An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://thausanovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.thausanovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
ο»ΏBatul Mamman
Sunday, 29 May 2016
Batul Mamman at 14:49
MEYE DALILIN KA
MEYE DALILINKA π 1
Bismillahir Rahman Rahim
Haj Munnira ta tsaya ta karewa dakin kallo cikin takaici komai a hargitse gado kamar yara biyar ke kwana, filo daya a kasa da kayan bacci sai ledojin sweet dana capri sonne. Gefe kuma wardrobe shima a bude duk an hargitsa har wasu kayan sun fado kasa. A takaice dai dakin tamkar yayi sati baa gyara shi ba. Me zan mata ne idan ta dawo abinda take ta tambayar kanta kenan. Can dai ta kwalawa Inno kira Inno yaushe rabon da a share dakin nan? Inno tana raba idanu tace Hajiya yau ne kawai ban share ba kuma zan gyara shi tas kafin ta dawo har bandakin duk zan wanke.
Hajiya Munnira tace ni ba dalilin da yasa na tambayeki ba kenan jiya ba tare muka gyara ba dake har na shirya mata wardrobe? Haka yake Hajiya ta bada amsa. Hajiya tace to wallahi idan ta dawo kika nemi hanani dukanta zamu saba dake na fada miki tun wuri. Tana gama magana ta fita. Nan da nan Inno ta hau kwashe kaya zata fara gyara.
Da gudu ta shigo tayi jefa da school bag dinta a kasa, lunch box ma ya bi shi sai takalmi wanda ta rinka cilla kafafunta sai da suka fita da kansu. Na kafar hagun yana fita sai a kan fuskar Haj Munnira. Ai tana ganin haka tayi saurin durkusawa kasa tace Assalamu alaikum Ummana na dawo na sameki lafiya? Ko kulata batayi ba don in da sabo to ta saba da halin Khairi na bada hakuri da nutsuwa idan tasan bata da gaskiya wayar rediyo ta ciro tayi kan tilon yar tata. Tsoron duka ne da Khairi kamar me don haka iyakar muryarta ta bude tana ihu. Ummana kiyi hakuri kada ki dokeni wallahi na dena jifa da takalmina. Inno ta fito da sauri Hajiya kiyi hakuri. Ya mukayi dake Inno? Ta tambayeta cikin fushi sannan ta cigaba. Yarinya ita kadai ta rinka caja min kai. Ke ba namiji ba Khairi amma gara wasu mazan da ke. Dakinki kamar filin dambe ga kazantar tsiya. To daga yau babu me sake yi miki shara ko wankin toilet da gyaran kaya kuma kullum sai na tabbatar kin gyara zaki fita makaranta. Khairi ta kalli Umman tata tace na dena Umma daga yau Allah kuwa. Ni tashi ki bani wuri. Tana tafiya Umma ta lura hijab dinta ya yage ta baya tace Khairi me ya sami hijab din? Umma kusa ce a seat dina ina tashi ji kike kyeeeet. Inno abin dariya ya bata ita kuwa Umma bata jira ta rufe bakinta ba ta bi ta tace sai dan banzan baki kamar reza zo nan ta sake daga wayar zata dake ta.
Yi hakuri Anti taji an fada daga bakin kofa. Da gudu Khairi taje ta rungume shi. Umma tace ai yau ko zaka ari baki Ahmad sai ta zane yarinyar nan. Khairi wadda tuni ta fara hawaye ta kankame shi Uncle Ahmad don Allah ka bata hakuri. Dan murmushi yayi wanda ya kawata kyakkyawar fuskarsa yace Anti Munnira kiyi hakuri kinga yarinya ce idan ta girma zata dena.
Umma tace kayya dai ai ba alama ta maida kallon ta ga Khairi tace idan kika girma a haka bana jin zaki sami mijin aure.
Subhanallahi Inno tayi saurin fada tace haba Hajiya kada kiyi wa yar tawa baki mana. Umma ta tabe baki ta zauna bakin kujera tace yo yar shekara tara tana wannan abin ai ban ga ranar girman ta ba. Ahmad shima zaman yayi yace ni ina sonta Anti so bata da matsalar miji. Ya kama hannun Khairi kinsan bana son kazanta ko? Eh ta bashi amsa. To daga yau kada ki bari na sake jin zancen rashin tsaftarki. Tayi murmushi har gibinta ya fito. Ai na dena daga yau Uncle Ahmad. Tashi tayi taje ta cire uniform dinta sai dai kafin ta kai dakin yana kallonta tasa hannun damanta a hanci ta share hannun a rigarta. Wayar hannun Umma ya karba ya bita yana cewa ashe ni zan fara zaneki tana gudu. Umma dariya tayi tace wai! Gaskiya Ahmad kayi sa'ar mata.
Batul Mamman
π MEYE DALILINKA π 2
Filo ta jawo ta dora kanta ta cigaba da karanta wasikar jaki. Gadon duk books ne da handouts ko ta ina amma yau ma tunanin Uncle Ahmad ta tashi dashi ta kasa mayarda hankali tayi karatu gashi test gareta gobe.
Kausar ce ta shigo dakin ta daka wa Khairi doka a cinya ba shiri ta tashi zaune tana murza wurin. Tace to muguwa me nayi miki. Kausar ta zauna kan gadon tace tun dazu nake sallama baki amsa ba kina ta juyi kamar waina. Nasan bazai wuce tunanin Uncle Ahmad ba. Har kin manta muna da test gobe ko? Ni karatu nazo muyi malama tashi ko na kara miki ta sake daga hannu.
Wani hoto ta nunawa Kausar din wanda Uncle din ya turo mata ta whatsapp. Shi da yaransa ne Iman da Sadiq a bakin ruwa. Komai hassadar mutum dole ya yaba domin duk sunyi kyau. Kausar ta ajiye wayar a gefe tace Khairi har yaushe zakiyi ta son wanda bai san kinayi ba? For God's sake he is married with two kids. Murmushin yake Khairi tayi tace Allah Kausar ban damu na zama ta hudu a gidansa ba. Ni tunda yace wa Umma shine mijina nake gina rayuwata dashi. Tun bansan so ba har na sani duk akansa. Kausar ta tabe baki to zan cigaba da taya ki addua idan ya dawo kasar hankalinsa ya dawo kanki. Allah Ya amsa Khairi tace sannan suka fara karatu.
********************
A falo ta hadu da Malam yana ta rubuce rubuce ga Qur'ani da sahihul muslim a gabansa yana kokarin hada khudbar juma'a ya turo glasses dinsa can karshen hanci. Tsugunawa tayi ta tura masa shi ciki sannan tace Malam ya aiki? Lafiya kalau ya bata amsa yana murmushi Ummulkhair kin mayar dani kakanki ko? Tace to idan babu kaka ai da uba ake yi. Ajiye biron hannunsa yayi yace tun jiya nake aikawa kizo kina wasan buya dani. Keya ta sosa to ai nasan dalilin kiran. Umma wadda ta shigo falon lokacin tace to sarkin zance meye dalilin. Shiru tayi ta sunkuyar da kanta kasa Malam yace zauna ayi maganar a gabanki Munnira.
Ya ce to a ajiye wasa a gefe Ummulkhair ina zancen miji ya kwana? Na baki dama ki fitar da miji amma abin mamaki duk yadda ake zuwa samuna akan maganarki har yau babu wanda kika amince dashi. Umma tace to ai Malam irinsu Khairi ba'a basu wannan damar ko cikin almajiranka kawai ka bawa daya. Almajiri kuna Umma? Khairi ta fada tana zaro idanu sannan tacewa Malam ya kara mat lokaci. Ni dai ba haka naso don a yadda na tsara kina gama secondary zan aurar dake amma tunda hakan bai samu ba gaskiya bana son ki cika shekara 23 a gabana. Alh Mahe yazo dazu kina makaranta akan maganarki da dansa Tahir kuma na amince. Gabanta ne yayi mummunan faduwa
********************
Kuka take a daki Inno tana ta bata hakuri Khairi tace Inno ta yaya zan fada musu Uncle Ahmad nake so? Inno ta cigaba da share mata hawaye kiyi hakuri 'yata da yardar Allah komai zai zo da sauki. Yau kwana hudu da maganar nan amma baki da aiki sai kuka? Ina baki shawara da kada ki taba bijirewa Malam domin sabawa mahaifi ba karamin hatsari gareshi ba.
