shishigi ne be karasa ba,
In zaki iya tuna kollon da cute tai miki zaki fashinci abunda nake nufi.
Bari dai in miki gwari gwari, kamar yanda kike wankuwa dakyau a wajan kwaliyar jiki ba Wanda zai raina miki don kin fita daban a cikin kawayan ki, so kamata yayi muga fatar jikin ki itama tasha bambam da tasu, sai kuma ba haka ba, wasu friends din nakima sune abun kallo a fatar jiki ba keba,
Hakan shiya tabbata mana cewa baki kai ba akwai sauran kauyanci a tattare dake, kuma ahakan ke kina ganin babban yarinya ce, amma in kika lura zakiga kananan yara suke bibiyar ki, a yanda kike yanzu ba zaki dinga manyan kamu ba, cox dik wani mai hannu da shuni ko dan *BABBAN GIDA* maiji da kansa bazai kawo miki hari ba, don mazan yanzu ba suturar jiki suke kallo ba no,
Sunfi so suga yarinya taci ta koshi gaba a cike baya a cike fatar jikin nan kamar ka ta6a jini ya tsirto,
Yauwa yanzu za kiga manyan qwari suna miki layi, to sun hangi romo kwance a tattare dake,
Amma ahaka dan wai kinyi ado, ana kallonki haka a tsaye ba gaba ba baya, ilahirin jijiyoyin jikin ki a warwaje ana iya kirga yawansu, dan Allah wani maiji da kansa ne zekai kansa gareki, sedai kiga kwananan qwarika sun dabai bayeki kina kakka6e su suna kara like miki to duk an hada villages Asy ta kece da dariya mai sauti.
[11:02PM, 8/16/2017] +234 803 858 3423: 🌷 *HUDAH YAR KARYA*🌷
*BAIWA WRITERS ASSO*
Na
Hudallah A. Yusuf Mrs JH✍🏻
*SANARWA*
Aure aure aure sunnar Manzo, aure nufin Allah hausawa sukace matar mutum qabarinsa, wannan gaskia ne..
Amadadin iyalan Alhj Yusuf alheri. Muna farin cikin gayyatar daukacin al'uman musulmi zuwa wajan daurin auran Autarmu Auta dangware shalele Auta yar shagwaba, wato
SALHAT A. YUSUF
&
DR IBRAHIM SULAIMAN
Wacce akafi sani da
( *CUTE SALHEART*)
insha Allah auren zai kasance rana daya dana yayanmu.
ENGR YUSUF A. YUSUF
&
FA'IZA MUHAMMAD
( *ISUHU MAGAJIN ISUHU*)
Za a fara shagalin bikin ne a ranar.. Karku damu invitation card nanan tafe very soon insha Allah😘
*LABARI*
Page4⃣4⃣
Tinda Asy ta fara magana Hudah ta zama kamar status, dai-dai da ga6ar jikinta bata iya motsaya duk dan kada afadi wata kalmar da bata jita ba,
Yanda ta tattaro dukkannin nutsuwar ta bana tunanin ko sallah take tana taro hankalin ta haka, ohh ya Allah ka shiryi masu irin wannan hali amin.
Itama dariyar ta biye Asy suka dan taba, daga bisani Hudah ce ta dan tsagaita sannan ta daura da cewa,
"Wlh kawata duk abunda kika fada hakane kuma na yarda dake, ina matukar farin cikin haduwata daku, sedai ni ina ganin ba yanda za ayi in zama kamarku, sbd ni iyayena talakawa ne hasalima mahaifina ya dade da rasuwa, suturar ma ni keyi ma kaina abinci kuwa sai Mamy tayi sana'a take siya mana, kinga ina zanga abunda zan dinga ci har jikina yayi irin naku?
