Share this page
3 / 4
tayi haba Inno wallahi ba da son ranshi bane. Na dai fada miki...munari ba fa sadakarki aka bani ba. Haihuwarki nayi kamar kowanne da. Kyautace Allah Ya bani to nayi hakurin da zanyi Allah Ya yanke miki wahala. Inna Ladi tace hakane amma kada muyi saurin yanke hukunci. Sallama suka ji daga waje. Inna Ladi ta amsa don ta gane mai muryar tare da yi masa izinin shigowa. Yana shiga gidan ya zube a kasa yana basu hakuri. Inno tace ai ni so nake ka cike mata sakin gabadaya. Inno kiyi hakuri don girman Allah. Zan kama mata gida sai na mayar da ita can. Kaga tun ina ganin mutumci da kimarka ka bar gidan nan kafin ayi abun kunya. Yadda Uwale ta karbi Ummita to zan aikawa Yayansu ya dawo maka da danka. A'a inno na bar masa ki dena maganar nan don Allah. Ya kalli Inna ladi ki bata hakuri, ko kula shi bata yi ba taja hannun munari tana tirjewa cikin dakinta. Haka ya gaji da zama ya koma gida. Washegari kafin azahar Inna Ladi ta aika Tani tazo da mai binta Shafa suka raka Munari birni gidan Salihu bisa umarnin iyayensu. Haka Dijengala inji kakarta uwale ta tashi cikin kuncin rayuwa da wahala. Mahaifinta ne kadai gatanta. Tana da shekara biyu Sabuwa ta kara haihuwa. Dama ba wata kulawa Digengala ke samu ba hatta wanka sai babanta ya matsa ake yi mata. Watarana ya fita da sassafe Sabuwa ta kai ruwa bandaki a katuwar roba ta kira Hanan da Dijengala tayi musu wanka. Tana gamawa yarta tace muje in shafa miki mai tukunna. Dije wadda aka yiwa tsirara sai rawar dari take saboda sanyi tace Mama nima wanka. Wani mari Sabuwa ta gaura mata ta dauki yarta suka fita. Dije tana kuka ta taka sabulu ta zame ta fada cikin robar ruwan. Sai da sabuwa ta gama shirya Hanan bayan kusan minti goma ta dawo ta tarar da Dijengala ta kusa shidewa a robar ruwa. Batul Mamman💖 [8/22, 3:11 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰14 BAYAN SHEKARA 17 Cikin daga murya irin na wadanda basa ji sosai tace Inna ina kwana? Uwale ta sha kunu matsa can ni kada ki tofe ni da yawo kinzo kina min ihu a ka. Dijengala tace naam? Alamun bata ji abinda kakarta ta fada ba. Tsaki Uwale tayi tare da daga hannu lafiya nace. Murmushi tayi wanda yake kara mata kyau tace au banji ba ne. Dama ai ba jin kike ba. Ta sake daga hannu tashi ki bani wuri. To..to..to ta mike ta koma dakin su ita da Hanan da kanwarsu Zaliha. Wata yaloluwar katifa ta nufa ta kwanta. A hankali idanunta suka ciko da hawaye. Ita meyasa bata da Umma? Ina dangin ummanta suke? Hawayen ne suka gangaro sai tari ya sarke ta. Zaliha ce ta ganta bayan ta dawo daga makaranta. Yaya Dije sannu ta dafe mata kirji. don idan ta fara tarin numfashinta har neman daukewa yake. Rashin kudi sosai yasa Babanta ke yawo da ita gidan masu maganin gargajiya, wasu suce sanyi wasu suce asma. Zaliha ta dago kan dije ta bata ruwa bayan tarin ya lafa. Ta daga murya Yaya Dije kuka kika yi ko? Tayi saurin girgiza kai tari ne Zaliha. Allah Yasa da gaske kike, bari naje na dauko mana abinci nasan yunwa kike ji ma. Haka dokar Sabuwa ta koma abincin Hanan daban, Zaliha da Dije tare ake hada musu. Tunda Dije ta gama secondary school wadda ba wani abin kirki ta iya ba saboda rashin kunne kullum sai ta jira Zaliha ta dawo zasu ci. A cewar sabuwa kada dije ta cinye abincin. Babansu bai taba sanin wannan dokar ba don har yanzu yana so da