Share this page
tura masa ta WhatsApp. Bayan ya koma yakira haneefah yake sanar da isowarsa tace na tura maka sako ka bude ka gani. Idonsane suka sauka kan hotunan, sun matukar yin kyau, ya tsaya wani kan rika da siket da bata da gele.. zubawa surar jikinta ido yayi ko giftawa baya yi. Lallai haneefah shiyasa kullum kike cikin hijabi. Farin ciki da godiyarsa ya nuna gareta, sannan addu'a Allah mallaka musu juna. Dariya tayi tace ai nazama taka, fatiya da shaidu muke jira. Shima dariyar yayi yace Allah nuna mana *Dr HANEEFAH* 👩🏼18 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Tun daga wannan lokaci alaqarsu ta dada nunkuwa, kullum kowa so yake ya faranta ran junan su. Anje har adamawa ansa ranar aure rahma nan da wata daya. Murna gurin umma nusaiba ba'a magana, sai dada hura kunnen yar tata take da hudubar banza, ita ko rahma burin magaifiyarta zai kaita gidan ba zaman har abada ba. Su haneefah an koma makaranta amarya hadiza ma ta fito. Haneefah ke tsokanarta har tagaji. Hadiza tace nidai bazaki ji komai abakina ba zaki gani da idonki in lokacin ki yazo. Haneefah ta kawar da kanta ta danne zuciyarta kan auren yusuf, domin ta fahimci damuwar ta itace tashi, ita ko batason bacin ransa. Ita yanzu karatu tasa agaba, domin cike burin mahaifanta da mosoyinta. Bangaren nana ma bata samun wata matsala abangaren karatun ta. Sai dai muce Allah basu ikon cimma burinsu. Biki yazo momy sai shirye-shirye, shiko yusuf baisanma suna yiba. Kayan lefema momy ce ta hada, sannan rahma ta da meshi kan occation, shidai yace babu ruwansa haka ta hakura. An daura aure amma ko ango bai halarci wannan aure ba. Momy tace ya aiko kudin jirgi a wuce da amarya rashin son gardama yace a kawo ta kano side nashi inyaso inya gama gyaran gidanshi sai suzo abuja. Haka ko akai, aka kawo amarya kano. Haneefah har wata daya yayi yusuf baice an daura auren ba, hakan yasa taja bakinta rayi shiru. ***** ***** ***** Bayan wata biyu amarya na jiran ango bata sashi a ido ba amma yakan kiranta su gaisa. Momy ma in sukai waya yace zaizo, so yake in yazo ya koma da ita, hakan yasa ta saurara mishi. Haneefah ko saura wata shida ta kammala makaranta, a sannan ta bukaci tafiya gidan aunty muhibbat domin cikinta ya tsufa. Yau lahadi suna gida. Haneefah ta gama shara tana mopping sai yaron aunty muhibbat yazo da gudu tsantsi ya dauke shi kadan ya rage ya fadi yace auucchhh! Aunty haneefah badan kin rike niba da na fadi... tseye tayi tana kallonshi, bismillah zaka ce in kazo fadiwa ko wani abu daban? Mu haka muka saba fada! Muhibbat dake jinsu tace bari haneefah babu yadda da su ba amma sunki dainawa. Haneefah tace waya ce tun farko ki koya musu? Zakiga yaro shekaranshi shida amma baisan banbancin wuta da aljanna ba! Don ki tsoratarshi in kikace wuta bai sani ba sai spider man, wlh gomma ku farka, ya zamto yara su tashi da dabi'a ta addinin musulunci ba dabi'an wasu ba. Aunty muhibbat tace toh malama sakita cika ni da surutu. Gaskiyace saina fada.... jin sautin wayarta ta jefarda mop ta wuce amsar kiran masoyinta domin sautin shima daban ne Sallama tayi suka gaisa, yace zaki iya fitowa da safennan ina kofar