Sannan ni a tsarina ina kyamar yin bleaching sam banason kurajen nan irin na masuyin bleaching , kinga ba wai kauyanci ne ya hanani zama irin ku ba, kawai rashin wadatane dan haka cute tayi koskuran kirana village"
Dariya Asy ta sake yi sannan ta ce,
"Ba kinga halin kauyancin naki ba, ana kaiki kina qin zuwa, ance miki ke bakauya ce kinqi yarda, to bari kiji har yanzu kanki a duhu yake, mudin da kike ganin mu wasune kinga matsayin mu ne?
Kinsan sirrin mu ne?
Maybe ma kin fimu wani abun, duk yanda kike tunani ba haka abin yake ba, kawai idan ka iya takunka dolene adama dakai, waima kina shiga social media kuwa?"
Asy tadan dakata tana sauraron Hudah dake cewa,
"Eh na taba bude whatsapp sedai ban Dade ba naga 6ata lkc na zanyi abanza, na rufe shi"
"Ai naga alamun haka da kina harka da mutane a online tabbas da kinfi haka sanin wasu abubuwan, amma karkiji komai ki koma online zamu hadu soon, zan hadaki da classic ladies fitattun matan da suka amsa suna mata,
Sannan ya dace kisan bawai yawan tara sutura kadai shike futo da yarinya ba no, wani lkcn tara kayan beda wani amfani idan kika lura babu wacce takeso aganta da kaya yau in wani hidimar ya taso a sake ganin ta dashi, kokari ko wacce take yazamana kullum kalar shigarta daban, ko ba haka ba kawata?
Ajiyar zuciya Hudah ta sauke ta ce,
"Hakane wlh don ni kaina wasu kayan nawa har mantawa dasu nake, atsarina indai nayiwa kaya sawa biyu zuwa ukku wlh sun suremin sedai inta ajiya"
"Toh kin gani ashedai kin gane abunda nake nufi, shin waima da kike fadin baki da abunda zaki gyara jikin ki, ina kike samun na dinki ko kina nufin wani keyi miki ne,
Naga dai akalla dressing dinki na yau abeja kudi ba ya lashe sama da 25k kai zema iya fin haka yanda kika hada komai to match ina kika samo kudin?
"Wlh ni nakeyi kin san inada sana'ar hannu, babu kalar dinkin mata wanda banayi, yawancin ankon bikin nan duk ni na dinka su, toh matsalar dayace dazaran kudin sun shigomin kaf a kaya nake narkar dasu, don ni gskia Allah ya sani banason aganni cikin qasqantacciyar shiga"
Sosai Asy ta jinjina mata sannan ta ce,
"Ke ashema kina da sana'a mai kawo kudi, to bari kiji abunda baki sani ba, wannan dressing din ba irin ta zakiyi ba a yanzu,
Zaki daina saka atamfar kasa da 20k
Zaki daura lace harna sama da 50k
Zaki saka material komai tsadarsa
Zaki saka voyel, shadda irin ta yayan manya,
Zakiyi shigar larabawa, turawa, indiyawa inyamurai yarbawa, ke in takaice miki har mota Zaki shiga kisha sha'anin ki da ita irin na Wa'inda suka isa, kuma duka a kudin da basu taka kara sun karya ba,
Amma abin sirrine sai mun hadu zan sanar dake yanda tsarin yake,
Yanzu abunda nakeso dake duk wasu kudin da zasu shigo miki, ki dage da gyara jikin ki ya zama boobs naki sunyi duma duma hips naki ya fito sosai abubuwan zaman nan suyi tandama tandama ga fadi ga tsini, ya zamto ko wani juyi in kika yi suna fadin ya kagani?
