Share this page
haife mu yara ne mu fa,Islaha duk wasa ta dauka yana yi shi kuwa da gaske yake fadar komai,tace to bari na baka a baki. Su Khalisat suna palo shuru shuru sun ga Sahil shuru yaki fitowa tsoro ya kama su,Khairat tace bari na leka ta mike sadaf sadaf tace dole abi sahu bako ne ba a san halinsa ba,Islaha tana ta bashi zobo a baki yana shanye abinsa sai da ya kusa gamawa ya tankade cup din ya fadi kasa ya tarwatse yace da girmana,nifa ba dan iska bane irinki me neman maza yaja tsaki ya juya sai suka yi karo da Khairat. Khairat ta matsa da sauri taga Islaha tayi zugum ga cup a tarwatse bata sani ba Sahil aljaninsu fada musu abu suke yi iya tsiyarka watarana baza ka iya kure su ba,kafin kazo sun sani,Khairat ta harari Islaha tace stay away from him yafi karfinki,gashi nan kin jawa kanki sai ki gyara wajen. Sohail yana komawa wajen su Khalisat kamar munafukin miji yace yawwa ni gaskiya indai itace kar ta dafa min abinci a gidan nan,kar ta yi min komai,Aunty tace karka damu girkin ma da hannunmu zamu dinga yi maka har wanki da komai,yace yafi muku,Khalisat tace bari nazo mu fita a mota na kaika yawo,Aunty tace da kin bari tunda zan fita na fita tare da shi,Khalisat taji haushi da kishi tace ai na shirya,Khairat tana jinsu tace ni na kaishi next week. Sahil yace ayi haka? Kunki sharar masallaci zaku yi ta kasuwa,ko girki bakwa yi ga me yi can bakwa wanki duk yi muku akeyi yanzu da kanku zaku yi min nawa? Aunty tace laaa ba komai ai bakonka annabinka,Sahil yana kallonsu dai dai yace alright ku kuka ga zaku iya ai! ya furta kai tsaye ba ko darrr. Free page 400 ne 0175487861 Asmau Garba Muhammad Gtbank 'Yan Niger +22790795939 AsmaBaffa 08061929616 [7/17, 3:17 PM] Asmabaffa: 🪸MUMMUNAR DABI'A 🪸 16-20 Official By AsmaBaffa SADAUKARWA NE GA 'YATA TASNIM Page naki ne Baby Ak MASU AUDIO BAN YARDA A SATAR MIN NOVEL BA A JUYA BA,DUK WANDA YA DORA A CHANNEL DINSA SAI YA SAUKE. *ZINARIYAR MACE⚡* *Wai shin 'yar'uwa menene matsalarki? zubewar nono, ko kuma rashin kwankwason juyawa a falo maigida ya shiririce ya manta da tibi da matan tictok, menene matsalarki ne? rashin ni'ima ko kuma mugun sanyin da ya yi miki katutu, shin rashin taushin fata ne ko kuma kuraje da tabbani, ko bala'in ramar da ta addabeki kuma babu rashin ci ba rashin sha a gidan auranki, gwaigwayewar gashi ce matsalarki ko kuma kaushi da faso na tafin kafa da bushewar fata, kina bukatar fatarki ta yi glowing kalarki ta fita kuraje su mutu, ko kuma kina bukatar azababbun turaruka da humra tare da turarukan wuta. Na san dai kuna da yawa matan da tumbi ya yi musu karan tsaye ina nufin ya katse muku hanzarin yi wa maigida gwalli da muskuce-muskuce a falo😃 Nesa fa ta zo kusa AL-KUTUBIYYA ISLAMIC MEDICINE sun tanadar muku da nau'in magungunan da suke magance kowace irin matsala da izinin Allah. Babban burinmu shine sha'ani na aure ya inganta a samu daidaito. Muna da.* Na gyaran nono. Na sanyi. Dilka tare da hadin sabulu. Duk Wani nau'in maganin mata. Humra turarukan wuta perfumes, original miski tahra 3in1, ciccibi budurwar kaza. Had'addun supplement irin wad'anda ba su da matsala. Maganin Sliming wato narka tumbi. Abubuwan da muke sayarwa suna da yawa, kuma babu asarar dukiya. Muna garin kano kuma muna tura kayanmu kowane gari fad'in Najeria da Nijar har ma da kasashemn ketare. Kai tsaye a tuntu'bemu ta lambobin wayarmu domin karin bayani. *08089965176* *07084653262* Zuwa yamma Khalisat tace Sahil ya shirya su fita,Islaha ta fito lokacin