An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://thausanovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.thausanovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
🥀🌹MAILAAH🌹🥀
Follow the 🌹MARYAM STAR⭐⭐⭐ HAUSA NOVELS AND MORE 𝐶𝐻𝐴𝑁𝑁𝐸𝐿✍️📚📙✏️ channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133
🥀🌹𝑴𝑨𝑰𝑳𝑨𝑨𝑯🌹🥀
𝑳𝑨𝑩𝑨𝑹𝑰 𝑴𝑬 𝑪𝑰𝑲𝑬 𝑫𝑨
𝑭𝑨𝑫𝑨𝑲𝑨𝑹𝑾𝑨
𝒁𝑨𝑳𝑳𝑨𝑹 𝑪𝑨𝑲𝑾𝑨𝑲𝑰𝒀𝑨
𝑫𝑨 𝒁𝑨𝒁𝒁𝑨𝑭𝑨𝑹 𝑺𝑶𝒀𝑨𝒀𝒀𝑨 𝑴𝑬 𝑻𝑺𝑨𝒀𝑨𝑾𝑨 𝑨𝑲𝑶𝑲𝑶𝑵 𝑲𝑨𝑰
𝑾𝑹𝑰𝑻𝑬 𝑩𝒀
𝑴𝑨𝑹𝒀𝑨𝑴 𝑺𝑻𝑨𝑹⭐⭐
𝒀𝑨𝑹 𝑩𝑨𝑰𝑾𝑨𝑹 𝑱𝑨𝑱𝑰𝑹𝑻𝑨𝑻𝑻𝑼.
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
🦚🦋THE NOBLE WRITER'S TEAM🦋🦚
PAID BOOK
FREE PAGES
BOOK ONE
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
الْحَمْدُ لِلَّهِ نَحْمَدُهُ وَنَسْتَعِينُهُ وَنَسْتَغْفِرُهُ وَنَعُوذُ بِاللَّهِ مِنْ شُرُورِ أَنْفُسِنَا وَمِنْ سَيِّئَاتِ أَعْمَالِنَا مَنْ يَهْدِهِ اللَّهُ فَلَا مُضِلَّ لَهُ وَمَنْ يُضْلِلْ فَلَا هَادِيَ لَهُ وَأَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ وَأَنَّ مُحَمَّدًا صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ
---------Chapter 1 & 2
Miƙa na yi tare saka hannuna na rufe bakina da wa ta iriyar waskekiyar hamma ta kwace min ba tare dana shirya ba, ahankali na fara warware ƙafafuwana daga tankwasar da nai musu ta tsawon awanni, sai na ji sunyi min tsami har wa ta ƙara suke saki ƙas-ƙas, amma ahaka na daure na miƙe su a zaune, zura hannuna na yi tare da shafo daga dokin wuyana zuwa wuya, ina jin yanda ƙashin wajen kemin wanu iri saboda tsabar gajiya da duƙiyar da nayi, yawata idanuwa na nike a ko wane saƙo da lungu na ɗakin ina mamakin sanda har duhun dare ya mamaye ko ina ba tare dana ankara ba, sai na koma baya ina tariyo abin da ya faru.
Hayaniyar muryoyi mabanbanta ke tashi, kowace murya da abin da take faɗi, sai na girgiza kaina da naji yayimin wani irin nauyi kamar dutse, na tariye wurin hayaniyar da koma daidai inda najiyo muryar wacce nikewa kallon bango abar jinginata ke faɗin.
"Yo maraici hauka ne da za'a gallabi rayuwar baiwar Allah wacce bata ji ba bata gani ba, dan anga bata da wani zaɓi sai yanda rayuwa ta juyata shine za'abiyewa son zuciya acutar da ita, dan anga tana nuna kamar batason farin ciki ba shine za'a kashe ma ta rayuwa a tsaye, na rantse da girman Allah babu inda zanje imbar MAILAAH a wannan baƙin gidan me kama da akurkin kaji, dan kawai Allah ya jarabceta da ciwo sai a maidata kamar kamar mujiya a cikin mutane, wallahi ba zata zauna agidannan da sunan aure ba, sai na tafi da ita inda babu me sake jin ɗuriyarta.