kula da lamuran yarsa. Shekararsu goma sha biyar da baro kauyensu suka koma birni da zama. Takurawar iyayen Munari kan sai an basu Dije yasa Uwale sayar da filayenta harda gidansu ta matsa masa sai sun tashi indai ba so yake ya kulleta a gidan yari ba. Tayi mamakin yadda aikin malam bai kama su ba sai dai kuma bata kara jin duriyar Munari ba tunda tasa Yakubu ya saketa. Aikin gini da noma yake yi a haka yake ciyar da iyalinsa yake saka su a makarantar gwamnati. Tun tafiyarsu wadda basu yiwa kowa sallama ba iyayen Munari suka sanar da ita duk abinda ya faru. Tayi kuka sosai saboda tana matukar son 'yarta kuma ta kara tsanar Yakubu akan guduwa da yayi da ita. Allah Yasa ma Sadi yana wurinta. Hanan ta fara karatu a polytechnique ta garin kano tana ji da kyau da gayu. Duk gidansu babu wanda take so kamar kakarta Uwale saboda yadda take shagwabata tana kuranta kyaunta. Duk yar yaudarar samarin da take da izinin kakarta take yi. Tana kwance kan gadon uwale tana chatting Mal Yakubu ya shigo dakin. Wani wuntsulowa tayi da sauri zat gudu. Hannunta ya rike ya dawo da ita dakin munafuka ina zuwa. Ya zaka kirata munafuka dan nan ka kiyayeni fa akan Hannan wallahi. Inna kina bata yarinyar fa. Kalli wayar hannunta abinda take saurin boyewa kenan kada na gani. Uwale tayi murmushi zancen banza ai kudin dashi na na bata ta siya dashi. Hanan tace Allah Baba ita ta bani.bari saurin rantsuwa ni tsakanina daku shawara ce. Iya abinda zanyi miki nayi na tarbiya. Allah Ya shirya. Ficewa yayi rai a bace ya tafi dakin yaran wurin Dije da Zaliha. Baba sannu da zuwa...yauwa Zulaihatu. Taba min yayarki nasan bata ji shigowata ba. Tsinkin tsintsiya Zaliha ta sawa Dijengala a kafa ta mike a firgice. Wayyo Allah...muryarta duk ta cika gidan. Tana ganin babanta ta matsa kusa dashi. Baba kaga Zaliha ko...zan zane ta fa. Guje guje suka rinka yi a tsakar gidan yana dariya. Yaran nan biyu kadai ne suke wanke masa bacin ransa da damuwa. Sune kuma Uwale bata so don abin mamaki duk farin Sabuwa haka ta haifo Zaliha baka har tafi Dije duhu. Shiyasa uwale bata shiga sabgarsu kamar babu su a gida. Batul Mamman💖 [8/22, 3:12 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰15 Ranka ya dade ga takardun filayen guda uku aka samu a wuri daya. Alh Sulaiman Hassan ya kalli sakatarensa Modibbo nagode dan fillo. Zanyi magana da managers din sauran kamfanin sai muyi finalising project din. Modibbo yace hakan yayi ranka ya dade amma akwai sako daga wurin Hajiya fa. Murmushi yayi alamun yasan sakon Hajiyar yace nasan cewa tayi ka tabbatar yau na tashi da wuri ko? Shima Modibbo murmushin yayi ni dai umarni nake bi kuma lokaci ya riga yayi. Wai ni waye ke biyanka ne ni ko ita? Ai Alhaji da kai da kaya duk mallakar wuya ne. To naji ya fada tare da mikewa. A hankali yake tuki don yau drebansa bai zo ba matarsa ta haihu. Karatun Al-Quran yake ji kira'ar Sheik Khaleel Husary yana bi cikin nutsuwa har ya isa gidansa a unguwar bompai ta cikin garin kano. A falo ya tarar da ita ta gama hade rai alamun tana fushi dashi. Mata ne biyu zaune tare da ita. ko da ya gaisheta da kyar ta amsa masa shima yasan yayi laifi bai matsa mata ba yayi hanyar bene tace cikin fushi Sulaiman ina zaka je kuma? Umma zan canja kaya ne na dawo. To kayi sauri yaran kawata ne suka zo gaisheni shine nace su jira kazo ku gaisa. To