An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://thausanovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.thausanovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
[16/08 1:17 pm] ~ Mrs Yerima📚✍🏼: NI DA ASWAD!!!!!!!
1
Writing by
Subee Moh'd Gombe👩🏻💻
Mrs yerima
@Admin
SHAGALINKU MATA GROUP📚✍🏼
SUBEEASLAM GROUP📚✍🏼
GODIYA:
Godiya ta tabbata ga Allah subahanahu wa ta'ala! Tsira da aminchin Allah sutabbata ga fiyeyyen halittu annabi Mohammad S.A.W da sahabbanshi da iyalenshi.
FATAN ALKHAIRI:
Fatan alkhairi gareku iyayena! Allah yasaka muku da mafificin alkhairi amin.
JINJINA:
Jinjina gareka rabin raina! Mijina'uban ya'yana AD yerima Allah ya barmu tare! Ya kuma karemu daga sharrin mahassada.
GARGADI:
Ba'ayarda wani ko wata yacanja wani'abu daga cikin wannan littafinba! Seda 'izinin marubuciyar arubuce, AKIYAYE.
SADAUKARWA:
Nasadaukar da wannan littafin nawa mesuna NI DA ASWAD!!! wa 'iyalaina.
KUNA RAINA:
Kuna raina ya'yana! Allah ya albarkace ku da duk kan yan'uwa musulmai, Allah ya raya mana ku bisa koyarwar annabi S.A.W amin
Najwa
Safwan
Muhseen
Jawaheer
GAISUWA TA MUSAMMAN:
Gaisuwa ta musamman gareku aminaina
Hajiya Suwaiba Sudan (Maman Siyama) da
Aishatu Haruna Gombe (Maman Na'ima) da
Zuwaira Abubakar Gombe (Maman Ihsan) da
Hajiya Rukayya Saudia (Ummu Najeef) ban manta dakeba Hajiya Zahra Cairo Allah yabar zumunci amin.
YAN'UWA RABIN JIKI
Yan'uwa rabin Jiki! Allah ya bar xumunci amin
Sis Mami da
Aunty Adiyya
Page 1
DASUNAN ALLAH MAI RAHMA MAIJIN KAI!
Malam Abideen Saaleef babban malamine na islama kuma sananne acikin garin Yobe! Asalinshi mutumin Yobe ne, acikin 'karamar hukumar fataskum.
Haka kuma cikakken Arab ne tare da matarshi Halmata! Malam Abideen da Halmata auren soyayya sukayi, sede kuma tsawon shekaru shida Allah be basu haihuwa ba.
Wannan yasa yan'uwanshi matsamishi dole ya'kara auren yar'uwarshi Maryam! Duk dacewar beso hakan ba, domin shide yana matukar kaunar matarshi! Kuma suna zaman su lafiya cikin rufin asiri.
Allah da ikonshi cikin shekarar daya auri Maryam ne Halmata tasamu ciki! Murna awajen malam Abideen ba'a magana.
BAYAN WATANNI TARA:Halmata ta haifo yar'ta kyakykyawar gaske! Wacce taci suna Hanan, Hanan ta taso cikin gata tare da kulawar iyayenta! Shekarunta biyu Halmata tasake haihuwa, awannan karon namiji ta aifa kha'af! Bayan kuma shekaru biyu tasake aifar khuhail.
[16/08 3:26 pm] ~ Mrs Yerima📚✍🏼: NI DA ASWAD!!!!!!!
1
Writing by
Subee Moh'd Gombe
Mrs yerima🌹
@Admin
SHAGALINKU MATA GROUP📚✍🏼
SUBEEASLAM GROUP📚✍🏼
Page 2
Awannan lokacin kuma tare da Maryam suka aihu! Ita Maryam ta aifi Khadija, itade Halmata tun daga kan khuhail bata sake haihuwa ba.
Ayayin da Maryam tasake haihuwar Rukayya da kuma Hajara! Haka gida yacigaba da ciki cikin ikon Allah.