A daidai wannan lokacin Dr Ahmad ke saukowa daga jirgi shi da matarsa Mufida da yaransa guda biyu bayan shekaru uku da yaje yayi wani course a kasar Singapore.
Taku Batul Mamman ce
π MEYE DALILINKA π 3
Ko da wasa babu wanda ta bari ya san sirrin dake boye a ranta daga Inno sai aminiyarta Kausar Mukhtar wadda makota suke tun suna yara. Tare suka yi secondary sai kuma suka nemi course daya a jami'ar Bayero. Khairi da Kausar wadanda kawayensu ke kira da 2K basa boyewa juna komai. Tsayinsu kusan daya sannan dukkansu suna da matsakaicin haske. Khairi akwai kyau kuma akwai fara'a idan ka cire lokutan da take tunanin Uncle Ahmad da wuya ka ganta fuskar nan babu murmushi. Da kuruciya dai anyi fitina yanzu da ake ji da 'yan matanci kuwa nutsuwa ta danzo musamman da take 'yar daya taga cikin malaman da ake ji dasu a kano Dr Abdallah Saraki. Sai dai ba'a raba ta da tsokana da tara shirgi a dakinta. Ummulkhairi Abdallah Saraki.
Ta gama kukanta na yamma yau saura na darw kamar yadda ta tsarawa kanta kullum tunda Malam yayi mata zancen Tahir. Idar da sallar ishan takeda wuya Inno ta shigo dakin da sauri har tana tuntube da takalman da Khairi ta cire a bakin kofar daki. Albishirinki 'yata ta fada tana wangale baki. Goro Inno ta amsa mata a sanyaye. Inno tace tunda naga kamar ban burgeki ba to kije falon Malam ana kira. Dammm taji gabanta ya fadi. Har tasa hijab wanda ya dace da kayan jikinta sai ta fasa ta jawo wani a kayan wanki ya gama yamutsewa ga manjan wainar filawar da suka ci ita da Kausar a gidan Lami makociyarsu. Tasa ta fita idan Tahir ne tasan dole ya ce ya fasa. Yau kazanta zata yi mata rana ta fada a ranta tana murmushin mugunta.
Qamshi ne mai dadi ya bugi hancin Khairi tana daga labule suka hada ido. Yarrr taji a jikinta kamar wuta ta ja ta. Ta bude baki galala tana kallosa...wallahi ya kara kyau da haduwa ta fada a ranta. A zahiri kuwa ta kasa magana tana karasa shigowa ya mike kamar an mintsine shi. Kada ki karaso wurin nan ya fada yana mata wani irin kallo. Umma ma cewa tayi Khairi meye wannan? Sai a lokacin ta kula da umman ta. Tace Umma me kika gani? Uncle Ahmad yayi tsaki ni duk na zata zanzo naga kina ji da gayu kin girma ashe kina nan a Khairin kazanta. Subhanallahi ta fada sannan ta koma ciki da gudu. Ba komai bane illah hijab din korar Tahir da ta saka sai dai tana dawowa falon Umma tace ya tafi gida domin dare yayi dazu jirginsu ya sauka.
Da wani kukan ta koma daki tana share kwalla taga bakuwar number na kiranta. Tana dauka bayan tayi sallama taji muryar dake sanyaya mata zuciya. Khairi ya kira sunanta (kai sunan ma daban yake a bakin Uncle ta fada a zuci). Naam Uncle shine ka tafi kafin na dawo ko? To ai kece kanwata ina ta dokin surprising dinki shiyasa ban fada miki ma zamu dawo ba kawai sai na ganki kamar anyi wasan kura dake. Murmushi tayi ai na zata Tahir din da Malam yace zai aura min ne yazo. Yanzu dai a bar maganar hijab mai datti don yanzu na zama yar gayu. Ina Anti Mufida da su Sadiq? Lafiya kalau suke ya bata amsa. Gobe kizo ku hadu dasu Umaima ku taya Mufida gyaran gida zan turo azo daukarki da safe nasan sunday ne ba school.
