Share this page
1 / 2
An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://thausanovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.thausanovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels MAFARAUCI JATAU Marubuci - Shuraih Usman © 2020 Shuraih 99% - HAUSA EBOOKS Part 1 A can wani kauye mai suna Zauna da shirinka anyi wani hatsabibin Mafarauci mai suna Jatau, A kullum izan jatau zai fita farauta sai ya lissafa sunayen dabbobin da zai kamo da Kuma adadin yawansu, Babban Abun mamakin kuwa shine da zarar ya dawo daga farautar sai mutane su gansa da dabbobin daya lissafto Wannan yasa mutane da dama ke yiwa jatau kallon hatsabibin mutum wasu ko gani suke Yana aiki da almatsutsusai Ance dakwai ranar da jatau ya bugi kirji a tsakiyan kasuwa yaci alwashin zai shiga dauji ya farauto zakanya mai 'ya 'ya da 'ya 'yanta a Raye ba amace ba Mutanen kauyen zauna da shirinka sunyi matukar mamakin jin furucin MAFARAUCI JATAU, inda wasu daga cikinsu ke ganin shakka babu zai iya farauto abun daya fada Rannan yara da manya sukai cincirindo a filin kasuwa suna jiran dawowar MAFARAUCI JATAU, A ka'ida izan jatau ya futa farauta baya wuce sa'o'i Biyar yake dawowa amma a wannan rana sai da ya shafe kusan sa'o'i takwas bai dawo ba Koda Jama'ar dake jiran dawowan jatau suka ga har magriba ta gabato jatau bai dawo ba sai suka yanke shawarar su tafi bayan gari hanyar da jatau yake biyowa izan zai dawo daga farauta su tarbeshi Suna zaune a bayan gari suna jiran jatau na tsawon lokaci amma babu shi babu labarinsa wasu daga cikin mutane suka fara zunguro baki suna cewa "ai duk karyar banza ce, wancan lokutan ma Allah ne ke bashi sa'a, yanzu kuwa Allah ya karbe Abarsa " "Haba tayama za'ai ace mutum ya farauto zakanya da 'ya 'yanta a raye dama a mace ne da sauki" "Kai da Allah ku zo mutafi gidajenmu ku kyale makaryacin nan inajin zakanyar ma ta ruga data handameshi" masu fadin hakan suka juya da zummar su koma cikin gari suna masu gunaguni da karyata mafarauci jatau Ana cikin haka kwatsam sai aka hango jatau yana tafe cikin shirinsa na farauta wani mutum dake gaba gaba ya wangame wangamemen bakinsa mai kama da shantu yace "ga MAFARAUCI JATAU nan tafe " Mutanen da suka juya da zummar komawa cikin gari suka juyo cikin al'ajabi suna hangen jatau dake nesa dasu, abun daya daurewa mutane kai shine jatau bai taba cin alwashi batare da ya cika ba amma a yau alkadarinsa ya karye domin kuwa shi kadai yake tafe batare da zakanya da yayanta ba, Mutanen da suka juyonnan sukai tsaki wani mai zungureren kai yace "shin bana fadi maku Alkadarin jatau ya karye..." Maganar tasa ta katse lokacin daya hango jibgegiyar zakanya tayi fitar burgu daga cikin dajin dake bayan jatau 'ya 'yanta na take mata baya Koda mutane suka hango zakanyarnan da yayanta sai suka rude suka ruga cikin gari a guje suna kiran sunan jatau ya taimakesu kada zakanyar ta kashesu Babu abun da ya sake tabbatarwa mutane cewa jatau ba karamin hatsabibi bane face ganin zakanyar da sukayi babu takunkumi a bakinta hakanan babu wata igiya a jikinta kuma haka jatau ke tafe tana biye dashi tamkar bawa da ubangidansa Haka jatau ya shiga kauyen zauna da shirinka da zakanyar yana bi lungu lungu sako sako yana yiwa kansa kirari Zan cigaba MAFARAUCI JATAU Marubuci - Shuraih Usman © 2020 Shuraih 99% - HAUSA EBOOKS Part 2 Wannan rana gabadayan mutanen