Haka Halmata da Maryam sukacigaba da rayuwar su cikin jin dadi da kwanciyar hankali! Tare kuma da fahimtar Junansu, inba an gayamaba kace yan'uwane najini.
BAYAN SHEKARU SHA BAKWAI:Matashiyace wacce barata wuce shekaru goma sha bakwai ba! Cikin sauri tafito sanye da uniform dinta na islamiyya, kasancewar tadan makara.
Kitchen ta tarar da mahaifiyar tatah! Cikin sanyin muryar ta tace da mahaifiyar tatah, Mamna nashirya zan tafi, Allah ya bada saah mahaifiyar tatah tace! Wacce suke kira Mamna, ayayin datah fice tana fadin amin.
Gidansu aminiyar tatah tawuce! Ganin babu kowa atsakar gidanne yasakata wucewa d'akin aminiyar tatah kaitsaye.
Da'alama wanka take! Hakan yasakata neman wuri ta zauna tana jiran fitowarta, harara tasakar matah ayayin datah fito.
Ganin tana nema ta'bata matah shirin natah! Sannan tace, ammade Muhibba kinsan munyi da ASWAD d'ina zamu had'u yau! Cos kusan kwanaki biyar kenan bamu had'u ba.
Kasancewar babu makaranta! Gashi kuma yanzu har 'ankusa shiga aji.
[16/08 3:49 pm] ~ Mrs Yerima📚✍🏼: NI DA ASWAD!!!!!!!
1
Writing by
Subee Moh'd Gombe
Mrs yerima🌹
@Admin
SHAGALINKU MATA GROUP📚✍🏼
SUBEEASLAM GROUP📚✍🏼
Page 3
Ayya Hanan kiyi hakuri mana! Mama ce tasakani aiki, se yanzu nasamu na kammala! Kinsan sunjesu biki tace, ayayin da take saka natah uniform d'in 'agurguje! Sannan su ka fice.
HANAN yarin'yace mai matukar kyau da kwarjini! Kallo d'aya zakayi matah kasan hakan, cos kyanta irin bayyanen nen kyawune.
Hanan irin fararen shuwa Arab ne na asali! Wanda kuma ba su bar komai ba, tana da dara-daran 'ido masu d'aukan hankali! Wanda ako da yaushe idan takalleka kace bacci takeji.
Tana da tsawo mai tsari kuma marar Jiki ce! Saide kuma tana da shape mai daukar hankali, 'kirar jikinta irin wanda ake kirane da coca cola shape! Cos bata da wani Jiki se shape.
Tana kuma da yalwar gashi akanta mai tsawo irin na shuwa Arab! Tsayawa fad'in kyawunta'bata lokaci ne, cos kyanta ya kai matuka.
Hanan yarin'ya ce mai basira da saurin fahimta sosai! Gatah kuma gifted ce, irin wanda turawa suke kwatance.
Tun tana da shekaru shida ta sauke al'kur'ani mai girma! Ganin irin basirartane yasa Abiy (mahaifinta) d'inta d'ora buri akanta, nason yaga tayi karatun boko dana addini me zurfi! Akan kuma duk 'bangaren datake ra'ayi akai.
[17/08 2:24 pm] ~ Mrs Yerima📚✍🏼: NI DA ASWAD!!!!!!!
1
Writing by
Subee Moh'd Gombe
Mrs yerima🌹
@Admin
SHAGALINKU MATA GROUP📚✍🏼
SUBEEASLAM GROUP📚✍🏼
Page 4
Layin daze kaisu unguwar G.R.A sukabi! basuyi wani tafiya mai nisaba, kasancewar babu nisa sosai daga nasu area din.
Bayan wani 'kayatatcen gida suka tsaya! Waige-waige takeyi ko zata hango masoyin natah, ayayin da Muhibba kuwa ke faman duba agogon dake manne ahannunta duk bayan yan'mintoti (minutes).
Sun dad'e ahaka babu alamarshi! Cikin kosawa Muhibba tace Hanan yakamatafa muwuce kinga harmun makara, don yanzu haka malam yashiga aji.
Cike da alamu irin na damuwa tace! Naso ace daga yau munkawo 'karshen wannan al'amarin NI DA ASWAD!!! Cos azahiri nagaji da zuwa area din su, ga shi kullum mune cikin latti! ga fargaba dake damuna.
Ina tsoro wani yaganmu yasanar da Abiy! Ajiyar zuciya tayi ta kalli aminiyar tatah sannan tacigaba dacewa, Muhibba bansan ya'akayi ASWAD yamin haka ba! bayan yamin alkawarin samamana mafita, ayayin da ta karasa maganar ta dacewa mutafi kawai Muhibba.
Han'yar su tawucewa islamiyya sukayi! Tafiya suke cikin nutsuwa ayayin da take ta faman sake sake acikin zuciyar ta, wani kyakykyawan saurayi ne yasha gabansu, wanda baze yuce shekaru ashirin da bakwai da haihuwa ba.
[18/08 10:09 am] ~ Mrs Yerima📚✍🏼: NI DA ASWAD!!!!!!!
1
Writing by
Subee Moh'd Gombe
Mrs yerima🌹
@Admin
SHAGALINKU MATA GROUP📚✍🏼
SUBEEASLAM GROUP📚✍🏼
Page 5
Fari ne Sol! dogo mai dara-daran idanuwa, dogon hancinshi wanda yayi matukar 'karamishi kyau! Cikin hanzari yasha gaban Hanan yana murmushi.
Yanayi irin ta shagwaba tace! Haba ASWAD kasamunyi latti fa, kunnenshi yakama yace! I'm so sorry my beauty, Muhibba ce takatsesu dacewa gaskiya ASWAD yaude kasamunyi lattin dabamu ta'bayin irin shiba.
Cike da zolaya HANAN tace! Sis kibarni da shi kawai ay na'iyayin displine, dariya sukayi gabadayan su! ASWAD yace, amini afwa ranki ya dad'e, amma de kar 'asake tace! angama ranki ya dade yasake cewa yanayi irin ta zolaya, wanda hakan ya'kara bata dariya har se da dimples dinta yadan lotsa.
Tace ASWAD muyi magana agurguje domin muje mu mubada hadda! Itade Muhibba kallonsu kawai takeyi, duk dacewar wani lokacin sunabata haushi! amma kuma sukam burgeta! ayanda suke nunawa junansu kulawa irin ta masoya.
Sun dan taba yar'hira! Sannan yafito da waya yabata! Wayace kirar tecno mekyau, yace my beauty zamu dinga yin waya yanzu! Idan kuma munason ganin junanmu zamusan yanda za'ayi.
Cike da fara'arta tayi mishi godiya! Sannan sukayi sallama sukawuce, tayi matukar jin dadin wayar da yabata! Cos yanzu zata dinga jin muryar masoyinta ako da yaushe, saboda hakane tadau niyyar boye wayar batare da wani yasan metake cikiba.
[18/08 10:33 am] ~ Mrs Yerima📚✍🏼: NI DA ASWAD!!!!!!!
1
Writing by
Subee Moh'd Gombe
Mrs yerima🌹
@Admin
SHAGALINKU MATA GROUP📚✍🏼
SUBEEASLAM GROUP📚✍🏼
Page 6
Haka soyayyarsu tacigaba da tafiya batare da iyayen su sunsaniba! Haka kuma akowane dare sunayin waya(night call), idan kuma zataje makaranta su kan haduwa ne akan han'ya domin suga junansu.
Duk da soyayyar ASWAD dake cikin zuciyar HANAN! amma hakan beshafi bangaren karatunta ba, cos HANAN yarin'ya ce mai hazaka da kuma kwazo! Wannan yasa take dad'a shiga ran Abiy d'inta (mahaifinta).
Ilimin islama kuwa tana kan samunshi! Domin Abiy yana koyaddasu sauran littattafan addini, wannan yasa take kara wuce abokan karatunta ako da yaushe.
