duqawan da yayi ya nufi wajen katangar suma su Abdul suka rufa masa baya.
A hankali suka hau katangar suka dire, Allah ya sosu ba wani security a gurin, Abdul yaga wani qarfe a gefenshi yayi saurin dauka incase of wata matsalan.
Dedicated to all my fans😘
_~Written by Beelybadaru😍~_
[05/11 12:35 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
_By Beelybadaru😍_
8⃣9⃣---9⃣0⃣
OHW 📚📲
Falon suka nufa cikin sand'a, can suka hango Hadixa durqushe an daure mata hannuwa da baki, sai kuka take, gefe kuma Ado driver ne shima a dauren kamar Hadixa, Abban Hadixa kamar yayi kuka haka yake ji, Mahmoud yace su dan jira shi a nan". Ba musu suka tsaya, ya miqe a hankali ya shiga falon ya saita mutane biyun da ya gani a falon da bindiga.
Gaba daya suka waigo suka daga hannayensu sama don babu bindiga a cikin makamansu, daya daga ciki yayi yumqurin duqawa ya dauki wuqarsa, Mahmoud ya daka masa tsawa "Don't moves Anywhere, i will shoot u if moves". Tsayawa yayi, Mahmoud ya waiga yayi ma su Abdul alama da su shigo, cikin sauri suka shiga Abdul ya wuce ya kwance Hadixa, bakinta har ya fara jini da hannunta, da alama kafin su qulle ta sai da suka axabtar dasu.
Bayan sun kwance su Abban Hadixa y riqe Hadixa suka miqe xasu fita, sai ga wasu securities din sun shigo hannunsu da bindigu, Mahmoud ya juyo wajensu su kuma wadancen ganin ya waiga suka yi saurin daukar makamansu da niyyar sararshi, Abdul na ganin haka ya dage ya qwala ma daya qarfen daya shigo dashi, nan take ya xube qasa yana qara, ya dauki wuqar wancen din ya yanki dayan, jin hakan yasa Mahmoud ya dan juyo, wani daga cikinsu ya harbeshi a kafada, bai san sadda ya saki bindigar hannunsa ba ya riqe wajen da aka harbeshi.
Mutumin ya qara saita shi xai qara harbinshi, cikin xafin nama ya cakumoshi ya hada kanshi da bango, da hannu daya yake aika mashi da saqonnin naushi, shi kuma Abdul ganin wancen na niyyar harbin Mahmoud yasa shima ya kai mashi sara a hannun da ke da bindingar, nan ta fadi qasa yayi saurin duqawa ya dauka.
Mahmoud kuwa sai da ya galabaitar da wancen sannan ya dauki bindigar hannunsa daya na dafe a wajen da aka harbeshi, da sauri Abdul ya riqeshi suka fito daga falon suka nufi hanyar da suka shigo, Abban Hadixa ya fara hayewa sannan Hadixa, sai Ado driver, Abdul ya taimaka ma Mahmoud shima ya haye, yaxo hawa kenan sai jin sara yayi a hannunsa, er qara yayi ya waiga ya harbi wancen din da bindiga a qafa, sannan ya haye, suka fara gudu har suka isa wajen motocinsu.
Suna xuwa suka shiga motocin suka ja Abdul ya qulle ma Mahmoud gurin fmda aka harbe shi da wani hanky fari, suka ja motar da gudun tsiya, dai dai lokacin su kuma wadancen suka fito, basu da yadda xasuyi dole suka koma don ba mota a wajensu balle su bisu.
Su kuwa gudu kawai suke na fitar hankali har suka isa Kano, basu xame ko'ina ba sai Asibiti, ganin Mahmoud yasa suka yi saurin karbarsa aka shigar dashi emergency don lokacin har ya fara fita hayyacinshi.
Abdul kuma aka wuce dashi wani dakin aka yi mashi dressing gurin da aka yankeshi, haka Hadixa ma da Ado driver. Lokacin har magrib ta gabato, ana kiran sallah Abdul da Ado driver suka wuce masallacin asibitin suka gabatar da Sallah, ita kuma Hadixa a dakin da suke tayi sallarta.
Suna dawowa dr ya fito daga dakin da aka kwantar da Mahmoud, Abdul yayi saurin qarasawa wajensa yace "Dr ya jikin nasa?". Dr Bilyamin yace " Mun cire bullet din dake jikinsa, ynx haka ya samu barci, kar ka damu xuwa anjima xai tashi insha Allah". Abdul yayi ajiyar zucuya yace "Allah ya tashe shi lpy". Suka amsa da " Ameen".
Sai a sannan Abdul ya kira Daddy ya sanar dashi suna Asibiti, ba'a dau lokaci ba sai gasu sun iso cike da tashin hankali har da su Naana, tana ganin Hadixa suka rungume juna suna kukan farin ciki, nan Abdul ya fada masu duk yanda abin ya faru, nan suka yi mashi Addu'ar samun sauqi.
Dedicated to all my fans😘
_~Written by Beelybadaru😍~_
[06/11 7:36 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
_By Beelybadaru😍_
9⃣1⃣---9⃣2⃣
OHW 📚📲
Sai bayan isha'i Mahmoud ya farka daga nannauyan barcin da yake, yana bude idanuwansa basu sauka kan kowa ba sai kan Naana da ke xaune saitinshi kusa da Zee, ita ma shi take kallo cike da tausayinshi, ya tsaya yana ta kallonta fuskarsa dauke da murmushi.
"Lah Mummy Yah ya tashi". Muryar Zee ce ta farkar dashi, sai a sannan ya waiga ya kalli su Mummy da suke xaune gefenshi, nan suka shiga yi mashi sannu, yana daga masu kai kawai. Suna haka sai ga Abdul ya shigo shi da Dr, nan Dr ya duba shi sosai sannan ya cire mashi qarin ruwan da aka sa mashi.
Nan yayi yunqurin tashi Abdul ya taimaka mashi ya miqe yace yana son shiga toilet, Dr Bilyamin yace ba damuwa ya shiga amma kar ya jiqa gurin, Abdul ya taimaka masa har toilet din sannan ya fito shi kuma ya watsa ruwa, yaji dan qarfin jikinshi, shi dama babu inda ke masa ciwo sai gurin da aka harbeshi, hakan yasa ya dauro alwalla don gabatar da sallolin da ke kanshi.
Abdul ya miqo mashi jallabiya, ba don yaso b haka ya sanya, yana fitowa ya watsa mashi harara tare da cewa "Meye na dauko min jallabiya, bayan kasan b sonta nake ba". Abdul yayi dariya yace " To ni miye laifina, naga dai cikin kayanka na ganta". Yace "To ai sai ka xo ka taimaka min, don baxanyi tafiya da ita ba haka kurum ta kada ni". Duk sukayi dariya Abdul ya riqo shi xuwa bakin gado, ya xauna.
Nan aka hada mashi tea mai kauri yasha sannan ya miqe ya gabatar da sallolinsa. Bayan ya idar yace da Daddy shi fa kawai a sallameshi, Daddy yace ya bari sai gobe in Allah ya kaimu, Mahmoud yace A a shi dai kawai a sallameshi,family dr dinsu sai y rinqa xuwa gida yana dubashi.
Daddy yaje ya samu Dr yayi mashi bayani, dr yace ba damuwa nan aka sallameshi, nan suka tattara suka nufi gida.
_Washe gari_
Naana ta tashi duk jikinta a sanyaye, gani take kamar wani abu xai faru da ita, wajen 10 suka gama shirinsu don 10:30 xasu koma kotu. Shima Mahmoud lokacin ya gama shirinshi tsaf ya nufi part din Mummy, bayan sun gaisa suka yi break sannan suka miqe suka nufi mota don tafiya.
Mota daya Naana da Mahmoud da Zee da Hadixa suka shiga, sai Mummy Daddy da Faheem a mota daya.
_10:50am_
Kotun ta cika maqil da mutane don ma tafi wancen karan cika, Alkali ya shigo an miqe kamar wancen lokacin sai da ya xauna sannan kowa ya xauna. Nan aka shiga gabatar da qara, Mahmoud ya kawo shedu da dama, ciki harda Hadixa, ta fadi komai da ta sani, har alqali xai fara magana mahaifin Sadeeq ya miqe tsaye yace "A dakata ya mai Shari'a".
Kowa ya kalleshi sannan ya cigaba da cewa " Ya mai Shari'a, dana Sadeeq baxai iya aikata haka ba, sai dai idan ciwonsa ne ya tashi". Da mamaki ake kallon Alh Ibrahim Naira. Alqali yace "Ko xaka iya fada ma kotu ciwon dan naka?". Ya numfasa sannan yace " Ya mai girma mai shari'a dana Sadeeq ya samu hadarin mota shekaru biyu da suka wuce, a lokacin kanshi ya bugu, wanda har yakanyi abu kamar mara hankali, koda ya samu sauqi likita ya tabbatar mana da cewa ciwon nasa xai ringa tasowa, xaiyi abu ba tare da yasan yayi ba". Alkali ya danyi shiru can yace "Ko xaka iya kawo mana takaddun asibitin da kuma likitan?". Yace qwarai kuwa". Nan ya waiga gefenshi ya kira Dr, sai gashi ya miqe ya miqa takaddun aka miqa ma Alkali sannan yace " Tabbas ni ne likitan da ya duba Sadeeq a lokacin da suka samu Accident..... "
"Qarya yake ya mai girma mai shari'a". Wata murya ta fadi hakan wadda ta sanya Naana mutuwar xaune, duk aka waiga don ganin ko waye, Hadixa da first lady suka miqe tsaye cike da firgici da tsoro, Naana ta miqe itama, ganin ko waye yasa ta shiga nuna shi da yatsa bakinta na rawa tana son furta sunanshi amma ta kasa...........
(nima dai garin firgicin ganinshi yasa na yadda wayana qasa).
Dedicated to all my fans😘
_~Written by Beelybadaru😍~_
[07/11 2:15 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
_By Beelybadaru😍_
9⃣3⃣---9⃣4⃣
OHW 📚📲
Sadeeq kuwa neman hanyar guduwa ya fara, sai dai ba hanya don duk yan sanda sun rufe hanyar.
Tsaye yake a qofar an daure cikinshivda bandage, ya rame sosai kamar ba shi ba, bakin Naana na rawa ta soma furta " *Ya... Ya... Nah*" sai kuma ta sulale a gurin, da sauri ya nufo inda take ya tallabota a jikinshi yana jijjigata, Mahmoud ma ya nufo gurin da sauri yana kallonshi cike da mamaki don sam bai sanshi ba, Faheem dake hannun Zee ya kalleshi tare da cewa " *Abee*". Abee kuwa hankalinshi gaba daya yana kan Naana data sume saboda tsabar firgicin ganinsa.
Cikin rudu yake cewa "Ku taimaka min da ruwa". Ruwan aka miqo mashi ya yayyafa mata sai gashi ta farfado a firgice, ganin yayanta yasa tace " *Yah Auwal* ashe dama kana raye?". Murmushi ya mata kamin yace "Ina raye Qanwata ban mutu ba".
Ita ta rasa me ma xatayi don murna da farin ciki, shigewa tayi jikinshi tana kuka wanda ita kanta bata san ko na miye ba, shima hawayen yake, ya juya ya kalli Faheem yayi mashi murmushi sannan ya miqa mashi hannu, da sauri ya qaraso wajenshi ya rungumesu su duka cike da kewarsu.
Alqali yayi gyaran murya kowa ya koma ya xauna inda yake, Yah Auwal ya miqar da Naana ya maida ta maxauninta da Faheem sannan ya juya ya kalli Ahmad da suka shigo tare da Aysha, suma suka samu guri suka xauna.
