Share this page
1 / 8
An dauko wannan littafi daga shafin https://taskarnovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://taskarnovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://taskarnovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://taskarnovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.taskarnovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [05/12 à 16:45] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9QNbIdKW *DA WATA KUSAN...* NA Zouley Sabitou (Émilia) Daga marubuciyar *KUSKURE* ☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️ (Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation) GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUƊE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA. +22780252 05/12/2024 *Page 01* Inalilahi wa ina ilaihi raju'un! Na sake maimaitawa a karo na ba adadi, radaɗin da nake ji a cikin zuciyata ya girmi tunanin duk mai tunani. Idanuna na rufe kwala na ci gaba da yi min tsiyaya kamar ana ruwa da bakin ƙwarya. Ganin dai zaman ba yi min zai yi ba sai na tashi na shige toilet ɗin ɗakina na sake yin wani wanka domin zafin da zuciyata ke yi irin shi sai nake ji a jikina. Ina fitowa daga wanka na shiga zaɓar kayan da zan saka tuni kuma na share hawayena na aro jarumtar duniya da wani kayatacen murmushi na ɗaura akan fuskata. Ta baya na ji an rungume ni sai na ture hannun na ce"Qalbi kaya nake sakawa" juyo da ni ya yi ya ce"An ki a saka kayan" murmushi na yi mishi na ce"Haba nawan a yi min afuwa na saka ko da riga ce" na faɗa ina haɗawa da yar shagwaɓa wadda na riga na san tun ba yau ba tana tafiya da duk wata nutsuwarshi. Saki na ya yi kamar dai yadda na sani Ni kuwa na dauki riga ta na saka na shafa mai na ce"Qalbi office fa?" Girgiza kai ya yi ya ce" Yau fa ba zan je ba" gyara tsayuwata na yi a daidai lokacin da na gama gyara rolling ɗin babban mayafina na ce "To Qalbi ni kam zan tafi idan ka gama hutun ka same ni a can" bai amsa min ba wannan ya bani tabbacin yau yan miskilancin sun motsa sai na ɗauki key din motata da Jakata na fice daga ɗakin. Ƙasa na sauka na tarar da ahalin gidan na fama yin breakfast sai na karasa na gaishe da iyayen har ƙasa amsa min suka yi kafin na fice zuwa office. Ina ba falon baya Mama Sa'a ta ja tsaki ta ce"A haka kuma a ce ana neman aljanna, ko mijinka ba ka damu da shi ba bare kuma ka tsaya kula da shi sai yawon gantalin zuwa office" dariya Rumana ta yi ta ce"Ke ma Mama da wani zance to ba sai mutum ya sami tarbiyya ba zai san mene ne hakkin miji ba" caraf Jidda ta amshe zancen da cewa"kar fa ku manta yar mace ce a ina za ta sami tarbiyya bayan ba su da uba" haka suka yi ta cirawa suna mayarwa har suka gama cin abincinsu. Sai da suka gama ne masu aiki suka shiga kwashe kayan abincin kafin Abdallah ya sauko ƙasa bin falon yake da kallo a cikin ranshi kuma yana tunanin kenan da gaske ne Sumayya office ɗin ta tafi ta bar shi. Taɓe baki ya yi kafin a fili kuma ya ce"Kin ga abin da zan yi miki" kafin ya ƙarasa fakon ya gaishe da Mama da ke zaune tana faman kallon TV kafa daya kan daya. Ta ce"Ya aka yi ba ka tafi office ba Abdallah?" Sosa keya ya yi ya ce "to da ba zan je ba amman kuma na ga gara kawai na je zan rage wani aikin" murmushi ta yi ta ce"Gaskiya kam Gara ka tafi , don mai kirjin na iya ɗin can har ta tafi kar ka je ka na zaune a nan ta sace maka kuɗi" kicin-kicin ya yi da fuska ya ce"Dan Allah Mama ki daina, bana son jin ki na zagin Sumayya don sai babu yadda zan yi ne" wani irin uban ihu ta yi har dankwalin kanta na kunce wa ta shiga tafa hannu tare da yin salati