ido ta kyafta masa tana makale kafada wai yace yaki bazai je ba,Sahil ya kalli Khalisat yace ni bazan je ba Islaha tace kar naje,baki Islaha ta rufe tare da sauri tace ba ruwana ni nace kar kaje? Sahil yace ido ta kyafta min tana min nuni nace wai bazan je ba. Khalisat tace to Allah ya kamaki,Islaha ta wuce bedroom dinta da sauri,Sahil kuwa tashi yayi yace ke Khalisat kike ko wa kilishi bazan je ba,ni ba sahoramin namiji bane da zan bi mace ta fita dani yawo,ai idan ban fita da mace ba to kuwa mace bata isa ta fita da dan uwan Sohail ba,duk gidan nan baku isa ba ko uwar ku ce bazan je ba. Haka kawai kun kawo ni gida an ajiye ni neman kudi fa nazo ba zan zauna gidan yan iska ba,Babarku ma jiya sai da tayi kawalci,ta hada kawarta da wani me kudi ya biyata kudi kuma anyi. Itama Khairat dazu dazu ta gama waya zata samu wani a hotel senator ne kuma arnene sunansa Michiel,bazan iya ba,ga yayarku can Shema'u a gidan ta ajiye yaro matashi tana kashe masa kudi yana biya mata bukata ina zaku kai wannan zunubin? Dakinsa ya wuce sai gashi dauke da jakarsa yana zarewa Khalisat ido yace akan ki fita dani wani yawon shakatawa gwara na bar muku gidanku ni dama bance a kawo ni ba,indai sai an kaini yawon shakatawa ne gwara na bar gidan. Abincinku kuma kuyi kudinsa na biya ku mutanen banza,ni dan iska ne ance muku?. Khairat da Aunty ne suka fito jin Hayaniya Sahil ya nuna su da yatsa yace duk iskancinku sai kun kyale min abu dita bata iya hasala komai,mata kun sani a gaba sai lashe lashen harshe kuke yi,bazan iya ba kuje ku zuba min magani a lemo na a rabani da mazantaka ta. Aunty tace kai ka iya bakinka wlh gidanmu kazo,butulu an taimakeka kazo kana mana wulakanci,Sahil yana ji yace ni nace a taimake ni? Kuma badan Allah tayi ba,Baba ki iya bakinki. Khalisat ta zaro ido tace uwar tamu? Uwar taku kuwa wata ta kirki ce,Islaha ce ta fito ta tsaya a gefen Sahil tace kuma ai ba fin wasu matan kuka yi ba asiri kuke yiwa maza ana baku kudi amma ai baku fi kowacce mace ba. Sahil yace kuma Taskirar ma duk Infection ne a ciki,gasu nan kullum a shan magani,matukar baku tuba ba baza ku warke ba,ai dama Khairat watanta Uku bata yi period ba ai Sanyi ne da ita,inji uban wa? Aunty ta furta amma kai Aljan ne idan ba Aljan ba a gidan uban wa ka sani. Sahil yace ai mijinki sai kunyi sharia da shi a Lahira dama kina da aure kina bin maza bai sani ba,Aunty ta zaro ido nan take ta fara hada zufa,tana kame kame,Sahil yace kuma Yaseer ba dan mijinki bane Sale me maganin yan bori shine ya miki ciki,Aunty ta shiga tsoro tace amma kai aikoka aka yi kaci zarafin mu fita ka bar mana gida. Sahil yayi tafiyarsa ya bar gidan,Islaha suka kama suka rufe ta da duka ta musu rashin kunya sai da suka mata lilis sannan suka kyaleta yashe a kasa tana kuka,Aunty daki ta shiga ta fara watso kayan Islaha dama kadan suke jira,tana masifa tace dauki ki bar mana gida kusan inda dare ya miki,Islaha ta mike da kyar ta tattara kayanta tana cewa dan Allah Aunty kiyi hakuri wlh bazan kara ba. Aunty tana masifa tace wlh sai kin bar gidan nan dama kin ishe mu,Yaseer ne ya shigo ya iske abinda ke faruwa yana gidan yayar su Shemau,shine ke tukata a motarta duk wani iskanci da zata je Yaseer kaninta shi ke kaita sannan kullum suna tare a gidanta ko hotel,kudi take kashe masa sabo da yanda komai shi take aike, shine kamar yaronta kuma kaninta uwa daya uba daya. Yaseer yace ke Aunty ki kyaleta 'yar gidan yar uwarki guda jini daya,wa take da shi bayan ke? Aunty