kauyen zauna da shirinka a gida suka yini sun garkame kofofin gidajensu da kwado suna daga ciki suna jiyo ihun jatau yanayiwa kansa kirari Hatta mai garin kauyen yammacinnan bai futo fada ba, liman kuwa sai a gida yai sallar magriba da isha'i Kauyen yai shiru bakajin motsin kowa tamkar garin da mahara suka kai wa hari, da jatau ya gama zagaya garin lungu da sako sai ya tasamma hanyar gida, yana karisowa bakin kofar gidansa sai yaga kofa a garkame abun ya fusatashi ainun yasa kafa ya banke kofar, dama kofar tasha ruwa da rana take ta karye ta fadi gefe guda Matar jatau dake cikin daki ta kwala ihu lokacin dataji karar karyewar kofa ko tantama batayi Jatau ne ya dawo, Tun lokacin da jatau ya dawo da zakanya wani ya tsegunta mata kuma tasan gida zai kawo zakanyar hakan yasa ta kulle kofan gidan nasu da kwado "Ke uwani kina inane" jatau ya kwala mata kira lokacin daya karisa shigowa cikin gidan haryanzu zakanyar da yayanta bakwai na biye dashi, zakanyar sai gurnani take tamkar ta fada rumbun dabbobi, Jin gurnanin zakanyar ne ya kara tsorata Uwani matar jatau nan da nan ta fada kasan gado, jatau ya shigo dakin yana kwala mata kira ga mamakinsa bai ganta ba hakan yasa yafara dube dube yana lekawa kasan gado kuwa sai ya ganta a takure jiki sai rawa yake tamkar injin markade Hannu ya sanya ya daga Gadon ya ajjiye a gefe uwani ko sai t kwala ihu take, tana kudundune kanta a cikin kafafuwanta, Jatau ya kariso gabanta yana mai fashewa da dariyar keta yace haba uwani kefa matar MAFARAUCI JATAU ne ko da mutanen gari zasuji tsoron zakanyarnan ke bai kamata kiji tsoronta ba kada ki badani man Uwani dake takure a kasa ta dago kanta tace haba maigida kamanta cewa ni macece kanafa ganin yadda gabadayan mazan garinnan suke gudun zakanyarnan shine saboda rashin tausayi ka daukota ka kawomin gida kumafa magnarki hakane dun wallahi har liman yau ya gagara fitowa sallar magriba kuma ma nasan ba zai futo na issha'i ba, jatau ya fadi yana kokarin zama kusa da matsoraciyar matar tasa Uwani ta dubeshi tace dun Allah mai gida ka fitar da ita daga gidannan mana Jatau ya danyi jim kafin yace duk da dai ba haka naso ba amma gobe zan mayar da ita cikin dawa,ai dama saboda masu cikamin bakine a kauyennan shi yasa na daukota wallahi badun ke ba da sai nabi gidan kowa gobe da safe da zakinnan, ammana dai da asubahin farko zan mayar da ita A matukar rikice uwani tace Asubahin farko mai gida, me zai hana ka maidata yanzu tunda dama kai dawa gidanka ne, Nan dai uwani ta rungi lallashin jatau tana bashi baki gamida yi masa kirari har ya ya tashi cikin daren ya maida zakanyar da 'ya 'yanta cikin jeji. Washe gari kuwa babu wanda ya fito sallar asubahi har rana ta keto gari ya waye babu mahalukin daya fito waje a cikin jama'an kauyen Zauna da shirinka, Sai da jatau yabi layi layi ya sanar ya koma da zakanyar sannan jama'a suka fara fitowa cikin kaffa kaffa don tsoron ko karya jatau yai masu ... Zan cigaba MAFARAUCI JATAU Marubuci - Shuraih Usman © 2020 Shuraih 99% - HAUSA EBOOKS Part 3 Tundaga wannan rana da jatau ya kamo zakanya da 'ya 'yanta mutanen kauyen zauna da shirinka suka sallama al'amarin jatau, mai gari da kansa ya sanya aka kira jatau ya nada shi SARKIN DAWAn kauyen **** Ina ya Allah babu Ya Allah Rannan Jatau yayi gagarumin shiri zai fita farauta, kamar yadda dai ya saba izan zai shiga dawa ya kan sanya