kai na a sunkuye na ce"mama wai ce wa ya yi yana sona".da sauri mama wai mama sona ya ke mama".
"khairat kinfi kowa sanin ce wa bara'atu fa ya ke so,tun kafin a gane kuna tare dashi ki rabu dashi don gaskiya ni bana son tashin hankali".
GyaƊa kai kawai na yi don nima daƊin hakan na keso,don ni zuciyar nan tawa A.D,Ne kawai acikinta ma'ana yaya Bilal.
****
sosai filin saukar ya cika ana sauraran Ƙira'ah mai masifar daƊi daga bakin jikar hajiya kaka ABIN CIKIN ƘWAI,wato khairat da yawan mutane hankalinsu na kan khairat yawancin mazan wajen kuma ce wa suke dama khairat ta zama matarsu don yarinyar Allah ya yi mata baiwa sosai,khairat dai ba wata mai Ƙyau ba ce,tana dai da baiwa sosai diri tana da shape wanda ake ce wa coca cola shape ga wani dimfil wanda ya Ƙawata doguwar fuskarta,kuma ita dai ba fara bace kamar sauran Ƴan gidansu,amman tana da baiwa ta ilimi na arabi da boko.
abin mamaki da aka kira jidda wata Ƴar ajinmu da Ƙer ta kai karatun saukar na ta,amman wai sai mukaji ana sanarwar wai wani wanda ake kira da ADMIRAL BILAL ABDULLAHI,wanda aka fi sani da A.D ya bata Ƙyautar mota.
Sosai kowa ya yi mamakin jin hakan duba da irin yadda karatuna ya Ɗauki hankalin mutane da dama,kuma nima na samu Ƙyautuka sosai ciki har da Ƙyautar wata hamshaƘiyar computer wanda Ɗan majalisa ya bani,sannan na samu Ƙyauta ta dubu Ɗari biyu daga hannun wani mai kuƊi.
har muka dawo gida zuciyata tana wajen Ƙyautar da yaya Bilal ya bawa jidda Ƴar ajinmu.
To me ye tsakanin jidda da yaya Bilal?babu mai bani amsar hakan,don haka na zubawa sarautar Allah ido ammab zuciyata sai kai kawo take,saboda tunanin abunda ya shige min duhu.
satin bikinsu Rashida ya kama,sosai ƘwaƘwalwata ta yi busy duk hankalina kacokan yana kan bukin,ni da maryam ne manyan Ƙawayen amarya don haka tare muke komai.
Wata rana ranar da bazan taƁa mantawa da ita ba,ita ce rabar dinner Ɗinsu rashida,yaya Bilal naga ni da jidda ya sama mata kujera ta zauna tasha anko irin namu sak,onion color ne material Ɗin sai mukayi pitet gown amman ita jidda riga da siket ta saka wanda sukayi masifar yi mata Ƙyau.
Sosai jikina ya ke rawa hankalina idan ya yi dubu to ya Ɓaci,wasu zafafan hawaye masu zafi suka zubomin,na fito daga wajen baki Ɗaya,na samu wani wajen flower's kuraye shar,na tsugunna na fara wani irin kuka mai tsanani,ina jan doguwar rigar dana saka kamar ita ce ta yi min laifin.
Dafa kafaƊa ta naji anyi,maryam ta bayyana agaba na,ta Ɗago haƁa ta cikin tausayi sannan ta ce"ki yi haƘuri khairat naga duk abinda ki ka gani,amman ina son ki daurewa zuciyarki ki yi haƘuri don Allah a Ƙarasa bikin dinner Ɗinnan kada kowa ya gane abinda ke faruwa,shi so haka ya ke yana da zafi musamman idan wanda ka keso baya sonka,to tabbas zaka shiga wani hali,nasan abinda ki keji tunda nima na taƁa shiga irin wannan halin."
ta damƘe hannuwa na sannan ta ce"khairat ina tare da ke ako ina insha Allah sai kin auri yaya Bilal,ni Ɗinnan zan tsaya miki insha Allah",Ta kalleni tana saukemin idanu itama duk hankalinta atashe amman kuma tana dauriyar dannewa saboda ni.
Nan dai ta cigaba da rarrashi na ta bani hoda na Ɗan shafa saboda kada a gane kukan dana yi.
yaya salim yana zuma akan kujera,mero wacce take ta faman zuba ita da wata Ƴar Ƙyauye irinta,ga kuma wani lemo a hannunta tana ta faman zuƘa kamar za ta shanye har da bottle Ɗin.
Tsi ta zubawa yaya salim a jikinsa duk ta Ɓata mishi kayansa,da sauri ya tashi alokacin yana waya da budurwarsa mai suna salimat yana jiranta ta shigo reception Ɗin,da sauri ya tashi yana karkaƊe lemon daya zube masa a fuskarsa,ya kalle mero wacce duk ta Ƙwalalo mishi fici ficin idanuwanta,tsoro ya cika ta sosai da gudu ta shiga cikin mutane,ya neme ta bai ganta ba dole ya koma gida ya canjo kayan jikinsa,amman fa ya shirya abinda zai yi wa mero,sai ya gyara mata zama.
