jatau ya fara bayaninsa shugaban sojojin yai zuru baki bude yana duban jatau, koda jatau ya idda bayanin nasa ya numfasa zai tafi ai sai shugaban sojojin ya daka masa tsawa yace "kai bamu gane kwatancen kannan ba don haka ka zo tare damu ka nuna mana kauyen in yaso bayan ka nuna mana sai ka dawo abunka"
Duk da cewa jatau ya tsorata matuka da tsawar da sojan yai masa amman bai nuna a fuska ba, hasalima bata rai yayi ya juyo ya dubi sojan yace "gaskiya bazan iya binku ba don kauyen nada nisa sosai sannan ni yanzu farauta na fito yi kunga kuwa babu dalilin da zai saka na bar farautata na biyoku"
"Aiko dolenka ka biyomu ko kana so ko baka so" shugaban sojojin ya fada bai jira amsar da jatau zai bashi ba ya dubi wasu kartin sojoji uku yace su taho da shi, sojojinnan suka zabura kaman dama abunda suke jira kenan sukai kan jatau da nufin su kamashi
Jatau kuwa koda yaga sojojin sun yo kansa sannan ya tabbatar da babu hanyar tsira kuma gashi bazai iya bugun su ba ai sai ya latsa layar batarsa nan take ya bace bat tamkar bai taba wanzuwa a wurin ba,
Ran shugaban sojojin ya baci ya dubi yaransa gabadaya yace su bazama a dajin duk inda jatau yashiga ya futa su kamoshi su kawo masa shi,
******
Bayan mintuna talatin da tafiyar sojojin sai gasu sun dawo da jatau a rataye a kafadan wani jibgegen soja mai kirar mutanen farko, sojan na karisowa ya jifa da jatau a gaban shugabansu yadda kasan yai jifa da kayan wanki.
Shugaban sojojin ya durkuso ya dubi jatau yace "wato taurin kai zakai mana ko ina da maganin irinku" yana rufe baki yai wa katon daya dauko jatau inkiya da hannu nan da nan katon ya cire bel din jikinsa ya hau jibgar jatau da ita, jatau yana kara gamida ihu amman sojan ko yasan yana ma yi daya gama jibgarsa suka tasheshi ya runga nuna masu hanya duk da kuwa cewa yana matukar galabaice har suka isa kauyen MAZURARI a lokacin yammaci yayi shugaban sojojin yai masa godiya suka kara gaba suka barshi a wurin
Jatau na yashe a bakin kauyen mazurari aka kece da ruwan sama tamkar da bakin kwarya, ya mike a jigace ya fara tafiya yana nufar hanyar da zata komar da shi kauyen zauna da shirinka
MAFARAUCI JATAU
Marubuci - Shuraih Usman
© 2020 Shuraih 99% - HAUSA EBOOKS
Part 7 - karshe
A iya sanin jatau tun daya fara sana'arsa ta farauta bai taba cin karo da kwatankwacin irin wannan rana ba ace wai ya fita farauta ya dawo gida hannu rabbana sannan ga karin dam banzan duka da sojoji suka lakada masa gamida gigitaccen bugun da ruwan sama yai masa, sai a wannan lokacin jatau ya fara tariyo abun duk da ya faru da shi a wannan rana tamkar cikin majigi har lokacin da tunaninsa ya kawo sanda matarsa uwani ke yi masa gargadi akan batun Insha Allah.
Jatau yayi kwafa gamida dunkule hannun hagunsa ya naushi hannun damansa da shi, yace a zuciyarsa "wannan duk laifina ne dana sani sanda uwani tace na fadi kalmar nan dana fada na fice daga jaraba ai kuwa IN ALLAH YA YARDA bazan sake aikata wani abu ko in furta wata kalma batare dana ambaci kalmar In Sha Allah ba"
Haka dai jatau ya cigaba da tafiya a jigace har ya iso kauyensu ya nufi gidansa lokacin kusan sha biyun dare kauyen yayi tsit bakajin motsin kowa in ka dauke kukan tsuntsaye da kananun kwari gamida kukan kwadi.
Jatau ya isa kofar gidansa ya kwankwasa, yana mai doka sallama
Jiyayi shiru ba a amsa sallamar ba hakan ya tabbatar masa uwani ta dade da yin barci, ya zage iya karfinsa ya runga dukan kofar yana kwada sallama
Uwani dake kwance ta farka firgigit tamkar wacce aka tsikara da allura kasa kunne tayi don ta tabbatar da abunda take tsammani, ji tayi an doka sallama da wata shakakkiyar murya mai kama da muryar mijinta, da fari ta dan tsorata har tayi tunanin ta koma barci abunta sai wata zuciyar tace da ita kul jeki dubo dai kiga ko waye,
Ta mike tsaye ta dau fitilar kalanzir dake ajjiye a saman wani kututturin itace wanda ke tsakiyar dakin ta fice, har yanzu ana dukan kofar gamida doka sallama, a tsorace ta ce "waye wannan ke damuna da tsakiyar darennan" ta fadi yayinda ta kariso bakin kofar gidan,
Jatau dake daga waje yace "Mijinki ne Jatau IN ALLAH YA YARDA"
Cikin hanzari uwani tayi maza ta bude kofar, koda tai arba da mijinta jatau taga yanayin dayake ciki sai ta kamu da tsananin mamaki ta fara dube duben bayansa da gefensa don ganin dabbar daya farauto yau har daya sha wannan dan karan wuya haka, daman ita tun da taga magaruba ta wuce jatau bai dawo ba tasan kila yau mijinnata yayi kamun da bai taba yin irinta bane, sai gashi yanzu ta yo arba da shi hannu rabbana ta dubi jatau dake a matukar galabaice ya durkushe a bakin kofar gidan tace " mai gida yana ganka haka me ka kamo ne yau"
Jatau ya yamutsa fuska yace "yau kam ban kamo komai ba Insha Allah"
"A'a ban gane ba maigida me kake nufi ne"
"Kedai bari kawai mu shiga daga ciki nayi wanka, na kimtsa cikina sannan na baki labarin duk abun daya faru Insha Allah"
** *** **
Tun daga wannan rana ya zamanto duk wata jimla da jatau yayi sai ya karasheta da kalmar In Allah ya yarda,
Alhamdulillah
Anan na kawo karshen wannan labari fatan za'ai hakuri da duk wasu kurakurai da aka ci karo da su,
Shuraihu Usman
-2020
Matukar godiya ga ahalin group din
DANDALIN LITTATAFAN YAKI BY IBNI ABDALLAH
DANDALIN LITTATAFAN YAKI BY SMART RAYYANU
TSANGAYAR LITTATAFAN YAKI
DANDALIN LITTATAFAN HAUSA BY SHURAIH USMAN
HAUSA NOVELS ONLY
TASKAR LITTATAFAN HAUSA
dama dukkan waƴanda ke bibiyan labarin
Zan dan sarara na ƴan wasu kwanaki kana na fara kawo maku wani littafin nawa mai taken ABOKAI
An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://thausanovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.thausanovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels