Share this page
ido jin muryarta. Ta sake maimaita tambayar tare da cewa banaji fa.. shima a hankali ya furta DEARIE Idanuwanta ta bude baki daya jin muryar shi, ta nemi bacci ta rasa amma ta dake ta qara tambayar wanene? Murmushi yayi yace in hukunta ni zakiyi kada ki hukunta ni ta wannan fannin bazan iya jurewa ba. Wani irin farin ciki ke ratsa illahirin gabobin jikinta, kasa magana tayi ta lumshe ido tana sauraronsa. Jin yayi shiru yasa ta fashe da kuka Hankalinsa ya soma tashiwa yana tambayarta meya faru? Lallashin duniyar nan yayi amma taki shiru, ganin hakan yasa ya soma bata hakuri amma nan ma taki shiru, da kanta ta katse wayar ta kashe baki daya tana murmushin jin dadi. Shima hankalinsa a tashe tunaninsa baki daya ya karkata gari ya waye ya soma shirin tafiya amma wannan daren bai iya runtsawa ba farin ciki sosai yake tare da godewa Allah. Da safe dakyar ya kai karfe tara ya nufi gidan su Haneefah. A waje yayi parking yana kokarin fitowa yaga Ahmad da yaya jibril. Sallama ya fito yayi musu suka amsa. Bayan sun gaisa ne Ahmad ya mishi iso zuwa falon Abba shi ko jibril ya nufi gida sanar da Abba yayi bako domin gidansu ya kwana. Kasancewar su Amal sun fita yasa Ahmad da kanshi ya kawo masa ruwa tare da yiwa Umma magana dake shirin fita aiki. Har kasa ya sauko gaida Umma, Umma da fara'arta ta amsa tare da tambayar mutanen gida? Duk suna lafiya, ya qara da cewa Umma ina nemawa mahaifiyata afuwa.... bai karasa ba ta katseshi da cewa babu koma ya wuce, ai komai lokacine sai yanzu Allah ya nufa babu komai Allah hada zuciyarku ya baku zaman lafiya. Cike da murna ya amsa da ameen. Sukai sallama ta fita. Bai jima ba Abba ya shigo. Bayan sun gaisa ya dauko da maganar afuwa Abba ya masa nuni da komai ya wuce fatan zaman lafiya ya musu tare da yi masa nasihar akan rayuwa baki daya. Yusuf yaji dadin lafuzzan mahaifan Haneefah, hakan ya qara masa qimar Haneefah a idanunsa. Ya sanar da Abba yana son tafiya gurin Haneefah. Fatan tafiya lafiya da zuwa lafiya yayi mishi. Agurguje yaje gida ya tattara abin bukatarsa ya nufi Abuja daukan excuse gurin aikin shi. **** **** Zaune take tayi shiru ta zubawa takar dun gabanta ido, duk da irin karatun dake gabanta hakan bai hanata tunanin sa ba. Meya hanasa kiranta? Sau daya ta gwada kiransa amma bai daga wayarba. Raihana cikin tsokana tace an zama ma'aurata amma ana yawan tunani. Bata ce da ita komai ba ta dauki wayarta tayi dialing number shi amma bata samun sa. Ji tayi kamar ta jefar da wayar ta tarwa tse. Suna cikin haka wata balarabiya ta nufo su ta sanar dasu lectures suke dashi yanzu. Bayan ya sauka a airport batare da bata lokaci ba ya nema taxi domin yana da address dinta. Da murmushi ya nufo kofar ta ya danna qararrawa amma yaji shiru, ya dauki tsawon minti goma yana haka amma ya tabbatar babu kowa domin ba'a bude kofar ba. Nesa da gidan kadan yayi yanemi guri ya zauna yana kallon mutanen da suke zarya. Kusan karfe tara na dare babu alamarsu gashi gajiya da yunwa ta addabeshi, ruwa ya ciro cikin kayansa ya sha. Karfe tara da minti arba'in suka yi parking. Sunzo daidai zasu shiga Raihana ta ja ta tsaya ta hangosa yana bacci kasancewar gurin haskene