wata falmara ta fatar zaki, sannan ya cika damutsansa da guraye, ya kuma soke dagage a kugunsa wani lokacin ma har angara yake sabawa a kafadarsa, sannan ya rataye battar ruwa a kafadar hagunsa, kafadar dama kuwa kwari da baka yake ratayawa dauke da kibbau, sannan ya rufe kafarsa da takalmin jeji yar ubansu kuma ya shafe fuskarsa da bakin shuni tamkar sojan da zai fita shahada, Aduk sa'in da jatau yayi irin wannan shiri mutanen kauyen da sun hangesa suke canza hanya, izan kuma tsautsayi yasa sukai kicibus sai dai kaga mutum ya fadi akasa yana yiwa jatau kirari, inko bako ya shigo kauyen zauna da shirinka yai arangama da jatau cikin irin wannan shiga saide kaga ya zura a guje yana ihu yaga Aljani akwai wani lokaci da akai wasu baki mutanen birni a kauyen sun zo duba lafiyan mutanen kauyen, ranar da bakin zasu koma birni a motarsu sun kamo hanya sunyi nisa sosai da gari ai kuwa sai akaci sa'a rannan jatau ta gefen ya fita farauta kuma ya harbo kura, haka ya saba matacciyar kurar a wuyansa yana tafiya shi kadai akan hanyar Direban Bakin 'yan birnin na cikin tuki bai ankaraba sai ya hangi mutum a gabansu cikin gagarumin shiga sannnan ga fuskarsa tasha bakar shuni, ihu direban ya kwala lokaci guda ya taka birki, sauran mutane uku dake cikin motar har sun fara gyangyadi suka farka a firgice suna tambayar direba ko me ya faru, a razane direban yai masu nuni da jatau dake dan nesa da su ya tsaya yana kallonsu, ai koda sukai ido biyu da jatau sannan kuma suka hangi kurar dake sabe wuyarsa sai dukkaninsu suka kwala ihu lokaci guda suka firfito daga motar suka yanki hanya a guje gudu suke iya karfinsu suna cikin gudunne suka ci karo da wasu dattijai biyu, dukkansu suka fadi a kasa daya daga cikin dattijan yai saurin mikewa, kafin ya ce wani abu tuni har mutanen birnin nan sun mike sun rantaya a na kare koda ganin hakan ai suma dattijannan sai suka sabi na kare kai inka gansu ka rantse da Allah baza su iya tafiya mai tsayi ba amma sai gasu sun zage suna runtuma gudu, suna cikin gudunne daya daga cikin dattijan ya daga murya ya tambayi bakin birnin kome ya sa suke gudu, direba dayafi kowa tsorata yace Wallahi Aljani mukai arba da shi a can baya... kafin ya karisa maganar tasa ne dattijan.suka hada baki suka ce Aljani Direban yace eh wallahi, kan direban da sauran bakin yan birnin nan su farga tuni har dattijan nan sun wuce su sun basu muguwar rata, direban ya daga musu murya yace dan Allah baba kujiramu mana Aiko amasawa basuyi ba suka cigaba da runtuma gudu tamkar zasu tashi sama tun daga bakin kauyen wani saurayi ya hango dattijan na sharar gudu, ya tsaya yana jiran suzo yaji me ya faru ai koda suka kariso basu tsaya ba suka ce dashi Aljani ke biye da mu, dan saurayin najin an ambaci Aljani shima ya runtuma a guje, cikin dakiku kadan kauyen zauna da shirinka ya hargitse da guje guje gamida iface iface, duk inda dattijan nan sukai dazar sun hangi tarin jama'a sai su kwala masu kira suce kai yan banza ku gudu Aljani ke biye damu, MAFARAUCI JATAU Marubuci - Shuraih Usman © 2020 Shuraih 99% - HAUSA EBOOKS Part 4 mai gari dake zaune a shingensa shi da sauran manyan gari, suna zaune suna tattaunawa akan cigaban da suke hangen ya kusa cimmasu tunda gashi har anfara aiko baki daga birni, "yanzufa inajin taki za'a aikomana " mai gari ya fadi yana duban liman Liman dake sanye da babban riga ya