Share this page
3 / 8
ce miki aka yi haihuwar banza ne?" Girgiza kai na yi alamar a a sai ta kuma cewa "Don ba ki san zafi da radaɗin da ake ji tun daga daukar ciki har haihuwa ba ne shi ya sa za ki ce na bar shan magani na haihu, ko da yake ma ta ina za ki san ciwon haihuwar bayan kuma ko ɓatan wata ɗaya ba ki taɓa yi ba" kamar dirar wani mashi mai dafi na ji maganganun ƴar uwata a cikin zuciyata, idona taf da hawaye amman sai na yi saurin dakatar da su na ce"Haka ne kam, to ki bari ki huta kafin nan" tsaki ta ja ta ce"Haka kawai duk dawainiya ta yi maka yawa, zan je Dubai sarin kaya next week zan kawo miki Aisha ta yi miki kwana biyu ko ba komai Abdallah zai rage zafin rashin haihuwarki" gyaɗa kai na yi na ce"Allah ya kai mu sati mai zuwan" kitchen na tashi na shige a ɓoye na saka bayan hannuna na share hawayen da ya zubo min duk kokarin ɓoye su da nake yi amman a banza. Falon na koma na tarar da ita wannan karan tana waya zama na yi sai da ta ƙare kafin na ce"Less ɗin da na tura miki pics ɗinsu wancan watan sun ƙaraso?" "A a sai dai gobe za su iso amman fa sai kin ƙara 200k" "Ke Rumaisa ki ji tsoron Allah duk wannan uwar dibar" dariya ta yi ta ce"Matar Abdallah idan fa ba ki bani 200k wani zan siyar wa da su" girgiza kaina na yi ina mamakin hali irin na yar uwata na ce"To zan yi miki transfert amman sai an yi albashi" dariya ta yi ta ce"Ko ke fa Hajiyata na fi son haka ai" shiru na yi mata ban kuma amsa mata ba sai ta ce"Ina maganin da na turo miki last week ba ki ban labarin abin da ya faru ba, Abdallah ya yi ihun daɗin kamar yadda Mustapha ya yi?" Girgiza kai na yi ina mamakin wannan lamari babu abin da ya dame ta za ta yi iya yi min rahoton mu'amalar aurenta ko ɗan ɗigo ɗaya ba za ta manta ba ita wannan bai dame ta ba na ce"To ai ban yi anfani da shi ba" "Ke wallahi sake gare ki" dan murmsuhi na yi irin na ba za ki ji komai daga gare ni ba na ce"Ba sake ba ne lokaci ne ba mu samu ba" ido ta zaro ta ce"Ci gaba da zama ba za ki biya masa bukatarsa ya nemo wata sai ki huta" dariya na fashe da ita na ce"Rumaisa idan fa ta zo ba a kaina za ta zauna ba da halinta za ta zauna" tsaki ta ja a fili kafin ta ɗauki wayarta ta fara cire code ɗin ta ce"Nake ɓata raina a banza ma ni na manta da ba ki san ciwon kanki ba" tashi na yi daga kan kujerar da nake zaune na ce"To uwargidan Mustapha da ta san ciwon kanta bari na zubo miki abinci" "yi sauri kam don dama na yi missing ɗin girkinki" kitchen ɗin na nufa ina yi mata dariya sai dai kuma zuciya fal hawayen baƙin ciki ne ke zuba daga cikinta. *Cmnts nd share* [07/12 à 19:02] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW *DA WATA KUSAN...* NA Zouley Sabitou (Émilia) Daga marubuciyar *KUSKURE* ☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️ (Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation) GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUƊE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA. +22780416252 *Page 05* Falon na fito ɗauke da tray ɗin abinci na dire shi a gabanta, na shiga zuba mata kamshi ne ya daki hancinta kafin ta ce"Sumy kin samu wasu sabin spices da alamu?" Gyaɗa kai na ce"To Rumy ba dole ba, su fa maza sai a na kula da cikinsu" "E to kuma fa kin