tamkar rana. Haneefah ma ta tsaya tana kallon inda Raihana ke kallo, da sauri ta mika mata takardun hannunta ta nufo shi da sauri. A zaune yake ya lumshe ido tamkar mai bacci, tausayinsa taji ganin wahala tattare dashi a tunaninsa bacci ya soma. Tsugunowa tayi tana tunanin yadda zata tashi daga bacci, jin motsi yasa ya bude idanunsa a hankali yana kallonta. Da sauri ta mike zata juya shima ya mike da sauri ya fara binta amma yakasa cewa komai. Juyowa tayi tana kallonsa taga duk ya canza, hannayensa ta gano empty dan haka tace dashi ka shiga ina zuwa. Kasa motsawa yayi yana kallonta har tazo ta wuce ta nufi inda jakarsa take ta dauko ta nufi gida shima yana biye da ita. ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼63 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Basu tarar da Raihana a falo ba dan haka ta ajiye jakarsa ta nufi dakin da zata sauke shi ta shiga gyarawa. Bayan dakin yayi fes ta nufo falo amma ta kasa karasawa. Ta rasa me zata fara ce masa dan haka ta tsaya nesa da mashigan falo. Kusan mintuna goma tana tsaye taga Raihana ta fito. Ajiyar zuciya tayi tace pls inkin je falo ki mishi iso zuwa dakin shi Tsaye Raihana tayi tana kallonta tace nifa na dauka kuna daki, nemo ruwa na fito ashe ko masauki baki kai shiba kuma kinsan nisan Nigeria a London akwai gajiya.. Haneefah ta wuce ta shiga daki batare da tace mata komai ba a zuciyarta tana cewa ni nasan gajiyar da ya dauko amma bansan me zance dashi bane. Raihana tashigo falon da fara'arta tana cewa irin wannan zuwan bazata haka? Shima murmushi yayi baice komai ba yana ware idanu ko zai ganta. Tsaf Raihana ta gano shi ta tashi tace yazo masauki. Yana shiga ya lumshe ido yace ina kike? Shiga toilet yayi. Tunda tashiga daki ta kasa zaune sai zarya take. Tana jin budewar kofar Raihana tazo da sauri tace kin kaishi? Raihana har dariya abin yabata sannan ta amsa da eh, yana jiranki, sai..... Tun kafin ta karasa ta fita da sauri ta nufi kitchen. Cikin mintina kalilan ta dafa masa abinda zaisa abaki, ta hado masa da fruits ta aje kan try ta nufi dakin da yake. Duk da gabanta ba karamin faduwa yake ba amma yazama dole ta je inda yake domin bazata barshi da yunwa ba. Sallama tayi taji shiru, ta dauki kusan minti biyar tana sallama amma ba'a amsa ba. A hankali ta bude kofar ta shigo da sallama amma bata ga kowa ba, da sauri ta ajiye abinda ke hannunta ta fice a dakin. Tunda yaji sallamarta yake sauri amma kafin ya fito babu ta fice a dakin. Da sauri ya nufi inda try yake ya bude su, murmushi yayi ganin abinda ta kawo masa yace delicious!! Tunani tare da farin ciki ke ratsashi wai yau shine zaici abincin Haneefah a matsayin matarsa? Murmushi ya kuma yi ya tashi yayi sallah sannan ya zauna cin abinci. Rabonshi da yaci abinci ya koshi har ya mance amma yau har kari yake nema. Bayan ya kammala komai ya zauna tare da zubawa ko fa ido ko zata shigo amma shiru. Tam yasan bazata zo ba dan haka ya tashi ya lallaba ya kwanta domin bacci da yake ji. Itama haka abin yakasance agun nata, farin sosai tayi da ganinsa amma bazata iya komawa gurinsa ba domin tambayar kanta take me zata ce dashi? Ga murmushin jin dadi da baya yankewa a