Share this page
5 / 9
abinda ki ke so"?.murmushi ta yi sannan ta ce"wallahi ga ɗakin nan sai ƙamshi ya ke Allah dai ya yi albarka ya baki miji nagari abin son kowa".da Amin na amsa mata na ɗan daure na ce wa Yaya Bilal"sai anjima".ko kallona bai yi ba ya cigaba da danna wayarsa yana dariya,kaka ta kula da hakan sai dai bata yimai faɗa ina nan ba sai da na fita ta ce"haba Bilal wai me yasa ka kewa yarinyar nan haka ne?ina fa lura da kai ko gaishe ka ta yi baka amsawa me yasa haka ne?". Ɗago kansa ya yi sannan ya ce"kai kaka ni fa idan damuna zaki yo sai in fita?kawai daga shigowarta sai ta haɗamu".?ganin irin mirmisisin da ya yi da idanuwa bata ƙara ce masa komai ba suka cigaba da hirarsu kaka na ɗarsa wani abu azuciyarta. Ina fitowa na samu wani ɗan lungu na fashe da kuka mai ƙarfin gaske,na yi mai i'sa ta sannan na juya xan tafi sai muka ci karo da yaya Aliyu da Yaya Mukhtar.da mamaki suke kallona sannan suka haɗa bakinsu wajen ce wa"a'ah little sis me kuma ya sameki haka?me ya faru agidan?".saurin goge fuska ta na yi to me zance musu?ce musu zanyi inason yaya Bilal shi kuma yana wulaƙanta ni ko me?no ai abin da kunya. Ganin bance komai ba suka sakani agaba wai sai na gaya musu abinda ya faru?bakina yana rawa na ce"kukan rabuwa ta na ke yi da Rashida".na faɗi hakan cikin shagwaɓa.dariya sukayi dukansu musamman yaya Aliyu ya ce"to ikon Allah kukan kuma tun yanzu?ai haƙuri zakuyo dukanku don ku daman rayuwar mace ƙanƙanuwa ce daga gidan iyayenta sai gidan miji,don haka ki share hawayenki kinji?"da to na bisu sannan na wuce. Yaya Mukhtar ya ce"bro ni fa na samu mata agidannan Tun khairat bata kai haka ba na ke matuƙar sonta har yanzu,amman na rasa ta inda zan faɗa mata".?dariya yaya Aliyu ya yi sannan ya ce"bro me gaskiya kada ka yi sakaci kamar yadda na yi akan Rashida ka gabatar mata da kanka ka ga kawai sai a haɗa bikinmu asha biki".ya faɗi hakan yana kallon mukhtar wanda shima shi ya ke kalla. *** Har na isa sashenmu jikina duk a sanyaye ya ke,ban kula da mutanen da ke farlon ba na yi wuce wa ta sai kuwa naji anty Hamdala ƴar Mama wato uwargidan su maman mu wacce take aure a Abuja ta ce"ikon Allah ita kuma wannan ƴat baƙar yaushe ta fara raina mutane har haka?".mata ce"hmm Hamdala ta gaisheki tana ganin kakarta da uwarta sun ɗaure mata gaba agidannan sai wanda taso ta gani da mutunci a gidannan sannan take gani da gashi,ai kinga gwara mutum ya kama kansa kafin kuma a koma dukanka".cikin jin kunyar maman nawwara wato antyna Hamdala na ce"mmn nawwara ina yini?wallahi ban kula da zuwan ki bane amman don Allah ki yi haƙuri".na kama kunnuwa na alamar ban haƙuri,sai kuwa ta ce"ai ke dai kam Khairat kin shiga ukunki da iya haɗa munafunci yanzu da ki ka saka za'ayi wa su Nadiya auren dole me ye ribarki?baki da wata riba sai ta munafunci da iya haɗi,to wallahi ni dai kada ki yadda gulmarki tazo kaina don ba Hajiya kaka ba ko Hajiya wacece agabanta zanyi maganinki ehe don ni ba kunyar wata tsohuwa na ke ji ba,idan su Baba ita ta haifesu to mu ba'ita ce ta haifemu ba". Sosai na yi mamakin abinda Anty Hamdala ta faɗa na rasa me yasa iyayensu suka koya musu rashin sanin darajar mutane,Daman Hajiya kaka sun saba yi mata rashin kunyarsu da fitsararsu abin yana