Zaune suke tare da aminiyar tatah! Hirarsu sukeyi irin na aminan juna, Muhibba aminiyace awajen Hanan! Sun shaku da junansu sosai, wanda adalilinsu abotan iyayen su takullu! Itama Muhibba tana da tarbiyya sosai, haka kuma tasamu ilimin addini mai zurfi itama kamar Hanan din.
Asalinsu mutanen damaturu ne! Idanuwanta masu daukan hankali ta zuba matah, ayayin datah dawo kusa da ita ta zauna! Sannan tace, Muhibba naga kamar kina sonyin magana! amma kuma kinyi shuru.
Cikin sanyin muryar ta mekama dana Hanan din tafara magana! Hanan banaso soyayyar Aswad tasaki manta da alkawarin da kika daukawa Abiy, nabazaki taba sauraron wani saurayi ba! har se kin kammala karatunki na secondary.
Haka kuma bamaso kizamo daya dagacikin irin matan wannan zamanin da SO" ke rufe musu ido, natabbata Abiy zefi kowa farin ciki idan har kika kiyaye hakan.
Hanan kiduba irin burin da Abiy yadauka akanki! Abiy bayi da watah magana datawuce taki, shin bakyaso kiga kincika burin ki ne? Ehhye Hanan??
[20/08 4:49 pm] ~ Mrs Yerima📚✍🏼: NI DA ASWAD!!!!!!!
1
Writing by
Subee Moh'd Gombe
Mrs yerima🌹
@Admin
SHAGALINKU MATA GROUP📚✍🏼
SUBEEASLAM GROUP📚✍🏼
Page 7
Ajiyar zuciya tayi donjin maganganun Muhibba! Tabbas maganar ki gaskiya ne tace, cos Abiy yanason yatemakeni wajen ganin nacika burina na zama cikakkiyar lawyer, domin nadinga ka re hakkin yan'uwana mata! Marassa karfi.
Kai tadago takalli Muhibba da itama kallon natah takeyi! Tacigaba dacewa, Muhibba soyayyar Aswad tashiga zuciya ta! Batare dana shirya ba, wanda hakan yasa ba na 'iyayin katabus 'akan soyayyar shi.
Muhibba inaso ki san cewa ba ni nasawa kaina soyayyar Aswad ba! Inaji kamar sonshi acikin jinina yake, jinake bazan'iya barin shi ba! Cos ina matukar kaunar shi.
Na so ace nacika wa Abiy alkawarin dana dauka! Amma kuma nakasa Muhibba, ayayin da kwalla ne yacika matah 'ido, kafadarta Muhibba tadafa tana cewa! Nayadda dake Hanan.
Duk dacewa bansan miye SO" ba! Amma na tabbata bazaki'iya ba ne, cos nasan kawata! da'ace zaki'iya nasan da tunin kin rabu da Aswad.
Sede kuma inajimiki tsoron Abiy! Domin natabbata 'idan har ya ji ko yagani bazeyi farin ciki da hakan ba.
Hakane Muhibba! Saboda hakane nadau aniyar boye wa har sai lokacin da Abiy yabukaci na fito da miji tukun, sede ina rokonki ki rikemini shi amatsayin sirri batare da kowa yasan ina tare da Aswad ba tace.
Amma Hanan bakya tsoron Mamna ko Aunty Maryam wani ya fahimci hakan? Aah! Insha Allah bazasu taba fahimta ba tace, zanbi kuma duk han'yoyin da bazasu ganeba.
Shikenan insha Allah babu wanda zeji daga wajena tunda haka kikeso Muhibba tace! Ayayin datacigaba da assignment dinta.
[20/08 8:38 pm] ~ Mrs Yerima📚✍🏼: NI DA ASWAD!!!!!!!