yi gaskiya gara ki riƙa yin girki mai daɗi da kamshi ko babu komai Abdallana ba zai ƙara miki kishiya ba" baki na saki ina kallon ta "Ke Rumy wai mene ne matsalarki da kishiya? mene ne abin da ta yi miki?" Zamanta ta gyara tana wani cin magani ta ce"Ni fa ba iya a kishiya matsalata take ba, duk wani wanda ya ce yana son abin da nake so sai inda karfina ya ƙare wajen daukar mataki" dariya na yi na ce"Allah ya shirye ki Rumy, Allah ya sa mai babban suna kar ta yi halinki" ido ta zaro ta ce"Wace ni ta yi halina ai wallahi sai dai irin halin juyar uwarta ko babu komai na san ba za ta sha wuya a duniya ba muddin ta yi irin halinki" kamar saukar aradu na ji zancenta sai dai kuma sanin wace ce Rumaisa sai kawai ban ɗauke shi a wani abu ba muka ci gaba da hira har yamma ta yi. "Shi Abdallana har na gaji da jiran shi bai zo ba ga yamma ta yi" na ce"Ikon Allah kenan dama zaman jiran Qalbi ki ke yi ba don ni ki ke zaune ba" ido ta zaro ta ce"Tab ke wa? Wannan ziyarar ai ta rabin rai ce" "yar rainin hankali ai da office za ki je ki tarar da shi ko" "kwantar da hankalinki tashi zan yi yanzu na tafi, idan na ganshi kin ga sai in ji daɗi zuwa gidana ko?" "Haka ne kam tashi ki tafi tun kafin dare ya yi miki" Hira muka ci gaba da yi har yamma lis kafin ta yi shirin tafiya, ƙasa na yi mata rakiya ba mu tarar da Mama Sa'a ba sai ta ce"Idan Mama Sa'a ta fito ki ce mata na tafi" da kai na amsa mata don duk abin da ya shafi Mama Sa'a tsoro yake bani ni kam don yanzu za ta yi maka wulaƙanci babu abin da ya dame ta. Sai da Rumaisa ta ɗauki motarta ta bar harabar gidan har zan juya sai kuma na ga mai gadi yana sake buɗe get da alamun Abdallah ne ya ƙaraso gidan. Tsayawa na yi jiran shi. ★ABDALLAH★ Tunda na bar office ɗin Sumayya raina ke yi min zafi, haƙiƙa a can baya ba ta taɓa nuna ƙyashin na yi wa wani daga cikin dangina hidima yau ne za ta fara kuma ma a kan mahaifiyata abu ne da ba zan lamunta ba a cikin gidana. Yau duk wuni ranar da wannan tunanin na wuni a cikin raina matakin da zan ɗauka a kan ta amman da na yi nazari sai na ga rashin jin daɗin da na nuna mata tun a office ɗinta ma kaɗai ya isa ta gane kuma ba za ta kuma ƙara tafka wannan Kuskuren ba, Sumayya ta kasance mutum ce da ba ta da matsala ko kaɗan a rayuwarta da ka yi mata nuni da Kuskurenta ba za ta ƙara aikata irin shi ba wannan na ɗaya daga cikin dalilin da ya sa nake ƙara kaunar ta a cikin raina. Ko da na je office ɗinta ba ta nan handle ɗin kofar na kama na ji a rufe, a raina kuma sai nake tunanin ina ta je ba ta sanar da ni ba. Motata na dauka na nufi gida. Daidai bakin get na haɗu da Rumaisa, glass ɗin motar na sauke na ce"Uwargidan Mustapha barka da wannan lokaci" murmsuhi ta yi ta ce"Ban gane uwar gida ba kar dai ka ce min ɗan uwanka aure zai ƙara?" Hannu na tafa kamar yadda mata ke yi na ce"Tabdi kar ki ce min ba ki sani ba" girgiza kanta ta yi alamar ba ta sani ba na ce"To kuwa idan kika je gida ki tambaye shi" "wata tambaya, da na je zan ce ya bani takardar saki , kuma sai na ce mishi ai kai ka ce min ya yi amarya" dariya na yi wannan karon domin kowa ya san halin Rumaisa na kishi akan abin da take so ko a gaban waye kuwa babu ruwanta tsaf za ta nuna kishinta, kuma kan abin da take