Share this page
2 / 3
yar'iskar yarinyar can, ni sai yanzu ma na kejin haushin bata ita da nayi, ka da kiso kiga rashin mutuncin da tamin yau kawai don na makara wajan sallah." Sakin baki zainab ta yi ta na kallon ta,wani bakin ciki da haushi suka kama ta. "Ai tamin dai-dai kin san na fita bukatar waya, amma kika dauka kika bata ga shi nan ta maki halin, idan na ce bakin ciki ta ke dake ki ƙi yarda ai ga shi nan kin fara gani yanzu saboda Allah miye don kinyi lattin sallah?, ke ni fa idan ta riga da ta wuce bana ramata idan na yi a lokacin da akeyi nayi kokari ai." Daga ganin yadda take maganar cike da haushi take yinta. "Haba kawata ki sha kurumin ki mana kema kinsan tunda na samu kamar kin samu ne, sabuwa dal zan saya miki kedai bari Ahmad ya fara sakin kaya." Cikin murmushi ta ida maganar. "Yauwa na manta cikin satin nan Al'amin zai turo a yi tambaya." "To kuma. Uhm! Allah ya kaimu". Daga gani yarda ta yi maganar abin beyi mata dadi ba. Wayar da ke hannunta ce ta dauki kara alamar kira sai da ta diba sikirin din sannan ta mikama Zahra. "Mai kyau ya kike, ya kika tashi?" "Lafiya ƙalau." Ta amsa a yangan ce. "Kiyi hakuri ban kira ki na ji ya kike ba, tun dazu sai yanzu na tashi shiyasa". "Uhm! Lallai kana sha'anin ka, bacci har sha biyu na rana?" "Kai mai kyau ina sha'ani anan,da dai a ce kina kusa da ni ne da bacci sai yafi dadi". "Haka dai ka ce" "Haka zancen yake dai, ya maganar mu?". "Ai ba yau mu ka yi da kai ba." "Na kasa hakura ne har sai lokacin da kika dibar min ya yi, wani irin so na ke miki mai wuyar fassara, amma ke bakya ganewa." "Ina ganewa mana. Yanzu dai idan kana kana da lokaci kazo mu hadu in da muka hadu jiya, sai kazo sannan zan faɗa maka shawarar da na yanke." "Yanzu kuwa zaki ganni, bani nan da rabin". "Tai shike nan sai na ganka."ta katse wayar ta na dariya. 2018 [6/28, 8:44 PM] ‪+234 806 858 0203‬: ⚜🔱 *BAHAGON TUNANI*⚜🔱 . 👨🏻‍💻👩🏻‍💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร. _Rubutawa_✍🏼 *Badeeyerh Beauty Queen* *Da* *Fauziyya L. Ammany* _Labari_ *Queen Mermue* Ѕα∂αυкαяωα gαяєкυ мα ¢нєяιє Мυмуи ιℓнαм υммυ яαнмα υммυ ѕα∂єєq αѕєєуα *7* Hira suka ci gaba dayi ita da Zainab, suna nuna tsantsar farin cikin samun Ahmad cikin rayuwar su. Har sanda ya karaso ya kira ta, tare da Zainab suka fito bayan ta mai kwatancen inda take. Tun da ta taho yake kare mata kallo cikin tsantsar sha'awarta, yana fatan samun dama a kanta koda sau daya ne tunda ya lura ta na da rawar kai. "Amincin Allah a gareki kyakyawa matar Ahmad." cewar Ahmad. Murmushi Zahra ta yi aranta tana fadin"Matar Al'ameen dai." a fili ta yi murmushi tace "Barka da zuwa abincin ruhina, fatan ka iso lafiya?" Zainab ta kalli Zahra da mamaki jin kalamanta, amma ba halin magana don haka ta yi murmushi itama tare da fadin"Barka da zuwa Ahmad na Zahra." Ya kuwa ji dadin haka duba da yanda murmushin kyakyawar fuskar shi ke kara yawa "Yauwa kawar mu ya gida da mutan gidan?" "Suna lafiya kalau." Ta amsa ta na murmushi. "Madallah ya sunan kawar tamu?" "Zainab sunana." "Gaskiya naji dadi ga