Share this page
3 / 4
fara karantawa kamar haka....... Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [10/11 7:42 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 9⃣8⃣ OHW 📚📲 *24 hours make a lovely day, 7 days make a lovely week, 52 weeks make a lovely year, and knowing a person like me will make ur life lovely, hav a nyc day*. _Urs lovely_ Da mamaki take karantawa to wannan nmbr din waye? Tambayar da take ta ma kanta kenan. Haka ta shiga duba wayar, don tana iya karanta komai hakan yasa tayi ta shiga ko'ina har ta gane kan wayar. Ranar yini tayi tana duba wayar tayi mata kyau sosai, Zee tayi mata downloading WhatsApp. Ta nuna ma Yah Auwal shima ya taya ta murna, nan ya tura mata imdians films da waqoqi, da kuma complete Qur'an, su Mummy ma duk saida ta nuna masu, Yah Mahmoud ne kadai bata samu gani ba balle tayi masa godiya, bai shigo part din ba, ita kuma bata son xuwa part dinshi. Da dare xata kwanta bayan ta gama chatting har xata kashe wayar wani text ya qara shigowa a wayar na nmbrn daxu, hakan yasa ta bude don ganin ko miye a ciki, ta soma karantawa: *Still awake? Time to sleep gudnyt, sleep tight my lovely one* _Urs lovely_ Kallon Nmbrn ta shiga yi wata xuciyar na ce mata ta kira taji ko waye, wata kuma na ce mata ta tura mashi tex ta tambayi ko waye, shawarar xuciyarta ta biyu ta bi, nan ta shiga tura masa text kamar haka: *I'm sorry, i don't know who ar u, can u telling me who is on the line?* Tsawon lokaci aka dauka ba'a maido reply ba, har xata kashe wayar ta kwanta sai jin qarar shigowar reply din tayi, hakan yasa ta bude. *Don't worry my love, xaki sanni very soon*. Haushi ya cika ta ganin bai fadi ko waye ba, hakan yasa ta kashe wayar tayi addu'a sannan suka kwanta, tana so tayi barci amma ta tunanin text din kawai take, barin ma na farko da yafi tsaya mata a rai, sai kawai ta tsinci kanta da murmushi, haka barci barawo yayi awon gaba da ita. Mahmoud kuwa kasa barcin yayi, yana ta xaman jiran ganin text din Naana amma shiru, gsky ya xama dole ya furta mata yana sonta. _Washe gari_ Wajen 10 suna xaune a falo ita da Zee suna hira, Mahmoud ya shigo shida Yah Auwal da sallamarsu suka amsa sannan suka samu guri suka xauna yana kallon Naana. Ta miqe ta koma kusa da Yayanta. Yah Mahmoud Yayi murmushi sannan ya fiddo wayarsa daga pocket, ya soma rubuta mata text. Suna magana da Yah Auwal taji qarar shigowar text hakan yasa ta bude don ganin ko miye, *Do you want know who am i?* Ta maida masa da cewa *Yeah* Murmushi Mahmoud yayi tare da miqewa ya fita daga falon bai xame ko ina ba sai garden, ya samu kujera ya xauna sannan ya maida mata *So if u want, u can see me in urs garden*. "Garden?" Ta maimaita har Yah ya kalleta yace "Miye a garden din?". Murmushi ta qaqaro tace " Noo ba komai yaya, kawai ina son xuwa garden din ne". Murmushi kawai yayi yace "To kije mana". Miqewa tayi tace " Ynx xan dawo yaya". Daga mata kai kawai yayi ta fice daga falon xuwa garden din ba ko tsoro, ko kadan batayi tunanin Yah Mahmoud bane. Tashi yayi daga inda yake ya buya bayan wasu bishiyoyi yana kallonta har ta shigo garden din tana ta waige 2 bata ga kowa ba, ta ja kujera ta xauna tare da jawo wayarta ta rubuta mashi *I don't see anybody in dis garden, where ar u?