dashi komai.....ikon Allah yafi karfin wasa Abdallah, hakika Allah Yaso cire maka wannan tunanin na ka aikata zina shiyasa Ya hada zukatan yaran nan don gaskiya tayi halinta. Allah Ya kara mana imani.
Khairi da Ummanta gida suka wuce tare da Malam. Umma kamar ta ari baki wurin bashi hakuri ranar. Sai da suka kebe yace Munnira ban taba jin haushinki ba duk abinda kika yi akan gaskiya ne.
Bayan kwana biyu Baba ya matsa a sallame shi daga asibiti saboda yana son ayi ayi bikin Ahmad da khairinsa.
Bayan ya kai babansa gida, gidansu khairi ya taho. Kamar wadda kwai ya fashewa a ciki haka ta shigo falon. Shiru shiru babu mai niyar magana rabon da su hadu tun ranar da aka fasa kwai a gidan Baba. Ita carpet ma take ta kallo yau. Bata ankara ba taji shi a kusa da ita. Tana dago fuska suka hada ido...gaba dayansu sunji wani irin yanayi a tare dasu. Tayi kokarin matsawa yasa hannu ya riko ta gaba daya ji tayi kamar bata taba shiga yanayin farinciki kamar wannan ba. Bata ki su zauna a haka ba sai kuma ta tuna kada ta bada mata...uncle ka sake ni. Daya hannun yasa yana shafa fuskarta.... aure ni da ke mutu ka raba kinji ko. Ganin bai fahimce ta ba tace ba haka nake nufi ba. Daga gira yayi yana kallonta me kike nufi? In bari ki zauna kina kallon kasa kamar baki da abin kallo. Kafin ta bashi amsa wanda ita duk a rike ce take saboda yadda yake zagaye fuskarta da dan yatsan sa yace kin rame sosai khairi na. Bana son motsatstsiyar mace. Lallai ma nice motsatstsiyar? To ni kuma bana son kajamemmen miji. Dukkansu dariya suka yi. Sannan ya hada goshinsa da nata a hankali yace mata I love you Ummulkhair... khairin Uncle Ahmad. Dadi ne ya ratsa zuciyarta. Tayi saurin tashi ta gudu sai wayarsa ta fara ringing. Yana dubawa sunan Mufida ya gani.
Batul Mamman💖
💕MEYE DALILINKA💞 26
Yana dauka ta fara masifa. Na kira Umaima tace tun dazu ka mayar da Baba gida...ina ka tsaya? Ta tambayeshi cikin bacin rai. Bata jira ya bata amsa ba tace ina jiranka maza ka dawo gida. To kawai ya ce ya ajiye wayar domin shi mamaki yake yadda ta sami kwarin gwiwar ya masa magana a haka. Can ya tuna maiko-maikon daya gani a goshinta da kirjinta a daren jiya. Dariya ce ta kubuce masa daya gane kayan mallaka da juya miji akayi amfani dasu shine take gwadawa yau,Allah Yasa khairi ta fice ma yayi mai isarsa. Shegiya to ta Allah ba taki ba ina karanta Ayatul kursiyy har wani surkullen banza zai kamani.
Daga kofar falo Sadiq ya rugo da gudu ya rungume shi. Yana shirin daukarsa ya kula gaba daya hannuwansa da bakinsa harma da gaban rigarsa duk sun baci da miya. Da fada ya shiga gida Mufida tana zaune tana kallo ta galla masa harara. Dama jira nake ka dawo ka wanke masa....ga wurin da yaci abincin ma duk ya bata min ka goge don Atine mai aiki bata nan. Kallonta yayi shekeke sai kuma ya tuna yanzu fa tana tunanin aikin bokanta yayi. Daukan yaron yayi yayi masa wanka ma gaba daya sannan yazo ya gyara wurin. Ranar mufida sai faraa da farinciki. Uncle Ahmad kuma sai dariyar mugunta idan ya faki idonta. Yaro bai san wuta ba sai ya taka...ranar da zan damke ki a hannuna zaki wahala ya fada a ransa.
