Share this page
2 / 2
zafin azababben ciwon da kaina ke yi, sai zafin baƙar azabar da bansan yanda zan kwatanta ko misaltata ba, kwanyata bata aiki sam, hasalima bana iya tantance wacece ni karan kaina, amma nakan tantance nau'o'in azabar da a kullum dare nike kwana a cikinta. Buɗe idanuwa na da suka rine zuwa jajaye na yi, ina jin kamar in ciresu in huta saboda ciwon kan da nike ji har cikinsu, ban sauke su ako ina ba sai a saman farar fuskarshi wacce ke zagaye da lallausan saje, "ɗin,ɗinn,ɗinn". na ji wannan sautin ya doka a ƙoƙon kaina, a daidai lokacin da nayi tozali da ɗigo-ɗigo ɗin jinin da bansan ta inda yake fitaba a jikina, ya ɓata gaban farar rigarshi, ban san mi nike yi ba, amma naga hannuna ya miƙe zuwa kan ƙirjinshi a daidai saitin da jinin ya ɗiga, bazance ga abin da nike yi ba, sai kawai naga hannuna na zagaye inda jinin ya ɓata, caraf ya riƙe hannayena, tare da buɗe idanuwanshi ya watsosu a kaina. Wani tartsatsin haske ne me cike da tarin abubuwa waɗanda ke cakuɗe da hayaniya suka gilma ta cikin idanuwa, acikin abubuwanda suka gilma min nai nasarar cafke wani hoto, a cikin duhu ne a bakin ruwa, ina a tsaye yana a zaune ƙarƙashin bishiya na juya ma shi baya ina jefa ƙananun duwatsu a cikin ruwanda ke gabana, idan ruwan ya yo tsallo yalle sa'ilin da na jefa dutsen yakan fallatsa da ƙarfi har saman fuskata da ke a rufe ruf ba'a iya ganin komi, daga nan hoton ya yanke, sai kawai na damƙi gaban rigarshi da ƙarfi tare da rintse idona, ban san abin da zanyi kuma ban fahimci komi ba amma hakanan naji ina so in idasa ganin wannan hoton daya gilma min. Wa ta iriyar mummunar dokawa ƙirjinsa yayi, babu shiri ya rintse idonshi da ƙarfi, jijiyoyin da suka zagaye saman kanshi na sake fitowa raɗo-raɗo, wa ta iriyar zufa ta shiga karyo ma shi daga saman kai tana bin fatar fuskarshi, lokaci ɗaya jikinshi ya mutu murus, dama gashi ba wani isashen ƙarfi ne da shi ba, ko ina ciwo yake mashi a jikinshi, sake rintse ido yayi yana tunano mawuyacin halin da yaganni a ciki jiya da daddare. A CIKIN DARE Kwance ya ke kamshi na kallon sama, duda baya iya ganin komi saboda duhun da yayiwa ɗakin ƙawanya, tun da yaga yanda na firgita da ganin haske sai kawai ya kashe hasken yana tariyo maganganun kamikin mutumin da tun da yai tozali da shi, ya kasa mancewa da yanayinda yaganshi a ciki, zai iya ganewa idan wani na cikin damuwa koda kuwa yaso ya ɓoye hakan, kallon farko da yaiwa mutumin da aka sheda mashi ya zama suruki a gareshi, ya karanci tarin damuwa me ɗumbin yawa kwance akan fuskarshi, ya kasance cikin mutanen nan waɗanda basu damu da kowa ba, amma bai san yanda akai yaji ya damu da yanayinda yaga mutuminba, kalamanda yai amfani da su wajen yi mashi magana basada tsawo, amma sun samu wawakeken muhalli sun zauna daram a zuciyarshi. "MAILAAH ƴata ce, ka riƙe min ita amana, ka kula da ita, ka zame mata garkuwa kuma kariya ga dukanin wani abu dazai kusancet walau na cutarwa ko akasin haka, suna yi ma ta kallon mahukaci, sai de ba haka bane ƙaddarce ta mayarda rayuwarta haka, idan ka riƙeta amana nan gaba kaɗan zaka yi alfahari da ita, MAILAAH yarinya ce ƴar baiwa, wacce take rayuwa da ikon Allah kaje na miƙ ragamar rayuwarta a hannunka, Allah ya baka ikon kulawa da ita amin." .........