yimin ciwo don duk zagin da Hajiya kaka ke yi wa mahaifiyata bai saka ko kaɗan na raina ta ba,shiyasa sam bata bari a cuce ni ko kaɗan sai dai idan bata wajen don takan faɗa ce wa wai ni banyo mai sunan na ta ba,don ni ba mutum ce mai faɗa ba,sai ka yi min abu ban taɓa nuna maka ka yi min ba sai dai inyi kuka in share hawayena ko mama ba ta sanin komai idan ba ni ce na gaya mata ba. Ban sake ce wa komai ba na wuce ɗaki raina babu daɗi,a rasa me yasa ƴan uwana suka tsaneni haka?ko don suna ganin son da Baba ke nuna min ne oho?ko kuma fifita ni ɗin da kaka ke yi ne?don ita Hajiya kaka babu ruwanta ko agaban waye sai ta nuna min ƙaunar nan daga Allah take. Mama ta sameni aɗakina lokacin na fito wanka na gaisheta ta ce"yauwa Khairat ɗazu yayanki Aliyu yazo ya ce gobe zakije gidansa Khadija babu lafiya ga shi kuma zaiyi tafiya kinga sai ku zauna a atare".?to na ce mata amman ba don raina yazo ba don sam bana son zuwa gidan babban yayan nawa wanda shine babba awajen mama shine ɗan farin ta,abinda yasa bana son zuwa saboda Khadija aƙwaita da shegen son jiki sannan ba tada jan dangin mijinta ajiki,duk da itama ƴar uwarmu ce don auren dangi a ka yi musu Babanta baba faruku Ƙanine awajen babanmu kuma uwa ɗaya uba ɗaya suke. Babu yadda na iya washe gari da wuri na haɗa kayana bayan na gama gyara ɗakina harda babban farlonmu duk sai da na gyara sannan na nufi kitchen inda mama take aiki,na samu Nadiya tana cin ayaba sai zubar da ɓawon take,mama kuwa ko kallon ɓangaren Nadiyan bata yi ba,tana ta aikinta na rasa mama wata iriyar macece sam babu ruwanta da wani faɗace faɗa ce rayuwarta so simple ce,babu yadda za ayi inyi wa mahaifiyarsu Nadiya haka don mama bata taɓa bani ƙofar raina wani cikinsu ba,nima ko kallon Nadiyan banyi ba don nasan neman jaraba take na wuce wajen mama,da fara'a na ce"mama aƙwai abinda za'a ƙarasa miki ne?"ɗan murmushi ta yi sannan ta ce"a'ah na gama komai ɗauki abincin Kaka ki kai mata anjima kuma Boy zai zo ya ɗaukeki"?in dai kaji mama ta ce boy to yaya Aliyu take nufi ɗan farin mama don tana matuƙar ji masa kunya don ko hira sosai basu cika yi ba. Tsaki naji Nadiya ta yi sannan ta fita,nasan sarai dani da mahaifiyata take amman bance komai ba na girgiza kaina na wuce. Ina zuwa sashen Hajiya kaka na same ta tana kallon labaran safe a tv ɗinta,da fara'a ta amshi basket ɗin kayan karya kumallon na ta sannan ta ce"ABIN CIKIN ƘWAI Lafiya naga kin rame haka ko wanine ya taƁaki yanzu in saƁa masa". Girgiza mata kaina na yi kafin in bata amsa naji sallamar Yaya Bilal,a take naji gabana ya yi wani mugun faƊuwa don tsabar tsoronshi da na ke ji,hajiya kaka ta kalleni ta daka min harara don tasan abinda na ke wa tsoron. hajiya kaka ta ce"ke kuma me ye kika wani firgita kamar kinga wani namijin zaki"?.ɗan dai dai ta nutsuwa ta na yi sannan na ce"babu komai kaka bari inje mama za ta aike ni ne". Hajiya kaka ta ce"hmm kyaji dashi dai da kin gansa sai ki kama wani rarraba idanuwa kamar mujiya yo sojan har wani abu ne da zaki dinga tsoronsa haka?Ni fa kakanku nasha yi masa kuka akan ya kaini barrek Ɗinsu don a tafi filin daga dani saboda rashin tsorona,yo me aka yi aka yi wani soja". baiyi niyyar dariya ba amman sao da ya yi ya ce"to ke hajiya idan akaje naushi Ɗaya za'ayi miku ki baje awajen". ni dai raƁewa na yi a gefe kamar wata munafuka ya buga min wani banzan kallo sannan ya ce"ke tashi ki fita ni sa'anki ne da zaki zauna kina kallon bakina ina magana,comon dalla tashi ki fita Ƙazama kawai me shegen kallo kamar mayya". *Miss green ce* *GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE* 1, *MU GANI A ƘASA..