*. Murmushi yayi bayan ya gama karantawa sannan ya maida mata da cewa *Close ur eyes*. Ta kuma maimaitawa, to miye na wani cewa ta rufe idonta kuma? Don tana son ganin ko waye ne ya sanya ta rufe idon nata, a hankali ya fito daga inda yake riqe da wata flower mai shegen kyau da qamshi ya nufo inda take tare d xama kujerar dake facing tata ya boye flower a bayansa, yana wani sanyayyan murmushi a hankali cikin wata murya yace "Open ur eyes". A hankali ta bude fararen idanuwanta suka sauka kan kyakkyawar fuskarsa, da mamaki ta tsaya tana kallonshi, ko kadan batayi tunanin shi bane, can ta kawar da kanta tae da cewa " Yah Mahmoud baka ga wani a nan ba?". Murmushin ya kuma yi tare da cewa "Ai ni ne wanda kike maganar". Da mamaki tace "Yah kana nufin kaine kake turo min massages?". Gyada mata kai yayi ba tare da yace komai ba. Miqewa tayi tare da cewa " Tunda na ganka shikenan bari na koma cikin gida". Ji tayi an riqo hannunta hakan yasa ta tsaya cak ba tare da ta juyo ba. Miqewa yayi daga xaunen da yake ya dawo gabanta tare da kallon cikin idonta, ba shiri ta sadda kanta qasa don baxata iya jurar kalon idon nasa ba. Cikin wata sassanyar murya ya kira sunanta, har cikin jikinta taji kiran nashi, a hankali ta dago ta kalleshi ba tare da ta amsa ba. Cikin wata rikitacciyar murya yace "Naana i love u morethan ur expectations, Naana bansan ta yaya soyayyarki tayi nisa cikin xuciyata ba, may tumse bahoot bahoot pyar karta(I love u a lot) plx love me". Ji tayi duk jikinta yayi sanyi, ta rasa me take ji a cikin xuciyarta, kuma ta rasa amsar da xata bashi. Muryar shi ta katse mata tunaninta yace " Plx Naana say something for me, say u love me". Cikin rawar murya tace "Yah Mahmoud what do u want me to say about? I have nothing to say about what u ar saying". Cikin sauri yace " U have Naana, plx say u love me, Wllh Naana ban taba son wata mace kamar yanda nake sonki ba". Naana tace "I'm sorry Yah Mahmoud, bansan me xan ce maka ba". Tana kaiwa nan ta wucesa da dan gudu 2 ta nufi falon mummy, har ta wuce Yah Auwal dake tsaye yana jinsu bata lura dashi ba. Shi kuwa Mahmoud tsaye yayi a gurin, ya rasa mai xaiyi, ya koma ya xauna kan kujerar, tare da dafe kanshi, wani son Naana na qara shiga xuciyarshi, bai san sadda hawaye suka xubo masa ba tuna cewa Naana bata sonshi. Ji yayi an dafa kafadarsa hakan yasa ya dago da sauri don ganin ko waye, sai ganin Yah Auwal yayi, Yah Auwal yace " Ka kwantar da hankalinka insha Allah Naana xata so ka". Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [12/11 5:04 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 9⃣9⃣ OHW 📚📲 Naana kuwa tana shiga daki ta wuce, ta kwanta saman gadonta, tunanin Yah Mahmoud ta shiga yi, ta rasa me take ji game dashi, a duk lokacin da ta ganshi sai taji gabanta na faduwa, haka kuma indai ya wuni guda bai shigo ba sai taji duk ba dadi, ita ta rasa gane kan abin. (Ni kuwa da nake gefe nace nemsy u r in luv😉, ji nayi tace "Noo ba xai yuwu ba". Nayi saurin duqewa don nayi xaton ta jini). Haka ta wuni ranar sukuku, ta rasa me ke damunta, kuma gashi har dare Yah Mahmoud bai shigo ba, duk ta damu, Yah Auwal ma bai yi mata maganar ba, haka dai ta kwanta ranar cike da tunani kala 2 a xuciyarta, a ranta take cewa to wai ma miye nake damun kaina? Tunda ba sonshi nake ba. _Bayan kwana biyu_ Yah Mahmoud bai kuma yi mata maganar ba saboda Yah Auwal yace ya bari xaiyi mata magana, duk ya damu, amma duk da haka sai da ya dinga tura mata massages xafafa. Da rana suna xaune a falo Yah Mahmoud lokacin yana part dinshi, Yah Auwal ya shigo falon, ya nemi guri ya xauna, ya kalli Zee dake riqe da Faheem yayiushi tare da cewa " Qanwata