ta ce"Allah mai iko kai Abdallah yanzu Ni kake faɗa wa wannan magana, ba shakka biri ya yi kama da mutum" shiru ya yi yana jin babu daɗi abin da Mama ke faɗa kuma ta bangare ɗaya yana ji a cikin ranshi babu daɗi idan ya ci gaba da zuba ido kullum tana zagin Sumayya ɗin. Tashi ya yi ya bar wajen tare da nufar office. Yana fice wa Rumana da Jidda wanda tashin su daga barci kenan suka iso falon suka tarar da Mama tana ta bambamin masifa. Rumana ta ce"Me kuma ya faru?" Kwalla ta fara matso wa tana fadin "Ba Abdullah ba ne yau kam ya nuna min Sumayya ta fini a cikin gidanan, wai fa ce min ya yi na daina zaginta" wani uban ashar Jidda ta yi ta ce"Dama ba faɗa miki ki bari mu ɗauki mataki akan wannan yarinyar amman kika ki duba fa dan Allah yanzu har yaya Abdallah ya kai matakin da zai riƙa mayar miki da magana Duk a kanta" tsaki Mama ta ja tana mai ci gaba da kokarin ɗaura dan kwalinta da har yanzu ta gaza ɗaura shi ta ce"Ni fa tun farko da na san haka za ta kasance Allah ne shaida ta da ba zan bar wannan auren ya kasance ba" ita da ƴaƴanta suka ci gaba da jefa maganganunsu wadda duk rabi suna zagin Sumayya ne da su.. Ina zaune a office aka turo ƙofar tare da shigowa ban dago ba saboda na riga da na san idan dai ba Abdallah babu wanda da zai yi wannan ɗanyen aikin. Sai da ya ja kujera ya zauna kafin na ɗago da murmsuhina na ce"Yanzu sallamar ma wuya take yi wa wasu" bai yi magana ba sai ma watsa min wata tambaya ya yi "Me kika yi wa Mama tun safe take faɗa?" Girgiza kaina na shiga yi don tun tuni hawaye sun cika min idanu duk da kuwa idan dai da sabo ya dace a ce na saba da wannan hali na mijina a duk lokacin da ƴan uwanshi ko mahaifiyarshi za ta ce na yi mata wani abu wuni zai yi yana yi min faɗa yana cin magani sai na ce"Ni kuwa Qalbi gani nake wannan maganar ba ta dace a yi ta a nan wani zai iya jin mu idan muka koma gida sai mu tattauna a cikin nutsa ina ganin hakan zai fi" bai sake wata magana ba ya tashi ya fice daga office ɗin. Girgiza kaina na yi kafin na ci gaba da aikin gabana. Tun la'asar na haɗa komatsaina na nufi gida bayan na yi wanka na yi salla sai na sauka kitchen don haɗa abincin dare. Bayan na gama na jera a dinning kafin lokacin cin abinci ya yi don gabadaya a nan muke taruwa mu ci abincin. Ko da Abdallah ya shigo gidan ko kallon wajen da nake bai yi ba ya haura sama abin shi. Ko da lokacin yin dîner ya yi a falonmu na tarar da shi yana aiki a laptop ɗinshi zama na yi na ce"Qalbi ka yi hakuri ka san ba na iya ƙurar fushinka a kaina, da ka yi fushi da ni gara a yi min bulala ɗari da hamsin" sai na ƙara marairaice fuska na ce"Dan Allah ka yi hakuri Qalbi" sai yanzu na samu na ga ɗigon rahama a fuskarshi ya buɗe baki da niyyar ya yi magana sai Mama ta banko kofar falon tare da shigowa kamar an cilo ta daga sama ta ce"Ke munafuka algunguma tashi ki bani waje ina son ganawa da ɗana" ban tanka ba sai miƙewa da na yi na nufi ɗakina na zube akan gado tare da rafka wani uban tagumi *Assalama'aleikoum Allah ya sake haɗa mu a wani sabon labarin, ina fatan za ku bi shi domin daukar darasi da dama a cikinshi* [06/12 à 00:19] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW *DA WATA KUSAN...* NA Zouley Sabitou (Émilia) Daga marubuciyar *KUSKURE* ☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️ (Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation) GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUƊE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA. +22780416252 *Page 02* Bayan na shigo ɗakin na rafka uban tagumi sai ga Abdallah ya shigo ɗakin, zama ya yi a bakin gado ya watsa min manyan idanunsa masu rikitar da ni da sauri na kawar da nawa idon na fara wasa da yantsuna ina jiran jin abin da zai fara da shi sai kuma na yi shiru na tsawon lokaci. Na ɗago da idanuna sai kuwa ya sauka akan nashi don dukan alamu shi ɗin ma Ni yake kallo. Ya ce"Sumayya!!" Da wata irin murya mai nuni da gargaɗi, tuni na sha jinin jikina na ce"na'am Qalbi" "Sumayya me kike son zama ne a cikin gidan nan? Rigimar safe daban ta rana daban" idanuna tuni sun kawo kwalla ina gab da fara kukan da idan da sabo ya ci a ce na saba da shi na ce"Qalbi me ya faru? Ko ma mene abin da na aikata ina son ka yi min uzuri ka saurari nawa jawabin" wani tsaki ya ja wanda har cikin raina na ji shi sai ya ce"Ina son daga yau ki shiga hankalinki ba na so Mama ta kuma kawo min ƙara akan kin yi mata wani sai na yi mugun saɓa miki, kin ji ko?" Gyaɗa kai na yi kamar wadda ke tsoron magana na ce"Allah ya huci zuciyarka Qalbi" bai ko sake sauraren maganata ba ya bar ɗakin. Tashi na yi na yi wanka na fara nafila ina jero addu'oi wadda idan da sabo tun tuni na saba, Allah ne kaɗai gatana ba ni da wani wanda ya fi shi na riga na miƙa gabadaya lamurana a hannunsa. Ban san lokacin da barci ɓarawo ya ɗauke ni a wajen ba sai da na ji an fara kiraye-kirayen sallar asuba kafin na tashi na ɗauro alwala. Ina gama salla na fara aikin gyaran bangaren nawa. Ko da na isa ɗakin da Abdallah ya kwana na tarar bai dawo daga masallaci ba. Aikin gabana na ci gaba da yi har ya shigo ɗakin, har ƙasa na tsuguna na gaishe shi amsawa ya yi cikin fara'a kamar babu abin da ya faru a daren jiya, babban dalilin da ya sa nake ƙara jin kaunar shi a cikin raina bai kasance mutum mai riƙo ba duk abin da ya faru da an ɗauki lokaci zai sauko kamar ba a yi ba. Rungume ni ya yi tsam a jikinsa ya ce"Babe, fatan kin kwana lafiya?" Murmushi na yi na ce"Lafiya qlau Qalbi ina fatan kai ma haka" da kai ya yi min alamar lafiya qlau kafin ya ce"Ki je ɗakin Mama ki yi mata shara da mopping idan kika gama aikin da kike yi" idanuna na ɗago daga kan kirjinsa na ce"Amman Qalbi masu aikin gidan fa" yatsarsa ya saka akan lips dinsa alamar na yi shiru sai na yi gum da bakina na fice daga ɗakin. Ƙasa na sauka na shiga kitchen na fara haɗa kayan da za mu yi breakfast da shi. Dakin Mama na shiga da sallama a bakina tana zaune akan bed dinta tana faman jan carbi ta amsa min, har ƙasa na tsuguna na gaishe ta ba ta ko kalle ni ba ta amsa min daƙyar sai na ci gaba da cewa"Mama dama na zo ne don gyara miki ɗakin ne" tana cin magani ta ce"Sumayya tashi zan yi don ki share ɗakin" girgiza kai na yi na ce"A a Mama amman ki yi min uzuri na gyara kin ga zan je office" tsaki ta ja ta ce"Sai ki tashi ki tafi idan na gama abin da nake yi zan yi miki magana sai ki gyara ɗakin" kamar yadda ta faɗa ban ƙara furta wata kalma ba na bar ɗakin. ★Abdallah★ Tunda ta fice daga dakin na zauna tare da rafka tagumi tunani nake a raina ina zan samu mafita, bana da burin da ya wuce a rayuwa na ga Sumayya cikin farin ciki da kwanciyar hankali sai dai kuma hakan ta gagara kullum cikin musguna mata nake rana ba ta fito wa ta faɗa ba ta zubar da hawaye a kaina ba, ina zani da wannan alhakin? An ya zan iya kwanciyar kabarina da alhakin Sumayya a kaina kuwa? Ire-iren tambayoyin da nake jefa wa kaina a duk lokacin da zan kasance ni ɗaya a zaune sai dai kuma kash ba ni da amsar su. Ban ma san abin da yake hana ni saka matata a cikin jin daɗin duniya ba, duk maganar da aka faɗa min daram nake hawa kan ta na zauna, wannan lamari zai haifar min ɗa da ido kuwa? Turo ƙofar ɗakin ta yi har yanzu fuskarta