Sati biyu aka sa bikin Khairi sai dai sam Baba yaki yarda yace shi akwai shirye shiryen da zaiyi. Malam ya dube shi haba Yaya wane shiri kuma ya rage ai kawai a kaita dakinta. To nuna min iko zaka yi kuma Baba ya tambaya. Allah Ya baka hakuri ya bada amsa. Yana gyara karin hularsa yace ai nasan zaka ce baka son bidia sai dai kada ka manta bikin aure yana da bambanci da taron mutuwa kuma dole mu gayyaci mutane su taya mu murna. After all we have been through Abdallah dole muyi abinda ran kowa zaiyi dadi. Baba Hashim yace duk abinda ya faru da khairi ai baza mu kaita daki ba kamar ladan noma ko yakumbo. Haka ne ta bashi amsa a hankali. Har yau ta kasa sakin jiki da su kamar da.
Mahaifiyar Kausar ita ce ta dauki nauyim gyaran amarya ciki da waje domin mutuniyar nijar ce kuma sana'arta kenan. Hatta turaren wuta na gida duk ita ce take yi. Kwanaki uku kawai da fara gyaran jiki Khairi ta soma canjawa ga wani kamshi da take yi. Abincin da take ci ma ita take bata don a cewarta khairi ta rame saboda ciwo ita kuwa bata son ganin mace a tsamure kamar kudin guzuri. Tana zaune kan kujera umman kausar ta sa mata kaskon turaren jiki ta lullube ta da katon bargo wayar kausar ta fara ringing sai ta katse. Haka take ta yi da an kira sai tayi rejecting khairi kuwa ta sa ta a gaba da kyar ta fada mata wai Tahir ne yake yawan kiranta a waya. Khairi tayi murmushi to meyasa bakya son dauka ko don ina wurin ne? Lah wallahi ko baki nan bana dauka. Khairi tace to kinsan wulakanci ba halin mu bane. Kika sani ma ko ya fada ne...eyye eyye Kausar ta captain tahir. Nan suka fara aikinsu na cacar baki kamar kananan yara.
Umma ta zage da shirin aurar da tilon yarta su inno ma baa barsu a baya ba. Mufida dai ta cigaba da sa maigida aiki yana biye mata. Ko sau daya taba ce ya fasa auren ba don tasan ko a wurin danginsa bata isa ba. A cewarta zata yi maganin ta idan ta iso.
Batul Mamman💖
💕MEYE DALILINKA💞 27
Anyi biki na gani na fada sannan kuma ayi abin a tsaftace kamar yadda Malam yaso. Babu kwadon maza da mata ayi ta rawar rashin kunya ko kaga budurwa ta tafe kamar sanda wani lokacin harda masu aure a wurin biki babu mayafi sai gwaggwaro. Ayi dinkin nan riga ta matse duk kayan kirjin su rinka neman fitowa ta sama. Wani katon banza ya kalle ki a bati siddan. Wallahi mu kiyaye mata mu saya wa kawunanmu mutumci.
Ranar asabar za'a kai amarya tasa wani farin material me adon lemon green flowers. Takalminta da 'yar karamar jaka harda katon mayafin da ta lullube jikinta duk lemon green ne. Kamshi take me dadi Anti Rumana da Anti Sadiya kannen ummanta su suka shirya ta. Wata matar wan umman kuwa da suke kira Umma Zainab mouth freshner ta bata kafin ta fito daga daki tace ki fesa yaji kamshi mu ma iyayenki duk a haka muke gyara tsufanmu. Kunya ce ta kama Khairi. Ranar sun sha kuka ita da Ummanta dakyar aka raba su.