baki gajiya da hidimar Faheem ko?". Murmushi Zee tayi tace "Yah Auwal gajiyar me?". Yace " Ai naga kullum sai ya sanya ki hidima". Tace "Ai ba komai Yaya ai *Da na kowa ne*". Yayi murmushi sannan ya kalli Naana dake game da wayarta yace "Qanwa ina son magana da ke". Zee ta miqe xata fita yayi saurin cewa " A a dawo ki xauna ina kuma xaki". Zee tace "A a gani nayi xaku yi magana". Yace "To ki dawo ki xauna kawai". Ba musu ta koma ta xauna, Ya kalli Naana da ta maido hankalinta kanshi yace " Naana tambayarki nake son yi". Tace "ina jinka Yayana". Ya danyi jim sannan yace "Kina son Mahmoud ko bakya sonshi?". Da mamaki duk suka kalleshi ita da Zee, ita dama Zee tun tuni take xargin Yah Mahmoud son Naana yake ta dai yi shiru ne kawai. Yah Auwal yace "Ina jinki Sister fada min karki boye min komai kinji". Ta danyi shiru sai kuma tace "Yah nima bansani ba Allah". Dariya taso ta kucce mashi, ya sani sarai Naana bata san miye so ba hakan yasa yace "Ki fada min me kike ji a duk lokacin da kika ganshi?". Ta kalleshi cike da rashin fahimtar tambayarshi tace " Kamar ya Yaya?". Yace "I mean baki jin wani feeling a kanshi?". Ta danyi shiru tabbas tana jin wani abu akan Yah Mahmoud a duk lokacin da ta ganshi, ta dago tare da cewa " Yaya ni dai duk sanda na ganshi na kanji wani iri a xuciyata, in kuma ban ganshi ba sai naji ba dadi har sai na ganshi". Murmushi yah Auwal yayi tare da cewa "Nàana ki yarda kina son Mahmoud, don kuwa duk abinda kika lissafo alama ce ta so, in kuma baki yarda ba kije ki kalli cikin idonsa kice bakya sonsa". Shiru tayi tana naxari, Yah Mahmoud ba abin qi bane, koda ace bata sonsa bai kamata ta qi amincewa da soyayyarsa ba ko dan halaccin da suka yi mata, balle kuma tana ji a ranta tana sonshi din. Yah Auwal ya miqe yace " Tohm ni bari naje na dan huta". Fita yayi daga falon ya barsu nan Xaune, Zee kuwa itama tuni ta fada duniyàr tunani, tunda ta fara ganin yah Auwal abinda ta fara ji kenan a xuciyarta, hakan yana nufin itama sonshi take? 😳 (Ni kuwa Beely nace toh pa ana wata ga wata) Zee ta kalli Naana tace "Naana da gaske kina son Yah Mahmoud?, in kuwa haka ne xanfi kowa farin ciki, kiso Yah Mahmoud plx Naana". Tayi murmushi tare da cewa " Shikenan Zee amma kema ina so na roqeki wani abu". Zee tace "Ina saurarenki". Tace " Plx Zee Kiso Yah Auwal, ki maye masa gurbin Aunty Zarah". Da sauri Zee ta kalleta tace "What? Kina nufin na so Yah Auwal? To in shi kuma baya sona fa?". Naana tace " Zai soki insha Allah ke dai ki amince tukun". Zee ta danyi shiru can tace "Sai dai nayi tunani". Haka suka yini kowa da abinda yake saqawa. Bayan la'asar tana xaune a dakinta, haka nan taji tana son xuwa garden don haka ta miqe ta ta fito daga dakin, lokacin Zee tana dakinta, Faheem kuma na wajen Yaya. Yana xaune a cikin garden din kamar kuma an tsikareshi ya miqe xai fita, dai dai lokacin ita kuma xata shiga kanta na a qasa, bata yi aune ba sai ji tayi tayi karo da mutum tayi baya baya xata fadi yayi saurin tarbota ta fado jikinsa, da sauri ta tashi daga jikinsa ta juya xata fita yayi saurin kiran sunanta, cak ta tsaya ba tare da ta juyo ba. Gabanta ya xagayo ya tsaya ya kalleta cikin ido tare cewa "Naana me yasa bakya sona?". Ta sadda kanta qasa tare da cewa " Yah ba haka bane...... " "To yaya ne?". Ya katseta, ta dago ta kalleshi tare cewa "Yah Mahmoud...." Sai kuma tayi shiru, yace "Uhmm fadi ina saurarenki". Ta dago tare da cewa " Yah baxan iya fada ba". Ya