kawai yace a ransa kuwa harda dariya...umma kenan ta zama matchmaker karfi da yaji ita a dole sai yayi aure a wannan shekarar. Shima kullum yana adduar samun ta gari yasan kuma Allah mai jin rokon bayinSa ne. Wanka yayi yasa kananan kaya ya sauko. Yana zama Umma ta mike to bari na duba abinda ake dafawa. Yasan so take ta basu wuri ya ce to kawai. Tana tashi dayar wadda take ta yi masa kirikiri da ido tace Yayanmu ni sunana Ainau wannan kuma kanwata ce Bilkisu. Ko kallonsu baiyi ba don basu yi kama da masu kunya ba ya zaro kudi a aljihunsa ya mika musu ga kudin mota nice meeting you. Sai anjima muje nasa dreban Umma ya kaiku gida. Ainau ta bata rai ai Hajiya tace mu jira zaka kaimu da kanka idan ka dawo saboda kaga gidan. Ashe ma doluwa ce yarinyar ya fada a ransa. Kinga naji ciwo a hannun bari a kaiku. Bani number dinki zan kiraki musamman. Kanwar tace nifa? Itama karbar tata yayi yana so suyi su fita kafin Umma ta dawo. Sai da yaga fitar motar daga gate din gidan ya dawo ya zauna. Muryar ummansa yaji tace Sulaiman ina su Ainaun suke. Ai sun tafi wai sauri suke yi...amma yaron nan baka da kirki. Wai so kake na mutu banga jika na ba shekarunka talatin da shida fa...jin ta fara shakar hanci yasan kukan blackmail ne ya tashi. Kiyi hakuri Ummana na sami mata ina jira mu gama daidaitawa ne. Ta washe baki hakoran makkanta suka bayyana. Da gaske Sulaiman? Da gaske Umma..to ai da kayi magana da wuri bazan kira yaran nan ba, dama nima duk basu yi min ba. Yadda tayi maganar yasa shi dariya sosai. Modibbo da abokinsa Mal Yakubu suna zaune kofar wani gida da su mal yakubu ke aikin ginawa yace mutumina Alhajin kamfaninmu ya sayi wasu filaye manya guda uku. Ban dai san abinda zai gina a wurin ba amma naga so yake ayi ginin da wuri. Zanyi masa magana akan ka ka samu shiga cikin masu yin aikin. Nagode Modibbo Allah Ya bar zumunci. Wallahi kudin karatun yaran nan da ciwon Dije sune suke damuna. Kada ka damu in sha Allah zaka sami wani abin yanzu don Alh Sulaiman akwai kirki. Haka suka zauna suna ta hira har laasar tayi suka tafi gida tare. Batul Mamman💖 [8/22, 3:13 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰16 Hannu yaji ya sakalo masa wuya ta baya. Daddy oyoyo...tashi yayi ya daga Ammar sama yana ta dariya. Umma ta fito ni kun cika min gida da ihu abinda kuka iya kenan. Dariya suka sake yi mata Ammar yace Daddy dazu mamana tazo kafin ka dawo daga office. Umma ya kalla tace Ammar je ka daki ka dauko wa daddy tsarabar da tayi maka. Yana fita tace zuwa tayi ta sanar dani ta sami mijin aure. Ai gara tayi auren ta dade shekara shida ai ba kwana shida bane. Sulaiman yace Umma Allah Yasa dai ba fushi kike dani ba akan rashin aurenta. Gyara zama tayi ko kadan duk uzurin da ka bani na karba. Idan ka kai mata Ammar ranar jumaa sai kaji ko waye mutumin. Alh Sulaiman Hassan shine da na biyu a wurin Haj Bintu. mahaifinsa babban dan kasuwa ne kuma yana da kamfanin yin kafet har uku a kasar. Shekarar Sulaiman ashirin da daya baban nasa ya rasu bayan yasha jinya yayansa Yusuf ya cigaba da kula da kamfanin baban. A lokacin da yake masters dinsa a fannin aikin banki , Yusuf ya rasu sakamakon hatsarin mota da yayi. Ya bar matarsa sakina da ciki wata biyar. Bayan ta haihu ne Umma tayi ta kokarin hadasu da Sulaiman yaki yarda a cewarsa bazai dena kallonta a