Zahra ga Zainab kuma kawayen juna." ya fadi yana kallon Zahra dake danne-danne a wayarta. Ita kuwa Zainab ji ta yi dama Ita ke da Ahmad, lokaci daya ta fada sonsa domin kyakyawa ne ajin karshe ga kuma alamun kudi duba da kalar motarsa. Gaskiya ya tafi da imaninta irinshi take fatan samu irin mazan nobel kenan, "Ashe haka ya hadu wannan banzar take cewa ba ta sanshi?" ta fadi a zuciya tana kare mai kallo. Ganin hankalinshi nakan Zahra suna hira yasa taji wani takaici a ranta, amma ta danne ta dube su"Tantabaro zan tafi tunda an manta dani." "Haba mana Zainab ki tsaya." cewar Zahra. "In tsaya mene bayan Laila da majnun sun hadu?" ta fadi tana yake. "To kawar mu mun gode, ga wannan." ya mika mata rafar yan dari biyar guda biyu. Ta amsa cikin farin ciki ta ce" Na gode Ahmad, sai kinzo." ta wuce tana boye kudinta kar mamanta ta gani. Hira suka sha irinta masoya, amma Zahra badan tana jin dadin hirar ba saboda tana jin kalaman Al'ameen dinta a ranta sunfi na wannan dadi, dan haka biye mai kawai take daga karshe ta mai sallama zata tafi. Ya dauko wasu ledoji da tambarin sahad store a jiki guda biyu ya mika mata da bandir din kudi. Ta amsa ba tare data nuna d'okinta akai ba cike da jan aji ta mai godiya ta shige gidan su Zainab. Murmushi Ahmad ya yi"Zahra a hankali zan samu abun da na ke nema tare dake." ya fadi yana shafar sajen dake kara fito da kyawunsa. Zahra na shiga ta zube kan katifar Zainab cikin murna ta hau bude ledojin, kayan sawa ne irin dogayen Arabian dinnan masu tsada guda biyar, daya ledar kuma kayan make up ne da yawa a ciki sai daya ledar kayan ciye-ciye ne ciki. Murna Zahra kamar tai hauka yau ita ce da irin wadannan kayan wanda take ji a nobel yau ta samu. "Ke Zainab zo kiga kayan mana kin wani kwanta." Zainab dake kwance gefen Zahra cikin tunanin Ahmad ta ya mutsa fuska ta ce"Wanda baki so meye abun murna a kayan sa?" "Malama idan zaki duba ki tashi, danni gida zan wuce." Zahra ta mayar mata da amsa tana cin cakulet. Tabe baki Zainab ta yi cikin kishi ta duba kayan, ta na fatan dama na tane, amma zuciyarta na karfafa mata gwiwa kan cewa zata samu Ahmad tunda Zahra bata sonshi. Cikin kwarin gwiwa ta yi murmushi"Zahra kin dace fa nayi murna da kayan sosai." Zahra dake aikin chart ta kalleta ta ce"Dauki riga daya a ciki." "To na gode k'awata" ta dauka a ranta tana fadin "Nan gaba sai dai na baki yarinya nafi karfin ki bani." Zahra kuwa komai sai da ta dibar ma Zainab kasancewarta ba mai rowa ba, sannan ta wuce gida ta na murna tasan yau ita 'yar gata ce wurin gwoggo. Haka kuwa ta na zuwa ta dire ma Gwoggo kayan gabanta. Gwoggo ta ce"Wannan kaya kuma daga ina?" Tana bude ledar da Zahra ta aje ma ta. Zahra dake chartin ta dube yanda Gwoggo ke washe hakora ta ce"Ahmad ne ya kawo min a gidan su Zainab." Da murna Gwoggo ta dinga duba kayan ta na fadin "Kinyi farin jini Zahra kin dace a kira ki mai sa'a, amma wancan matsiyacin yaron ya hure maki kunne." Da sauri Zahra ta mike ta shige dak'i tana fadin"Zaki sha mamaki Gwoggo idan Al'ameen ya yi kudi, kuma gaskiya ki