Share this page
1 / 4
An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://thausanovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.thausanovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels BASO A RAINA 2[02/11 9:59 am] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 7⃣9⃣---8⃣0⃣ OHW 📚📲 *Note:- Assalamu alaikum, dafatan kun tashi lpy masoyyana, kuyi min uxuri a bisa dan kuskuren da nayi na rubuta 08/11/016, ba haka naje son rubutawa ba, 08/10/016 nake son rubutawa, ku huta lapiya, luv u oll😘* *************** Suna komawa gida duk suka wuce su don gabatar da sallar axahar, bayan sunyi duk suka fito falo don yin lunch amma banda Naana tana daki duk damuwa tayi mata yawa, ita tasan Sadeeq baxai tava bari a hukunta shi ba. A falo duk suna xaune a dinning, Mahmoud ya shigo shima ya xauna, nan ya duba kujerar Naana yaga bata nan, hakan yasa ya kalli Zee yace "Sis ina Naana take ne? Naga bats fito ba". Zee ta miqe tana cewa " Ynx nake shirin shiga na kirata". Bai kuma cewa komai ba, ta wuce Dakin Naana. Tunda suka fito yake ta kallonta, wani irin sonta ne ke qara shiga xuciyarsa, ji yake a duniyar nan in ya rasa Naana baxai iya rayuwa ba ma baki daya. Har suka xo suka xauna bai sani ba, sai da Zee ta dan taboshi tare da cewa "Yah kaci abincin mana". Sai a lokacin ya dawo daga duniyar tunanin da ya lula, ya dan dafe kanshi sannan ya cigaba da cin abincin nasa, a hnkl yana dago kai yana satar kallon Naana. Mummy duk tana lura da yanayinsa, ta share kawai, amma ta dau aniyar da an gama wannan Shari'ar xa'ayi bikinshi da Haleesa. A haka har suka gama cin abincin nasu, kadan Naanata tsakura ta miqe, Mummy tace " Ba dai har kin qoshi ba". Murmushi ta qaqaro tare da cewa "Mummy na qoshi". Gyada kai kawai tayi ita kuma Naana ta wuce dakinta. Tana shiga Mahmoud ya miqe shima, Mummy ta saki baki tana kallonshi tace " Son kaima din ka qoshi?, ji fa dan abincin da kaci". Kallon abincin yayi, ko rabi bai yi ba, kuma kadan ne a cikin plate din, ya kalli Mummy yace "Mummy I'm satisfy wllh". Daddy dai bai ce komai va har ya fice daga falon ya nufi part dinsa, kafin ya shiga sai ga motar Abdul ta shigo gidan, nsn ya tsaya har yayi parking ya fito ya sameshi a gurin. Abdul yayi murmushi tare da cewa " Hey frnd y kk?". Mahmoud shima murmushin yayi tare da cewa "Ina lpy frnd, daga ina haka?". Abdul yayi er dariya tare da cewa " Daga gida mana, naxo jin yadda aka yi ne a court, ban samu xuwa ba cox I'm busy wllh". Mahmoud yace "Ynx dai muje ciki tukunna". Ba musu Abdul yabi bayanshi suka shiga cikin falon. Kan kujera suka xauna, Abdul ya kalli Mahmoud yace " Ina sauraronka". Mahmoud ya dago kai ya kalli Abdul, nan ys fada masa duk yanda akayi. Abdul ya jinjina kai tare da cewa "Tab lallai gayen nan mugun mutum ne, kuma na tabbata shi ne xai sa a tsoratar da mutumin nan ya kasa fadar komai a kai". Mahmoud yace " Nima hakan nayi tunani, amma kasan me xanyi?". Abdul ya girgixa kai alamun sai ya fada, Mahmoud yace "Gobe in Allah ya kaimu xanxo tun ds safe ka rakani Katsina, zan qara samo shaidu da yawa sai na taho dasu nan". Abdul ya danyi shiru yana naxari sai kuma yace " Tabbas hakan yayi Allah ya kaimu lpy". Nan ya amsa da "Ameen". Nan suka cigaba da tattaunawa kamin Abdul ya tashi ya tafi, shi kuma ya watsa ruwa ya kwanta don ya dan huta. _Washe gari_ Tun da safe ya gama shirinshi ya shiga part din su Mummy nan ya gaishe su, Mummy tace " Ina xuwa kuma da safen nan?". Mahmoud yace "Mummy Katsina xani". Cike da mamaki mummy tace " Katsina kuma me akeyi?". Kafin yayi magana Daddy yace "Kema dai da wata tambaya, ina ce yarinyar nan a Katsina take? Kinga a dole xaije can don neman shaidun da xai gabatar a kotu" Mahmoud yace " Hakane kam Daddy, Mummy dole inje Katsina". Mummy tace "To shikenan a dawo lpy". Ya amsa da " Ameen Mummyna". Nan ya fice ya wce gidansu Abdul, shima lokacin ar ya shirya yana breakfast, don shi sam baya wasa da cikinsa, ba kamar Mahmoud ba da ba sosai ya cika cin abinci ba, bayan sun gaisa da Mum din sa ya xauna a dinning ya dan ci kadan, sannan suka miqe suka yi mata sallama, tayi masu Addu'a sannan suka fito. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [02/11 2:08 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 8⃣1⃣---8⃣2⃣ OHW 📚📲 A motar Mahmoud suka tafi, wurin qarfe 10 suka isa katsina, basu xame ko ina ba sai unguwar katarda, nan sukai parking a wajen wani babban chemist, sannan suka fito suka jingina da motar. Abdul ya kalli Mahmoud yace "Aboki ynx ta ina xamu fara?". Mahmoud ya danyi shiru yana naxari can yace " Bari muga ni". Wani mutumi ne yaxo wucewa Mahmoud yayi saurin tsayr dashi ta hanyar cewa "Malam don Allah ina da tambaya ne". Mutumin ya tsaya yana kallon Mahmoud sannan ya tsaya, su Mahmoud suka qarasa inda yake. Hannu suka miqa mashi, bayan sun gaisa Mahmoud yace " Don Allah tamabaya muke". Mutumin yace "Allah yasa na sani". Ya gyara tsayuwarsa tare da cewa " A unguwar nan kasan wani Sadeeq Ibrahim Naira?". Da sauri mutumin ya kalli Mahmoud ya girgixa kai tare da cewa "Sadeeq? Ni bansan shi ba, sai dai ku tambayi wani". Yana kaiwa nan ya kama hanyar tafiya, Mahmoud na tayi masa magana amma ya share shi yayi wucewarsa. Mamaki ya cikasu, sai kuma ya bar mamaki saboda tuna ko waye Sadeeq a garin katsina. Haka suka yi ta tsayar da mutane suna tambayarsu amma duk amsa daya suke basu cewa basu sanshi ba, haka suka haqura har xasu shiga mota sai ji sukayi ance " Ai baxaku taba samun wanda xai fada maku ko waye Sadeeq ba". Da sauri suka juyo don ganin ko wacece don muryar mace sukaji. *Hadixa* ce tsaye a bayansu, suka tsaya suna mata kallon rashin sani. Ganin hakan yasa Hadixa tace "Kuxo muje can nesa don bana so a jini ina fada maku wani abu akan Sadeeq". Ba musu suka bi bayan Hadixa har xuwa bayan Chemist din inda ba mutane sannan suka xauna akan dandamalin da ke gurin. Mahmoud ya kalleta yace " Wacece ke? Shin kina da abinda xaki fada mana akan Sadeeq ne". Hadixa ta gyada kai tare da cewa "Kwarai kuwa, ni a shirye nake da na bada hadin kai wajen ganin an hukunta Sadeeq, amma kafin nan ku fada min ku suwaye, ba dai cutar damu xakuyi ba ko?". Mahmoud yace " Ko daya, Ni sunana Br, Mahmoud wannan kuma aboki nane Abdul-wahab,a garin kano muke munxo ne don samun cikakken bayani akan Sadeeq, saboda muna zarginshi da kisan iyayen wata yarinya a garin nan kuma itama yana so ya kasheta". Da sauri Hadixa ta kalleshi tare da cewa "Wacece yarinyar?". Abdul yace " Kafin mu fada maki ya kamata ki fada mana ko ke wacece da kuma abubuwan da kika sani akan Sadeeq". Idonta ya ciko da qwalla tace "Sadeeq shi ne ya rabamu da er uwarmu kuma qawarmu, ya kashe mata iyayenta da kuma yayanta don sunqi amincewa ya aureta, shi ne ta gudu da dan yayan nata, tun daga lokacin yake nemanta..... " Kuka ne yaci qarfinta tuno qawarta Naana da tayi. Mahmoud ya kalli Abdul da mamaki sannan ya maida kallonshi kan Hadixa yace "Kece Hadixa ko Aisha?". Itama da mamaki ta kalleshi jin ya ambaci sunansu, tace " Ya akayi kasan mu?". Mahmoud yace "Kafin nan, ai kinsan Bilkisu ko? Wacce ake kira da Naana". Da sauri Hadixa ta miqe tsaye tana cewa " wai duk ya akayi kasan mu?". Mahmoud yace "Calm down xauna ki fada min komai nima xan fada miki". Jiki a sanyaye ta koma ta xauna ta fada masu tun daga farkon haduwarsu da Sadeeq har xuwa lokacin da ya kashe mata iyayenta, wanda wani maqwabcinsu ne akayi komai a gabansa yaxo yake bada labarin. Mahmoud ya jinjina kai tare da fada mata duk ynd akayi tun faga gudun su Naana har xuwa kawo yau da ake shari'a. Hadixa sosai ta tausaya wa qawarta jin irin gwagwarmayar da tasha a rayuwa, tabbas ya xama dole a gareta ta bada shaida a kan Sadeeq don ta taimaki qawarta wajen ganin ta qwato encinta. Mahmoud yace karta fada ma kowa wannan xancen xuwa anjima kafin su tafi xai qara nemanta asan yadda xa'ayi. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [04/11 12:48 am] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 8⃣3⃣---8⃣4⃣ OHW 📚📲 Haka kuwa akayi nan Hadixa tayi masu kwatancen gidansu, bayan sunje restaurant sunci abinci sannan suka nufi gidan su Hadixa, a nan suke fada mata cewa karta fada ma kowa, ana saura kwana daya a koma kotu xai turo mota a dauketa don ta bayar da shaida. Ta amince da hakan, nan suka mata sallama sannan suka shiga mota suka nufi hanyar kano. Wajen La'asar suka isa, sai da ya sauke Abdul gida sannan ya wuce nasu gidan, yana yin parking ya fito ya wuce part dinsa, toilet kawai ya fada ya watsa ruwa sannan ya fito ya xura wasu qananan kaya da ganinsu kasan na shan iska ne. Fita yayi xuwa masallacin gidan bayan sun idar da sallah ya nufi part din Mummy. Yana shiga ya iske ta xaune a falo tana kallon news a Aljazeera, gefenta ya xauna yana "Washh!". Mummy ta waigo ta kalleshi tare da cewa " Son Wash kuma sai kace wata mace?". Ya dago brown eyes dinshi ya kalli Mummy tare da cewa "Mummy I'm so tired wllh". Mummy tayi murmushi tare da cewa " Ayya to ya kamata aje a huta". Miqewa yayi ya kalli Mummy tare da cewa "Ina su Zee suka shiga ne naji su shiru?". Mummy ta dan tabe baki tare da cewa " Zee tana dakinta ita da Faheem, Naana kuma na dakinta". Juyar da kai yayi tare da wucewa wajen frigde ya dauko juice ya tsiyaya a cup sannan ya dawo falon ya xauna, kadan yasha ya ajiye sauran ya miqe tare da cewa "Mummy bari naje na dan huta". Mummy tace " Hakan na da kyau my son". Murmushi yayi ya wuce side dinsa, yana xuwa ya fada kan kujerar falon barci mai nauyi ya daukesa cike da dreams kala2. ****** Zaune yake a cikin garden din gidan hannunsa riqe da Apple yana balla a hankali yana lumshe ido saboda iskar da ke kadashi mai dadi. Yana bude idon nasa sai ganinta yayi ta nufo wajensa fuskarta dauke da mumushi, tana sanye da wata doguwar riga Arabian gownt tayi rolling kanta dz mayafin, ba qaramin kyau tayi ba, cikin takunta mai daukar hnkl ta iso wurinsa. Zama tayi a daya daga cikin kujerun, har a lokacin bai bar kallonta ba, sai da ta dan tafa hannunta saitin fuskarsa sannan yayi firgigit ya dawo daga duniyar tunanin da ya lula. Wani lallausan murmushi ys sakar mata cike da so da qaunarta, sam ya kasa furta mata ko da kalmar A ne. Ganin hakan yasa tayi murmushi tare da cewa cikin muryarta mai sanyi "Yah Mahmoud tunanin me kake haka?". Kallonta dai yake bai ce komai ba. Ta kuma cewa " Say something mana Yah Mahmoud ". Sai a lokacin ya bude bakinsa a hankali yace " *I love you Naana*. Murmushi tayi ba tare da tayi magana ba. Tasowa yaui daga kan kujerar da yake ya dawo inda take tare da riqo hannunta ya miqar da ita sannan yaja hannun nata xuwa wajen Flowers din dake garden din. Suna xuwa ya tsinko wata flower red nd green, ya dawo inda take tsaye tare da duqawa da qafa daya, dayar kuma ya dora hannusa mai flower a kai tare da miqa mata flower yace " *I so much loving you Naana, i can't live without telling u dat i love u, pls say u love me*". Murmushi tayi mai sanyi tare da amsar flower daga hannunsa ta shinshina, qamshi mai dadi taji hakan yasa ta lumshe idonta tare da budewa ta kalli Mahmoud dake duqe har lokacin, a hankali ta bude bakinta tare d cewa " *Yah Mahmoud i......* ******A firgice ya farka daga nannauyan barcin daya daukeshi sakamakon qarar wayarshi da yaji. Wani mugun haushi ne ya xiyarci xuciyarshi lokaci daya, ya jawo wayan bai duba ko waye ba yayi swiching off dinta sannan ys koma ya kwanta tare da runtse idonsa wai ko xai cigaba da mafarkin nasa amma hakan bai samu ba, don ya kasa komawa barcin ma gaba daya. Ya miqe ya koma dakinsa ya watsa ruwa tare da yin alwallar magrib ya fice xuwa masallaci don gabatar da Sallah. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [04/11 11:24 am] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 8⃣5⃣---8⃣6⃣ OHW 📚📲 Naana kuwa tana daki don ji tayi bata son fita, ta dan kishingida barci mai nauyi ya dauketa, a cikin barcin take mafarkin wani mutum ya bata flower kuma ya furta kalmar so a gareta, sai dai bata ga fuskarshi ba ko kadan, haka ta tsinci kanta da furta masa kalmar *I love you*. Firgigit ta miqe daga barcin nata tana addu'a , sai kuma ta shiga girgixa kai tana cewa "No... No it can't be possible, baxai yuwu ba, babu wanda xan fada wa haka". Shiru tayi tana tunanin mafarkin, to waye shi mutumin? Tambayar da take tayi wa xuciyarta kenan, amma ta rasa amsarta, haka ta miqe ta fada toilet ta dauro alwalla taxo ta gabatar da sallah. Tana idarwa ta miqe tare da linke hijabin da carpet din ta maidasu gurin da suke sannan ta fito xuwa falo. Koda ta fito ba kowa a falon, hakan yasa ta wuce kitchen ko Zee tana can tana hada dinner. Yah Mahmoud ma yana fitowa masallaci ya nufo cikin gidan yau bai tsaya ayi isha'i ba saboda wata irin yunwa da yake ji. Part din mummy kawai ya wuce, ya shiga falo bai ga kowa ba, hakan yasa ya wuce kitchen don samo abinda xai danci don baxai iya jira ba har lokacin da xa'ayi dinner. Ita ma Naana ganin Zee bata nan yasa ta nufo hanyar fita, dai dai lokacin Mahmoud kuma xai shigo, wani uban karo suka ci har sai da Naana tayi baya xata fadi, da sauri ya taro ta ta fada jikinsa, runtse ido yayi sakamakon wani irin yanayi da ya tsinci kansa a ciki na riqon da yayi ma Naana. Ita kam xafin qumewar da suka yi shi ya addabeta, ita har ta sadaqas ma sai ta fadi amma ga mamakinta sai ji tayi ya riqota don tayi xaton kamar wancen lokacin xai barta ta fadi ne. Dai dai lokacin kuma Zee ta shigo kitchen din, tsaye tayi da mamaki take kallonsu, Zee tayi gyaran murya hakan yasa Mahmoud yayi saurin sakinta tare da dafe goshin shi, shi sai a ynx ma yaji xafin. Zee kuwa kallonsu take cike da tuhuma, ganin hakan yasa Naana ta sadda kanta qasa, Mahmoud kuwa ficewa yayi daga kitchen din, don ji yayi ma ya daina jin yunwar. Bayan fitarsa Zee ta kalli Naana tare da cewa "Ya akayi Naana". Naana ta dago da kanta ta kalli Zee sannan tace " Karo mukayi dashi shi ne na kusa faduwa ya taimakeni". Kallon goshinta tayi ganin har ya fara kumburi yasa tayi saurin qarasawa wajenta cikin muryar tausayi tace "Ayya sannu kinji, gurin har yayi kumburi, kawo na matsa miki". Nan ta fara matsa mata gurin, Naana tayi er qara tace " Ke da xafi fa?". Zee tace "To ai dole xaiyi xafin, in kika barshi girma xaiyi". Haka ta matsa mata gurin sosai sannan suka kwashi kayan abincin suka jera a dinning sannan suka wuce daki suka gabatar da Isha'i, bayan sun idar suka fito gaba dayansu suka xauna a dinning har da Daddy da Mummy. Sai da suka fara ci Mummy tace " Ina Mahmoud ne". Kafin suyi magana sai gashi ya shigo da sallamarshi, nan yaja kujera ya xauna suka fara dinner. Mummy ta kalleshi sosai ganin ynd goshinshi yayi ja, abinka da farin mutum, tayi saurin cewa "Son me ya sameka a forehead naga yayi ja?". Kallon Mummy yayi sannan ya saci kallon Naana suna hada ido ta sadda kanta qasa. Murmushi yayi tare da cewa " Daxu ne da xan fito toilet na xame na fadi". Dariya ta so kucce ma Zee jin abinda yace Mummy tace "Ayya sannu kaji". Daddy ma yace " Ruwa ka taka ko ya xameka". Yace "Eh Daddy ruwa ne ya xuba a qasan". Daddy yace "To Allah ya sawwaqe" Duk suka amsa da "Ameen". Nan dai sukayi dinner dinsu bayan sun gama suka koma Falo, Mahmoud ya fice xuwa side dinsa don yana da aikin da xaiyi. Naana kuma ta wuce dakintadon yau bata sha'awar kallon. Dedicated to all my fans😘 _~Written by Beelybadaru😍~_ [05/11 12:35 pm] Beelybadaru😍: [04/11 4:59 pm] Beelybadaru😍: *🌹🌹BA SO A RAINA🌹🌹* 🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹🌹 _By Beelybadaru😍_ 8⃣7⃣---8⃣8⃣ OHW 📚📲 _5 days later_ Ana gobe kenan xasu koma Kotu, ita dai Naana duk jikinta yayi sanyi, gani take Sadeeq xai yi yanda zaiyi wajen ganin ya kubuce wa hukuncin kotu. Yah Mahmoud ya tura mota a dauko Hadixa, tun safe amma har wajen la'asar shiru ba labarin su, ko ya kira nmbr'n driver din baya samun shi, ya shiga damuwa, ya kira Abdul ya fada masa, Abdul yace ya kamata suje Katsina su gano ko lpy, bai yi masa musu ba ya hau shirin xuwa Katsina. Koda suka isa gidansu Hadixa suka wuce, a qofar gida suka iske Abbanta, da yake sun gabatar da kansu gareshi wancen xuwan hakan yasa suka gaisa cikin fara'ah, ya qara da cewa "Hadixa tun wajen Axahar suka tafi, in ce sun isa ko?". Da mamaki suka kalli juna shi da Abdul, sannan ya kalli Abban Hadixa yace "Abba kana nufin tun daxu suka tafi Kano?". Abba da mamaki yace " Qwarai kuwa, nan wani yaxo yace kai ka aikoshi ya tafi da ita kamar ynd muka yi da kai, kana nufin basu isa ba har kuka taho?". Mahmoud ya danyi shiru yana naxari can yace "Abba shin yaran Sadeeq suna shigowa unguwar nan kuwa?". Abban Hadixa yace " Qwarai kuwa, kullum sai sun shigo unguwar nan". Dafe kanshi yayi tare da cewa "Oh my god, ai kuwa bamu ga ta xama ba, dole mu san abinyi don na tabbata yaran ne xasu tare su Hadixa a hanya". Salati Abban Hadixa ya hau yi cike da tsoro da rudu, yace " Yaro ka taimakeni, Hadixa ita kadai na mallaka, ku taimaka ku nemo min inda yata take". Abdul yayi saurin cewa "Abba kayi hkr insha Allah xa'a ganta". Abba kam har ya fara hawaye. Mahmoud ya furxar da iska mai xafi tare da cewa " Abba yanxu abinda za'ayi ka taho muje Kano din in yaso ni xan san abinda xanyi". Ba musu Abba yace "Bari to na shiga na fada ma mamanta". Da sauri Mahmoud yace " A a Abba in ka fada mata hnklinta xai tashi, ka dai ce mata xaka je unguwa". Gyada kai yayi duk ya rude da lamarin ya shiga gidan, bai jima ba ya fito suka shiga motar Mahmoud suka kama hanyar Kano. Har sunyi nisa sosai da Katsina, daga nesa yake hango mota kamar ta gidansu wacce ya ba Driver yaxo daukar Hadixa. Ya kalli Abdul yace "Abdul waccan motar kamar tawa wadda na ba Ado driver ya dauko Hadixa". Kallon motar suke sosai har suka xo kusa da ita, Mahmoud ya duba nmbr'n motar yaga tashin ce kuwa. Da sauri yaja burki can nesa da ita suna kallon motar, gani suka yi wani mutum ya fito daga motar ya nufi cikin dajin, da sauri Mahmoud ya fiddo da wata qaramar gun, Abdul yayi saurin cewa " Mahmoud ina ka samu bindiga? Me kuma xakayi da ita?". Mahmoud yace "Bincike ai sai da bindiga, bamu da lokaci fito muje". Ba musu Abdul ya fito, Abban Hadixa har xai fito Mahmoud yace " A a Abba ka tsaya a nan ka jiramu ynx xamu dawo". Abban Hadixa yace "Inaa, ai kuwa baku bari na anan dole na biku". Ganin lokaci na qure masu yasa suka barshi ya biyosu, da sanda suka isa wajen motar sai dai basu ga kowa a ciki ba, hakan yasa suka dinga bin itacen suna kutsawa cikin dajin. Sunyi tafiya mai dan nisa amma basu ga alamun akwai wani mutum a ciki ba, da ace basu ga shigar mutumin ba da sai suce ba kowa a ciki. Haka suka yi ta bi a hnkl har suka hango wani dan qaramin gida wanda shi kadai ne a gurin. Kai tsaye suka nufi gidan suna samun gurin buya har suka isa gidan. Sai dai qofar gidan duk securities ne, Mahmoud ya waiga ko ina don samun hanya, sai ganin wata katanga yayi ta danyi qasa xai iya hawa, hakan yasa yayi saurin miqewa daga

Chapter 1 of 4