matsayin matar wansa ba. Shekaru shida kenan sai yanzu ta sami wani zata aura. Saboda matsin layin daga can baya Sulaiman yayi parking motarsa shi da Modibbo suka taka da kafa zuwa kofar gidan Mal Yakubu. Kwata ce a kofar gidan dole suka shiga daga dan zauren waje inda Uwale ke kiwon tumaki. Banda wari da zarni babu abinda ke tashi a wurin. Sulaiman ya gimtse fuska. Modibbo sarai ya gane warin ke damunsa yace yallabai kayi hakuri shiyasa nace ka zauna a mota na kira shi. Ba komai Allah Yasa ya fito yanzu dai. Wata kyakkyawar yarinya ce ta fito fara tas harda dan karin mai. Cikin yanga take tafiya. Gaba daya hankalin Alh Sulaiman ya koma kanta. Baba yace yana zuwa ta fada ba tare da tayi musu sallama ko gaishe su ba. Ciki ta koma tana taunar cingam. Mal yakubu ya fito ya gaishe da Alh Sulaiman sannan ya gabatar da kansa. Alh Sulaiman yayi masa bayanin wurin da filayen suke ya kuma bukaci yazo kamfani ya same shi washegari. Ihun da suka ji yasa su yin shiru Dijengala ta fito da gudu tana kuka. Murya can sama tace Baba kaga Mama ta hanani wanka yau ma wai zan karar da ruwa. Kaji yadda nake tsami kuwa...matsawa tayi gabansa tana daga masa hannuwanta har gashin hammata Alh Sulaiman yana gani. Kuma fa jinin wata na yazo tun jiya . Subhanallahi Dije sauke hannun mana ya kama hannunta zai koma cin gidan da ita. Tirjewa tayi Baba dukana fa zata yi kuma kullum Yaya Hanan tana yi da Zaliha. Duk kunya ta kamashi ya daga murya don taji abinda yake fada...muje nace zan mata magana. Burinsa kawai su koma cikin gida. Sai lokacin taga mutane tsaye...lahh baba modibbo sannu da zuwa. Sai ta rike baki au...duk kunji abinda na fada ko? Wayyo kunya ta dafe kai tare da komawa cikin gida. Alh Sulaiman kuwa dariya ce ta kwace masa ganin yadda Dije take baragada a gabansu. Sai dai fa akwai wari dan kare. Batul Mamman💖 [8/22, 3:13 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰17 Wani murmushin ya sake yi shi kadai Umma ta jefe shi da pillow din kujera kai ni dariyar me kake yi kamar kwancen hauka....wata dariyar ya sake yi sannan ya bata labarin Dijengala kurma. Itama dariyar tayi maimakon ka taimaka mata shine kake dariya. Ni mubar wannan zancen dai ya sunan yarinyar da kayi min zancenta ne? Ga mamakinsa sai yaji yace Hanan. Daren ranar tunaninta ya rinka yi. Tana da kyau mai daukar hankali gashi da gani tana da tsafta ba kamar Dijengala ba. Wani murmushin ya sake yi da ya tuno yadda take magana. Daga nan har yayi bacci tunaninsa yana kan Dije yana dariya. Ranar litinin duk ya kagu modibbo ya iso. Yana zuwa kuwa tambayarsa tayi ko anyiwa Hanan miji. Modibbo yadan yi turus...Hanan dai yar abokinsa ce amma ko kadan bata da hali. Ranka ya dade ba ayi mata miji ba a iya sanina. To ka sanar da mahaifinta idan ya amince zan nemi aurenta. Modibbo ya nuna farincikinsa a fili amma ba don yadda Dije ta tashi ba sai shirme da shiririta ga lalurar kurumta da ita zai so Alhajin ya nema. ******************* Rana duk ta dami Hanan a kofar banki inda take jiran kawarta. Wata mota take ta kallo, ba karamin kyau tayi mata ba...duk mai motar nan ko ba'a fada ba mai kudi ne kuma mai kyau. Tayi dan tsaki ita kyau ma bai dameta ba indai akwai kudi. Tana zaune a wurin wani matashi ya fito ya bude motar. Gaba daya ya tafi da hankaliñta ta bishi da ido. Kana ganinsa kaga kudi don yawan