Share this page
2 / 4
tubure tace sai Mal Yakubu ya shigo dakinta ranar girkinta. Batul Mamman💖 [8/22, 3:02 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰7 Haka rayuwa ta kasance a gidan Mal Yakubu yau fari gobe tsumma a wajen Munari. Ba don soyayyar da suke ma juna ita da mijinta ba da tuni ta bar gidan. Sabuwa na kwance a kofar dakinta da daurin kirji tana shan rake Uwale ta fito daga bandaki tace kai sabuwa ki raba kanki da zaki fa saboda nakuda. Kinji ki Inna kamar wata sabon shiga? Haihuwa ta uku har sai kin karanta min yadda zanyi? Ta yatsina fuska ke fa daya kawai kika yi ta tsaya miki cak. Munari daga cikin dakinta tace Allah Ya kara ta cigaba da yiwa yarta Ramlah kitso. Uwale har wani tsoron sabuwa take ta ajiye butar hannunta tace to Allah Ya baki hakuri uwar biyu. Wannan ciki naki badai girma ba. Gaban Sabuwa ya fadi ita bata taba ciki mai girman wannan ba ma gashi a karyar da tayi baifi wata bakwai ba. Bata sake tankawa Uwale ba don kada a ja maganar ta cigaba da shan rakenta. Bayan sati uku wata rana Uwale da zulai sun fita unguwa tun safe nakuda ta kama Sabuwa. A muguntar Uwale kulle gidan tayi ta waje wai kada munari ta fita saboda taji Mal Yakubu yana cewa ta dawo da wuri tasan sarai unguwa zata. Da munari ta shirya ta shirya yarta zasu fita taji kofar a garkame. Ta gaji da ja ta dawo daki rai a bace. Dama gidan kanwar Inno zata je ziyara. Tana ajiye gyalenta taji kamar ana kiranta daga dakin Sabuwa. Shiru tayi ta tabbatar sannan ta fito cikin sauri. A kwance ta ga Sabuwa tana nishi da kyar duk ta hada gumi duk da sanyin gari. Munari jika na rawa don itama bata saba ba tace Sabuwa kinga Inna ta kullemu ta waje kuma saboda zurfin soro babu mai jinmu kiyi hakuri na dubaki. Cikin masifa tace kiji dadin kasheni ko...ki fita ki nemo taimako Munari don idan na mutu sai nayi miki fatalwa. Babu irin bugun da Munari batayi ba babu wanda yazo kashe reza ta samo a daki ta dawo kan sabuwa. Tace kiyi hakuri inajin bakwaini zaki haifa don kai ya fito. Da taimakon Allah Munari tana ta yi mata addua ta samu Sabuwa ta haihu. Yarinya ce santaleliya fara tas irin wadda Uwale take so. Munari ta yanke cibi ta taimaka mahaifa ta fito. Kai Sabuwa wannan 'ya da takai wata tara ban san irin girman da zata yi ba. Ruwan wanka ta dora ta wanke jaririya ta kaiwa sabuwa ruwan wanka. Sai bayan laasar Uwale da zulai suka dawo. Tun daga tsakar gida uwale ke yiwa Munari dariyar keta ta hanata fita. Munari ko a jikinta tace Inna kinyi kawa fa. Ko kulata bata yi ba harda tsaki zata wuce tace Inna nace kinyi kawa fa Sabuwa ta haihu. Zulai ta yi dakin cikin sauri Uwale tana binta tana cangala kafa. Allah Kasa fara ce, Allah Kasa fara ce. Haka take fada har ta shiga dakin. Baby ta dauka ta rungume. Yarinyar akwai kyau ga hasken da Uwale ke buri. Zulai ta rike yarta. Sabuwa bakwaini kika haifa? Me ya faru haka? Waya karbi haihuwar? Sabuwa tace nakuda ce ta kamani gashi kun kulle gidan. Munari ce tayi komai, Uwale ta rungume yar ta fita. Munari ta gani tana kwasar tuwo ta dan saki fuska nagode fa Munari sannu da kokari. Zulai da ta gama zige yarta a cikin daki ta fito da sauri wace godiya zakiyi mata uwale? Ashe kina fita ta kama Sabuwa da kokawa shine haihuwar tazo ba shiri. Ai don kada a kamata da laifin kisa ta karbi haihuwar. Uwale ta bata rai muguwa azzaluma da mai kyan zaki kashe min. To ta Allah ba taki ba baka mai bakar aniya. Tuwon ma bazata ci ba kada kisa guba. Kwashe abinki ki bace min da gani. Hawaye ne ya saukowa Munari ta je har kofar dakin ta leka Sabuwa na kwance a kan gado. Cike da takaici tace Sabuwa abinda zaki saka min dashi kenan ko? Allah na gani kuma baya bacci. Zulai tayi tsaki muguwa kinga farar haihuwa kina bakin ciki. Mal Yakubu dai yayi farinciki daidai gwargwado yace to Inna sai asa mata sunanki ko. Tunda kan Ramlah kika ce kada asa sunanki. Uwale tace yo haka kurum zaka sawa wancan mummunar abar sunana? Ya jawo abarsa ya rungume suk yaransa yafi sonta. Inna tace itama wannan bazaka sa mata sunana ba saboda kyanta. Akwai sunan gayu dana taba ji wallahi wata rana dana je gidan Harira jikanta ya kunna talabijin. Sabuwa tace ni fa Inna kada ki bata wa yata suna. Inna tace ni dai Hannan naji an fada ai ko yayi dadi ko? Sabuwa ta bata fuska Hannan kamar marowaciya Hanan ake cewa. Na yarda Malam a saka mata. Mal Yakubu yace to Allah Ya raya ya dauki Ramlah ya tashi yayi waje. Ranar suna aka radawa yarinya suna Hanan. Uwale sa guda ta bayar aka yanka cikin shanunta uku. Anyi bushasha ranar suna kamar haihuwar fari. Yan uwan Sabuwa suna ta zuba habaici ga Munari. Ga 'ya mai goshin arziki an haifa. Haka dai akayi ta taro Munari da nata yan uwan suna daga cikin daki. Yayar sabuwa na suyar nama ta bawa duka yaransu aka tsallake Ramlah. Ta rinka binsu da kallo har Uwale ta kula tayi tsaki ai idan baki bata ba Hanne yarinyar nan kamar mayya sai tasa ki kone da mai. Cillo mata kashi ta gwaigwaya. Hanne ta dauko wani guntun qashi ta jefawa Ramlah. Qashin bai zame ko ina ba sai bakin rijiya Ramlah ta bishi da dan gudunta. Tana zuwa bakin rijiyar takalminta daya ya zame daga kafarta santsi ya kwasheta sai cikin rij[truncated by WhatsApp] [8/22, 3:03 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰9 Sai da cikin Munari yayi wata shida Uwale da sabuwa suka san dashi. Gaba daya Sabuwa hankalinta a tashe yake tana tsoron kada Munari ta sake haihuwa hankalin Mal Yakubu ya koma kan abinda ta haifa. Yanzu ma kamar yasan Hanan ba yarsa bace baya bi ta kan ta sai Inna Uwale ta dame shi. Ita kuwa kullum tana rike da ita a tsakar gida ko dakinta tana mata waka. Hannan farar jikar Uwale. Zaki auri mai kudi mai mota,zaki kaini makka da madina. Duk wahalar da Munari ke sha saboda cikinta yakai watan haihuwa Uwale bata daga mata kafa akan girki ba irin yadda aka yiwa Sabuwa gata. Ganin aka Mal Yakubu ya siyo risho har biyu yasa a kitchen din. Uwale bata san dashi ba sai da ta fito da goyon Hanan tana ta cangala yar kafarta. Eyye me zan gani haka? Fito fiti kinibabbe ta kirawo Mal Yakubu daga daki. Wato don munafurci shine zaka wani siyo risho saboda matarka ta dena wahala ko? To ban yarda ba. Ni nafi son abincin da aka dafa da itace. Yafi dadi da inganci. Sabuwa tace a'a fa inna waye baya son sauki ni gaskiya nafi son rishon. To...to ai shikenan saboda kada fatarki tayi duhu a bakin murhu ba. Ta harari Munari kunyi sa'a uwar mai kyau tana son rishon ba don haka ba da kunga tsiya wallahi. Kamar