🔥* _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚* _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..*💥 _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎 _Mrs Bukhari_ 5_ *AUREN WATA TARA👩‍❤️‍👨* _Miss Hajo_ Guda ɗaya N300 Guda biyu N500 Guda uku N600 Guda huɗu N700 Guda biyar 1k *ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇* Fatima Rabiu Sunusi 0037219728 StanbicIBTC Bank. Shaidar biya tanan 👇 0810 433 5144 Masu tura katin MTN👇 0814 179 9224 ...........🥚👩‍❤️‍👨💥🌎.... *ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇 Guda biyar 1000f Guda huɗu 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda ɗaya 300f Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇 +227 84 50 64 76 *MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO* [23/09, 16:17] Miss Green🍀: _*🥚ABIN CIKIN ƘWAI...!*_ 📃Littafi na 1 By🪶 *Ummu maher(Miss green)🍏* *GAWURTATTU 5* ----------------------- *Wattpad user name* https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333 ------------------------- *Arewa book user name* https://arewabooks.com/u/rabiattu0444 ---------------------- masu buƙatar talla 2k Ne,zamu dinga Ɗora muku a dukkanin shafukanmu a kowani social media don samun costumer cikin sauƘi. *Sirrinmu* Manzon Allah(S.A.W)ya hanemu da cin naman mutane,ma'ana gulma ka yi gulmar mutamin da baya wajen Allah ya tsaremu amin. ----------------------- 13🟦14 ........sosai sukayi mamakin kalamin kakar ta su,wai su za'a mayar ƴan aiki ko kuwa?bata ƙara kallonsu ba ta yi wucewarta,don ta yi alƙawarin sai ta koya musu hankali har kuka sai da ta yi don jin abinda jikokinta suke ai'katawa. Washe gari a babban farlon gidan aka haɗu na cin abinci ƙaton teburine wanda ake haɗuwa duka family aci abinci don ƙara zumunci,kowa ya yi tsit baka jin ƙarar komai sai ƙarar cokali,wasu suna ci amman kamar suna cin kashi don hankalinsu a tashe ya ke da wannan haɗuwar wasun kuwa ba wasu bane illa su Nadiya,iman,samira,unaisa,khalisat,intisar,raudar,amina. Duk hankulansu a matuƙar tashe ya ke don sun san har wanda bai san abinda sukayi ba to yau sai ya sani don wannan kakar tasu sai ta faɗa. "To kunyi zungui zungui kuna kallona kamar baku sanni ba?to daman mun haɗune anan don wani gangarumin taro,don haka kowa ya buɗe kunnuwansa yaji." Kowa kallon kaka ya ke saboda sun san aƙwai wata a ƙasa aƙwai wanda ya ke da rabon shan wulaƙanci shiyasa kowa ya kama bakinsa daga su har iyayensu,itama kakar kallonsu take azuciyarta ta ce yau kowa sai ya gane kurensa don wallahi baza'a janyo musu ɓarna har acikin gidansu ba. Su kuwa ƴaƴanta babu wanda baisan abinda kaka za ta faɗa ba,don jiya da daddare sunyi meeting akan hakan,Hajiya kaka ta kalli Baba Abdullahi ba tare da ta ce komai ba,sanin abinda take nufi ne ya yi gyaran murya ya fara jawabi kamar haka. "Abisa yarjejeniyar da muka yanke tsakaninmu da mahaifiyarmu mun ɗaukar mata alƙawari kuma ayau zamu cika mata shi,ba neman shawarar kowa muke acikinku ba a'ah saboda haƙƙin kune a faɗa muku,mun yanke shawarar haɗa aure ga ƴaƴanmu don ƙara ƙulla zumunci." gaban jikokin na su ne ya yanke ya faɗi karma ace maka su Nadiya sukayi tsiru suna kallon iyayen na su don jin waɗanda aka haɗa auren,ko har dasu oho?kai har dasu ɗinma tunda dai sune ƴan matan gidan,tuni cikinsu ya bada sauti ƙuuu alamun gudawa. Baba Abdullahi ya cigaba da ce wa"to mun yanke shawarar gaɗa,Aliyu aure da Nadiya".zaro idanuwansu sukayi waje daga Aliyun har Nadiyar. "Salimat kuma da Abbas,Amina da munir,khalisat da Sadiƙ,intisar da Hafiz,iman da Irfan,unaisa da maher,samira kuma da Arman." dukkansu tashi sukayi tsaye suna kallon ikon Allah don basu taɓa tunanin wannan abin ba unexpected.babu wanda ya basu damar ce wa komai Baba malik mahaifinsu Khairat ya ce"mun saka ranar aure nan da wata biyu masu zuwa,dukkanku bama neman wani abu daga hannayenku duk abinda ya kama zamuyi sauran abubuwa ku tuntuɓi iyayenku".yana faɗar hakan ya tashi ya ce"to ni zan tafi wajen aiki ina da meeting sai anjima ".ya yiwa ƴan uwansa sallama da mahaifiyarsa sannan ya tafi. Kallon juna aka shiga yi a babban farlon musamman waɗanda aka haɗa auren,gabansu sai faɗuwa ya ke acikinsu aƙwai waɗanda basu damu ba da haɗin da akayi musu amman fa Nadiya tafi shiga cikin tashin hankali don ita gani take ma kamar baza ta iya zaman auren ba. Bayan taro ya tashi ko wa da abinda ya ke saƙawa acikin zuciyarsa,Rashid ta kalli Khairat cikin tsokana ta ce"to ikon Allah yanzu fa agidannan mune muka zana gwauraye don kowa da mijinsa".nima ƴar dariyar na yi sannan na ce"gaskiya wannan haɗin ya yi min sosai wallahi kinga ni daman su Nadiya na ke tunanin amman kinga yanzu rayuwarsu za ta inganta kuma yaya Aliyu mutunne mai mutunci da karramawa."Rashida ta yi min sannan ta ce"wai kina nufin daman Nadiya da Aliyu aka haɗa?".saurin ɗaga mata kai na yi alamar eh.hawaye naga yana fitowa a idanuwan Rashida na ce"a'ah me ya faru kuma"?. ruƙo hannuwa na ta yi duka biyu muka shiga ɗan lungu da ke manne dana kaka,a hankali cikin siririyar murya ta ce"Khairat muna soyayya da yaya Aliyu fa?".da sauri naja ɗan baya na zaro idanuwa na waje alamar tsoro. tausayi ta bani sosai a zuciyata kuma ina tuna girman zurfin cikin ita Rashidan da ko ni ban taɓa sani ba,a hankali na ce"haba Rashida gaskiya kinyi kuskure ba kaɗan ba wallahi,ko ni baki taɓa gayawa ba?ballan tana ma in taimaka miki ta wani ɓangaren,kin san yanzu kan iyayenmu a haɗe ya ke kada azo ayi abinda kansu zai rabe,kin san kawu Auwalu matarsa ta fi ƙarfinsa sai yadda ta yi dashi gashi kuma basa shiri da Mamanku kinga hakan kamar zai janyo wata matsala fa"?. "Na sani Khairat amman wallahi mundaɗe muna soyayyarmu daman munƙi bayyanawa ne sai har mun gama makaranta. Kasa ce wa komai na yi cen dai na ruƙo hannuwanta duka biyu na ce"Rashida aduk halin da zaki shiga bazan taɓa gudunki ba ina nan tare da ke,tun daga kan wasan ƙasa har zuwa yanzu munanan tare babu wani mahaluƙin da ya taɓa shiga tsakaninmu don haka kinga yanzuma dole in tsaya kaida ƙafa inga wannan al'amarin ya dai daita". Kamar daga sama mukaji ana ce wa"ya dai dai ta ma ai".muryar kaka mukaji ta nufo inda muke ta ce"munafukar yarinya au ke yanzu daman kina son gadanga ƙusar yaƙi kika ƙi magana sai yanzu".?