shige shigenta tana gane mai kudi tana gane yaron mai kudi. Wannan matashin kam shine da kudin. Tashi tayi ta kade skirt dinta tayi saurin zuwa gaban motar inda yake shirin rufe kofa tace Alhaji kwana biyu. Ya dan dago kai a dakile yace ya kin sanni ne? Tayi baya yi hakuri sai naga kamar wani da na sani ne. Sai kashe murya take tana magana ciki ciki. Ya bata rai bashi bane to...matsa na rufe kofar. Kafin ta gama matsawa ya bugeta da kofar ya figi motarsa. Kafin ya bace ta gama haddace numbar motarsa. Batul Mamman💖 [8/22, 3:14 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰18 Kawarta Hajara ce ta fito jaka cike da kudi. Sorry Hanan na barki jira ko? Gaskiya da mita zan miki amma na fasa. Wani kamu nayi mai kauri. Hajara tace haba a yana ina? Hanan ta fada mata yadda suka yi. Amma zancen gaskiya kawata yayi min akwai kudi. Ji nayi kamar kudin jikinsa yana kirana. Shegiya uwar son kudi nasan wannan mai cangala kafar zaki kaiwa. Allah sarki innata tafi kowa kaunata. Ni ba wannan ba Hajara ki rakani gidan Babba mana. Akan mutumin nan sai anyi aiki. Dayake halinsu yazo daya shiyasa kullum a makaranta tare suke. Hajara da Hanan suka wuce gidan Babba wani malamin tsibbu. Don yanzu bin malamai harda yan mata. Allah Ya kara shirya mu. Bayan dukkan bayani Babba yace Hanan kin san sunansa? A'a amma ga numbar motarsa, ka taba yi min aiki akan wannan wawan malamin da numbar waya ai. Ba damuwa Hanan ga wanan turaren ki saka kan garwashi sai ki rubuta numbar motar a takaddu goma ki rinka dorawa akan wutar har su cinye duka. Sai ki lazumci zuwa wurin da kuka hadu na kwana goma. Idan baki ganshi ba to motar ba tasa bace. Godiya tayi sosai tace idan ciniki ya fada zaka ganni. Bayan kwana uku Modibbo ya sanar da Mal Yakubu bukatar Alh Sulaiman. Murnarsa bazata misaltu ba ya sanar da Uwale. Burinshi dama tayi aure ya gaji da sintirin da samari ke yi masa a kofar gida. Sabuwa ma tayi murna har ta sanar da babarta Zulai. Cikin dare ta bawa mijinta shawarar ya aurar da Dijengala. Banda abinki Sabuwa ina Dije take da saurayi. Tayi wani murmushin keta...wani kurma ne dan uwan Zainab makociyarmu. Tace a kauyensu yake Kura. Hade rai yayi dakata malama ni 'yata bata gama kurmancewa ba kinji ko. Ki rike abinki rabonta na tafe. Kuma dama ina son yi miki magana Allah ranar da kika sake hanata ruwan wanka zaku yini a gidan nan ba ruwa. Yar hirar tuni ta watse ya juya yayi kwanciyarsa. Gari na wayewa cike da zumudi Uwale ta sanar da Hanan zancen Sulaiman. Ta wani harareta jiya tasha uban hayaki akan wani yau a kawo mata zancen wani Alh Sulaiman. Kinga Inna ki bar maganar nan ina da wani. Haba Hannan mutumin nan fa kudi gareshi sosai. Mafarkina a kanki ne zai tabbata. Hanan ta wuce zata shiga wanka. Kinga Inna ki bar maganar nan ku bashi Dijengala ko Zaliha. Auzubillah uwale ta fada tana tofar da yawu. Dije ai ai musaki irinta. Yarinya ga baki ga muni. Batul Mamman💖 [8/22, 3:14 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰19 Hanan tayi sati daya tana zuwa bankin da suka je da Hajara tun safe har sai sun tashi amma mai motar bai dawo ba. Rai a bace ta koma gida duk ta kusa gama kashe kudin hannunta a hawa motar zuwa banki. Dakinsu ta shiga zata cire kayanta tayi wanka Dije ta shigo tana waka da karfi. Hakan ya kara batawa Hanan rai ke rufa min baki banza