gida. Mamakine ya cika ta tace yaushe kazo? Jirgi na biyo. Ok ina gidan aunty muhibbat, saika karaso ta katse wayar. Bandaki tashiga ta watsa ruwa ta fito. Tsaf ta gama shiri yakirata tace ya shigo . Zaune tasame shi a falo, taga ya canza mata yadan rame. Ta zauna nesa dashi, suka kara gaisawa yace inason ganin kine shiyasa na biyo jirgin safe nanda awa daya zan koma. Murmushi tayi tace nagode da ziyara nima kamar kasan kewar ka nake, ka wuce gida? Aa, mesa? Banason zuwa. Shiru tayi tana ganinsa bata ce komai ba. Kasa hakura tayi tace meke damun ka? Me kika gani? Ka rame sosai. Ya kalleta yace aure suka min, ina bin yadda zan sauke hakkin wannan aure, banasonta, na jure amma ko ganinta banason yi. Narasa me zanyi, tun 6years back nace bana so amma sai da akamin, gashi yana son halakani. Duk zafin kishinta amma ta tausaya mishi. Tasowa tayi yazo kujeran da ke fuskantar shi tace haba yusuf bansan ka da haka ba. Da ilmin ka kada ka soma daukan halayen jahilai. Saboda soyayya bazaka sauke nawin da ya rataya a wuyar kaba? Haba ka dadayin hakuri insha Allah wata rana sai labari, yaushe akayi auren ? Kuna tare? Aa ya bata amsa, tana gidanmu, anyi auren watanni biyu da suka wuce. Zaro ido tayi sosai tace ai zaka bata lamarin mu. Cikin rashin fahimta yace wani lamari? Taya kake tunanin momy zata amince da auren mu in kana yiwa diyarta haka? Rufamin asiri ban shirya rabuwa da kaiba. Dariya ya soma jin yadda take maganan. Murmushi tayi tace inaso ka kasance fiye da daa, ka kwantar da hankalin ka. Allah sa hakan shine mafi alkhairi agare ka. Maza kaje gida ka gaishesu pls, ran momy da amarya zai baci, shiru yayi. Kaji ango ya bata rai. Ta soma dariya tana cewa jama'a kuzo kutayi shari'a amarya batayi fishin kishi ba ango yana fishi. Dariya ya soma. Nan haneefah ta fara zolayarshi yanata dariya har ya manta bacin rai dake tattare dashi. A hankali take kallonsa yadda yake dariya cikin nutsuwa tace zanso ka kasance cikin farin ciki har karshen rayuwarka koda bana tare dakai. Shiru shima yana kallonta yace kece farin cikina... zatai magana taga agogon dake manne jikin bango tace ai lokacin tashin naka yayi, ya mike itama ta mike domin yi masa rakiya. A hankali take binsu a baya har suka iso bakin titi, haneefah ta tsayar da mai adaidaita sahu yusuf ya shiga sannan ta koma. Ganin haka yasa momy tabi bayan a dai daita sahun daya shiga har taga inda ya tsaya wato airport. Juyawa tayi ranta abace tana kissima hukuncin da zata yankewa yusuf da wadda tagansu karo na biyu dashi *Dr HANEEFAH* 👩🏼19 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Tafiya take amma tunanin yusuf take da auran shi har ta iso gida. Aunty muhibbat ta iske a falo take tambayarta har ya tafi? Haneefah ta amsa da eh. Shiru tayi ta samu guri ta zauna tana tunani, aunty muhibbat ta kura mata ido tace meya faru? Haneefah ta dago ido cike da hawaye tace yayi aure! Ta bata labarin yadda abin yake da yadda suka rabu, ta qara da cewa wallahi ni yanzu shi nafi tausayawa baki ga yadda ya canza ba duk yabi ya dami kanshi. Aunty muhibbat tace Allah sa haka shine mafi alkhairi agare ku, sannan yanzu lokacine da zaki dada janshi a