da kawa, a nanne suka hadu da classic Feedoh inda suka kullah abota mai ban sha'awa wanda har yayi sanadin kulluwan zumunta a tsakanin iyayen su,
Classic Feedoh
'Ya ce ga Alhj Lawal, babban ma'aikaci ne a gwamnati, suna zaune a Malali Lowcost Kaduna, Alhj Lawal mutum ne mai tausayin nakasa dashi ko kadan abun hannun shi be rufe masa idoba, hakama matarsa Hajiya Hafsat, mace ce maison jama'a suna kyautatawa makusantan su, ganin shakuwar dake tsakanin 'yar su da Hudah yasa Momi ta aje lokaci ita da yaranta suka kaiwa Mamy ziyara.
Tin da Dad din Feedoh ya gane Hudah marainiya ce yake temaka masu har yakai ga sunzama tamkar yan uwa, lokaci lokaci Mamy takanje gaishesu daganan tayi gdy bisa kokarin da Dad keyi dasu,
Tsakanin Hudah da Feedoh Shakuwa ce maiban sha'awa, duk weekend suna tare da juna, in suka hadu basa kaunar abun dazai kawo rabuwansu, tahaka dai kawancen nasu ya sami asali, sedai kuma kash.
An samu banbancin hali a tsakanin wa'innan amienai, kasancewar ita Firdausi tana maraba da duk wani wanda ya furta mata Kalmar so, sam babu ruwanta da kallon na wuce da ajin wance, mai kudi ko talaka duk abu daya ta daukesu, shiyasa ma Hudah batasha wuya ba wajan kulla abota da Classis Feedoh. Feedoh ta fara karantar halaiyar Hudah ne ganin yanda take nuna halin ko in kula ga samari, ko alama Hudah bata sauraron masoyanta, inba dai ta gyalla ido ta hango abun data hango ba atare dakai, wato kudi,
(masu gidan rana)
Wani lkc takanji haushin Feedoh in taga tana amsa sallamar samarin dake tsayar dasu suna akan hanya, acewar Hudah wannan ai zubar masu da aji takeyi, haba tarasa wa'inda zata tsaya dasu sai wa'innan kananan qwarin, girgiza kai Feedoh tayi hade da murmusawa tace my Hudancy kenan matar manya,
Allah dai yanuna mani auranki lfy, harna hangoki hakimce a gidan mulki, dariya sukayi tare da bama junansu hannu.
Sosai Feedoh tazage dan ganin ta fashintar da kawarta hakan bedace da ita ba, ai baka yawaita burin duniya aranka bakasan ya rayuwa zata zo maka ba, Hudah sedai ta amsa da toh naji Hajiyata, haka suke gudanar da lamuran su babu maijin tsakaninsu, sedai dazaran Hudah ta kauce Feedoh tana kokarin dawo da ita hanya, ammafa ko kadan Hudah bata canja ra'ayinta ba, kusan duk wasu friends din Feedoh masuji dakansu sunyi sabo da Hudah, dazaran wani hidima ya samu kaman biki ko birthday party sai sun gayyaci Hudah don tana matukar burgesu, acewar su yarinyar tayine tako wani fanni, gata dakyau ga iya dressing uwa uba tsabar iya takunta da jan class don indai ba wanda yasan asalinta ba, ba wanda zaiyi zaton, wai Hudah ba yar wani mai fada aji bane a cikin garin kaduna,
*Sai kinyi Hudah yar karya👍🏻😛*
****
(Munirah tailoring shop)
Seda Hudallah
tayi 5years cikakku sannan Munirah tayi mata Freedom, inda ta hadata da shatara na arziki, don ita kanta Hudah tayi mamakin Aunty Munirah, sam batayi zaton zata mata adalci haka ba, a iya sanin Hudah Munirah tayi kokarin gaskene ta hadaka da karamin sewing machine, scission, da dai dan kayayyakin aiki masu saukin kudi,
Saiga Hudah da babban keke na wuta sabo fitikil, generator sabo dal da duk wani abunda tasan tailor yana bukata sai data hadama Hudah, aifa Hudah duniya sabuwa.
Hargida customers suke biyo Hudah da dinkuna, haka idan biki ya taso kawayanta suna mata hanyar samun aiki sosai, irin gown din amare da sauransu, shiyasa kullum tana cikin dinkin anko, masha Allah kudi Hudah take samu bana wasaba dan bata dinkin kasa da 5k, sedaifa data samu zata shiga market ta fatattako siyayyah, dik bikin da aka gayyaceta sai tayi anko, kuma komai set take hadawa, irinsu takalmi jaka mayafi su abun wuya komai to Match take hadawa ta yanda babu taron da zata shiga a raina mata,
Haka dai rayuwan Hudah yacigaba da tafiya masoya kam gasunan sunmata chaah, sedai anyi rashin sa'a ba irinsu Hudah ta tsara a rayuwanta ba, tadai yarda yau taci kudin wannan garan gobe ta wankin sha-aha-sha,
Kullum ita kenan tana wajan biki ko party, kai da abu yai abu Hudah sai ta aje ashobi amatsayin kauyanci, ayanzu tsarin datake kai shine,
Duk wani bikin daya taso tayi cancel din anko a tsarinta,
Haka kuwa tana kallo abokan karyan nata zasuyi ta buga-buga kowacce hankalinta baya kwanciya sai tayi anko,
Hudah sedai ta lafe da aiki yaimata yawa batada time din shiga kasuwa,
Sharewa dasu take sai ta kammala duka dinkunan mutanen data amsa, inta dai-daici ta cika jakarta taf da kudi, sai irin ana saura 2days afara events sa'annan zata shiga kasuwa,
Idan an fitar da atamfar 5k ne Hudah inta tashi na 10k take saya, haka in material sukayi ita saita sayi babban wanda aka fitar, sannan ta tsara masa dinki, maganar high heel, bag, costume, abun wuuuuuh,
Haka take fasawa cikin tsararrakinta tamkar gimbiya da kuyangunta, a wani taron ma Hudah takanfi amaryan hadewa hakan yasa yan mata suka fara tsanarta, shine silar lakabin da suke mata da.
*HUDAH 'YAR KARYA*
Tin suna fada abayan idonta harya kai, ga da ga kawayenta ke kiranta da hakan, tayi masifa akan su bari bataso harta gaji ta hakura.
Ganin abun na Hudah bana hankali bane yasa Mamy tazo mata da shawarar ya kamata tariqa adana wani abun, indata daura da yar nasihanta na cewa,
"Haba Hudallah ya kike mance matsayinki ne, kefa marainiya ce yanzu idan hidiman auranki ya taso wa muke dashi wanda zai tsaya mana?
Nayi nayi dake koda dan adashin nan kishiga kin ki, ace dazarar kin samu kudi sedai ki tafi kasuwa ki kwaso kayayyaki, ke kadai akwatunki uku ciccike da kaya, wasu kayanma kin mance kalarsu kuma kullum kokarin kwaso wasu kikeyi, wannan ai shirme ne gara kodan kayan kitchen ki rika siya kina adanawa watarana zasuyi mana rana"
Budar bakin Hudah sai cewa tayi, "toh Mamy yanzu so kikeyi in ringa fita tsumma tsumma?
Ko kin manta ance gatan miji yafi gatan gara?
Nidai ki tayani da addua in sami irin mijin da nake so, bama iya kayan kitchen ba har dana bedroom duka da kudinsa za a hada, kinga kuwa gara in gyara kaina ina fita dagwasgwas kona samo miki maidan maiqo maiqo, koya kikace Mamyta?"
Murmushi Mamy tayi hade da girgiza kai tace, Allah ya nufa, dukda haka adai riqa sara ana duban bakin gatari,
Ayau su Hudah sun tashi da farin cikin kammala secondary school da kawarsu Feedoh tayi, kayataccen celebration sukayi anci ansha anyi farin ciki, da yammaci Dady ya damkawa Feedoh dan makullin motor, woww fadar murna bata baki, wajan Feedoh da kawarta Hudah, qanqame junansu sukayi Hudah tanajin tamkar ita aka baiwa motar tasan dai tasuce su biyu, yanzu kam dole a sake sabon taku💃🏼
Kusan atare suka koyi motor da Hudah dik sanda driver zai fita da Feedoh saita gayyaci kawarta Hudah kafin wani lkc sun iya, yanzu HK babu inda basu fita ba tare da anyi driving nasu ba,
Bikin kawarsu Humaida ne ya taso Hudah tayi dinkuna har taba uku lada, yayinda ita kuma ta fifita tata shigar, cikin tsadadden material suka halarci taron dinner da aka shirya anan Hamdala hotel Kaduna.
*_toh masu bibiyata kundaiji cikakken tarihin Hudah, yanzu kuma zamu garzaya Hamdala hotel dan ganin wace wainar ake toyawa._*
Pls pray 4 me am sick😵
[10:58PM, 8/16/2017] +234 803 858 3423: 🌷 *HUDAH YAR KARYA*🌷
*BAIWA WRITERS ASSO*
Na
Hudallah A. Yusuf Mrs JH✍🏻
*SANARWA*
Aure aure aure sunnar Manzo, aure nufin Allah hausawa sukace matar mutum qabarinsa, wannan gaskia ne..
Amadadin iyalan Alhj Yusuf alheri. Muna farin cikin gayyatar daukacin al'uman musulmi zuwa wajan daurin auran Autarmu Auta dangware shalele Auta yar shagwaba, wato
SALHAT A. YUSUF
&
DR IBRAHIM SULAIMAN
Wacce akafi sani da
( *CUTE SALHEART*)
insha Allah auren zai kasance rana daya dana yayanmu.
ENGR YUSUF A. YUSUF
&
FA'IZA MUHAMMAD
( *ISUHU MAGAJIN ISUHU*)
Za a fara shagalin bikin ne a ranar.. Karku damu invitation card nanan tafe very soon insha Allah😘
*LABARI*
Page4⃣1⃣
Guri yayi kyau sosai an kayata side na amarya da ango da flowers masu ban sha'awa isowar su kadai ake jira,
Isar su Hudah sun tadda Hall din a cike da yan mata da samari,
Waigen inda zasu samu wajan zama suke,
Can daga nesa Hudah tahangi space akusa da wasu yan mata, su biyu ne zaune agaban dinning table mai dauke da kujeru hudu,
"Woww Fee dearie kallo gefanki na dama ga space a wajansu mu karasa"
Hudah tayi maganar kamar mai rada tanama Feedoh nuni dasu ,
"A'a fa Hoo dearie karki kaimu inda za a mana kallon raini ko kuma amana korar kare, ki kalla yaran dakyau mana sonfi karfin mu daga gani manyan kai ne, ji mutanen dake tsaye suna neman gun zama amma ba wanda ya nufesu saimu, kalla snacks and juices dake shakare da table din gabansu ko ba a fada ba kinsan ba banza ba, maybe ma suna tare da guys nasu"
" Toh matsoraciya in zaki zauna kizo muje koma su waye ni wlh sunyi bala'in burgeni tin dana shigo dasu nayi tozali,
Shiru Hudah tayi nadan lkc tana kare musu kallo.
"kutt gaskiyar ki Fee dearie zai yi wuya su mana kallon arziki, duba kiga su kansu kaman ba tare suke ba, wannan ta juya face wancan ta kauda kai, tsabar yanda ko wacce take ji da kanta yasa, ko irin hira tsakanin su babu, kai gsky fine chicks nan sunyi ba karya"
Su Hoo dearie manyan gari, suwaye sukayi da har suka fiki acikin hall dinnan?,
Sarkin kalle kalle, ke wlh kibi a sannu, ina miki tsoro kada wata rana ki kalloma kanki aljanu"
Muryan Queen Mermue suka tsinkayo tadan jima a bayansu batare da sunsan da isowanta ba, dan taji duk abinda suke fada, rungumeta sukai suna daria, cikin murna Feedoh tace, "shiyasa nake sonki Marcy akwai fadin gsky , ina kuka shige ne sai raba ido muke bamu ganku ba, har wannan uwar hange hangen tanaso ta kaimu wajan da za'aci ubanmu"
Dariya sukayi tare da tafawa, "ai Hoo dearie ba sauki Allah dai ya shirya mana ita"
Cewan Queen Mermue sa'annan ta jasu suka yi wajan friends insu,
Zamansu keda wuya, amarya da ango suka shigo. an gudanar da komai akan tsari. Anci ansha amarya da ango sun rausaya inda friends da yan uwa, suka tara masu kyaututtuka. sai fatan Allah basu zaman lfy, agurguje jama'a keta harramar tafiya don dare yayi, fitowa su Hudah sukayi sai raba ido take ko Allah zai sa ta sake ganin yan matan nan, gaba daya hankalin ta yana wajansu,
Har zasu shiga moto ta hango fitowansu daga hall din, daaam taji gabanta ya fadi ganin kyawawan samarin da suka sakosu a tsakiya, daga yan matan har guys din ko kai waye dole ka lalace wajan kallon su, duk wanda ka kalla kasan Allah yayi hallita a wajan, ga kamu sassaucin rayuwa wanda yanayin dressing da fatar jikin su kadai ya isa shaida, sosai Hudah ta susuce wajan kallon fitattun masoya, yanda suke takawa kamar masu tausayin kasa shi yafi komai tafiya da hankalin ta har suka wuce ta gabanta batare da ta daina kallonsu ba, take ta raina kanta wani sabon rashin godiya yasake dira mata azuciyarta,tana raya ashe duk shirme mukeyi villagers ake kallon mu,
Feedoh tuni ta dade da shigewa moto, ganin wucewan su yasa tayi kasa da glass din motar tadan leko da kanta,
"Toh Hajiya tunda sun wuce ai sai kizo mutafi ko in kama kaina"
tana fadan haka ta bushe da dariya harda dukan seat din kusa da ita tana fadin,
"ohh Hudancy Allah rabaki da wannan fitinan nan sha'awan. Gsky kanki akwai matsala"
Hudah kam kobi takanta batai ba, ganin sunyi sallama da samarin sun nufi inda suka paka motarsu, tayi hanzarin nufan inda suke da saurinta,
"Assalamu alaikum"
Atare Asy and Salheart suka waiwayo jin muryan dake musu sallama, kallon up and down cute salheart tai mata tawani yamutsa face kamar taga kashi, batare da ta amsa mata ba taci gaba da tafiya,
Murmushi Asy tayi sannan ta amsa da,
"Ameen wa alaikissalam, young lady hw r u?"
"Wlh am fine ina fata kema haka?"
"Lafia kawata meke tafe dake"
Asy ta jeho mata tambaya,
"Alheri ne my friend wlh tun da na ganku hakanan naji kun burgeni, zanso jin sunayanku idan babu takura"
Asy tadanyi murmushi, "sunana Asy Khaleel kawata cute salheart"
Woww NYC names, ni kuma Hudallah, Asy zatai magana sukaji an saki wani wawan horn ba shiri suka dode kunnuwa,
"Haba cute miye haka zaki kashe mana kunnuwa"
Asy tafada tareda juyawa, da sauri Hudah tace number ki plss, agurguje Asy ta karanto mata batare data jiraba tace,
" byee"
"Owk bye bye friend, thanks 4 given me ur tym 2 talk on phone"
Sai da ta adana lambar tajuya ranta fari sol tamkar tahadu da 'yan matan aljanna,
Sosai ran Feedoh yakai kololuwa wajan baci, sedai ko alama bazata iya tafiya tabar Hudah ba, da tuni tasan inda dare yamata, yanda sukama Hudah shiyafi kona mata rai dan ta tsani wulakanci a rayuwa, shiyasa bata taba koskuran wulakanta mutum, wani bangaran koma tafi jin haushin Hudah ai ita take kai kanta don haka kome aka mata ita taso,
Seat din mai zaman banza, Hudah ta zauna, ganin yanda Feedoh ta murtuke face yasa ta rungumota
"Haba Fee dearie am sorry tawa, na tuba kuma daga yau nagama kalan kawaye tinda na hadu da Asy Khaleel, ta isheni ga kuma Fee dearie ta"
Figan motar Feedoh tayi bata ko saurari Hudah ba, suka fice daga hall din.
By Hudah A. Yusuf Mrs JH
[11:00PM, 8/16/2017] +234 803 858 3423: 🌷 *HUDAH YAR KARYA*🌷
*BAIWA WRITERS ASSO*
Na
Hudallah A. Yusuf Mrs JH✍🏻
*SANARWA*
Aure aure aure sunnar Manzo, aure nufin Allah hausawa sukace matar mutum qabarinsa, wannan gaskia ne..
Amadadin iyalan Alhj Yusuf alheri. Muna farin cikin gayyatar daukacin al'uman musulmi zuwa wajan daurin auran Autarmu Auta dangware shalele Auta yar shagwaba, wato
SALHAT A. YUSUF
&
DR IBRAHIM SULAIMAN
Wacce akafi sani da
( *CUTE SALHEART*)
insha Allah auren zai kasance rana daya dana yayanmu.
ENGR YUSUF A. YUSUF
&
FA'IZA MUHAMMAD
( *ISUHU MAGAJIN ISUHU*)
Za a fara shagalin bikin ne a ranar.. Karku damu invitation card nanan tafe very soon insha Allah😘
*LABARI*
Page4⃣2⃣
Seda Feedoh ta fara sauke Hudah gida, sannan ta kama hanyan gidansu, zuciyar ta cike da fargaban abunda zata tarar saukin ta daya dady baya gari,
Direct Hudah tayi dakin ta ganin Mamy tayi bacci, da shigarta kayan jikinta ta sauya, izuwa na bacci tana yi hade da yan wake waken ta,
Bayan ta kammala taje ta tada Mamy dan ta sheda mata ta dawo,
Fada Mamy ta fara yi mata akan daren da tayi, Hudah najin haka ta fice tabar mata dakin tana kumbura baki,
"Duka ko goma batai ba shine wani dare yayi za a isheni da sababi ai sai kiyi tayi ke kadai"
Abunda take fada kenan tana qunqunai harta isa dakinta,
Tana shiga ta datse kofar, ta juya ta haye gado abinta,
Da sauri ta janyo phone dinta dake saman drawer, nan take murmushi ya bayyana a fuskarta, tunawan da tayi yaufa tayi kasaitattun new friends, don harta rada masu suna Queen and star,
Da azama tayi dialling num din Asy sai kuma tayi tunanin ko basuje gida ba,
"karfa in cika zakewa taji haushi na"
Tafada a ranta, yanke call din tayi, ta fara aikawa Feedoh text naban hakuri tasan yau fada wajan Momy sai abunda hali yayi, Mamy ma maidan sauki tayi fada inaga Momy, wacce ko alama bata so 'yarta tayi dare a waje.
Tana aika wa Feedoh text din, zuciyar ta ya gaza hakuri, nan take ta dannama Asy kira,
Daure take da towel iya cinyarta, isowarta gida kenan tayi shirin shiga wanka. Jin kara a wayarta alamun shigowan kira yasa ta maida kallon ta ga screen din wayar,
Tsaki ta doka ganin batasan num dinba ta juya tashige toilet,
Haka hardai kiran ya katse ba a daga ba, jiki a sanyaye Hudah ta dangwarar da wayar a gefe, sai a sannan ta tuna batai ko sallar magrib ba, nan ta tashi ta dauro alwalla, a gurguje ta gabatar da kara'in sallan ta, tana idarwa, again wayarta ta dauka ta sake try lamban Asy,
Dai-dai tana zaune gaban mirror tana ta yan shafe shafen ta, taji ringing a wayar ta, again dai number dazuce ta gani,
Saida ta doka wata uwar tsaki ta dauka a fusace don taji ko waye ke shirin takura mata yanda ta gaji hutu kadai take bukata,
Cikin ruwan sanyi taji an ambaci, "Hello"
Take Asy ta gane muryan don haka tadan kwantar da murya ta amsa da "Hello"
Hudah tai saurin cewa,
"Nice Hudallah da muka hadu daku dazu"
"Owk Hudah ya kikaje gida?"
"Lafia lau wlh ina fata kema haka!"
"Alhamdllh yanzu ma shirin kwanciya nake naga call inki,"
"Syyah Sorry my Asy star Allah yasa ban takura ki ba!"
Saida Asy ta dan murmusa jin sunan da ta kirata dashi , nan take taji yarinyan ta burgeta kunsan Asy wajan son girma ko gyambo yana kunyarta,
Cikin nishadi ta mayar mata da cewa,
"Haba Hudancy wani irin takura, ai yawan gaisuwa yafi yawan fada, nima saida nazo gida naji haushin rashin amsar no din ki da banyi ba,
Gashi kuma lkc daya naji kin kwanta min arai kamar mundade da sanin juna gskiya kinyi min, komai naki yana burgeni, gaki haddadiyar yarinya ga iya dressing, I luv u my Hudancy"
Wani irin zillo na dadi Hudah tayi tsananin murna yasata kankame pillow da take rungume dashi,
"Tnx my Asy star, Dik ni kadai wannan yabo, I really appreciate it, gskia kina da kirki ba kaman kawar nan taki ba, koda yake girmanta ne yakai shiyasa banma ji haushin ta ba, har nayi mata suna da Queen"
Asy tai daria tace, "bazaki gane halin cute lkc daya ba, tanada kirki sosai, matsakar daya ce ita dai bataso haka kawai ka shiga lamarinta, but ahankali in kika saba da ita da kanki zaki bani story, kuma fa kin san me?"
Sekin fada dear!"
"Dazufa Bayan mun tafi a moto take cewa dressing dinki ya burgeta kin iya make up kamar ba yar village ba lolx"
[11:01PM, 8/16/2017] +234 803 858 3423: 🌷 *HUDAH YAR KARYA*🌷
*BAIWA WRITERS ASSO*
Na
Hudallah A. Yusuf Mrs JH✍🏻
*SANARWA*
Aure aure aure sunnar Manzo, aure nufin Allah hausawa sukace matar mutum qabarinsa, wannan gaskia ne..
Amadadin iyalan Alhj Yusuf alheri. Muna farin cikin gayyatar daukacin al'uman musulmi zuwa wajan daurin auran Autarmu Auta dangware shalele Auta yar shagwaba, wato
SALHAT A. YUSUF
&
DR IBRAHIM SULAIMAN
Wacce akafi sani da
( *CUTE SALHEART*)
insha Allah auren zai kasance rana daya dana yayanmu.
ENGR YUSUF A. YUSUF
&
FA'IZA MUHAMMAD
( *ISUHU MAGAJIN ISUHU*)
Za a fara shagalin bikin ne a ranar.. Karku damu invitation card nanan tafe very soon insha Allah😘
*LABARI*
Page4⃣3⃣
Sakwakwaf Hudah taji ilahirin jikin ta babu sauran nakka, har lkcn wayar na makale a kunnin ta sedai ta kasa furta komai tunanin ta, wai yau ita ake kira da yar village,
Lallai gaskiyar masu Karin magana, gaba da gaban ta don ko Baba ma da Baban shi,
Daurewa tayi tadan kirkiro murmushin karfin hali, jin datayi Asy ta fara bata hakuri don ita kanta Asy taji ba dadi data gaya mata hakan, kunsan ance magana zarar bunu, in tariga ta fito sai hakuri,
Dakyar Hudah ta iya furta,
"Babu komai wlh karki damu kawata, a yanda nalura da yarinyar tana jin kanta sosai, kuma da gani yar *BABBAN GIDA* ce kinga kuwa abunda yafi hakama zata iya kirana dashi girman ta ne yakai,
Amma plss mai kuka gani alamun kauyanci a tare dani?
Dan Allah my Asy star karki 6oye min komai, bawai da wani manufa nayi miki tambayar ba no, ina so ne nima in karu da ilmin ku kasancewar kun burgeni tsarinku yayi min, shiyasa nashiga lamarin ku batare da neman izinin ku ba, don haka na yarda dake na baki wuka da mana, na aminta dake Asy star ina so ki wayar min dakai tayanda bani ba hatta friends dina susan lallai na hadu da mata masu aji"
Asy ta kada kai tana daria, azuciyarta tace lallai yarinyar nan za aje dake, afili ta ce,
"Insha Allah my Hudancy zan kuwa fede miki biri har wutsiya,
Saikin zama star acikin kasaitattun mata bama cikin villages people ba"
Wani irin dadine ya mamaye Hudah cikin tsananin murna ta furta,
"Wayyo Allah dadi kai amma fa yau nayi farin fita haduwata daku, my asy *KE ALHERI CE,* please dan kyankyasa min miye sirrin abin?"
"Me kikeci na baka na zuba, kisa ranki a inuwa kina tare da Asy, wannan sai mun hadu, kuma a ina kike da zama?" cewan Asy khaleel.
"Ina nan U/dosa akan layin sarkin margi, ke kina inane?" Hudah ta tambaya.
Abuja street U/rimi no 15"
"Yes nasan gurin kice min kuna G.R.A ne, ai da gani biri yai kama da mutum, insha Allah kuwa zaki ganni but kidan tofa min kadan mana pls my Asy star"
"Yaasalam"
Asy ta furta jin kosawa irin na Hudah, kwantar da murya tayi tace,
Haba kawata idan baki jin kudin da muke konewa, ki kalli tym yanzu 11pm ake nema dare yayi ki bari zan shigo next week insha Allah,"
"Kutt next week kike magana ai kamar 1year take awajena, ni yanzu haka jina nake tangaras kamar yanzu gari ya waye min. kudin waya kuma karki damu akwai ni da wani sauna wanda shi dama aikinsa kenan lolz"
"Shikenan kice in gyara zama yau ba maganar bacci"
Asy ta fada tana daria,
"Yauwa tawa ashe kin gane pls muje kai tsaye ina sauraronki, dan Allah banda boye komai.
To malama Hudah nasan abinda kike son karin bayani akai, bazai wuce cewan danayi kin iya dressing kamar ba yar village ba!.
So agskiya zamanin nan da ake ciki kanmage ya riga ya waye, indai ke din wayayyan ce kallo daya idan kikama mutum, ba saikin kara na biyu ba zaki karanci abubuwa da dama a tare dashi, anan zaki gane koshi waye, shin yakai inda akeso ko kuwa