Gidan Baba aka kaita yayi mata nasiha. Ana shirin tafiya yace ai Malam ya sanar dashi a bar mijinta yazo ya dauketa saboda haka kowa ta je ganin daki daga baya. Momi dai sai mita don ta gama shirin kai amarya tunda Umma da Hajiya duk babu su. Ko da Uncle Ahmad ya iso da abokinsa daya Baba har waje ya rako su jikin wata sabuwar mota kirar honda silver colour mai kyau. ya kama hannun Khairi ya sa mata makulli a hanunta...cike da mamaki ta dago kanta yace Ummulkhairi wannan kyautar ki ce fatana ku zauna lafiya da dan uwanki. Sai ka daure ka koya mata don ba taka bace yace da Uncle Ahmad. Godiya suka yi masa yace maza maza ku tafi dare na kara yi. Ahmad ka bar motarka a nan gobe Hashim karami sai ya kawo maka ku tafi a wannan.
Tana kuka baba ya bude kofa da kansa ya zaunar da ita a ciki suka tafi. Kusan mintuna biyar yana tuki sai sautin kukan khair ake ji. Can sai taji shima kamar yana kukan ta dago kai murya duk ta dakushe saboda kuka Uncle lafiya? Shiru yayi ya cigaba da abinda yake yi. Hankalinta ya fara tashi....uncle dina me ta faru? Kwaikwayon muryarta yayi yace Khairina ce bata so na. Bude idanunta tayi wadanda suka yi ja tace wallahi ban fada ba, waye ya gaya maka. Ganin ta rude yasa shi yin dariya ashe kukan gulma kike yi ana turo ki kina wani makalewa. Kin bashi amsa tayi wai ita tayi fushi. Haka yayi ta tsokanarta har suka iso gidan.
Ta kofar kitchen ya shiga da ita sannan ya wuce da ita part dinta. Ita dai bata tambayeshi dalili ba shi kuwa yayi haka ne saboda Mufida da kawayenta da suke babban falon gidan wanda take sada mutum da dukkan parts din gidan. Suna zaman jiran kwakwaf.
Tun daga falo take jin kamshi lallai su kausar da umaima sunyi aiki. Tana shirin zama ya kama hannunta suka shiga daki. Wani guntun zazzabi taji ya kama ta lokacin da ya rufe kofar...wai itace a daki daya da Uncle dinta. A darare ta zauna a bakin gado ta sake jan mayafi ta rufe fuska. Hmm wai ko wacce amarya don gulma sai tayi ta rufe rufe da an kwana biyu ta fi ruwa iya gudu. Sarai ta fahimce shi amma sai tayi shiru. Hula da rigarsa ya cire daga shi sai dogon wando da singlet ya dawo gabanta ya zauna. Tun dazu kamshinta ke tada masa hankali amma yanzu da ya zauna gabanta abin karuwa yayi....da kyar yace khairina yau ya akayi baki da amsar bayarwa idan nayi magana? Ko har an zo ranar da zan kashe bakin aku ne....tsit ya sake ji sai ya mike ya shiga toilet. Alwala ya dauro ya fito yace itama taje ta yi.
Bayan sunyi sallah ne ya dafa tsakiyar kant yayi addua sannan yayi musu doguwar addua da fatan zaman lafiya. Kazar amarci ta al'adar bahaushe ya kawo mata da lemo, ruwa tare da shawarma don yasan tana son ta. yau dai khairi jiki ba kwari kadan ta ci bayan ya matsa mata. Tashi yayi bayan sun gama yace zaije ya rufe gida tana iya yin wanka kafin ya dawo.
Ko da ya shiga falon mufida ya tarar da kawayenta biyu suna ta shewa. Tayi mamakin ganinsa sai kuma tace ko an fasa kawota ne munji shiru tun dazu...tafawa kawayen suka yi. Shi bai ma taba ganinsu ba kila a gidan boka suka hadu ya fada a zuci. Ku tashi ku tafi zan rufe kofa dare yayi. Kai!!! Mufida tace daga zaune. Kawayen nawa kake kora to babu mai fita sai an kawo wannan ragowar asibitin. Tsawa ya daka musu yace idan basu fita ba zai kira maigadi yayi waje dasu. mikewa tayi cike da mamaki . Yau ita yake wa haka kuma a gaban wadanda ta gama cika baki a gabansu. Suna fita ya rufe kofar gidansa sannan yace mata sai da safe. Kafin tayi magana yayi gaba.