jiki kibasa kulawa ta musamman, duk da kuna son juna wasu mazan in suka dandani zumar amaryansu zasu manta da wata a waje, ki kwantar da hankalin ki sannan lokacine da zaki dage da addu'a kan wannan lamari. Haneefah da tuni ta fara hawaye tace wlh yusuf bazai iya rabuwa dani ba, ni matar shi ce, shi mijinane, we belong to each other..... cike da dariya aunty muhibbat ta katseta da cewa mai da wukar hajiya, an daura muku aure shaidu muke jira. Haneefah tace kullum haka yake cewa, makaranta muke jira na kammala. Ta tashi ta qarasa ayyukanta na cikin gida, tayi girki ta koma daki ta dauko qur'ani tana karantawa har aka kira sallah azahar. Bayan ta idar aunty muhibbat tace yaushe kikai alwala da har zaki tashi kiyi sallah? Aini da alwala nake zama. Aunty muhibbat tace duk surutun da kikai dazu alwalan ki bai karye ba? Haneefah tace wayace surutu yana karya alwala? Abubuwan da suke karya alwala shine; yin iska, yin bayi, fisari, suma, nauyayyan bacci, kiss da sauran su... amma banji yadda surutu ke karya alwala ba, sai dai in mutum baya iya rike najasar da zata fito masa daga jiki misali in mutum baya iya rike iska, sannan in yana hira baisan sanda zayyi ba to wannan rike alwala bazayyu masa ba saboda lalurarsa. *SAKAMAKO (LADAN) ZAMA DA ALWALA* Daga Abdullahi Ibn Buraidah daga Babansa Allah shi kara masu yarda yace: Watarana da safe Manzon Allah SAW ya kira Bilal RA da me ka rigayeni a Aljannah, na shiga Aljannah sai naji karar takalminka a gaba na, sai Bilal yace Ya Manzon Allah SAW da dai ban sanni da wani abu ba sama da yin Sallah rakao'i biyu kuma dazarar alwala ta warware nike sabuntawa, sai Manzon Allah SAW yace itace. [ Ibn Khuzaima ] Ko shakka babu zama da alwala na kare bawa daga sihiri in sha Allah. Ya Allah ka azurtamu da kasancewa cikin alwala a tsawon rayuwarmu ameen. Suna cikin tattaunawa yusuf yakirata ya sanar mata sun sauka lafiya amma ta dadana nuna mishi rashin jin dadin baije gida ba. Ko sauraron ta bayyi ba ya katse wayar. **** Kwance take tana fuskantar kofar shigowa daki, gidan da wadda suke ciki baki daya sun fice mata arai. Tunanin barin gidan take. Tasan a baya tana son yusuf amma yanzu gaba ki daya ya fice mata arai tun kafin auren su, inba dan mum ba ai wannan wulakanci ne. Ace yau watanta kusan uku bata sashi a ido ba... zan bar gidannan amma nayi alkawari bazaka auri zabin ka ba ko wacece ita. Wayarta taji yana ringing ta daga hello mum ina kwana. Daga daya bangaren tace ya kike baby? Lafiya lau mum, mum nagaji da gidannan wlh nifa banyi tsammanin burin ki zai cika ba. Mum tace wai har yanzu ba ciki ne ko kinje scan suka ce macece? Takaicine ya kama rahma tace mum tun da nazo gidannan ban sashi a ido ba bale maganar ciki ni gaskiya nagaji. Cikin rarrashi tace kada ki damu namiki alkawarin zuwa gobe zai dawo, yanzu zan kira yaya in sanar da ita. Bata kira amsar taba ta katse wayar. Momy na office tana ayyuka kiran yar uwarta ya shiga. Bayan sun gaisa mum tace haba yaya, ni nayi tunanin rahma zata fi samun kwanciyar hankali yasa na baku ita amma gashi har yau wata uku bata sa mijinta a ido ba? Nidai nayi mamaki, tunda abin yazama haka gobe zanzo