Ranar Khairi bacci mai dadi tayi harda mafarki ta haifawa Uncle Ahmad yan biyu. Gari na wayewa ta kira Kausar a waya ta bata kyakkyawan labari. Suna ta shirmen murna domin kuwa dai ba'asan suna yi ba. Kafin takwas na safe ta gama shiryawa taje ta gaishe da itayenta. Malam ya kalli Umma yace yau lafiya kuwa Ummulkhair take? Ina wucewa naji tana share dakinta. Umma tace ai tun jiya Ahmad yace zai turo a dauketa shine take ta doki.
Abincin ma da kyar taci tana ta kallon agogo shi kuwa driver din gidan Alh Aliyu wanda wan mahaifin Khairi ne baizo ba sai 9:30. Kafin yazo kuwa ta kira Umaima da Ummi yafi a kirga su gane mata ko ya taho. Hijab dinta yau light blue ne kamar atampar jikinta. Ba wata kwalliya sosai tayi ba tunda Malam bazai yarda da hakan ba amma ta tabbatar tayi fes yadda Uncle zaiji dadi.
4rm Batul Mamman
π MEYE DALILINKA π 4
Gidan Baba Aliyu ya wuce da ita suka dauki Umaima suka wuce sabon gidan Uncle Ahmad a unguwar 'yan kaba. Mufida tayi farinciki da ganin su tare suka hadu da kannenta suka share gidan tunda kafin su dawo an riga an gama jeren komai.
Baba Aliyu shine babba a gidansu, Malam ke binsa sai Hashim wanda ya gamu da lalurar paralysis sakamakon fadowa da yayi daga bene shekaru 35 da suka wuce. Baba babban dan kasuwa ne yana da mata biyu da Hajiya Karima wadda ake kira Hajiya shekararsu 5 da aure sannan ta haifi Ahmad daga shi bata sake haihuwa ba. Sai Hajiya Zainab wadda ya aura daga baya ta haifi Amina, Rahma, Umaima da Hashim. Suna kiranta da Momi. Suna zaune ne tare da matar babansu Yakumbo. Ita bata taba haihuwa ba amma ko da iyayensu suka rasu ta kula dasu sosai musamman Baba Karami wato Hashim wanda ya gamu da lalura. Haj Zainab amaryar Baba 'yar kanwar Yakumbo ce.
********************
Khairi tana yiwa Umma tsifa Inno ta shigo cike da fara'a tace Hajiya yanzu mai gadi yace na sanar ana sallama da 'yata. Shiru tayi kamar bata ji me akace ba sai da Umma tace Khairi bazaki tashi bane? To sakar min kaina ta fada tana kokarin daura dankwalinta. Tashi Khairi rayi taje ta dauko hijab ta saka. Tana dawowa falon Umma tace kije falon bakin Malam ki same shi. Tahir ne wanda an sanar dake babansa ya yi magana.
Sallama tayi ta shiga falon hannunta da tray wanda ke dauke da juice, ruwa da meat pie. Bayan ta ajiye masa a kan centre table ta sami kujera can nesa da shi ta zauna ta hade fuska ita kada ma ya kawo mata wargi. Yanayin Khairi dariya ya bawa Tahir amma sai ya gintse yace mun wuni lafiya? Lafiya ta bashi amsa a dakile.
Haka suka zauna suna kallon kallo. Tahir yana karanta wata journal da ya gani a kan kujera ita kuwa Khairi waya ta dauko tana dannawa.
Kusan mintuna 15 suna haka daya gaji da shirun ya ajiye jaridar ya dubeta. Ina fata Malam ya sanar dake dalilin zuwana. Gyada kai tayi kamar kadangare, a ransa yace lallai ina da aiki. Ya cigaba da magana kamar yadda aka sanar dake suna na Tahir, ina aiki da Nigerian airways ni pilot ne. Ina da yayye uku da kanne biyar. Ina fata wannan ya isheki for now, uhm kawai tace. Ganin bata da niyyar magana yasa shi mikewa har ya kusa bakin kofa yace oh ni wane laifi na yiwa Alhaji ya rasa matar da zai nema min aurenta sai bebiya. Kafin ta bashi amsa har ya fice.
