Share this page
4 / 6
take maganar don kokarinta yaji haushi ya fadi dalili kowa ya sani. Bai kula ta ba ya dubi khairi yau ko sannu da zuwa bata yi masa ba yace Ummulkhairi...ta dago fuskarta idanunta sunyi ja kamar gauta kiyi hakuri ki cire Ahmad a ranki. Bai ma jira ta amsa ba ya shige daki. A dakin umma ta kwana tana ta aikin kuka. *************** Ahmad bai taba shiga tashin hankali ba kamar yanzu da yake ganin zai rasa khairi da gaske. Baba da su Yakumbo sunyi iya yinsu amma ya dage kan bazaayi auren ba. Gashi uwa uba yaki fadin dalilinsa. Zuwa yanzu duk 'yan gidan sun san abinda ke faruwa Mufida tayi murna sosai jin malam yaki yarda. Wato da don munafurci babu wanda ya fada mata zancen auren, maganinsu kenan. Kawu Hadi wanda shi kadai ya rage a kannen babansu Malam shima har ya gaji da magana. Malam yace sai dai suyi hakuri shima ba a son ransa bane. Yana kwance a daki yau kwanansa biyu baije aiki ba don bashi da nutsuwa da kwanciyar hankali. Mufida bata gabansa tun ranar da yaga kulle kullenta. Waya ya dauko ya kira ta Khairina...kana jin muryarsa abin tausayi. Naam Uncle Ahmad sai kawai ta fashe da kuka. Tamkar tana watsa masa ruwan zafi haka yake jin kukanta. Ki yarda dani Khairi bazan taba bari a raba mu ba indai ba auren namu zai zama hatsari bane a rayuwarki. Bata ce komai ba sai shesshekar kuka...kiyi min magana mana. Uncle kada ka bari a rabamu tana fada muryarta na rawa. I won't, I promise Bayan ya ajiye wayar text yayi mata ( I Love you Ummulkhairi ina fata you feel the same way about me.) Text dinsa dai kuka ya kara mata tana cikin yi kirjinta ya fara bugawa numfashi yana sama sama. A haka Inno tazo ta ganta ta yi saurin kiran Umma. Kuka ta saka tana wargaza magungunan khairin ta rasa wanda zata bata. A haka Malam ya shigo hankali a tashe zai daga khairi ,Umma ta daga masa hannu tana kuka dakata Abdullahi kada ka taba min 'ya. Ba so kake ta mutu ba kowa ya huta ai gara ta mutun. Amma wallahi kaji na rantse maka idan na rasa 'yata na gama aurenka. Ana maka kallon malami a waje amma ni yanzu nasan cewa ina tare da mutum mara tsoron Allah. Shi kanshi idan ka kalle shi sai ka tausayawa yanayin da yake ciki. Munnira kada kiyi sabo saboda fushi. To Dr Abdullahi Saraki sai ka fada min MEYE DALILINKA na hana auren khairi da Ahmad ta fada tana rike kugu kana ganinta kasan bata cikin hayyacinta sosai. Batul Mamman💖 💕MEYE DALILINKA💞 20 Shima magungunan ya rinka dubawa da ya rasa yadda zai yi waya ya ciro da aljihunsa ya kira uncle Ahmad. Cikin bacci ya dauka jin muryar malam yasa ya ce me ya faru don wayar malam a daren nan yasan ba lafiya. Khairi ce ciwonta ya rashi ya bashi amsa a gigice. Doguwar riga ya dora akan kayan baccinsa gaba a baya ya suri keys din mota ya fita. A kan gado ya ganta kamar ta suma. Allurai yi mata har uku sannan yasa mata drip. Umma kallon malam take kirikiri yace bai yadda da aure ba amma da yaga babu yadda zaiyi ai ya kira shi ya ceci ran 'yar sa. A falon gidan ya kwana da asuba Malam yazo ya tashe shi. Tare suka je masallaci yana son tambayar Malam amma yayi masa kwarjini. malam dai bai ce komai