fuskarta. Raihana tace ni kada ki dame ni da wannan murmushi in zaki tashi ki tafi to, in ko so kike in bar muku gidan ne zan iya komawa hostel Da sauri Haneefah tace na daina yi hakuri, muyi karatun mu. Cike da farin ciki na musamman tayi karatun ta. Washe gari da safe ta tashi tayi breakfast sannan ta shirya domin fitan safe zasuyi. Bayan sun shirya ta dauki karamar ta karda tayi rubutu ta ajiye daidai kofar Yusuf tana murmushi suka fice. Tunda yaji tashiwar mota yadan suna suka fice, bai kawo komai aransa ba yaci gaba da kwanciyarsa sai kusan karfe goma ya tashi. Bayan yayi wanka ya shirya ya bude kofa ya fito domin zuwa kitchen. Yana bude kofa yaga karamar takarda an ajiye biro akai kada iska ya dauke shi. Saka hannu yayi ya dauka domin bazai wuce sakon sa bane yaga an rubutu: _Ina fata ka tashi lafiya? Ya gajiyar hanya? Nasan kana tattare da gajiya shiyasa banyi yunkurin bude maka kofa ba domin nasan kana bacci. Na fita makaranta breakfast naka na falo, a huta gajiya_ Murmushi yayi tare da kissing paper yace Allah dawo dake lafiya. Ya nufi falo ya tarar da lafiyayyun breaskfast ya soma ci. Bayan ya kammala ya tattara kayan ya tashi ya nufi kitchen. Zaga gidan yafara yana nazarin yadda akai ginin, gidan ya mishi kyau gashi ba babbane sosai. Bayan ya gama yazo ya kunna tv ya soma kallon news. Zaune suke suna karatu dayan uwanta amma hankalinta ya soma tafiya gida, ganin karfe daya yakamata ace sunje ta dafa masa lunch. Tun kafin tayi magana Raihana tace mu zamu wuce gida sai zuwa gobe. Daya daga cikinsu tace haba Raihana da wuri haka? Raihana tace daliline yasa, sukai sallama suka tashi. Bayan sun iso gida sukai parking Raihana ce agaba, da sallama ta shiga falo. Ganin Yusuf zaune yasa ta nufi inda yake da fara'arta tana gaisheshi. Shima gaisheta yayi yana tambayarta ya karatu? Tace Alhamdulillah. Yace Allah taimaka ya amsa da ameen. Suna dan taba hira Haneefah ta shigo da sallama, ta kasa kallon inda suke zaune tace wani kalma tayi wucewarta. Raihana baki bude take kallonta harta shige Yusuf yace inkin shiga ciki ki turomin ita. Tunda ta shiga taji kunya ya lullubeta, mesa nayi haka? Tana cikin tunani Raihana tashigo cike da mamaki tace Haneefah lafiyarki kuwa? Nifa nakasa gane kanki, keda kanki kike wahalar da kanki? Mutum yazo tun daga garin ku mai nisannan amma kinkasa ce masa ya yadawo? Koma menene kije yana kiran ki. Jin yana kiranta yasa taji babu dadi, maimakon ita taje ba sai ya nemeta ba. Jiki babu kwari ta nufi banda ki ta watsa ruwa ta fito ta shirya cikin mintuna kalilan ta fice ta nufi falo. Wayam ta gani bayanan, hakan na nufin yana dakin shi. Kamar zatayi kuka ta nufi dakin shi. Knocking daya tayi taga an bude mata kofa, da sallama ta shiga amma taji shiru. A hankali ta shigo dakin tare da maimaita sallama. Daga bayanta taji an amsa tare da rufe kofa. Da sauri ta juya tana kallonsa. Shima kallonta yake cike da tsananin so. Dukkaninsu sun kasa cewa junansu komai, a hankali ya tako yazo dab da ita, ganin haka yasa ta soma ja da baya. Tsayawa yayi yana kallonta yakacewa komai. Sulalewa tayi ta zauna kasa tana furta ina yini Baice da ita komai ba, ganin yayi shiru a hankali ta dago idanunta suka hada ido. Abinda taganine yasa gabanta ya fadi tare da mikewa. ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFA* 👩🏼64 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Hawayene cike a idanunsa wadda yake kokarin zubowa abinda bata taba gani ba. Bakinta na rawa tace meyafaru? Bani bace ko?? Da sauri ya matso kusa da ita tare da rike hannayenta yace na rokeki ki daina fushinnan, zan iya jure komai amma banda fishin ki, bani da laifi cikin al'amarin nan sannan in kika duba mahaifiyata ce bani da zabi da ya wuce inbi umarnin ta, amma badan raina ya so ba, ina sonki kina so na kada wannan abin yasa mu wahalar da kawunan mu bakisan yadda nake jiba lokacin da na rasaki amma yanzu Allah ya qara hadamu plss ki huce.... Kasa karasa maganan yayi ya lumshe ido sai ga hawayen dake makale ya zubo. Haneefah tsananin tashin hankali ya bayyana a fuskarta. Itama fashewa da kuka tayi zata gudu ta fita ya rikota. Tsayawa tayi tana kokarin fizge hannunta domin kukan yaci karfinta amma yaki sakinta dan kanta ta tsaya hakan taci gaba da kuka. A hankali ya janyota jikinsa ya rungumeta yana cewa shikenan tunda nine bakison gani nizan koma inda na fito. Cikin kuka tace a'a Yusuf yace toh me abin kuka? A hankali tace farin cikine yamin yawa amma ni ina sonka, ban taba kawo araina ina da sauran rayuwa tare dakai ba, yau gashi lokaci daya mun kasance tares. Alhamdulillah ya furta a hankali, nima ina sonki sosai Haneefah mukasance masu godewa Allah... kokarin kwace kanta take ya saketa yana kallonta tace lunch zanje in girka maka. Murmushi yayi yace akoshe nake domin jinki atare da ni... da sauri zata fita ya rikota a tsoroce ta tsaya domin da gaskenta tsoro take ji. Zagayowa yayi zuwa gabanta, ganin yadda ta sauke kai ya saketa yace jeki... tana fita yabi bayanta da murmushin jin dadi yana kara godewa Allah cikin zuciyarsa da ya azurtasa da abin kaunar sa wato Haneefah a matsayin mata. Kamar jiya abinci mai kyau ta dafa masa amma tsoron kaiwa take, ta dauki ita da Raihana ta wuce dakin su. Bayan takai tazo ta dauki nashi ta nufi dakin shi tayi knocking ya amsa ta shigo a hankali. Zata juya ta fita yace ina zaki? Ganin ta tsaya bata ce komai ba ya ta so da kansa yazo yace bazaki zauna muci tare ba? Nan ma tayi shiru ganin yana kokarin riketa ne tace a'a naka ne ni naci nawa. Ganinta a tsoroce yace toh zauna ki tayani hira. Rashin son jayayya yasa ta koma inda ta ajiye abinci ta fara zuba masa. Duk wani motsin ta akan idonshi, ji yake tamkar ya maido ta ciki amma ya lura kamar a tsorace take. Bayan ta gama ta samu guri ta zauna ta sunkuyar dakai domin jikinta ya bata idanunsa na kanta. Ya soma cikin abinci, yace yaushe exams naku? Next month ta bashi amsa. Farin ciki ya bayyana a fuskar shi yace ashe kun kusa. Tace eh amma zamuyi sati uku that's mean sai upper month zan gama. Yace good. Ya zakiyi da aikin ki? Bazanci gaba da aiki dasu ba, zan san yadda zamuyi mu rabu lafiya. Dauko wayarsa yayi ya nuna mata hoton kyakykyawar yarinya yace wannan itace diyar Aisha sunanta Ra'ima. Haneefah ta karba tana murmushi tace Allah raya ta ya amsa da ameen. Garin mika masa wayar ya tsanta ya taba wayar nan ya canza zuwa hoton sa rike da jariri. Nan da nan hawaye ya ciko a idanunta tace ya sunan babyn ka? Kallon hoton yayi yace ba nawa bane na salma ne, ni bani da yara amma inshaaww Allahu mun kusa samuwa ni da ke. Shiru tayi tana kallon hoton tace yaran Rahma nawa? Murmushi yayi yace har muka rabu bamu haihu ba. Cike da mamaki ta dako kai tana cewa rabuwa? Wacce kenan? Yace already tayi aure, tun shekaru uku da suka wuce. Mamakine ya cika Haneefah amma bata kuma cewa komai ba. Ya gama cin abinci ta soma tattarawa zata fita yace inkin kai ina son ganin ki. Kamar yadda ya bukaci ganinta ta shigo ta same shi zaune kan gado da alama yana jiran isowarta. Nesa dashi ta zauna a kasa. Murmushi yayi yace ta so ki zauna nan ya nuna mata kan gado. A hankali tazo ta zauna dan nesa dashi ta sunkuyar da kai. Yace Alahmdulillah, aduk abinda dan adam zayyi kada ya gajiya da godewa mahaliccinsa, yau gashi ni da ke mun kasance tare matsayin ma'aurata, burina ya cika arayuwa, bayan mun fidda rai a mallakan juna sai gashi yau mune abu daya, gaskiya bazan so nesa da ke ba amma zan baki daman karasa karatun ki in yaso nizan koma in soma shirin tarewar mu amma zan rika kawo miki ziyara immediately kina gama mkaranta sai mu kasance tare. Babu shiri Haneefah ta soma hawaye. Ganin haka Yusuf ya rikice yace menene? Bakya son na koma? Zan zauna it's ok stop crying. Haneefah tace ni dan Allah ka fahimce ni nasaba karatu ni daya, zanzo na kammala ni daya kuma inna koma gida ina son hutu kamin na tare gidan ka. Tsaf ya gano ta yace hutu kamar zuwa yaushe. Haneefah tace inna koma gida kamar 5-6months. Mikewa Yusuf yayi ya taso yazo kusa da ita yace in kyaleki ki gama makarnta ke kadai kuma in barki a gida wata biyar kina matsayin matata? Fashewa tayi da kuka tana gyada kai alamar eh. Yusuf yace ya salam! Shikenan naji hkan kika fi so hankalin ki zaifi kwanciya tace eh. Yace shikenan tare da mikewa yaje ya zauna wani bankare daban. Ganin haka yasa ta tashi ta fice a dakin, binta yayi da kallo azuciyarshi yana mai cewa nidai ba iyawa zanyi ba. Bayan ta koma daki ta tarar Raihana na bacci. Tajo plate na abinci ta soma ci tana murmushi. A zuciyarta tace ya Allah nagode maka, amma bansan mesa nake kunyarsa da yawa ba? Kwata-kwata na kasa sakin jiki dashi. Murmushi tayi data hango rashin amincewa a fuskarshi. A haka ta kara shi cin abinci ta zauna zuwa minti goma sha biyar tukun muke ta maida plate kitchen itama ta zo ta kwanta ta soma bacci. Sai bayan la'asar suka tashi. Saida sukai wanka domin samun karfin jiki sannan sukai sallah. Bayan sun idar suka zauna shiru domin kowa gajiya tattare dashi. Raihana ta dubi Haneefah tace ke bazaki je gun mijinki bane? Ko kallonta batai ba bale ta bata amsa. Raihana ta kuma cewa innine fa zan bar muku gidan. Nan ma bata ce komai ba ganin haka yasa itama tayi shiru da bakinta. Sai kuma suka dauko hiran karatu. *8:30pm* Dauke take da try, knocking daya aka bata izinin shigowa. Zaune ta samesa kan sallaya yana waya. Tana ajewa zata fita ya mata nuni da ta tsaya. Nesa dashi ta zauna ta sunkuyar da kai. Bayan ya kammala cike da nutsuwa ta gaishe shi. Amsawa yayi yana murmushi, baice komai