Share this page
3 / 3
nayi nadamar bijirewa Abiy. Natsani Aswad! Natsane shi!! Tun lokacin da nasan cewa yaketamin mutuncina, soyayyar shi tafi ta daga cikin zuciya ta. Tsanarshi ne kawai tsantsa nakeji acikin raina! Natsane shi Muhibba. [11/09 5:18 pm] ~ Mrs Yerima📚✍🏼: NI DA ASWAD!!!!!!! 1 Writing by Subee Moh'd Gombe Mrs yerima @ GIDAN MARUBUTA📚✍🏼 SHAGALINKU MATA GROUP Page 26 Idanuwanta tadago ta kalli Muhibba! Wanda tunin sun canja launi zuwa ja, sakamakon kukan datayi har tagaji! Tacigaba dacewa!! Muhibba ashe dama abinda Aswad yake bukata kenan agareni! Ashe dama yaudara ta yake yi Muhibba. Zan rungumi Humaid amatsayin miji! Zan kuma dau duk wani wulakancin dazebiyo baya, idan har yasan ban kawo mutuncina gidanshi ba, ashirye nake nad'auki duk wani wulakanci. Amma bazan iyah jure irin hukuncin Abiy ba agareni! Cikin muryar kuka tacigaba dacewa, Muhibba bansan yazanyiba idan har Abiy yasan wannan maganar ba. Cike da rarrashi ta da fa kafadarta tace! Ya'isa haka Hanan, dena kuka! Ki nutsu, kinga yanzu Mama takusa dawowa! Nan makota tashiga. Sundade cikin jimami! Sannan tatemaka matah da ruwan zafi tagasa jikinta, zazzabi ne mezafi ya rufeta! Ayayin da Maman su Muhibba tashigo take tambayar lafiya? Muhibba ce tayima za tace! Zazzabi ne yake damunta, seda Mama tabata magani tare da yimata sannu sannan ta fice. Haka sukayi kokarin rufe wannan al'amarin dayafaru da Hanan atsakanin su! Batare da sun bari wani yajiba. A'BANGAREN ASWAD! Kwance yake cikin jini, tafiyar Hanan keda wuya maigadi yadawo daga aikan da Aswad din yamishi. 'Bangaren nashi yawuce yana kwala kira! Amma shuru, bangaren Mom dayagani abude ne yatabbatar mishi da Aswad yana can! Domin Key's din bangaren ahannun shi yake. Hakan ne yasa shi wuce wa ayayin da yaketa faman kwala sallama! Amma kuma shuru. 'Karar wayar dayajine yatabbatar mishi da Aswad yananan! Yadad'e atsaye yana kwala sallama, amma babu alamar shi. Hakan ne yasaka shi le'kawa d'akin! Ganin shi kwance cikin jini ne ya'karasa cikin sauri. Be 'bata lokaci ba yawuce da shi asibitin medical center! Cikin gaggawa aka shiga da shi (emergency). [12/09 5:08 am] ~ Mrs Yerima📚✍🏼: NI DA ASWAD!!!!!!! 1 Writing by Subee Moh'd Gombe Mrs yerima @ GIDAN MARUBUTA📚✍🏼& SHAGALINKU MATA GROUP Page 27 Baba maigadi ne yakira wayar Dad yasanar da shi! Cikin hanzari Dad yanemi flight me zuwa Yobe aranar. Anyi saah yakuma samu! Saboda hakane suka baro birnin tarayya Abuja tun karfe biyar na yammah (5:00pm) Mom kam se sambatu takeyi! Ma'kiya zasu kashe matah son d'inta, isowar su kedawuya Dr yafito yasanar da su babu watah matsala! Buguwa ce yasamu akanshi, amma yadan samu bacci! Idan yafarka kuna'iyah ganinshi, sannan hankalin su yad'an kwanta. Befi 40 minutes ba nurse tasanar da su ya tashi! Hakan ne yasakasu shiga gabadayan su domin su gan shi. Dad ne kalli baba maigadi yace! Malam mansur wai meke faruwa ne? Wallahi Alhaji nima acikin wannan halin nashiga natadda shi! Malam mansur din yace. Ayayin da Dad din kuwa yamaida kallon shi kan Aswad dake kwance yace! Son meyafaru ne? Mom ce takatse shi dacewa! Haba Alhaji ka barshi mana yad'an