kullum shi dai Mal Yakubu sai aikin bada hakuri. Tun dare Munari ke fama da ciwon baya kadan kadan tana daurewa. Zuwa asuba abin ya ta'azzara gashi ba girkinta bane. Da kyar ta iya mikewa ta bude kofar dakinta. Dakin Inna uwale ta nufa tana tafiya da kyar. Tana ta kwankwasawa Uwale na jin muryarta ta sake gyara kwanciya....aikin banza haihuwa ta hudu ai zaki iya da kanki. Haka ta koma kofar dakin Sabuwa tana bugu. Mal Yakubu ne ya fito ya kamata zuwa dakinta yace Sabuwa ta tashi Inna su kula da ita sannan ya fita zuwa gidan makocinsa mai akori kura ya taimaka masa su tafi asibiti. Yana dawowa daga bakin kofa ya jiyo kukan jariri. Da gudu ya karasa ya ganta kwance kan tabarma ita kadai da baby a gabanta. Duk ya rude yace bari na kira Inna...hannu ta daga masa barshi kawai Malam ga reza can dauko ka yanke cibiyar. Su kadai suka yi abinsu su Inna ko leqe. Ya fita ya bawa makocinsa hakuri ya dawo ya buga kofar daki cikin fushi. sabuwa ki fito kafin na shigo dakin nan don wallahi na shigo jikinki zaiyi tsami. Ta fito tana mika...yanzu don wulakanci ince ki tashi inna ku taimakawa Maimunatu sai ku barta ita kadai? Inna ta fito dan nan ni kake cewa munyi maka wulakanci? To mungode Baba sai ka fadi me kake so muyi yanzu. Inna ni ba haka nake nufi ba amma ai ko sannu ayi mata. Sannu maigida to me aka samu? Mace ce ya fada ya kasa boye murnarsa. Batul Mamman💖 [8/22, 3:05 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰8 Salati da ihun mata yasa su Munari fitowa daga daki. Mata na ganinta suka yi cirko cirko an rasa mai magana tana ta tambayar me ya faru. Uwale tace ni dai ba ruwana ,fa bani bace. Munari tace wai meye ne? Me kuke leqe a rijiyar? Wata makociyarsu ce tayi karfin halin fada mata...Ramlah ce ta fada. Wata kururuwa Munari tayi cikin zafin nama ta nufi rijiyar ana rirriketa. Tani tace cikin rudewa garin yaya ta fada? Wata yar cin shinkafar sunan tace qashi ne Hanne ta jefa mata bakin rijiya shine ta bishi ta fada. Mal Yakubu aka fita kira a majalisarsu. Munari tun tana kuka da sauti har muryarta ta dashe....wayyo Allah kawai take cewa. Abin tausayi ta zama. Mal Yakubu ya shigo yana tambayar me ya faru ake nemansa. Munari ta mike ta rije wuyan rigarsa. Baban Ramlah idan na rasa 'yata bazan zauna a gidan nan ba. Yi hakuri ki fada min abinda ya faru. Wani yaro yana cin nama yace 'yarta ce ta fada rijiya. Mal Yakubu yace Ramlah? Babbar riga ya tube zai shiga shima aka rike shi. Uwale ta soma kuka don Allah dan nan kada ka shiga kaima ka mutu. Suna haka Sabi mai hakar rijiya ya shigo da wasu maza. Igiya mai kauri aka daura masa ya shiga. Duk sakan a wurin su Munari tamkar shekara suke jinsa. Kamar wata zautacciya haka ta koma. Sai bayan kusan minyi goma ya fara jan igiyar. Cikin sauri aka jawo shi da Ramlah a kafadarsa. Mal Yakubu ya karbe ta ya kwantar akan tabarka. Cikinta ya danna ruwa y rinka fita ta bakinta da hanci. Munari ko wurin bata je ba tana zaune inda wasu mata suka riketa ta share hawaye Allah Ya jikanki Ramlah kawai take fada. Duk yayi iya yinsa ya tabbatar yarsa ta rasu. Cikin kuka ya bude hannun da yaga ta damke sosai. Qashin data dauka ne ashe ba rabonta bane. Wace 'yar....din ce ta jefa kashin bakin rijiya? Jin kowa yayi tsit