fiddo wayarsa tare da miqamata yace "To rubuta min a nan sai na gani". Da kamar baxata amsa ba sai kuma ta amsa ta rubuta mashi sannan ta miqa mashi kafin ya karanta ta ruga ta shige falon mummy, krntawa yayi yaga ta rubuta: *I love you Yah Mahmoud* Murmushin farin ciki ya saki cike da jin dadi ya kaima wayar kiss tre da cewa " I love u too My Habibty". Tun daga ranar soyayya da shaquwa mai tsanani ta shiga tsakanin Yah Mahmoud da Naana wadda ko su Mummy sun san da ita, Naana tayi ma Yaya maganar Zee, shima kuma ya amince daga nan suma suka kulle suka fara soyayya amma fa da farko bai amince ba, sai daga baya kuma ya amince. (Toh Haleesah fa?😳🤔) Bayan kwana biyu mommy ta kira Yah Mahmoud sai da gabanshi ya fadi lokcin da ta kira sunan Haleesah, amma ya dake, a nan take gayama sa cewa an fasa aurenshi da Haleesah don har ynx bata dawo daga Germany ba, kuma da aka yi mata maganar auren sai cewa tayi bata yi niyyar yin aure ynx ba sai nan da 3yrs, don hakan yasa Mummy ta fasa. A ranar in kaga Yah sai kayi mamakinsa, baxaka ce shi ne wanda baya dariyar nan, koda ya fada ma Abdul sai cewa yayi shi ma dole yaje neman soyayyarshi wajen Aisha. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [13/11 9:22 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 1⃣0⃣0⃣ *~THE END~* Kamar kuwa yanda Abdul ya fada yaje ya samu Aisha ya sanar da ita kalar son da yake mata, bata wani ja rai ba ta amince don itama ta kamu, sai anan suke sanin ashe Hadixa da Yah Ahmad soyayya suke tuntuni. _2 weeks later_ An sanya ranar bikin Yah Mahmoud da Naana, da kuma Yah Auwal da Zee, wata biyu kacal, a kuma lokacin aka sanya ranar bikin First lady da Muhammad Lamido, sai dai nasu wata hudu ne. Murna wajen maskyan bata misaltuwa musamman ma Yah Mahmoud da Naana abin sai wanda ya gani. ****** Kwanci tashi ba wuya wurin Allah yau gasji har satin bikin su Naana yayi, yau ta kama Talata, sunje sunyo saloon, su Hadixa ma duk sunxo, Mummy ta samo mai gyaran jiki tayi masu gyara sosai in ka gansu har wani kyalli suke, Mummy ta hana Mahmoud ganin Naana sai dai a waya, shi kuwa baiji dadin hakan ba, haka ma Zee itama sai dai a waya. An shirya programs wajen kala 4 ranar laraba xa'ayi Indian Nyt, Alhamis Arabian Nyt, Juma'a kuma walima da rana, sai da yamma Party. Shirye 2 kawai ake, gidan Mummy ya cika taf da en'uwa, abin mamaki sai ga en uwan Ummansu Naana, ashe Yah Auwal ne ya binciko inda suke har suka xo. *Day 1* Bayan sallar isha'i, kowa ka gani shigar india ne a jikinsa, daga masu sari sai masu riga da wando, a nan filin gidan za'a gabatar da program din. (Da sauri na na wuce dakin da amare suke don ganin shirin nasu wowww, abinda na fada kenan ganin su Naana da Zee da nayi cikin wani matsiyacin sari na indiyawa) Pink nd milk ne jikinshi, an chaba masu make up, wayyo Allah in ka gansu sai ka rantse da Allah ba su bane, don kuwa sak sun koma indiyawa, musamman Naana da aka baxa gashinta baya abin ba'a magana. (Sakin baki nayi ina kallonsu, da sauri naje nima na sanya nawa sarin sai dai naga ban kai Naana kyau ba☹) Bangaren su Mahmoud ma abin ba'a magana don suma shiga iri daya sukayi na kayan indiyawan, in kaga Yah sai ka rantse ba indiyen ne, Yah Auwal ma da yake shima fari ne yayi kyau sosai, in ka gansu sai ka rantse da Allah ba su bane. Kowa ya hallara a gurin Amare sun fito sun xauna a kujerunsu dake kusa da na angwayensu, sunyi bala'in kyau, Yah Mahmoud ya kasa dauke kanshi ga kallon Naana