Alqali yace " Komai ya lafa, Malam ko xaka iya fada ma kotu ko kai waye?". Yah Auwal ya kalli Alqali sannan yace "Qwarai kuwa ya mai shari'a". Nan yaje ya shiga gurin da ake tsayawa ya tsaya ya kalli Sadeeq da tuni xufa ta gama jiqeshi sharkaf, yayi murmushi sannan ya maida kallonshi ga Br, Salman dake tsaye a gabanshi.
Br, Salman yace " Shin ko xamu iya sanin sunanka?". Yace "Sunana Auwal Almustapha Yusuf". Br yace " ko xaka iya fada ma kotu dangantakarka da wannan yarinyar?". Ya qarshe tare da nuna Naana". Yah ya kalli Naana sannan yayi murmushi yace "Ko ban fada ba ya kamata ace kun gane, but bari na fada kawai, Naana qanwata ce uwa daya uba daya, Faheem kuma da ne a wajena".
Tsit kake ji na dan wani lokaci kamin Br yace " Dama yayyanta biyu ne? Don kuwa tace mana Sadeeq ya kashe mata yayanta kenan qarya take". Murmushi yaya yayi tare da cewa "Yayanta daya kuma gaskiya ta fada maku, Sadeeq shi ne wanda ya kashe mana iyayenmu kuma yayi yunqurin kashe ni, sai dai Allah bai nufa ba, saboda ina da sauran numfashi a doron duniya, kuma yayi hakan ne a dalilin munqi amincewa ya auri Naana, idan kuma qarya nake gashi nan ka tambayeshi, ko da yake ba ma sai an tambaya ba, ku dubeshi ku gani, me yasa ya firgita da ganina a raye?".
Kowa ya kalli Sadeeq da ya jiqe sharkaf da xuba, Alqali yace " Sadeeq shin ka yarda da abunda ya fada?". Sadeeq ya dago da kanshi ya watsa ma Yaya wani mugun kallo sannan yace "To sai me? Don na kashe su sai me? Ku baku isa ku yanke min hukunci ba, mahaifina na da kudi kuma xai fitar dani daga hannunku". Kowa da abinda yake fada a cikin kotun, Br, Mahmoud ya sauke ajiyar xuciya ganin Sadeeq bai bata masu lokaci ba. Br, Salman da mamaki yake kallon Sadeeq yace " Kana nufin Kaine ka kashesu?".
Sadeeq yace "Qwarai kuwa ni ne na kashesu da hannuna". Nan aka hau salati kowa da abinda yake fada, Alqali ya buga wani abu nan kowa yayi shiru.
Nan dai Alkali ya yanke ma Sadeeq hukuncin kisa ta hanyar rataya bayan ya biya diyyar rayukan da ya kashe, sannan kuma mahaifinshi da Dr aka ayanke masu hukuncin xama gidan kaso na tsawon watanni shidda, sakamakon qaryar da suka yi na cewar Sadeeq na da ciwon hauka.
Nan yan sanda suka fitar dasu, Naana da gudu taje ta rungume Yayanta cike da farin ciki, shima farin cikin ya cika mashi xuciyarshi, Nan Br, Salman da Br, Mahmoud sukayi musabiha, Nan suka dunguma gaba dayansu suka nufi gidansu Mahmoud.
Dedicated to all my fans😘
_~Written by Beelybadaru😍~_
[08/11 2:11 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
_By Beelybadaru😍_
9⃣5⃣---9⃣6⃣
OHW 📚📲
Duk suna xaune a babban falo gaba dayansu harda Ahmad da Aisha da Hadixa, Naana da Faheem na maqale kusa da Yah Auwal, Daddy ya kalli Yah Auwal yace "Mu fa mun shiga rudani, ya kamata ka fada yadda abun ya kasance".