ya sake kunduma zagi cikin tsawa. Aka samu wata ta nuna Hanne. Kanta yayi kamar zaki cikin fushi wani abokinsa ya rike shi. A tsorace tace Uwale ce tace min mayya ce na jefa mata qashi shine tautsayi yasa na jefa bakin rijiya. Suna wannan fadan Munari ta dauke gawar yarta ta kai daki ta fara shirin yi mata sutura. Taron suna ya koma na mutuwa ita dai Uwale tayi tsit don yau dan nata ya bata tsoro. Yana matukar son Ramlah sosai. Bayan an tafi kaita ne Munari tana zaune gaban iyayenta da suka zo ta fara jan numfashi da kyar. Mal Yakubu aka kira ya zo ya fitar da ita a rude. Ya kalli innarsa cikin bacin rai. Idan itama ta mutu yau zan saki Sabuwa kuma ta tafi da yarta bana so. Asibiti suka nufa inda likita ya tabbatar jininta yayi mugun hawa kuma tana dauke da ciki na wata daya. Duk da bakin cikin dake damunsa Mal Yakubu yayi matukar murna. Ta taga yake leken matarsa saboda ance a barta ta huta sosai. Yana adduar ta sami lafiya. Bayan kwana takwas da rasuwar Ramlah Inna Ladi tazo gidan da sauran yaransu mata hada kayan Munari. Mal Yakubu yana ta bada hakuri yana zubar da hawaye. Inna Ladi tace kaga ka bari mu tafi ta laluma kafin yayanta ya zo kaima tunda baka ganshi ba kasan baya gari ne. Kiyi hakuri inna ya zan saki Maimuna a wannan lokacin ga rashin 'ya ga kuma rabo a tare da ita. Inna Ladi ta kalle ta Munari da gaske ne? Kanta ta sunkuyar kasa sai hawaye. Yi shiru kinji kada ciwonki ya tashi. Ta dubi Uwale dake zaune tana yiwa Hannan rawa Sabuwa tana bacci a daki. Yakubu kasan kashe min jika akayi da gangan muka hakura yanzu haka zata zauna cikin bakin cikin rayuwa a gidanka? Kiyi hakuri inna babu fa wani yanayi mai dorewa. Zan kula da ita muddin raina bazan bari wani ya wulakanta ta ba,yana magana yana kallon Inna Uwale. Ta dago kai nasan dani kake dan nan ka cigaba da zargina don kawai yarka ta mutu. Ba ga wata Allah Ya baka ba? Girgiza kai yayi ya cigaba da bawa su Inna hakuri. Tun daga lokacin babu me shiga harkar Munari a gidan saboda yadda iyayenta suka sa musu ido. Sai habaici daga gefe. Mijinta kuma yana nuna mata so da kulawa sosai suna ta rainon cikinta cikin sirri. Wata rana suna cin abinci tace ni kuwa Mal meyasa baka so su inna su san ina da ciki? Munari kenan ai ba murna zasu yi ba. Karshenta a rinka yin abinda zaa bata miki rai har ciwonki ya tashi. Ko kin manta Yaya Salihu yace duk ranar da jininki ya hau ko zanyi kukan jini sai na sakeki. Dariya tayi masa aikuwa gobe zanyi masa aike. Au tsokanata ma kike ko? Zan rama ne... yanzu dai kiyi ta sa hijab da zaman daki so nake kawai Inna taji haihuwa. Allah ba don darajar ta haifeni ba da tuni nasa an daure....hannu tasa ta rufe masa baki. Haba Mal? Ka manta Allah Yace kada mu fadi kalma mara dadi game da iyayenmu? Kada ka manta kwananta ne ya kare mu kuma hakurinmu shine ladanmu. Hakane Munari nima yau na dana. Allah Yayi miki albarka Ya saukeki lafiya. Amin M[truncated by WhatsApp] [8/22, 3:06 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰10 Inna uwale ta tabe baki sai mace ta takarkare ta haihu amma karshe kaga bakin jariri. Allah Ya raya dauko min abin na gani a nan bana son doguwar tafiya saboda kafa. Ba musu ya je ya dauko mata 'yar da kansa ya kawota. Ba yabo ba fallasa