tace tana da su tunda ta iya yi min rashin kunya ta bar min gida na gaji,taje ta bi bako Sahil ya bata uwar da zai bata,Islaha ta mike tana dingishi ta zuge jakarta me dauke da tsumman kayanta zata fita" Yaseer ya rike ta tare da furta dan Allah kuyi hakuri Aunty, Aunty da kyar ta hakura ta kyale Islaha tace ta zauna badan halinta ba. Sahil kuwa machine ya tare ya hau abinsa yace kaini Banana Island ko Lekki,Me machine yace ai nan yankin bama shiga da machine wani wajen amma zan kaika kusa da Banana sai na ajiyeka ka shiga mota,Alright muje. Me machine dai wuta yake kawai a titi ta wajen wata katuwar gada suka zo wucewa mutane 'yan cirani gasu nan fululu,Sahil yace sauke ni a nan ga gidanmu,Me machine yayi dariya ya tsaya yace nan ne gidan ku? Kace Banana Island ko Lekki, Na fasa zuwa can to ko zaka min dole ne? Sahil ya furta ransa a bace. Me machine yace ni a wa! bani kudi na kawai,Sahil ya bashi kudinsa ya wuce shi kuma ya nufi kasan gada. Mata da maza ne a wajen ga karuwai nan iri iri wasu a nan suke badalar su idan Allah ya taimaki mace ta tara kudi ko ta hadu da me kudi sai ta kama gida a wata unguwar ta koma shike nan taci gaba ita. Sai faman kallon Sahil suke yi,ga maza nan wasu duk sun bar kayansu a wajen sun tafi neman kudi,Sahil ya tsaya yana ta kallon wajen in banda kazanta da wari babu komai a wajen,kamar zaiyi amai ga kudaje na dole wanda kazanta ta kawo su ta dole. Sahil gajiya yayi da tsaiwa ya tsallaka gefen wasu flowers yayi fitsari,ashe ba a fitsari a wajen sai gani yayi 'yan sanda sun zo sun kama shi,daya a ciki da rashin mutunci yazo yana kiransa da Aboki zai mari Sahil hannun dan sanda baras ya balle ihu ya saki ya tsuguna a wajen,Sauran su tunaninsu kuskure ne yasa Oga ya karye,suka fincike jakar Sahil a jikinsa,duk yana kallon su bai ce kala ba,cikin yan sandan su biyar daya a ciki ya rataya jakar a kafadarsa ya cakumi kugun Sahil yace muje Office suna masifa ya jawo Ogansu ya karye,Sahil ya kalle su yace ku jani ku kaini Office din,Suka fisgo Sahil amma suka ji gam gam kamar sun taba jikin katanga,sai da suka hadu su hudu ko zasu iya daukan Sahil amma gam gam a tsaye,kuma yana motsa jikinsa yana komai amma sun kasa,tsorata suka yi,wanda ya rataya jakar Sahil ya fara kokarin cire jakar zai bashi abarsa amma jaka taki ciruwa. Yayi yayi ya cire jakar ya kasa,sauran suka tayashi amma taki ciruwa,Sahil suka dawo suna roka Oga please....hannu Sahil ya daga musu yace na yafe muku kuje kawai,wanda jaka taki ciruwa a kafadarsa ya kwabe fuska zaiyi kuka yace Sir....Sir....please....yana nunawa Sahil jakar ya fara sheshekar kuka,Sahil ya barsu a cikin rana ya juya zai tafi ai binsa suka yi da gudu,me jaka yana faman tiri tiri da ita ya rike Sahil tare da durkusawa a kasa yana bashi hakuri yana rokonsa, wanda ya karye kuwa yana yashe a kasa rike da hannunsa yana ta ihu da danasani. Sahil hannu yasa ya janye jakarsa a kafadar dan sanda sai gashi dansanda ya mike yana murna suna godewa Sahil,Sahil yayi tafiyarsa ya barsu. A haka ya dinga garari a gari idan ya gaji ya samu waje ko jikin bishiya ya zauna ya huta,ga ruwan sama ko yaushe sai dai ya nemi wajen fakewa. Bashi da inda zai kwana gashi ruwa zai iya tsinkewa komai dare,tafiya ya dinga yi har ya samu sabon gini kango ne an rufa shi kofa da window ba a sa ba,ciki ya shiga ya ajiye jakarsa a nan sai da ya huta sosai sannan ya samu ya fita ya nemi abinci ya siya ya dawo ya zauna ya cinye abinsa ya sha ruwa pure water,a