Yah Auwal yayi dan murmushi sannan yace _"Bayan da Sadeeq ya caka mana wuqa, Umma da Abba sun rasu, nace da Naana ta gudu, to tun daga nan ban kuma sanin inda nake ba, sai dai na farka na ganni a inda nake, Ahmad na fara hangowa yana daukar gawar Abba, naga maqotanmu da dama a cikin gidan, hakan yasa na maida idona na rufe, Bayan sun fita da gawar Umma da Abba, Ahmad ya shigo don daukar tawa gawar, ganin shi kadai ne yasa na bude idona, ya tsorata sosai da ganin na bude ido, har xai kira sauran mutanen nayi saurin dakatar dashi cikin muryar wahala nace " Karka bari su san ina da sauran numfashi, bana so Sadeeq ya sani"._
_Dai dai lokacin wani maqocinmu ya shigo yana cewa "Ahmad bari na taimaka maka a daukeshi". Ahmad yace " A a baba ka barshi kawai na daukeshi, ina so na kaishi gidanmu ayi mashi wanka a can, ku kuma kuyi ma su Umma da Abba a kaisu makwancinsu". Mutumin yace "Toh shikenan Allah ya jiqansu da gafara" Ya amsa da Ameen shi kuma ya fice._
_Nan Ahmad ya daukeni xuwa gidansu, yayi ma Ummasa da Abbansa bayanin komai kuma ya roqesu da karsu fada ma kowa, sun kuma amince, Aisha ma akayi mata bayani, nan aka cuccusa kaya cikin likafani yayi kamar mutum ne ko dauka akayi baxa'a gane ba, lokacin har anyi ma su Abba da Umma sallah an kaisu makwancinsu, nan shima aka dauki kayan aka yi mashi sallah aka kai makwanci._
_Da dare sosai Ahmad da Abbanshi suka daukeni suka kaini wani asibiti suka roqi likitan da kar ya bari a san suna cikin asibitin, tun daga nan aka cigaba da kula dani, Ahmad shi ke kawo min duk wasu bayanai akan Sadeeq, har xuwa wannan lokacin da mukaxo kotun"_
Kowa ya jinjina ma lamarin, Daddy yace "Toh Allah shi kyauta gaba, ynx dai komai ya qare Sadeeq dai tuni an rataye shi, sai dai kuma tarihinshi". Duk suka amsa da " Ameen". Yaya yayi masu godiya akan riqon da suka yi ma Naana da Faheem.
Mummy ta kalli Naana tayi murmushi tare da cewa "Toh su Naana Yaya ya dawo shagwaba ta dawo kenan". Duk aka sanya dariya, Yah Auwal yace "Naana har ynx bakin naki yana nan ko?". Tayi saurin cewa " Waa ai Yaya tuni ya mutu, ai na daddara". Nan ma aka kuma yin dariya, Shi kuwa Mahmoud murmushi kawai yakeyi yana kallon Naama cike da so da qauna, lokaci yayi da xai bayyana mata sirrin dake ranshi, Abdul yayi masu sallama Mahmoud ya raka sa har wajen motarsa sannan ya dawo cikin gidan.
Da dare bayan an gama dinner duk aka dawo falo ana kallo, Naana wani farin ciki take ji, yau gata ga yayanta farin cikinta, ga kuma qawayenta Hadixa da Aisha.
Wurin 9:20pm Mahmoud ya miqe ya kalli Yah Auwal da Ahmad yace "Toh ya kamata ku taho muje mu kwanta haka nan". Ahmad yace " Aiko balle mu masu tafiyar safe ba". Naana tayi saurin cewa "Amma banda Yaya Xa'a tafi ko?" Sukayi dariya Ahmad yace "Da shi kam xamu tafi". Tayi saurin riqo hannunshi tace " Plx Yaya banda kai ko?" Ta qarashe maganar kamar xatayi kuka. Yaya yayi murmushi yace "Oh dear don't cry banda ni xasu tafi, ni xan dan jima kafin na tafi".
Tayi dariyar jin dadi, Faheem yace " Abee ai badaka kara tafiya ba ko?". Yaya yayi dariya tare da shafa kan Faheem yace "Ba inda xan qara tafiya My boy". Duk akayi murmushi, Daddy yace " Ai gaskiya bai kamata ka koma katsina ba, in ba damuwa xaka iya cigaba da aiki a company na kai da Ahmad".