Kyakkyawar fara tas ɗin matar da hutu da naira suka nuna jikinsu akanta ta faɗi tare da warware mayafinta ta ci ɗamara dashi a ƙugu ta na jijjiga jiki.
"Haba Hajiya Munubiya, dan Allah ki kyale musu yarinyarsu suyi yanda suke so da ita, Allah yasan zuciyarki da niyyar taimakonta da kike tun tana ƙanƙanuwa, yanzu ba lokacin tada jijiyoyin wuya ko yin faɗa bane, kawai kibita da fatan alkairi da addu'ai Allah yasa auren ya zama silar canzawar ƙaddararta, dan Allah kiyi haƙuri kowa yasan kina tsananin son MAILAAH kuma kin ɗauketa kamar ƴar cikinki, yanzu kiyi ma ta nasiha da huɗuba akan abin da ya shafi zaman aure."
"Hajiya Umma ba za ki gane yanda nike ji ba, ba za ki gane yanda nike tsananin tausayin MAILAAH ba, ina jin rashin dacewa akan banzatar da ita da ake yi dan kawai an ganta a haka, yarinya tun tana ƙarama take shan wahalar rayuwa har girmanta haka, sannan ace abiyewa son zuciya ayi ma ta irin wannan auren, ki kalli gidan da ke amsa sunan gidan mijinta, wallahi ko me gadin gidnsu yafi ƙarfin zama a irin wannan gidan bare ita." tana magana tana kuka, idanuwanta suka kaɗa sukai jawur, cikin hanshaƙan matan da ke tsaitsaye su na yatsine fuska wa ta taja dogon tsaki tare da faɗin.
"Mtswwwww aikin banza da wofi, kinsan kina jin tausayinta har haka kika gagara aura ma ta ɗaya daga cikin jiga-jigan ƴaƴanki, sai yanzu da waɗanɗa keda ita suka aurar za ki zo da guntuwar gulmarki kina kuka munafurci wai ke gamai tausayi." maganar da matar ta yi ta sake tunzura tunzurarra, wato Hajiya Munubiya, nan ta koma kanta ta fara gaggasa ma ta magana, matar itama ba daga baya ba, sai ta zage ta dinga macifa tare da zagin Hajiya Munubiya, nan take ɗan ƙaramin ɗakin amarya ya hauci aka hau faɗa.
Ina zaune akan ɗan ƙaramin madaidaicin gadon ɗakin, tun da aka zaunar da ni akai na duƙe ina kallon farin zanin da aka shimfiɗa, jin hayaniyarsu nike tana zaman lafiyar kwanyata, nan take jikina yahau tsuma, hannayena da ƙafafuwa suka hau karkarwa kamar wacce aka jonawa shocking, iya yanda hayaniyarsu ke ƙara yawa iya haka nike sake birkicewa, nan take da kwarara wa ta iriyar ƙara me shiga har tsakiyar kwanyar du wanda yaji ta, lokaci ɗaya na miƙe tsaye tare da soma neman guduwa ina kwarara ihu, kafin kace me, tuni rabi da kwatar mutanen ɗakin sunyi waje a mugun kiɗime, ina shirin fitowa naji anfizgeni baya tare da ɗagani saka sannan aka sake ni ƙasa na faɗi timmm, nan take kaina ya bugu da ƙasa, sai nayi wani shiru ya gifta, hayaniyar da nike ji anamin a cikin kai ta daina, sai duhu daya lulluɓe ganina duniyar tai min tsif kamar babu kowa acikinta.
Ban san tsawon wane lokaci na ɗauka bana hayyacina ba, sai farkawa na yi naga wacce muke kira da Anty Ummie riƙe da ƙaramar fanka a saitina tana yimin tofi, kamar kullum bance komi ba sai tashi da nayi na zauna inabin saura da kallo, wasu suce min sannu wasu kuma su kalleni su taɓe baki, sai da marice yayi sannan kowa yayimin sallama suka watse bayan sun lulluɓemin fuskata da farin mayafi, daga inda nike zaune ina iya jin yanda motocinsu ke tafiya ɗaya bayan ɗaya, duƙar da kaina na yi na shiga tunanin iska dan babu abin da nike iya tunawa sai de inyi shiru ko inyi kamar na zurfafa a tunani, haka nike kaina babu komi sai fanko.