*******************
Kwanan Tahir hudu da zuwa Khairi ko zancensa bata so taji anyi a gidansu. Kausar kuwa ta sami abinyi kullum sai ta tsokane ta. Ta kusa gama karatun da take na bayan sallar isha Indo jikar Inno ta leko tace Umma tace kizo inji Tahir.
Ai tuni ta kara karatun, bayan kamar minti goma Umma da kanta tazo cikin fada tace bana son wulakanci Khairi, ganin karatun dai take yi tayi wata 'yar dariya tace haba Khairi ai ko ban fada miki ba kinsan karatunki babu lada don kuwa babu niyya ki tashi tun ranki bai baci ba. Yace sallama yazo yi miki zaiyi tafiya yau. Ko da ta dago kanta idonta cike yake da hawaye. Ta yaya zata fahimtar da iyayenta akwai wanda ta riga ta mallakawa zuciyarta?
Batul Mammanπ
π MEYE DALILINKA π 5
Saroro Umma ta tsaya tana kallonta. Khairi ko dai aljanun ne dake da gaske? Daga magana sai hawaye, to daure kije ki dawo kizo muyi magana kinji 'yar Umma. Share hawayen tayi ta fita Umma ta bita da ido. Bari Malam ya dawo dole asan abin yi.
Yauma sallama tayi a hankali ta shiga falon. A tsaye ta tarad da shi yana sanye da kayansa na matukan jirgi. Sunyi masa kyau don sai yau ma ta kalle shi sosai. Dogo ne sosai don yafi Uncle Ahmad tsayi,kalar fari ne amma har yafi Uncle din nata kai kila ma zabiya ne ban kula ba. Gashi yana da kyau amma dai Uncle ya fi shi. Duk wannan zancen zuci Khairi take shi kuwa Captain Tahir kallonta kawai yake. Ko ba komai tana da kyau kuma 'yar Malamin da yake matukar jindadin tafsirinsa ce. Littafin aljihunsa ya dauko mai suna Sign Language ya dan duba wani page sai yayi mata alama da hannu. Dariya ce ta kwace mata ganin yadda ya dage yana ta motsa hannuwansa. Sai da ta gama tace idan ka gama excercise din ka fada min. Shima dariyar yayi yace ai na zata bebiyar gaske ce.
Kafin ta sake magana Uncle Ahmad ya daga labulen falon ya shigo da sallamarsa rike da ledoji biyu a hannunsa. Gaban Khairi har faduwa yayi da ta ganshi tayi saurin mikewa tsoronta kada ganin Tahir yasa kara lalata chance din ya gabatar mata da soyayyarsa. Su biyun sun mika wa juna hannu sun gaisa Uncle yace Khairi shine baki fada min zanyi inlaw ba. Ya juya ga Tahir gaskiya nayi murna dana ganka Allah Ya tabbatar da alkhairi sai kayi a hankali kanwar tawa akwai kiriniya bata san ta girma ba. Tahir mikewa yayi yace to babban yaya ni zan gudu dama a hanya nake idan Allah Ya dawo damu lafiya zan nemeka. Allah Ya tsare ya fada sannan yace ni sunana Ahmad shi kuma yace Tahir.
Tare suka fita daga falon Khairi ta koma ta zauna tana tunane tunane har Uncle ya dawo. Ga tsarabarki ta Singapore ya fada yana mika mata ledojin hannunsa. Ko dago kai bata yi ba sai alamar sheshshekar kuka yaji. Khairi me ya sameki ko kukan rabuwa da masoyi kike yi? Kamar ya kara zugata ta sake bare baki tana kukan ta mike ta fita daga falon yana kiranta bata amsa ba.