Cike da farin ciki Yah Auwal yace "Gsky da naji dadi sosai, don bana so na kuma yin nisa da Qanwata da kuma dana". Mahmoud yace "suma kansu baxasu ji dadi ba in ka tafi". Daddy yace " To ai shikenan xuwa nan da 1 week sai kaje ku dauko takardunku da na Naana don itama ina so na sama masu makaranta ita da Zee".
Nan suka yi mashi godiya sosai yace ba damuwa. Suka miqe suka fice xuwa part din Yah Mahmoud har da Faheem da ya maqale ma Abee dinsa, su kuma su Naana suka wuce dakinta, har sun kwanta suna labari sai ga Zee ta shigo tace baxa'a barta ita kadai can ba. Duk sukayi dariya, daga nan suka dasa fira, basu suka kwanta ba sai wurin 2, hakan yasa suka makara sallah.
Shima Yah Auwal yayi barci cikin farin ciki yau, yana rungume da Faheem sukayi barcin, rabon da yayi barci irinshi har ya manta.
Washe gari, su Ahmad wurin 10 suka gama shiri, Mummy tace a bar su Aisha su dan qara ko kwana biyu ne, b musu kuwa aka barsu, sunyi farin ciki sosai, Driver aka sanya ya kai Ahmad har gida.
Da rana First lady taxo, nan suka hade aka dunga shafta kamar karsu rabu, sai dare Muhammad yaxo ya dauketa.
Kwanan su Hadixa 4 suka fara shirin tafiya, Naana ba don taso ba, Abdul tunda yaga Aisha yaji ta kwanta masa a rai amma sam ya kasa fada mata, sai dai kullum sai yaxo gidan har Mahmoud ya qyaro jirginsa. Tare suka shirya da Naana da Zee don har dasu xa'a je maida su Hadixa, mota biyu suka hau, da ta Abdul da yace hada shi xa'a da kuma ta Yah Mahmoud.
Dedicated to all my fans😘
_~Written by Beelybadaru😍~_
[09/11 2:48 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹*
🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹
_By Beelybadaru😍_
9⃣7⃣
OHW 📚📲
Suna isa ta fara tuno rayuwarsu a unguwar tuni hawaye suka fara xubo mata, tace ma Yaya su fara xuwa gida, shi kanshi yana son xuwa, amma ya tabbata suka shiga gidan sai sunyi kuka daga shi har Naana.
Matsa mashi tayi akan lallai sai sunje, ba yadda ya iya nan suka fara xuwa gidan, ita ta fara fitowa ta shiga gidan, yana nan yadda yake sai dai uban qura, a hankai ta fara tafiya har suka shiga ciki, hawaye sai xarya suke a fuskarta, daki ta wuce, tana shiga idanuwanta suka sauka kan hotonsu da sukayi na family, da sauri ta qarasa cikin dakin ta dauki photon tana shafa fuskar Abbanta da Ummanta, wani kuka ne ya kufce mata, ta rungume photon tana kuka mai tsuma xuciya.
Yah Auwal yayi saurin qarasowa cikin falon, ya durqusa inda take tare da dafa ta shima hawayen yake, da sauri ta fada jikinsa tana mai cigaba da kukan, shima kukan yake balle ya lallasheta. Zee ta duqa wajen itama tana share hawaye ita dasu Aisha, yayin da Mahmoud da Abdul suka fita waje yana riqe da Faheem don shi baxai iya jurar ganin Naanarshi tana kuka ba.
Sai da suka yi mai isarsu sannan Yah Auwal ya tsagaita nashi kukan tare da dago kan Naana ya shiga lallashinta har ya samu tayi shiru sannan suka miqe suka fito daga gidan suka wuce gidan su Hadixa da yake shi ke kusa.
A ranar su Mahmoud suka koma shi da Abdul, su kuma su Naana sai da suka yi sati, kuma sai da ta kwana gidansu, amma fa ranar ba wani bacci sukayi ba, kuka kawai tasha har gari ya waye. Mahmoud ya dawo daukarsu, kamar karsu rabu haka suka tafi.