A bakin gadon ya sake ganinta ya wuce ya shiga toilet yayi wanka. Ko da ya fito daga shi sai tawul a kugunsa ya tarar ta juya baya tana ninke mayafi. Niyyarta ta kwanta baccin karya kafin ya fito. Tsayawa yayi yana kare mata kallo ta baya. Riga da skirt din duk sun matse ta ga gashinta da ya fito ta dankwalunta ya kwanta wurin kafadunta. Ji tayi kawai yayi hugging dinta ta baya...nan da nan jiki ya fara rawa. A ya dawo da kansa daidai kunnenta yayi mata rada a kunne. Zaki yi wankan ne ko nayi miki ya fada bata ma iya bashi amsa ba domin ji tayi yana mata kiss a wuyanta. Duk isakar dakin ita zafi take ji. Juyu da ita yayi ya sake jawota jikinsa ya sake yi....Khairina shiru ba amsa. To ta ina ma zata yi magana bayan yau uncle din nata ya sauya gaba daya. Shi kuwa kasa hakura yayi ji yayi idan bai rike ta ba bazai iya shirin bacci ba. Da kyar ya sake ta ya koma ya shafa mai a jikinsa....a sace ta rinka kallonsa har ya gama ya sa kayan bacci itama ya miko mata wasu riga da wando. Bari na saka miki tunda ke baki iya tattalin miji ba. Ba shafa min mai babu saka min kaya . Sai yanzu tayi magana tace kamar wani baby? Bata ma san maganar ta fito ba. Karbar kayan hannunta yayi yace idan na bazaki min kamar baby ba ni zan miki. Nan suka fara kokawa ya dage shi zai cire mata kaya ya sa mata kayan bacci.
Suna haka suka ji wani irin bugun kofa kamar zaa ballata.
Batul Mamman💖
💕 MEYE DALILINKA💞 28
Bugun aka sake yi kamar maiyi na da tabin hankali. Fita Uncle Ahmad yayi yaje ya bude kofar ita kuwa khairi tana cikin daki. Yana murda mukulli ta banko kofar dakin. Don wulakanci sai ka dawo dakin nan ka zauna idan ba'a kawo amaryar ba sai ka hakura. Yana kallonta fuskar nan tasha hoda har ta so tayi yawa ga uban kwalli ido rambajau. Lallai mufida ta dage da son juya miji. Daga daki Khairi na jiyo maganganun da take ita mamaki ne ya kamata dama haka Anti mufida take. Lallai zata koya mata hankali don ko bata auren Uncle bazata jure matarsa taci mutumcinsa ba a matsayinsa na yayanta.
Mufida ki koma dakinki khairi na ciki. Me ka ce? To ta ina ta shigo wannan karon cikin ido take kallonsa. Tare muke Mallam baya son taron kai amarya ya bata amsa. Ganin ya kalli fuskarta da idonta yasa tace kaga Abban Iman nifa ban yarda ka kwana a dakin nan ba ka wuce kawai mu tafi. Yana kokarin magana tace dakata bana son jin komai kawai ka wuce. Khairi dai abin duniya ne ya isheta lallai uncle ya bari ake masa haka. Muje kawai yace da ita Khairi tayi saurin fitowa daidai lokacin da yake jan hannun mufida. Wani azababben kishi ne ya kama ta suna fita ta kama kofar dakin ta kulle ta ciki. Ta fada gado tana kuka.
Dakinsa ya wuce da ita don baya son tashin yaransa a dakinta sannan baya son yin hayaniya gaban khairinsa saboda bata da ishasshiyar lafiya. suna shiga yace ke ni kike wa tsawa saboda baki da kunya? Ko kina zaton ban san abinda kike yi ba? Wallahi idan kika sake kokarin maimaita abinda kika yi yanzu sai na fasa miki jiki. Shashashar banza da iliminki da wayonki kin mayar da kanki mahaukaciya. Ganin yadda ya rufe ido yana mata fada yasa tayi shiru har ya gama fadansa ya fita. Da sake wallahi damanasan zaa rina kishi da yar malam . wato itama tazo da shirinta.
Ko da ya koma sai ya shiga falon nata ya kulle kofa ya kama kofar daki yaji a rufe. Murmushi yayi wato tayi fushi tun yanzu kenan. Khairina please ki bude kofar. Tana daga kan gado ta share hawaye anki din....tohhh rashin kunya kika fara kema? Shiru yaji tayi. Idan baki bude ba zan koma wurin mufida. Sai ka dawo ta bashi amsa amma a zuciyart tana tsoron kada ya tafin da gaske. To ki taso ki kulle kofar falon sai da safe. Tasowa tayi ta dauki mayafinta ta yafa kan rigar baccin da ta saka ta dawo bakin kofar da sabon kukanta. Yanzu maimakon ka bani hakuri sai ka koma? Ashe fushin karya kike ma tunda har kin karaya ya bata amsa. Sweet dreams kinji khairina. Alamar an bude kofa an rufe taji hasken fitilar da take hangowa ya bace. Cike da takaici ta bude kofar daki da gaske ka tafi take magana cikin muryar kuka tana shafa bango don bata san inda makunnin filar yake ba. Lallai ma sai na fadawa Umma gobe ta sake fada. Ji ta yi an daga ta gaba daya ya shiga dakin ya ajiye kan gado.
Kulle kofar dakin yayi tare da kashe fitila ya dawo ya kwanta tare da jawota jikinsa. Me zaki fadawa Umman? Uhmmm tace a hankali. Baki ji me nace ba zo na maimaita miki. Kwacewa tayi ta koma gefen gado ka koma wurin anti mufida. Allah Ya baki hakuri khairina yace tare da sake janyota jikinsa. A haka suka yi bacci. Kamshin da take yana dada tada masa hankali sai dai yasan yadda take rai a bace ta wani kankame jiki gara ya barta ta huta.
Batul Mamman💖
💕 MEYE DALILIKA 💞29
Har yadawo daga masallaci tana bacci. Ji tayi ana ja mata yatsun kafa ba shiri ta tashi tana dariya don ita ana taba mata kafa ji take kamar cakulkuli ne. To shashashar madina daga taba kafa ya fada yana zama kan gadon. kinyi sallah kuwa? Saurin mikewa tayi tace a'a meyasa baka tashe ni ba ta fada tana tabe baki. Har dundu nayi miki ashe haka kike da nauyin bacci. To daga yau da ruwan sanyi zan rinka tashinki. Wucewa tayi toilet tayi alwala bayan ta idar da sallah ta jira ya kammala karatun Qur'an ta gaishe shi. Kin amsawa yayi sai da ya ajiye Qur'anin yace wa ya fada miki haka ake gaishe da miji. To ya zan gaisheka Uncle? Lips dinsa ya nuna mata tayi kamar bata gane ba. Bushewa yayi ne kake son na miko maka mai. Kin manta tsagewa yayi ki miko allura da zare. Biyota yayi tayi saurin shiga toilet ta rufe.