ba har suka koma gida. Ya sake shiga tana kan abin sallah. Fita yayi bayan ta idar ta zo falo ta same shi. Ya tambayeta ya take ji tace masa da sauki daga nan ta koma daki domin malam yana zaune yana kallon su. Bayan yaje gida yayi wanka gidansu ya tafi ya yi saa Baba bai fita ba. Ya sanar dashi abinda ya sami khairi Baba yace Ahmad kayi hakuri bana son tashin hankali da Abdullahi amma kasa a ranka zanyi maganin abin da yardar Allah. Gwaggo baki ga halin da khairi take ciki ba kamar baya tausayinta. Ni ba don ina tsoron Baba Malam ba wallahi gida zan taho. Gwaggo mahaifiyar Munnira tace kul na sake jin zancen tahowa kiyi hakuri babanki yana hanyar kanon ma. Umma ta share hawaye me zaiyi a kano kuma? Akan maganar auren ne dai, Allah Yayi miki albarka. Tana ajiye wayar itama hawayen take yi tana tausayin 'yarta. Lallai yau kila asiri zai tuno me zasu fadawa Munnira bayan sun san komai. Ana idar da sallar Juma'a Alh Aliyu ya matsa kusa da liman ya sanar dashi akwai daurin aure suyi hakuri abin yazo a haka. Liman yayi sanarwa ta loudspeaker saboda haka wasu daga cikin mutanen suka tsaya. Ya dubi Baba Hashim ya ajiye masa kudi a kan cinyarsa yace kaine waliyin Ahmad yace to yana cike da mamaki wato shirun da Alh Aliyu yayi ba na wasa bane ashe . A take a nan yayiwa khairi walicci aka daura aurenta da Ahmad akan sadaki dubu hamsin mutane suka shaida. Text ya turawa kaninsa yana sanar dashi daurin auren kuma yazo yana jiransa a gida. Shima Ahmad text din ya gani murna da farinciki suka rufe shi. Gumi ne ya rinka karyo wa malam yana ta salati Umma ta dauki wayar tana karanta text din ta rangada guda tace Allah Ya saka wa Yaya da alkhairi. Dakin khairi ta shiga ta same tana karatu. Khairi ki gode Allah yanzu Baba ya daura muku aure da Ahmad. Tana kai karshen aya ta rungume umma tana kuka. Suna tsaye a haka sai jin muryar Malam suka yi yace su fito zasu tafi gidan Baba. Umma ko a jikinta domin dai bukata ta biya. Yana parking din mota a kofar gidan sai umma ta lura da kaninta Umar shima yana gyara parking yace mata tare suke da Baba Malam yanzu ya shiga ciki. Khairi har kasa ta durkusa tana gaishe shi tace kawu umar ina su ibty da zainab. Suna nan kalau ya bata amsa kafin itama ta bi bayan iyayenta. Baba Malam ne zaune kan kujera sai iyalan gidan Baba dana malam tare da Kawu Hadi. A yara kuwa daga Uncle Ahmad sai khairi. Bayan sun gaggaisa Baba ya nuna mamakinsa na ganin babban Malamin a gidansa wato Shiek Hamza Samaru daya daga cikin malaman da kasa ke ji da su. Baba Malam yace naji dadi sosai Aliyu yadda kake kokarin habbaka zumunci tsakaninka da 'yan uwanka. Hakika abinda kayi yau na kokarin ceton rayuwar 'yar kaninka aikin lada ne babba sai dai akwai kuskure a yin hakan. Umma wadda dama ganin baban nata a gidan itama yasa tasha jinin jikinta ta fara tsorata. Ya mayar da kallonsa ga Malam, yace Abdallah ranar wanka ba'a boyon cibi. Malam gumi yake ga jikinsa har tsuma yake yau sirrin boye zai fito fili. Ji yayi bakinsa gaba daya babu yawu idanunsa sunyi ja saboda firgici. Yakumbo tace yi magana mana ka barmu da zulumi. Hmmm yayi