ba ya zuba mata ido kamar mai nazarin wani abu. Ganin yayi shiru ta dago idanunta karaf suka hada tayi saurin sunkuyar da kanta. Allah-Allah take tayi sallama dashi batare da yayi mata komai ba.... tana cikin tunani taga ya ta so a inda yake ya nufo ta... ~Bintu Ramadan~ *Dr HANEEFAH* 👩🏼65 Dedicated to Batul Mamman (Mrs)💖 Ganin yazo dab da ita ta nannadu guri daya kamar taga wani abin, shi abin dariya ma ya bashi anan ya fahimci tsananin tsoro tattare da ita. A hankali yace Dr HANEEFAH! Duk da cike take da tsoro hakan bai hanata tsananin jin dadi yayin kiran sunanta ba, ji take tamkar shi kadai ya iya kira. A hankali ta dago kai amma ta kasa hada ido dashi. Yace shikenan ina tare da matata amma sai in tafi in barta, kimin adalci ki bari na ci gaba da zama dake hankalina zaifi kwanciya. A hankali tace ni fa banqi zaman ka ba, ayyu kan ka kuma ni karatuna.... ta karashe maganan cike da soma kukan shagwaba. Yace shikenan naji but nikam zan rika zuwa kuma tare zamu rika kwana da matata a daki daya.... tun kafin ya qarasa ta turo baki ta soma hawaye. Shiru yayi yana kallonta. Mikewa tayi ta soma zuba masa abinci, har gabansa ta kawo ta ajiye zata tashi ya jawota ta fada jikinsa. Riko sosai ya mata ya soma mata rada a kunne ina zakije? Nagaji da kwana ni daya yau da ke zan kwana. Lamo tayi jikinsa tace kamin afuwa mubar kasarnan kafin mukasance tare dakai daki daya, kada ka manta mu biyu ne a cikin gidannan, kuma karatuna yazo karshe kullum nake cikin karatu yanzu haka karatu Raihana take na barota, amma in kana son in kara maimaita shekara daya ne zanyi yadda kace amma bawai nima inason nesa dakai bane, inka sabarmin bazan iya ci gaba da karatu ba. Da gota yayi yana kallonta, tana dago idanunta yace mai wayo, na fahimce ki. Zan koma gida in soma mana shirin inda zamu zauna kema saiki karasa karatun ki amma kina gamawa a gidana zaki sauka... Zatayi magana ya rufe mata baki da nashi, dakyar ta kwaci kanta ta gudu tana cewa cikin zuciyarta saika kara ganina ai. Kamar yasan abinda take fadi ya fashe da dariya yace zanga yadda zakiyi in muka koma gida. Kwanan sa uku ya soma shirin tafiya domin gurin aikin sama na bukatar sa sosai sannan yana son yaje ya soma shirin inda zai saukar da amaryarsa, babu yadda zayyi domin Haneefah ta dage saiya koma gida. Har airport ta rako shi a motar ta, zata fita yayi saurin riko hannunta ta juyo suka hada ido, tayi saurin kawar da kanta domin duk sanda suka hada ido sai taji wani irin abu mara misaltuwa. A hankali yace ina sonki sosai Haneefah, pls take care of ur self. Murmushi tayi ganin yana matsowa tayi saurin fitowa ta zagaya ta zo ta bude mishi kofa. Qin fitowa yayi, ko kallon inda take bayyi ba. Zuwa tayi gabansa ta durkusa tare da kamo hannuwan sa tace nima inason ka sosai... da sauri yace naaqi ai ban karasa ba kika fito. Murmushi tayi tace kada kayi missing flight naka! Yace in baki komo mazaunin ki ba sai dai inta zama anan. Bata son musu domin zai aikata yasa ta tashi ta zagayo tashiga ta zauna tare da sunkuyo da kanta. A hankali yasa hannu ya dago fuskarta ya manna mata kiss a goshi sannan ya bude mota ya fito ya zagayo ya bude mata. Da murmushin jin