so sai dai karfinta ya ƙare sai na ce"Kai mistake ne fa na yi, ina son cewa uwar gida kuma amaryar Mustapha ai daga ke babu ƙari" sai yanzu ta yi murmushi ta ce"Yanzu kam hankalina ya kwanta" gaisawa muka yi kafin ta tafi ni ma na figi motata sai cikin gida. Ina gama parking da sanyin idanuna na yi tozali, motar na kashe na fito, da gudu ta ƙaraso ta rungume ni a kunne ta raɗa min "oyoyo Qalbi" wani irin sanyi ne yake ratsa ni a duk lokacin da na ji muryarta tana kira na da wannan sunan. Wayar hannuna ta amsa kafin ta zare makulin motar daga jikin motar. Sai da na ƙare mata kallo kafin na ja hannunta zuwa cikin gida. Kai tsaye bangarenmu na yi wa tsinke don yau ko zuwa gaishe da Mama ban yi ba. A kan kujera na zaunar da ita kafin na haɗa hannayenta guda biyu na riƙe su game a nawa hannun na ce"Babe" ɗago idanunta ta yi ta sauke su a kan fuskata na ci gaba da cewa"Me yake damun ki? Ina hango damuwa a cikin kwayar idon ki" girgiza kai ta yi ta ce"Babu abin da yake damuna" "Babe kar ki fara ɓoye min damuwar ki , ina son ki sanar min abin da yake cikin ranki kin ji matata" ta buɗe baki da niyyar ta yi magana Mama ta turo ƙofar ta shigo falon ta ce"To hamshakiya, ɗan nawa ma ba za a bari da ya dawo daga office ya fara tozali da mahaifiyarsa ya kwashi albarka ta ba, an wani jawo shi an shigo ɗaki da shi za a fara yi mishi zanen ƙarya da gaskiya ko?" Ɗago kaina na yi na kalli Mama na ce"Ba laifinta ba ne, ni na bukaci na fara jin matsalarta kafin na je na gaishe ki" ido Mama ta zaro ta ce"Babu shakka an wanke an zuba ma a baki ka sha ko?" Ta ƙasan idon nake bin Sumayya da kallo wadda har yanzu ba ta ce uffan ba, tamkar wata yar tsana haka take zaune a wajen Mama ce ta ci gaba da cewa. "Tashi to mu je ɗakina don ina son ganin ka" gyaɗa kai na yi na ce"To bari na watsa ruwa sai na zo" "yanzu nake da bukatar ganin ka idan kuma ban isa ba sai mu gani" tashi na yi ba dan raina ya so ba na fice daga falon Mama na biye da bayana. ★SUMAYYA★ Fashewa na yi da kuka zuciyata kamar za ta fasa kirjina ta fito haka nake jin zafi rana zafi inuwa ƙuna ba ni da wani madogara face Sarkin sarakai Ubangijin da ya halicce ni. Ina zan saka kaina ga baƙin cikin dangin miji akan abin da ba ni na ɗaura wa kaina ba, babu wanda zai saurare ni bare kuma har na samu mafita. A wajen na ci gaba da kukana ina tunanin mafita, mahaifiya da ke zama bango, babban jigo a rayuwar ƴaƴanta ni tawa fushi take da ni babu ruwanta da lamurana idan zan shekara goma ina sanar da ita damuwata babu abin da ya dame ta da matsalar da nake ciki. Ta yi fushi da ni ta ɗauki karan tsanar duniya ta ɗaura min bayan ba ni da laifi, ba yin kaina ba ne son mijina da son ɓoye sirrin aurena su ne suka jawo min duk abin da ke faruwa da ni a halin yanzu. Ban san lokacin da barci ya ɗauke ni a wajen ba sai buɗe idona na yi na tsinci kaina a tsakiyar gadona duk da na san aikin Abdallah ne. Haka na tashi na yi wanka na ɗaura alwala na yi sallolin da suke kaina ban gushe a wajen ina rokon Ubangijin samai ya kawo min mafita a rayuwata ya kawo min haske kafin na koma gare shi. Yau kam da wani irin ciwon kai na tashi wanda na daɗe ban yi irin shi sai yau shi ya sa na nema wa kaina salama ko office ɗin ma ban