nan ya kwanta bacci ya kwashe shi wurin duk yashi da siminti. Islaha ce kwance tana ta tunani ko Ina zai je oho,mikewa tayi tana kwance ta zuba tagumi a hankali ta mike ta dauki wasu kudi ta saka rigar ruwanta a saman doguwar rigar atamfarta wata maroon ta fito. Tana ta duba Sahil unguwa unguwa bata ganshi ba,ta nufi kasan gada inda marasa galibu suke tafiya taje ta duba ko ina babu shi,ta sake hawa machine tayi ciki ta kangon da Sahil ke kwance ta wajen ta wuce haka ta gaji da nemansa ta koma gida cikin dare. Washe gari ma da wuri ta tashi ta gama ayyukanta ta sake fita nemansa duk inda tasan yan cirani na zama sai da taje bata ga Sahil ba,har sai da ta kwashe 5days kullum sai ta fita nemansa,shi kuma yana cikin kangon sai dai ya fito ya siyi abinci ya koma. Kudinsa ya kare bashi da ko sisi babu kudin siyen abinci,Sahil sai da ya kwana ya yini bai ci komai ba ruwa ma a wani pampo ya samu ya sha,zama yayi a cikin kangon yace gwara na koma gida kawai wannan ciranin bazai yuwu ba babu riba a cikinsa,gwara na kira Sahil ya turo min kudi na koma naci gaba da bauta bazan iya ba. Please call me ya yiwa Sohail nan take Sohail ya kira shi,yace ya lagos din ko ta samu ne? Sahil yace Allah ya tsinewa lagos wlh gwara arewa mutum yana cikin mutunci da sutura,ni dawowa zanyi gida ka nemo kudin mota ka turo min,Sohail yace da wuri haka? Yace ai gwara ka dawo gashi me shago ta zama kawar mu,Sahil yace nemo kudi ka turo min jira nake yau na kwana na yini ba uwar da naci kaje ka roki Adnan a bani kudi dan Allah yunwa zata kashe ni. Sohail wayar ya kashe ya nufi bedroom din Adnan yayi knocking Adnan sai da ya gama yangarsa ya bude kofa sanye cikin gajeren wando,yana ganin Sohail ya bata rai,Sohail yace dama dan Allah kudi za a turawa Sahil zai dawo gida,Adnan ya kece da dariya ba shiri ya dinga dariyar mugunta harda shakewa yace yaji wuya,ina neman kudin? shi a dole me zuciya,ai ba abinda zai samu dama na fada muku ku hakura da rayuwa ku zauna ku dinga bautar mu kunki ji,baku da gata amma ku kunki yarda shi a dole zaiyi kudi to sai yayi kudin mu gani idan yana da kwakwalwar tara kudi. Sohail yace arziki dai na Allah ne,Adnan yace au nasiha zaka min? Kai ka isa kayi min fada kana talaka? Me yasa baka yiwa kanka fadan ba ka zama me kudi,kayi tunani me kyau akanka ka zama me kudi in ka isa,amma ina me kudi ai kuwa nine nake da hankali da tunani,talaka ai bashi da hankali tunda ya kasa yin hankalin yin kudi. Sohail yana jinsa yace hmm bani kudin na tura masa to,Adnan yace sai nan da 2weeks,bashi da kudin abinci fa Yaya dan Allah ka bani na tura masa dan Allah.....Adnan yace wlh na rantse sai nan da 2weeks kuma ko ka kira Daddy bazai bayarba sabo da komai naku yana hannunmu an dawo da rikon ku hannun mu. Sohail juyawa yayi ya tafi kawai ya wuce bedroom dinsa yana rufe kofar ya jingina da jikin kofar ya zame ya zauna a kasa hawaye ya fara zubarwa sosai yana kuka,ya daga hannaye sama yana rokon Allah yace Allah kaga halin da muke ciki Allah ka fitar damu Allah ka bani kudin da zan turawa Sahil,ya zauna yana addua yana kuka,ya dade a haka ya wanke fuskarsa sanna ya fito. Maheera ya gani tana Gyara kujeru ta kalle shi taga alamar kuka yayi. Murmushin karfin hali yayi ya zauna kawai ya zuba tagumi,Maheera zama tayi a kujera daya suna Facing juna tace Sohail lafiya? Me suka yi maka? Sohail ya kwashe labari ya fadawa Maheera yace kuma Sahil yana can ya kwana baici komai ba a kango yake kwana,Maheera tace to kwantar da hankalinka jiya Zayna ta bani dubu talatin tace na siyi kayan sawa ta gaji da ganina cikin tsumma wai kyankyamina take yi a haka,Sohail yace a hakan kika yi kalar kyankyami? Maheera ta daga masa kai tare da furta haka tace. Aljihun doguwar rigarta ta duba tace gashi sai nayi mata karya nace tela bai dinka min kayan ba,dama dubu talatin a zamanin nan wanne kaya zata siya min na kirki kuma a garin Abuja sai dai atamfa karama da gwanjo. Sohail ya karbi kudin yace na gode Maheera,tace to ba gashi Allah ya rufa asiri ba ai dai ko a trailer ya dawo kamar yanda ya tafi. Murmushi yayi sai yanzu hankalin Sohail ya kwanta ya fice da sauri ya nemi POS ya turawa Sahil kudin,ya kira shi a waya ya sanar masa,Sahil ya mike yana murna cikinsa ba komai ya fito daga kangon zai nemi me POS ya cire kudin,yana fitowa Islaha tana zuwa wajen a kafa tana ta dube dube tana nemansa,ido biyu suka yi ta ganshi ya rame sosai yayi busu busu da siminti ,Murnar ganinsa tayi tace ina ka shiga dan Allah Sahil yau nafi kwana shida ina nemanka Sahil ya kalle ta yace ina nan wajen ai yanzu ma fita zanyi kika zo ina zan samu me POS? Kudi zan cire na siyo abinci,Islaha tace zo mu tafi,bayan ya cire kudin suka wuce wajen cin abinci, a nan suka zauna yace ke me zaki ci? Islaha zuciyar Sahil na birgeta yanda yake kula da mace,tace a koshe nake,ai daga gida nake fa,yace to lemo fa? tace zan sha to ta dauki nasa ta sha,yana cin abincin yana kallonta yace kika sa min baki a lemo na bazan sha ba,sai kace kazama ta dauke tace to siyi wani bari na shanye wannan din,lemonsa ya kwace yasa aka kawo mata wani. Wani matashi ne ya zauna in banda kallon Islaha ba abinda yake,Sahil ya kalli matashin yace kai dauke idonka,Saurayin yace ai da gani budurwa ce baka da ikon hanani kallonta,Sahil ya kalli Islaha a fusace yace ke kika bashi dama ya kalle ki? Islaha tace ni kaga nace ya kalle ni. Idan kin san na iskanci kike nema kiyi magana tunda sana'arki ce,Islaha tana zaune ta share zancen tace nifa da zan samu wani aikin a wani gidan barin gidan Aunty zanyi. Sahil ya kalleta kawai ya gama cin abincinsa ya mike tare da furta nifa Abuja zan koma gidanmu na fasa neman kudin bazan iya ba,Islaha tace da wuri haka dan Allah karka tafi,. Ke da Sohail aka haifo ni bada ke ba. A ina gidan naku yake a Abuja? Address ya fada mata,tace number waya please wlh kana da hankali kai nutsatse ne,dariya Sahil yayi yace tab ni din? dan baki san yanda ake cewa bani da hankali bane,ai har mahaukata ake fada mana,amma ai ni na sani me hankali ne,ya bata number wayarsa daga wajen ya mata sallama ya wuce Tasha a kafa yake tafiya. Yana cikin tafiya a titi wata mota me bala'in tsada ta gaske ta fara wala wala a titi kamar zata yi hatsari Allah yasa ya ganganre kasa a hankali yayi parking a gaban Sahil. Wani dattijo ne fari da alama bahaushe ne sabo da yana ta waya da hausa sannan kayan jikinsa shadda ce me tsadar gaske,agogonsa da takalmi duk masu tsada ne sosai,gaban motar ya bude yana tunanin kiran me gyara sai Sahil ya tambaye shi yace Baba gyara motar ta samu ne? Yayi murmushi ya kalli Sahil sannan ya furta yaro kana gani karambani yasa nayi tuki da kaina amma bana driving sabo da ido na baya gani sosai ma. Sahil yace bude motar na duba maka to,Dattijon yace thank you ya bude gaban mota yace ka iya gyara ne? Sahil yace a'a zan gwada dai ko zan samu sa'a,Dattijon yace to Alhmdllh gwada mu gani gaba daya taki tashi ma mutuwa take a hanya. Sahil yayi tabe tabensa ya gama