✍️MARYAM STAR⭐ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/HbYjxC6ucFxK95Gxo1yN9i 🥀🌹MAILAAH🌹🥀 WRITE BY MARYAM STAR ⭐ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* PAID BOOK BOOK ONE FREE PAGE بسم الله الرحمن الرحيم. Chapter----------- 5 & 6 Bai mance yanda yaga Alhaji Sha'aban yakai hannu na ɗauke guntayen hawayen da suka sulalo daga idonshi ba, ya amshi amanarta tun a lokacin, ko da ace Alhaji bai roƙeshi akan ya kula da ita ba, zaiyi hakan, kodan albarkacin sunanda ya zama sillar haɗuwar ƙaddararsu waje ɗaya, daga lokacinda matar da yaji sam bata kwanta mashi arainba ta ambaci sunan MAILAAH ya rasa nutsuwarshi, akan sunan kaɗai ji yake zai iya sadaukar da rayuwarshi gaba ɗaya, MAILAAH sunane me matuƙar muhimmanci a rayuwarshi, zai iya mance da kowa, da komi amma banda sunan da mamallakitar sunan, a du faɗin duniyarnan babu abin da ke saka shi tsananin farin ciki irin tunowa da ƙanƙanin lokacin da ya yaru da ita, ya gama sadaƙarwa akan ya rasa farin ciki tun da ta kubce ma shi, ya tabbatarwa kanshi zai yi rayuwa amma bata farin ciki ba, zai rayune kawai dan karya ɓata gyara da kwaskwarimar data sadaukar da lokacinta wajen yi ma shi, itace wacce ta gyara ma shi rayuwa, a lokacin da ya fita yawon neman mutuwa ido rufe, bayan ya tsallake wahalhalun rayuwa sai kwatsam ta diro cikin rayuwarshi, ta shafe ma shi du wani tabo da dattin wahalar da yake ciki, ayanzun da babu ita sai yake tattalin rayuwarshi kamar yanda a lokacinda take a tare da shi take tattala masa, bai yadda ko ƙuda ya haushi da sunan cizo ba, kiyaye lafiyarshi ya ke sosai da sosai, shiyasa yau daya wayi gari yaji jikinshi na ciwo kamar wanda akaiwa duka, sai yaji ƙunci ya dabaibaye rayuwarshi. Idan bai manta ba yana a kwance ya fara jiyo nishi da gurnani, da farko bai maida kai ba, amma ji da yayi abin na sake yawa ya saka shi tashi zaune ya watsa idanuwanshi a daidai saitin inda take a zaune, da sauri ya tashi zaune zuciyarshi na dokawa, bazaice ga sadda ya miƙe tsaye ba, kawai ya tsinci kanshi ne riƙe da ita. Cikin ficewar hayyaci na shiga fizge-fizge a sa'ilinda ya riƙeni gam a cikin hannayensa, har lokacin ban daina gurnani ba, da nayi nasarar fuzge jikins daga nashi, sai kawai na shiga buga kaina da nike jin wa ta iriyar hayaniya na tashi a ciki a bango, da tsananin ƙarfi nike doka kan nawa cikin fitar hayyaci, sake kamoni yayi ya rungume ni tsam, sai na shiga sauke ma shi duka tako'ina ina ihu, na ɗauki lokaci me tsayi a haka, yayinda shi kuma yake riƙe da ni har lokacin, duda ihuna na tsananin shiga ma shi kai, amma bai sake ni ba haka ya dinga haɗa gumi, a sa'ilinda ya ke gab da fita hayyacinsa gaba ɗaya, ni kuma jikina ya fara saki sannu a hankali, kafin ya ankare har na fara sakin numfashi irinna me barci, lumshe idonsa yayi shima nan take barci me nauyi yayi awon gaba da shi. Damƙar hannuna yayi daga kan ƙirjinsa, a hankali ya zameni daga jikinsa sannan ya miƙe tsaye yana rangaji har ya fice daga ɗakin zuwa ɗan madaidaicin tsakar gidan, ruwa ya tara a tanki ya shiga ɗan mitsilin kewayen da ke tskar gidan dan yayi wanka. Kallon bayanshi na yi har ya fice daga ɗakin, tashi na yi tsaye ina jin yanda ƙafafuwana ke zugin azaba gasu sun kumbura sunyi suntum, ina jin zafi da azabar da suke min amma haka na takasu cikin rashin sanin abin da kemin ciwon, kaina tsaye na nufi hanyar toilet ɗin ko buta ban ɗauka ba na shige kaina tsaye. Wanka ya ke, kuma na ganshi amma ban damu da wanzuwarshi wajen ba na tsugunna gefe na tattare rigata da ruwan fitsari ya fara ɓatawa na tsula fitsarina, tashi na yi bayan na gama babu maganar tsarki na taka ta cikin fitsarin na wuce. "Mutane da yawa suna yi ma ta kallon mahaukaciya, sai de ba haka bane, ƙaddara ce ta zaɓi mayar da rayuwarta haka." Fes kalan Alhaji Sha'aban suka dawo ma shi lokacinda komi nashi ya tsaya da aiki na wucin gadi, rasa abin da