da ta chanja mashi. An gabatar da program din lafiya, anyi bajaga da kudi, (Don ni sai da na cika jakata da en dubu dubu😉). Abokan Yah Mahmoud na india duk sai da suka xo, ranar dai ansha selfie. Can na hango su Yah Mahmoud da wasu abokanshi suna ta xuba indiyanci, sauri na fara don xuwa dauko maku, har na kusa isa na hango su Naana ana selfie, ni kuma da son selfie nayi wajensu na manta da dauko maganar su Yah. Haka aka sha shagali, sai, munci abincin indiyawa da kaji irinsu Chicken tandoori, chicken masala, chicken afghani, da dai sauransu. wajen 10 kowa ya watse. *Day 2* Kowa ya shirya cikin jallabiyoyi da rawani, shigar larabawa sosai, nan ake yinta, Mahmoud yace sam shi baxai sanya jallabiya ba haka kurum yaji kunya a bainar jama'a, ba yanda Abdul bai yi dashi ba amma ya qiya dole ya hqr yasa wani farin yadi mai kyau da uake rigar har kusan qasa ne sai tayi kamar jallabiyar. Su Naana ma sun sha kyau cikin Arabian gown. Haka dai akayi aka gama shima cikin farin ciki, an xuba larabci sosai ni dai ina can ina kwasar nama ban samu damar dauko maku ba😜. *Day 3* Manyan malamai aka gayyato maxa da mata suka gabatar da wa'axi, kowa sai da ya dan matse kwallanshi, da yamma kuma aka shirya xuwa party a wani hotel dake nan kusa dasu, su Naana ansha wedding gown mai shegen kyau, su Aisha kuwa anko suma sukayi na gown din, su Mahmoud kuwa shigar turawa akayi, suit suka sanya sunyi kyau kamar turawan. Haka dai aka gama partyn aka koma gida. Washe gari aka daura auren *Mahmoud Isma'il Kwangila da Bilkisu Almustapha Yusuf* sai kuma na *Auwal Almustapha Yusuf da Zainab Isma'il kwangila*. Dubban jama'a sun shaida, kowa ka gani murna yake. Da dare aka kai amare gidajensu, A nan cikin unguwar gidajensu suke wanda Daddy ya mallaka masu iri daya ne, duk aka watse aka bar amaren su da qawayensu. Mahmoud Abdul kadai ya rako shi, nan akayi sayen baki suka sha rahar su suka tafi. Naana tasha kuka da su Aisha xasu tafi, suka fita aka barta ita kadai don Shima Mahmoud ya fita kullo gida. Shima Yah Auwal Ahmad kadai ya rakasa sannan shima suka tadi bayan anyi sayen bakin. Yana dawowa ya ganta xaune kan gadon tna shan kuka, bai son jin kukanta ko kadan ya qarasa saman gadon ya yaye mayafin dake fuskarta ya shiga share mata hawayen yana lallashinta, amma kamar qara xugata yake, rungumeta yayi tsam a jikinsa yana lallashinta da kyar ya samu tayi shiru. Nan sukayi sallah don godiya ga Allah sannan Mahmoud ya jawo ledar da ya shigo da ita. (Ni kam leqe kawai nake naga mai xa'a fiddo duk da nasan kaxa ce, ita ce ya fiddo kuwa nan falon ya dau qamshi na hadiye miyau) Mahmoud ya yanko cinya ya kai bakin Naana tayi saurin kauda kai wai ita ta qoshi, da qyar ya lallabata taci kadan shima kadan din yaci suka kora da lemo. (Ni kuwa ina daga gefe ina jira ya miqo min tawa sai gani nayi ya nufi wajen frigde da ita, kamar na bishi na qwato amma ba hali don xai iya batattakani na bar masa gida) (Dauko fresh milk yayi ya nufo bakin qofa, wurgo min yayi tare da cewa gashi nan ki dauka ki fice mana daga daki tun kafin na makeki, kaxa ce dai baki cinta duk qunatarki, kamar inyi kuka haka na duqa na dauki fresh milk din son in rage xafi na fice daga dakin ya banko qofa) _After 2 months_ Anyi bikin First lady anyi shagali shima yah Mahmoud ke kai Naana ya dawo da ita har aka kammala bikin. A lokacin aka sanya ranar bikin Aisha da Abdul da kuma Hadixa da Ahmad wata biyu suma. Bayan wata biyu aka yi bikin su