A hankali na sauke ƙafafuwa zuwa ƙasan gado, sai nayi saurin janyesu jin na taka wani abu me sulɓi, haka nike inada wuyar sabo musamman da sababbin abubuwa, rayuwa tafi yi min sauƙi a ɗakina na gidanmu, du bayan lokaci ana yin aiki da sauye-sauyen abubuwa, amma bani yarda ayi a ɗakina, du randa aka sauyamin wani abu sai na daɗe ban sake a ɗakinba, haka zanta zama a takure kamar raƙumi a keji.
Har nakoma na sake jingina sai kuma na sake tashi tunowa da ai Sallah nike so inyi, ahankali na sauko duka ƙafafuwa tare da yunƙura kamar me tsoron taka ƙasa na miƙe tsaye akan ƙafafuwana da nike jinsu kamar ba ajikina suke ba saboda tsami da ciwon da suke yi, ahankali na shiga takasu harna fice daga cikin ɗakin wanda duhu ya mamaye babu haske ko kaɗan, tsayawa nayi ina ƙarewa tsakar gidan kallon badan komi ba sai dan tap da nike nema, wani ɗan ƙaramin tanki na gani a kusa dashi ga famfo shima ƙarami, sai na tsugunna nayi fitsarin da cika min mara, sannan nai tsarki tare da ɗauro alwala, du sai da na jiƙe farar lafayar da ka naɗamin, a haka na koma ɗaki ina jina wani daban, sai tin da Anty Ummie ta nuna inda makunin haske yake kafin tafiyarsu na kalla, sai na miƙa hannuna bayan na rintse idanuwa gam na kunna haske, da sauri nakai zaune ina shesheka lokacin da nike ji a jikina farin hasken ya gauraye ko ina, kuma da alama hasken me ƙarfi ne sosai, nakai kusan mintuna arba'in ahaka ba tare dana tashi kona buɗe idona ba, sai da hasken yabi jikina, du wani gashi daya miƙe sai da ya kwanta sannan na tashi, jakar da nike aje kayan sallahta a ciki na gani agefe tare da wasu sabbin akwatinan, ban tsaya kallon komi dake wajen ba na kwalle kayana na saka rigar sallah da abayata.
Zazzaune suke agaban wanda daga gani babbane ko me faɗa aji, nasiha yake musu me ratsa jiki, fuskar kowanensu aɗan maraurace, amma banda shi, zaune yake a tsakiyarsu baice komi ba, kuma ko kaɗa kai alamun amsawa bayayi kamar yanda sauran suke, aduƙe yake ba'a iya ganin ainahin fuskarshi, saboda baƙi wuluk ɗin gashin kanshi daya zubo har gaban fuskarshi, ganin sauran sun miƙe ya saka shima ya miƙe, ba tare daya ko kalli kowa ba ya saka kai gaba ya juya ya kama tafiya, tafiya yake cike da sadaukantaka kuma cikin isa da ƙasaita kamar wani jinin sarauta, matasane biye dashi a baya har suka zo daidai inda ya tsaya a ƙofar wani ɗan ƙaramin gida, gidanda a ido zaka iya hango ƙanƙantar da zaiyi a ciki, tsayawa yai saitin ƙofar daya buɗe, ya juyo da baya yana kallon matasan da birkitattun idanuwansa waɗanda suke sheƙi a cikin hasken farin watan, ganin yanda ya tsaresu da ido yana kallo, sai kawai suka juya suka tafi, sai da sukai mashi nisa a ido sannan ya juya ya shiga gidan ya kulle.