1
Writing by
Subee Moh'd Gombe
Mrs yerima🌹
@Admin
SHAGALINKU MATA GROUP📚✍🏼
SUBEEASLAM GROUP📚✍🏼
Page 8
WAYE ASWAD:- Aswad d'a ne tilo awajen Alhaji Musbah Mujaheed! da Hajiya Sadiya, Alhaji Musbah Mujaheed shahararren dan kasuwa ne! Wanda ya'ansa sunanshi, kasuwancin shi ba'iya karar Nigeria yatsaya ba! Har kasashen ketare (Africa) an kuma san da shi.
Alhaji Musbah Mujaheed yana da rufin asiri sosai! Aswad shi kadaine danshi daya haifa tare da matarshi Hajiya Sadiya, wannan yasasu nunamishi gata iri-iri.
Alhaji Musbah Mujaheed da Hajiya Sadiya duk kanninsu mutanen asalin garin borno ne! Acikin karamar hukumar Bama.
Aswad irin san gar tattun yaran nan ne! Wanda sukataso kuma acikin gata da tarun dukiya, cos babu wani abin da yake nema yarasa awajen iyayen shi! najin dadin rayuwa, wanda hakan yake kara shagwabar da shi.
Aswad yayi karatunshi ne a kasar England har yakai matakin digiri! bayan yadawo gida(Nigeria) ne mahaifin nashi yabude mishi katafaren store and plaza.
Wanda duk cikin garin Yobe babu kamar shi! Cos babu irin abinda ba'azuba acikin shi ba, ga shi kuma komai nasu yana da kyau da kuma inganci.
Kasancewar baya sha'awar yin aikin govnt ne yayi zamanshi! Sede yafita yawon shan iska idan yabukaci hakan, ayayin da kudi kuma yake shigo mishi anytime.
[20/08 9:26 pm] ~ Mrs Yerima📚✍🏼: NI DA ASWAD!!!!!!
1
Writing by
Subee Moh'd Gombe
Mrs yerima🌹
@Admin
SHAGALINKU MATA GROUP📚✍🏼
SUBEEASLAM GROUP📚✍🏼
Page 9
ASALIN LABARI:- Kasancewar yau ranar Sunday (lahadi) don haka su ka dukufa don ganin sun kammala duk kanin assignment dinsu.
Seda su ka gama tsaf! Sannan ta lalibo wayar ta takira masoyin natah su ka sha hirarsu, sannan ta tashi don ta wuce gida! Muhibba ce da yayanta uncle D. Su ka kaita har gida.duk da cewa babu wani nisa sosai da nasu gidan.
WASHE GARI:-Yauma kamar yanda sukasaba haduwa! a makaranta idan antashi, kasancewar uncle D. ne yake zuwa daukar Muhibba! Se yahada da ita, idan sun sauketa se suwuce.
Hirarsu suke irinta masoya! Cikin yanayi irinna wanda ya goge abangaren dabi'un turawa yafara magana.
My beauty! Yakamata ace yanzu Abiy yasan da ni, cos ina tsoron ranar da za'ace narasaki! Hanan ina matukar kaunar ki.
Hannunta datajine acikin nashi hannun yasakata maida kallon ta gareshi cikin sauri! Cos wannan shine karo na farko da wani dan namiji kuma saurayi yafara taba jikinta.
Magana yacigaba dayi ayayin da ya saka idanuwanshi acikin natah idanun! My beauty sonki yana karuwa acikin zuciya ta, ina miki soyayyar da ban taba yiwa watah ya'mace irin shi ba arayuwa ta, inaso ace nakasance dake har karshen rayuwa ta Hanan.
Cike da salo irinta soyayya yacigaba da magana! Hanan wallahi idan har narasaki bansan irin halin da zan shigaba, Hanan kece farin ciki na! rabuwata dake tamkar rabani da farin ciki na ne, ba ni da wani burin da ya wuce ace kinzamana mallakina! Hanan anya kina jin abin da nakeji kuwa?
Kalamanshi sunyi matukar kashe matah Jiki! Wanda hakan yasakata kasa janye hannunta daga cikin nashi hannun.
Cikin sanyin muryar ta maidadin sauraro tace! Aswad kasan nima ina matukar sonka, kuma kai kadaine acikin zuciya ta! Naso'ace mun wuce wannan matakin yanzu.