itama dai bakar ce amma ba sosai ba gata kyakkyawa kamarsu daya da mal Yakubu. Inna tana kallonta ta mika masa gata nan bari naje nayi sallah. Ita kuwa Sabuwa ko kallon yar bata yi ba ta juya zata koma daki. Dawo nan ya daka mata tsawa. Wuce kije ki dora mata ruwan wanka. Inna uwale tace ka ma isa...ita da take da jaririya. Dama ai gasa ce tasa munarin haihuwa yanzu. Girgiza kai yayi cike da takaici yaje ya dora ruwan da kansa. Daga ranar 'yan uwan munari ke yi mata komai. Ana saura kwana biyu suna tace Mal wane suna zaka saka mata ne? Haba munari ai shawara zamuyi dake. Ta sunkuyar da kanta kasa nasan wanda ya mutu baya dawowa amma inda hali a saka mata Ramlah. Murmushinsa ya fadada dama haka naso ina dai tsoron yi miki fami ne. Allah Ya raya mana ita. Tace amin. Uwale dake bakin kofar dakin ita da Zulai wanda dama gulma suka zo ji ta shigo tana matsar kwalla. Yanzu dan nan ko kara bazaka min ba kasa sunana sai zabin matarka. Inna ke fa kika ce ba kya so tun a haihuwar marigayiya. Akan Hanan ma kika sake cewa bakya so kika zaba mata wanan sunan. Ta dan fito da ido ni dan nan? Abin harda sharri? To ba damuwa ka saka mata sunan da kake so. Tana juyawa zata fita Munari tace haba Inna kiyi hakuri sunanki za'a saka mata. Ba haka inna uwale taso ba, so tayi Munari ta ce bata son sunan sai ta hadasu fada da Yakubu. Tsaki tayi ta fice Zulai na rufa mata baya. Duk da abin baiyiwa munari dadi ba sai ta nuna wa Mal Yakubu jindadinta sosai. Ranar suna aka radawa yarinya suna Khadija. wata yar uwar baban Mal yakubu ce tazo ta karbi jaririyar wanzami yazo za'a cire mata beli. Uwale ta gama lura da yadda munari ke matukar kaunar jaririyarta sai ta fita wurin wanzamin tare da waziriyarta zulai. Basu dade da fita ba aka jiyo sautin kukan Khadija da katuwar murya kamar zata shide. Mata an sami abinyi suka yo soro da gudu. Tani ce kan gaba tana zuwa ta tarar uwale ta kwaye gefen fuskarta wanzan yana kallon kalangunta ya fara zanawa jaririya a gefen fuskarta na dama. Fizgota Tani tayi ta koma cikin gidan da sauri. Munari ta karbeta zata bata nono amma taki karba sai wani irin kuka take. Har dakin Uwale ta biyosu. Amma Tani baki da ta ido. Yanzu nace ayiwa yarinya kalangu zanen fulani irin nawa shine zaki dauketa. Munari tana hawaye tace yanzu Inna duk gidan nan wa aka taba yiwa zane a fuska shine zaki ce ayi mata. Au kema rashin kunyar zaki min? Bani ita a karasa mun barshi a zaune. Munari tasa zani ta goya yarta tana ta kuka. Wallahi Inna idan kinga anyi wa yarinyar nan zane a fuskarta to mutuwa nayi. Ya kike so nayi da raina ne? Matsalar yau daban ta gobe daban. Allah bari Mal ya dawo idan mutuwar aurena ce tazo sai dai na tafi da yata. Zanen nan fa Allah Ya tsinewa maiyi da wanda akeyiwa. Kuka wiwi Uwale tasa ita a dole anyi mata rashin kunya. Nufinki Allah Ya tsine min ko? To yau zanga wanda dan nan zai zaba cikin mu biyu. Daga gefe wasu mata suka ce gidan uwale duk taron suna sai anyi dirama. Ai munari ta kyautawa kanta yau. Batul Mamman💖 [8/22, 3:09 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰11 Wasa wasa har magariba ta gabato ana ta mayar da zance a gidan Mal Yakubu. Shi dai tun a kofar gida da labari ya riske shi komawa yayi ya kira wan