shima sun sha shagali, tun ana saura sati Mahmoud ya kai Naana yace dashi xa'ayi bikin don baya so a kalle mishi mata, Hadixa a Katsina aka ajeta da yake Ahmad ya maka babban gidanshi, Aisha kuwa Kano aka rankayo da ita. Bayan bikin ne Naana ta fara ciwo, daga yau tace Xaxxabi sai tace ciwon ciki sai ciwon kai, ga kuma yawan kasala da take ji, Mahmoud duk ya damu ya dauketa ya kaita asibiti aka tabbatar masa da ciki ne da ita wata biyu, kar kuso kuga murna gun Yah Mahmoud, har kyauta ai da yayi ma Dr din. Bayan watanni Naana ta haifi Erta santaleliya mai kama da ita, lokacin kuma Zee na dauke da tsohon ciki, ranar suna yarinya taci sunan Umman su Naana wato *Aminatu* ake kiranta da *Meemah*. *After 5 years*. Zaune na hango Naana a kan cinyar Mahmoud sai xuba masa shagwaba take wai ita sai taje gidan Mummy shi kuma ya kafe akan lallai baxata ba sai gobe, Meemah ce ta shigo falon da sallamarta ta xauna gefen Iyayen nata sannan tace "Papa plx ka kaini gidan Uncle ina son ganin Yah Faheem da Adeelah" (diyar Zee ta farko kenan sai Afeef wanda yaci sunan Abba). Mahmoud yace "Oh god da wane xanji? Ur Momma tace sai na kaita gidan Mummy ke kuma kince na kaiki wurin Faheem wane xan fara?". Kafin suyi magana sai ga wani dan kyakkyawan yaro sak Mahmoud ya fito da gudu daga wani daki yana cewa "Papa, Momma ku tashi ku shirya muje gidan Uncle Abdul ina son ganin Airah". Meemah ta bata fuska tace "Kai *Safraz* baxamu je ba gidan Uncle Auwal xamu". Harararta yayi kamar wani babba yace " Anqi din ni baxa'a je can ba". Naana dai komawa tayi kan kujera ta xauna tana kallon ikon Allah, Shima Mahmoud kallonsu yake sunyi su gama ba inda xasu je yau. "Pa pa, Pa pa". Wata qaramar murya naji tana kiran sunan Papa cikin gwaranci, hakan yasa nayi saurin waigawa don ganin ko waye, wani dan qaramin yaro na gani yana , da sauri Meemah taje ta daukoshi tana cewa " *Muhib* dina ka fito kaima kaga Papa ". Mahmoud yace Gidan Mummy kawai xasu, haka suka shirya gaba dayansu suka nufi gidan Mummy a can suka iske Yah Auwal da Zee sunxo suma nan fa yaran suka kaure da hayaniya, Faheem yaja Meemah suka koma gefe suna ta labarinsu don sun shaqu sosai har cewa suke su mata da miji ne. Suna nan sai ga Aisha da Abdul, da Diyarsu Airah sai tsohon cikin da take dashi. Kamar hadin baki sai kuma ga su Hadixa da danta Mahfuz sai ta goyen mai suna Sahra, nan fa akayi ta shafta, basu suka rabu ba sai wajen magrib sannan kowa ya nufi gidansu. Naana da Zee an xama cikakkun likitoci, Aisha da Hadixa kuma aiki suke suma, Bayan kwana biyu da komawarsu First lady ta kawo masu Ziyara, sun yi murna sosai. Suna xaune a falo lokacin su Meemah duk sunyi barci, ya kalleta da lumsassun idanunshi yace " Baby nifa gsky so nake ki tara min ya ya da yawa don haka yau xamu sama ma Muhib qani ko qanwa". Yana gama fadar haka ya miqe tare da daukarta cak a hannunsa kamar wata baby, tayi saurin cewa "My Jaan Muhib fa baiyi girma ba". Murmushi yayi mata yace " Nasan da hakan ai" yana fadar haka ya wuce da ita daki. (Banyi yunqurin binsu ba don nasan fatattako ni xaiyi, nace na tafi dai na barku hakanan). *Alhamdulillah*, to nidai a nan na kawo qarshen wannan littafi nawa mai taken *BA SO A RAINA* Kuskuren da ke ciki Allah ya yafe mana Allah kuma ya bamu ikon Yin amfani da abinda ke cikinsa. *Jinjina gareku* Beely's novels grp Online Hausa writers Excellent writers Clever writers Afma's nvls grp Dandalin Autar Hajiya

Chapter 3 of 4