in tafi da ita. Tana kaiwa nan ta katse wayar. Momy ta rasa mezatayi, wato rahma har ta sanar da mamarta. Kiran umma nusaiba tayi tace haba nusaiba, kinsan ni maison kwanciyar hankalin zuri'ar ki ne. Ki zauna kada ki dawo, nasan yadda zan bullowa al'amarin. Bayan sunyi sallama takira yusuf tace lallai yabiyo jirgin yamma yazo kada ya kuskura ya kwana a abuja. Ya amsa mata da insha Allah zaizo. Cike da faduwar gaba ya iso ya sameta zaune a falo. Ko gaisuwarsa bata amsa ba zata fara magana yayi saurin cewa momy dan Allah kiyi hakuri, nasan na bata miki rai amma na miki alkawarin hakan bazai kuma faruwa ba. Shiru tayi tana kallonsa bata ce komai ba tace shikenan tashi ka tafi. Duk da yasan ba cira yayi ba amma yana addu'an Allah sa ta sassauta masa. Rahma tana kwance a falo tana kallo ya shigo da sallama. Ko kallonsa bata yi ba bale ta amsa. Jin shiru bai fito ba yasa ta bishi. Waya yake da haneefah idanunsa a lumshe da alama yana jin dadin wayar. Kare masa kallo tayi tsaf sannan taja dogon saki ta fice. Haneefah tace next month fa zamu shiga last semester. Tsaban dadin jin maganarta baisan sanda ya mike ba yace Allah dear? Wayyo mun kusa kasancewa tare. Murmushi tayi tace Allah kaimu rai da lfy. Nan suka soma hiran yadda zasu tsara auren. Bayan sun kammala wayar yake tunanin yadda zai bullowa momy da maganar. *** *** *** Tun daga wannan lokaci kowani weekend yusuf zaizo kano amma babu abinda ya taba shiga tsakaninsa da rahma. Ita ko kallonsa bata kaunar yi bale ta kaiga su tsaya suyi hira. Haka shima baya shiga tsabgarta har tsawon wata biyu. Daga nan hankalinsa ya karkata kan auren sa da haneefah, yadda zai dauko da maganar. Yau lahadi dukkanin su suna gida. Ya shiga bangaren mahaifinsa domin gaishe shi ya tarar da momy. Bayan sun gaisa mahaifin nasa ya fahimci kamar da magana a bakin dan nasa yace yusuf kamar kana da abin cewa. Yace eh abba dama wadda muke tare ne tana shirin gama makaranta nan da watanni biyar shine nake son aje neman mun auren ta... Momy ce ta daka masa tsawan da yasashi yin shiru. Har kana da bakin cewa zaka kara aure? Yaushe kayi auren wlh yusuf ka kiyayeni kada kaga ina daga maka kafa. Abba yace tunda ke zaki daura masa auren saiki hana in gani. Tun da farko yana da wadda yake so amma kika dage sai ya aureta, saiki bari shima ya auri wadda yake so yusuf Allah tabbatar mana da abinda yafi alkhairi, anjima zan sami abokaina da sauran yan uwa insha Allah gobe zamu je nema maka aure, saika sanar da ita zasuyi baki. Cike da farin ciki ya amsa da toh ya tashi ya fice. Momy ma ficewa tayi ranta a bace ta nufi sashenta. Zama tayi bakin gado tana tunanin maganan mijinta. Alhaji sai dai kai hakuri amma wlh ko bayan raina yusuf bazayyi zaman aure da kowa ba sai rahma *Dr HANEEFAH* 👩🏼20 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Yusuf yana fita ya nufi sashin sa cikin sauri ya kira haneefah yana sanar da ita yadda sukai da abba, itama ta nuna farin cikinta. Da yamma ya dauki hanyar gurin aikinsa. Yasan momy na fishi dashi amma yasan yadda zai shawo kanta. Haneefah ta sanar da umma, umma ma taje ta sanar da abba. Kwarai sunyi farin ciki, a sannan abba