Fatar jikin ki tazamo lugui lugui kamar ta yaran goye, and ya zama dole ki shafa mai yanda zaki dan haska duk da kedin farar ce amma ance in kana da kyau to ka kara da wanka, maganar quraje, wannan kananan mai kike magana, ya za ayi in cire 5k in sayi mai ko sabulun wanka qwaya daya jal a 5k koma sama da haka, sannan ya sani kuraje ai kuwa da anyi bura uba dani don wlh saina mayar an biyani kudina,
So yanzu dai kinji abunda nace akwai kayayyakin tado da breast na Muslim in kina kyamar na bature, in kin shirya sai ki nemeni zan hadu miki Wanda zasu dace dake,
Zan sanar dake abubuwan da zakina chi Wanda zasu temaka wajan gyarar fatar jikinki acikin sauki,
Ina ganin anan zan dakata don bacci nakeji dear, ga kuma wayata naji ta fara bara zanar kamawa da wuta, don tadauki zafi sosai, akwai sauran bayanai dole sai gani gaki abun zetafi yanda akeso, sedai na jiki my Hudancy!.
"Tirqashi"
Hudah ta furta, sanan ta numfasa ta cigaba da cewa,
"Laillai fa masu iya magana sukace wani wan wani wani ko baban wani ne, ai dole ma in nemoki my Asy star Asy my mentor my lovely aseeyata. Dole in gano inda kike a gobe gobe kodan inji wa'innan surruka, insha Allah kuwa zaki ganni tin safe,
Sannan zan taho da10k, ko zasu isa afara kafin in karasa wasu dinkuna,?
Heheheee Asy ta buga shewa jin an anbaci kudi, tasan ko banza zata yagi rabonta, ta amsa da
"Eh to sedai adan fara gyaran breast kinsan mayuka suna tsada, zamu fara da boobs nd hips, sai kuma fruit din da zakina ci b 4 kudin su shigo, dear saina jiki byee,
Kit Asy ta katse kiran don kadama Hudah ta sake tsareta da wani maganar, rabonda tayi doguwar hira haka ko ita ta manta,
Dogon miqa tayi hade dayin salati ga manzon tsira, jijjiga hannunta tayi alamun gajiya ta ce,
"Wannnan yarinya duk ta wahalar dani, amma ba komai ta kawo 10k din ko banza zanci 3k don ba a banza zanyi wannan dogon bayanan ba dan uwarta.
[11:04PM, 8/16/2017] +234 803 858 3423: 🌷 *HUDAH YAR KARYA*🌷
*BAIWA WRITERS ASSO*
Na
Hudallah A. Yusuf Mrs JH✍🏻
*SANARWA*
Aure aure aure sunnar Manzo, aure nufin Allah hausawa sukace matar mutum qabarinsa, wannan gaskia ne..
Amadadin iyalan Alhj Yusuf alheri. Muna farin cikin gayyatar daukacin al'uman musulmi zuwa wajan daurin auran
Autarmu Auta dangware shalele Auta yar shagwaba, wato
SALHAT A. YUSUF
&
DR IBRAHIM SULAIMAN
Wacce akafi sani da
( *CUTE SALHEART*)
insha Allah auren zai kasance rana daya dana yayanmu.
ENGR YUSUF A. YUSUF
&
FA'IZA MUHAMMAD
( *ISUHU MAGAJIN ISUHU*)
Za a fara shagalin bikin ne a ranar.. Karku damu invitation card nanan tafe very soon insha Allah😘
*LABARI*
Page4⃣5⃣
Juye juye kawai take a saman gado sam bacci ya gagara daukan ta,
Kalaman Asy su suketa kaikawo a qwalwarta, ba abunda yafi d'aure mata kai sai cewan da Asy tayi,
Zaki daina daura atamfar kasa da 20k
Zaki daura lace harna sama da 50k
Zaki hau moto irin ta wa'inda suka isa!.
Anya kuwa?
Karfa San gayu yasa inkai kaina makasa, Anya yarinyar nan ba yar mafiya bace?
karfa ta hadani da yan shanjini in shiga uku!.
Nooo gskia Asy batayi kama da yar mafia ba, don naji tana cewa a kudin da basu taka kara sun karya ba, to kodai suna da masu siyar masu da kayan ne da sauqi?