Su Umma ma haka ta wuce su. Uncle Ahmad na fitowa Inno tace masa lafiya? Nima daga na fita raka bakonta ta dawo na tarar tana kuka. Kila ko don zai tafi ne. Inno ta girgiza kai anya kuwa? Yau ne fa zuwansa na biyu, akwai abinda ke damun yarinyar nan. Umma wadda ita kanta abin ya fara damunta tace ka fara tambayarta Ahmad idan abin ya faskara zan sanar da Malam.
*******************
Tun ranar da ya ga wannan kukan Ahmad ya rasa sukuni. It is so unlike Khairi ta bar abu a ranta har ya sata kuka. Duk cikin kannensa yafi shaquwa da ita kuma bata boye masa komai amma wannan karon yayi yayi taki magana. Bayan ya gama ganin last patient dinsa na yau ya yanke shawarar ya sami Malam suyi magana idan bata son Tahir abar zancen. Bazai iya jure rashin walwalar Khairi ba.
Kausar tana ta ban baki da rarrashin kawarta tace Kausar son Uncle ya zame min cuta. Zuciyata kamar zata fashe nake ji tunda ya dawo abin ya karu. Ko kinsan yanzu har waya suke da Tahir tunda ya dawo daga tafiyar da yayi kwanaki sun dinke kamar wasu abokan da suka dade. Kausar gama kwasar tuwon da take tace to Khairi idan abin nan bazaki iya hakura ba why not ki sanar da uncle Ahmad din. Kai bazan iya ba idan har bai fahimta don kansa ba shikenan.
*******************
Kwance yake yana kallon kyakkyawan hatonta a wayarsa. Hakika Jalilah taci amanarsa. Ita din mai kyau ce kuma tasan tana da kyan. Sati uku ya rage ayi bikinsu Yayanta yazo har gida ya dawo musu da kudinsu da kayan lefe wai ta fasa. Ya jima yana maimaita abinnan a ransa yaje gidansu kuma taki fitowa. Sati ukun na cika yaji sanarwar aurenta a kafafen yada labarai da Senator Bukar Danbuba. Wannan dalilin yasa ya tsorata da lamarin mata domin iyakar so Jalilah ta nuna masa na shekara ukun da suka yi tare. Shiyasa ya dena neman kowacce mace sai yanzu da Alhajinsu ya nemar masa Khairi. Sai dai yarinyar ta zame masa kamar karatun littafin da baa ganewa. Abu daya ya sani shine tun ranar da ya fara zuwa ta shiga ransa
Batul Mammanπ
π MEYE DALILINKA π 6
Khairi ta duka tana kokarin turawa Malam glasses dinsa Umma ta kallesu tace ni cikinku bansan wanda yafi wani ba, kullum ka turo glass gaba zata mayar maka ciki amma baka fasa turowa. Ke kuma kinsan ko kin tura masa ciki gobe ma zai kara amma ba kya gajiya. khairi ta zauna kusa da Malam tace aini ina jin dadin turawar shima Malam yace inayi ne kawai don jin dadin Ummulkhairi na. Suna cikin dariya suka ji sallamar Uncle Ahmad da Mufida tare da yaransu.
A take taji jikinta ya fara rawa. Ina zata kai son Uncle? Yanzu abin har ya kai tayi loosing composure dinta idan yana kusa?
Sun gaisa da kowa sai dai ta kula da yadda Mufida ta dan daure fuska amma bata kawo komai a ranta ba don tasan ba soyayya take da Uncle ba. Uncle da Malam sun koma daya falon inda Uncle Ahmad ke yi masa bayanin abinda ya kawo shi. Murmushi malam yayi irin na manya yace to Ahmad mai kanwa munyi magana da kanwar taka sai tace min ranar haka nan ta tashi da bacin rai. Na fada mata ta rinka azkar safe da yamma. Ya cigaba da cewa Ummulkhairi ta gama girman da zata yi a gida kuma nasan iyaka abinda Allah Ya hore mana mun bata tarbiya abinda ya rage kawai aure ne. Ina fata Tahir ya zama mijinta. Ahmad ya gamsu da maganar Malam kuma a yadda ya fahimci Tahir yana ganin kamar mutumin kirki ne.
********************
Ajin tun daga waje ake jin hayaniya kasancewar babu malami. Kausar