huta, inaganin da zefi ay. Tambayar tazo mishi abazata! Amma kuma dole yasan abin cewa, domin bayason iyayen nashi su fahimci akwai wani abun da yake 'boyewa. Ganin gabadaya hankalin iyayen nashi nakanshi ne yafara magana! Dad bayan aiki baba maigadi ne zuwa Mujaheed plaza, kamin yadawo wasu mutane dabansan ko suwaye ba ne suka shigo gidan. Alokacin danagansu nayi 'bangaren Mom domin neman tsira! Amma kamin na rufe 'kofa sunfarmini!!!!!!! Mom ce takatseshi da salati tare dafad'in! Son ma'kiya ne kawai, Allah de yatsaremin kai. Dad yace! Zaka'iya gane ko d'aya daga cikinsu? Aah! Dad aysun rufe fuskar su yace, toh Allah yakiyaye! Se kadinga kula sosai, zanyi kokari nasanar da jamian tsaro. Ahaka Dr yashigo yatarar da su! Sannan yabasu sallama sukawuce gida. Haka Aswad yacigaba da jin'yar raunin da ke kanshi batare da iyayen shi sunsan aynihin gaskiyar abinda yafaru da shi ba. BAYAN KWANA BIYU! Gasar karatun da su ka sa agabane sukafara, sede kuma dakyar takeyi! Sakamakon damuwar dake tare da ita, ga kuma rashin walwala. Bayan sunkammala gasar karatun ne kuma sukafara jarabawar su ta kammala secondary (WAEC da NECO) Shima de dakyar ta'iyayin shi! Ita kanta Muhibba cike take da damuwa, ganin irin halin da aminiyar tatah keciki! Dakuma rashin walwalar natah. [12/09 7:07 am] ~ Mrs Yerima📚✍🏼: NI DA ASWAD!!!!!!!! 1 Writing by Subee Moh'd Gombe Mrs yerima @ GIDAN MARUBUTA📚✍🏼& SHAGALINKU MATA GROUP Note Kuna raina yan'uwana rabin Jiki! Wannan shafin nakune, Aunty Adiyya da Sis Mami inakewarku cikin Umma. Page 28 Yau tun da wuri tawuce parlourn mahaifin natah! Domin ba wa iyayen natah hakuri, duk dacewar basa ansa ko da gaisuwar ta. Kusa da Abiy ta'karasa tare da dur'kusawa agaban shi! Cike da ladabi tafarayin magana. Abiy don Allah kayi hakuri kuyafeni! Nasan nayi kuskure nabijire muku danayi, kayi hakuri Abiy! Zan kar'bi duk wanda kaza'bamin amatsayin miji. Kukane ya ku'buce matah! Ayayin datacigaba da magana, tadad'e tana kuka mefitar da sauti. Sannan yace! Ya'isa haka nan Hanan, dena kukan! Nayafe miki, Allah yamiki albarka. Ba ma itaba! Hatta Mamna dake zaune agyefen su taji dad'in hakan, domin bijirewar Hanan din ga Abiy dinta tamkar wani abin kun'ya ne agareta! ganin yanda yake matukar ji da d'iyar tatah, tamkar ita kadai ya aifa. Tun da ga wannan lokacin iyayen natah suka sauko daga fushin da sukeyi da ita! Hakan yad'an dawo matah da kulawar iyayen natah atare da ita, sede kuma damuwa da rad'ad'in abinda Aswad yamata dake matukar damunta. A'BANGAREN ASWAD KUWA! Tunin yarufe shafin Hanan acikin rayuwar shi! Hakan yasa besake bin takan taba, sede kuma aduk lokacin da ya tuna abinda yashiga tsakanin su da itah yakan tsinci kanshi acikin sha'awar ta. Batare da amincewar shi ba Dad yasamamishi aiki acan garin Abuja! Cos shide har yanzu ba ya ra'ayin aikin gvrty, domin shi gani yakeyi kamar wahalar da kanshi kawai zeyi! Tunda babu wani abinda yake nema yarasa najin dad'in rayuwar shi. Dad'i da 'kari kuma kudi yana shigomar akowane lokaci! Wannan dalilin yasa shi barin garin Yobe zuwa birnin tarayya Abuja. Batare da sonranshi ba! Sede aduk 'karshen mako yakan biyo flight yazo Yobe domin ganin iyayen na shi. [12/09 8:27 am] ~ Mrs Yerima📚✍🏼: NI DA ASWAD!!!!!!! 