daina zagin shi." "Shegiya na zage shi din mara mutunci me ake da malamin makaranta" Nana dake kwance kan kujerar dak'in su ta yi dariya tana fadin"komin shirin da suke sai anji kansu kullum suna musayar kalamai kan bawan Allah." Zahra ta dibe riga biyu taba Nana sauran kayan, ta amsa ta yi godiya kawai don bata tunanin zata sanya. Da daddare Al'ameen yazo, ya aika a kirata. Taci kwalliya cikin rigar ta yi kyau sosai ga kamshin turare na tashi ta fice. Tanajin Gwoggo na fadin "Andai ji kunya, wanda ya siyo baiga kwalliyar ba sai wancan talakan." Ba ta juyo ba ta wuce abun ta, cike da takunta na kasaita. 2018 [6/28, 8:44 PM] ‪+234 806 858 0203‬: ⚜🔱 *BAHAGON TUNANI*⚜🔱 . 👨🏻‍💻👩🏻‍💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร. _Rubutawa_✍🏼 *Badeeyerh Beauty Queen* *Da* *Fauziyya L. Ammany* _Labari_ *Queen Mermue* dedιcαтed тo zυωαιrα мαdαrα мαмαn нαneeғαн. υωαr gιdα ĸυмα αмαryα тαĸα dα lαғιyα тαωαn, ĸe тα мυѕαммαn ce gαrenι ιnα yιnĸι ѕoѕαι α rαyυωα Allαн yα вαr мυ тαre αмeen.❤❤❤ 8 Ta na fita ta same shi jikin tsohon mashin da ya saba zuwa dashi. Murmushi ta yi wanda ya kara fiddo kyawunta. "Barka da fitowa sarauniyar Al'ameen." "Barka da zuwa sarkin Zahra." ta mayar mishi. Yana kallonta ta yi mai kyau sosai ga kamshin turarenta dake tashi yadan ya mutsa fuska yace"Da alama sarauniya bata san farin cikin sarkinta." "Tuba nake sarkin Zahra, ina fatan ban yi maka laifi ba?" "Kinyi mana tunda bakijin maganata kan sanya turare mai yawa idan zaki fito." Ajiyar zuciya ta sauke ta na murmushi ta ce"Ayafe ni saraki duk murnan zuwa gareka ne, amma bazan kara ba." Shima murmushi ya mata domin ta burgeshi, yana kaunar ta. Nan suka dora hira har da zancen zuwa wurin dangin mahaifinta da baban Nana ya ce za suyi gobe. Taji dadi ta kusa zama mallakin abincin ruhinta don haka ta zage tana nuna mai murnarta cikin kunya. Haka suka gama hira ya bata dubu biyu da sunan tasa kati. "Al'ameen kai nake so ba kudin ka ba, don haka ka barshi nagode." Yaji dadin kalamanta amma ya da ke "Zahra kin raina ko?" "Wallahi Al'ameen ban raina ba, kawai bana bukatar kudin kane domin kaima baka dasu ga umma da Khadija duk kana dawainiya dasu." "Na gode Zahra ina alfahari da samun mace irin ki nasan ko ban dashi zaki zauna dani." "Karka damu kaima zaka yi kudi ai, domin duk nobel din dana karanta a karshe jarumin nayin kudi idan baya dasu da farko kuma a...." hannu ya daga mata, wanda yasa tayin shiru bata karasa maganar ba. "Ya isa haka Zahra, na rokeki ki daina daukar wannan rayuwar don Allah." "To sarakin Zahra na daina, kayi murmushi mana kafin ka tafi." Murmushin kuwa ya yi yana duban kyakyawar fuskarta har sukai sallama ya tafi. ******* ***** Rayuwar jin dadi sosai Ahmad keyi ma Zahra duk abun da tace shi zai mata. Ta canza sosai ta koma babbar yarinya ga kyau ga aji, kudi kuwa sosai take amsa tana siyayyar kayan dak'inta. Duk abun data gani koda bata san amfanin shi ba muddin an fadeshi cikin kayan dak'i a nobel sai ta siya. Shi kuma Ahmad yana ta binta a sannu domin kaiwa ga manufar shi. Zainab