Share this page
8 / 9
bane kamar yadda kike zato. A lokacin ya dan cire hulan daya rufo a kanshi ya kalleta da kyau tare da hada hannayenshi wuri daya kamar mai rokon gafara kana yayi wani abu kamar bissalam da hannu tare da dan rankwafawa daga haka suka juya suka ffice sauran suka bi bayan shi da sauri. Ina ganin haka na mike da sauri na rufo kofan dakin tare da saka sakata na dawo inda umma tayi mutuwar zaune don ko motsi bata iya yi ba har lokacin sai bin kofa takeyi da kallo inda suka fita. Umma idan baki yarda dasu ba ki kawo kudin nan yanzu inbi bayan su dashi duk inda suka shiga a garin nan. Sai lokacin umma tayi wanin irin ajiyan zuciya tare da kallona tana fasin ke din Sahiba kike fatan in barki kibi wa yan nan da suka tsaya gabana kamar mala,ikun duniya. Maza ki samu wuri ki koma ki kwanta saidai muyi adduan nufin su yazama alheri a garemu amma ba zan barki ki bi bayan wa yanda bansan asalinsu ba ko daga ina suka fito. Umurnin umma din nabi cike da fargaba a zuciyana na samu wuri na kwanta a makure ina faman tunane sai gizo fuskan shi da ya tsaya min arai ya ke mun a lokacin. Ina ganin kyawawan maza ban taba ganun mai kyau irin nasa ba a rayuwana har barci ya daukeni a hakan. Washe gari nikan na makara da sallah saida umma ta tayar dani a gurguje nayi sallah namike ina gaida umma da kwana kafin na fara tattara kayan da muka dan bata na fita dasu wurin wankewa . Tunawa nayi dana hjy na shiga dakin da sallama na samesu a ciki na gaida su a cikin ladabi nake tambayan mai jiki suka amsa da sauki Nake fadi nazo na kwashi kayan na wanke masu ne don zan tafi na wanko namu a famfo. Allah sarki yar albarka wallahi keda ai jiya an tafi dasu gida a wanke a can saidai cup din nan da suka sha tea da dare dashi. Na duka na kwasa na fita yau kan ban dade ba son yanayin dana tashi cikin sa ba dadi don haka ban kula kowa wirin ba nayi abinda ya kaini na bar wurin. Yanzu ya kike so ayi don ban fahinci inda zancen ki ya dosa ba ya dago yana fadi tare da kallon inda hjy karima take tsaye. Eh akan zancen Abubakar daine nace kai masa magana idan zai bamu kyauta ya rika bayarwa ta hannun ka sai taja tayi shiru. Ya dan dago ya kalleta yace uhumm ina jinki cigaba mana tace a, a shine dama nace zan ma magana don ka kafa wanan dokan . Eh lalai karima tunda gani dattijon banza ko don kawai in farauta maki rai sai inyi bakin jini ga iyalina saboda ke kece ko ? Wai karima ina tunanen ki yake zuwa kwanan nan ne ko dai wani abu na faruwa dakene ba a farga ba ta jefo mai wani irin kallo tare da fadin . Watau na haukace ke nan ba a sani ba ake zaune tare dani hakan kalaman ka ke nufi yanzu Alh don kawai na fadi gaskiya shine laifi ? Hakan nake nufi kin taba jin inda akaiwa uwa da danta shamki don kawai wani ko wata yaji dadi a rayuwan Yau ko cewa Addah tayi ya daina baki kudin shi ga baki daya ai ban tambayan ta dalili don datane ita ta haifi abinta. Balle ya bada sakon har abaki kike ganin kamar Addah ta rage ko bata son a baki din ko wani abu don haka zaki zo wurun dattijon banza ki izani in saba masu ko ? Ai dama nasani nasan haka zaka fada Alh haka dinne ai har kin sani kuma kika fada min yanzu ? Ta wani mikewa tana fasin ni in ma kyautan ya zama magana daga yau a bari don Allah ai ba rasa kudi nayi ba a hannu na. Ina da aikina ko yanzu naga daman komawa sai in koma yace badai gidana ba keda aiki sai idan baki gidan nan. Don Allah yaga halinki na boye da kika boye min da farko ya kareni daga fita aikin ki tun farko kyautan kuma abarshi zan fadawa modibbo din. A daina sai me zaka wani lauyeni kace nace matar kana ragewa ko wani abu can don hadin fada ta fita daga dakin. Tafita tana dan kunkumi don dabaranta ba soici ba gashi kuma zata kulawa kanta tsiya a gidan kan hakan. Dama shawaran kawace data bata tace ta gwada duk ranan da maigida ya kwana da ita har ya nuna jin dadin shi gareta to ita kuma ta gwada sa,anta a wurin miji ga abinda take bukata . Acewar kawar a take miji ke biyawa mutum bukatan shi a wanan lokacin don kawai jin dadin kasamcewan su a tare da suka raya dare suna sunna. Shine tayi kokarin gwadawa gashi kuma ita batayi sa, a ba abin yana neman kwabewa da ita ga baki daya a yanzu. Dakin ta nufa kai tsaye wurin wayan ta taje ta kira kawar ta nan take labarta mata komai daya faru tsakanin ta da Alh. Wani irin tsukin takaici taja tana fadin Allah karima ke banza ce waya fada maki da safen nan ya dace kiyi wanan maganan dashi ? Ai tun jiyan ya kamata a daidai lokacin da abin bai gama fita masa kai ba ke kuma saiki sako zancenki ki gani. Sallaman da taji daga kofa yasa ta katse wayan tana amsawa tare da fadin waye hjy nice Talatu dama wai nazo na fada maki Alh karami zai tafi. To sai akace me to hjy babba ce dai tace nazo na sanar maki Allah kai lafiya mana ko ta fada adan hasale. Talatun ta amsa mata da amin ta juya ta tafi yana zaune kannen shi sun dan mane suna rokon shi kudin anko yana ja masu hankali da hakan talatu ta dawo. Yanayin fuskanta kawai hjy Adda ta kalla tasan da akwai bacin rai a lokacin saidai bata nuna hakan ba don cewa da tayi Allah saukeka lafiya zata shiga wankane yana jin hakan ya mike tare da fadin . To mommy ni zan tafi ke nan sai kuma Allah ya sake hadamu da alherin sa uwar ta mike da sauri a cikin yanayin rashin jin dadi da tafiyan da dan nata zaiyi a lokaci. Modibbo Allah ya tsare ya kare muna ku a duk inda kuka shiga ya dawo muna da kowa lafiya shi da kannen sa suka amsa da Amin. Sai lokacin ya kalli kannen sa yana fadin to ni zan tafi ko sukace aaaa yaya gaskiya ka ganmu kafin ka tafi. Wani gani kuma zan maku bayan wanan gaskiya mudai ka ganmu yana dariya ya saka hannu ya ciro kudi masu yawa mika masu suka hau murna da Allah ya tsare Allah ya kiyayye a cikin murna . Nabila ya kalla yace nasan su Amira ba barci yanzu basu tashi ba idan sun tashi sai ku basu wanan suma su sayi alawa suka ari bakin yaran suna mashi godiya. Haka ya karasa inda daddy ke tsaye yana magana dasu malam mudi ya dan kai rusunne yana fadin daddy zan tafi ke nan . Dafa kafadan shi mahaifin nasa yayi ya mikar dashi yana fadin ka gama da yan rikicin can ke nan yace wallahi daddy . Na dai sallamesu ai mun rabu lafiya yanzu yau su Amira basu fito ba ke nan eh daddy naba Amira nasu ta basu idan sun tashi. Dan murmushi mahaifin ya sake kafin yace ka kyauta dan ko yanzu nasan akwai rikici idan sun tashi sukaji ka tafi ai . Cikin dabara ya fara tafiya da dan nasa don su bar wurin dasu malam mudi suke tsaye ma,ana zaiyi maganan siri dashi ke nan. Ganin hakan suma suka ja suka dan tsaya daga nisa dasu kadan sai da suka danyi kamar tako biyar suka tsaya har lokacin hjy da yaran ta na tsaye daga kofa suna kallon su. Don jira suke suga tashin shi su koma cikin gidan haka ka,idan rakiyan su yake idan maigidan na gida iya kofa suke tsayawa. Yanzun lagos din kuma zaka koma ya dan murmusa kadan yana fadin can zamu koma daddy don yau akai min waya sun gano mai wanan sunan. Allah ya bada sa, a ya amsa da amin ya kara fadin ka kula da kanka don Allah irin wanan aikin nasan hatsatin dake cikin sa sai anbi a hankali. Daga yayi mai fatan nasara ya juya ya dagawa mahaifiyar shi hannu tare kannen shi ya nufi motar da za a kaishi airport dashi. Likita yazo round ya duba Amar din yaga ya samu sauki sosai don haka yace zai bamu sallama zuwa yamma idan yaga yadda jikin nasa yakara samun sauki. Ranan umma ta dan daure ta fita har ta shiga gaida hjy nan datake taimaka muna tun haduwan mu da ita. Sun dan dade suna hira tana jan umma da dan hira sai dai duk dabaran ta umma bata yarda ta fada mata komai daya shafi rayuwan ta har ta fito. Ta samemu zaune muna hira da Amar din dake zaune saman kujera tana shigowa dakin nake fadin umma kinji danki ko . Wai keke za a saya mashi idan mun koma gida da kudin nan wani irin kallo umma ta watsa muna kafin ta juya ta kalli kofa ta koma da sauri ta rufo kofan ta dawo wurun mu duk muna binta da kallon tsoro dan yadda tayi din. Ku saurareni kuji a binda zan fada maku dukkan ku a yanzu kada inji wanan zancen a bakin kowa duk tambayan da wani zai maku akan zancen yaron nan daya bamu kudin nan kuce baku sanshi ba. Mena fada maku muka amsa da bamu san shiba har muna kada kai kada ku nuna tsoro a fuskan ku ko kadan don nuna tsoron ku zaisa su dauka mun sanshine. Shiru mukayi gaba dayan mu na dan lokaci kafin can na dago ina fadin umma wani abune kuma yanzu ? Babu komai jikinane kawai ke bani cewa akwai abinda bamu sani ba a game dasu kawai nayi shiru ina tunane saidai na kasa gano komai a yanzu. Dakin yayi shiru na dan wani lokaci kuma kafin Amar ya mike ya koma saman gadon ya kwanta. Allah ya gani nice duk silan jefa umma a cikin wanan halin damu kan mu ma yanzu idan wani abu ya samu umman mu fa ina zamu saka kan mu na tambayi kaina. Dakin aka turo likitane tare da nurse suka shigo ya dan kara duba jikin yaron kafin yace zai bamu salama sai mu tafi gida. Najin dadin jin hakan don na matsu mu bargidan saida likitan ya gama bayani ya mikowa umma wasu kudi yana fadin canjin mu ne da suka rage ta bamu kudine kuma masu yawa. Saida muka shiga mukaiwa hjy nan sallama take tambayan umma lamban waya umma tace bata da waya ita ai. Tana mamaki take fadin har da ke nayi murmushi tace a kwatanta mata gidan mu wata rana zata kawo muna ziyara. Nan dai mukai mata kwantace ko ta gane ko bata gane ba muka kara gaba abin mu muka barsu a asibitin don sukan basu san ranan sallama ba sukace. Kamar ba asibiti muka fito ba don yan gidan ba wanda yai muna an dawo lafiya ya maijiki. Karshe mu muke gaidasu da u na weldone su amsa muna a gadarance da thank u jo mu wuce har muka kai dakin mu da har lokacin a hargitse yake. Umma taga yadda aka tone dakin wurin bincike ta tsaya nikan ban tsaya ba dole na shiga gyaran dakin namu don ba zamu iya zama haka ba dakin a hargitse. Nan dai har na gyara suka koma ciki ni kuma na dan tsaya waje ina wanke wasu kayan mu a lokacin ne naji gudu na dago don ganin me akewa gudu din. Yan sandane cikin wani irin kaya mai ban tsoro suka shigo gidan yasa kowa ke gudu zuwa dakin shi ashe. Nima na shige dakin mu na mayar da kofa da sauri na rufe suna shigowa gidan mukaji ana sanarwa kamaf haka. Mun san kana cikin gidan nan don haka ka mika wuya a cikin saukin kai a hankali na kalli umma ina fadin wa sukazo nema umma ? Bakina ta kaiwa duka tana fadin inyi shiru da surutun tsiya can mukaji na banke banken kofan muka kara make junan mu mu uku a dakin a cikkn tsoro har suka kawo dakin mu da ba wani kofan kwarai ke garemu ba dama. Wani dan sandane ya shigo yana fadin ku shigo kofan a bude take ya shigo babu dadin gani yana bin ko ina da kallo. Har kayan mu ya dan dadaga ya fita yana fadin bai wanan dakin karshe suka tataro kowa na gidan dayan su ke nuna muna photon wani guy yana fadin mun san wanan kowa yaba hirgiza kai mukace bamu sanshi ba. Wani tsawa ya daka kowa ya firgita yace a gidan nan yake har tsawon mako hudu yake nan ma shiriru akayi ba wanda yace ya san shi a gidan. Sunyi iya binciken su basu gane komai ba har suka aikinsu da yan tambayoyi akace ba a sanshi a gidan suka gaji suka tafi bayan sunce zasu sake dawowa ZAINAB IDRIS MAKAWA qANA DARA GA , , , , , , , , , , , 1️⃣0️⃣ BY ZAINAB IDRIS MAKAWA, , , , , , , BISSIMILLAHI RAHAMANIN RAHIM WA, LAL DALIN AMIN, , , , , YAR UWA PAID NOVEL NE DON ALLAH KI BIYA KI KARANTA A CIKIN SALAMA DARI BIYAR NE KACAL YAR UWA. Hankalin mu bai kwanta duk da sun wuce sun bar gidan amma kowa na waje cirko cirko ana faman mayar da magana kan zancen. Dukawa nayi naci gaba da wankin kayan da nakeyi daga can bayana naji muryan wale na fadi. U sahiba wen wan trobe for ur self thank god that day d man no kill u sai kowa ya kallo ni na daga ina fadi. Wale, i beg , me i no wan wahala wooo, mey u no comfire me wit that men sha bi i no dem before ? De fall me down, nd my food dont fawl, nayi i say mey de pay, nd de pay me , de give me anoda food ogwa ? witin consen me with dem again ? Maman shi tace dashi, wale may u no cary ur wahala come rich me shabi u no say dat mater no be smol case wooo . Uwar ta kwaba shi tana koran shi daga gidan ya fita yana wani irin tako na yan iska tabi shi tana zagi. Na dauki kayan dana wanke na nufi wurin da muke shayi a nan idona yakai kan wayan dake kasan yashe bayan wani kwandon roba na kayan iya bisi dake kusa da dakin mu. Na faki idon mutane na duka na dauka na tura a aljihun dan rigan dake jikina da sauri na karasa shanyin na koma dakin mu har lokacin umma na waje na bi wayan da kallon mamaki ni kadai a dakin. Ko da ban san waya ba nasan cewa wanan wayan babbace kasancewa umma na waje har lokcin bata shigo dakin ba. Yasa na fita don zuwa in debo ruwa a inda muke diban ruwa fitana yayi daidai da sake dawowan yan sandan gidan. Suka zo neman wayan duk an tara mazan gidan da yan matasan mata kan wayan sai binciken su akeyi kan wayan. Don ya nuna a cikin gidan wayan yake kuma yanzu sunzo signal bai nuna wayan na gidan ba duk an bincika ba a samu wayan ba . Inda Allah ya taimakeni shine ba wanda ya kawo ranahi a kaina cewa wayan yana hannu na a gidan har yan sandan suka tafi don ya nuna an bar gidan da wayan lokacin. Hankalin shi ya tashi matuka na rashin ganin wayan nasa daya fado gurin mayarwa a aljihu bayan sun gama waya an fada mashi wanda suka zo nema baya gidan ya bar kasan ga baki daya. Yabi ta ghana ya fita har yabar kasan ghana din a lokacin shine dalilin da suka bar yan gidan mu din suka koma bincike ga landlord din gidan ta yaya ya bashi gida haya a ina kuma suka hadu dashi har ya bashi hayan ?. Ko dana dawo kowa na dakin sa wasu kuma sun gudu sun bar gidan a lokacin fita na sake yi na je nemo muna abinda zamuci duk da mun dawo da abincin da hjy ta bamu kafin mu bar asibitin. Sai dai shi Amar yace tea zai sha shi yasa nafita wurin nema kayan hada shayin a hanya ne wayan ya fara vibration a cikin aljihuna sai dan kara har hakan yasani firgita. Don sam na manta da zancen wani waya dana tsunta ga baki daya sai lokacin har kiran ya katse ban san yadda zan dauka ba ashe tun wurin diban ruwa ake ta kiran layin ban sani ba ina can ina daga bohol. Ashe hjyn su modibbo ne take kiran layin dan nata tunda ya bar gida basu samu wayan shi ba sai wanan lokacin shine hankalin su a tashe ta samu aka dauka kuma ya katse Aka sake kiran layin nayi sa,a na danna daidai na dauka naji muryan mace tana fadin haba modibbo ka daga muna hankali haka ? Nayi shiru ina sauraren hausan matar da muryab ta ta sake fadin wai bada kai nake magana bane ga daddy kuma yana ta kokarin neman ka tun dazun. Ba mai wayan bane na fada tare da fadi me ego hausa kosi hausa fa hausa kadan kadan mama don jin danayi tace daddyn ku. Who are you aka fada wanan karon muryan namiji ne nace iam d one who found d phone i don't know d owner self. Kinji me take fada aka fada a cikin wayan ina ganin wayan ta fadi maine watace ta tsunta nace eh na samune a cikin gidan mu dazun. Ke wacece ni ni sunana sahiba na fada kai tsaye a cikin hausawa gwari gwari mai kama dana yare wani unguwa na fadi sunan unguwa . Na karashe da fadin a fada mai yazo ya karbi wayan shi idan kun same shi nakarashe da nagode. Allah yayi maki albarka nace amin woo nagode kada ki kashe aka fada a kausashe nace oyah oda Yan tambayoyi ya dinga min ina bashi amsa a cikin irin hikiman su na tsufin ma,aikata har ya gane komai da yake son ji a wurina ban sani ba . Muna gama wayan dasu na kali wayan ina jin dadin jayi waya mai tsayi a cikin yaren hausa duk da bansan da wanda nayi wayan ba a lokacin. Shi kuma daddy su neman layin wani abokin aikin dan nasa yayi ya fada mai ya nemi moddibon ya fada mai yadda mukayi. Kodana shigo gida nake fadin ni bazan sha tea ba wanan abincin zanci wanda ya saura muna na rana. Har na fara ci na tuno nake ba umma labarin wayan dana tsunta din har iyayyen maishi suka kirani. Da farko kirji ta buga amma tana jin har nayi kwantancen inda za a sameni a karbi wayan sai ta dan sake take min fada dana tsunta me yasa ban bata ba a lokacin ? Nayi shiru kafin ince umma naga kowa a wurin ne lokacin kin san kuma gidan nan da tsunce. Modibbo yana kwance daki abin duniya ya dameshi na rashin ganin wayan shi gashi kuma bukatan abinda suke ganin zasu kawo karshen shi ba samu ba a garesu. Yaji anyi nocking din kofan dakin shi da alaman akwai wani a kofan lokacin dake son shigowa wurin shi . Ya mike daga shi sai dogon wando da fari singlet a jikin shi haroon ya gani tsaye a kofan mamaki ya kamashi. Sun gaisa ya bashi wuri ya shiga dakin suka kara gaisawa da shi yace oga yace na zo na fadama anga wayan ka a hannun wata yarinya Sahiba. Sunan ya maimaita a cikin mamaki Sahiba a ina ta samu wayan ya kwashe yadda mukayi da mahaifin shi ya fada mai. Nan ya nufi wurin dan jakkar kayan shi da sauri ya dauko riga ya zuru ya dauki bindigan shi ya soka a bayan shi suka fita a waje yake fadawa security din da su biyo shi anga wayan shi a wanan gidan hannun wata yarinya. Suka biyo shi da sauri baya suka shi shiga motocin su zuwa gidan mu basu samu isowa ba sai sha daya da wani abu duk yan gidan sun dawo a lokacin sai yan kalilan ne basu dawo ba. Mukan har mun kwanta sai jin jiniyan mukayi a kofan gidan naji umma na fadin kai innalillahi wanan masifa yau da me yai kama hakane ? Kamar mahaukata suka shigo duk abinda suka gani a gaban su suyi ball dashi ina yarinyar da ake kira Sahiba suka fada. Ga kowa ya fito hankali a tashe matan daga su sai daura gaba wasu kuma sai dan guntun wando a jikin su . Umma na kokarin budan kofan aka bamko kofan da karfi tace subbanallahi wetin we do again ? Sahiba are you ? Sukace wa umma ta girgiza kai kafin tace na my daughter be Sahiba sukace ina nake ? Sai gani na fito daga dakin ina mutsukan idanu aka tambaya a bayan su kun ganta eh ya bada amsa tare da fadin karamace fa ogo. Ku kawo ta nan ya fara tunkudani na juyo ina fadin na wetin i do ? i no be criminal woo stop pushing me like dat. Ai kafin yace me gulma ya fara tashi a gidan kowa da abinda yake fadi har gaban ogan nasu aka kaini naja na tsaya gaban shi kim kam. Where is my phone ya tambayeni nace saka hannu a cikin aljihun riga na dauko na mika mai ai sai gida ya dauka olusi omo buruku. Na dis smal rat stil d officer phone ? smol girl like u shame on u omo kowa dai yan gidan namu da abinda ke fitowa bakin shi lokacin . Wani tsawa ya daka duk aka natsu yace yarinyar nan ta tsunci wayana ba sata tayi ba don ta kira parents din na ta fada masu da inda zamu same ta. Kuma mahaifina yace nayi mata

Chapter 8 of 9