Share this page
1 / 4
An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://thausanovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.thausanovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [YARDA. 1 Zaune suke cikin cikin ajin nasu,Su kadaine azaune sabida anfita break adaidai lokacin. Kuma janyemata hannu tayi akaro na uku kamin tace" Zahra yakamata kidaina wannan tagumin ki gayamin matsalarki,Kindaisan duk fadin makarantarnan babu Wanda nake kulawa saike bansan damuwarki sabida Allah yagani NA YARDA dake to damme ke bazaki saki jiki daniba?Ko kina tunanin har yanzu bankai matsayin da zansan damuwarki bane? "Ajiyar zuciya ta sauke me k'arfi kamin ta kamo hannuwan me maganar ta farko" Wallahi ba haka bane Jidda kema kinsan NA YARDA dake kilama fiye da yanda kika daukeni amma matsalata ta cikin gidace nakuma rasa ta yanda zan bulloma damuwar saidai inaso ki tayani da addua Dan Allah idan Allah ya kaimu wani lokaci zan gayamiki komai ammadai yanzu kifara tayani da addua tukunna kinji? "Kwace hannuwanta tayi tana hararar zahra din kamin tace dalla ni kyaleni indai bazaki gayamin matsalarkiba to wallahi babu ruwana dake. " Murmushi tasaki tana kuma kamo hannuwan jidda din kamin tace"yi hakuri sahiba Dan Allah wallahi dama matsalar dady ce yana cikin takura sannan muma muna buk'atar wadda zata dinga kula damu amma yakiyin aure,Jiya naji abokinshi yanamishi fada akan ya daina yima kanshi allurar kashe sha'awa tun kamin ta cutar dashi Amma nasan bazai dainaba hajiya kaka ma kullun saitamishi fada Amma yaki ji,Shine sai indingajin hankalina yanatashi wlh. "Eh gaskiya akwai damuwa zahra amma ni sai inga kisameshi kimishi magana mana idan kika nunamishi kinaso yayi aure ai kila yayi nasandai damuwarshi bazata wuce kadda ya auro wadda zata cutar dakuba danhaka ke zaki nunamishi abinda kukeso tunda yanasonku kuma yanajin maganarki ko? Murmushin jin dadi tasaki kamin tace eh hakan yayi nagode sosai wlh insha Allah yau dinnan zanyimishi magana komekenan zuwa gobe idan munzo makaranta sainaimiki bayani nagode jidda. Yarane kusan sa'annin juna wanda shekarunsu bazasu wuce 15-16 ba sabida jidda ta Dan dara ita zahra din dakusan shekara daya amma kuma Kansu daya. K'awancene tun farkon fara karatunsu Wanda har iyayensu sun san da zaman amintarsu. Tsaye suke aharabar makarantar lokacin anata zuwa daukar yaran wasu amotoci wasu amashina,Sukuma suna tsaye har lokacin agefe duk da cewa tuni direban dake daukar jidda yazo amma dayake yasaba ko'ajikinshi hasalima yana zaune cikin mota yanashan rake,Dan yasan indai ba mezuwa daukar su zahran yazoba to jiddan bazata yadda tabishi konan da can ba. " Zahra Dan Allah ki yima yarinyarnan kitso cikin satinnan kalli yanda kitson duk ya zanzare Allah da wuya idan ba k'azanta zakiyiba zuwa nan gaba. Wani uban tsaki zahran taja kamin tace amma kin rainani jidda,Wallahi haka kan Mimi yake duka yaushe dady yaimata wannan din nifa dama kinsan ban iyaba shiko ya iya tunda yanama momee kamin ta rasa nima bejima da dainaminba sabida beso muje ko ina wannan inyamurar ke zuwa tanamin saiya biyata,Itako Mimi kukan tsiya shiyasa yace inbari kawai ya dinga mata amma zan tsefemata anjima tunda babu islamiyya. Da gudu Sadiq da faruk suka shige cikin motar bayan kowa ya mannama dadyn nasu Sumba akunci yayinda Mimi ta saka ihun kuka sabida sunrigata zuwa wajan dady din. Dole yafito daga motar yana dariya tare da daukarta duk zata iya kaiwa shekara biyar amma tsabar gata yasa saikai tunanin bata wuce shekara biyu