Kanshi tsaye ya nufi kwalli ɗayan ɗakin da ke gidan ya shiga, ɗan turus yayi ganin yanda duhu ya mamaye ko ina, ba tare da jinkiri ba yashiga laluben makunin fitilar ɗakin dake jikin bango, bai yi aune ba ya ji ya sauke ƙafarshi akan wani abu lallausa kuma me ɗumi, da hanzari ya ja da baya, sai yai rashin sa'a ƙafarshi ta zame, ki kake timm ya faɗa akan wani abu me laushi kuma tattausa wanda ke fitar da lumfashi da alama hallitace me rai a wajen.
Tun shigowarshi ina iya ganinshi, musamman da yake sanye cikin farare tas ɗin tufafi masu haske, naga sanda ya ke ta laluben bango da alama abu yake nema, ban motsa daga inda nike zaune ba, sai de na ɗaga kaina acikin duhun na dubi wajen da swetch ɗin ya ke, ban sa'ilin da ya ƙaraso inda nike ba, daidai saitin ƙafata, juyowar da zanyi dai kawai naji lallausa tafi me tsananin taushi ya taka ƙafata, ba halina bane zabura ko tsorata aduk lokacin da naga wani abu wanda zai cutar da ni, sam ni bana tsorata kamar sauran mutane, sai de in shiga wani yanayi me wuyar fassara, yanayin da ke tsorata du wanda ya raɓe ni.
Second ɗaya, biyu, uku, har zuwa sakannin goma banji abin da ya tausheni me taushi da tsananin nauyi ya ɗagani ba, can cikin maƙoshi na furta sauti, "auch" saboda ji danayi zuciyata na zullo har tana ƙoƙari fucewa ta maƙogarona, wani irin luguden duka take min lokcin da naji hannunshi na laluben jikina kamar meson tantance wani abu, saurin tallafe hannunshi na yi ina girgiza kai kamar yana gani na, ina jin yanda ya sauke wa ta ƙaƙƙarfar ajiyar, sai kuma ya janye jikinshi gefe ya kwanta a ƙasa, wani irin shiru marar hayaniya ne ya mamaye ɗakin yayinda sautin komi ya ɗauke saina shaƙa da fesarwar iskar numfarfashinmu, mu kanmu bamusan iya adadin tsawon lokacin da muka kwashe a haka ba.....✍️
SOMIN TAƁI KENAN A CIKIN LABARI ME TAKEN MAILAAH KU BIYO NI DAN JIN YANDA ZATA ƘARKE
Follow the 🌹MARYAM STAR⭐⭐⭐ HAUSA NOVELS AND MORE 𝐶𝐻𝐴𝑁𝑁𝐸𝐿✍️📚📙✏️ channel on WhatsApp: https://whatsapp.com/channel/0029Vb5xdoy2975BcTM5m133
🥀🌹𝑴𝑨𝑰𝑳𝑨𝑨𝑯🌹🥀
𝑾𝑹𝑰𝑻𝑬 𝑩𝒀
𝑴𝑨𝑹𝒀𝑨𝑴 𝑺𝑻𝑨𝑹⭐⭐
𝒀𝑨𝑹 𝑩𝑨𝑰𝑾𝑨𝑹 𝑱𝑨𝑱𝑰𝑹𝑻𝑨𝑻𝑻𝑼.