babansa Baba Hadi. A tsakar gidan ya tarar dasu gaba daya da sauran mata 'yan jin kwakwaf. Baba Hadi na shigowa yace duk su fice su bar gidan. Sum sum suka rinka fita daya bayan daya. Ba dai haka aka so ba don sun so jin yadda zata kaya aji dadin ba da labari. Suna fita Inna Uwale cikin kuka take labarta masa abinda ya faru. Baba Hadi yace ba matsala ke Munari bani yar . Ba musu ta mika masa jaririyar bayanta. Yace to Yakubu karbo yayarta ya nuna Hanan dake hannun Sabuwa. Bari na sa Yau ya kira wanzamin duk sai ayi musu. Shima Sadi idan suka zo gari sai a karbo shi a yi masa. Uwale ta wurgo kafa cikin sauri bangane ba Yaya Hadi wai harda Hannan za'ayi wa? Eh ya amsa a takaice. Dukkansu ba jikokinki bane? Tayi tsuru tsuru da ido...anya ayi harda ita? Sabuwa ta ce Al-Quran ba za ayi mata ba. Mal bani 'yata. Baba hadi yace au ita wannan da baki isa da uwarta ba shine zaki ce kada ayi mata, amma ita munari ko kadan baki damu da lamarinta ba? To wallahi ki fita idona Uwale. Akan yadda kike takurawa matar yaron nan zan nuna miki ni ba marigayi bane. Shine yake jure halinki na tsiya. Kai ta sunkuyar kasa bata ce uffan ba. Ya mikawa munari yarta. Ki kara hakuri kinji Maimunatu. Allah Ya raya muku yaranku. Tana ta godiya ya fita Mal ya raka shi. Tun daga lokacin uwale ta kara kunnawa Munari karan tsana. Duk lokacin da Mal Yakubu ya fita sai wulakanci kala kala. A can birni kuwa Yaya Salihu yasa Sadi a makaranta tare da yaransa. Lokacin da Ummita ta shiga wata na ashirin da haihuwa Munari tayi shirin yayeta. Wata rana tana kwasar tuwo Ummita tana ta zillo a bayanta. Tace haba mamana so kike na kona hannu ne? Uwale wadda tuni zulai ta bata shawarar yadda zata kori munari daga gidanta ta daga waje ni kuwa munari kin fiye kinibibi yaushe ta zama mamanki. Na zata sunan uwarki Baraatu. Munari tayi murmushi Inna ai kema uwata ce. To indai haka ne daga yau tunda dai nike da iko da kowa a gidan nan yarinyar nan zaa rinka kiranta Dijengala. Ni na tsani suna Ummita dinnan. Gara dai a kirata dijengala a gargajiyance. Munari tace to ba komai inna ai yadda kike so haka zaayi. Ba haka inna uwale taso ji don fada tazo takala. Sabuwa ta fito daga dakinta tace inna kinji da yadda ta amsa miki kuwa? Ai gatse tayi miki. Allah Ya kyauta uwar miji ace bata isa da surukarta ba. Ni kina ji ai sanda ta sawa tawa yar suna. Wannan ma idan na haife ita zata sa suna. Munari dai bata kula ba don tasan neman rigimar tasu ne ya tashi. Da Uwale taga haka zama tayi a wurin sai da mal yakubu taji sallamarsa tasa kuka. Karya da gaskiya ta rinka hada masa Sabuwa na mara mata baya. Ganin ko kadan bai yarda ba tace kai na gaji so nake indai ba tare na haife ku ba ka saketa ta koma gidan ubanta. Munari ta soma hawaye tana bata hakuri. Ta tabe baki kyayi kya gama. Yau abincinki ya kare a gidan nan. Idan baka saketa ba yanzu a gabana ba wallahi sai na tsine maka albarka. Haba inna ya kike so nayi ne? Babu abinda kike nema da bana miki. Don Allah kiyi hakuri. Itama kukan tasa masa idan baka saketa ba Allah Yakubu zan maka mugun baki. Naki jinin bakar matar nan. Ka saketa yanzu. Munari tace mal idan kana son gamawa da duniya lafiya kabi umarnin Inna. Yana kuka tanayi yace na sakeki saki daya. Wani