ƙada da kai Rashida ta yi tana zubarda hawaye tausayinta ya ɗarsu a zuciyar Hajiya kaka ta ruƙo hannun Rashida suka nufo ɗakin kaka Yaya Aliyu yana zaune akan kujerar kaka wadda aka zuba mata ƙwanannan kansa a ƙasa idanuwansa sunyi jawur kamar harda kayan aikinsa ma ajikinsa ba tare daya ciresu ba,kayan aikin likita yaya Aliyu likita ne na ganycology ma'ana likitan mata. Yana ganin Rashida ta shigo ya tashi da sauri yana kallonta jikinsa duj babu ƙwari ya zauna yana ce wa"Rashida kinga yanzu abinda shirin mu ya ja mana,kin fiya zurfin ciki Rashida kin hanani gayawa kowa saboda sai kin gama makaranta za'a sani how comes hakan ya faru."ya faɗi hakan yana kallon Rashida.mu dai duk muna tsaye mun kasa zama sai da kaka ta ce"to aadarawan sarki ku zauna kun wani tsayamin akai".zama mukayi a kan capet ɗin ɗakinta ba ta ce komai ba ta janyo wayarta ta ce"ke Abin cikin ƙwai kirawo min abdullahi dai malik dai auwalu duk ki kirawomin su alokaci ɗaya." Gabana yana faɗuwa na fara kiran Babana faɗa masa,sannan na kirawo su suma duk akayi sa'a suna cikin gidan dawowarsu kenan,su dukansu ta tarasu sannan ta ce"kun gane min waɗan cen ja'iran yaran".ta nuna su Rashida da Aliyu dukansu sunkuyar da kansu sukayi don kunya sannan kaka ta ɗora da cewa to kada ku ɗoramin laifi don nima ban sani ba?sai yanzu".duk iyayen nasu su suke kallo sun kasa gane inda maganar mahaifiyartasu ya dosa.Baba Auwalu ya ce"to umma me kuma ya ƙara faruwa kin sakamu acikin duhu?". "Duk yanzu zaku fito daga cikin baƙin gawayi ma ku ƙara tsundumawa cikin baƙin gawayin tsabar na sakaku acikin duhun?to waɗannan yara Rashidatu da Aliyu ashe soyayya suke basu taɓa barin wani ya sani ba sai yanzu ne fa ni na kama su". ni da bama dani ake ba kunya kamar ta kasheni dukanmu mu ukun muka sunkuyar da kai,ana cikin hakan Baba ya ce"shin da gaske kuna soyayya?".da sauri kaka ta ce"ikon Allah ka jini da malik au tambayarsu ma ka ke da gaske ne ko?na sambaɗa ƙaryar dana saba muku ko?to ko ubanku kafin ya mutu bai taɓa ce min na yi masa ƙarya ba sai kai soja marnari daga ne sa".ganin mahaifiyar ta su za ta sauka daga bigeren da suke ciki ya ce"ki yi haƙuri umma ba fa nufina kenan ba kin san yaran yanxu suna iya canja ra'ayi a ko da yaushe".ya faɗi hakan yana kallon mahaifiyar ta su. "Au to na ɗauka ƙaryata ni xaka yi ai ga Abin cikin ƙwai nan tasan komai sai ta faɗa maka,shegiya baƙar banza ai duk tare da ita aka ɓoye komai tunda sun iya munafunci".da sauri na ɗago kaina ina kallon kaka ta ce"daina kallona da idanuwanki gwala-gwala irin ns baba tunde inyamurin kakanki".da sauri na ɗauke idona don nasan kaka tana cikin fushine,arayuwarta ta tsani abinda zai taɓa mata jikoki sai kaga duk hankalinta ya tashi. "na ce daku na ke magana".cikin tsawa Babana ya yi maganar don shi aƙwaishi da zuciya Aliyu ne ya buɗe baki da ƙer ya cire farin glass ɗinsa irin na likitoci ya ajjesa acikin ma'ajiyarsa sannan ya ce"ƙwai Baba da gaske ne muna soyayya tun 2 years da ta wuce". "amman Aliyu anyi lusari wallahi yanzu kana son yarinya amman shine ka yi shiru har sai da aka fitar maka da mata?to yanzu yaya ka ke so muyi?so ka ke ka raba mana zumunci ko?to wallahi baka isa ba".inji Baba Auwalu wanda ya harzuƙa sosai don shi arayuwarsa baya son raini ko kaɗan. "To ni fa bawai na tara kune anan kuyi min wani ƴan faɗa ce faɗa ce ba,Aliyu dai ya tabbata mata 2 zai aura shikkenan sai ku tashi acigaba da shirye shirye,kuma duk shegiyar matarda ta canza muku karatun dana yi to wallahi sai ta fece garinsu".tana faɗar hakan ta tashi ta shige uwar ɗakinta. Sim sim ni da Rashida muka bita kawunanmu a ƙasa,shima Aliyun zai tashi suka zaunar dashi sukayi masa nasiha sosai sannan suka cigaba da hirar yadda abubuwan zasu tafi na biki.to Aliyu babu laifi yana da kuɗinsa doj yana samun kuɗi na albashinsa sa sannan yana sana'ar siyarda motoci daga cotonou zuwa nigeria wannan kuma shi da yaya Bilal suke don daman a manyan gidan daga Yaya Mohd sai Yaya Bilal sai Yaya Aliyu,su biyun duk rana ɗaya aka haifesu don haka tare suka taso babu abinda suke banbantawa,ko shawara ce sai Aliyu ya tambayi Bilal sannan ya ke jin daɗi,ammanfa akan zancen son ƙanwarsa ya kasa gaya masa don kunyarsa ma yanxu ya keji don ya zama suruki. Jin wannan maganar ba ƙaramin hargitsi ya haɗa ba,don mama mairo mahaifiyar yaya Aliyu tuburewa ta yi ita fa ɗanta bazai auri ƴar maƙiyiyarta ba,da ya ke macece tsayayyiya sai gashi tana neman canzawa Baba Aliyu tunani,ai kuwa kaka ta kirasu ta sillesu tsaf ta kuma ce"ke Mero sanda za'a aureki ba tuwo tuwo ki ke a bakin titi ba?".sai kuwa mero ta bazo idanuwa waje kunya duk ta isheta,ta sunkuyar da kai tana jerowa tsohuwar Allah ya i'sa. "Oho ke ban hana a aureki ba sai ni zaki hana a auri jikata ko?ta haɗiyi zuciya ta mutu ko?to wallahi baki isa ba aure kamar an ɗaurashi ne,don haka ki fita daga idanuwa na in rufe duk abubuwan da ki ke bana son yin magana ne don kada in zama uwar banza don haka kada ki yadda ki shigo gona ta don haka ki ki yaye duk sanda kika cikani sai na faɗawa kowa sirrinki". da sauri mama mero ta ƙwalalo idanuwanta don tasan kaka za ta iya faɗa to tabbas ta tarwatsa mata rayuwarta shikkenan ƙarshenta yazo,da sauri ta ce"Allah yaja daran Hajiya kaka insha Allah haksn bazai ƙara faruwa ba."harararta kaka ta yi sannan ta ce to ass- ass na sallami mutum ya tashi ya bani waje don nan ba filin tuƙa tuwo ba ne ehe". da sauri ta yi fit ta fita don ba ta son ƙara jin maganar da kaka za ta faɗa don yanzun ma ta gama faɗin abubuwa marasa ƙyau akanta. Tana tashi kaka ta kalli Baba Auwalu ta ce"to sallamamme ni kam yanzu na sallamawa mero kai dai ka tashi ka bita don na ga jikinka har rawa ya ke ka bita". Sunkuyar da kansa ya yi sannan ya ce"umma ki yi haƙuri daman wai ina tausayawa masa ne riƙe mata biyu a ƙananun shekarunsa".ya faɗi hakan kansa aƙasa. "Oh ni Ramatu idan baka mutu ba zaka yi kallo wai ni Auwalu ji ka ke na manta ne yanzu fa matanka biyu kuma kana son ƙaro ta uku ita mero kana aurenta ko shekara bata yi ba ka yi mata kishiya ba?babu yadda banyi ba akan kada ka ƙara amman ka ƙara saboda ka gano shuwa duk ka gigice to ka fita idanuwa na wallahi,daman kai Auwalu duk ƴaƴana kai ne sallamamme akan mata Kamar wani zakara,to dai Allah ya tsari Aliyu da haka". Sunkuyar da kai ya yi sannan ya ce"to umma na tuba ki yafe min