1 Writing by Subee Moh'd Gombe Mrs yerima @ GIDAN MARUBUTA📚✍🏼& SHAGALINKU MATA GROUP Page 29 BAYAN MAKO 'DAYA! Sati d'aya kacal yasaura ad'aura auren ta da Humaid, kwance take akan makeken gadonta. Banda sa'kar zuci babu abinda takeyi! Ayayin da adaya 'bangaren kuwa zuciyar ta take cike da fargaba na auren natah, ban da kuma tarun nadama da danasanin datakeyi. Wayar da Humaid d'in yabata tun kwanakin baya tad'auko! Kasancewar bata ta'ba bud'etaba. Wayace kirar SAMSUNG J1 GALAXY! mekyau da tsada irin kuma wacce ake yayi. Sa'kon text message ne sukafara shigowa na kalaman soyayya ayayin datah bud'e wayar. Befi yan' minutes ba kuma call yashigo (kira)! Tadad'e tana ringing ('kara) batare datah daukaba har takatse. Wani kiran ne kuma yasake shigowa! Wanda hakan yasakata d'auka batare datayi magana ba, cos tasan babu wanda zekirata idan ba Humaid ba. Jin batayi magana ba ne ad'aya 'bangaren yace! ranki shi dad'e kina lafiya? Lafiya kawai tace batare datasake cewa komai ba! Domin itade yanzu magana ma wahala takebata. Jin tayi shuru yacigaba dacewa! Hanan har yanzu ba ki hakura ba, haba Hanan! Menayimi ki ne da baraki soniba, dazakiyi hakuri ki kar'be ni amatsayin miji danafi kowa farin ciki da hakan. Cikin nutsuwa yacigaba da magana! Hanan bansan yanda yanda zan misalta soyayyar ki agareni ba, domin ina miki son" da kowace mace ke burin samun wanda zesota kamar haka. Hanan kizo gareni kiga irin tanadi da kuma soyayyar da namiki acikin gidana! Tun da nad'ora idanuwa na akanki naji babu wacce nakeso se ke Hanan. Cike da yanayi irin ta kauna yacigaba dacewa! Inasonki Hanan, ina matukar kaunar ki! Please Hanan say u love me ko zansamu nutsuwa acikin zuciya ta. Ajiyar zuciya kawai tayi! Domin yanzu itade tagaji da jin irin makamantan wa'yan nan kalaman, asalima yanzu tatsani duk watah kalma ta soyayya. [12/09 9:35 pm] ~ Mrs Yerima📚✍🏼: NI DA ASWAD!!!!!!! 1 Writing by Subee Moh'd Gombe Mrs yerima @ GIDAN MARUBUTA📚✍🏼& SHAGALINKU MATA GROUP Page 30 Wai shin Humaid din nan besan cewa nakar'beshi ba ne kawai amatsayin'kaddara ba tace acikin ranta! Sannan tabude bakin ta dakyar tace, Humaid kayi hakuri zan kwanta! Sannan kuma kar kadamu dase ka kira ni, saboda haka base ka kira ni ba! Domin ba na bu'katar hakan. Batare databari yasake magana ba takatse wayar! Dole yasa shi ajiye wayar, kasancewar dare yad'an fa ra ta kwanta! Duk dacewar babu wani bacci a idanuwanta. Ayayin da shi kuwa yake ta faman juyi akan gadon shi! Tunanin ta kawai yakeyi. Ranar da yafara ganin ta yake tunawa! Wani sanyayen murmushi yakeyi tamkar tana gaban shi, don jin dad'in tunanin da yake! Ahaka bacci yayi awun gabada shi. WASHE GARI! Gari nawayewa text message din shine yafara shigowa kamar haka, hello my Darling! Hw ws d 9t? Hp u hd a 9ce drm! Ayayin da wani kuma yasake shigowa kamar haka. Rabin raina jiya tunanin ki yahanani sakat! Ina ishiruwar ganinki sosai, Kodayake idan nayi hakuri kwanaki biyar ne kawai yarage akawomin ke amatsayin matata! Allah yanuna min wannan