kawai. Ta fice tana tsaki. Babanta ta gani a kofar kitchen yana magana da Sabuwa...yauwa zo hanan dama zancenki muke yi. Ta turo baki gaba ta karasa gabansa ta tsaya. Nasan an fada miki maganar Alh Sulaiman ko. Wanda kuke aikin gini dashi baba? Eh ya amsa mata. A zuci tace tabdi magini zan aura? Allah Ya kiyaye, itama Mama tsautsayi ya kawota gidan nan. Mal yakubu yace dama tafiya ce ta kamashi amma ya dawo zai zo yau da daddare inji modibbo. Uhmm tace ta wuce bandaki. Wallahi bazai sameta a gida ba ma. Me zatayi da talaka. Haj Bintu tana ta kallon yadda Sulaiman ke shirin fita daga dawowarsa ko abinci bai ci ba. Ina zaka ne don nasan wannan shigar bata zaman gida bace. Hular hannunsa ya gyara Umma gidansu Hanan zani amma da Ammar zan tafi saboda zan kaishi aski. Wato ka dawo zaka nuna min ban iya kular maka da danka ba ko? Yana dariya ya bata hakuri. To ina tsarabarta ko haka zaka tafi? Mata fa sai da ihsani. Zan biya na siyo wani abun a hanya. Hannun Ammar ya kama suka tafi yana ta yi masa hira. Hanan ta rasa yadda zata yi ta fice daga gidansu tunda babanta yaki fita tun safe. In ba rashin aikin yi ba kakkarfan mutum kamarsa ya zauna a gida wuni guda....tayi tsaki. Zaliha tace lafiya. Hararar ta tayi ban sani ba ta bata amsa tare da fita daga dakin. Mal Yakubu na fita zuwa masallaci sallar magriba ta fice ba tare da sanin kowa ba. Alh Sulaiman yana dosar gidan ya fara jin warin kwatar kofar gidan. Shifa harkar warin nan baya kaunarta. Ya rasa dan aike gashi bashi da numbar wayar kowa a gidan.Ammar ya tura ciki ya sanar da zuwansa. Yaro ya shiga kai tsaye dakin da ya hango haske ya nufa. Uwale ce da Sabuwa suke kallo yace salamu alaikum wai daddy na yace ya zo. Sabuwa ta kalli dan kyakkyawan yaron kai kuma daga ina wa ya turo ka? Mal Yakubu ya shigo yace dan Alh Sulaiman ne mai son Hanan. Kirata Sabuwa yana jirantaa soro. Batul Mamman💖 [8/22, 3:15 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰20 Sau uku ta kira taji shiru. A zaune ta tarar da Dije tana gyangyadi kafin Zaliha ta dauko musu tuwo. Shureta tayi da kafa ke kurma tashi...a firgice ta tashi tace mama me ya faru? Ta dungure mata kai tare da rage murya ubanki ne ya faru. Dije ta bata fuska tana nuna kirjinta ubana? Ubana?? Sai hawaye...ke yi min shiru munafuka ana magana sai kiyi ta kallon bakin mutane ina Hanan? Dije tace ta fita tun dazu. Kai yarinyar nan zata ja min masifa ta koma daki ta fadaw Mal yakubu. Ransa yayi matukar baci gashi yar wayar tasa ma ba kudi bare ya kirata. Uwale tace yarinyar nan neman tona min asiri take ga wayata kirata. A kashe suka ji wayar. Bari na fada masa kawai ,ita kuma yau tamu ce ni da ita. Jin Zaliha bata dawo daga dauko musu tuwo ba Dijengala ta duba kitchen bata ganta ba ga yunwa yana cinta. Ita kuwa Zaliha cikinta ne ya kada ta tafi bandaki. Wata tsohuwar naira ashirin ta dauko a kasan akwatinta ta saci jiki zata je siyan wainar fulawa a gidan Zainab makociyarsu. Tana saka kafarta a soron aka dauke wuta, saboda duhu hannunta take mikawa kamar makauniya tana neman hanyar fita, wani mulmulallen abu mai dan gashi gashi taji ta shafa ta tabbatar ba kan daya daga tumakin Sabuwa bane. Ammar data tabawa kai ihu ya saka. Daddy kamani naji an taba min kai. Sulaiman yace ina zuwa Ammar wayata nake nema. Dije sake taba kan tayi don ta tabbatar da