ajiyar zuciya kafin yace kuyi hakuri amma Ahmad............................... .........shirunsa ya kara tada musu hankali. Ahmad.....dana ne ya karasa da kuka. Batul Mamman💖 💕 MEYE DALILINKA💞 21 INNALILLAHI WA INNA ILAIHI RAJIUN kowa abinda yake fada kenan. Lokaci guda tsanin rudani ya shiga tsakanin 'yan uwan. Haj Karima ta kadu sosai da kyar ta iya mikewa tana nuna Malam kamar zata yi magana sai dai kafin ta iya takawa ta fadi kasa a sume. Nan da nan hankali ya koma gareta. Umma tace Malam wallahi na gama auren nan. Ka sake ni gidanmu zan tafi. Tana magana kamar mai sumbatu sai da Baba Malam ya daka mata tsawa. Ta koma ta zauna tana kuka. A wannan lokacin kuwa Ahmad ji yayi inama ya mutu ya huta ga tashin hankali ga hajiyansa a kwance. Khairi kuwa kirjinta ta dafe idanunta babu ko digon hawaye....ashe kuka ma rahma ne. Baba kuwa kallon kowa yake dai dai zuciyarsa na sake sake. Baba Malam da Kawunsu Baba da kyar suka shawo kan jamaar wurin aka yi shiru. Haj karima tana tashi ta dubi Malam tace Abdullahi ba sai kayi min sharri ba don baka son auren nan...ta juya ga Ahmad idan ka haifu cikin uwa da uba ka saki yarinyar nan a yau, a yanzu saki uku. Shi kam jikinsa babu kwari ko kadan bashi da sauran katabus bai iya cewa komai ba. Dattijan suka ce kowa ya saurara Baba Malam yayi gyaran murya. Nasan kowa a nan ya shiga cikin rudani da tashin hankali amma yana da kyau ku saurari uzurin Abdallah kafin a yanke hukunci. Malam dai kuka yake yau din da yayi ta gudu for the past 36years tazo ta cimmasa. Yaya idan ka tuna shekarunku hudu da Hajiya baku haihu ba. A lokacin dukkanmu gida daya muke tare da ku. Muna karatu ni da Hashim kana kasuwancinka. (Tana jin haka tasan karshenta wannan maganar dalilin makircin da ta kulla ne shekarun baya) Malam ya cigaba da bayani to wata rana na dawo gida ina cin abinci sai ta shigo falon da zobo ta zuba min itama ta sha. Daga nan na farka na ganni a dakinta kan gadonta. Tana daya gefen a kwance....kuka yaci karfinsa. Sai da ya numfasa ya cigaba. Har na fita bata sani ba. Kuma a ranar ne hashim ya fado daga bene. Bayan wata uku ka sanar dani tana da ciki wannan dalilin ne yasa na koma zaria har na hadu da Baba Malam. Yasan komai don ban boye masa ba. Bayansa ya kwaye musu shatin bulala ne ya dai yi fading baa gani sosai. Zuwa nayi aka yi min bulala dari a matsayin kaffara. Wannan shine dalilin da yasa nake da yakinin Ahmad dana ne. Wallahi Abdullahi kayi karya haka take fada cikin gunjin kuka. Baba haki ya fara Malam yayi yunkurin kamashi ya mike ya doke masa hannu. Uncle Ahmad ne ya fitar dashi da kyar ya sa shi a mota domin falon tamkar kurkuku kowa yake jinsa. Umma ta kama hannun Khairi fuuuu ta tashi suka fita. Ita dai khairi binta kawai take yi idanunta a bude amma bata ganin inda take takawa. Sai da suka fito Umma ta suma kuka ina suka nufa? Ita dai bazata koma gidan Malam ba. Ace wai Ahmad wan khairi ne uba daya??? Shiru taji daga bayanta tana juyawa don taji shiru khairi ba magana sai taga jini ke fita daga bakinta. Ihu ta kwala don ta shiga tashin hankali. Da gudu Malam ya fito ya ciccibe ta ya