Share this page
9 / 9
alheri don wanan halin nata na kirki data nuna ba wanda zai tsunci wayan nan ya maida min shi kamar yadda ta mayar min a yanzu ba tare dana sha wahala ba. Don haka ga wanan ki rika ya fada yana miko min kudin da sai lokacin ya kalleni ya gane yarinyar nan ne ranan ashe ? Yasan ban shedashi ba don irin yadda yayo shiga ranan ba zan taba sheda shine ba a yanzu gabana tsaye . Ya juyo ya kara kallona yana miko min kudi na gurgiza kai tare da fadin i no de colete ur money i just do wam becouse of Allah. Tsuki yan gidan suka fara suna fadin olopopo see d person wen no get any tin de reject d money now . Eh i no go coletem my religion no teach me like dis wani officer ne daga bayan shi ya amshi kudin a hannun shi yana fadin where ur mama. Na nuna mashi kofan dakin mu yace ur mama go colect d money naw yana dan washe baki. Shiko yana tsaye ya soka hannu daya cikin aljihu ya kura min ido a cikin mamaki hali irin nawa. Suko yan gidan namu sai fadin suke ehh givan to her mother she will colectam, suna wani bubuda mashi hanya don ya wuce. Su kuma na fadin haba dis enosent girl can do dat may she found it some where mafi yawan su haka suke fadi suna kallon yadda za a kwashe tsakanin mu dasu. Har guntun dan sandan yayi nisa a cikin muryan shi na kasaita yace dashi look Samuel called d mother for me first. Duk mama na tsaye a kofan mu a cikin tashin hankali tana jin abinda kowa ke fada lokacin kafin ma ya karaso itace ta fito suka juyo tare. Sunzo wurin ta dan tsaya a inda nake tsaye itama tana kallon yawan su duk wai a kaina suka zo can yace da ita. Yarki ta tsunci wayana ta kuma kira azo a karba shine nake son bata alheri don halin data nuna na kwarai taki karba. Ai domin Allah yata tayi hakan ka tambaya nan kaji idan mun taba rigima da wani tsakanin mu da kowa a gidan nan sai mutunci. Daga gefe suka shiga fadin gaskiya ne kwarai kuwa hakane don baka sanin ma suna gidan nan idan ba sun fito ba agansu. Oya ki karbi kudin nan don hakan umurnine na tabbatar da na baku alheri don yaba abinda kukai min don kinga wayan nan duk wani baiyanin sirina yana cikin sa kuma tunda ta dauka bata taba shi ba. Woman colet d money u be luck woman to born pikin like u knowadays with good heart wani tsohon iyamiri dake sayar da kayan part na mashin din hawa ya fada daga gefe inda suke tsatsaye. Woman colect de money now iyamirin ya kara fada sai umma takai hannu ta karbi kudin don iya shegen bariki sai suka ihu da tafe wai har sun manta wa yanda ke zagaye dasu a lokacin . Nan dai gulma ya kare bayan sunga sunyi godiyan hakan da akai musu suka shiga motocin su suka tafi. Tafiya sukeyi amma hankalin shi baya tare dashi duk da yana bin wayan shi da bincike a lokacib don ya tabbatar ba a taba mai ita ba bayan batar ta. Saidai hakan bai hanashi shiga zurfin tunanen da yakeyi ba tare da tantama ko a ina yasan wanan fuskan a baya. Haka nan a bangaren mu sai bayan wucewan shi ne umma takai kudin a hancin ta tayi saurin cirewa da sauri don irin kamshin da taji kudin nayi. Nima a daidai lokacin kwakwalwata ta hasko min kamar shi da wancan guy din daya taba ban kudi a cikin mota lokacin dana fita da ruwa. Umma na fada da sauri a cikin hausa nake fasin kamar wanda ya han kudi da nake tallan ruwa fa shine wanan mutumin. Tambayan da zan maki yanzu ke nan kika rigani ashe shi din dan sandane ke nan nifa Sahiba wanan abin yanzu ya fara bani tsoro gaskiya. Fada muka ji an rikice dashi a wajen gidan mu tsakanin yarabawan gidan da iyamurai da muke haya tare. Da sauri muka fito don hayaniyar yayi yawa duk dako darene wai wani iyamuri yace da ace yaran yarbawan gidan suka tsunci wayan nan ba zasu bayar don duk barayi ne son kudi yayi masu yawa sasai. Tofa ashe a gaban iya wale ya fada aiko nan ta saka kururuwa duk sauran yarbawan suka fito a cikin dakunan su ana fada. Saida kyat suka watse a lokacin nikan nayi barci ni da Amar sai umma dake zaune tana sallah take jin abinda suke fada a cikin fadan nasu. Washe gari kuma tunda asuba suka dasa fadan a inda aka tsaya a cikin zafi iya wale ke fadin wai e go say dat naw for yaruba becos sahiba mother na his ashawo. Inna lillahi naji umma ta fada da karfi na dago daga saka takalman da nakeyi na dan kalleta a inda take zaune din. Naji tana girgiza kai tare da fadin ni iya wale zataiwa kazafi a gidan nan kan wanan maganan yanzu kuma. We all know dat u are sleeping with her when your wife is not in d town shabi na lia i de talk ta tambayi sauran. Ai kafin umma tace me nakai waje ina fadin iya wale so ur tin don come to my mama again ? Na kalleta kallo a cikin fushi cikin turanxin su na lagos nace yau zan fadi abinda kikeyi da mazajen su a cikin dare idan suna barci basu sani. As from today u wil not tell lie for any body again in dis house no be u i see dat night with baba tunde on d floor ? An dat day again d same tin i saw u nicked baba Alaba de for ur back abi na lia i talk ? Swear if i tell lia for u naw, haba kai kace wani irin ruwan zafi na wasa matar shi yadda ta yanka ihu hankalin kowa saida ya tashi wurin. Ita ko iya wale dafe kirji tayi tare da fadin yeh Sayiba ehmi ? Yes u iya wale, na u a i saw dat day in d night with dem abi na lie i talk a wani irin maraice tace ah haba sayiba why why please ? Why u de telling dem lie sayiba ? Shabi lie no good wen u tell dem lie naw for my mama ai kafin tace zata bada amsa iya Alaba ta zo gaban ta tana girgiza tare da gyara danmaran da tayi tana fadin . Ai sai ihu ya tashi suna fadin sham sham on u iya wale , u no de feel sham sleeping wit somebody husband wuuuu. Danta wale yazo daga baya ban sani ba ya kai min duka sauran mazab gidan suka taso mai suna why , why go beat her ? Sai fadan ya koma a tsakanin su suka shiga zagin shi iya wale da yau taga masifa daga inda take ido yayi ja ta shiga surfawa wale din kuma ashar . Wanda da alama bata ma san abinda takeyi ba a lokacin don tashin hankalin data shiga a lokacin kan abinda na fada tayi. Nikan bayan na gama hada fadan na tatara na bar wirin cikin sulalewa na shige dakin mu na zata umma zatayi min fadan hakan danayi mata don tana babba sai naji shiru bata tanka min ba. Wayan shi ne yai kara daga gefen shi ya dago yana kalon mai kira daddy ya gani don haka ya daga da sauri yana fadin daddy yanzu nake batun kiranka na bari gari ya kara wayewane dama. Gari kan ai ya waye na yau sai kuma gobe idan Allah ya kaimu kuma sai yayi murmushi wa daddy nasa . Shi kuma yaci gaba da fadin masha Allahu dada waya dai ya shiga hannun ka ke nan tun jiya haroon ke fada min kun karbo. Ai tun jiyan uana zuwa muka tafi muka karbo wayan ya fadawa mahaifin nasa sai daddy yace a gaskiya yarinyar nan tana da mutunci sosai da wata ai duk abinda za ayi sai dai ayi ba zata bayar ba. Ta bayar dadi yarinyar tana da saukin kai matuka irin hausawan nan ne haihuwan can yarinya don ba hausan take ji sosai ba. Allah sarki ina dai kai mata alheri yadda ya dace ko don irin wanan akan ba mutun abinda bazai taba mantawa bane akan shi. Wallahi daddy na bata kuma sun gode don da farko sunki amsa sunce don Allah sukayi su. Saidai daddy wallahi yarinyar nan yadda kasan yar zuri,an gidan Namadi sak haka zubin ta yake ba zakace ba yar gidan bace sai idan tayi hausa. Kaji harshen ta zaka gane hakan gaban daddy sune yayi wani irn mumunan faduwa lokaci guda da kyat ya furta Allah mai iko. Shekarun yarinyar zaikai nawa yace karamace sosai dadi don da gani bata kai sha biyar ba ma haka mahaifiyar su ba wata babba bace sosai ga shekaru. Wayan ce ta mutu lokaci guda ya dago ya dan kalli wayan yaga ya katse ya kara kira sai computer kece masa wayan a kashe yake. Yayi mamakin hakan don yasan service baya katsewa a unguwar su su sai dai ya basar ya mike ya shiga bandaki yayi wanka ya fitone yayi odan abincin da zai karya kafin su shiga office su dan kara tataunawa kan criminal din su daya gudu bayan yayi nasaran shigo da kayan shi Nigeria ta barau niyar hanya da ba a san dashi ba. Yagama shirin shi tsab yana saka aninin rigan daya sa yaji wayan ya dauki ruri kuma ya nufi inda take saman gado ya dauka. My Mom ya gani a rubuce da sauri yakai hannu ya dauka yana mata kirari tace kai ni ba wanan ba wani zance kukayi da Alh ne haka har ya daga mashi hankalin shi haka. Sai da kyat aka samu ya dawo daidai saidai har yanzu baya magana don bai furtawa kowa komai ba sai ido da yake bin mu da kallo dashi da kalloyana jijiga kai. Inna lillahi yace nikan bamuyi zancen komai da daddy ba illa zancen waya na daya bace na gani shine kawai hiranb da mukayi din daga nan kuma naji shiru na kira kuma wayan ya mutu. ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , DUK WACCE TAKARANTA MIN LITTAFIN NAN BATARE DATA BIYABA BAN YAFEBA An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://thausanovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.thausanovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 9 of 9