Domin kusan shekaranmu daya kenan muna tare kuma aboye batare da sanin iyayen mu ba! Sede kuma nagayamaka irin alkawarin dana dauka wa Abiyna, da kuma irin ra'ayin Abiyna akaina.
[21/08 1:27 pm] ~ Mrs Yerima📚✍🏼: NI DA ASWAD!!!!!!!
1
Writing by
Subee Moh'd Gombe
Mrs yerima🌹
@Admin
SHAGALINKU MATA GROUP📚✍🏼
SUBEEASLAM GROUP📚✍🏼
Page 10
Cikin alamu irin ta damuwa tacigaba dacewa! Natabbata idan har Abiyna yasan da kai yanzu bazeyi farin ciki da hakanba, cos nayi watsi da alkawarin shi.
Amma insha Allah komai yakusa zuwa karshe! Domin yanzu yan' watanni ne yasaura mufara jarabawarmu ta karshe (WAEC da NECO).
Nasan dazarar mungama Abiyna zece nasaurari duk wanda yazo neman izini gurinshi! Domin fidda gwanina, kaga adede wannan lokacin kai kuma zaka turo magabatanka wajen Abiy.
Kaga idan antsai da magana se nawuce jamiah! Ayayin datakarasa maganar ta dacewa, daganan kuma se zancen biki doncika burinmu tare da yin yar'dariya cikin yanayin jin kun'ya.
Murmushi shima yayi donjin dadin kalaman natah! Muryar Muhibba ce takatsemusu hirar tasu, toh Romeo and Juliet sai kuyi hakuri hakanan da soyayyar gacan uncle D. Yazo tace tana dariya.
Gabadayan su dariya sukayi sannan sukayi sallama da junansu! Har bakin motar yarakasu, shima yashige tahi motar kirar BMW yawuce.
BAYAN WATA DAYA:- Ganin yau girkin Mamna ce hakan yasakata shiga kitchen da wuri! Domin yiwa Abiy irin girkin dayafi so.
Kunun kwakwa tahada da Alalen doya! Se kuma pineapple ginger da ta hada shima, ayayin da tabar Mamna da tuwon shinkafa miyar Alayyahu.
Agurguje tashiga wanka! Sannan tagabatar da sallar isha, kasancewar lokacin su nayin karatu yakusa.
[21/08 4:16 pm] ~ Mrs Yerima📚✍🏼: NI DA ASWAD!!!!!!!
1
Writing by
Subee Moh'd Gombe
Mrs yerima🌹
@Admin
SHAGALINKU MATA GROUP📚✍🏼
SUBEEASLAM GROUP📚✍🏼
Page 11
KUNUN KWAKWA:
Ingredients:
Citta
Sugar
Madara
Kwakwa
Kanumfari
Farar shinkafa
*Sedatafara wanke dan'yar shinkafa irinta tuwo! Sannan tasaka mishi citta da yar kanumfari kadan tayi blending nashi sannan ta tace, tabarshi ya kwanta! Kwakwa tad'auko takankare bayanta har se dataga yayi fari tas, sannan tayankata tayi blending natah ta tace! Sannan ta dora tacecciyar kwakwar akan wuta har se da yatafaso sosai sannan ta dauko wannan kullun shinkafar nan da ya kwanta tadamashi, haka tacigaba da juyawa akan wutar har se datah tabbatas yayi matah kauri yanda ake bukatar shi sannan ta safke, yana dan hucewa tasaka mishi madara ta gari maidan dama, tasaka sugar dede sannan tazuba acikin flanks don kar ya huce kamin lokacin shan shi yayi.