na nan da dakon soyayyar Ahmad tana kuma jin zafin yanda duk suka hadu yake yi ma Zahra musamman kalar soyayyar sa mai tsayawa arai. Zahra cikin watanni biyu ta canza komai na dak'in kwanan su, sai dai ta fasa yin shafe-shafe sanadin wani Nobel data karanta taga jarumar ta mutu sanadin shafe-shafe ta had'u da ciwon fata, daga nan tace ta fasa itama gara ta zauna da kalarta mai kyau. Su Al'ameen sunje an basu auren Zahra nan da wata biyu. Murna shida Zahra baa magana. Sai shirin aure take yi na kece raini da makudin kudin da Ahmad ke bata. Ta shirya sosai kan bikin, kaya kuwa harta gaji da dinkawa. Akwati hudu ta siya ma kanta harda kananan kaya, tana karantawa cewar jarumar littafin bata maimaita kayan sawa tsawon sati daya, don haka itama ta shirya. Sosai komai yake tafiya yanda take so, duk da habaicin da Gwoggo ke mata kullum rana kan auren talaka da barin mai kudi. Ita dai ido take sanya ma Gwoggo ko kuma tace"Zaki sha mamaki idan Al'ameen ya yi kudi." Nana kuwa murna take yanda Zahra ta dage sai Al'ameen, tasan yar'uwarta ta yi dace da mijin kwarai don haka da ita akeyin komai na shirye-shiryen biki. Kwanci tashi ba wuya, yau bikin Zahra saura sati uku don haka ta shirya fadi ma Ahmad zata yi aure. Ta kira shi tana son ganin sa. Ta zauna zaman jiran sa amma bai zoba, kuma ta kira wayarsa a kashe. Wasa-wasa har tsawon sati ba Ahmad ba labari, tun tana ganin zai zo harta fara tunanin ba lafiya ga wayarsa bata shiga. Yau bikin saura kwana uku, ana ta shirye-shiryen kauye day data hada. Zainab ta shigo duk t rame kamar mara lafiya tace"Zahra kin kuwa fadi ma Ahmad?" "A'a wayarsa bata shiga wallahi nima naso muyi sallama dashi." Zainab ta kalle ta "Don Allah ki kara gwada kira mana." Da mamaki Zahra ke kallonta tace" Tsaya Zainab meye damuwarki da Ahmad ne?" "Dame ya faru, dan nace ki kira sa?, kawai ina miki tuni ne karki manta alheri." cewar Zainab tana daure fuska, amma kasan ranta damuwa ce fal ta rashin Ahmad. Tabe baki Zahra ta yi tace"oho! Kedai kika sani 'yanmata"ta dauki wayar tana kiran Ahmad, aikuwa wayar ta fara amsawa alamun kiran yaje. "Hello" aka fadi. "Hello Ahmad ne?"Zahra ta tambaya. "A'a abokin sane." "Don Allah ina Ahmad din yake?" "Ayya ai Ahmad yana kasar malesia ba lafiya tsawon sati uku ya yi hatsari,amma da sauki sunma kusa dawowa." "Innalillahi wa inna ilaihir raji'un, Allah sarki Ahmad Ubangiji ya bashi lafiya ya sanya kaffara ne." "Ameen ya Allah mun gode." "Yauwa idan da hali ka fada mishi Zahra ce." "Insha Allah zan isar da sakon."sukai sallama, taji ba dadi sosai balle Zainab da tana jin duk abun da aka ce kamar zata yi kuka. Zahra ta dinga kallonta da mamaki wannan sauyin, amma da yake bata fadi mata ba ita ma saita share ta cigaba da hidimar aurenta. Yau juma'a aka daura auren Zahra da Al'ameen a garin su wurin kanin mahaifinta, kuma a ranar mahaifiyarta tazo garin. Nasiha sosai Maman ta yi mata kan zaman aure da kuma hakuri kan dukkan yanayin data samu kanta ciki. Gwoggo ta yi mata gyaran jiki sosai kuma ta saduda tunda har an daura aure. Gidan su Al'ameen aka kaita dak'inta ciki da falo sai kishin a gefe, bayi kuma na gidan ne gaba daya, dak'in ya yi ba laifi ta siya kayan k'awa sosai da kuma wanda mamanta da sauran dangi suka siya mata, anyi jere dai-dai karfin talaka. Da dare aka rako ango dak'i. *Wani irin zama Zahra zata yi da Al'ameen bayan bashi da kudi?