ya sanar da dangi su biyu da makocinsa akan zuwan bakinsa. **** **** *** Su aunty muhibbat da humaira sune kan gaba wajen shirye shiryen taran baki. Inna ko lekowa bata yiba ita a yaranta sai tura jabir tayi ya kalle musu wani irin mutane zasu zo. Haneefah ko tana gidan aminiyarta hadiza anata ta hiran yadda auren zai kasance. Zaune momy take tana tunanin yadda zata bullowa lamarin. Rahma ta shigo ko sallama babu ido cike da hawayen munafurshi tace momy da gaskene yau yusuf za'akai kudin auren shi? Cike da tausayi momy tace zo diyata. Tazo ta zauna kusa da ita. Kada ma ki tada hankalinki namiki alkawarin ba'ai aurannan ba koda bana raye. Toh momy ki hana tafiyar mana! Murmushi momy tayi tace abbanku ya dage yanzu, zan kyale suje amma wallahi aure dai bazai aurota ba. Murmushin jin dadi rahma tayi ta tashi ta fice. Aisha dake sauraronsu tayi maza taja da baya ta koma inda ta fito. Sai data tabbatar rahma ta tafi itama ta fita ta nufi sashin su... a daki ta tarar tana waya kan ta gama rusa maganar auren yusuf. Ba shiri aisha ta koma daki ta zauna bakin gado. Wannan wani irin son kai momy take son aiwatar wa?? In aka rusa maganar auren yayanta shinya zai kasance? Tabbas tasan yadda yake son haneefah ! Tunani ta tsaya yi ta yadda zata nemi mafita. Inta sanar da yusuf hankalinsa zai dada tashi, bata isa ta tunkari momy ba domin yadda itama ta dau zafi, mafita shine Addua. Ta daga hannu sama tana rokon Allah ya duba musu wannan lamari. Yadda aka tarbesu sunji dadi sannan abba yabada haneefah ga yusuf, an bada sadaki ranar aure kuma wata biyar aka sa, dai-dai da gama maarantar ta da wata biyu kenan. Labari yaje kunnen masoya. Babu wadda yakai yusuf murna a wannan rana . Tun daga wannan rana ya fara irga ranar auren shi. Su inna bakin ciki sun rasa inda zasu shiga ganin yaron daga gidan masu hali yake. Abba da umma an fara shiri ba kamar umma ba, yadda take ji da haneefah. Haka sauran yan uwa dukkaninsu suna murna tare da Allah nuna musu wannan rana. ***** ****** ***** _BAYAN WATA BIYU_ Haneefah jinta take complete. Komai yazo mata dai-dai. Babban burinta takasance ta kammala karatu tana tare da abar kaunarta. Haka abin yake ga yusuf. Yana bawa rahma kulawa. Zaune take ta baje takardu tana hira. Taji wayarta na ringing taga matar Dr Mubarak na kiranta tace nashiga uku nidai bani da kirki. Ta daga cike da kunya tace dan Allah kiyi hakuri kullum inason kiranki Allah bai bani iko ba. Barrister ramlat tace ba komai haneefah kina lafiya? Lafiya lau, ya Dr da yara? Duk suna lafiya. Barrister tace dama nakira in sanar dake na haihu gobe suna amma dan Allah wannan karon kizo gidana. Haneefah tace Allah raya bisa tsarin addinin musulunci, zanyi kokori insha Allah inzo, yauwa haneefah nagode yanzu zan tura miki address din gidan nawa. Haneefah taje ta gayawa umma tace Allah kaimu goben sai kije . Washe gari haneefah ta tashi da matsanancin faduwar gaba, so biyu wannan abin ke faruwa mata. Na farko haduwarta da yusuf sai yanzu na biyu. Ko wanni abu zai faru Allahu a'alam. Suna waya da yusuf amma kwata-kwata jinta yake wani iri yace dearie lafiya? Haneefah ta bashi labarin abinda ke damunta. Shima yace abinda yake fama dashi. Cike da mamaki tace Allah sa da mu da alkhairi. Yanzu kina ina? Yusuf ya tambaya. Zanje anguwane. Ya dubi agogon hannun sa yace turomin address din gidan da zaki. Haneefah tace meza kai? Yace kedai turomin. Ta katse wayar ta tura masa. Yusuf dake aiki ya tattara kayan shi ya nufi gida. Bayan yagama shiri ya dauki mukullin mota ya dauki hanyar kano. Misalin karfe daya da rabi haneefah ta sauka bakin gate da ta tabbata shine gidan. Ta sallami mai a daidaita sahu ta tsaya tun daga bakin gate tana karewa gidan kallo tace mashaa Allah . Ta kira barrister tace ta iso. Duk da jama'an dake gidan hakan baisa ta fito ta dauki haneefah ba. A tare suka shigo ta zaunar da haneefah ta mika mata baby. Barister ta shigo da wata mata ta nuna mata haneefah. Suka karaso wannan mahaifiyata ce cewar barrister . Cike da ladabi haneefah ta gaisheta. Bayan sun gaisa tagabatar mata da sauran yan uwanta. Matuka haneefah taji dadin karrawa da sukai mata. Bayan awa biyu haneefah ta tashi tace zata tafi. Godiya suka mata har bakin gate suka rakata. Tana fita zata tari abin hawa taga motar yusuf. Cike da mamaki ta qarasa ta bude tashiga tace dama kana garine? Tun fitowarta ya kafa mata, tayi kyau sosai. Yace yanzu zuwana. Ya tada mota suka soma tafiya. Ganin ya dau hanyar gida tace zan biya gidan hadiza in amshi sako, ya nufi inda ta fada masa. Tuki yake ko magana bai mata ba har suka iso gidan yayi parking. Ta lura da fuskarsa a daure shiyasa ko magana batayi masa ba. Zata fita ya kulle motar. Ta juyo suka hada ido ganin idanunsa sun kada sunyi ja ga hawaye da ke kokarin taruwa a idonsa. Yace dearie bana jin dadin zuciya ta bansan meyake son faruwa dani ba. Kwarai ya bata tausayi yadda yake magana. Ta danne nata abinda take ji a zuciya tace babu abinda zai faru sai alkhairi, ka kwantar da hankalin ka. Babu abinda zai faru. Ciro wayarsa yayi yace kiyi hakuri abinda zan miki. Bata ce komai ba ya jawota kusa dashi kansu a hade ya dauke su a hoto kusan kala uku sannan ya dauketa ita daya. Karban wayan ta yayi ya tura mata hotunan da sukai da nashi shi daya. Abubuwan da yakene yasa ta fara zubar da hawaye. Ganin haka yasa yace pls dear kidaina haka kawai yau najini wani irine. Mika mata wayar yayi yace next year war haka kina dauke da babyn mu.... wayar ta amsa zata fita tace ni kabudemin kofa cikin shagwaba. Ya koikoyeta tasa dariya tace baka iya bama. Haka har suka mantar da junansu abinda suke ji yayi mata sallama kan anjima da dare zai dawo. Tana shiga gate din harta iso bakin falo zata shiga taji an bude ko fa. Wadda taganine yasa bugun zuciyarta ya tsananta wato mahaifiyar yusuf. *Dr HANEEFAH* 👩🏼21 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Tsananin fargaba da tsoro ya hana haneefah ko da taku daya. Ganin ta tabbatar momy ce ta sunkuyar da kanta kasa. Har kasa haneefah ta durkusa gaida momy, da fara'a ta amsa tare da cewa inason magana dake. Nan da nan zuciyar haneefah ke bugawa da sauri. Ta musu jagora zuwa ciki. Babu kowa a falon kuma tayi mamakin ganin falo a bude. Guri momy ta samu ta zauna, sannan ta karewa haneefah kallo. Yarinya qarama amma