zai yi yayi lokacin da na danna kaina cikin kewayen yana tsaka da wanka, hakanan ya ji yana ƙaryata zuciyarshi da take son aminta da cewa niɗin mahaukaciya ce, akwai wani abu wanda bai san minene ba da yagani a tattare da ni, shidai iya ganin mintunan da basu gaza biyu ba da yayi min cikin haske, sai ya yardarwa kanshi ni ba mahaukaciya bace, akwaide wani sarƙaƙen ƙulli dake dabaibaye da ni, wanda idan aka sakashi ya kunce zai sha matuƙar wahala kafin ya gane ainahin bakin zare, hakanan wa ta iriyar fargaba ta dirar ma shi, yayinda tsoro ya lulluɓe shi wanda shi kanshi bai san na minene ba, a gurguje ya idasa watsa ruwan wanda yake jin sanyinsu na ratsa gaɓɓan jikinshi suna sakar mashi kasala. Hannunshi riƙe ta fari ƙal ɗin towel yana goge ruwan jikinshi ya shiga ɗakin, sai yayi turus baki a sake yana kallona. Sallah nike yi hankalina a kwance, kuma anutse du iya kokonton mutum ba zai gane waje ɗaya da nayi kuskure ba, da mamaki ya idasa shiga ɗakin yana kallona, harna sallame, sai yayi kamar zaiyi min magana sai kuma ya fasa, dan shi ba mutum ne meson yawan magana ba, zai iya wuni zungur bai ce kanzil ba, koda yaushe bakinshi a rufe yake ruf Wani abu ɗaya da na yi wanda ya kusa sumar da shi da mamaki shine, ina gama sallar na kalleshi a ɗan fizge sannan nace. "Alhaji barka da kwana ka tashi lafiya." A mugun zabure ya ja da baya, yayinda sautin muryata ya dira a kunnuwansa a bazata, nan take wani abu ne nauyi ya motsa a ƙirjinsa, bai san ya buɗe raunanniyar muryarshi da yake ɓoyoba yace da ƙarfi. "Kkkekeke ke, kece!!! inmalillahi." Sai kuma ya zabura ya miƙe tsaye ya nufo ni kamar mayunwacin zaki, wa ta iriyar damƙa yayimin ya shiga girgizani da tsananin ƙarfi kuma a birkice kamar zautacce yake faɗin. "MAILAAHHHHHHHH! ki amsa min pls ke,,,, keece MAILLAH ɗin Tajjjjj ko?, nasani ai kece, baki gane ni ba, nine Taj ɗinki, wannan wanda kika taimaka kuma kika tafi kika barshi cikin kewa da nemanki, why' why zaki tafi ki barni, zuciyata ba zata iya jurewa ba, mi nayi maki da za ki nisanceni???."......✍️ TOFAH WATA SABUWAR, KU BIYO NI DAN JIN YANDA ZA'A ƘARKE🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️🤸🏻‍♀️ M STAR⭐..........✍️ Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/HbYjxC6ucFxK95Gxo1yN9i 🥀🌹MAILAAH🌹🥀 WRITE BY MARYAM STAR ⭐ƳAR BAIWAR JAJIRTATTU 💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️ *(J.W.A)* PAID BOOK BOOK ONE FREE PAGE بسم الله الرحمن الرحيم. ------------Chapter 7 & 8 Dummm, haka na ji kaina yayi sa'ilin da yake magana, du da fahimtar shi nike yi ba, amma akwai wani abu a tattare da shi wanda ke gilmawa a ƙwaƙwalwata, ina jin zafin yanda ya ke jijjiga jikina, da kuma yanda hannuwansa suka matse kafaɗuna, amma ban san mi zanyi ba, sai kawai na buɗe ƙaramin bakina ina kallonshi, kamar daga sama na ji ance. "Taj." da wa ta iriyar murya me tsananin rauni, na ji yanda sautin ya doka tare da bugun zuciyata, amma tunanina bai bani damar gane nice nai maganar ba. Da wani irin sauri Taj ya jefani a ƙirjinshi yai min murfi da hannayenshi sannan kuma kanshi daya kwantar akan kaina nawa kan, wasu irin zafafan hawaye na kwaranyowa daga idonshi, da wa ta iriyar murya me tsananin rauni ya ce. "MAILAAH!!!! ke ce ko, kece Mailaar Taj, miya faru da ke haka, Innalillahi wa'inna ilaihi raju'un, na sadaukar da lokacina ina neman ki, miyasa Mailaah, why kika zaɓi ki sabauta zukatanmu da ƙaddara ta haɗesu a waje guda, miyasa kika zaɓi ki tafi ki barni ba tare da sanina ba, kin mance alƙawarin da kika yi min cewa idan za ki tafi atare da ni za ki je, kin mance kince za ki kula da rayuwata ki ingantata, ko kin mance kince min zaki bani gata ki kula da rayuwa ta yanda zan mance rayuwata ta baya, ban taɓa son kowa ba sai ke, ban taɓa yarda da kowa ba sai ke ban taɓa jin zan iya rayuwa kamar yanda sauran mutane ke yin rayuwaba sai da kika shigo rayuwa, na rantse da tsarkin mulkin Allah bazan yi sake wajen kulawa da ke ba, ke ɗin tawa ce ni kaɗaina, bazan yafewa kaina ba idan wani abu ya cutar da ke." Haka ya dinga sakin sambatu yana kuka kamar ƙaramin yaro, yayinda rayuwar da muka gudanar a baya ke sake haskowa ta cikin idonshi. MIYE ALAƘAR MAILAAH DA TAJ A BAYA???. 2024-1-1 KATSINA MAKURƊA. Sanye yake cikin riga da wando na yadi, dogone sosai kuma yana ƴar ƙiba ba laifi, fari tas, amma yayi duhu da alama dauɗa ce danƙare a jikinshi, kayan jikinshi kansu kamar wanda aka tono daga rami yayi futu-futu, ƙafafuwanshi babu ko takalmi suna sunyi buɗuɗu da ƙura da dauɗa, yayinda ya isa daidai waje wa ta bishiya da ke kusa da ƙodama, zama yayi a wajen yai shiru yana ƙarewa ruwan da sanyinsu ke ratsa shi kallo, kafin ya fara jin ƙarar takun takalmanta, waɗanda a tsawon kwanaki biyu kenan da take zuwa wajen kullum da daddare ya haddace yanayin ƙararsu, du tako ɗaya da zata yi tana tunkaro wajen yana ji kamar tana takowa da nutsuwarshi ne. Kamar kullum fuskata a lulluɓe ta ke ruf cikin niƙabi, wanda bada son raina nike saka shi ba sai dan babu yanda zanyi, da taimakon hasken farin watan daya haske ko'ina nike ganin gabana, ina jin yanda sautin takalmin kwalbar ƙafata ke amsakuwa saboda shirun wajen. A daidai bakin ruwan na tsaya, ina jin nutsuwa na safko min, lumshe idona na yi dake rufe ina shaƙar ƙamshin ƙasar wajen, zan iya rantsuwa cewa tun daga ranar da ƙafata ta dira a garin ban taɓa samun nutsuwaba kwatankwacin wacce nike samu idan ina a bakin ruwa, nayi iya yina wajen ganin na hana kaina juyawa kallon ƙasar bishiyar, amma abu yaci tura, sai da na juya na kalli wajen, kamar kuma ko yaushe idan na kalli wajen gabana kan doka da ƙarfi, yanzuma ina iya jiyo sautin yanda zuciyata ke tsallen bugu kamar zata faso ƙirjina, a hankali na fara takawa zuwa inda yake a zaune yana kallon ƙafafuwana, kamar meson haddace wani abu. Zillo zuciyata ta yi a daidai lokacin da na tsugunna agabanshi ina kallon fuskarshi wacce nagaza gane yanayin da yake ciki, ban damu da yanda zuciyata ke dokawaba na tsinci bakina na faɗin. "Mi kake yi anan, inane gidanku, kaci abinci miyasa bakayi wanka ba, bakada lafiya ne ko wani ya biyoka?." na dinga jera mashi tambayoyi muryata a karye, danakai dubana zuwa ƙafarshi bansan sanda na zauna a ƙasa tare da kama ƙafar tashi wacce nike iya ganin dauɗar da tayi ta cikin hasken farin watan, idona na tsiyayar hawaye ta cikin niƙabina na ce. "Ya Allahu ya Rahama!!! a ina kaji ciwo, akwai zafi ko, sannu, sannu kaji bara inje gida in ɗauko maka magani, jirani mintuna biyu yanzu zan dawo." Na faɗi muryata na sarƙewa saboda kuka, a hankali na aje ƙafar tashi tare da tashi da hanzari na fara tafiya gudu-gudu, har naɗanyi nisa sai kuma na dawo da sauri ina faɗin. "Kaci abinci, ko kanajin yunwa bara in taho maka da tuwo ban saniba ko zaka iya ci tunda bakada lafiya." Sai kuma na sake juyawa na tafi da hanzari.....✍️ KU BIYO NI DAN JIN YANDA ZAMU WARWARE ZAREN SARƘAƘIYAR LABARIN. KUYI HAƘURI BA YAWA INA BUSY. MARYAM STAR⭐....✍️ An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://thausanovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.thausanovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels

Chapter 2 of 2