* *Ina labarin Ahmad?* *Ya Zainab zata kasance?* 2018 [6/28, 8:44 PM] ‪+234 806 858 0203‬: ⚜🔱 *BAHAGON TUNANI* ⚜🔱 . 👨🏻‍💻👩🏻‍💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร. Dedicated to Hussaini Atk❤❤❤ _Rubutawa_✍🏼 *Badeeyerh Beauty Queen* *Da* *Fauziyya L. Ammany* _Labari_ *Queen Mermue* *9* Kamar yanda al'ada take, bayan an gama hira akai addu'a sannan kowa ya yi haramar tafiya. Al'ameen baki yaki rufuwa, sai murna yake yau shine mallakin Zahra tauraruwar zuciyar shi. Ya raka abokanshi tare da shiga ya yi ma Maman shi da k'anwarshi sai da safe. Nasiha ta kara yi mai sosai sannan sukai sallama. Da sallama ya shiga dak'in, tana zaune bisa gadonta fuska rufe da mayafi tana kuka. Ya zauna kusa da ita yana fadin"Zahra auren nawane bakya so kike kuka kamar wacce akai ma dole?, haba Zahra nine fa Al'ameen dinki mai kyaunarki, mai son ganin farin cikin ki, mai fatan kasancewa dake har karshen rayuwarsa. Wannan alkawari ne bazan taba gajiya da kaunarki ba kuma bana fatan nagaji, ina sonki ina kaunarki ina fatan kema ki kaunaceni ki maidani dan gata gareki. Zahra zan samu hakan?" ya yi maganar cikin alamun karaya. Kalaminshi sun tsuma Zahra sun sanyata jin bata da wani sauran dana sani a rayuwa, don haka ta daga mishi kai alamun eh. Da sauri ya mike yana dariya yace"Girman kujerar ki amarya, ban siya baki ba ashe shiyasa aka kimin magana." ya dauko wani dan akwati karami na sarka ya kama hannunta ya daura mata akai yana fadin"Bude Zahra wannan kyautar kice na amincewa da aure na Zahra, na siya da kudina domin ke." Ganin bata da niyar budewa yasa Al'ameen bude mayafin nata, aikuwa harda sauke ajiyar zuciya ganin tsantsar kyau da Zahran ta yi. Sarkar ya bude yana nuna mata, ta amsa cikin kunya ta yi mai godiya ganin sarkar zinari da abun hannu. Sallah ya umarceta da suyi, bayan sun idar ya yi musu addu'o'in neman zaman lafiya da kuma zuri'a dayyiba, sannan ya dauko musu abinci. Suka kammala kafin suka koma dak'in bacci. *Washegari* Zahra ce tsugunne kusa da umman Al'ameen tana gaisheta, yayin da Khadija ke zaune ta rike hannun Zahra wacce kanta ke kasa. Sauran yan'uwa 'yan biki aka gaisa kafin Khadija ta sake yi mata jagora zuwa dak'inta. Al'ameen na kwance ta shigo amma taki karasawa gadon, ganin haka yasa ya mike yana fadin"Guduna kike kamar wani dodo ko zumata?, zan kama ki ne." harara ta galla mishi kuma taki karasawa dak'in, ganin kamar yana shirin zuwa wurin ta ne yasa ta yi saurin juyawa zata gudu. Dariya ya yi yace"Matsoraciya kuma raguwa matar Al'ameen yi zaman ki, ba zuwa zanyi ba." Haka rayuwarsu ta kasance cikin mutunta juna da tsantsar kauna. Al'ameen na kokarin ganin ya kyautata mata ta ko wacce hanya, har aikin girki yana