Hajiya kaka kuwa wannab karon ciwon Ƙafa take shiyasa bata zo ba,anci ansha amare kowa fuskarsa da annuri,amare har 10 kuma duk agida Ɗaya.
Sam mamana bata son ayi min auren zumunta don ita a ganinta mai makon ya Ƙara zumunci,sai dai kaga zumuncin na neman taƁar Ɓarewa musamman ita da ba sonta ake agidan ba,duk don kasancewarta inyamura kuma tuba ce.
[02/09, 20:52] Ummu Maher(Miss Green): koda muka dawo gida rufe kaina na yi aƊaki nasha kuka na,son raina maryan sai buga Ƙofar take tana yimun magiya akan na buƊe amman naƘi buƊewa don kukan shine solution na samun sauƘi a cikin zuciyata.
washe gari ranar yini ranar ne na Ƙara kuka irin wanda ban taƁa yin irinsa ba,don alokacin muna Ɓangarensu rashida,jidda ta shigo ta gaida iyayenmu,kowa yana ce wa budurwar Bilal ce don jiya awajen dinner ya nuna ta,har Ɗakinmu ta shigo ana ta hira,wuf na fice daga Ɓangaren,ina fita kuwa maryam ta biyoni,daga baya sai ga rashidan da kanta,rarrashi na suka dingayi amman ranar har zazzaƁi sai da na yi,muna cikin hakan yaya Bilal da maryam suka fito,shine ya tuƘa ta har zuwa gida.
Tun suna rarrashi na har dai suka gaji,zazzaƁi mai zafin gaske ya rufeni har aka kai su rashida gidajensu ban san me ke faruwa ba,duk sanda zanyi sallah sai na roƘi Allah ya cire min son yaya Bilal tunda shi baya sona,amman kuma madadin ya fita,sai kuma Ƙara Ƙaruwa ya ke,Allah kaƊai na ke roƘo Allah yasa wannan karatun da zan fara in aika ta abin arziƘi saboda wannan damuwar da ta kunnomin kai.
***
wayar Bilal ce ringing fitowarsa daga wanka kenan daga ashi sai tawul,ya ruƘo wani a hannunsa yana goge gashin kansa har zuwa wuyansa.
muryar captain yaji bakinsa yana kakkarwa ya ce"A.D ka yi gaggawar fitowa yanzu,Ɗan gidan Damas ya zo unguwarmu ya Ɗauke wata yarinya Ƙarama Ƴar shekara sha huƊu,kuma kasan halin tumasancinsa sai ya yiwa yarinyar nan fyaƊe,na yi ƘoƘari na bi sawunsu na gano yana sharaton hotel."
Cikin tashin hankali ya sanya kayansa,zuciyarsa na wani irin bugawa,tabbas yau sai ya kawo Ƙarshen shaiƊanin Ɗan gidan Alhaji Damas wanda ubansa ke ɗaure masa gindi akan komai.don ko shara'a ba ayi dashi don suna da kuɗi da kuma ɗaurin gaba a ƙasar baki ɗaya.
Ya yi nasarar kama Aliyu wato ɗan gidan Damas.har ya fara yagawa yarinyar kayanta Allah ya kawosu.
Kai tsaye captain ya ce mu ɓoye sa kada mu bari ubansa yasan inda ya ke."
ƙwanan Aliyu uku ba'asan inda ya ke ba,hankalin Damas baki ɗaya ya tashi,sai da suka tabbatar sun yi wa Aliyu dukan ba ta kashi sannan Bilal ya danna wayar Aliyu ya kira Damas ɗin da i'ta.
Hankalinsa ya tashi sosai da jin muryar ɗansa,jikinsa na rawa ya tambayi abinda su Bilal ɗin suke so.
Anzo wajen don daman abinda suke jira suji kenan,sai kuwa Bilal ya ce"so na ke ka jawa ɗanka kunne sosai akan lalata ƴaƴan mutane da ya keyi,idan ba haka ba rayuwar ɗanka tana cikin mummunan lahani don a ko da yaushe zamu iya kashesa."
zuciyar Alhaji Damas ta sosu ya ce"to me ku ke so in baku ku sakar min ɗana".
Murmushi Bilal ya yi sannan ya ce"Damas ka ke ko wa?ni ba kada abinda zaka bani,don haka ni dai saƙona kenan,sannan gobe da misalin ƙarfe uku na rana zanzo har gidanka.
Bayan haka suka jefar da Aliyu akan hanya ,Alhaji Damas yasa aka zo aka ɗauko ɗansa Aliyu,Allah2 ya ke goben ta yi yaga mugun da ya yi wa ɗansa haka.