tana son birkita rayuwar familinta. Momy ta fara magana da cewa nasan kin sanni, ko da a hoto ne yusuf zai nuna ma ki ni amma niko bansan ki ba saida kika so raba kan dana sannan na nemi sanin wanene ke. Yanzu zuwan shi amma ko matarsa baije ya gani ba yazo inda kike. Toh inaso ki bude kunnen ki kiji abinda zance miki. Ina so kimin alkawarin abubuwa biyu: na farko ki janye aurenki da yusuf, na biyu ki fita arayuwarsa ma'ana ki yi nesa dashi inko ba haka ba zan tsine mishi, kinga ko bazai amfane ni ba nima bazai amfane niba... amma in kikamin alkawarorinnan biyu to tabbas masoyinki zai kasance cikin albarkana har tsawon rayuwarshi. Hadiza dake bacci taji alamun mutane ta tashi ta nufi falo. Abinda kunnuwanta suka jiye mata ne yasa ta qaraso da sauri ta durkusa gaban momy tace Dan Allah mama kiyi hakuri, wlh suna son juna. Haneefah tana da kirki bazata cutar miki zuria ba. Kada kira ba soyayyar da Allah ya hada. Momy ta miki tace nidai nagama magana, muddin tana so masoyinta ya gama da duniya lafiya toh tayi abinda nace tana kaiwa nan tayi ficewarta. Haneefah tunanin tane ya tsaya, ta nemi koda yawu abakinta ta rasa. Ta rasa tunanin me zata yi. Murya a dashe ta cewa hadiza ki tasheni a mafarkin da nake. Hadiza dake kuka ta qaraso gurinta ta rungumeta tace haneefah dan Allah na rokeki da girman Allah kada ki tada hankalin ki, ki dauka a matsayin kaddara ne ... bata qarasa ba taji wayar haneefah na ringing. Haneefah ce ta daga wayar tana kallon mai kiran. Tace yusuf ne hadiza a sannan ta tuno da kalamun momy. A tayi rejecting kiran, ya qara kira. A sannan haneefah ta fashe da matsanancin kuka. Kuka take kamar ranta zai fita. Hadiza na tayata. Kimanin mintuna arba'in suka dauka haka. Nan take haneefah ta tuno da nasihar yusuf: A matsayinka na musulmi, a koda yaushe, ka shiryawa zuwan kaddara da zata iya samunka, mai kyau ko marar kyau, ta alkhairi ko ta sharri. Idan ta alkhairi ta same ka, sai kayi godiya ga Allah, idan kuma ta sharri ce ta same ka, to sai kayi hakuri. wannan shi ne mataki, kuma matsayi na zama cikakken mumini. Sannan godiyarka da hakurinka akan nau'ikan kaddarori biyu da suka same ka, suke nuna cewa dukkanin al'amuranka alkhairi ne. Babu wanda ke samun wannan matsayin a cikin Musulmai sai Mumini. Wannan shi ne ma'anar fadin Annabi s.a.w. "Abin mamaki, abin sha'awa ga al'amarin mumini, hakika dukkanin al'amarin sa alkhairi ne, babu wanda ke samun haka sai mumini; idan abin farin ciki (alkhairi) ya same shi, sai yayi godiya (ga Allah), sai hakan ya zama alkhairi a gare shi, idan kuma abin bakin ciki (sharri) ya same shi, sai yayi hakuri, sai hakan ya zama alkhairi a gare shi ". Imamu muslim ne ya rawaito. Ya Allah kasa mu sifantu da wadannan sifofi na mumini. Allah kasa mu zama muminai. Haneefah ta qara fashewa da kuka tana mai ambaton Allah. Momy ko tana isowa gida ta nufi sashin su yusuf. Kwance ta same shi a falo yana tunanin meye dalilin rashin daga wayarsa da haneefah tayi. Ganin momy yasa ya tashi ya zauna. Bata amsa gaisuwar shiba tace inaso kaban aron hankalin ka. Da farko inaso ka janye maganar auren ka. Ba shiri yusuf ya dago kai

Chapter 5 of 19