Yah ya daukar masu takardunsu gaba daya, suna komawa Daddy ya sama masu aiki a babban company'nshi dake nan kano, amma aikin Yaya yafi girma, su Naana kuma aka samar masu School of health a nan Kano suka fara xuwa ita da Zee. Itama first lady ta fara xuwa BUK kuma har ansa ranar bikinta da Muhammad.
Mahmoud yaje har Katsina ya sama ma su Hadixa Schl a nan Katsinar sunyi murna sosai, suma suka fara xuwa.
******* Suna xaune a falo gaba dayansu, da Yah Auwal Mahmoud Naana da kuma Zee sai Faheem dake xaune jikin Zee yana shan choculate. Zee ta kalli Yah Mahmoud tace "Yah nace wani abu?". Mahmoud ya kalleta yace " Kice muje shopping ba?". Duk sukayi dariya, Zee tace "Plx mana Yaya, muje kaga fa mun rabu da xuwa". Mahmoud yace " Sai dai in Naana xata je da Yah Auwal". Zee ta kalli Naana tace "Sis muje ko?". Ta kalli Yah Auwal tace " Yah Auwal muje plx".
Murmushi Yah Auwal yayi yace "Toh shikenan muje din". Nan suka miqe ita da Naana suka wuce daki suka shirya cikin kaya iri daya atamfa Naana tace hijab xata sanya, Zee ta dinga lallabarta da qyar ta yarda ta sanya gyalen, sunyi kyau kuma sosai.
Nan suka fito suka iske su Yah har sun shiga mota suna jiransu, tunda suka taho Mahmoud ke ta kallon Naana, Yah Auwal duk yana lura dashi, bai dai nuna mashi ba, don shi tun xuwanshi ya gane Mahmoud son Naana yake kawai dai ya kasa fada mata ne.
Nan suka bude baya suka shiga suka wuce super market, sunyi siyayya sosai daga nan suka wuce suka sha ice-cream, sannan suka kamo hanya don komawa gida. Sunyi nisa har sun kusa xuwa gida, Mahmoud yayi parking a gefen titi sannan ya kalli su Yah Auwal yace " I'm sorry ynx xanje na dawo". Yah Auwal yace "Ba damuwa Mahmoud".
Nan ya fita ya tsallaka xuwa wajen wani shagon sai da wayoyi, ya siya guda biyu iri daya qirar Sumsung galaxy S7, ssannan ya siya sim daya mai register sannan ya dawo cikin motar suka wuce gida.
Suna xuwa har xasu shiga ciki Mahmoud ya tsayar da Zee bayan sun shige ya miqo mata wayoyin yace " Ga wannan taki daya ta Naana daya da wannan sim dinki bata". Wani tsalle ta buga ta rungumeshi tana murna tare da yi mashi godiya, don dama ta gaji da tata wayar.
Bayan sun baje a dakin Zee ne suna duba kayayyakin da suka siyo Zee ta miqo mata wayar tace "gashi inji Yah Mahmoud yace na baki, iri daya ya siyo mana ni da ke". Naana tace "Waya kuma? A a ni baxan amsa ba". Zee ta bata rai tace " Miye haka Naana? Kinsan fa bana son wannan abun, ki amsa". Ta qarashe maganar tana mai miqa mata wayar. Naana tace "Kiyi hkr Zee amma ni banga amfanin riqe wayar ba". Zee ta miqe tace " Shikenan tunda baxaki amsa ba xanje na kai masa abarsa nace kince baki amsa, kuma kinsan dai baxai ji dadi ba yayi maki kyauta ki qi karba".
Sai kuma taga baxai ji dadi ba, hakan yasa tayi saurin riqo Zee tace "Shikenan kawo". Zee ta miqa mata wayar nan tayi mata godiya tace xata je tayi ma Yaya shima.
Tana komawa daki ta sanya sim din ta kunna wayar, tana kunmawa text ya shigo a wayar, tayi mamaki ace daga kunnawa sai kuma text. Nan ta bude text din ta