dauke da mutmushi wanda idan ba ni da na yi mata farin sani ba na san sarai wannan murmushi ne mai kama da kuka ne take yi, sai da ta ƙaraso wajen da nake zaune kafin ta zauna akan cinyata ta ce"Qalbi mutanen gidan ba su tashi ba, na kawo maka breakfast ɗin ka nan ne?" Gyaɗa mata kai na yi alamar e mutmushi ta kuma yi kafin ta ce"Yau kam da ƴan miskilancin muka tashi" daga nan ta fice zuwa kitchen da dukan alamu. Ina zaune a wajen jim kaɗan sai ta dawo ɗauke da katin plate mai kayan breakfast a ciki. Ba ta damu da sakawa a cikinta ba haka ta zauna tana bani a baki ina ci har na koshi kafin na riƙe mata hannu tare da girgiza mata kai alamar ya isa haka. Ajiye cokalin ta yi ta shiga goge min baki sai na ce"Kin yi abin da na saka ki?" Girgiza kai ta yi ta ce"Mama ba ta tashi ba ta ce min idan ta gama za ta kira ni" ban ce mata komai ba sai gyaɗa kaina na yi kafin na zame ta daga jikina na nufi toilet. ★Sumayya★ Kayan breakfast ɗin na kwashe na kai kitchen haushi Qalbi duk ya mamaye min zuciya kenan bai gamsu da bayanin da na yi mishi ba ne ko mene ne da zai wani ture ni ya fice zuwa toilet. Ban damu da cin wani abinci ba ne haka na haura ɗakina na yi wanka kafin na yi shirin zuwa office. Ko da na gama ban kuma bi ta kanshi ba don na tabbata ya bar gidan na sauko ƙasa na dauki motata na nufi office ɗina. Da yamma ko da na dawo gida ina buɗe kofar falon da Mama Sa'a na ci karo ta watso min wani kallo wanda ko sallamar da na yi ba ta amsa min ba. Gaishe ta na yi duk dai na san babu tabbas ɗin amasarta sai na fara kokarin haura steps don zuwa ɗakina ta ce"Ke Sumayya zo nan" juyawa na yi na je na ce"Mama gani" tsaki ta ja ta ce"Ni sa'ar ki uwarki ce da za ki tsaya min a ka kikam" zama na yi akan cafet ɗin fakon ba tare da na yi magana ba ta ce "Ɗazu da safe ba na ce miki ki jira ni zan yi miki magana akan gyara min ɗaki shi ne tsabar isakanci kika fice daga gidan don ban isa da ke ba ko?" Girgiza kai na yi na ce"Mama ba haka ba ne na ga zan makara ne shi ya sa na tafi" wani kallon mai saman ruwa take yi min ta ce"To ai yanzu kin dawo tashi ki je gyara min" tashi na fara kokarin yi ina faɗin "To zan kai canza kayana sai na zo na gyara yanzu" girgiza kai ta yi ta ce"Ajiye jakar ki je ki yi min abin da na saka ki" ban kuma tanka mata ba don na san idan na tanka ma a kaina za ta ƙare, kawai sai na cire mayafina da jakar na zubar da su akan kujera har wayata da makulin mota na nufi ɗakin Mama. Mama Sa'a na ganin Sumayya ta shiga ɗakinta don gyara shi sai ta ja tsaki a ranta a fili kuma ta ce"Shegiya mai sunan mage" zama ta yi don ci gaba da kallon tv sai kuma hankalinta ya sauka a kan handbag ɗin da Sumayya ta ajiye ta shige ɗaki. Nan ta buɗe ta ido ta zaro tozali da idanunta suka yi da bandir ɗin ƴan jika goma sababi a miƙe. "Tabdi, wannan yarinyar a ina ta samu kuɗi haka?" Ta faɗa tare da ciro kudin ta shiga juya su a hannunta "wannan kudin kam idan dai ba a office ɗin Abdallah ta sato su ba, zuwa ta yi ta budé wa wani gardin kafa ya bata su, jika ɗari (200k) ne fa" ta faɗa tana ƙara karewa kudin da ke hannunta kallo ji take kamar ta ɗauke su ta ɓoye ko kuma ta mayar da su cikin jakar Sumayya. Daƙyar ta yaƙi zuciyarta ta amince mata akan ta mayar da kudin cikin jakar da ta ɗauko su. Haka kuwa ta yi ta maida su ciki kafin ta yi wani murmushin mugunta don ita ɗaya ta san irin makircin da za ta ƙulla wa Sumayya akan kuɗin, kila ma silar su ta bar mata gidan ko ta huta da jaraba... Ko da na gama gyara ɗakin na saka turaren wuta na fito falon na ce"Mama na gama" da ka ta amsa min, na kwashi kayana na bar falon a cikin raina ina cewa "Wannan miskilancin na Qalbi da dukan alamu wajen Mama ne ya gado shi" ina shiga ɗakin na ajiye duk abin da ke hannuna na kuma sauko wa kasa don girka abincin dare. Ya riga ya zama kamar wata ibada ne a kaina, ni zan yi girkin safe na kuma yi na dare ko kuwa na je office safe da yamma duk masu aikin gidan a banza suke baya da haka ma Rumana da Jiddah da ke zaman banza babu abin da suke yi sai dai su wanke goma su tsoma biyar amman duk da haka ko tsinke ba sa iya ɗauke wa a cikin gidan. Ina gama abincin na koma ɗakina na yi wanka tare da yin kwaliyya don tarbar Qalbina ba a ɗauki lokaci mai tsayi ba kuwa sai gashi ya shigo gidan rungume shi na yi ina yi mishi oyoyo kamar dai wata ƙaramar yarinya. Shi ma biye min ya yi a haka har ya gama wanka ya tafi masjid don yin sallar magariba da isha'i. Ni ma tawa sallar na yi ina zaune a kan tapis har ya dawo gidan zama ya yi ya ce"Babe dan Allah a ban abin da zan ci don yunwa nake ji" murmushi na sakar mishi kafin na tashi na ce"To mu je dinning sai ka ci ka koshi ko" kamar wani karamin yaro ya maƙale min kafaɗa ya ce"Ni a nan zan ci" girgiza kai na yi na ce"Dama da safe a nan ka yi breakfast tashi mu tafi falon don kar Mama ta damu ta yi tunanin ko babu lafiya ne" tashi ya yi ya bi bayana muka sauko ƙasa don cin abincin dare. ★Mama Sa'a★ Ji nake yi tamkar na shaƙe wannan yarinya Sumayya ta mutu ko na huta da bakin cikinta wannan yarinya tun ranar da aka kawo ta wannan gidan na tsane ta sai dai kuma babu wata hanya da ban bi ba don ganin na saka ta bar min gida amman a banza har yanzu shiru kake ji malam ya ci shirwa. Wani shu'umin murmushi na yi tunawa da na yi yau kam kashinta ya bushe don da dukan alamu yau ranar sa'ata ce domin yau na ɗauki alwashin sai ta bar mana gida ko na huta da ganinta munafukar banza munafukar wofi. Mutmushi da ke fuskata ne ya ƙara yalwatuwa ganin sun sauko daga ɓangarensu ita da Abdallah sai da suka zo daidai wajen da nake na ce"Ke Sumayya kira su Jiddah mu ci abinci" sakin hannun Abdallah ta yi wanda tun fitowar su falon yake sarke cikin na juna sai na raka ta da harara tamkar idona zai faɗo. Jim kaɗan sai ta dawo tare da su Jiddah. A dinning muka haɗu gabadaya don cin abinci yau kam har da Malam mahaifin su Abdallah wani daɗi nake ji yana ziyartar ko wane sashe na jikina. Sai da na tabbatar fakon gabadaya ya yi shiru sai na ce"Sumayya wani mutum ya kawo saƙon kudi ya ce a baki ɗazu da na saka ki aiki, kuma ya ce kar ki manta da jini za ku haɗu a wajen da ya ce miki, na saka miki kudin a cikin karni" gabadaya idanun mutanen fakon na kan Sumayya wadda da dukan alamu har yanzu ba ta fahimci abin da nake nufi ba. "Wane ne ya zo neman ta?" Na jiyo muryar Abdallah yana watso tambayar. "ka ji ka da wani zance daga ungo kai, shi ke nan sai ka san ya wa aiko da su" sai yanzu ta yi magana duk ta ruɗe ta ce"Mama ina ga fa babu wanda ya zo nema na gidan nan" fashe wa na yi da kukan munafurci na ce"Sumayya ai nafi karfin na yi miki ƙarya bare kuma yau na fara, idan ƙarya ne a duba jakarta mana ai za a ga kudin da na saka a ciki" Tun kafin na gama rufe bakina tuni Rumana ta tashi ta nufi hanyar ɗakin Sumayya don ɗauko jakar ni kuwa raina fari tas kamar farar takarda. *Cmnts nd share* [06/12 à 12:50] Émilia: https://chat.whatsapp.com/H9Q7z3J09hnDQuUJNbIdKW *DA WATA KUSAN...* NA Zouley Sabitou (Émilia) Daga marubuciyar *KUSKURE* ☀️FIRST CLASS WRITER'S ASSO...☀️ (Home Of Qualités And Trusted Writers Of The Nation) GA DUK MAI BUKATAR A TALLATA MATA HAJJARTA KOFA A BUƊE TAKE, ZA KU SAMU BIYAN BUKATA.

Chapter 1 of 8