💪 *JAJIRTATTU WRITER'S ASSOCIATION*💪 ✍️
*(J.W.A)*
PAID BOOK
FREE PAGES
BOOK ONE
بِسْمِ اللَّهِ الرَّحْمَٰنِ الرَّحِيمِ
الْحَمْدُ لِلَّهِ نَحْمَدُهُ وَنَسْتَعِينُهُ وَنَسْتَغْفِرُهُ وَنَعُوذُ بِاللَّهِ مِنْ شُرُورِ أَنْفُسِنَا وَمِنْ سَيِّئَاتِ أَعْمَالِنَا مَنْ يَهْدِهِ اللَّهُ فَلَا مُضِلَّ لَهُ وَمَنْ يُضْلِلْ فَلَا هَادِيَ لَهُ وَأَشْهَدُ أَنْ لَا إِلَهَ إِلَّا اللَّهُ وَحْدَهُ لَا شَرِيكَ لَهُ وَأَنَّ مُحَمَّدًا صَلَّى اللَّهُ عَلَيْهِ وَسَلَّمَ عَبْدُهُ وَرَسُولُهُ
---------Chapter 3 & 4
Ban saniba ko ƙosawa yai da yanayin sai jin motsinshi nayi ya tashi, fita yayi zuwa waje kafin ya dawo hannunshi riƙe da wani abu me haske, banyi aune ba sai ji nayi anhaske saitin inda nike a zaune, a mugun zabure na miƙe tsaye jikina na karkarwa, cikin ƴan sakanni ƙalila du nabi na ruɗe inata faman kare farar fuskata da hasken ke neman nakasa min ido, ja da baya na yi ganin yanda yake sake tunkaro ni da hasken, yaraf na faɗa akan gado inata faman shesheka, lokaci ɗaya hasken ya fitilar da yasamu damar kunnawa ya bibaye ɗakin, direct ya sauke birkitattun idanuwansa akaina, sai wasu maganganu suka shiga yi mashi amsa kuwa cikin kunne.
"Haske!!!, ka kiyaye kunna haske kai tsaye a inda ta ke, bata son haske, yana kassara zaman lafiyarta, kuma yana zautar da ƙaramar ƙwaƙwalwarta, haske ne matakin farko da ke fara rikita tunaninta, takan shiga tsoro da firgici a lokacin da haske ya haskata kai tsaye ba tare da dabara ba."
Ƙaramar ajiyar zuciya ya sauke, kafin a hankali ya shiga taka dogayen ƙafafuwansa har ya ƙaraso inda nike zaune dafe da kaina inata faman shesheka idanuwana a warwaje, wani itin tartsatsin haske ya gilma ta cikin kaina lokacin da na ɗago da fuskata wacce tafara tirewa zuwa kalar jah, saukar idanuwa a cikin nashi birkitattun idanuwa wanda nike hango sheƙi da walwali wani kalar rauni, raunine irina na tsoro da fargabar faruwar wani abu, ban gama tantace inda kaina yake ba kawau naji na tafi luuuu duniyar na juya min, daga nan ban sake sanin komi ba, duhun da yake lulluɓe cikin ƙaddarar rayuwata ya ratsa da masarrafar tunani da ganina, shirun da ke cutar da tuhina ya ziyarceni ba tare dana shiryawa hakanba.
Jijiyoyine ruɗu-ruɗu duka firfito a gaban goshi da kanshi, yayinda gumi ke tsatstsafo mashi ta kowace hudar gashi dake jikin fatarshi, da iya ƙarfin da Allah ya azurtashi yake riƙe da kafaɗuna yana jijjigani da tsananin ƙarfi ko zan dawo hayyacina, amma ina, a maimakon ihu da gurnani me ban tsoro da nacika gidan da shi, sai kaina ya shiga lauyewa gefe da gefe, wani irin fari tas ɗin yawu ya dinga gangarowa daga bakina, nan take jikina ya saki sautina ya ɗauke dif jikina yai wani irin sanyi ƙalau, a mugun tsorace ya sake ni nai baya bakinshi a buɗe idanuwan a waje ya dafe kanshi da ƙarfi sannan ya furta. "MAILAAHHHHHHHHHH!!!!!!!."
Da wani irin hanzari magidancin da ke zaune akan sallaya yana tasbihi ya miƙe, lokaci ɗaya shaƙuwa ta kama shi, cikin sarkewar murya ya ke faɗi bayan ya dafe saitin zuciyarshi dake barazanr tarwatsewa.
"MAILAAH, innalillahi wa'inna ilaihi raju'un, hasbunallahu wani'imal wakil, yah Rahaman." sai kuma ya duƙe a wajen wasu irin zafafan hawaye na ɓalle mashi, ga kuka da zafin zuciya sannan ga shaƙuwar data addabeshi.