Bayan ta fito daga wanka ta tarar baya dakin. Riga da skirt ta saka na atampa dinkin yayi mata kyau. Turare da humra kuwa sunyi aiki. Tana fitowa falonta ya shigo shima yayi wankan yana ta kamshi. Fito muyi breakfast yace tare da komawa. Biyo bayanshi tayi. Tana shiga babban falon taji an rikota ta baya. Anti Khairi wai kin zama maman mu kema? Iman ce yar shekara hudu me sunan hajiyar uncle. Na zama ta amsa mata sannan ta daga ta sama yadda ta saba yi mata. Sadiq ne ya taho yana cewa nima nima. Shima daga shi tayi yana ta dariya. Uncle Ahmad yana kan kujera yana musu dariya. Suna haka Mufida ta fito da tray a hannunta. Khairi tace Anti Mufida ina kwana....wace irin anti kuma ana zaune kalau? Idan ni antinki ce ai bazaki aure min miji ba. Shiru khairi tayi bata ba ta amsa ba. Mufida ta dubi mijinta ina fata ba zuwa kayi da ita ku ci abinci ba don wallahi bazanyi mata girki ba Kura da shan duka gardi da kwashe kudi. Uncle Ahmad yace Khairina muje dakina akwai kayan tea.
Bayan sun gama ya kira mufida a waya. Sai da ta fi 20minutes kafin ta zo ran Uncle duk ya gama baci. Khairi tana ta kallon yanayin fuskarsa ranta yana sosuwa. Ita tasan har ga Allah bata zo da niyar fitina ba gidan amma tana ganin zata saitawa Mufida zama indai ta nemi batawa mijinta rai. Banko kofar tayi ta shigo ta sami wuri ta zauna tana ta kumburi fuskar nan tasha hoda. A ransa Uncle yace narambada wannan boka ya cuceni. To dama magana zanyi muku game da yadda nake son tafiyar da gidana. Bana son rigima ko tashin hankali saboda haka ku kiyaye....abu na biyu kowa nayi mata kitchn dinta duk me girki ita zata dafa abincin duka gida. Ga store nan duk abinda babu magana zaku yi. sannan zaku rinka raba kwana bibbiyu bayan an gama kwanaki bakwai na farko. Idan da mai tambaya sai tayi. Mufida mikewa tayi kayi ka gama rawar kafarka akan wannan yarinyar da ta rasa miji. Wani takaici ne ya kama khairi tana ganin Uncle Ahmad ya tashi da niyar fada sai kawai ta ja hannub rigarta daya zip dinta ya bude ta baya ta tashi ta tafi gabansa. Uncle dina zuge min zip dinnan please. Yadda take maganar yasa yayi murmushi ya tashi. Ai da gudu Mufida ta fita tana kuka. Iskancin har a gabana Allah Ya isa.
Batul Mamman💖
💕MEYE DALILINKA💞 30
Tana fita suna jiwo muryarta tana ta fada. Ina kokarin daidaita matsala kina karawa ko Khairina...ashe kin iya rigima. Don Allah kada ki biye mata kema kila kiyi abinda ya fi nata idan kika ji zanyi aure. Yana magana yana jan hancinta.
Karar mota suka ji yayi saurin sakin khairi tare da lekawa waje ta window. Mufida ce taja mota ta fita da yaranta a ciki. Yadda ya juyo ransa a bace ya nuna khairi wallahi duk yarinyar da ta yi min yaji sai dai iyayenta su kawota. Ba 'yar da zanyi biko. Yadda yake fada sai ka ce khairi ce tayi laifi. Ficewa tayi daga dakin itama rai a bace.
Ranar haka ta wuni sukuku shi kuwa Uncle ko dakinta baije ba. Ko da wasa bai taba tunanin rabuwa da mufida ba saboda yana sonta amma ya rasa waye ya bata gurguwar shawara har ta fara neman hanyar bata. Mukullinsa ya dauka shima ya fita daga gidan. Har ya kusa kwana ta tuna baiyi wa khairi adalci ba. Dawowa yayi ya tarar tana toilet. Duk yadda ya buga taki budewa. Dakin Mufida ya koma ya nemo yan tarkacen mallakar da take amfani dasu ya nufi gidan Malam.