zuwa ukuba. Gaidashi mukai tare nida zahra sannan ya wuce yasata gaban motar domin dama nan dinne wajan zamanta,Sallama mukai sannan nima na wuce wajan Wanda yazo daukata. So daya ya kalleta ta madubi yaga Sam yau bata da walwala danhaka shima saiyaji hankalinshi yatashi,Shifa behada yaranshi da komaiba na duniya. Kasancewar yau alhamis babu islamiyya shiyasa abincin safe kawai suka girka kamin sutafi danhaka yanzu data huta zatafara Neman abinda zatayimusu kamar yadda tai dadyn ya horata akai. Saidai yau damuwardatake ciki saita saukar mata da kasala Allah yasama tai sallah amakarantar danhaka kawai saita haye gado bayan ta kwabe kayan jikinta. Mimi tashigo dakin da kukanta tana shafa cikinta da alama dai kuka n yunwa takeyi. Harararta tayi kamin tace"To sarkin fitina ai mundawo gidan yanzu zaki hana uban kowa kwanciyar hankali me akaimiki kike kuka? Hawayenta ta share kamin tace yayanmu Abinci zanci ni bansan tea. Harararta tayi kamin tace wuce bani wuri yau banda Lafiya sai zuwa anjima zanyi girki duk uban ciye-ciyen da kikayi dazu amma yanzu Dan kar mutun ya zauna Lafiya zakice yunwa wuce tai wajan dady. Hannunta ya rike suka nufi falo domin dama yana tsaye kofar dakin yana sauraren mesukeyi,Da kanshi ya shiryamusu indomie danshima yunwar yakeji. Saida yaga yaran sun natsu sannan ya yakoma ya jingina da kujera tare da lumshe manyan idanunshi wata irin kewar matarshice ta dabaibaye zuciyarshi jiyake kamar yasaka kuka kozaisami sukunin zuciya. Tashi yai ya nufi dakin zahra Dan beso damuwa tai tasiri cikin zuciyarta da gangar jikinta. Gabadaya ya rungumota jikinshi yanajin zuciyarshi na tsananta bugawa,Bubbuga bayanta yafara kamin yafara magana ahankali cike da lallashi"Bansan damuwa zahra kinfi kowa sanin hakan shiyasa nabaki dama akan komai Wanda yashige miki duhu gayamin menene ya canzaki? Rungumeshi tayi tana kuka"Dady mungaji da ganinka hakanan Dan Allah kayo aure musami wacce zata dinga debemana kewar mahaifiyarmu bazai yiwu ace koda yaushe Kaine komai dinmu ba kaima kana bukatar hutu kamar kowane mahaifi. "Karki damu inshaAllah zanyi matsalar banso in dauko wadda zata zamemana matsala danhaka ki kwantar da hankalinki zanyi aure amma ba yanzu ba idan kuma kinada wacce ta kwantamiki arai to nabaki zabi Zahra. Maman khadija NA maman khadija. Page 2 Tajima cikin halin tunani bayan barinshi cikin d'akin saidai tuni zuciyarta tafara kawo Mata wani kyakykyawan tunani,Wani mayen murmushi tasaki tare DA sakin k'aramin ihu murna fal cikin ranta lallai kakusa angwancewa my dady. Duk da yanajin kamar zai iyayin danasani saidai ya Hana tunanin hakan tasiri cikin zuciyarshi musamman idan yai tunanin cewa yo wa zahra tasani balle hartayi abotar da zata iya bashi YARDA irin wannan shi bumma saiya bashi dariya danhaka tuni ya saki wani lafiyayyen murmushi saman kyakykyawar fuskarshi kai dady fa badai kyau ba. Bayan nakoma gida wanka kawai nayi bataredana nemi abinciba danni abinci bawani damuna yayiba musamman idannacika cikina da cibanza ci wofi amakaranta,Kwasar littattafaina nayi na nufi falo jin muryar Yayana Usman dan shine ke kuma koyamin dukkan abinda akaimana amakaranta matukar yana gida. Kayan dayagama cin abincinakwashe nakai madafa sannan nadawo kusa dashi na lafe Dan Allah yayoni dason jikin masifa. Janyeni yayi daga jikinshi yana hararata"To mage sarkinson jiki waike bakisan kibar mutun ya hutabane? Indai baki tashi daga jikinaba Allah kwallo zantafi yanzu inbarki. Bakina na turo gaba tare da d'an dagamishi jiki kamin in koma dannariga nasaba rayuwa dashi. "Haba Usman waikai Dan Allah meyasa kacika mitar masifane sabida Allah yarinyar nan idanbata rabekaba wa kakeso taje ta raba?Nifa bansan kana takurata da shegiyar mitarka ta gado,Kakarmu hajiya hauwa itace tai wannan maganar tanayi tana watsa hannu Dan ita Sam bata yarda kowaya tabaniba. Be kulataba dan yasan kadantake jira yanzu ta taramishi mutanen dake kofar gida indai akan jidda ne Ina kwance ajikinshi yaimin k'arin bayaninduk karatunan sannan yatashi zai fice,Rikeshi nayi ina kyafula manyan idanuna alamar kuka zan sakarmishi. Waigawa yayi yaga gabadaya hankalin hajiya yana kan labaru datake kallo danhaka saiya koma ya zauna tare da zaunar Dani gefenshi gayamin menene kinji sweet sis? Cikin yanayin muryatadatake me sanyi ga shagwaba nace pls Yayana kaje Dani Dan Allah. Dama yasan fitinar bata wuce ta hakan danhaka saiya rungumeni jikinshi cikin muryar wayau yace yanzu zanje indawo bawani jimawa zanyiba zantaho miki da ice cream me shegen dadi kinji ko Samu yai ya fice yanajin dadi cikin zuciyarshi godiya yake kumayima Allah dayasa berasa kanwarshiba kamar yadda ya rasa iyayenshiba. Washe gari. Can muka hade da zahra wadda yau naganta fayau da ita cikin farinciki sabanin jiya da take cikin damuwa da rashin walwala. Rungume juna mukayi da ita kamar yadda muka Saba sannan sukuma suka gaidani. Saida akaimana break kowa Yakama gabanshi sannan nazaro kular da hajiya ta zubomin dambun nama mukafaraci bayan na dibarma kannen zahra kamar yadda nasaba. "Uhum saiwani murmushi kikeyi har yanzu kinkicemin komai KO dady yasami matar ne? Dan tsaki taja kamin tacemin kinjiki saikace wani Wanda yarasa mashinshini aidama shi dady akwai masu kaunarshi da yawa kawaidai yaki basu dama ne amma jiya munyi magana dashi kuma yabani wuk'a da nama Zan zabamishi matar aure kalar wacce ta dace dashi wadda nasanta nasan halinta sannan na YARDA da ita fiyema da yanda ita ta yarda Dani. Murmushi kawai nayi kamin ince amma naji dadi Allah yasanya alkhairi kinga nima wataran saiki ganni nazo gidanku yini tunda akwai mace amma yanzu danace zanje sai hajiya tace a a wai sai dadynku yayi aure. "Murmushi itama tasaki kamin tace ki kwantar da hankalinki har kwanama zakiyi,Am yau juma'a sonake in nufi wajan hajiyakaka muyi shawara kome kenan zan taboki cikin wayar hajiya kokuma inzo ranar asabar. "To babu damuwa Allah ya kaimu Lafiya. Anan hirar tamu ta tsaya har akatashi bamu tsaya jiraba yau Danni yayana Usman yazo daukata sukuma tuni dama dady na jiransu. "Wannan k'awar taki daga gani itama sarkin rikicice kamar ke ko? Cewar dady,Wanda ke farimciki ganin walwalar yarannashi duka. Dariya tayi sosai kamin tace"Kai dady babu wani rikici damukedashi itakam gatane yai Mata yawa amma kuma bame cutarwaba kasan bata da iyaye duk sun rasu saidai yayanta da kakarta hajiya saikuma sauran dangi kowa yana sonta sunajin tausayinta shiyasa take shagwaba Amma wallahi dady jidda tayi saima ka zauna da ita gashi ta iya girki kamar kamar me kowane iri shiyasa nake kaunarta har cikin raina. "Kuma dady tanasonmu sosai kullun saitabamu abinda dadi dama zata dawo gidanmu,Cewar Mimi wadda ketajan jelar kitsonta. Wani irin murmushine ya kwacema zahra din Wanda har saida dadyn ya kalleta. ********* Da ciwon Mara na isa gida duk da saida muka biya ya Usman ya saimin magani Wanda tun cikin mota yabani nasha Amma tsabar sangarta da kuka nashiga gida. Da sassarfa tafito zaninta ahannu tana salati da sallallami kamin ta Dora da to keda ubanwaye wani shegene yatabaki incimishi uwa? Hajiya kenan iyayen rikici shiyasa nima nake sonta wallahi bata hada soyayyata da komaiba. Jikinta nashige ina shesshekar kuka kamin ince hajiya marata ke ciwofa. Saida ta lissafa kwanakin wata taga daidaine sannan ta furta"Wayyo Allah na sannu wallahi na manta da yaune zuwan abun muje ki wanka saiki kwanta kihuta ai ki kwantar da hankalinki akwai hisabi tsakaninki da wannan ciwon. K'annen mahaifina na tadda zaune afalon sunacin dambu Wanda hajiya tayi abunta da kanta dan itafa har yanzu jinta take garau,Gaidasu nayi sannan nawuce daki yayinda sukabini da albarka kamar yadda suka saba dan sosai suma suke nunamin kulawa. YARDA. Na maman khadija. 3 "Fatima bintu zahra 'yar gidan manzo,Me zaki gayaminne naga bakinki yanata motsi alamar lallai akwai wani bayani dai,Cewar hajiya kaka wadda take mahaifiya ga dady. Murmushi tasaki sannan ta riko hannuwan farar tsohuwar wadda itama idanunta nakan zahra din domin tanason zahra sosai musamman da itama take takwara wajanta. "Kaka alfarma nake nema wajanki dangirman Allah kadda kice bazaki iyaba domin dole kece karfin guiwata kinji kaka? "Karki damu zahra indai har inada dama basaikin hadani da Allah ba insha Allahu bakida matsala Allah yasa alkhairice maganar. Cikin yanayi nakuma marairaicewa domin aji tausayinta tafara magana"Kaka nasan kina iya bakin k'okarinki wajan ganin dady yayi aure tunkamin Mimi ma tai wayau saigashi beda ma alama har zuwa yanzu musamman Dana Lura ko maganar ma beso, Rannan naji abokinshi nayimishi fada akan zai halaka kanshi indai beyi aureba amma sainaji yana gayamishi shifa bazai yadda ya auro wacce zata watsamishi gidaba kinga kenan sabida mu yaki auren,Saidai awashegari naita fushi da damuwa har saida ya tsareni da tambaya shine nace aure mukeso yayi sabida muna buk'atar makwafin uwa sannan yara da yawa kamar yadda kowayasan burinshi kenan Tara yara da yawa,To shinefa yace yabani zabi inje in zabomishi duk wacce nake ganin tadace dashi sannan bazata cutar damuba,To Alfarmar da nake nemadai wajanki itace sonake ki shirya yanzu muje gidan wannan k'awartawa ki ganta idan har tayimiki saimu dawo mufara shirya yanda abubuwan zasu kasance duk da nasan cewa dakyar idan hajiyar zata yadda da shirinmu. Fuskarta cike da farinciki take furta Alhmdulillah amma naji dadi sosai Allah ubangiji ya shigemana gaba insha Allah komai zaizo da sauki indai kin amince da ita Sannan kin YARDA da ita babu matsala saimudage da addua yanzu tashi muje mudawo anshi wayata kiramin babanki tahir ya kaimu dan inaga shine kawai beyin nisa ranar juma'a. **** **** Wando da rigane jikina na fakistan masu laushi tuni sunbi jikina saidan siririn kllabinta Wanda na daure gashinadashi. Wainar fulawa nakeyi hankalina kwance inayi Ina karanto suratul Maryam kamar yadda d'abi'ata take nayin karatu musamman idan aiki nakeyi. Sallamar zahra nadingaji sama-sama saidai banyi tunanin itan bace musamman dayake dazu muka rabu kuma tace kila sai asabar zata shigo wajena tabani labari. Wani uban tsalle na buga lokacinda na tabbatar itace,Nan muka rungume juna muna murna yayinda hajiya batabi ta kanmuba sai sannu da zuwa da takeyima kaka. Cikin mutunci suka gaisa sannan nakawoma kaka lemo da ruwa itadai sai kallona takeyi suna hira da hajiya muko ai cikin dakina muka shige mukafara hira saikace ba Dazu muka rabu ba. "Dallah dazufa da ciwon Mara nashigo gida wallahi damma saida ya usi ya siyomin magani. Dariya tai kamin tace ah kice abun yazo niko wallahi idan zanyi banjin komai saidai kawai inji yanayina ya sauya kuma danaduba sai inganshi. Saida mukasha hirarmu sannan muka koma falo lokacin tuni su hajiya anzama k'awaye duk da dama sunsan juna amma hirar tasu tayau tafi armashi. Jikin hajiya na shige tare da lafewa Ina leken kaka wadda keta dan kallona irin asace dinnan. Shatara ta arziki hajiya ta hadamusu mukai sallama cikin jin dadi bayan hajiya tagama jaddadama kaka cewa itamafa tana nan zuwa. ***** Hummm Ammma gaskiya harkinsa jikina yai sanyi zahra banda abinki yaya dadynku zaiyi da wannan yarinyar danya jagal da ita inagama ai da kadan ta girmeki yo ai duk shiririta gidan naku zai zama KO? "Haba hajiya ya zakice haka dan Allah wallahi jidda babu abinda bata iyaba,Bama wannan ba ku lokacinda akemuku auran ai ko kaimu girma bakuyi,Nidai yanzu kawai temakon da zakimin guda dayane Shine idan nagayama dady zabindanaimishi kawai ki jajirce sai anyi hakan nikuma insha Allah Zan shawo kan ita jidda din. "Uhumm to shikenan Allah yashigemana gaba insha Allah Zan kokarta. Alhamdulillah,Cewar zahra tana lumshe manyan idanunta. YARDA. Na maman khadija. 4 Ranar asabar kwance nake saman cinyar hajiya tana tsefemin kaina yayinda idanuna suke lumshe harwani sauke numfashi nakeyi,Dan wani irin barci ke neman yin awon gabadani duk da nasan ba lallai tabarni inyiba tunda yamma tayi. "Inason kalar gashinki dan irin na mamanki ne lokuta da dama abbanki kan hanata yin kittso wai yafison gashin ahaka'Cewar hajiya. Kuma muskutawa nayi ina murmushi,Dan ba k'aramin dadi nakejiba aduk lokacinda take bani labarin mahaifana. "Uhumm ashedai Abbana dan soyayya ne shima inasonsu DA yawa hajiya nayi kewarsu. Shafa kaina tayi tana hadiye wani kululu daya sakkomata kadda ki damu suna cikin kwanciyar hankali da farinciki kedai ki dage dayimusu addua kinji KO?. "To hajiya. *** *** *** "Zahra ki tsefe kanki ai kitso yau kinji ko? Turo bakinta tayi kamin tace dady tun jiya nakecema zamuyi magana amma ka shareni kumafa nasan kanasane. "Zahra kemafa kin iya rikici hadda na banza gayamin meya faru? Kuma matsawa tayi jikinshi yayinda kirjinta kewani irin matsanancin bugu,Dady dama akan maganar da mukayi dakaine Dan Allah kadda kace a a dady kadda ka juya baya hakanshine farincikinmu. K'ureta yai da manyan idanunshi yana kallonta yayinda zuciyarshi tai wani irin bugawa,Shifa ganewa kowa beyiba Amma wallahi tsoron matan yakeji duk da yanacikin matsanancin buk'atar macen. "Uhumm ina jinki 'yar gidan waye? Kuma Ina kikasanta da har kikai mata YARDAr da zata iya shigowa cikin rayuwarmu? Wani irin numfashi ta sauke tana sadda kanta k'asa Dan sai lokacinne taji wani mugun shakka da zullumin yimai maganar,Dady, Dady jiddace wadda mukeso ta maye gurbin mamarma idan ka amince da hakan. Shiru falon ya dauka nawani lokaci yayinda idanunshi ke kanta yana karantar duk wani motsinta. "Uhumm zahra jidda da yawa cikin garinnan kimin bayaninta da inda take idan naga dacewar hakan sai inyi yanda kikeso ko "Dady Jidda k'awata wadda muke karatu tare nasan ka santa ai? Wata irin zazzafar dariya yasaki wadda tasa gabadaya yaran maido hankalinsu kanshi sunamai kallon mamaki domin dariya ba d'abi'arshi baceba komai zai faru bewuce murmushi. Yatsanshi yasa yana nuna zahran yana dariya saida yayi me isarshi sannan ya sarara,"Nagode zahra KO babu komai yau kinsani nishadi Wanda narasashi tun kamin rasuwar mamanku,Amma inaso kima daina wannan tunanin dama nasan da wuya idan ba shirme zakiyiminba inba hakaba daganace nabaki zabi zahra saikimin maganar wannan danyar yarinyar wadda ko zata girmeki da kadanne? To bama hakaba ni kodacan danake saurayi bantaba sha'awar auran k'aramar yarinyaba mamanki ahekararta sha Tara na aureta lokacin inada ashirin da biyu koda kike ganina haka zahra inada shekaru bawai yaro bane ni, Dan hakamudaina wannan maganar kedai kawai kitayani da addua idan inada rabon kumayin auren to Allah yabani ta gari wacce zatayi daidai da tsarina,Amma ke yanzuma ai abin aimuku dariyane ace mahaifinku ya auri k'ank'anuwar yarinya kamar wannan ko? Ya idasa maganar har lokacin yana dariya mara sauti. Bakinta ta tunzura tare da tashi tabashi waje tuni idanunta sunfara zubar da hawaye Dan takaici. Da kallo yabita fuskarshi cike da murmushi shi abunma mamaki da dariya yabashi kamarshi da auran sa'an diyanshi ai abun aimishi dariyane ma. Ganin yaran natakallonshi har lokacin yasashi watsamusu hannu tare da d'agemusu gira. Duk maida hankulansu sukai akan kallon da sukeyi amma bunu-bunu sun waigo su kalleshi dole yasashi tattare kayan da yake aiki dasu yatashi,Kuma har lokacin murmushin be gushe daga fuskarshiba. K'okarin shigewa bedroom dinshi yakeyi saiga zahra tafito janye da akwati tana kuka. Kirjinshi yaji yai wani irin bugawa Ashe da gaske take,Watsar da takardun hannunshi ya nufeta yana kwace akwatin hannunta,"Ke bansan hauka da rashin hankali gidan ubanwa zakije nifa bansan rashin hankali da Neman fitina Ina zaki? YARDA. 5 Wani irin kuka tasaki me matukar k'arfi Wanda yakuma rudashi balle da sauran yaran suka nufosu ko wanne fuska akwabe alamar kukan zasu taya yayarsu. Rungumeta yayi ajikinshi yanadan buga bayanta alamun lallashi zuciyarshi ta raunana Dan beyi tunanin da gaske takeba. "Kinga ku koma d'aki kidaina wannan kukan zanyi shawara da hajiya kome kenan saimuyi magana amma ni bansan wannan damuwar haba mana fatimana ko so kikeyi duk ki sakamu cikin damuwa? "Girgiza kanta tayi tana kuma sharbe hawaye,Ammafa cikin zuciyarta cike take da farinciki tunda dai magana zataje wajan hajiya to kuma dama sungama tsara komai. Tun shigarshi cikin d'akin zagaye kawai yakeyi tsabar damuwa da tashin hankalin dayake ciki,Yanason farin cikin yaranshi domin beda kamarsu saidai bejin zai iya biyemusu Dan wannan dalilin idan har auran sukeso tayi to gara ya nemi babbar mace ya aura hakan zaifimishi sauki akan auran wannan kwailar yarinyar me shagwabar tsiya. Kayanshi ya canza tare da daukar key din motarshi yabar gidan dole ya sanarma hajiya da maganar nan tunkamin abun yai nisa har rayuka su baci, gara idan fada zaikai zahra din aimata to da sauki akan hakan. *** Zaune muke muna hira nida hajiya sa ya Usman Wanda lokuta da dama nake kiranshi da ya usi,Hankalina kwance NA kalleshi jiya kanacan yawonka zahra tazo da kakarsu hajiya kuma sunjima wlh. "Mirmushi yayi yana shafar suman kanshi tare da kallon hajiya,Aiko bansan zasuzoba Dana tsaya mun gaisa inafatan kinadan shigar dani wajanta Dan gaskiya nida gaske nake indai sunshirya. Hajiya dake rike da haba takama dariya"Lallai yau naga yayan banza kai bazaka iya kai kankaba sai k'anwarka zata tura aiko indai hakane inaga baka da rabo cikin jikinta. "Kai hajiya"Kai hajiya Dan Allah yanzu idan bakinki beda kyau ai shikenan kin kasheni kinyimin baki haba mana,Wallahi Ina sonta da gaske,Kinga auta tashi ki shirya mukai musu ziyara ma. Da gudu na shige dakina na shirya cikin atanfa Riga da siket bawata kwalliya nayiba amma fuskata fes take Dan sosai nakeda baiwar kyau. Wani irin k'amshi nakeyi me kwantar da hankali Dan nifa akwaini dason k'amshi koda yake gadanayi wajan hajiya nima Gefenshi na zauna Ina cewa to yanzu gidansu zamuje ko gidan hajiyarsu sabida ba lallai ataddasu waje dayaba balle yau asabar. "Haba ai kamata yayi ace ko k'ananun waya akwai ahannunku domin ganin junankuma,amma muje gidan kakarsu din kawai idanma basunan saita kiramanasu amma zuwanmu gidansu akwai matsala tunda basu da mahaifiya. *** *** Zaune yake gabanta k'afafunshi atankwashe yana faman jiranta bayan yagama koramata bayanin duk abinda ke faruwa. "Hummmm To ai Ni abinne ya dauremin Kai wallahi kuma wannan abun duk laifinkane babu yanda banyi dakaiba akan kanemi matar aure idan ma ba kaiba kodan yaranka amma alokacin sabida bakason maganar saima ka dauke k'afa da zuwa gidannan saida na nemeka nariga nagamaka yaranka na buk'tar matar da zata zama uwa agaresu tunda kai biris da maganar aigashinan yanzu diyarka taimaka zabi ko? "Umma Dan Allah kice wani Abu nidai kiyi hakuri sabida Allah Ina zankai sa'ar diyata? Bama wannanba wayasan kalar haukan da zasu dingayi cikin gidan bannan Dan wallahi wannan yarinyar tafisu rikici Dan gata yaimata yawa. "Uhumm yanzudai kasa direbanka ya kawomin su zahra din kaikuma ka kiramin yayanku yazo kawai aje gidansu ayi tambaya danni hakan yayimin daidai dama duk Wanda beji bariba ai saiyaji woho. "Kuma marairaicewa yayi yanajin yanakuma shiga wani mugun tashin hankali,Idanunshi ya zubama hajiyar yanajin kamar ya Dora hannu aka yaita sakin ihu kozaisami sukuni. Wayarshi yasa yakira habu Direba sannan ya kira yayanshi din kamar yadda hajiyar ta buk'ata sannan yakoma gefe ya makure saikace almajirin daya rasa abinci. Suna nan zaune zaman shiru lokaci zuwa lokaci hajiyar NA kallon yaron nata tausayinshi takeji sosai,Saidai tanaso yasami nutsuwa shima kamar sauran magidanta tunda yasami shaida kudi basu rudeshiba yafara harkar banza dukda yanada damar hakan saidai gara adauki mataki tunkamin abun yazo yafi karfinshi,Dan sha'awa mugun abuce. Sallamar Alhaji musa tasa dadyn kuma tunzuro baki kamar k'aramin yaro danshima dadyn autane Amma ahaka har yakema wani sherin shagwaba. Dariya Alhajin yayi kamin yace"hajiya meya farune naga autanki nata kumburi kamar fanke yaji yis Dariya tayi sosai kamin tace kaimadai ka fadi waifa ahaka wata yakema sharrin tacika shagwaba alhalin gatashinan alike yana fama da ita,Diyarshice ta nemomishi matar aure shine yazonan zaimin rikicinshi. Gama bayaninta ga Alhaji musa saiga su zahra sun dira gidan,Nanfa Falon ya dauki wani shiru na musamman. Sallamar mu cikin falon takusa dauke numfashin dady Wanda dama yake cike da fargaba musamman ganin har lokacin zahra bata da walwala. YARDA. NA maman khadija. 6 D"aure fuskarshi yayi tamau irin karma arainashi dinnan,Ammafa saiya samu kanshi da kasa dauke idanunshi daga gareni so yake yaga wata alama dazatasa aga dacewar aurena dashi. Tsallen zahra da ihun su faruk yasaka hankalin kowa komawa kanmu rungumeni sukayi muna murna,Akunyace ya usi ya gaidasu sannan nima na gaidasu muka wuce cikin bedroom din hajiya kaka. Tsam yatashi kamin yace hajiya bari injirata waje kamin sugama gaisawa dama wucewa zamuyi nace bari inbiyo mu gaisa ashema su zahran na nan? "Eh fa amma aidakayi zamanka usmanu ai anriga anzama daya ko? "Babu komai hajiya bari injirata waje. Ajiyar zuciya dadyn ya sauke me k'arfi tare da maida hankalinshi kan hajiyar ya kafeta da idanunshi jiyake duk ya muzanta. "Dariya tayi kamin tace"dady me amarya lallai zakasha amarci. Dariya alhaji musa yayi shima kamin yace"To kai Habib menene

Chapter 1 of 4