Kai inaaa ba haka bane indai ba kayan sata suke siya ba, ina zasuga kudin siyan kayanda take lissafo min bare kuma ni, zan dai bari zuwa goben in naje naji yanda abun yake,
Da wannan tunanin bacci barawo yai nasarar sace Hudah sedai.
Kiran sallan farko a kullum Hudah, don ta aje abin a ranta har mafarki seda tayi, dirowa tayi daga saman bed, take tafara harhada dad'add'un d'inkunan mutanen data aje batai ba, wasu an biyata wasu kuma ta raina kudin ne irin wanda take kunyan su, to saita amsa taita ajiya,
Aikuwa dik ta fito dasu kafin akira sallan asubahi harta yanka wasu.
Yau kam ita ta tada Mamy yin sallah sa6anin da sai Mamy tasha fama da ita sannan ta tashi, wani sa'in ma sai gari yayi haske take tashi, Mamy batai mamaki ba tasan hakan nada nasaba da taso kudi, don haka takeyi da duku duku take tashi tahau keke kafin wayewan gari kuwa ta hada wasu.
Misalin shadaya na rana Hudah ta gama shirin tafiya U/rimi, tsaye take gaban Mamy tana mata magiyar ta ranta mata dubu biyar kafin anjima za a zo kar6an dinki, dayake a wayewan garin nan harta hada kala biyu ta kuma kira duk wasu datasan kayan su yana hannunta tace su kawo kudi zata hada musu.
Mamy dai cewa tayi "Allah ya tsareni d'an jarin da nake juyawa muna cin abinci shi zan tatara in baki ki watsa su, duka sai mu taru mu tsuguna, ke kuma naki dama ba amfani yake mana ba, dakin samu sedai kwashi banza kwashi hofi, to kima bar had'ani da Allah sisin kwabona bazan baki ba"
Dole Hudah ta hakura ta fita dana hannunta daman 12k ne taso Mamy ta bata aran 5k sai taba Asy 15k yanda za'adan fara da tsoka, haka ta kama hanyar U/rimi batasha wuyan gane guri ba, har kofar gida mai nappe ya ajeta.
Wayarta ta fiddo a cikin jakar dake rataye a kafadarta, irin mai dogowar igiya ce wanda ake kira suwaga, d'and'asheshiyar bag ce milk colour wanda take kala daya da tsikareran takalmin dake makale a qafarta, shima me igiya ne wanda shi kansa abun kallone gashi yayi masifar dacewa da qafar , duka sunyi match da d'an siririn mayafin dake sagale a wuyata,
Jikinta kuwa tawa hadaddiyar gown ce purple colour, English wars ne ta kama jikinta dam, duk wani tudu da qwari babu abin data 6oye,
A idonta kuwa sanye take da dansiririn farin glass wanda ya qara fito da asalin kyawun face dinta, dogon hancin kawai kake gani.
Yayinda Zara zaran yatsun hannun ta ke sanye da wasu zobuna na azurfa, Wanda musamman taje museum aka qera mata masu harafin name enta,
Dayan hannun wani tsadadden agogo ne wanda saurayin ta ya siya mata, sai zube daya a yatsar ta na tsakiya Wanda shi akoda yaushe yananan a hannunta, tin ranar da suka hadu da Feedoh, daga tace zoben nan yamin kyau take Feedoh ta zare shi ta zurama Hudah shiyasa takemai laqabi da,
*TSANTSAR HALACCI* kai in takaice muku, mutum ko shine hasidin iza hasada, wajan iya kushe da hassada, lallai in har yaga Hudah a cikin wannan shiga to dolene yace ta hadu iyakar haduwa.
Cikin takonta na isa da qwarewa wajan sarrafa kowace ga6ar jiki, ta isa jikin bishiyar flower wanda akaima bangon gidan su Asy ado dashi,
Jingina tadanyi jikin itaciyar sannan tayi dialling no din Asy, bugu daya ana biyu aka dauka,
"Cikin muryan bacci Asy ta ambaci welcome my Hudah kin iso kenan?
Dayake Hudah ta sanar da ita gatanan a nappe.
"Murmushi Hudah tayi ta amsa da,
"Eh wlh gani a waje sarkin bacci har yanzu baccn ne be barki ba?
Asy tadan dara gami da cewa,
"Ai *kece sila* jiya kin wahal dani dayawa, dani nan fitowa koma ki qaraso kawai!.
"A'a nidai futo kimin jagura idan nashigo in doshi ina?"
"Owk gani nan"
Nan dai Hudah ta tsaya tana jiran futowan ta, sai kuma ta fara kalle kalle, sosai tsarin uguwan ya burgeta, azuciyarta tace,
Gaskia G.R.A yayi yaushe zaka hada da getto erea, wanda hayaniyan yara kadai ya isa ya buwayeka, nan kuwa silent baka ganin d'an kowa awaje kai arziki da dadi, ya Allah ka azurtamu duniya wa lahira,
Ni da nake kusa da ita na amsa da ameen namesake don wlh ba wanda beson jin dadin rayuwa,
Sedai haushin rashi makaho yace ido da wari inji bahaushe.
Hankalin ta tamaida ga gidajen alfarma dake unguwan kaf babu na kushewa, sedai wani ya daranma wani dama kuma Allah beraba dai-dai ba kome kake ganin kana da to wlh wani yafika, mai hakuri dai shiyake da riba awannan rayuwa. Ajerin 6angaran su Asy zamu iya cewa gidansu shine baya agurin, shidin ma babban gidane sedai daganin tsarin ginin bana zamani bane irin dai da anyi tashe yanzu kuma abun ya lafa,
To dama haka Allah ya fada mana, sauqi yana tare da qunci haka qunci yana tare da sauqi, shidai Allah yanaso dik yanda ka samu kanka to kayi godiya.
Tana tsaka da kallo nan kallo can Asy ta fito,
Tayi kusan 2mns idonta kyam akan Hudah, azuciyarta kuwa cewa tayi.
Woww gskia yarinyar nan tayi ba karya, yo wannan ai kwanan nan zatace mudin me?
Murmushi kawai Hudah take aika mata, ganin haka.
da gudu Asy ta nufota ta rungume tamkar ta dade da saninta, babu wani fargaba ko shakkun datake akan Hudah, don Asy tana da son jama a, bare kuma Hudah da take sakaran kofar samuce ta bude.
Ganin irin tarban da Asy ta mata hakan yasa tasaki jikinta rai daya tabi Asy suka karasa cikin gidan..
[11:05PM, 8/16/2017] +234 803 858 3423: 🌷 *HUDAH YAR KARYA*🌷
*BAIWA WRITERS ASSO*
Na
Hudallah A. Yusuf Mrs JH✍🏻
*SANARWA*
Aure aure aure sunnar Manzo, aure nufin Allah hausawa sukace matar mutum qabarinsa, wannan gaskia ne..
Amadadin iyalan Alhj Yusuf alheri. Muna farin cikin gayyatar daukacin al'uman musulmi zuwa wajan daurin auran Autarmu Auta dangware shalele Auta yar shagwaba, wato
SALHAT A. YUSUF
&
DR IBRAHIM SULAIMAN
Wacce akafi sani da
( *CUTE SALHEART*)
insha Allah auren zai kasance rana daya dana yayanmu.
ENGR YUSUF A. YUSUF
&
FA'IZA MUHAMMAD
( *ISUHU MAGAJIN ISUHU*)
Za a fara shagalin bikin ne a ranar.. Karku damu invitation card nanan tafe very soon insha Allah😘
*LABARI*
Page4⃣6⃣
Cike da nutsuwa Hudah ta gaisa da mahaifiyar Asy, sa'annan ta kawo tsaraban turaruka masu kyau ta bata..
Kyakkyawar dattijowar da suke kira Mama, cikin sakin fuska ta amsa tana sanya mata albarka,
Daga bisani ta maida duban ta ga yar tata ta ce.
"Asy banfa gane yarinyar nan ba, anya na santa kuwa?
"Mama ba zaki santa ba, kawata ce tin muna makarantan Malam yunus, karatu ta tafi can qasar Egypt kwanan nan tazo"
Asy na kaiwa nan tabi hanyar kitchen tana daria.
Allah sarki Mama ta fada,
"Ashe 'yar tawa bakuwa ce, ya sunanki ne?
Murmushi kadai Hudah keta zubawa, jin shareriyan da Asy ta shara lkc guda, a kunyace ta amsa da,
"Sunana Hudallah"
"Masha Allah sunanki mai dadi da ma'ana, ya karatu Hudallah?
"Alhmdulillah Mama muna ta6awa"
"Madallah to Allah ya temaka, cewan Mama, suna cikin haka Asy ta dawo hannun ta rike da dan madai daicin tray tayi ripping dinshi da wata leda mekyau.
Kallon Hudah tayi tace mukarasa daga ciki ko Hudancy!
Owk tafada tare da mikewa ta bi bayan ta suka yi dakin ta,
Gefan gado Asy tai mata nuni data zauna, wani qaramin table Asy ta janyo ta aza tray din akai, sannan ta dai-dai ta zamanshi a gaban Hudah ta ce.
"Bismillah my Hudancy 'yar sudaniya... Atare suka bushe da dariya,
"Aifa my Asy kin iya gillota babu ko kunya.
Ni din da ko hanyar Lagos bansani ba, rana daya harkin kaini Egypt.
Cikin dariya Asy ta ke cewa.
Yo ai dressing din jikin ki na kallah take naga kinfi kama da yar qasan Egypt din, bakiga Mama harta shiga ba, wlh kin hadu Hudancy na kuma yarda bakya shigan qasqanci wanan irin kashe kala aini sakin baki da hanci nayi ina qare miki kallo.
Hmmm Hudah tadan murmusa gami da cewa,
"Ah haba dai miye abun kallo a yar villg.... Bata qarasa ba Asy ta toshe mata baki tana daria.
"Kai Hudah baki da dama ashe baki manta ba.
To kisha kurmin ki kin tashi a yar village kin zama wise girl ..
Hudah zatai magana Asy ta tari numfashin ta da cewa.
"Yanzu dai kafin mu tsunduma kogin hira. Kidan ta6a wannan takai hunni tana 6are ledan data rufe trey din.
Fruit ne aciki ta kawo mata masu energy irin su.
Kwakwa, gwaiba, Apple, danino, inibi, kankana lemon abarba, tarkace kala kala ta hado mata duk ta yankasu kanana ta shirya su kashi kashi abun saiya bada ma'ana.
Sosai Hudah ta jinjina karamci irin na Asy, don ta burgeta matuka, dubanta tayi ta ce.
"Kai my Asy star duk ni kadai wannan kayan dadi haka ina zan kaisu kaman dai mu goma zamu sha?
"Duka ki take cikin ki dasu, kinga ni babban abincina kenan, bana sauraron waise an kawo na duka gida,
Ke nifa ko irin saurayi zaizo gurina yadan kirani kafin. Yana cewa mai zan taho miki dashi cewa nake fruit ko in fadi wani drink din mai energy.
Kema yanzu na baki samples don duk suna cikin plan dinmu,
Irin wannan ciman shi akafi so mu yawaita cinsu musumman mu mata,
Bawai koda yaushe ki take ciki da abinci me nauyi ba no.
Anfi so muna yawaita cin fruit wani lkc in kina da dama kiyi juice na kayan itatuwa zallah .
Ina fada miki in har kika jure cin ya'yan itatuwa wlh cikin qanqanin lokaci zakiga yanda fatar jikin ki zata sha bamban data wanda bata samun cin irin su, ga kuma qarin lafia ajiki.
Betsaya iya nan ba, indai wannan ciman ya kama jikin ki to wlh ko mijin da kika aura seyasan ya auri mace mai ni'ima, in kuwa kina da kishiya ayi dace ita din ballagaza ce, to wlh sunanta sorry dan zata kwashi kashinta ahannu.
Ke Hudah amfanin fruit yana da yawa, yar uwa ki gwada zaki bani lbr.
Bari mu koma 6angaran na Fulani da kuma mazaunai.
Akwai had'e had'en da akeyi na kunun alkama da farar shinkafa,
Kayan hadin suna da yawa domin dadi ake hada mai sosai, sai ayi garin su, kullum da safe ki malkada gyadarki ki dafa sai ki rinqa damawa da ruwan gyadan,
Bayan kin dama sai ki kawo garin madara ki zuba in kina son sugar kisa wlh akwai dadi sosai ga kuma gyara fatar jiki, yazama shine abin breakfast din ki,
Za kiga yanda nonowa zasu yi tantsama tantsama, nan da nan zaki ga kin canja,
Sannan akwai tablet da cream Wanda zaki hada dasu, na yarda da aikinsu kuma ba suda illah na gwada na kuma yaba,
Sai kuma sabulun wanka dasu mayuka, irin su turarukan jiki, akwai na Muslim akwai na bature wanda ya amshe ki shi zakiyi, ko kuma muyi mex kinsan bature shegene nashi emergency ne.
Hannu Hudah ta bata suka tafa,
Murmushi kawai Hudah takeyi.
Lokaci lokaci takan dauki abunda ya mata takai baki. Sedai hankalin ta na wajan abunda Asy take fada.
Asy tacigaba da cewa,
Matakin farko daya kamata ki fara dauka kenan kin tsaya sai tara tsummoki kinan adole ga yar gayu.
Yanzu kije na baki nanda 6months zakiga yanda zaki canja,
A lokacin ne zakiga masu qumban susa suna yi muku kara kaina da manyan motoci a kofar gida.
"Hahah kina bani dariya Asy, inafa zanga irin wa'inda kike nuji nida nake a ghetto erea!.
"Ke dalla wayace miki na miji yana kallon wani ghetto?
Ai wlh sedai in baki cika yanda suke so ba,
Tabb wai ghetto hmmm hudah dakwai sauranki wlh,
Yo namiji indai ya hanga ya ganki fara sol, yanda kike da dogon hancin nan kaman ke ki kaiwa kanki, ga kuma gashi dai-dai gwargado, ya ganki gaba acike baya masha Allah.
Nonowan nan nayi atsaitsaye kyam suna yi kaman zasu tsokale mai ido,
Maganar hips kuwa,
Duk inda kika motsa suna fadin.
(Bana yara bane in ka isa taso ka taya!)
Fatar jikin ki taushi li6is, by mistake hannun ki in yadan hadu da nashi ilahirin jikinsa saiya amsa, to yashi lallausar hannu wanda ko audugan rimi albarka,
Tuni dama kin gwane wajan iya dadadan kalamai da kuma sarrafa idanuwa, dama gaki dasu dara dara tubar kallah.
Dik sanda yazo hira, cikin kissa zakina watsa masa wani sahihin kallo mai dauke da sakonni kala kala,
kutt ai wlh ko Ubanshi ne gwamnar garin nan tuni zakiga ya haukace miki, sai abunda kika ce, hidiman da baya yima uwar data haifesa shi zakiga yazo gidanku yana yi,
Gaisuwar da ko Uwarsa da Ubansa basa samun kwatan kwacin ta,
Gwuiwa bibiyu zaki ga yana kwasa a gaban iyayenki.
To ya hangi gidan dadi,
Ke wlh wani ma take zaisa a rushe gidanku amaida shi ginin zamani koda beyiwa iyayensa ba,
Hmmm kedai kibar