yace shiga ka kunna mu gani,Dattijon ya shiga ya kunna ta tashi normal,yaji dadi yace ta dawo dai dai amma da har wani kuka take yi,Sahil yace ta warke ai baza ta kara yin komai ba,amma ka dinga kiran Engineer suna mata service akan lokaci. Dattijon yace na gode ya zaro kudi da yawa yan dubu dubu ya mikawa Sahil,Sahil yace ka barshi akan dan wannan sai ka bani kudi bana bukata,Dattijon dai yayi ta godiya yace sunana Alhaji Isah Danjuma,Sahil yayi murmushi kawai ya juya zai tafi,Dattijon Alhaji Isa yace zo na rage maka hanya mana ina zaka je? Sahil yace aini bako ne ma zan koma gida da kaina,Alhaji Isa yace ko kana cikin masu zuwa cirani? Sahil yace kamar ka sani. Okay Okay da alamarka kayi karatu? Na dai fara University aka cire mu sabo da bamu da kokari bama ganewa mu dakikai ne. Dariya Alhaji Isa yayi yace kana da kokari mana gashi ka gyara min mota ai kasan me kake yi tabbas,karka damu muje gidana ni ka kwanta min a rai zan taimaka maka karka yi rayuwar da wasu suke zuwa suna zubar mana da mutunci hausawa. Sahil cewa yayi na gode Alhaji a wajen Allah nake nema,Alhaji Isa yace ka taba ganin anyi ruwan kudi a duniya duk adduar ka? Sahil yace idan Allah yaga dama fa ni yayi min ruwan kudin? Ni Inshaallah Allahruwan kudi za ayi min daga sama! Alhaji yace ba a ja da ikon Allah amma duk da haka na gode,Sahil ya juya yayi tafiyarsa yana cewa haka kawai ka cuce ni za ayi min ruwan kudi. Tasha ya wuce ya shiga wata trailer din zuwa Abuja,rana tsaka sai ganin Sahil suka yi ya dawo a rame yayi duhu yayi futu futu,Adnan da Ibrahim suna palo suka dinga sheka dariya harda buga kafa,Zayna ce ta sakko itama daga sama ta hau dariya tace masu zuciyar neman kudi. Sohail ne ya fito tare da janye Sahil suka wuce bedroom dinsu,Sohail yace duk ka rame sai da na fada maka karka tafi,ya fita yaje kitchen ya kawowa Sahil girki,Sahil ya zauna yaci ya koshi yace Alhmdllh Allah ka raba mu da cirani. Sohail yayi dariya,Sahil ya shiga toilet ya dinga wanka sai da ya dade yana abu daya haka ma brush duk da yana yi kullum amma na yau na musamman ne. Yana fitowa sai gashi fes da shi ya canja kaya masu kyau,jakarsa kuwa gaba daya kayan ciki ya zuba a washing machine ya sake wanke su,jakar ma ya wanke ta du ya shanya sannan yayi sallar Azahar. Sohail yace tashi muje kaga Baby Maheera kawar mu,kwanaki ta rungume ni sai ta maka kaima dama nace sai ta dauki Alkawari. Sahil yace Good hakan yayi muje,fitowa suka yi gidan ba kowa da Alama mutanen gidan sun fita,a kitchen suka iske Maheera cikin riga da skert yan kanti,Maheera tace barka da zuwa Sahil tana murmushi,Sohail yana gefe,tace ya hanya? barka da dawowa,kaci abinci kuwa? Ta tambaya tana murmushin birgewa,Sohail kawai sai yaji ai bai kamata ace Sahil ta yiwa haka ba,amma sabo da kar Sahil yaji haushi sai ya wayance yace kin fiye dariya da yawa da murmushi,saukinta ma Sahil kika yiwa amma wannan surutun da kike ba birgewa a ciki,kin fini son dan uwa nane da zaki zauna kina surutu? Ki tsaya a matsayinki,abinci dai yaci na kula da abina karki kawo mana iyayi kice ke zaki kula da shi. Maheera tace kuka ce ni kawar ku ce duka na ma tuna da alkwarin Hugging da muka ajiye yau ga Sahil yazo shima ayi masa,Sohail yace ba yau ba sai ya huta ya gaji yanzu,Sahil yace da Islaha ce ma tayi mana nata zai fi dadi,Sohail yace wace Islaha? Sabuwar kawace nima na yo mana ita Allah ta hadu tafi wannan ma Maheera din,Sohail yace kai anya kuwa zata kai wannan? Ta kai wannan

Chapter 6 of 20