumbo kowa kansa a daure. A daki ta tsare Ahmad lallai ya fada mata abinda yayi wa Malam. Karshe tace ko dai kana da cutar nan ne ka boye mana. Wace cuta kuma Hajiya ya tambayeta a razane. Kanjamau mana. Haba hajiya wallahi bani da ita. To ba komai nasan babanku bazaiyi shiru da maganar nan ba. Ni dai babu komai a tsakaninmu na fada da zai sa yaki jinina amma da safe zan kira Munnira naji ko tasan dalili. Khairi tana dafa indomie zata ci ta tafi makaranta ta ji muryar Umma tana cewa wallahi haj karima nima yadda kika ji maganar nan haka naji ta. Ko kinsan yanzu ko dakinsa baya bari na shiga da sassafe yake fita sai khairin ma tayi bacci yake dawowa. Ni tsoro na daya kada taji cewa mahaifinta ne baya so ta auri Ahmad. Kirji ta dafe sakamakon wani zafi da taji zuciyarta tana yi. Batul Mamman💖 💕MEYE DALILINKA💞 19 Da gudu ta ta shigo falon Umma na ganinta tayi saurin katse wayar. Khairi tace Ummana me ya faru? Meyasa Malam baya son auren tana magana hawaye suna wanke mata fuska. Umma bata da amsa ta fara rarrashinta duka duka yaushw ta fito daga asibiti malam zai janyo musu tashin hankali. A kasa ta zauna tana ta kuka Umma na bata baki sai ga indo ta shigo daga baya da gudu ta nufi kitchen saboda kaurin indomie din da khairi ta dora. Daki ta koma ta dauko waya ta kira Uncle Ahmad tana kuka yana jin yanayinta yasan abinda ya faru yace khairina kina ji na? Da kyar ta iya amsawa. Bana so ciwonki ya kara tashi kiyi hakuri ki dena kuka Baba zai masa magana. Ni kaina bansan ma abinda nayi masa bane but dont nasan Allah zai mana magani. Makaranta dai tasha ruwa haka tayi ta jiran Malam sai can dare ya dawo. Jugum jugum ta gansu ita da Umma yace me ya faru Munnira? Dole kace me ya faru mana kana neman kashe min 'ya da fada

Chapter 3 of 6