yasan ansami cigaba cikin gidanshi,Gawani k'amshi dayaketa shakowa
tunda yatashi barci.
K'afafunshi ta rike tana lilo "dady kalla aunty taimin wanka da kwalliya kuma tayi girki me
dadi amma ta hanani wai saika tashi barci.
Murmushi yayi sannan ya d'agata sama ya sumbaci bakinta "inye gayun ba to zauna nan
ingama shiryawa sai muje ayi break fast ko?Tunda sun Hana Mimi Dina abinci gashi kuma
tanajin yunwa ko?
Anatse ya shirya yana ayyano kalar kwamacalar da zai tadda Dan dama ko zahra shike
kokarin koyamata wasu abubuwa tundashi ya iya,Tunaninshi Jidda babu abinda ta
iya,Musamman idan yai la'akari da irin gidan data fito,Uwa uba kuma gatan da takeciki,Beson
mu'amala da masu aiki amma yasan yanzu dole ya cigito kodan ta dinga ayyukan gidan.
Babu kowa babban falon ammafa daga gani yasha gyara dan gashinan sai walwali ko Ina keyi
da tashin k'amshi,Mamaki ya kamashi to waye yai wannan aikin haka?
"Mimi Ina abincin yake to?
"Dady duk suna wajan aunty A can zamuyi anjima saimu dawo nan da rana.
"Hummm" Shine kawai abinda yasamu ya furta Sannan yabita zugui zugui yana mamakin ganin
ko Ina kal saikace bajiya yaga gidan yafita hayyacinshiba sabida taro,Betashi Kara tsinkewaba
saida yasaka kafafunshi cikin sabon falon,Ya hangi yanda akaima wajan cin abincin wani irin
gyara yanda duk tsiya sai wajan ya birgeka,Gawani mayen k'amshi dayacika falon,Ya kalli 'yan
samarinshi yagansu tsaf yau babu fama akan suyi wanka ko wanne yasha gayunshi saiya
maida idanunshi akan zahra da kwailar matarshi ,Can k'asan zuciyarshi ya furta Alhamdulilah.
Kusan tare duk muka mike munayimishi Sannu tare da gaidashi,Itadai Mimi na jaye da
hannunshi saida taga ya zauna gaban kulolin abincin sannan takoma gefenshi itama ta zauna
tanafadin aci dady.
Da kaina na zubama kowa inayi Ina doka murmushi Dan gaskiya abun ba k'aramin kayatar
Dani yayiba wai ina zubama babba abinci da wasu kuma yau da kaina nai komai babu korafin
hajiya,Dan haka mukeyi da ita gashidai zanyi komai yanda tace harma ta yaba amma hakan
bazai hanata tanaci tana korafi ba.
Be tambayi inda akasami garin kunuba ammayai mamakin ganin kunu da kosai,Gakuma
lafiyayyen tea idan akwai me bukata saikuma farfesun naman kaji Wanda zahra ta debo can
bangarensu,Na sarrafasu.
Dagajin kamshin da gurin yakeyi kasan komai dake wajan zaiyi dadi.
Abazata yaji wani irin farinciki da nishadi ya lullubeshi,Aiko ganin batashi nakeyiba yasa
shima yasaki jiki cikin yaranshi ya narki abinci Dan rabonshi da walwala irin wannan tunkamin
matarshi ta rasu.
Yanayi yana satar kallona niko bammasan yanayiba Dan babu tunanin aurenshi akaina,
Yanda su zahra kedan tsokanarshi nima haddani Dan matsayi daya nake ganinmu akai.
Alhamdulillahi yaketa nanatawa fili da boye bayan mun kammala, Sadiq nasa ya kwashe
kayan yakai kitchen shikuma faruk ya goge wajan,Sannan na kalli zahra "muje mu wanke zahra.
Ajiyar zuciya ya sauke me karfi bayan munshige,Ah lallai da Alama Allah ne yaimishi wani
gata na musamman Dan gaskiya abun ya k'ayatar dashi fiye da tunani,Shafa cikinshi yayi jin
yanda ya cikashi sosai.
Kallo ya hada duk suka komatsakiyar falon suka zauna kafet sunayi yanadan jansu da hira
sama sama ya kosa su fito kuma yaga menene aiki na gaba da za akirkiro.
Muna tafe muna hirarrakinmu da dariya muka dawo falon,Nidai ban zaunaba saida na dauko
wani littafi Wanda yanzu nakeso mutsara ayyukanmu yanda komai zai dingazuwa mana da
sauki sannan kosu yaran kowa zaisan aikinshi.
Yiyai kamar bamu yake kalloba ammafa gabadaya hankalinshi yana wajanmu.
"Yauwa zahra ke zaki dinga gyara ko ina daga yau amma wancan babban bangaren dakuma
d'akunan yara nikuma Zan gyara nan dakuma dakin dady,Kaikuma Sadiq Kaine babba zaka
dinga share harabar gida kullun dakundawo sallar asuba, kaikuma faruk zaka dinga
kwashewa,Dakun gama sai wanka idan kukabari muka rigaku to zamutai makaranta mu barku.
Ihun Mimi yasa mukai shiru muna kallonta,Dirza kafa tafara wai ita menene aikinta,Duk
dariya mukayi kamin ince ke zaki dinga d'auko kayan da zamudinga cin abinci Amma duk ranar
da kikafasa wani Abu daya to Zan canzaki.
"Banji kinyi maganar girkiba"cewar zahra.
"A a ai nice zandingayin girki safe da Rana dakuma dare amma daidai cikinmu Zan dingayi
kadda mubarshi ranar da ake makaranta kuma zamuyi break me kyau yanda bazamuyi saurin
jin yunwaba harmu dawo,Amma idan kingama aikinki da wuri zaki iya kamamin girkin tunda
kince ke baki iyaba sosai.
Mamaki da tsoron yarinyar yaji yana neman kamashi sannan yanaso yai magana sabida ai
alissafin da akayi aikinta yafi na kowa yawa kadda taita wahala kuma,Saidai beso yasamusu
baki tunda basusa dashiba.
""""*****"""""
Shinkafa da miya naimana da Rana wadda na wadata miyar da namansa sai kayan lambu.
Ina gama sallar azahar nasaka kuka sabida kewar hajiya.
Duk kewayeni sukai yayinda sukai dako dako kamar zasu saka kukan suma, Mimi ce ta
zanzare ta Kira dady Wanda gama wayarshi da hajiyarshi kenan tana tambayarshi badai
matsala gidan nashi ko!!!.
Da mamaki ya biyo bayanta sabida yaga Lafiya lau akagama cin abinci gwanin ban sha'awa.
Tasasu zahra tayi sukabar dakin ganin shigowarshi,Jiyai wani nauyima ya dabaibayeshi,Amma
saiya sami kanshi da rashin jin dadin kukan Nata musamman yanda tsakanin jiya da yau
gidannashi yake cikin farinciki kuma yasan itace sila.
Matsowa yayi kusa dani tare da riko hannuwana Niko uwar 'yanson jiki ai gabadaya na
rukunkumeshi ina kuma bare bakina.
Rungumeni yayi ajikinshi yanajin wata irin nutsuwa dayajima beji irintaba,Besan lokacinda
yafara shafar gadon bayanaba yanadan jijjigani alamar lallashi,Saida yaji na daina kukan sai
ajiyar zuciya sannan ya Fara magana cikin sanyin murya"Jidda meyafaru kike kuka?uhum
gayamin me kikeso?
Bakina na turo gaba kamin ince ni gida zani.
Damm kirjinshi ya buga kamin wani tsoro yanemi rufeshi,Kaddai ace hartagaji damu,"Sorry
Hajiya kikeson gani?
"Kaina na dagamishi inakuma lafewa cikin krjinshi danjinai yanawani mayen kamshi gwanin
dadi.
"To daina kuka kinji ko!duk lokacinda kikeson ganin hajiya ki gayamin kawai zankaiki
basaikinyi kukaba kinji ko?Tashi maza ki shirya saina kaiku anjima saina koma na daukoku
hakan yayimiki ko?
Jiyai hankalinshi yatashi da amsar da zanbashi danhaka inadaga kaina alamar na amince
harwata ajiyar zuciya ya sauke.
Dan Allah kuyi hakuri banda caji ne
YARDA.
Na maman khadija.
12
Kasancewar dama nai wanka yasani jawo hijab Dina Ina kallonshi alamar na shirya.
Dariya yayi kamin yace"Haba hajiya Jidda ki d'an watso ruwamana sannan kiyi kwalliya har
gidanmu zamuje fa!!
Yana barin d'akin na lek'a falo wajansu zahra"Banza kuyi sauri Ku shirya unguwa zamuje.
Duk mikewa sukai suna dariya yayinda shikuma ya idasa ficewa yana murmushi,"Ji Dan Allah
saikace ba itace yanzu tagama bare baki ba tana kuka.
Nida Mimi agaban motar kusa dashi su zahra suna baya,Tsabar hirarmu gabadaya babu me
sauraren kowa,Yayinda yakejin kamar ya saka ihu sabida shifa Sam ba ma'abocin son hayaniya
bane shiyasama ake kiranshi da miskili wani lokacin,Amma ya lura zuwan Jidda gidan kowa
bakinshi ya bude.
Da ya usi mukafara cin Karo mamaki ya kamashi lokcinda yaji na makalkale jikinshi Ina
dariya,Lallai aiki gameyinka,Abinda yake nanatawa kenan cikin zuciyarshi.
K'arasawa yayi wajan motar yana gaida dady,Yayinda su zahra suka gaidashi lokacin duk sun
fimijinki, motar.
Cikin girmamawa ya usi yace to kashigo mana.
"A a kuje ciki kawai anjima idan nadawo d'aukarsu sainashigo mu gaisa ku gaishe da hajiyar.
Baki ahangame take kallonmu kamin tace"Nashiga uku ni Hauwa wane mahaukacin yace ku
fito yau?Ke Jidda hardake Dan gidanku akaiki jiya yau kidawo ubanme zakiyi anan din?
Bakina na turo gaba Ina harararta Kai hajiya nifa nayi kewarki ne shine nai kuka sai daddy
yace in shirya ya kawomu.
"Oh inkana duniya zakasha kallo ammadai na yadda shi kanshi dadyn naku bawai hankaline
dashiba,Tunda zai iya biyema shirmenki kajifa Usman!!!
'Dakina muka shige nida zahra mukabar hajiya nan tana sababi Number hajiya kaka take nema
ta turomata ta dady ta wankeshi yanzu yanzu Dan abun ai hadda shirme akai amarya jiya
amma yau ta dawo ganin gida?
****
"Kai dago idanunka nan ka kalle nima in kalleka Danni nan da kakegani bawai kanwar lasa
bace,Ashe kaima sakaraine habibu?Sabida Allah haka zaka dinga biyemata tana shirme
kenan? Dama ai kasan dole sai ahankali zata Saba da rashina ko! Amma shine dagayin kuka
zakawani kwasota ka kawo gida ubanme zanyimata tunda ita tace tanason auren iye To bari kaji
idan kakuma debo wa innan dogayen kwaurin naka ka kawomin ita gidannan saina cinyeku
d'anyu daga kai har ita, Danhaka idanma zaka koyi yanda ake lallashi saika fara.
Shidai yana zaune yana jinta hasalima masifar tata dariya takebashi.
Saida ta rakamu har wajan mota sannan ta kalleshi"To dady aita hakuri Dan Allah Ana
kwabawa ba komai ake biyewaba Ku gaida gida Allah ya tsare,Jidda idan kika kuma zuwamin
gida bakiyi wata dayaba to kitabbata sainasa usmanu ya karye miki wa innan siraran kakafun
naki.
Jan motar yayi yana dariya kai hajiya akwai mita da fada tai lallashi tai fada ita da hajiyarshi
besan wacce tafi wataba.
""""*****"""""
Itamadai hajiya kaka saida tai fadan fitowar ammadai ba kamar hajiya ba.
Ina zaune d'akin hajiya kaka bayan na idar da sallar magriba sukuma su zahra duk suna
falonta sabida zahra abun yazo Mata wajan la'asar babu halin yin sallah.
Zamatai gefena tana mirmushi "ah Jidda anyima miji addua ko?
Murmushi nayi ina rufe idona sabida kunya.itama dariyar tayi kamin tace" badai kunyata
kikejiba nida nazo muyi hira kuma!
Kaina na girgiza ina kallonta amma ba yi maganaba.
"Washe baki tayi kamin tace gayamin jiya tare da dadyn kuka kwana ko?
Manyan idanuna na fiddo gabadaya ina kallonta,Kai hajiya mezai kaini dakin dady
kuma,Nidasu zahra muka kwana fa!!!!
Dora hannuwa tayi akirji alamun tashin hankali kamin tace"Innalilllahi naga ta kaina ni binta
ke kuwa Jidda kina haukane da auren naki zakibar mijinki ki kwana dawasu shikenan Ashe jiya
kinsha tsinuwar Allah data mala'iku yo Ashe shiyasa naga fuskarki tafara duhu.
Tsalle daya nai saigani kusa da ita Dan na masifar tsorata wallahi,Tuni idanuna sunfara tsiyayar
da kwallah Ashe shikenan nagama yawo tunda Allah ya tsinemin,Kuka nasaka ina riko
hannuwanta.
"Dadine taji yakamata Amma saita fuske,"Kinga kwantar da hankalinki ai Allah zai yafemiki
ainasan baki saniba ko?
Kaina na dagamata ina share hawayen idanuna.
"To bari Ingayamiki gaskiya Danni bazanso wani Abu ya samekiba tunda ina sonki danhaka ki
nutsu inyimiki bayani kinji ko?
Hawayena na share ina kallonta.
"Yauwa to kingadai anriga an dauramiki aure yanzu dole zaki kiyaye wasu abubuwa sabida
kisamu ki sami tsira wajan ubangiji,Nafarko dole zaki dinga kula da mijinki duk abinda yakeso
shi zaki dinga yimishi zai kuma sonki sannan ga lada da Allah zaitabaki,Kinga yimishi sannu da
zuwa darakashi idan zaifita yimishi addua da kuma hadamishi ruwan wanka da temakamishi ya
shirya sannan inkinga ya gaji saiki dinga temakamishi da tausar jikinshi,Sannan dole ki dinga
kwana dashi.
Hannuwana na Dora aka zansaka kuka,Tai gaggawar jawoni jikinta tare da rufemin
baki"Shikenan tunda bakiso agayamiki gaskiya tashi kutafi.
Shiru nai amma har lokacin kirjina bekoma daidaiba yo ai abinne yazomin asama.
Ahankali ta dinga nunamin yanda zanyi cikin nutsuwa da kwantar dakai tun ina zare zaren ido
harna koma ina dagakai alamar dai na fahimta sannan tace tashi kiyi sallar isha'i saiku wuce
ammafa lallai yau kadda ki kwana d'akinki kibi mijinki inba hakaba aure zansa yakumayi wacce
zata kula dashi.
Bakina na turo gaba kamin in mike"Nikuma wallahi yana auran wata zanyi tafiyata gida
wajan hajiya.
Kamin mu wacema saida hajiyar takuma jama zahra kunne akan kadda ta kuma yarda
mukwana tare inba hakaba babu wata shakuwa dazata shiga tsakanina da dadyn,Aiko nan da
nan tai na am da hakan Dan itakanta tunanin yanda zata hada tsakaninmu takeyi.
****
Ko cikin mota lamo nayi ko hirar nakasa sabida tunanin yau Zan kwana da dady,Shidai bekawo
komai arashiba hasalima tunaninshi ya tsayane akan kila kewar gidane ke nukurkusata.
Itako zahra ai tsara yanda za ai kawai takeyi.
YARDA.
Littafin maman khadija,Kamar yadda kukasani maman khadija tasaba kawo muku labarin
littatafai domin nishadanwarwa agareku,To wannan karonma gata DA wani sabon salo cikin
labarin YARDA.
Ina Mata masu gudun soyayya DA babban mutun? To kuzo zakuji yanda manyan mutane ke
baje kolin soyayyarsu me matukar birgewa da tsayawa arai.
Duka wannan labari zaizo muku akan naira Dari biyu kacal game buk'ata,200.
Account number.
0005074141 Aisha sabiu ja'iz bank.
Kokuma number waya.
08142643253
Maman khadija.
Duka zaku turo shaidar biyanku ta wannan layi👆🏻Nagode sainajiku.
Maman khadija.
Haske writer's asso.
YARDA. 13
Duk dacewa cikin kowa acike yake amma saida ya biya damu yaimana siyayyar kayan kwadayi.
Har wannan lokaci jikina asanyaye yake nifa mamakin yanda Zan kwana DA dady
nakeyi,Afakaice nad'an waiga kadan na kalli girman jikinshi musamman kirjinshi,Ai sainaji wani
kwattt na hadiye wani miyau batare Dana shiryaba.
Kamin mu k'arasa Mimi tai barci,Dayake dama nida itane gaban motar.
Dan kallona yai kad'an kamin yace"Jidda ko baki da lafiyane?
Bakina na turo gaba tare DA kauda kaina ga barin kallon inda yake kuma banyi maganaba
saima Mimi Dana gyarama kwanciyarta ajikina sabida barcin nata yai nisa.
Murmushi kawai yayi tare da 'dan buga sitiyarin motar,Fadan da yasha wajan hajiyarshi
kemai yawo cikin zuciya,Shiko taya zai shawo kan wannan rigimammar.
Kasa motsawa nayi koda motar ta tsaya saida duk suka gama ficewa sannan ya zagayo
wajena ya sabi Mimi akan kafadarshi"Idan kin kintsa ki kawomin tea d'akina.
Bayanshi na harara kamin in fito cikin motar,Ina gyara hijab dina.
Ruwa kawai na watsa sabida zafi-zafin da akeyi,Ina k'okarin saka kayane zahra ta
shigo."aunty dady na kiranki fa kadda ki manta ki kwanta"
Zahra nifa bansan wulakanci gaskiya nace ki daina cemin aunty ko?
"Kema fada kikeyi amma kinsan dolene mu kiraki da aunty daddy kike aure fa! Bama wannan
ba ai ki godema Allah da ba mum muke kiranki dashiba,Hayewa gado tayi tana
murmushi,Yayinda nabita da harara kamin ince dan Allah kikaimishi tea din Allah kaina ciwo
yakeyi.
"Hahhhha aiko banzuwa wlh aiyasan danidin amma yace saike danhaka kije kawai amma
yakamata kidan k'ara turare yanda zai gigice gaba daya.
Baki na hangame Ina kallonta"Ah lallai zahra Ashe tuni kikazama 'yar iska dady nefa?
Lumshe idanunta tayi kamin tace wayyo soyayya dadi Allah hadani da mai sona zanbashi
tsantsar soyayya,To dallah dazakice dady nefa,Cemiki akai shi dadyn be iya soyayyaba KO
beson soyayya?Ai zakiban labari waataran Amma wallahi dady k'arshene wajan iya love.
Hijab Dina nasaka nabarmata dakin dannaga yau wani tashen iskanci takeji,Saida safe aunty,
Cewar zahra ganin zanbar dakin.
Bantashi jin wani mugun tsoroba saida nai sallama cikin D'akin babu wani haske sosai amma
Ina hangen dadyn zaune gefen gado da babbar wayarshi ahanunshi,Dakin saiwani mayen
k'amshi ketashi musamman yanda ac din tagama sanyaya d'akin.
Fararen idanunshi ya zube akaina kamin ya Saki murmushi sabida ganin yanda bakina yake
ad'ane da alama rigimar na kusa.
Niyyar cokana yayi danha saiya maida wayarshi ya ajiye gefe"Amarya shigo mana keda d'akin
mijinki"
Tuni idanuna sun kawo ruwa jin abinda yace,Kuma ban motsaba saidai kaina Dana sadda
k'asa.
Sam banji motsin tasowarshiba saidai naganshi gabana yana niyyar amsar tea din Dana
hadomishi.
Saurin sakarmishi nayi Ina niyyar juyawa,Danhaka da sauri ya riko hannuna daya yana fadin
"Ah to kuma inazaki inace yaran duk sunyi barci ko?
Cikin murya wadda take cike da shagwaba nace to ai nima barcin zanyi ko.
Zaunar Dani yayi bakin gado yacigaba dashan tea dinshi saidai lokaci zuwa lokaci inajin
idanunshi akaina.
Saida ya wanko bakinshi sannan yadawo kusa Dani ya zauna har guiwarshi nadan tabo jikina
tuni nakuma takurewa saidai shi yaiwani irin basarwa dinnan kamar ma besan abinda yayiba.
"Gobe zakuje school ko?
Akunyace na dan kuma muskutawa sannan na dagamishi kaina batare danayi maganaba.
To tube hijab din saiki kwanta ko?
Manyan idanuna na fiddo waje kamin ince Ina Zan kwanta dady?
Kauda kanshi yai gefe yana dariya cikin zuciyarshi lallai yarinyar nan da wayanta kenan.
"Kinga Jidda ki tube hijabin ki kwanta gobe zakuje makaranta nikuma zanshiga abuja idan
Allah ya kaimu so kinga zamu iya makara ni sai inkwana falo hakan yayi miki?
Kusan Adan tsorace na d'aga kaina,Sannan na raba gejenshi na kwanta batare danacire
hijab dinba ammadai araina naji dadi tunda yau mala'iku bazasu tsineminba tunda nazo kwana
dakin dady.
Saita ya tabbata barcina yai nisa sosai sannan ya lallaba ya janye hijabin jikina idanunshi
nakan kyakykyawar fuskata domin betaba tunanin haka nakeba hasalima betaba zama ya
k'aremin kalloba duk ganin da yakemin idan yaje makaranta wajansu zahra.
Saurin kauda kanshi yayi lokacinda idanunshi suka sauka akan 'yan madaidaitan kirjina wa
inda bawai gama tasowa sukaiba hasalima yanzune suke tashensu.
Daki-Daki haka yadinga bin surar jikina da kallo Wanda har saida yaji idanunsu sun wadatu
da hakan dan Kansu sannan ya lallaba ya kwanta kusa Dani,Kamar mejin tsoron wani Abu ya
cutar dashi haka ya rungumoni jikinshi.
Wata irin ajiyar zuciya me k'arfi ya sauke,Musamman dayaji nakuma shigewa
jikinshi,Hancinshi ya kuma mannawa wajan wuyana danjin wani sanyayyan k'amshi me matukar
kwantar da hankali.
Motsawar farko da yayi saijiyai Ana sallar asuba,Ahanzarce yaso tashi saidai jin yanda aka
nannade jikinshi yasa ya tuna bashi kadai ya kwanaba,Rabon da ya rasa sallah tun kamin
mariganya ta rasu domin alokacinne da cikinta ya tsufa sosai to basucika samun barciba sabida
ciwo.
Da kyar ya yakiceni jikinshi sannan yatashi,Niko ai duk tunanina hajiyace na makale.
Saida duk yatashi yaran sannan yadawo dakin yafara tashina,Dan lokacin tuni angama sallah
ma.
Addua nayi sannan na bude idanuna aiko sai akan dady Wanda ya zubamin ido yana
kallona cikin hasken daya kunna.
Akunyace natashi nai saurin maida hijab Dina kayi hakuri dady yau na makara.
Murmushi ya saki kamin yace"Aidole tunda kinji dadin jiki ba irin na hajiyaba ko?
Kusan da gudu nabar dakin Ina murmushi.
Zahra na tadda ta idar da salla,Da sauri nima nayo alwalar nazo na kabbara sallar.
Ban tsaya biyema zahraba wadda keta tsokanata wai kamshin turaren dady nakeyi,Na wuce
bedroom dinshi domin gyarawa.
Saida na gaidashi sannan nawuce na wanke toilet bayan na daurayemishi wandunanshi
safuna danaga yajik'a.
Yana zaune akan doguwar kujera harsaida na gyara ko Ina nasa turare sannan na kalleshi
"dady yanzu zakai wanka ne?
"A a jeki abinki ki huta amarya Ashe haka kike da zafin nama? Allah yaimiki albarka anjima
saikizo kimin wankan.
Da gudu na fice kai dady Anya ba d'an iska bane kuwa,To yanzu saiya dinga min maganganu
irin haka,Dan Allah aga naimishi wanka ai sai acemana 'yan iska.
****"""""****
Bakwai saura duk muna zaune afalo Mimi Nata kwaso kayan buk'ata kowannenmu da kayan
makaranta jikinshi yayinda dady ke zaune saman kujera yana waya amma wani Abu Dana
fahimta shine duk idan nadanyi satar kallonshi sai inga idanunshi na kaina shiyasa sainaji duk
kunya ta kamani.
Yayinda shikuma mamakin halayena yakeyi saikace wata babbar mace,To kuma dama haka
abin yake indai iyaye zasu Fara nunama yaransu yanayin ayyukan gida Dana zamantakewa
musamman ta aure to lallai komai kankantarsu babu abinda zai gagari yarinya,To matsalar da
akesamu yanzu wasu itayenma sai bikin yarinya ya Fara matsowa sannan za ace za
akoyamata ayyukan gida girki da kula da Mijin wannan ko ai kowa yasan ba lallai idan wani ya
shigaba wani ya shiga.
Saida mukaci muka koshi sannan muka maida sauran akulla Wanda zamu wuce dashi
makaranta dan yau sai yamma sabida islamiyya.
Idanunshi akaina yake fadin Baku da wata matsala ko?Zan wuce abuja amma kila zuwa
dare indawo inkuma kunji shiru to Zan turo sulaiman ya tayaku kwana wancan room din
danhaka saiku kula bansan yawo kunji ko?
Da to duk muka amsa mishi tare damai fatan dawowa Lafiya.
Dallah kije ki rakashi ke wallahi kamar wata bakauyiya!!!Cewar zahra.
Bakina atunzure nabi bayanshi aiko yanajin takuna ya juyo da sauri,Dan jiyai kirjinshi
yawani buga musamman daya tuno yanda kayan makarantar suka fiddo surar jikina kuma
yasan da wuya idan nasako hijab din,Ilai kuwa yana juyowa muka hada ido,Ganin yaran babu
Wanda yafito yasashi jawoni jikinshi,Abinda ban zataba haka zalika bankawoma rainaba.
Ajiyar zuciya ya sauke yanawani saukemin numfashi akunne Wanda yasani jin wani fitsari
zai kuccemin.
"Kiji tausayina kidaina sa turare idan zaki fita sannan kidaina fitowa harabar gida babu mayafi
kinga gamegadi sannan ga Direba zasu kallemin iyali kinji?
Neman kwace kaina nakeyi daga gareshi kawai sainaji wata zazzafar Sumba saman goshina
Abazata.
Wani taga-taga nai zanfadi lokacin lokcinda yasakeni,Shiko ficewa yayi yana murmushi
yayinda yakejin wata nutsuwa na ratsa jikinshi.
Saida zahra tazo tajani sannan muka koma cikin falon dan tuni jikina yagama
mutuwa,Gaskiya hajiya Zan gayamawa dan da alama dady lalatani zaiyi.
TUSHEN LABARI.
Yanzu Kai tsaye zamu farkon labarin shin wai wayema Dr.Habib?
YARDA.
Labarin yarda na kudine idan kina buk'ata zakibi wannan tsarin domin samu.
Acct no.
0005074141 Aisha sabiu,Ja'iz bank.
Kokuma katin waya ta wannan layi,08142643253.
Maman khadija.
Tura shaidar biya ta wannan number👆.
14
Alhaji ishaka inkiya Alhaji nabature,Babban mutunne sosai cikin garin Kaduna haifaffen garin ne
domin anan ne duk tushensu yake,Alhaji nabature me arzikine sosai dan D'an kasuwane na
nunawa cikin jaridu.
Yanada matarshi guda d'aya hajiya binta wadda sukai aure tun saurayi da budurwa kuma
Allah besa yaimata abokiyar zamaba harta Allah ta kasance akanshi.
Hajiya binta itama 'yar nan cikin garin Kaduna ce kusan kowa Nata anan yake shiyasa duk
inzaka bada tarihinsu to lallai zakace sudin 'yan kadunane gaba da baya.
Yaran hajiya binta bakwai maza biyar sai Mata biyu,Habib shine k'arami dan shine
autanta,Cikinsu babu Wanda beda rufin asirinshi har matan domin ko wacce tana aikinta
sannan duk sukan hada da kasuwanci kamar yadda mahaifinsu ya shawarcesu tunkamin k'asa
ta rufe idanunshi.
Hajiya Aisha na aure kano sai hajiya Rukayya dake aure hadejia ko wacce tatara iyalinta.
Sauran mazan kuma ko wanne da muhallinshi babu wanda yai sha'awar zama da ita koda
yake itace batason zama da surukai.
Allah ya temaketa wajan ganin hade kan dukkan iyalanta dan gaskiya akwaisu da hadin kai
da son juna sosai sukeson junansu.
Ayanzu hajiya tana tare da jikanta tahirr kamin yatashi dan yanzu haka da ranar aka,To
hakafa hajiya binta take Sam bataso ta zauna ita kadai amma kuma bata yadda ta zauna da
surukaba shiyasa takema jikokinta haka idan ta zauna da wannan dayai aure saita kuma daukar
wannan komace ko namiji.
Saidai duk da haka lokaci zuwa lokaci kakan sami gidan Nata cike da jikoki dan Sam bata da
matsala,Wasuma sukanje Mata weekend.
Dr.Habib me kimanin shekaru akalla 41 yanzu shine yaron hajiya na karshe yayi karatunshi
na likitanci a kasar China Wanda saida yazama cikakken likita sannan yadawo najeria afarkon
samartakarshi,Habib irin miskilan mutananne saidai yanada duk wasu halaye na kwarai da ake
burin samunsu akan mutumin arziki.
Dawowarshi yafara aiki awata babbar asbt cikin kwarewa da sanin makamar aiki ga kulawar
dangi tako Ina domin awannan datsin ne Allah yaima mahaifinsu rasuwa,To saikowa yake bashi
kulawa duk da cewa alokacin yakusa shekaru 30 Saidai ganin shine k'arami yasa ake
nunamishi hakan.
LALURARTA ce sanadi;Tazo ganin likita sabida azababbane ciwon ciki Wanda takanyishi
duk wata aiko ranar Allah ya dorota akan sa'a sabida alokacin shi ganinshi ma saikayi sa'a.
K'amshinfa shine Abu na farko daya fara yimishi sallama dalili na farko dayasashi sanin eh
budurwace wadda zaigani yanzu.
Saida yayarta ta temaka Mata tadan zauna sannan suka gaisheshi,Amsawa yayi batare daya
kallesuba saidai tuni zuciyarshi ta azalzaleshi akan ya kalli fuskar Mara lafiyar.
Danhaka dole ya kureta da kallo Wanda besan lokacinda yai hakanba har saida kukanta ya
fargar dashi.
Magunguna ya rubuta mata da allura bayan yarubata wasu gwaje gwaje da za aimata,Saidai
alokacinne yasamu kanshi da bata umarnin ta dawo bayan kwanaki uku,Alhalin shi kanshi
alokacin besan dalilin dayasashi Neman hakanba.
Awannan lokacin bata isa tace ga kalarshiba dan ciwo be barta ta kalli ko fuskarahiba.
Wannan shine silar haduwarshi da Maryam wato mahaifiyarsu zahra.
Kunsandai miskilin mutun be iya son abuba danhaka irin kulawar dayabawa matarshi abar
ayi koyi da itane.
Haduwarsu da watanni bakwai akaimusu aure,Dan itama haifaffar kadunace aiki mahaifinta
keyi zaria shine sukan bishi wani lokacin,Wani lokacin kuma suyi zamansu nan kd din.
So bawani wahalar bincike bangarorin zasu samuba.
Idan kashiga gidansu to lallai zaka fito da kunya domin Maryam wayayyace musamman data
Lura da abinda mijinta ke buk'ata kenan kulawa,Shiyasa bata hada kulawa dashi da komaiba
hasalima bata da wani lokaci Nata matukar yana gidan.
*****"""""*****
Haihuwarsu ta farko suka sami me sunan hajiya wato fatima saidai suna kiranta da Zahra,Duka
shekarar zahra uku da haihuwa ta haifi Abubakar Sadiq taso kwarai alokacin ta tsaida haihuwa
amma yai biris da hakan domin shi haka Allah ya halicceshi da son Tara zuri'a.
Kasancewarta mace me hakuri sai bata damuba saidai Sadiq ko shekara biyu be idasaba ta
haifi Umar faruok to alokacinne hankalinta yatashi hadda kukanta akan tasami tazarar haihuwar
sannan ya amince Wanda ba aje ko inaba yace yafasa yara yakeso tunda dai babu ta inda
yagaza da gidanshi.
Datai hakuri saigashi Allah ya dagamata kafa dan koda ta yaye Sadiq saida yai shekara
biyu sannan tasami cikin auta Maryam wadda taci sunan mahaifiyarta ake kiranta da Mimi,
Satin Mimi biyu da haihuwa Maryam tace ga garinkunan irin mutuwarnan da bahaushe yake
Kira da kwanta shiru,Domin Lafiya lau aka kwanta da ita amma saidai gawarta da safe.
Mutuwarta tai matukar gigita zukata balle me gayya dan saida yakoma ko magana beyi sabida
tsabar tashin hankali da damuwa.
Be yarda kowa ya rainar mishi yaraba shiyasa suka taso da d'abi'unshi kaf domin rainonshine.
Dangin marigayiya sunso su karbi yaran musamman Mimi datake k'arama amma ya kiya
domin yamafi jin tausayinta akan sauran ita kanta batasan dadin uwaba sai shi,Haka itama
hajiya tagama kwakwarta amma ya hanata yaran ko daya saidai datayi magana saiyace
zankawomiki hajiya amma duk ranar daya kaisu din to anagama yini zaizo ya kwashe yaranshi.
Dole ta hakura ta zubamishi ido tunda taga yana iyakar bakin kokarinshi.
Bayan rasuwar matarshi da kusan shekara daya yafara kasuwanci kamar yadda yaga 'yan
uwanshi nayi aikosaiya fada sana'ar saida motoci to filaye cikin ikon Allah kuma yanasamu fiye
da tunanin me karatu shiyasama wani lokacin yake taushe zuwa aikin yai tafiyarshi harkokinshi.
Tun awannan datsin hajiya binta tafara mishi tayi akan lallai yakamata yai wani auren,Saidai
kullun amsarshi itaece To daga wannan to din bazai kuma k'ara komaiba.
Ganin beson maganar yasa taima yayunshi magana nan ma dai hakan take domin kuka
yasakamusu ma wai basujin tausayinshi dole suka zubamishi ido saidai basu taba mantawa
dashi wajan addua ba.
Girman zahra yasa tafara fahimtar Dawainiyar da dadyn yakeyi dasu tai yawa yakamata ace
shima yasami nutsuwa amma datayi mishi magana saiya bata amsa da maganar dakesa jikinta
sanyi da tsoro"Zahra bawai aurene bansoba nasan nima Ina buk'atarshi saidai inajin tsoron
wacce Zan dauko amatsayin matar da zata rikeku amana,Mutane da yawa yanzu Kansu kawai
suka sani saikuma kwadayi musamman Mata na tabbata yanzu duk wadda tashigo gidannan
saikunsha wahala danhaka kidai tayani da addua insha Allah komai lokacine.
Wannan maganar itace