ranar dazan ganni tare da ke amatsayin mallakina, zan faranta miki rai Hanan sosai. Ajiyar zuciya tayi tanagama karantawa! Ayayin da abinda Aswad yamatah yadawo cikin ranta. Cikin muryar kuka tafara magana! Tamkar wacce ta zare, Humaid da'ace kasan abinda yafaru da ni nasan da barakace haka akaina ba. Nasan dakasan matsayina ayanzu da baraka dinga d'okina ba! Kukane yadawo matah sa bo, tamkar yau ne yafaru da ita! Se datayi me 'isarta sannan tayi shuru. [13/09 3:42 pm] ~ Mrs Yerima📚✍🏼: NI DA ASWAD!!!!!!! 1 Writing by Subee Moh'd Gombe Mrs yerima @ GIDAN MARUBUTA📚✍🏼& SHAGALINKU MATA GROUP Page 31 BAYAN KWANA BIYU! Yau tunda natashi nakejin jikina babu dad'i, ga wani matsanancin zazzabi da ya rufe ni. Aman danakeyi kuwa har nafara fita hayyacina! Hakan yasa nakasa fitowa koda gaida su Mamna. Jin shurun yayi yawa ne yasa Aunty Maryam le'kowa d'akina! Halin dataganni acikine yasakata fita cikin sauri tasanar da Mamna, sannan takira Abiy awaya tasanar da shi. Batare da 'bata lokaci ba ya'iso tare da likitanshi Dr Hilal. Su na shigowa yaduba ni tare da yan'tambayoyi! Sannan kuma yace naje nakawo fitsarina. Datemakawar Aunty Maryam natashi! Domin jikina babu wani 'karfi, saboda aman da naketa famanyi tun safe. Da'alama begamsu da sakamakon ba! Se kuma yad'auki jinina yafita, bayan yad'auramin ruwa. Hankalin Abiy duk ya tashi! Ganin yanda nazama awuni d'aya, se kuma tausayina yakamashi. Hakan yasakashi ka sa fita ko'ina! Yazauna yanata faman rarrashi na tare da yan'nasihohi, domin hankali na ya kwanta! Seda yaga bacci yad'auke ni ne sannan yafice. A'BANGAREN HUMAID KUWA! Bayida wani tunanin da yawuce na Hanan, duk dacewar ba ya ganin ta! Amma kuma gabadaya hankalin shi yana kanta. Sede dolene yayi hakuri har ranar auren nasu! Kamar yanda Abiy yace da shi. Idanuwanshi kyakykyawar fuskar nan natah suke hango mishi! Ga shi kuma cike yake da zumud'in amaryar shi takusa zuwa. Hakan yasashi cigaba dayin duk wani shirye-shiryen shi! Don ganin yaburgyeta. Hatta kayan aure (lefe) a'kasar nan ta daular larabawa yasa akasiyomishi su! Yakashe kudi kam sosai, abinka da man'yan yara. Sede Abiy yace bayason Al'adar nan! Ya'ajiye idan ankawo mishi matarshi yabata kayan. Su ma su Abba su na matukar ji da wannan aure! Kasancewar Humaid shikadaine d'ansu namiji. Humaid kam tunin har yagaiyaci abokan shi! Har ma da na 'kasashen waje duk yatura musu da gayyata. [13/09 4:59 pm] ~ Mrs Yerima📚✍🏼: NI DA ASWAD!!!!!!! 1 Writing by Subee Moh'd Gombe Mrs yerima @ GIDAN MARUBUTA📚✍🏼 SHAGALINKU MATA GROUP Page 32 Sau'kar belt d'in danajine ajikina yasani tashi agigice daga baccin danake. Abiy ne ri'ke da belt yana huci! A'iyasanina ban ta'ba ganin Abiy acikin irin wannan'bacin ran ba! Yanayin shi yayi matukar ba ni tsoro. Haka yacigaba da dukana! Tun ina ihu har se danakasa, kasancewar ya rufe kofar d'akin ne yasa Aunty Maryam bugawa! Domin ta'kwace ni, amma ko sauraron ta bayayi. Haka yacigaba da dukana se da yaga nadena motsi sannan yafice. ABUJA! Aswad ne rungume da ester akan d'aya daga cikin kujerun dake 'kayatatcen parlourn gidan nashi. Wasannin su kawai sukeyi! Seda hankalin su yakai'kololuwa da tashi sannan su ka afka wa junansu. Sun murji junansu sonransu! Kafin subaje kuma su na kwasar bacci anan. WAYE ESTER! Tunda Aswad yazo Abuja sukahadu da ester! Asalin ta mutuniyar minna ce, jihar Niger! Yawonta ne (bariki) yakawota cikin birnin tarayya Abuja. Tunda sukafara mu'amalarsu ta ashsha da Aswad taji tana sonshi! Wannan yasakata d'aukar aniya naraba shi da duk watah ya'macen datah ra'beshi. Tun daga wannan lokacin kuwa yazamana Aswad nabiye da itah! Tamkar ra'kumi da akala. Hakan yabata damar juyashi yanda takeso! Sede kuma abinda yafi damun Aswad d'in shine, yanda yanzu tadawo gidan nashi gabadaya da zama. Wannan yasakashi ko dayaushe cikin fargaba da kuma kaffa-kaffa! Aduk lokacin da su Dad su ka sanar da shi su na han'ya. Haka yacigaba da zama agidan nashi tare da ester tamkar wasu ma'aurata. [13/09 5:25 pm] ~ Mrs Yerima📚✍🏼: NI DA ASWAD!!!!!!! 1 Writing by Subee Moh'd Gombe Mrs yerima @ GIDAN MARUBUTA📚✍🏼& SHAGALINKU MATA GROUP Page 33 YOBE! 'Karar fankar dake juyawa ne ad'akin yasakata bud'e ido! Aunty Maryam ce zaune agyefen ta, cikin hanzari tataso tare dayimatah sannu. Cike da kulawa tatemaka matah tatashi ta zauna! Abinda yafaru ne yadawo matah, ayayin da 'kwalla su ka cika matah ido. Cike da yanayi irinna damuwa tamaida kallon ta ga Aunty Maryam wacce itama kallonta take. Cikin sha'ka'k'ken murya tace! Aunty meke faruwa da ni ne? Kai kawai tad'aga matah! Alamun aah, kuka ne yasubuce matah! Ayayin datacigaba dacewa, Aunty kifada min! Meke faruwa da ni?? Please Aunty. Naga Abiyna acikin halin da ban ta'ba ganin shi ba! Abiyna beta'ba dukana ba, se ga shi yau yamin duka irin wanda ban ta'ba gani yayi ba. Cikin muryar kuka tacigaba dacewa! Don Allah Aunty ki gayamin ko hankali na ze kwanta, please Aunty!!! Kuka tacigaba dayi! Irin mefitar da sauti, ayayin da Aunty Maryam tadafa kafadarta tafara magana. Hanan bansan ta inda zanfaraba! Domin mun shiga tashin hankali, irin wanda bamutaba shiganshi ba. Ko atarihin zuriyarmu kaf Hanan babu wanda yataba aikata irin abunda kika aikata. Cike da rud'ani tad'ago ta kalli Aunty Maryam! Cikin kuka tace, shikenan Aunty! Abiyna yasaniko? Itama Aunty Maryam d'in kallon ta takeyi! Ayayin datacigaba dacewa, Aunty kigayamin meyake faruwa da ni ne??? Kafadarta tadafa ayayin da tafara yin magana! Hanan bansan ta'ina zanfaraba, Kodayake anason duk wani mumini yazama me rungumar 'kaddara aduk san dataris ke shi. [13/09 9:03 pm] ~ Mrs Yerima📚✍🏼: NI DA ASWAD!!!!!!! 1 Writing by Subee Moh'd Gombe Mrs yerima @ GIDAN MARUBUTA📚✍🏼 SHAGALINKU MATA GROUP Page 34 Ajiyar zuciya tayi mecike da jimami! Sannan tacigaba dacewa, Hanan alokacin da naga Abiy d'in ku yabude d'akin ki yafito ne hakan yabani damar shiga cikin hanzari. Ganin ki danayi cikin jini yayi matukar tayarmin da hankali! Azatona ma babu rai atare da ke, cos ayanda nasame ki. Cikin hanzari nabi bayan shi ina ro'ko domin yakai ki asibiti! Amma fir ya'ki, hakan yasani kiran Dr Hilal yadawo! Cikin gaggawa mukawuce da ke asibitin shi(emergency) Bayan muntaho asibiti ne Mamna taga sakamakon da Dr Hilal yakawo wa Abiy din ku! Wanda hakan yayi sanadiyyar tashin hawan jininta nan take. Cikin tashin hankali Abiy din ku yataho da ita Hilal clinic! Tunda Aunty Maryam tafara magana banda kuka babu abinda take. Kuka take iya karfin ta! Hanan test d'in farko yanuna kina dauke da ciki har na kusan watanni biyu. Cikin yanayin damuwa tacigaba dacewa! Shi kan shi Dr Hilal yayi mamakin ganin hakan, wannan yasa besanar damuba har se da yad'au jininki. Sede anmiki wankin ciki! Saboda cikin da yafara fita (zubewa), sakamakon dukan da Abiy din ku yayi miki. Hanan ya'akayi kika aikata wannan d'an'yen aiki! Ayayin datakarasa maganar ta dacewa, Abiy din ku yayi matukar ba'kin ciki. Hanan munyi ba'kin ciki da irin wannan d'an'yen aiki da kika aikata! Hanan meyisa kika aikata haka? Haba Hanan ba halin ki bane wannan! Nariga nasan waye Hanan, nasan bazaki ta'ba aikata irin wannan aikin ba Hanan! Amma meyisa, ya'akayi haka tafaru Hanan??? Cike da tausayawa tacigaba da magana! Abiy din ku yana matukar fushi da ke Hanan, nayi 'ko'kari domin naga nashawo kan shi amma abin yaci tura. Kwata-kwata ya'ki saurarana! Wallahi tun da nake da shi banta'ba ganin 'bacin ranshi da tashin hankali irin haka ba. Yamaba ni lokaci nayi magana da shi sam ya'ki! Gabadaya yanuna min idan ma maganar ki ne tohfa bayaso. [13/09 9:46 pm] ~ Mrs Yerima📚✍🏼: NI DA ASWAD!!!!!!! 1 Writing by Subee Moh'd Gombe Mrs yerima @ GIDAN MARUBUTA📚✍🏼& SHAGALINKU MATA GROUP Page 35-40 Yacuce ni Aunty tace cikin kuka! Aswad yaci amanata!! Ya yaudare ni da soyayyar shi, shikenan yanzu ko Aunty yagama da ni. Ayayin da wani sabon kuka yasake ku'buce matah! Ya'isa haka Hanan dena kukan Aunty Maryam tace, tare da jawota jikinta cike da tausayawa. Kaitadago takalli Aunty Maryam tace! Dolene nayi kuka, dolene nayi kuka me cike da tarun ba'kin ciki. Cikin shashshe'kar kuka tacigaba dacewa! Yau kwanaki hudu kacal yaragye ad'aura min aure da Humaid, tabbas Aswad kacuce ni! Kamin illar da bazan ta'ba mantawa ba, katarwatsamin rayuwa ta. Hawaye ne mecike da takaici yacigaba da kwaran'ya afuskarta! Ayayin datah maida kallon ta ga Aunty Maryam tacigaba dacewa, shikenan Aunty banida wani sauran kima 'a'idon duk wani wanda yazama miji agareni yanzu! Domin yazubarmin da mutuncina. Tohma wai shin yanzu awane matsayi Humaid d'in zed'aukeni Aunty? Tabbas baze ta'ba d'aukata da daraja ba Aunty! Domin yanzu ba ni da watah daraja!!!!!! Kuka ne yaci'karfinta maifitar da sauti wanda yahanataci gaba da magana. ALHAMDULILLAH!!! MUHA'DU ALITTAFI NA BIYU (2) MASU KARATU! Masu karatu ina matukar Jinjina muku! dafatan alkhairi aduk inda kuke, ina ganin sa'kon ninku! Nagode sosai, musamman wanda suke Nigeria, Nijar, Sudan da kuma Cairo! Allah yabar kauna. GAISUWA TA MUSAMMAN! Gaisuwa ta musamman gareku yan'uwana! Dafatan kunacikin koshin lafiya da iyalan ku Sister Mami Sister Fa'iza Sister Haseena Sister Haleema Sister Hauwa'u LOKACIN RUBUTU📚✍🏼 From 16/8/2017 13/9/2017 to An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://thausanovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.thausanovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 3 of 3