dora a kan kafadarsa yasa ta a mota sai asibiti. Batul Mamman💖 💕MEYE DALILINKA💞 22 Kwana biyar kenan ana faman abu daya, kokarin ceto rayuwar Baba wanda jininsa yayi mugun hawa da Khairi mai fama da ciwon zuciya. Kausar kullum tana asibitin amma khairi bata gaya mata ainihin abinda ke faruwa ba domin wannan sirrin gidansu ne. Tahir ma yazo dubiya rabonsa da duk su biyun tun ranar da ya sanar da Uncle Ahmad zancen khairi na da wanda take so. Kausar ina kyautata zaton akwai matsala a tare da friend dinki. Ina fata ba hanata auren aka yi ba. Ya gyara tsayuwa kuma naga kusan dukkansu kowa yana tattare da damuwa. Kausar tace to Captain nima haka na gani mu taya su addua dai. Haka ne ya bata amsa. Sai kuma yace kina ganin ya dace na tafi na barki kina jiran abin hawa? Ah haba kada ka damu ai basa wuya. No ya fada yana girgiza kai. Kizo na ajiye ki. Kememe taki yarda karshe dai kudin mota ya bata yace idan bata karba ba zai hana kowa daukarta. Yana wurin ta sami taxi ya biya kudin tare da kashedin kada a dauki kowa. Khairi ta fara samun sauki sai dai har yanzu jinin Alh Aliyu yaki sauka. Baya kaunar Malam ya shiga dakinsa da sunan dubiya. Ita kanta khairin girman babanta ya sauka a idonta. Abin duniya yayi masa yawa gashi ko sau daya Umma taki sauraron sa. A corridor din asibitin ya hadu da hajiya Karima ta dawo daga raka 'yan uwanta. Niyarsa ya wuce don bashi da idon kallonta tace Abdullahi....yau ba malam din...tsayawa yayi cike da fargaba. Idanunta fal hawaye kayi min tabo wanda baya taba bacewa ka sheganta min da daya da Allah Ya bani.. ka cutar min da rayuwa. Ajiyar zuciya yayi ki sani da mutumci na bazan so na jawowa kaina mummunar matsala irin wannan ba. Sai dai idan na bari akayi auren yaran azabar da zan gamu da ita mai radadi ce. Duk abinda nayi na yi shi ne domin mu rabauta a wurin Allah. Ta sa mayafi ta goge hawayenta ba komai Allah zai mana sakayya jira nake Alhaji ya sami sauki ayi gwajin jini amma duk da haka ka bata min suna. Har ta shige yana jin sautin kukanta...shima hawaye ya share da hannunsa. Duk abinda yayi yasan saboda tsoron Allah ne. (Tana labe tana sauraronsu ita ma ta rasa farinciki tunda aka fara maganar nan. Wai da wane bakin zata tona gaskiyar da ta binne tsahon shekarun nan?) Yau aka sallami Khairi suna shirin fita ta kalli Ummanta. Umma ina muka nufa? Zaria zamu je idan Baba Malam ya hana mu zama ina da gidan haya a ja'in sai na sallame su mu koma. Yakumbo ce ta shigo bayan sun gaisa tace Mannira ku shigo dakin Alhaji mana ina son ganin ku. A raku be suke a dakin wannan ya kalli wannan. Tun ranar da abin ya faru sai yau ta ganshi sati biyu kenan. Uncle Ahmad ya rame sosai. Hajiyansa tana kan tabarma ita da Momi sai Malam dake tsaye bayan wheelchair din Baba hashim. Baba dake kan gado juya musu baya yayi. Yakumbo tace to Alhamdulillah tunda duk mun taru a nan. Lokaci yayi da zan fadi sirron boye. Baba yayi saurin.juyuwa a tsorace yace Yakumbo kada dai kice ni ko daya daga cikin kannena ma ba mu da uba. Dariyar da tayi mai cike da nuna takaici ce da damuwa. Aliyu, Abdallah, Hashim kowanne tana kiran sunansa tana kallonsa. Ku yafe min abinda nayi muku amma hakika Ahmadu ba danka bane Abdallah. Aliyu ne ubansa. Wata irin ajiyar zuciya Uncle Ahmad ya saki. Haj Karima kuwa cewa tayi uhmm kunji ko? Ai na fada muku wallahi dannan dan aure ne. 