tayata. Idan ta yi girki zata zuba ma Umma nasu, ko yaushe cikin faranta ran juna suke, tana mutunta umma kamar yanda umman ke nuna kulawarta sosai akanta. ***** ****** Bayan sati biyu da auren Ahmad ya dawo, yaje gidan a kace mai ta yi aure, da mamaki ya nufi gidan su Zainab. Tana zaune tana sana'ar karatun yaro yazo ya kirata. Bata yi jinkiri ba ta fita, hango wanda ba ta yi tsammani ba yasa gabanta faduwa cikin farin ciki ta isa gareshi. Bayan sun gaisa yake tambayarta "Wai Zahra ta yi aure?" "Eh ta yi ashe baka sani ba?"ta fadi cikin alamun damuwa. "Wallahi bana kasar ne saboda wani dalili, amma auren dole a kayi mata ko?, domin nasan Zahra tana sona." Murmushi Zainab ta yi ganin ga damarta tazo, ta kalle shi da alamun tausayi tace"Ayya ai Zahra dama tana da mijin aure, kawai bata fadi maka bane, naso fada maka amma naga kada nayi tsegumi shiyasa nayi shiru." Cije lebe ya yi, wato ya yi aikin banza kenan tunda har ta yi aure. Ya kalli Zainab aranshi yace"Bari na rage zafi da wannan kawai." don haka ya nuna mata ba komai ta bashi lambarta, aikuwa ta bashi sukai sallama tana murna. *BAYAN WATA BIYU* 2018 Muje zuwa [6/28, 8:45 PM] ‪+234 806 858 0203‬: ⚜🔱 *BAHAGON TUNANI* ⚜🔱 . 👨🏻‍💻👩🏻‍💻 *ZAMANI WRITERS ASSOCIATION* Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Мσтιναтє αи∂ єитєятαιи συя яєα∂єяѕ _Rubutawa_✍🏼 *Badeeyerh Beauty Queen* *Da* *Fauziyya L. Ammany* _Labari_ *Queen Mermue* *10* *BAYAN WATA BIYU* Zaman soyayya ya fara karewa, soyayyar ta fara raguwa saboda aynahin halayyar juna da suka fito cikin wannan watannin. Matsala ta farko shine Zahra ta fara gajiya da girki tana ganin ita fa an matsa mata domin ita dama ba ma'abociyar son girki bace. Shikuma Al'ameen yana ganin bata isa tace ba zata girki abinda mahaifiyarsa zataci ba, domin auren shi yana nufin hutar da ita. Zahra kullum zata yi wanka ta kwanta tana chatin a waya. Bata fara girki sai taga shabiyu da rabi lokacin Al'ameen ya kusa dawowa, sannan take tashi ta fara niyar dorawa, kafin ta dora ya shigo gidan. Shi zai amsa ya yi girkin domin mahaifiyarsa. Yana jure dukkan halayyar Zahra saboda soyayya. Yanzu kam ya fara gajiya sai Umma ce ke tausar shi, kullum tana fadi mai " kayi hakuri Aminu Zahra yarinya ce zata girma, ka kara hakuri." Yau ma ta dora ruwan tuwo, ta dawo dak'i ta kwanta tana karatun novel, bata san anyi sallah ba balle girkin data dora tana hira da sababbin kawayen da ta yi masu mata huduba da cewa " idan mace ta yi aure kyau take karawa saboda hutu da kuma cima mai kyau." Al'ameen ya shiga ya faka mashin din yana fadin" Umma sannu da hutawa." "Yauwa Aminu an dawo ya aikin?" "Alhamdulillah Umma sai godiya ga yaran basa jin magana wallahi, kullum sai na siya musu alewa muke shiryawa." "Ai gara haka yaro sai da hakuri da kayan dadi."umma t fadi tana dariya. Kallon Khadija ya yi data hada tagumi yace"Deejana waya taba ki?" "Yayana yun..." shiru ta yi bata karasa ba sakamakon kallon da Umma ta yi mata. "Fadamin mana Deejana banasan ganin damuwarki fa." "Kaina ke ciwo." "Ya Salam! Kinci abinci