PINEAPPLE GINGER:
Ingredients:
Sugar
Ginger
Flavour
Pineapple
Lemon tsami
*Tana bare dan'yar citta ta wanke (ginger) sannan tabare abarbar tacire baqi-baqin jikinshi tayanka tahadasu a blender tayi blending nasu ta tace, sannan tasaka sugar dede! Takawo flavour na ruwa pineapple tadan diga kadan aciki ta juya shi, sannan takawo ruwan lemon tsami tasaka dan kadan shima tasake tacewa, asaka a fridge don yayi sanyi yanda ake bukata kamin lokacin shan shi.
ALALEN DOYA:
Ingredients:
Mai
Kwai
Doya
Curry
Hanta
Maggi
Gishiri
Albasa
Attaruhu
*Doyar tafara yankawa (dan'yar doya) sannan ta wanke takankare ajikin greater! Se ta juye acikin blender tasaka dan attaruhu da albasa dede tadan zuba ruwa kadan aciki tayi blending nashi, sannan tajuye akwano tafasa kwai danye ta zuba acikin kullun doyar tajuyashi, batasaka ruwa dayawa ba! Tabarshine kamar yanda akeyin na wake kaurin, sannan ta kawo dafaffen hanta wanda tamishi kananan yanka tazuba, sannan ta kuma ta kullashi acikin ledar kulla alale iya girman da take bukatar shi, setahawar dashi kan wuta kamar yanda ake dafa Alalen wake, abarshi kamar tsawon 30 minutes kamin asafke.
Tana fitowa shinfida sukahauyi tare da kannen natah! Kamar yanda sukasaba, adede lokacin Abiy yashigo tare da kha'af da khuhail! Kasancewar an fito daga masallaci.
Shigowar Abiy ne yasa hatta su Mamna neman wurin xama domin yin karatu! Se dasuka kammala sannan suka wuce parlour domin yin dinner.
Al'adar Abiy ne cin abincin dare tare da iyalen gidanshi idan yana gida! Se da sukagamacin abincin sannan kowa yawuce dakinsu, kasancewar basucika yin wani dogon hira ba.
Kiran da mahaifin natah ne yamata yasakata dawowa parlour ta zauna! Tabbas tasan magana ce mai muhimmanci Abiy zeyi da ita, hakan yasakata kara tattara hankalin ta guri daya tana sauraron shi.
[21/08 5:33 pm] ~ Mrs Yerima📚✍🏼: NI DA ASWAD!!!!!!
1
Writing by
Subee Moh'd Gombe
Mrs yerima🌹
@Admin
SHAGALINKU MATA GROUP📚✍🏼
SUBEEASLAM GROUP📚✍🏼
Page 12
Sede kuma fargaba datakeji! Cos batasan akan miye zeyi matah magana ba, tadade a zaune! Sannan yayi gyaran murya, cikin yanayi irin ta man'ya kuma dattijai yafara magana.
Hanan munyi iya kokarinmu wajen ba ki tarbiyya yadda yakamata! Sannan kuma mun ba ki ilimin addini wanda ko iyanan kika tsaya alhamdulillah.
Ayanzu kina gab da kammala karatunki na secondary! Wanda kuma bewuce yan watanni ba ne yaragye ba.
Saboda haka amatsayina na mahaifin ki naba da auren ki wa Humaid! Da ga zarar kuma kinyi Candy (s.s.c.e) insha Allah za'ayi bikin ku.
Cike da rudani ta kalli mahaifin natah! Cikin tashin hankali ta tashi tsaye! Ganin babu alamun wasa afuskarshi, hakan yakara tabbatar matah da maganar da yayi.
Bakuma kunnuwanta bane sukayi matah 'karya! Bakuma mafarki takeyi ba, cikin muryar kuka tafara magana cike da tashin hankali.
Don Allah Abiy kayi hakuri! Abiy kar karabani da wanda nake SO", please Abiy! Kutemakeni, wallahi ina sonshi! Ayayin da wani sabon kuka yasake ku'buce matah.
Kusa da mahaifiyar tatah takarasa tace! Mamna don Allah ki saka baki, Mamna nasan inkinyi magana Abiy ze fasa rabani da Aswad! Please Mamna ki temakeni.