'Yar tsohuwa tasa kuka ta fayyace musu gaskiyar abinda ya faru shekaru 36 da suka wuce. Nima nace ku biyo ni don jin wannan labari Taku Batul Mamman 💕 MEYE DALILINKA💞 23 AINIHIN ABINDA YA FARU SHEKARU 36 DA SUKA WUCE Mahaifinsu sunan sa Ahmadu amma jamaa sunfi kiransa da Saraki. Sana'ar dinki yake yi wadda ya koya wa 'ya'yansa Aliyu da Abdallah domin lokacin Hashim yana karami. Bayan rasuwar mahaifiyarsu ne ya auri Yakumbo Larai. Ta rike su da gaskiya kuma ita Allah bai bata haihuwa ba. Aliyu yana aji biyar a sakandire baban nasu ya rasu bayan gajeriyar rashin lafiya. Ko da aka raba gado sai ya kasance Yakumbo bata da rabo a cikin gidan, gasu maza sun fara tasawa basa son a rabasu tsakanin gidajen yan uwan babarsu ko babansu. Dalilin haka suka roki Yakumbo kuma akayi sa'a ta amince ta cigaba da zama dasu. Da dadi ba dadi haka suka cigaba da zama, itama tana dan sanaar sayar da kayan kamshi kamar su citta da kaninfari. Aliyu da Abdallah kuwa sun cigaba da dinki. Lokacin da Aliyu zai shiga aji biyu a jamia Abdallah yake bukatar kudin jarabawar gaba da sakandire. Kudin hannunsu kuma mutum daya zai isa har ma da ciko. Aliyu na zaune gaban Yakumbo yake fada mata yaje wurin Kawu Hadi amma kudin basu samu ba. Nima nasa akuya ta a kasuwa Ali har yau ba'a siya ba ta fada tana share hawaye. Ni shawara gareni idan zaka yarda. Ina jinki ya bata amsa. Da kanka kake cewa Abdullahi akwai kwakwalwa ga hadda a kan nan nasa. Mu shaida ne kullum na daya yake yi. Ka daure a biya masa idan yaso ina sayar da akuyar da dan kudin dinkinku sai ka biya. Mutmushi yayi haba Yakumbo bazan taba musa miki ba. Allah Yasa kada ya bamu kunya ni zan hakura in jira. Abdallah yayi jarabawa kuma cikin ikon Allah sakamakonsa yayi kyau sosai zai sami gurbin karatu a jamiar bayero ta kano. Zuwa wannan lokacin Aliyu yayi nisa a kasuwanci ya ma bar zancen makaranta. Kokarinsa duk bai wuce kanen nasa su sami ilimi ba. Bayan shekara daya ya auri Karima 'yar makotansu. Kuma daga lokacin ne suka fara samun sabani da Yakumbo. Ita a ganinta ta sha wahalarsu dole tafi Karima jindadi a gidan duk da cewa babu abinda aka rage ta dashi. Shekaru hudu kenan babu haihuwa Yakumbo kullum gori da bakar magana. Sai dai Aliyu yayi ta bata hakuri a daki domin yace bazai iya sa in sa da Yakumbo ba. A dalilinsu taki kara aure duk da bata rasa manema ba. Abdallah ya samu nasarar gama karatunsa na jamia inda ya zakara a wannan shekarar na daliban da suka karanci Mass Communication. Karatun ya dace dashi saboda akwai shi da baki ga iya tsara zance. Yana jiran a kirasu bautar kasa ne tsautsayin ya faru. Yakumbo ta jima tana bawa Aliyu shawarar ya auri Abu 'yar kaninta saboda zuwa lokacin arziki ya karu gareshi har mota ya siya ya kuma sayawa Abdalla vespa. Kullum korafinta ai karima bata haihuwa shi kuwa Abdallah idan yaji haka ranar zai wuni nasiha ga 'yar