Girgiza kai Malam ya rinka yi da yaji bayanin Ahmad. To ka kira ta a waya kaji inda ta tafi ne? A'a malam amma nasan gida zata je. Wayar babanta Malam ya kira ya tabbatar da zuwanta. Ai nima kiranka nake shirin yi ka rigani. Daga anyi mata kishiya sai yaji. Abinda nake so ka kyale ta har sai tayi sati taji uwar da ake ji a gidan sai muyi maganar. Malam yace ai bazaayi haka ba ni ina da karatu ne yau na kusa makara amma gobe in Allah Ya yarda zanzo mu tattauna. Godiya yayi masa sosai. Bayan ya ajiye wayar ya sanar da mahaifiyarta. Itama ko kadan bata goyi bayanta ba.
Khairi dai ana fushi da angon saboda haka da ya dawo bayan laasar ta hade masa fuska. Dariya yayi Khairina kinyi fushi ne...ko dago kai bata yi ba tana daddana waya a kan kujera. Zama yayi ya kwashe kafafunta ya dora kan cinyarsa. Tana jin haka ta fara murmushi sai kuma ta dake kada tayi saurin sauka. Tafiyar tsotsa ya fara mata sai dariya tana kokarin kwacewa. Rungume ta yayi yana mata magana a kunne. Kiyi hakuri kinji khairina. Bata bashi amsa ba jin yadda yake shafa mata baya. Can taji yace nifa yunwa nake ji. Ta tura baki bayan baka bani komai naci ba ka fita. Da sauri ya tashi tun safe haka kika zàuna. Don Allah kiyi hakuri. Bari na dafa miki indomie da kaina sai na hada miki gas cooker dinki ta baya. Ganin ya rikice tace kai dai wasa nake. Naga zaka min horon yunwa ne shine na hada ai ba wuya. Ga naka abincin can amma ba nama don ban gani ba. Kissing din goshinta yayi duk da haka kiyi hakuri.
Daren ranar kuwa anyi kwanan farinciki tsakanin ma'auratan. Khairin Uncle har Allah Ya isa tayi masa karshe tace masa mugu saboda ganin yadda ta wahala yayi mata allurar bacci. Da taimakonsa ta tashi ya cika mata bucket da ruwan zafi tayi wanka. Sai da tayi sallah ta shirya tsaf ya dawo dakin. Tana ganinsa jiki ya fara rawa. Dariya yayi harda hawaye ta mugunta. Haka kike da tsoro dama...harararsa tayi kai amma kinyi kyau kamar a sake. Sai hawaye ya gani sharrr. Ikon Allah na auro mai arhar hawaye. Rarrashi ya zauna yi bayan tayi shiru yace yanzu khairina jiya fa kin min Allah Ya isa. Bude idanu tayi ni din? Kwarai kuwa harda kirana mugu. Gaskiya bani bace ta fada tana dariya. Ni har ina tunanin irin rakin da zaki yi lokacin haihuwa.
💕MEYE DALILINKA💞 31
Bai bari tayi komai ba ranar duk. Da kansa ya sama musu abinda za su ci. Yana dawowa daga sallar laasar yace mata zaije wurin Malam. Ta so binshi yace idan ba so take ayi musu fada ba su bari ko sati ta cika.
Har bakin kofa ta rako shi yana rike da hannunta. Sai ka dawo Uncle dina kada ka dade...kashe mata ido yayi akwai abinda zaki bani ne ko salon na dawo a bini da Allah Ya isa. Hannuwanta biyu tasa ta rufe ido cike da kunya ta koma ciki da gudu.
Kana ganinshi kasan yana tare da nishadi. Yana zuwa bayan ya gaisa da mutan gidan Malam yace ya tashi su tafi gidan su Mufida. Bata rai yayi ni fa har rantsuwa nayi bazan taba zuwa biko ba duk ranar da tayi yaji. Murmushi Malam yayi ai ba biko zamu ba. Ina