kukan ne ya zo mata da karfi ta shiga daki dauko mayafi. Inna don ta kara kuntata mata tace kwanto goyon ai ba dashi kika zo ba. Dama yar ta isa yaye. Munari ta kalli mal yakubu yace Inna don Allah. .hannu ta daga Allah Ya tsi....da sauri munari ta kwanto yar da take matukar so ta bashi ta fita daga gidan cikin kuka. Batul Mamman💖 [8/22, 3:10 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰13 Da gudu ta karasa don yau akan wannan yar Mal yakubu yana iya karairaya ta. Tana dagota wani irin tari ta rinka yi har uwale ta jiyo su ta fito. To 'yar nema zaki fara sanaar tarin ne....kai lafiya sabuwa me ya faru? Wallahi Inna bansani ba. A cikin robar wanka na ganta. Na shiga uku na yau a gidan nan. Ba kuka zakiyi ba dauko gyalenki mu kaita kemis. Kila ruwa ta shaqa. Su 'ya'yan munari kamar kifaye kowa ya tashi mutuwa sai ya tsumbula ruwa. Basu tarar da mai kemis ba dole suka wuce asibiti. A nan Mal Yakubu ya hadu dasu bayan dan aiken su inna ya riske shi. Likita yace gaskiya Mal akwai ganganci a tare daku. Yarinyar nan ba karamin kamu sanyi yayi mata ba tun kafin yau. Sannan idan ta tashi za'a sake yi mata wasu gwaje gwajen amma gaskiya a yadda na fahimta kunnuwanta sun tabu. Da kyar zata ji kamar da. Shi kam mal yakubu sarkin hawaye har ya fara. Sabuwa taci fada don ma inna ta tsaya mata ne. Karshe yace idan ta sake bari wani abu ya sami yarsa sakinta zaiyi ya hadata da hukuma. Labarin abinda ya sami Dijengala ya sami su Inno. Hanawa sukayi a sanar da munari son kada tace zata taho tunda ta fara karatu a wata makarantar addini. Inna Ladi da ce taje gidan ta bukaci a basu ita tunda basa sonta. Bayan doguwar muhawara tace su jira shammaci daga kotu. Wannan kalami nata na karshe ne yasa Zulai ta bawa Uwale shawarar suje wurin wani malami a dauke musu hankali daga kan Dije. Anya ayi haka Zulai? Nifa gaskiya bana son inyi shirka. Haba Uwale malami ne fa ba boka ba. Ai irin malaman nan ba bokaye bane, suna da ilimin islama gashi idan kika je zaki ga littattafai da carbi kala kala. Sannan idan kika bari aka shiga kotu daurin shekaru zasu yi miki duk da tsufanki da yar kafarki. Tuni Uwale ta tsorata .A haka ta ja raayin Uwale suka je wurin malamin. Bukatarsu biyu ce. Mal Yakubu yaso Sabuwa ya hakura da abinda ya faru sannan Munari da 'yan uwanta a dauke musu hankali daga kan Dije da zancen zuwa kotun nan. Ya kasance munari ta manta ma da yar tata gaba daya. Batul Mamman💖 [8/22, 3:11 PM] +234 812 673 9684: FARAR HAIHUWA💰12 Cikin kuka ta shiga gidansu da sallama. Inna Ladi ta ajiye butar hannunta ta taro ta. Me ya faru Munari? Ta shafa bayanta taji ba goyo. Ina 'yar? Ba dai ta mutu ba. Munari ta kasa magana sai kuka. Inno tace wai ba magana ake miki ba. Inna ya sakeni, inna uwale tace idan bai sakeni ba zata tsine masa. Innalillahi wa inna ilaihi raji'un. Ita kuwa Uwale tana son gamawa da duniya lafiya? Ina ruwanta da zaman ku inji Inna Ladi. Inno dama bata saka baki a lamarin gidan yarta saboda kara amma yau bakinciki ya isheta. An sako mata 'ya da magaribar fari. Tace ina goyon. Munari ta sake fashewa da kuka tace ba dashi nazo ba. Inno tace Alhandulillahi in anyi duniya don Manzon Allah SAW kin bar gidan Yakubu har abada. Saurin dago kai

Chapter 2 of 4