insha Allah hakan ba za ta ƙara faruwa ba".da hannu ta nuna masa ƙofa ya fita a hanyar fitowarsa ne yaci karo da hajiya Inna aminiyar Hajiya kaka gaisheta ya yi cikin mutunci sannan ya tafi. Bayan sun gaisa ne Hajiya Inna ta ce"Ramatu wai me je faruwa ne acikin gidannan na ga duk yaran suna wani ɗa-ri-ɗa-ri da mutum suna wani sunkuyar da kai." "ah to ai dole ki gansu a haka tunda gidan mutuwa kika zo?wai fa akan wannan haɗa wannan alkhairin da ki ka bani shawara ne to shine fa suke ta fushi dani,yanzu haka duk basa zuwa ɓangare na Abin cikin ƙwai ce kawai take zuwa sai Bilal daman kaf jikokina yasin ba fi sonsu don basa guduna akowani hali". "to Ramatu ai dole daman ki gansu a haka amman daga baya komai zai gyaru insha Allah suna yin auren idan suka ɗan ɗana zumar aure to fa zaki bani labarin irin yadda zasu kasance".nan dai suka cigaba da hirarsu gwani sha'awa. *GAWURTATTU BIYAR,5🤚TAFIYAR TA MUSAMANCE* 1, *MU GANI A ƘASA..🔥* _Ummu Affan_ 2, *ABIN CIKIN ƘWAI..🥚* _Ummu Maher_ 3, *GUNTUN GORO..*💥 _Mom Islam_ 4, *GISHIRIN ZAMAN DUNIYA*🌎 _Mrs Bukhari_ 5_ *AUREN WATA TARA👩‍❤️‍👨* _Miss Hajo_ Guda ɗaya N300 Guda biyu N500 Guda uku N600 Guda huɗu N700 Guda biyar 1k *ZAKU TURA KUƊINKU TA WANNAN HANYAR👇* Fatima Rabiu Sunusi 0037219728 StanbicIBTC Bank. Shaidar biya tanan 👇 0810 433 5144 Masu tura katin MTN👇 0814 179 9224 ...........🥚👩‍❤️‍👨💥🌎.... *ƳAN NIGER GA HANYOYIN BIYAN KUƊINKU👇 Guda biyar 1000f Guda huɗu 700f Guda uku 600f Guda biyu 500f Guda ɗaya 300f Kai tsaye ku tura da katin Airtel ta wannan number👇 +227 84 50 64 76 *MUN GODE DA KASANCEWA DA GAWURTATTU TAKUN FARKO* *Miss green ce* [23/09, 16:17] Miss Green🍀: *🥚ABIN CIKIN ƘWAI...!🥚* 📃Littafi na 1 By🪶 *Ummu maher(Miss green)🍏* _*TEAM GAWURTATTU BIYAR 5🔥*_ *Wattpad user name* https://www.wattpad.com/user/Rabiatu333 ------------------------- *Arewa book user name* https://arewabooks.com/u/rabiattu0444 ---------------------- masu buƙatar talla 2k Ne,zamu dinga Ɗora muku a dukkanin shafukanmu a kowani social media don samun costumer cikin sauƘi. 17🟩18 ...ina fita kaka ta kalli yaya Bilal ta ce"haba soja na me yasa ka ke damun yarinyar nan ne?ƴar uwarka ce fa?ni dai babu ruwana wallahi kada wataran kazo ka ce kana sonta Allah ko zaka mutu bazan baka ita ba. . ."da sauri ya ce"Allah ya tsare ni,ni kuwa duk matan garin nan sai ij rasa ƴar da na ke so sai wannan mai mugun halin,baƙa ƙirin kamar zunubi,ni dai kada ki ɓata min sauran nisha ɗina ni na yi nan".yana faɗar hakan ya tashi ya fita zuciyarsa fal haushin Khairat,shi fa yau ba zai iya cewa ya taɓa jin yana son wata mace ba ballan tana ma kuma Khairat da ya yi wa muguwar tsana. "Haba Khairat me yasa kullum na ke gaya miki magana amman kamar a banza ne?shi fa namiji da ki ke ganinsa muddin ki ka cika nuna masa so to tabbas za'a samu matsala don ƙarshe ma sai ya ce ke ce ki ke sonsa,gwara ma ki yi saffa2 don Allah Khairat ki nutsu kisan inda ya ke miki ciwo don gaskiya idan ba haka ba za ki yi nadamar wannan mugun son da ki ke masa,ni dai kinji na gaya miki." muna cikin wannan hirar ne Arman ya dawo daga makaranta,ya taho da gudu yana dariya ya ce"Sannu da gida Anty ABIN CIKIN ƘWAI".ɗan dukan wasa na kai mishi sannan na ce"wato ka ji hajiya

Chapter 5 of 9