nannade gangamin rawani a kansa ya ce "ai ranka shi dade ni bama ta taki nake ba, kasan sabon gwamna yai mana alkawarin zai janyo mana wuta da ruwa da zarar ya hau kujera ina zaton masu aikinne bakinnan suka zo duba wur...."Maganar liman ta katse lokacin da ya hango daya daga cikin bakin da suka zo kauyen ya nufo wurinsu a guje, cikin mamaki ya dubi mai gari yace ranka shi dade kaga daya daga cikinsu ya dawo anya lafiya kuwa" liman bai kai ga idda maganarsa ba ya hango sauran mutane biyun da suka zo daga birnin sun bullo suma a guje suna nufosu, Mai gari dake hakimce saman kujera ya dan yi kwanto kasa kadan ya hanga inda yaga liman na kallo, sauran mutanen fadarma suka duba inda suka hango bakin su uku daya a gaba biyu a baya sai runtuma gudu suke, Dagani ba lafiya ba irin wannan gudu haka, mai gari ya fadi yana duban wani dogari dake gefensa a tsaye, Bara su kariso muji meyafaru, dattijon dake zaune kusa da liman ya fadi yana sake hangen bakin bakinnan kuwa na karisowa suka afka gaban mai gari suna haki tamkar ransu zai fita, jama'ar dake wurin nayi masu sannu mai gari ya aika dogari gida ya debo nasu ruwa bayan dogari ya kawo musu ruwan sunsha hankulansu yadan kwanta sai mai gari ya tasammasu da tambayar me yafaru, Dukkansu suka hade baki sukace wallahi mai gari Aljanu Mukai arba da su a hanyarmu to komawa birni kuma nan kauyen suke tafowa Mai gari da sauran jama'ar dake wurin suka firgita da jin maganganun bakin sannan Liman yace Ranka shi dade inajin fa ko... Maganar tasa ta katse yayin da wani dattijo yai dirar mikiya a shingen . Kallo daya zakaiwa dattijon kasan a firgice yake duba da tsaban haki da yake gamida yanayin fuskarsa zumbur mai gari ya mike a razane yana duban dattijon yace malam tanimu lafiya naganka a haka dattijon da aka kira da malam tanimu ya maida numfashi yace inafa lafiya mai gari, Rundunar Aljanu sun bayyana a kauyennan gari ya dauka ko ina kabi baka ganin kowa yanzu haka mutane na can sun cika masallaci babu matsaka tsinke, Ehee mai gari yafadi cikin Razana A to bamuga ta zama ba amman kai malam tanimu don rashin imani shine kukaki sanar dani da wuri, Malam tanimu yace yallabai nifa duk tunanina kasani, don yanzu haka inkaita tsakiyan kauyennan girgizan kasa a ke acan ta wurin na biyo, Aljanu ne a jere sunfi milyan dubu kowannensu rike da bindiga da takobi da mashi da barandami da lauje da gatari da gitta, ni kaina badun ina tare da layar kakana na uku ba toh da tuni babu labarina Sauran jama'ar wurin suka sake kidimewa liman ya mike da sauri ya na kokarin cire malum malum dake jikinsa yana gama cirewa ya dubi su mai gari yace zamafa bata kama mu ba tashi zamuyi muma mu je masallaci a cigaba da du'a'i a can, mai gari ya mike sauran yan majalisa kowa ya mike suka dau hanyar da zata sadasu da masallacin kauyen kwallin kwal, suna cikin tafiyarne suka zo ratsawa ta wani rumfar baduku mai gari dake gaba yana jejjefa kafafuwa tamkar zalbe malum malumsa na yawo a iska kwatsam sai malum malum nasa ya makale a jikin wata kusa dake jikin rumfar mai gari yaja malum malum yaji an riketa ta baya ya juya don ganin ko daya daga cikin fadawan nasa ne ya riketa savanin hakan sai yaga babu wanda yai kusa da ita hasalima malum malum tana gefene a jikin rumfar kida ganin haka ai sai mai gari ya kwalla kara "wayyo Aljanu sun rikeni" Liman dake biye da maigari yana jin