ko?" Shiru ta yi ta na kallon umman, shima Umma ya kalla ya ce"Umma Deejana bata son magani, dubi ina magana ta yi shiru." "Ka cika tambaya Aminu ka wuce ka bamu wuri haka."cewar Umman tana dariyar yak'e domin yunwa suke ji. Shima dariya ya yi yace"Tuba nake Ummana bari nayi wanka nazo akwai labari kan saurayin Deejana, wannan mai kayan kolin."kuka Khadija tasa tana cewa"Banason shi wallahi Umma kina jin Yaya ko?" Ya yi hanyar dak'in su yana dariya. Kwance ya ganta ta sanya waya gaba ga iyafis manne a kunnenta. Girgiza kai ya yi ya daure ya iso wurinta tunawa da yanda suka karke da safe. Abun da ya faru shine yana shirin tafiya makaranta Zahra ta sameshi da maganar ita fa kwai zata ci. Yace mata bashi da kudi yanzu amma karshen wata idan anyi albashi zai siya mata,aikuwa t rufe idona ta zage shi tsab,tana fadin"Matalauci kawai, wanda kullum tsiya ke bibiyar shi." tuna da wa'innan kalamin yasa ya karaso yace "Zahra kina nan ina ta sallama." Mikewa ta yi tace"Gara daka dawo wallahi banjin dadi, kayi girkin gashi can na dora ruwa." wani takaici ya rike shi, Zahra bata iya cewa sannu da zuwa ba. Sai yanzu ya gane me Khadija ke kokarin fada mai Umma ta hana, agogo ya kalla biyu saura minti biyar,ranshi ya baci "Ke Zahra yanzu saboda Allah ba kiyi girki ba?" "Inda nayi da baka ganshi ba" ta amsa tana cigaba da danna wayarta. Baisan lokacin da zuciya ta dauke shiba ya fizge wayar tare da bugawa a kasa. Duba wayar ta yi ganin fuskar wayar ta fashe sosai ta dago cikin bakin ciki kawai ta kwalla ihu tana fadin"Na shiga uku, wayyo Allah na" Da gudu Umma dake zaune ta shigo yayin da Khadija farin ciki ya lullubeta tana tunanin gara Yayanta ya koya ma Zahra hankali. "Lafiya Zahra meyafaru?" "Wayyo Umma Al'ameen ya kasheni." "Fadamin me yayi miki Zahra, bar kuka don Allah yi magana." "Umma don nace mai bani da lafiya banyi muku girki ba, shine ya mareni ya fasa min waya." A harzuke Umma ta dago ta dubeshi cikin fushi tace"Banyi zaton marin mace daga gareka ba, amma gashi ka aikata nagode maka Aminu. Kasan bazaka iya rike amanarta ba ka aurota?, ko kuwa an fadi maka duka na maganin matsala, wallahi Aminu kayi na farko kuma na karshe muddin ka kuma dukan yarinyar nan ban yafe ba." ta juya wurin Zahra tana bata hakuri. Shi kuwa ko motsi ya kasa yi, sai da Khadija tazo ta riko hannunsa sannan ya fice daga dak'in. Dak'in Umma Khadija ta zaunar dashi tare da bashi ruwan sha, yasha ruwan sosai sannan ta ce"Kayi hakuri Yayana nasan baka dake ta ba." kai kawai ya daga mata ya kishingide kan kujerar yana jin yanda kijin shi ya yi zafi saboda bakin cikin Zahra. Umma ta shigo Zahra na biye da ita, ta jefa mai wayar Zahran kan jikin shi"Ka tabbata ka gyara mata kafin gobe, sannan na yanke hukunci zamu dinga yin girkin mu nan nida Khadija tunda abun hakane." Murna Khadija ta hauyi jin Umman ta raba su da abincin Zahra zasu huta da horan yunwa. Zahra kuwa bata so hakan ba domin kawayenta na mata hudubar amsar duk ragamar gidan, ta hakane zai mata duk abun da take so. 2018 An dauko

Chapter 2 of 3