tsohuwa. Hakan yasa ta fara tsanarsa saboda yana shigar wa Karima fadan da ba nasa ba. Basiru dan autansu ta samu suka yi shawarar yadda za'a kori Karima da Abdallah gaba daya daga gidan. Abdallah ya dawo daga shago saboda har yanzu basu tafi bautar kasa ba yaje ya dauko abincinsa ya zauna a falo yana ci. Ah ah malam Audu yunwa ta koro ka ne? Ta tambaya tan a kokarin zaunawa. Ke dai bari babbar yaya meye a jug din ne? Zobo ne ta bashi amsa. Shine ko ki dan sammin. Zuba masa tayi yana sha yace sukari bai ji ba. To shazumamu sarkin zaki ni kadan nasa saboda yayanka da Hashim basa son zaki da yawa. Ni ko oho kenan. Tana bayan kofa tana saurarensu. Jim kadan Karima ta fara gyangyandi, Abdallah yace shima cikin muryar me kama da ta maye ki shiga daki mana. Da kyar ta mike ta tafi. Ba'a jima ba shima ya fara baccin. Dariya tayi sannan ta fita ta kirawo kanin nata. Sun sha wahala kafin su ka iya kaishi dakin suka kwantar dashi a kan gadon. Yaya bari kiga na cire masa riga. Itama ki cire mata dankwali. Haka suka aiwatar kafin su fita tace ai in Allah Ya yarda sai ya auri Abu. Haka kawai ya ajiye juya a gida ga kudi ya fara samuwa wata sakarai tana ci. Tana gama magana ta juya kawai ta ga Hashim wanda yake SS3 a lokacin yana masu wani irin kallo. Batul Mamman💖 💕 MEYE DALILINKA💞 24 Gaishe su yayi ya wuce dakinsa domin ya cire uniform sai dai yana ta mamakin me suke yi ita da kaninta a sama bayan nasu bangaren a kasa ne. Wani irin ciwon kai ne ya kama shi kamar kansa zai fashe ya farka a razane. Kansa ne ya yuye domin bai ma gane a ina yake ba. A hankali ya fara tuna me yayi karshe kafin ya ganshi anan. Ganin jikinsa babu riga ga Karima a gefe ba karamin razana shi yayi ba. Me suka yi? Garin yaya ya biyota daki? Innalillahi wa inna ilaihi rajiun. Yana ganin ta fara motsi yayi saurin fita daga dakin. Kasa ya sauka ya shiga wanka don kansa yayi clearing. Wani irin yanayi ya tsinci kansa saboda bai san me ya faru ba a dakin. Haka ya zauna har laasar ga matsanancin ciwon kai. A tsakar gida Yakumbo ta ganshi yana alwala. Saboda tsabar gigita da tayi ruwan da ke bakinta har kware ta yayi. Garin yaya ya farka da wuri bayan maganin da ta zuba a zobon wanda zai sa su bacci har na awa biyar ne. Gashi Aliyu ya kusa dawowa. Ita kuma bata isa tace ta gansu ba. Dama niyarta Aliyu ya dawo daga kasuwa da laasar idanunsa su gane masa. Fakar ido tayi ta koma saman tana neman inda ta jefar da ledar maganin wadda ta yar cikin sauri don kitchen din karima a sama yake. Motsi taji a bayanta tana juyuwa ta sake ganin hashim ai kawai sai ta kwalla kara wai ga gizogizo nan don tasan akansa Hashim ya taba suma saboda yana tsoronsa a kokarinsa na guduwa yayi missing step ya fado daga benen. Ita tayi haka ne don ya dena binta shi kuma yadda yaga tana sanda ne yasa ya bi bayanta. A sume ta sauko ta sameshi ta fara ihu. Gidan nasu ya hadu da tashin hankali a lokacin da likitoci suka tabbatar musu da cewa bazai iya kara motsa wata gaba a jikinsa ba banda kansa. Yakumbo tayi nadama mara misaltuwa. Garin son zuciya ta cutar da dan maraya. Wannan tashin hankalin yasa Abdallah mantawa da abinda ya faru sai dai bayan wata uku Aliyu cike da farinciki ya sanar dashi karima na da ciki. Wannan dalilin yasa da posting dinsu ya fito ya tafi kaduna sai da yayi shekara guda bai dawo ba. Shi niyarsa ma ya tafi kenan don bazai iya cigaba da ganin karima da abinda zata haifa ba. A garin kaduna an tura shi wata makaranta a zaria bautar kasa wadda take kusa da masallacin da Baba Malam mahaifin Munnira yake koyarwa. Kullum bayan magariba ake karatun. Wata rana ana karanta suratul Nur yaji irin hukuncin da Allah Ya tanadar wa mazinata. Ranar yayi kuka sosai bayan sunyi isha ya tari Malam a hanya ya sanar dashi yana da matsalar da zaiso su tattauna a kai. Washegari yaje gidan malam din kamar yadda sukayi alkawari ya sanar dashi halin da yake ciki. Malam yayi masa nasiha yace ai ba da gangan kayi ba kaje ka yawaita istigfari. Yace to Malam maganar haddi fa? Idan baayi min ba bazan taba samun kwanciyar hankali ba ko da ita ce ajalina. Ba yadda Baba Malam baiyi ba ya dage sai an yi. Anyi masa bulala dari tunda da bakinsa yace ya aikata. Baba Malam ya tausaya masa sosai ya bashi daki a gidansa ya sanar da matarsa komai domin mace ce ta kwarai me rikon sirri. Da kansa yayi jinyar Abdallag har ya warke kuma a nan ne ya nuna shaawarsa ta son juya akalar kartunsa ga addini. Yayi karatu sosai tare da Baba Malam har aka gama bautar kasa ya kara lokaci. Da malam yaga bashi da niyyar komawa gida yayi masa nasiha sosai. A dole ya koma 'yan uwansa bayan doguwar mita suka hakura. Bayan wasu shekaru ne lokacin da Munnira ta gama secondary Baba Malam ya bashi aurenta saboda ya yaba da hankalinsa kuma yaga bashi da niyyar aure sai karatu. A lokacin ne kuma Aliyu da kansa ya nemi auren Abu wato haj zainab ko muce Momi matarsa ta biyu. Yakumbo ta dada tsorata da lamarin Allah. Wato zafin nema baya kawo samu. Gashi da kansa ya nemi auren. Ta kira Basiru ta roke shi da su binne maganar abinda ya faru zata cigaba da kulawa da hashim har mutuwarta. Kuma ba zata taba tona wannan abin ba tunda basu sani ba. Sannan ta gargade shi da kada ya bari baban Abu ya sani domin shi mafadaci ne akan abinda yake gaskiya ita ma yayarsa tsoronsa take ji. Batul Mamman 💖 💕 MEYE DALILIKA💞 25 Ko da Yakumbo ta gama bada nata labarin shima Malam ya fadi abinda ya faru a zaria. Dakin sai sautin kuka da salati ake ji. Har kasa Yakumbo ta tsuguna neman gafara. Baba ya sauko daga kan gadonsa yace ta tashi. Ai ni Yakumbo tunda dai ta tabbata Ahmad dana ne wallahi na yafe miki sai dai wadanda kika yiwa laifi suna da yawa. Komawa tayi gaban Baba Hashim wanda yake ta zubar da hawaye ka yafe min dana, ka yafe min. Ita ma kukan take yace Allah Ya yafe mana baki daya....ya tuna yadda ko sau daya bata taba nuna kyama ko gazawa akansa ba duk da tsufanta. Momi ta kalli Yakumbo yanzu duk a kaina kika kusa tarwatsa gidan nan? Nata kukan yafi na kowa bata taba tsammanin wannan badakalar ta shafe ta ba. Ita dai Yakumbo kuka take yi duk wanda ke wurin dole ya tausayawa tsohuwar. Kafin su fita daga dakin kowa ya yafewa dan uwansa. Malam ya kira mahaifin Umma ya sanar

Chapter 4 of 6