tarki zuwa ba. A nan kan tapis na ci gaba da kwanciyata ban san iya adadin lokacin da na ɗauka a wajen ba a kwance sai da na ji kamar ana shafa gashin kaina. Ido na buɗe na sauke su a kan Abdallah murmushi ya sakar min ya ce"Baiwar Allah duk barci ne har yanzu" tashi zaune na yi na fara ƙare mishi kallo na ce"Karfe nawa ne yanzu" don har ya shirya tsaf a cikin suit ɗinshi don zuwa office. "Karfe takwas fa har da rabi" dafe goshina na yi na ce"Ya Allah, bari na haɗa maka ko da ruwan tea ne ka sha kar ka fita haka ba ka ci komai" girgiza min kai ya yi ya ce"Ki bari kawai tunda dai kin makara idan na je office na yi oder abin da zan ci, ko na je cantine" girgiza kaina na yi na ce"Don Allah ka yi hakuri wallahi kawai barcin ne ya fi karfina" "Babu komai Babe, tashi ki shirya mu tafi ko" girgiza kaina na yi na ce"Ba zan iya ba kaina ke ciwo idan ka je ka ce da secrétaire ɗina ta turo min aikin da zan yi yau ta email" gyaɗa kai ya yi ya ce"Tashi to ki sha ko tea ne sai ki sha magani" "Zan sha ba yanzu ba sai zuwa an jima" miƙe wa ya yi ya ce"To ni zan tafi idan ba ki ji sauki ba ki kira ni sai na kai ki asibiti" da kai na amsa mishi kafin ya ja kofar ya fice daga ɗakin. Ni kuwa kan bed na koma na dasa sabon barci wanda sai da karfe goma ta yi na tashi, yanzu kam na ji sauƙin ciwon kan sai kawai na shiga toilet na yi wanka na canza kaya sai kuma a lokacin nake jin wata irin yunwa. Ba na son na sauka ƙasa na haɗu da Mama Sa'a sai na shiga kitchen ɗina neman abin da zan saka a cikina amman babu, dole uwar na ƙi na nufi ƙasa. Na yi sa'a ba ta falon har da murna na nufi kitchen na soya kwai da dankalin turawa kafin na haɗa tea mai kauri na jera a plate na ɗauko su don zuwa ɗakina. Ina shigo falon sai na hangi mutane biyu mata a zaune na gaishe su ban tsaya ba na ci gaba da tafiya don isa ɗakina. Sai na ji murya Mama Sa'a tana kira na ajiye plate kan ɗan tebur da ke karshen falon na yi sai na juya na koma cikin falon na ce"Mama ga ni" taɓe baki ta yi ta ce"ba ki ga baƙi ba ne?" Girgiza kai na yi na ce"Mama na gansu" "ba su kai matsayin da za ki gaishe su ba kenan, saboda ba ki samu tarbiyya mai kyau ba ko?" Ƙasa na yi da kaina cike da jin kunya na ce "Mama ai na gaishe su lokacin ba ƙƴa nan ne" hannunta ta shiga tafawa ta ce"Yanzu kuma ina magana ki na magana?" Ɗaya daga cikin matan da ke zaune ce ta ce"Haba dan Allah Sa'a ki rabu da ita mana ai ta gaishe mu" ɗayar kuma ta ce"Wace ce wannan ɗin Sa'a?" murmushi Mama ta yi ta ce"Ai matar Abdallah ce, kuma juya ce ba ta haihuwa" salati matar ta saki ta ce kuma ki ka ci gaba da zama da ita, ai kawai ko Abdallah ya sake ta ko kuma ki mutu ba ki ga jikokinki da za su fito daga tsatson Abdallah ba" shiru Mama Sa'a ta yi alamar tana nazari sai ta ce"Kuma fa kin yi gaskiya, zan san abin yi kuwa, ke tashi ki bar wa mutane falon" ban jira ta sake fadar wata magana ba na ɗauki kwanon abincina na haura sama. Ina hawaye domin tun da na zo duniya ba a taɓa yi min irin wulaƙanci da Mama Sa'a ta yi min yau ba. *Cmnts nd share* [08/12 à 22:45] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW *DA WATA KUSAN...