dadi ta fito. A hankali suke taku har suka shiga sai taji kamar kada ya tafi, shima Yusuf daurewa yayi. Saida taga tashiwarsa sannan ta koma gida. Yinin ranar bataji dadi ba sai da taga kiransa ya koma gida lfy kafin ta runtsa ta samuyin bacci. Cikin taimakon Allah ya soma shirin sa, Abba ya dauki nawin duk wani irin gini yake bukata a birnin tarayya. Can gida kano ma aka fasa sashin Yusuf aka masa gyara sosai. Kowa na murna da bikin Engineer Yusuf da Dr Haneefah. **** **** A kwana a tashi ba wuya wajen Allah, a yau ake yaye daliban kiwon lafiya dake jami'ar Oxford university London. Kowa cike yake da farin cikin wannan rana musamman dalibai. Raihana tare take da mahaifanta sai yayanta, hannunta na cikin Haneefah domin kada ta ji wani irin yanayi amma duk dauriyar Haneefah sai da taji tana sha'awar ganin mahaifanta a wannan rana. Makaranta ta soma nuna farin cikinta a game da dalibai da suka nuna kwazo da sukai karatu kan gaskiya... sannan ta bukaci dalibai guda uku da suka cancanta yabo agun illahirin malamai da maarantar baki daya.... Haneefah da Raihana aka kira abinda basu taba tsammani ba duk da sunsan ana ji dasu a bangaren su amma basu dauka dukkanin makaranta na Alfahari dasu ba. A hankali suka taso suna tafiya har suka iso gaban taro, sai wani bature mai suna Felix. Sun samu kyaututtuka da dama har Haneefah ta kasa hakura ta soma kuka. Raihana na lallashin ta, aka bukaci kowa yazo dan uwanshi. Nan Haneefah tayi shiru, Felix matar shi ce ta fito, Raihana kuma yayanta har akazo kan Haneefah. Sun kuyar da kai tayi kamar daga sama taji muryar Ahmad. Da sauri ta dago kai tana kallon sa da mamaki. Bayan ya gama yazo gurinta da sauri tana farin ciki ta kama hannuwan sa tace Ahmad kaine? Yana dariya yace eh nine. Zata kuma magana taga Dr Mubarak shi da Bar. Ramlat. Daga bayansa kuma Umma da Abba sai Yusuf dake biye dasu. Tana hawaye tana murna, da gudu taje ta rungumi Umma tana kuka. Dakyar Umma ta dagota tana ya'isa haka Ahmad dake gefen Umma yace in bakiyi shiru ba zamu koma inda muka fito, dagowa tayi da sauri tana share hawayenta tace ashe zaku zo? Abba yace Umma da Ahmad kika sani ko? Haneefah tayi murmushi tace Abba banyi tsammanin zuwan ku ba, nan ta soma gaishe su. Suna gaisawa kafin tazo gun Yusuf Raihana ta iso itada mahaifanta suna gaida su Umma, Haneefah ta gabatar da iyayen Raihana ga su Umma. Bayan sun sami guri sun zauna da mintuna kalilan aka yaye su Haneefah daga makaranta. Bayan an kammala aka soma dauka hoto anan Haneefah tazo gaban Dr Mubarak da Bar. Tana cewa nagode sosai da gudunmuwarku a rayuwata, bani da bakin gode muku sai dai in tayaku da addu'a, nagode sosai... Bar. Tace babu komai Haneefah, Allah qara mana zumunci. Shiko Dr Mubarak bai iya cewa komai ba sai murmushi domin farin ciki sosai yake da karatun Haneefah. Suna gama dauka hotuna saura Yusuf, tsaye yake daga gefe yana kallon ta. A kunyace take kallonsa har ta karaso inda yake. Shiru tayi yana kallonta ya cije lebe yace zaki gamu dani ai. Yayi gaba ta bisa a baya tana dariya kasa-kasa. Bayan sun gama komai suka kamo hanyar zuwa gidan Haneefah tare da Raihana da yan uwanta. Suna shiga

Chapter 17 of 19