Wannan shine karo na babu adadi datai juyi kamar me barci, ranta a mugun ɓace bayan ta buɗe ido kaɗan ta ga har lokacin zaune ya ke yana tasbihi, ji take kamar ta tashi ta shaƙoshi ta kwantar a gefenta, sai babu adadi take baƙin ciki da zagayowar ranar a matsayin ranar girkinta, da tasan haka abin zai juye da bata yi wannan tafiyarba, ta na tsaka da tunani mahita sai ta ji sallatinshi, ba tare da ɓata lokaci ba har tana mancewa da ashe barci take ta miƙe zumbur tare da ƙarasawa zuwa inda yake a durƙushe yana saƙuwa, hannunshi a saitin zuciyarshi, idan ta ce batai farin ciki da hakan ba to ta gillara ƙarya, cike da kwarewa da sanin makamar aiki tashiga bashi taimakon gaugawa, bayan ta bashi ruwa me matsakaicin sanyi ta kwantar dashi akan gado da kyar, sannan ta dallara mashi allurar barci me tsananin ƙarfi, bai haura ƴan sakanni ba barci yai awon gaba da shi, cike da murna ta fice ta na jin daɗin yanda ta samu wannan damar, kanta tsaye ta haura samman dogon stirs ɗin dake fitar da dum light a gefen matattakalarshi, bayan ta shiga sai da ta tabbatar da ta rufe ko ina, sannan ta sunkuya a ƙasan gaɗo ta janyo wani ɗan ƙaramin jan akwati, nan take sarka me tsananin tsada ta bayyana, cike da nishaɗi ta shafa bayan sarƙar sai sarƙar ta fara rikiɗewa tana sauyawa yayinda hayaƙi fari fat ya cike ɗakin ta yanda ba'a iya ganin komi, can bayan wasu ƴan mintuna hayaƙin ya soma raguwa ahankali har ya ɓace ɓat, abin mamaki sai wannan matar ta bayyana zaune, farar fuskarta ta ƙara haske, yayinda hancinta ya ƙara tsayi kamar anja shi, laɓanta suka sake rinewa zuwan dark pink, sai ɗaukar ido ta ke, ga wani gwarjini na bala'i dake bayyane akan fuskarta, cikin ƙanƙanin lokaci kyawunta ya linku sosai fiye da yanda ta shigo ɗakin.
Barci ya ke amma zuciyarshi naga ƴarshi jininshi, wacce yake zargin kanshi akan wofintar da rayuwarta, da ace ya rungumeta ya karɓeta da lalurarta, da rayuwa ba zatai ma ta ƙunci irin haka ba, da ace ya tsaya tsayin daka wajen kula da lafiyarta tare da juriyar nema ma ta magani, da yanzu wataƙila ta samu lafiya, yana matuƙar son ƴarshi MAILAAH, amma bai san dalilinda yasa ya kasa kulawa da ita ba, wani bin yakan mance da rayuwarta sai idan anyi zancenta ko Allah yasa ta fito waje su haɗu, yakan kalli tsakiyar jemamun idanuwanta waɗanda ruwa ke kwance masu sheƙi kamar hawaye, tsaf ya ke karantar rauni da kuma jarumtarta a cikin idonta, yakanji ya tsani kanshi daya kasa inganta rayuwarta, idan yayi niyar janyota jikinshi don ya kyautata ma ta, kuma ya zama inniwa a gareta, sai wa ta doguwar katanga wacce yayiwa laƙani da katangar ƙaddara ta gifta a tsakaninsu, taƙi ɗaya bazai ƙaraba daga inda yake sai de ya farka yaganshi kwance ana saka ma shi drip, tun abin na damunshi harya rasa sukuni har takai daya sadaƙar, yakuma cire hannunshi gaba ɗaya cikin safgar MAILAAH dan yana so ya tsira da lafiyarshi, badan abin baya nuƙurƙusar zuciyarshi ba, kawai de ya janye jikinsh daga ita ne dan samar musu da nutsuwa daga shi har ita.