* NA Zouley Sabitou (Émilia) Daga marubuciyar *KUSKURE* ☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️ (Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation) GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUƊE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA. +22780416252 *Page 06* Ina komawa ɗakina ko da wasa ban sake gigin sauko wa ƙasa don gudun abin da zai je ya dawo sai kawai na yi zamana a ɗakina. Har yanzu Ban ji sauƙin ciwon kan da ke damuna ba wayata na ɗauka na kira likitan da ke kula da duk wanda bashi da lafiya a Companymu, ban so kiran Abdallah dan kar na ɗaga masa hankali. Ko da ya ɗaga kiran cikin mutunta juna muka gaisa. "Madame Abdallah lafiya dai ko ?" Kamar yana gabana yana kallona na girgiza kai na ce"Docteur wallahi da wani irin ciwon kai na tashi kuma har yanzu da na sha magani bai daina" shiru ya yi yana ɗan nazari kafin ya ce"Iya ciwon kai ne?" Na amsa masa da "shi kaɗai ne" "Kawai défense ne kike yi, ki cire duk wata damuwa a ranki sannan ki kwanta ki huta zuwa gobe idan ba ki ji sauki zan zo Company na duba ki" godiya na yi mishi tare sallama na kashe wayar. Kamar yadda ya ce na yi haka kuwa na yi rage gudun ac falona na yi na dauko pilow daga ɗakin na kwanta a kan kapet. Kamar daga sama na ji ana kiran sunana buɗe idona na yi na sauke su tas a kan jiddah. Ina shirin yin magana ta ce"Mama tana kiran ki" daga nan ta juya ta fice ta bar falon. Tashi na yi na wanke idona kafin na sauka ƙasa don amsa kiran Mama Sa'a, ina zuwa na lura da matan ɗazu har yanzu ba su tafi ba sai na je kusa da Mama na ce"Mama gani" wani kallon sama da ƙasa ta yi min kafin ta ce"Ba shakka kin samu duniya Sumayya, ke yanzu har damar barci ki ka samu ko?" Girgiza kaina na yi na ce"Ba na jin daɗi ne" wata uwar harara ta jefo min kafin ta ce"Yaushe rabon ki da ki yi jini" Wata irin kunya ce ta kama ni tamkar kasa ta buɗe na shige ciki nake ji, na ma rasa abin da zance saboda ban shirya jin irin wannan tambayar daga gare ta ba. Ko mahaifiyata zan ji kunyar wannan tambayar daga gare ta bare kuma uwar mijina. "Haba Sa'a wannan wace irin tambaya ce haka?" Daya daga cikin kawayen Mama Sa'a ta faɗa. "Ba fa wani abu ba ne Larai, kawai don na tabbatar ko ciki gare ta" Mama Sa'a ta bata amsa cikin halin ko in kula don ita fa ba ta ga wani laifin tambayarta ba. Ɗayar matar ce ta ce"Ke ma dai Sa'a da son saka kai uku kike to ai wannan tunda dai tun farko ba ta haihu ba, ba fa yanzu ba ne za ta ɗauki ciki har ta haihu. Idan ma kin shirya neman mafita gara ki nema idan kuma ba haka ba ki zauna ki ci gaba da kallon ruwa har kwaɗo ya yi miki ƙafa" Wannan cin mutuncin da me ya yi kama shiru dai na yi ina kallon su domin lamarin nan ya wuce tunanina sai na tsinkayo muryar Mama Sa'a daga cikin duniyar tunanina tana cewa "Kin wani yi min kikam a ka, je ki ɗaura mana girki saboda rana ta fara" duk da ba ni ke girkin rana ba a gidan amman wannan dama da Mama Sa'a ta bani ta barin fakon har sai da na sauke ajiyar zuciya da sauri na juya har doguwar rigar da ke jikina tana faman harɗe ni na nufi kitchen ɗin. Sumayya na barin falon Larai ta ce"Maganar gaskiya Sa'a wannan abin da kike yi wa ƴar mutane ba yi ba ne don Allah idan ba ta haihu ba laifin na waye, Allah da ya baki haihuwar shi ne dai ita ma zai hore mata, amman ki saka ta gaba ki na yi mata cin kashi har a gaban baki idan ki ka yi ba abin kirki ba ne, kar ki manta ki na da ƴaƴa mata kuma ita ma ba don mahaifiyarta ba ta son ta ba, kamar yadda kike son naki bakya son ayi musu irin wannan cin kashi to ita ma ki daina yi mata" Baki galala su Mama suka buɗe suna kallon Larai kafin Mama ta ce"To fa Larai ai dole ki kare ta don ke ɗin ma da kaɗan ki ka fi juya. Don ɗa ɗaya ki ka haifa a shekara biyar da aure" da mamaki Larai take kallon Mama ta ce"Babbar magana yaro ya tsinci hakorin babansa ke yanzu tsakani da Allah ni ce yau za ki yi wa gori daga na faɗa miki gaskiya. Kar ki damu ba zan faɗi a ƙasa kamar ki ba amman a juri zuwa rafi watarana dole tulu zai fashe" tana gama kai wa nan ta dauki mayafinta ta nufi kofar falon. Ɗayar matar ce ta ce"Haba Larai ai ba za a yi haka ba dawo ku sasanta" banza Larai ta yi mata ta fice daga gidan. Tsaki Mama ta ja ta ce"Aikin banza kawai, to ita ina ruwanta ma da lamarin nan ni dai na ga ba maganar ɗanta ake yi ba" Ita ma kawarta shiru ta yi da bakinta don ta ga Mama ba ta son ana yi mata kutse a cikin lamarunta. Ina shiga kitchen na saka bayan hannuna na share hawayena daidai mai aiki gidan ta shigo don ɗaura girki ta ce"Hajiya yau ba ki je office ba" gyaɗa mata kai na yi sai ta ce"Me za a dafa yau?" Girgiza kaina na yi alamar ban sani ba sai kuma na ce"Jiya me aka dafa?" Amsa ta bani sai na ce"To ɗauko doya ki fere min" Sai da na gama girkin tas na jera a dinning na je falon na ce"Mama na gama girkin" ba ta ko kalle ni ba ta ce"Allah ya sa dai ba ki cika min gishiri ba" girgiza kai na yi na ce"A a Mama ban cika ba" gyaɗa kai ta yi ta ce"Sai ki bani waje ai" ban jira wani abu ba na bar falon ko abincin ban zuba ba na koma ɗakina. Wayata na tarar tana ringin na ɗaga tare da sallama Rumaisa ta ce"Ke malama a yi ta kiran ki amman a banza" dan guntun murmushi na yi saboda Rumaisa kullum cikin mita take ban san ya Mustapha ke iya zama da ita ba na ce"Baiwar Allah ina kitchen ina girki ne" "Tab ai da na san ba ki je office ba da na zo na ci abincinki mai daɗi" "Yanzu ma ai dare bai yi miki ba" dariya ta yi ta ce"Dare ya yi min yanzu kam sai dai ki girka dîner da rabona zan turo Mustapha ya amsar min" "To babu damuwa Allah ya kai mu daren lafiya" "Dama mai delivry ne zan ba kayanki shi ne na ce bari na ji ki na office ko gida" "Ina gida kam yau ki aiko shi kawai" daga nan muka yi sallama na ɗauko laptop dina na fara duba sakon email ɗin da sakatariyata ta turo min. ★Mama Sa'a★ Bayan Sumayya ta bar falon na ce"Balki mu je mu ci abinci ko?" Tashi muka yi muka nufi dinning ɗin sai na tura mai aikina ta kira su Rumana. "Tabdi wannan abincin ai daɗin ya yi yawa idan ka biye wa daɗin ai ba za ka koshi ba" Balki ta faɗa tana mai kai loma bakinta. Dariya na yi amman ban ce komai ba saboda a rayuwata ina son jin an yaba abin da ya fito daga gare ni. "To gaskiya Sa'a wannan yarinyar ta iya girki maganar gaskiya kar ki yi sake da ita domin wannan daɗin haka ai da wuya a yaran zamanin nan ka samu wanda ya iya girki kamar ita" murmsuhi na yi na ce"Balki ki daina wannan santi ki ci abinci" kamar an yi ruwa an ɗauke kuwa ya ja bakinta ta yi gum ta ci gaba da cin abincinta, wanda ni kaina

Chapter 3 of 8