Ayayin datahmai da kallon ta ga mahaifin natah tacigaba dacewa! don Allah Abiy kar kace zaka rabani da Aswad, wallahi rabuwata da Aswad kamar karabani da farin ciki na ne!!!!!!!
Marin da Mamna tayi matane yasakata yin shuru daga maganar da takeyi tamkar wacce ta zauce tare da dawowa cikin hayyacinta.
Shi kan Abiy cike yake da mamakin ta! Ba ma shi kadaiba hatta Mamna da Auntynsu, wai shin yaushe Hanan tafara soyayya basusani ba yace acikin ranshi! Har kuma tayi zurfi haka acikin shi yasake cewa acikin ran shi.
Cikin bacin rai yamai da kallon shi gareta datake faman rusa kuka yace! Hanan damah kina kula samari batare da izinina ba!!!!!
Cikin kuka tace! Abiy kayi hakuri! Nakarya muku alkawarin da na dauka, ayayin datacigaba da magana cikin muryar kuka.
Mun ketare Shari'a narashin neman izininka kamin mufahimci junanmu! Amatsayin ka na mahaifi agareni, nasan kamata yayi ace Aswad yafara neman izininka kamin yafara magana da ni.don Allah Abiy kayi hakuri! Ba komai yasakani yin hakaba se don!!!!!!!
Hannu ya d'aga matah cikin yanayi irin na 'bacin rai! alamun bayason jin duk wani maganar ta, Wanda hakan yasakata yin shuru.
[22/08 3:45 pm] ~ Mrs Yerima📚✍🏼: NI DA ASWAD!!!!!!!
1
Writing by
Subee Moh'd Gombe
Mrs yerima🌹
@Admin
SHAGALINKU MATA GROUP📚✍🏼
SUBEEASLAM GROUP📚✍🏼
Page 13
Cikin yanayin bacin rai yace! Hanan babu abin da zesa najanye auren ki da Humaid, idan kinga ba ki auri Humaid ba toh kindena numfashi ne adoron k'asa, amma muddin kina numfashi tohfa babu fashi! Saboda haka ki zauna cikin shirin ki domin auren ki da Humaid ko bayan raina shine mijin ki.
Cike da bacin rai yafi ce! Ayayin da wani sabon kuka yasake dawo matah, kuka takeyi! Ko kallo bata'ishi Mamna ba, itama tafi ce daga cikin parlourn! Aunty Maryam ce tahau rarrashinta, wanda se datayi kuka har tagaji.
BAYAN KWANA BIYU:Gabadaya cikin yan' kwanakin nan Abiy yacanja matah! Hatta gaisuwar ta yadena ansawa, wanda hakan bakaramin karasakata acikin damuwa yayi ba! Ga shi har itama Mamna tadena kulata.
Sede kuma duk da irin fushin da iyayen ta sukeyi da ita hakan besakata janye soyayyar Aswad daga gareta ba.
Zaune take adakinta! Kuka take ta faman rerawa, yanda yazame matah Jiki acikin yan' kwanakin nan! Muhibba ce tashigo dakin cike da fara'arta.
Ganin halin da aminiyar tatah kecikine yayi sanadin daukewar fara'arta! Cikin sauri ta'karaso inda take tana fadin lafiya Sis meke faruwa??
Wani sabon kuka ne yasake ku'buce matah! Tace shikenan Muhibba, Abiy yarabani da masoyina! Ya zanyi da rayuwa ta, Abiy yana neman yahanamu cikar burinmu NI DA ASWAD! Se da tayi kukan ta me'isarta, sannan tasanar da ita abin da ke faruwa.
Cikin yanayi irin na rarrashi tafara magana! Nasan kina matukar kaunar Aswad, amma kuma yakamata ki tattaro hankalin ki guri daya Hanan! Kizamo mai biyayya ga Abiy.
Duk dacewa kinyi zurfi acikin Soyayyar Aswad! Ammafa hakan baze zamo miki hujjar dazaki bijirewa Abiy ba, Hanan ki duba irin burin da Abiy yadauka akanki tare kuma