hakan ya a matukar razane ya arce sauran yan majalisa da bakinnan suma suka fice a guje suna masu rufawa liman baya ko duban mai gari basu tsaya yi ba bare ma ta kai ga sun taimaka masa Shi kuwa mai gari in banda ihu da karaji babu abunda yake wa innahu min sulaimanu wa innnahu bismillahirrahmanirrahim , ya ayyuhallazina amanu , inna anzalnahu fi lailatil qadri haka yaita sambatu yana jawo duk ayar da tazo bakinsa a jikin kokarinsa na janye rigar malum malum ne kusar data rike rigar ta bantalo daga rumfar hakan yasa mai gari ya zube a kasa sakamakon karfinsa daya tattara wurin kwatar malum malum din ai koda yaji sakayau an saki rigar tasa sai yai zumbur ya mike da rurrufe ya ari na kare Liman da yan majalisa gamida bakin birnin nan basu tsaya a koina ba sai a masallacin garin inda suka ganewa idanunsu abun mamaki, baki bude liman ya tsaya a kofar masallacin yana duban yadda mutane suka cika masallacin har waje, masallacin da in an cika kenan a cika sahun gaba dana biyunsa amma yau jamaa har a rufin masallacin. bakinnan suka ingiza liman ganin ya tsaya ya tokare hanyar shiga masallacin sukai sauri suka shige cikin jama'a dake ta karanto ayoyin kur'ani, kowa ka duba a masallacin a matukar firgice yake yana karanta ayar kur'ani kuma kowa da ayar dayake karantowa Mai gari kuwa Koda ya samu ya fizge malum malumsa daga jikin kusa Wanda shi a zatonsa aljanu ne suka rikesa, ya sharara a guje baya ko duban gabansa a cikin gudunnasa ne yaci karo da jatau dukkansu suka zube a kasa Mai gari na mikewa yai arba da kurar da jatau ya farauto ai sai ya kwurma uban ihu ya fara Jada baya jatau ko koda yaga haka sai ya Mike tsaye ya na kokarin fahimtar da Mai gari shine fa, "Mai gari me ya faru ne haka naganka a tsorace," sai a sannan Mai gari yadan ji Sanyi a ransa sakamakon Jin muryar jatau da yayi ya dago Kai ya dubeshi yace a'a jatau Kaine jatau yace e nine Tom kurar Nan fa " Mai gari ya bukata Matacciya ce ai maigari" jatau ya bashi amsa, sannan yacigaba da " Amma lafiya kuwa Mai gari" Mai gari ya Mike tsaye Yana kokarin cire malum malum sa daga jikinsa, "ina fa lafiya jatau Aljanu sun tasamma kauyennan namu, a daidai rumfar mudi baduku suka rikeni da kyar na samu na kwaci kaina yanzu haka gabadayan jama'ar kauyennan suna can a masallaci nima daka ganni yanzu can na nufa" Jatau ya jinjina maganar yace toh muje masallacin MAFARAUCI JATAU Marubuci - Shuraih Usman © 2020 Shuraih 99% - HAUSA EBOOKS Part 5 Tun daga nesa jama'ar dake cikin masallacin suka hango jatau da mai gari suna tahowa, dayawa daga cikinsu sun Dan ji Sanyi Sanyi a ransu na ganin jatau don sun San Jatau ma kadai zai iya kora Aljanun su koma inda suka futo Su kuwa bakin nan Koda suka kyallara ido suka hango jatau ai sai duk sukabi suka rude suka runga yiwa mutane sambatu suna cewa gafa Aljanin can yana zuwa a tare da maigari, wallahi aljanin ne dai da ya koro mu Dajin hakan mutane suka baibayesu suna tambayarsu waye Aljanin, bakin suka nuno jatau sukace gashi can ya kamo sarki suna zuwa tare, koda mutane suka hango jatau ne suke nunawa sai suka ce dasu ai ba Aljani bane jatau kenan mafarauci mai shirin Aljanu, Yayinda bakin suka tabbatar da cewa Jatau mutum ne ba Aljani ba adaidai lokacinne jatau suka kariso cikin masalllacin shida mai gari, jatau ya tambayi mutanen masallacin acikinku waya fara arba da aljanun, wasu dattijan mutane su biyu suka matso gaban jatau sukace , mudai bamuga Aljanun ba Amman ga wayanda suka gansa nan yana nufo kauyenmu suka nuno bakin birni, Bakin kuwa suka hau zazzare idanu sai direbane yai bayanin abunda ya faru na tsoratasun da jatau yayi da iriyar shigarsa suka zata ko Aljani ne, **** *** Yayinda jatau ya idda gawurtaccen shirin farautarsa ya samu matarsa uwani yafara lissafto mata irin dabbobin da yau zai farauto masu, kusan Inda sabo to uwani ta saba don duk sa'inda jatau zai shiga dawa sai ya lissafta mata irin dabbobin da zai kamo, wanda akarshe baya dawowa gida sai ya kamosu, abu guda dake damun uwani shine rashin furta kalmar inAllah yayarda da jatau bayayi akarshen zancensa, Ayau uwani taci Alwashin saita fadi masa muhimmancin wannan kalma ta dubeshi tace maigida Jatau yace na'am Uwani tace " maigida ka gama lissafto min irin dabbobin da zaka farauto amman banji ka ambaci Kalmar in Allah ya yarda ba a karshen zancenka" Jatau ya turbune fuska yace " dacan danake fita farautar na taba fadin In Allah ya yardanne, bafa nason kinibibi uwani" Uwani tace "gani nayi ya kamata tunda burine kake son cimmawa" "Naki na fada din, ki rike ya kamatar ki bana so" yana gama fadin hakan yai ficewarsa daga gidan fuska a turbune tamkar dan aiken mutuwa, yaiwa gida adabo ya nausa cikin jeji, Saida jatau ya shafe sama da sa'o'i uku batare dayai arba da koda tsuntsu ba hakan ba karamin batawa jatau rai yayi ba, a iyaka saninsa da zarar ya shigo dawa baya wuce mintuna goma yake fara arangama da dabbobin dawa amman a wannan rana gani yake ana neman asha banban, Jatau yai tsaki yayin daya kariso gaban wani shirgegen bishiyan kuka, yadaga kai ya kalli sama yaga rana a tsakiyar samaniya, jinjina kai yayi aransa yace da alama wannan rana bazatayi mana kyawu ba, Yadan kishingida a jikin bishiyar kukan don ya huta, kasantuwar inuwar bushiyar kukan na dauke da daddadan iska hakan yasa jatau bai farga ba har barci ya daukeshi Yana cikin daddadan barcinnasa ne yaji ana kokarin tashinsa zumbur ya mike zaune yana karewa mutanen dake gabansa kallo, jibga jibgan mutane ne madaka karti su talatin cif a gabansa sanye da kayan sojoji, Labarin ya kusan karewa MAFARAUCI JATAU Marubuci - Shuraih Usman © 2020 Shuraih 99% - HAUSA EBOOKS Part 6 Jatau ya dago kai ya dubesu cikin gagarumin shirinsu na yaki, kowannesu na dauke da bindiga kirar ak 47, jatau ya hadiyi miyau sannan ya mike tsaye Shugaban sojojin ya matso gaban jatau ya bude wangamemen bakinsa mai kama da mazugin jaka yace " bawan Allah dun Allah tambaya muke" Jatau yace " Allah yasa na sani" yana karewa sojojin kallo "Kauyen MAZURARI muke tambaya ko Allah yasa ka sani" shugaban sojojin ya fadi wannan karon yana yamutse fuska Jatau ya sauke doguwar ajiyar numfashi yace " eh na san kauyen kunga waccan hanyar datai gabas" ya nuna wani gefe na jejin da dan yatsansa guda sannan ya cigaba " tom izan kuka mike hanyar kai tsaye kukai tafiya ta kimanin sa'o'i uku zaku isa gindin wata bishiyar rimi babba, sai ku bi gefen daman bishiyar rimin zaku isa bakin wani dan karamin tafki, izan kuka tsallake tafkin sai kubi yammacin gabashin tafkin zai sada ku da lambun yazawa, daga nan sai ku bi kudancin lambun ku mike hanyar sanbal babu shataletale zaku isa wani rugar fulani sai ku tambayesu zasu gwada maku hanyar da zaku bi daga nan" Tun sa'in da

Chapter 1 of 2