abinda ta taba, gashi tana jin kamar maganganu amma ta kasa gane me ake fada. Ihu tasa iya karfinta wayyo Allah baba nayi gamo. Sulaiman tuni ya gano muryar yar kazamar yarinyar nan yace ke rufa mana baki yana neman hannun Ammar su fita. Ta soma kuka Al'Quran naira ashirin ce a hannuna waina fulawa zan siyo a gidan Zainab yunwa nake ji. Gashi don Allah kada ku mayar dani kaza ko doya. Ba shiri sulaiman ya soma dariya...hannun dansa ya kama. Yana jin yadda Dijengala take tsalle da ihu. Mal Yakubu ne ya iso soron da yar fitila. Shima bai kula da su Sulaiman ba don ya zata sun tafi. Dije dena ihu nine...tana ganinsa tayi saurin matsawa kusa dashi tana magana da karfi, baba aljanu ne suke son bude min ido, dansu suka turo min shegu. Kul kike zagi dije...shima baba zuciyarsa ta kusa bugawa daya ji ance daddy mu tafi. Sai a hankali ya gane Alh Sulaiman ne da dansa. Batul Mamman💖 [8/22, 3:16 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰21 Da kyar ya iya tsayar da dariyarsa yace Mal 'yar nan taka tana da abin dariya. Ai nima na tsorata don nayi tunanin kun tafi. Ammar ya nuna takalminsa ne ya kwance na tsaya daure masa sai aka dauke wutar kuma ina tunanin wayata tana mota. Sake sallama suka yi kafin Sulaiman ya gama fita yaji mal yakubu yana tambayarta ina zata.. wallahi baba yunwa ce kuma zaliha bata kawo abincin ba, dama wainar fulawa zan siyo ta ashirin. Dariya yayi haba Dije wainar ashirin ai sai da kiyi kuskurar baki da ita. Me kace baba? Banji ba. Muje na baki nawa abincin kici a daki kada sabuwa ta gani. Daddy mu tafi mana wari nan. Sai a lokacin sulaiman ya dawo hankalinsa yaja hannun Ammar suka fita bakin layin inda yayi parking motarsa. **************** Ashir ya rasa abinda ke masa dadi. Tun washegarin zuwansa banki zuciyarsa ke masa radadi ya rasa dalili. Ji yake kamar ya koma bankin ya nemi yarinyar da ta yi masa magana amma shi ko fuskarta ma bazai iya tunawa ba don bai kalleta da kyau ba. Wata biyu ya rage bikinsa amma yan kwanakin nan baya son ko jin sunan matar da zai aura. Dama dai auren baya gabansa don shine na uku ma. ba ya dadewa da mata suke rabuwa, hakan na damun yan uwansa shiyasa wannan karon babansa ya yanke shawarar hada shi da yar kaninsa da mijinta ya rasu shekaru shida da suka wuce, wato sakina mahaifiyar Ammar. Gidansu Ashir suna da rufin asiri dai dai gwarwado. Lokacin da ya fara aikin kwangila ga aikin office shine kudi suka zauna masa sosai. Kasa nutsuwa yayi karshe ya yanke shawarar zuwa bankin a daren bayan yayi magriba a kofar gidansu. Hanan na sauka daga adaidaita sahu suka hada ido da mutumin da take ta nema. Gabansa ne ya fadi yana ganinta. Banda kyawunta wani yanayi ya shiga mai wutar fassara. Idan bai auri yarinyar nan ba rayuwarsa tana cikin matsala. Har wani gumi ke keto masa. Karasawa yayi inda take ba tare da yayi mata magana ba ya mikawa dan sahu dubu daya yace mata zo mu karasa bakin motata. Ba musu ta bishi...lallai aikin Babba yayi kyau. Batul Mamman💖 [8/22, 3:16 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰22 Bude mata yayi ta zauna a seat din gaba. Shima yana zama yace me ya fito dake a daren nan? Ta rausayar da kai tana kare masa kallo, ga kyau ga kudi.ready made kenan..kai ya kamata nayiwa wannan tambayar. Hmm ina jin abinda ya fito dani ne ya fito dake. Me kenan

Chapter 3 of 4