Share this page
8 / 8
ta je asibiti" gyaɗa kai ya yi kafin ya matsa min daga hanya ya ce"Je ki kai mata" fice wa na yi daga dakin ina jan ɗan tsakin na sauka ƙasa na tarar da Umaimah na miƙa mata na ce"Ga wannan Allah ya sa dai sun isa" wani kallo ta watsa min ta ce"Haba Sumayya ya za a yi 20k su ishe ni zuwa asibiti" da kallon mamaki nake bin ta galala nake kallon ta wannan shi ne a baka ɗauki ka tambaya wa ya gutsiri nan na ce"Iya abin da gare ni ne yanzu idan kin ga sun ishe ki to idan ba za su ishe ki sai ki bi wani alazin ki nemi ƙari ke ya dama" ina gama faɗar haka na juya zan tafi sai ga Mama da kallo take bin hannun Umaimah ta ce"Sumayya ni ina abin da na tambaye ki?" Wani haushin ta ne ya kama ni na ce"Sai gobe idan Allah ya kai mu Mama, sai na tafi office zan biya na siyo miki atanfar" gyada kai ta yi ta ce"To shi kenan Allah ya kai mu goben amman dan Allah kar a siyo atanfar ƙarama a siyo min manya" wani haushi ya kama ni na ce"To Mama Allah ya kai mu goben zan kawo manyan" Ɓangarena na koma na tarar Abdallah ba ya falon sai na shiga ɗakinsa, a zaune na tarar da shi na ce"Qalbi ka na bukatar wani abu?" Girgiza min kai ya yi alamar ba ya bukatar komai, sai na buɗe drower ɗinsa na fara haɗa kayan wanki sai ya ce"Kun yi waya da Mustapha?" Na girgiza kai na ce"A a ba mu yi ba" "Rumaissa fa?" Ya kuma watso min tambayar "Ita ma dai Rumy" ɓata fuska ya yi cike da damuwa ya ce"Bari na je gidan na ji ko lafiya" ya faɗa tare da ɗaukar key ɗin motarsa, sai da ya kai bakin kofa zai buɗe na ce"Ba sa ƙasar sun yi tafiya" turus ya ja birki ya tsaya yana watso min shanyayun idanunsa ya ce"Tsakanin ki da Allah Babe sai yanzu za ki faɗa min Mustapha ya yi tafiya?" "To ai ba ka tambaya ni ba, yanzu ma bakina na ne ya kufce na faɗa maka" a hankali ya tako zuwa bakin drower ya tsare ni da manyan idanunsa ya ce"Babe yaushe raini ya shiga tsakanin mu da ke?" Girgiza kai na yi cike da fargaba na ce" Ba fa raini ba ne Qalbi" cike da tsawa ya ce"To mene ne?" Shiru na yi ina kallon yatsun ƙafata ya ce"Na ga yanzu har da wasu maganganu kike faɗa min" "Qalbi ka yi hakuri ba zan sake ba in sha Allah" gyaɗa kai ya yi ya ce"Shi kenan kar ki sake" daga nan ya fita zuwa falo ni kuma na ci gaba da aikin da yake gabana. Washegari tun safe Umaimah ta shirya ta tafi asibiti gwajin farko likita ya shaida mata tana ɗauke da juna biyu tsawon wata biyu murna a wajen Umaimah ba a magana ko sauran gwaje-gwajen ma ba a gama ba ta fito ta tare mai napep sai gida. Tana shiga gida ta fara kwala kiran sunan Mama da gudu Mama ta fito daga ɗaki ta ce"Umaimah lafiya me yake faruwa kuma?" Da gudu ta je ta rungume Mama ta fara ihun murna, Mama kuwa baki ta saki tana kallon Umaimah tana jiran ta faɗa mata abin farin cikin da ya samu haka. "Mama, mun kusa samun ƙaruwa, ina da ciki" wata irin guɗa ta murna Mama ta rangaɗa wanda ya yi ya saka Jiddah da Rumana fitowa daga dakinsu suka yo falon Mama ta ce"Kai ma sha Allah alhamdulilah kai Allah shi ne abin godiya abin farin ciki ya same mu" Rumana ce ta ce"Me yake faruwa wa ya samu kujerar Makka?" Mama ce har tana haɗa kalmomi wajen faɗi "Ba fa kujerar Makka ba ce aka samu Umaimah ce ke ɗauke da juna biyu" ihun murna Rumana ta saka ta ce"Anty Umaimah congratulations na ta ya ki murna wannan abin farin cikin da ya same mu" ita ma jiddah ta ce"Allah ya raba lafiya Anty Umaimah Allah ya kai mu babbar rana mu sha shagali" zama suka yi suka shiga hira. ★Sumayya★ Duk da wayar da muka yi da Mama bai ishe ni ba sai na je super market na yi mata siyaya kafin na nemi izini a wajen Abdallah akan zan je gaishe da Mama bai ko yi musu ba ya amince min tare da cewa idan na je na gaishe da Mama. Kashe kiran na yi bayan mun yi sallama na ɗauki motata na nufi gidan Mama, isa ta gidan na tarar da ita a zaune mai aikinta na matsa mata ƙafa da murmushi akan fuskata na ce"Kande ba ki je hutu ba?" "E anty Sumayya ban je ba sai wani watan an tashi lafiya?" Ta faɗa tana kokarin miƙewa don kawo min drinks na ce"Lafiya qlau ya aikin?" Tana tafiya ta amsa min da lafiya qlau sai na juya na kalli Ummi na tsunguna na ce "Ummi barka da safiya" "Barka Sumayya babu aiki ne yau?" Zama na yi akan kujera na ce"A a Ummi akwai aiki na ce dai bari na zo na gaishe ki" "To kin zo, sai ki faɗa min abin da ya kawo ki" girgiza kaina na yi na ce"Babu komai Ummi kawai ina son ganin lafiyarki ne" wani kallo ta watso min ta ce"Sumayya ba ki damu da lafiyata ba, ba ki damu da farin cikina ba hakika da kin samu da ni ba za ki buɗewa wani layin banza ƙafa a titi ya ɓata miki rayuwa bayan kuma ba mijinki ba ne. Farin ciki ya yaye daga cikin zuciyata tun ranar da na yi ido biyu da wannan farin tissu ɗin babu ɗigon jinin budurcinki a jikinsa" idanuna sun fara zubar da hawaye tunda daga farkon maganarta cikin kuka na ce"Ummi ba abin da kike tunani ba ina son ki saurare ni don jin gaskiyar lamarin" hannu ta ɗaga min tana girgiza kai ta ce"Sumayya ki yi min shiru da bakinki me za ki faɗa min? Lokacin da ki ka yi yawon ta zubar ɗinki a kasar waje ko kuma ranar da ki ka rasa budurcinki? A ciki wane ne za ki sanar da ni tashi ki kwashe tsimokaran ƙafafunki ki bar min gida" Kamar yadda ta yi min umarni haka na tashi na bar falon ledar da na kawo mata ma sai mai gadi na ba ya shigo da ita. Driving nake hawaye yana rufe min idanu ba na ma ganin gabana Allah ne ya kawo gida lafiya sai da na yi parking ba saka wani tissu na goge hawayen da ya bata min fuska duk kwalin da na saka ya zubo min, na shiga gyara fuskata sai yanzu na tuna da ban siyo atanfar da Mama Sa'a ta ce na siyo ba. Wayata na ɗauka na kira number Rumaissa wadda ba ta Niger ba tana ɗagawa ta yi sallama ta ce"Hajiya Sumayya uwar princesse dan princesse ta yi missing ɗinki shi ne ki ka kira ki ji to ga ta nan cikin koshin lafiya" dan murmushin takaici na yi na ce"Ba ma ɗan ita na kira ba ina son ki saka daga shago a aiko min da atanfa turmi biyu" "Sai ki ce magana ake ta ƴaƴan banki, wace iri kike so?" "Ni kam ban sani ba Mama Sa'a ce za ta yi biki da su" "To shi kenan yanzu za a kawo sai dai ban ji kash ba" murmushi na yi ina tuna irin amanar da ke tsakanin Rumy da kuɗi na ce"To nawa ne kuɗin yanzu zan saka su" sallama muka yi kafin na shiga cikin gida zuciyata sai zafi take yi min Ina shiga cikin falon na yi kicibis da maganganu Mama Sa'a a daidai lokacin da muka haɗa ido da ita tana cewa..... *Abin ya zo in ji mai tsoron wanka, Hajiyata ki na son sanin abin da ke luluɓe a cikin wannan labarin ne? To hanzarta biyan kudin karatunki* Don jin shin laifi da Ummi take tuhumar Sumayya da shi mene ne dalili, shin Sumayya nada hujja ko a a? A cikin Sumayya da Abdallah wane ne mai matsalar haihuwa? Ya karshen Mama Sa'a zai kasance Na san za ku so sanin mene ne asalin hujjar kafuwar labarin akan kalmar *DA WATA KUSAN...* MU HAƊU A PAID PAGES +22780416252 An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 8 of 8