Bai taɓa zartar da hukuncin da yai danasanin ba irin aurar da MAILAAH, bai samu halartar ɗaurin aurenba, saboda ciwon zuciya daya addabeshi a safiyar ranar, gaba ɗaya guyagunshi sun gama sakewa akan cakuɗaɗɗun al'amurranda ke faruwa da rayuwar ƴarshi, muddin zaiyi hwaɓɓasa akan yi ma ta wani abu babu shakka sai yaji a jikinsa, sau dayawa zuciyarshi kanyi rawa akanta, har yakan ji kamar ya yarda da zancen da ake faɗi akanta na lallai ta haɗa jinsi da Aljannu, amma idan ya tuno yanda yai rayuwa tare da mahaifiyar sai ya tuhumi kanshi, mahaifiyarta itace wadda ta sadaukar da komi nata, ta sallama rayuwarta akanshi, idan zaiyi tunani iri ɗaya da sauran mutane tabbas ya zama butulu, gaba ɗaya kanshi a kulle yake, yanada buƙatar sarari domin ya nutsu yayi tunanin komi tun daga tushe, sai de bai da wannan lokacin, lokaci yayi ƙaranci a gareshi, idan yace zai matsanta kuma, to abubuwane masu tarin yawa zasu ɓullo marasa daɗi.
Haka yaita tunane-tunane har lokacinda barci ya sake ɗauke shi.
Tunda gari ya waye ta caɓa uban ado, gwala-gwalai ne keta walwali a jikinta, ga wani haske da kyau da tayi kamar wa ta sarauniya, ba tun yau ba, ba jiya ba, ba shekaran jiya ba, tun shekaru masu dama da suka shuɗe zuciyoyin ilahirin mazauna gidan ALHAJI SHA'ABAN ke rawa akan matarshi ta biyu me suna SALIMA, ba kyawunta da kullum yake ƙaruwa ne ke rikita tunaninsu ba, hatta izza da kwarjinin da take da shi abin zargi ne a wajensu, amma kamar an saka kwaɗo an kulle bakunansu, haka suka kasa tattauna zancen koda a tsakaninsu ne.
Kamar yanda al'adar gidan ta ke na haɗuwa kowace safiya a ranakun aiki tun ƙarfe bakwai domin karyawa, yauma hakan ce ta faru, rankatakaf iyala Alhaji Sha'aban wanda suke kira da Alhaji ne zazzaune akan dogon dinning table, mecin mutane sama da ashirin, kowa ka gani daga matan har mazan shirye suke a cikin shirin fita aiki, yara kuma kowanne sanye da uniform, sai hayaniya ke tashi kamar gidan biki, da zuwanta wajen kowa yai tsit, hatta yaran du suka kama bakunansu suka nutsu, Hajiya Salima ta saki murmushi cike da ƙasaita sannan cikin izza da taƙama ta zauna akan kujerar da aka ware dan zamanta ita kaɗai, lokaci ɗaya suka haɗe bakunansu wajen gaisar da ita, sai da ta ƙare musu kallo one by one, sannan ta saki murmushin ƙasaita, tai amsawa ɗaya, daga nan kowa ya shiga sarving kanshi, tsit dinning ɗin yayi bakajin komi sai ƙarar cokulla, fuskokin mazauna wajen du sun nuna alamun ƙosawa da takura, muddin Hajiya Salima ta bayyana a waje wannan yanayin ne zai bayyan a fuskokinsu, basa sakew sai ta wuce ta basu waje, wannan ya saka idan ba dole ba babu me zama a kusa da inda ta ke, ita a wajenta tana ganin hakan kamar kwarjini ne, yayinda su kuma suke ɗaukar hakan a matsayin takurawa.
☆☆☆☆☆☆☆☆☆
Dummmm!! haka na ji kaina na sarawa da tsananin ƙarfi, yayinda na saka hannayena na dafe kan ina jujuyashi cike da azaba, idan akwai abin da nikewa zullumi, bai wuce gusowar dare ba, ni kaina bana iya tantance ainahin abin da nike ji, amma dazarar duhun dare ya kusanto, ina shiga matsanancin tashin hankali, zafin abu biyu kacal na sani, daga