Washe gari tunda wuri ya dinga saka idon zuwan Bilal,yaga kiran Bilal ɗin ya ɗaga wayar yana tama irin azabar da zai ganawa wannan bawan Allah.
Huro mai iska Bilal ya yi ta cikin waya sannan ya ce"kana dakun zuwana ba?to har na riga da na shiga gidanka har na yi maka ɓarna".
sosai Damas ya gwalo luhu luhun idanuwansa kamar Bilal ɗin yana kallonsa.
Ba tare da Bilal ɗin ya basa damar yin magana ba,ya ce"Damas ka duba gidan masana'antar barasarka zaka yanzu haka,na saka masa bomb ya tashi duka,bomb sannan ka duba gidan masana'antarka na shinkafa.talakawa na nan suna cika tsore ɗinsu da shinkafar bati,don haka daman wannan shine zuwan da na ce zan maka. .ƙit ya kashe wayar ya cire layin ya jefar ya ƙarawarsa gaba,don shi arayuwarsa ya tsani mugunta ko kaɗan shiyasa duk wani mugu tsoron A.D ya ke wato Admiral Bilal.
****
Ina tashi da safe na tsorata da ganin yana yi na,na tashi tsaye sai naji marata ta yi bala'in murɗawa,ina ciwon mara idan zanyi period amman na yau na dabanne,juyi sosai na ke ina kiran sunan Alkah babu kowa akusa dani balle ya taimakamin,jini sosai ya ke fita daga jikina kamar an yanka akuya.
Mama da ta shigo tashi na ne taga wannan halin dana ke ciki,da gudu ta rufo kaina cikin matsananci damuwa,jinin da ke zuba ajikinta shine abinda ya ƙara tsorata ni sosai.da sauri mama ta kira Babanmu lokacin yana gida,aka kira likitanmu ya shigo gwajin farko ya ɗago ya kalli Babanmu wanda shima a tsorace ya ke,Hajiya kaka na gefe tana tofa min addu'ah don ita wannan jinin gani take kamar aljanune suka taɓani.
"I'm sorry to say ƴar ka ta samu misscarriage ne(wato ɓarin ciki)".
kusan daskarewa dukkan mutanen wajen sukayi saboda ɗimuwa da tashin hankali,cikin fushi Baba ya damƙoni ya ce"Khairat sakayyar da za ki yi mana kenan?ciki agidana?kaf zuri'armu babu wanda ya taɓa abin kunyar nan idan ba ke ba?waye ya yi miki ciki har ki ka yi ɓari".?
kasa bada amsa na yi ina tunanin amsar da zan bayar mama ta matso kusa dani ta shararamin wani mugun mari wanda ya shuɗar dani na wasu minti na,tana tambayata waye ya yi min ciki?.
Hannunta mahaifina ya riƙe sannan ya ce"Xulaiha babu abinda zance da ke sai ince Allah ya isa tsakanina da ke,ke ce ke zama da yarinyar nan agidannan amman baki san tana da ciki ba?to ki sani bazan zauna da mayaudariya irinki ba,kije na sakeki saki uku".
*Miss green ce*
*kassssssssh!*
Hmm nasan kuna nan cikin tashin hankali da kuma ruɗun abinda ke faruwa.
*Shin waye ya yiwa khairat ciki?.*
Wannan tarin amsoshin na ku duk sai a littafi na gaba.
Wanda complte ɗinsa ya kasance naira ɗari uku kacal300 katin mtn ko acc.
Ga hanyar biyan wannan kuɗi👇🏻👇🏻
Anan NA KAWO K'ARSHEN FREE PAGE. KI BIYA KUD'INKI DANJIN YADDA ZATA KASANCE. WANNAN TAFIYAR TA Musammance.
*GAWURTATTU BIYAR, TAFIYAR TA MUSAMMAMN CE. 👯♀️👎👇👇*
1, *MU GANI A ƘASA...*🔥
_Ummu Affan_
2, *ABIN CIKIN ƘWAI..*🥚
_Ummu Maher_
3, *GUNTUN GORO..*💥
_Mom Islam_
4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎
Badi'at Ibrahim
_Mrs Bukhari_
5, *AUREN WATA TARA*👩❤️👨
_Miss Hajo_
Guda biyar 1k
Guda huɗu N700
Guda uku N600
Guda biyu N500
Guda ɗaya N300
*DOMIN TURA KUƊIN KAI TSAYE*👇
0037219728
Fatima Rabiu Sunusi
StanbicIBTC Bank.
Domin tura shaidar biya👇
0810 433 5144
Masu tura katin MTN👇
0814 179 9224
Ƴan Ƙasar Niger zasu tura nasu anan.👇
0817 952 3215
Guda biyar 1000f
Guda huɗu 700f
Guda uku 600f
Guda biyu 500f
Guda ɗaya 300f
*TEAM GAWURTATTU BIYAR TAKUN FARKO TAFIYA TA MUSAMMAN.* 🔥🥚💥🌎👩❤️👨
An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://thausanovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.thausanovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels