An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://thausanovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.thausanovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels
[6/28, 8:40 PM] +234 806 858 0203: ⚜🔱 *BAHAGON TUNANI*⚜🔱
. 👨🏻💻👩🏻💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
📚 Zaku iya samun littafan mu a Facebook 👇🏽
Fb.me,/ZAMANIWRITERSASSCIATION
📩 Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com
*RUBUTAWA*✍🏻
*Badeeyerh Beauty Queen*
*Da*
*Fauziyya L. Ammany*
*Labari*
*QUEEN MERMUE*
Za ku ga munyi gyaran lambobi, kada Ku damu yanzu da daya bayan daya samu dinga tafiya.
*2*
Nana ce ta shiga dakin dauke da abincin su, zama ta yi tana fadin,"aunty zahra taso muci abincin." "to." kawai ta ce ma ta taci gaba da chatin din ta.
Ganin an dauki lokaci ba ta taso ba ya sa Nana kara yi ma ta magana,"Anty don Allah kizo muci abincin nan, so nake nayi karatu ina da gwaji gobe, gashi ba wani karatu nai sosai ba."
Kafin ta rufe bakinta Zahra ta taso ma ta da masifa,"na hana ki cin abinci ne da zaki ishe ni da magana?, bana son iskanci fa kici naki mana idan na gama nazo naci, kawai kin wani zo kin ishe ni da surutu."
"Allah ya baki hakuri Anty." Abincin ta faraci ita kuma ta cigaba da chatin dinta ba tare da ta kara magana ba. Bayan Nana ta gama cin abincin ne ta aje mata na ta sannan tace,"Anty ga naki nan,naci nawa."
Kala bata ce da ita ba, kai ga dukkan alamu ma ko jinta ba ta yi ba catin dinta kawai take. Nana kam tashi ta yi ta dauko Littafinta ta fara karatu.
"Assalamu Alaikum".
"Amin wa'alaikussalam" gwogga ce ta ansa tana fitowa daga daki.
"Wai ana sallama da Anty Zahra".
"Wake sallama da ita?"
"Yaya Aminu ne na gidan malam Salimu".
Tsaki gwogga tayi sannan tace"Na zata wani mutumin arziki ne,ce mashi gata nan zuwa tunda ta makale mashi ai ita ta jiyo."
Yaron ya ce "to" sannan ya fita.
"Yaya Aminu na gaya ma gwogganta tace gata nan fitowa,Yaya wai miyasa tace kai ba mutumin arziki bane bayan kuma kana da kirki tunda idan kana da kudi kana saya mana minti da biskit,kuma ina ji su mama na fadin kana da kirki sosai."Murmushi Aminu ya yi sannan yace dashi"Baka gane abin da take nufi bane shiyasa, amma yanzu karbi nan kaje kasha minti kaji". Ansa yai yana murna yace "Nagode Yaya sai da safe."
"To sai da safe Jamilu a gaida su mama."
"Zahra! Zahra! Zahra!.
Wai baki jina ina kiranki?" "Ganinan Gwogga." tsaki ta yi sannan ta fara gunguni ta na maganganu kasa-kasa gudun kada Gwoggo ta jita ta fito.
"Wancan mara amfanin ne yazo wajanki,kinbi kin nace masa ko ubanmi zaki tsinta gare shi,(mi na sama yacci balle yaba na kasa.)"
Shagwaɓe fuska ta yi "to Gwaggo nidai ina son shi a haka ai yana da dan damar shi tunda ban samun wanda ya fishi ai gara in lallaɓa da shi."
Gyalenta da ke saman igiya ta ja,ta yi soron gidan nasu.
"Sannun ka da zuwa".
"Assalamu Alaikum"Aminun ya faɗa.
"Wai na manta ne yi hakuri" Zahra ta fadi tana murmushi.
"Assalamu Alaikum."
"Amin wa'alaikussalam,Malama Fadimatul Zahra'u".Aminu ya amsa yana kallonta.
"Na fa gaya maka bana son sunan nan ka kirani da Zahra ta mana". Ta fadi tana shagwabe fuska domin tana kaunar Aminu.
"Tuba nake Zahra farar mace alkyabbar mata".
Murmushi ta yi tana satar kallon shi, tana jin duk duniya babu mai rabata da Aminullah. Nan suka sha hirar su ta masoya, daga bisani ya yi mata sallama ya tafi cike da kewar juna suka rabu.
********
WASHEGARI
"Anti Zahra lokacin makaranta ya yi fa,kiyi sauri ki shirya kada a fara taron latti".
"Banason takura Nana akan mi zaki rika damuna inace har yanzu da sauran lokaci?"
"Amma Anty zahra har yushe ki ka bar wannan karatun litattafan da baya amfanin ki da komi kika ta shi ki ka shirya?" Nana ta tambaya tana gyara hijabinta.
"Kinfa raina ni Nana,wai ni sa'ar ki ce?, ki shirya warki ki tafi idan na shirya zan biyama zainab mu wuce tare".
"Allah ya kyauta muku,yasa ku gane gaskiya,idan Gwoggo ta dawo ki ce mata na wuce."Nana ta fadi tare da barin dak'in.
Tsaki Zahra ta yi hade da gyara kwanciyarta, domin tana mutukar jin dadin karatun da take yi.
Shigowar Gwoggo gidan ya sanya ta tashi ta fara shirin islamiya.
Gwoggo ta ce"Zahra baku zuce zuwa makarantar ba, ina Nana take?"
"Cewa nayi ta wuce kada abar gidan haka nan shiyasa na tsaya jiran dawowar ki"
"Tafi can kin dai tsaya latsar wayarta ki,ina ce gidan Ladi kuke kai min makullin,shiyasa sai da na fara shiga gidan ta ce baku kawo ba, Allah ya shirye ki kiyi maza don nasan yanzu an fara taron latti."
Da fitar ta gidan su Zainab ta wuce kamar kullum kwance ta iskota tana sana'arta ta,fahintar bata ji shigowar ta bane yasa ta fisge littafin da ta ke karantawa,zabura ta yi sannan cikin mamaki tace "Zahra yaushe kika shigo?"
"Yanzun nan mana ai naga alamun ba kiji shigowata ba ne da gani wannan littafin ya yi ba karya".
"Wallahi ko kamar kinsani jarumin cikin nan yana wasa da nera son ranshi,kai Allah ya kai damo ga harawa ko beci ba yai birgima,yau an yi posting?".
"Eh anyi sabo kai wallahi Prince Aryan na kasheni sosai dinnan fa".
Dariya Zainab ta kwashe da ita sannan ta ce "kedai bari, bani na karanta".
Ta mika mata wayar kasancewar ita Zainab bata da babbar waya, yasa idan Zahra ta karanta sai ta bata wayar ita kuma Zainab ta ba Zahra Littafi, a haka suke gudanar da rayuwar su.
Yauma bata bar gidan ba sai shidda sannan ta yi ma Zainab sallama ta kama hanyar islamiyar su.
Kamar kullum Nana na isowa kusa da ita ta hau fadan ta barta tana jiranta,ita kuma ta fara bata hakuri suka wuce gida.
2018
[6/28, 8:41 PM] +234 806 858 0203: ⚜🔱 *BAHAGON TUNANI*⚜🔱
. 👨🏻💻👩🏻💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
📚 Zaku iya samun littafan mu a Facebook 👇🏽
Fb.me,/ZAMANIWRITERSASSCIATION
📩 Zaku iya aika mana sako ko korafi, Ta email namu 👇🏽
Zamaniwriterassociation@gmail.com
*Rubutawa*✍🏻
*Badeeyerh Beauty Queen*
*Da*
*Fauziyya L. Ammany*
*Labari*
*Queen Mermue*
*3*
Haka rayuwar Zahra ta kasance kodayaushe tana online, bata da lokacin yin cikakkiyar ibada. Ko makaranta bata da lokacin zuwa saboda tsananin burin data dora kan karatun novel na online.
Saukinta daya tana mutuwar son Aminullah, duk kuwa da baya da hali sosai tana sanshi a haka.
Aminullah malamin makarantar firamari ne wanda albashinsa bai gaza duba talatin ba, gashi shike kula da mahaifiyarsa da kanwarsa mai suna Khadeeja, cikin rufin asiri suke rayuwa da dogara rayuwar su kacokan kan albashin sa. Khadeeja na aji shidda yanzu zata yi jarabawa gashi baya samun kudi kan kari sai dai maleji. Yana kaunar Zahra yana burin ta zamo uwar yayansa duk kuwa da sanin dogon buri irin na Zahra da ya yi, domin wani lokaci idan yazo hira takan karanta mai irin rayuwar da take fatan samu cikin daga abun data karanta cikin novel. Kullum yana kokari wurin nuna mata ba gaskiya bane amma bata fahimta, shiyasa ya dage da addua tare da fatan watarana ta fahimta.
Yau Zahra bata da kudin siyan data gashi Aminu bai tura mata kati ba, don haka ta shiga dak'in Gwoggo da nufin tambayar ta rancen kudi. Caraf ta hangi naira dari ajiye kan kujerar dak'in Gwoggo kuma bata nan, don haka kawai ta dauka ta fita. Kati ta siyo ta sanya a wayarta tun a hanya ta bude data domin ta kosa ta ganta online. Idanuwanta na kan wayar taji ana mata wani gigitaccen ham da mota. Rikicewa ta yi har wayar hanunta ta fadi kasa, a fusace ta juyo sai lokacin ta lura kan layi take.
Mai motar ya fito yana murmushi ya tsugunna ya dauko mata wayar tare da mika mata yana fadin "Yi hakuri mai kyau kin tsaya kan hanya ne."
Harara ta zabga mishi tana murguda dan karamin bakinta" Sai akace ka dinga min ham kamar wata kurma ko?"
"Tuba nake mai kyau.
Mika hannu ta yi da nufin ya bata wayarta. Kallonta ya yi ya kalli wayar yaga ta dan fashe kadan, ya sanya hannu cikin aljihu ya ciro wayar shi sabuwa iPhone. Ido Zahra ta zuba mishi ganin yana cire sim dinshi daga cikin wayar, bata kara tsinkewa ba sai da taga ya bude ta ta wayar tecno y6 ya cire sim dinta ya sanya cikin iPhone din. Ya dube ta yace"Ayi hakuri me kyau nayi laifi, amma ga wannan kiyi amfani da ita."Ya mika mata dukka wayoyin biyu.
Kallon hannun shi ta yi da yake miko mata wayoyin tace"Mezanyi da wayarka, nace ma ina son aro ne?"
"Kyauta na baki me kyau ba aro ba." ya fadi cikin sanyi domin yaga kamar ta yi fushi.
Da sauri kuwa ta amsa tana juya wayar a hannunta "Kyauta fa kace bawan Allah?"
"Eh me kyau."
"To na gode Allah ya saka."
"Ameen me kyau, amma baki fadamin sunan ki ba."
"Zahra sunana."Ta fadi hankalinta na kan wayar.
Murmushi ya yi "Ashe banyi kuskure ba da nace me kyau, gaki da kyau ga sunan ki ya dace dake Zahra."
"Na gode sai anjima."cewar Zahra tana kokarin barin wurin domin kuwa murna ta cika ta yau itace rike da iPhone.
"Sunana Ahmad ina fatan zan samu number ki?"
"Eh sosai ma."ta karanta mai ya sanya sannan sukai sallama.
Da gudu Zahra ta karasa gida tana kiran Nana. Nana dake zaune gefen Gwoggo suna neman kudin cefane ta mike da sauri tana fadin " lafiya anty Zahra da wannan kiran?"
"Kalli kiga."ta mika mata wayar.
Amsa ta yi tana kallon wayar cikin mamaki "Anty Zahra waya baki wannan wayar?"
"Yanzu wani ya bani kyauta wallahi."
"Ke Zahra uban me kika mai da zai baki wannan katuwar wayar?"cewar Gwoggo.
Turo baki Zahra ta yi "Nifa yarda min waya ya yi ta fashe shine ya ban tashi kuma wallahi ba rokon sa nayi ba."
"Idan ma rokon sa kika yi wallahi ba ruwana, domin wannan zamanin abun tsoro ne gara ki kula."
"To Gwoggo, wannan kuma zan ba Nana." cewar Zahra tana mika ma Nana tecno din.
Amsa ta yi tana juyawa a hannunta domin ita dai ba farin ciki ta yi da wayar ba, bata fatan ta yi irin rayuwar da Zahra keyi a waya. Tana kuma yi ma Zahra addua domin tasan yanzu ita da cikakkiyar ibada sai Allah, dama ya ya lafiyar kura.
Zahra ta kalli Gwoggo ta ce"Ga kudinki dana dauka."
Harara Gwoggo ta sakar mata tare da kai mata duka tana fadin"Ja'ira wannan matsiyacin aikin wayar sai ya sakaki sata." Da gudu Zahra ta shige dak'i tana dariya.
Da dare Aminu yazo, cikin doki ta shiga nuna mai wayar. Hankalinshi yai mutukar tashi yace " Zahra meyasa kika amsa, kinsan da manufar daya baki wayar?"
"Karka damu Al'ameen kai kadai nake so duk kuwa da ya fika kyau kai ne a raina."
Yaji dadin kalamanta ya kuma gasgata domin Zahra mai kyau ce, duk namijin daya same ta ya yi dace kuma tana da suffar matan manya, amma gashi shi da ba kowa ba ya samu soyayyarta, yana alfahari da hakan. Don haka duk da ranshi baya so ya bar maganar wayar.
"Zahra inasan na aiko da kayan auren ki kwanan nan insha Allah."cewar Aminu.
Rufe fuska ta yi tana dariya ta ce " Allah ya kaimu lafiya Al'ameen nawa."
Cike da jin dadi da tsantsar kaunar juna suka cigaba da hira har sukai sallama ya tafi da alkawarin sati mai zuwa zai turo gidan su.
2018
[6/28, 8:42 PM] +234 806 858 0203: ⚜🔱 *BAHAGON TUNANI*⚜🔱
. 👨🏻💻👩🏻💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
_Rubutawa_✍🏻
*Badeeyerh Beauty Queen*
Da
*Fauziyya L. Ammany*
_Labari_
*Queen Mermue*
*Bismillahir Rahmanir Rahim*
*4*
Kwance take tana chatting, da ka kalle fuskarta zaka fahimci irin dadin da hirar ta yi mata. Wayar ce ta hau kara alamun kira, sai da wayar ta katse aka kuma kira sannan ta dauka tana mai jan tsaki don ko kadan bata ji dadin katse ma ta hirar da aka yi ba.
"Hello."
Daga dayan bangaren da a ka kirata a ka amsa da,
"Hy me kyau ya kike kin isa gida lafiya?"
"Lafiya ƙalau ya ka isa gida kaima?"
"Lafiya kalau na isa,da fatan ban takura ki ba na ga da na kira baki daga ba?"
"A haba wace takura bana kusa ne shiyasa."
"To. Zahra zuciyata tana kaunar ki, ina fatan in kasance da ke matsayin masoyiya kuma uwar ya'yana. Ina fatan zaki amshi kokon barata?"
"Zan gaya maka gaskiya ina da saurayi sunan sa Al'amin ina son sa sosai."
Jim ya yi sannan yace "Na ji zancen ki, amma ai kin san ke allura ce a cikin ruwa mai rabo ke dauka don haka ki bani dama kawai in gwada sa'a ta".
"Ka bani lokaci in yi tunani".
"Ba damuwa amma kamar nan da yaushe?, don a hakika nin gaskiya bazan iya jira har na tsawon lokaci ba".
"Ka bani nan da sati daya".
"Har sati daya?, gaskiya bazan iya ba,bakisan irin son da na ke maki bane da baki ce har nan da sati daya ba. Na baki nan da kwana biyu zuwa uku."
"To shi kenan."
A haka suka ci gaba da waya ba shi ya barta ba har sai wuraren karfe biyu da rabi na dare,tana gama wayar maimakon ta kwanta sai taci gaba da sana'arta bi ma'ana karatun litattafai,wanda ya ke kara mata dogon buri na son ganin ta cimma nasarar zama hamshakiyar mai kudi ko matar hamshakin mai kudi, yadda zai kasance ana damawa da ita.
Ya kasance a yau tana hawa babbar mota a kowane lokaci ta na da kudi, yau ita ce wannan kasar gobe ita ce wannan ko sayayya zata yi sai a kasashen waje haka ma ganin likita koda kowa ciwon kaine kai duk ma abinda take gani a littafi burinta ta ganta ta nayin shi.
Take a nan tunanin Al'amin ya fado mata a rai ta na da yakinin ba shi da kudin da zata ji dadin rayuwarta kamar yadda ta ke buri, amma kuma ai ga dama ta samu na samun Ahmad da ta yi don ga dukkan alamu yana da kudin da zata wataya sosai da sosai kamar dai yadda take tunanin samu ga mijin auren ta, to amma wani hanzari ba gudu ba samba ta son shi Al'amin take matukar so matsalar kawai bashi da kudi to, amma ai yana iya samun su a kowane lokaci kamar dai yadda take gani a cikin littafai yana faruwa,tunda dai ko a cikin littafin nan *WANI HANIN* Taga jarumin ciki talaka ne talak, amma da ga bayan auren su cikin lokaci guda ya zama hamshakin mai kudi na sosai da sosai don haka tana da tabbacin Al'amin dinta ma zai zama hamshakin mai kudi koda a bayan auren su ne.
"To ya kuma zan yi da Ahmad din nan shin ci gaba zan yi da kulashi ko yaya?, amma ai kuma zan iya kulashi kamar yadda na ga yan'matan cikin littafai nayi sukan iya tara samari na wa, kuma ko ba komi zan samu wadda zai rika kashe main kudi tunda Al'amin baya da su,ko ba komi zamu rika zuwa sayayya tare na dauki duk abin da nake so,kai gaskiya haka za ai amma bari gobe idan naje gidan su Zainab sai muyi shawara." Da wannan tunanin kwana ya dauketa. Koda asuba da Nana ta tadata kasa tashi ta yi dole ta kyaleta tana mai jin haushin halaryar yayarta ta,ko ba komi zata so ta fuskanci tubalin tokar da take son gina ma kanta, ga shi ko addininta tana wasa da shi , a da tana kokarin yin sallah ko yayane zata rakkata amma daga jiya da ta samu sabuwar waya ta fara wasa da sallah,don jiya tana jin ta kafin ta kwanta tana waya kuma tana da tabbacin ba da Yaya Al'amin take wayar ba don shi da goma ta yi ya gama waya da ita sai kuma gobe duk da ba kullum yake samun kudin kiran nata ba, amma komai yana yinshi ne a cikin tsari ko kadan baya da halayyar nan ta samarin zamanin nan da muke ciki.
Shiya sa ta ke ma yayarta addu'ar samun shi a matsayin mijin aure ko da zai zamo sanadin yin hankalinta don ita kwata-kwata ba ta dauke ta asahun masu hankali ba,amma ga dukkan alamu za'a iya samun matsala saboda shigowar wannan sabon saurayin rayuwar ta,amma zata yi amfani da irin son da yayar kema Al'amin taga hakan be faru ba za kuma ta taya ta da addu'a akan Allah ya zabar mata abinda yafi alheri a gareta ku ma abinda zai zama sanadin shiryarta.
Da wannan tunanin ta fita tsakar gidan na su ta fara aikace-aikace,ta daura ruwan kamun koko bayan sun tafasa ta dama sannan ta yi dumaman sauran tuwan su na jiya ta na mai jin dadin ga dukkan alamu kalacin zai ishe su gaba dayan su.
2018
[6/28, 8:43 PM] +234 806 858 0203: ⚜🔱 *BAHAGON TUNANI*⚜🔱
. 👨🏻💻👩🏻💻
*ZAMANI WRITERS ASSOCIATION*
Wɛ ɑʀɛ ɦɛʀɛ tѳ ɛɗucɑtɛ, Mѳtiѵɑtɛ ɑɳɗ ɛɳtɛʀtɑiɳ ѳuʀ ʀɛɑɗɛʀร.
❤ Zamanawa naku ne wannan❤
_Rubutawa_✍🏻
*Badeeyerh Beauty Queen*
*Da*
*Fauziyya L.Ammany*
*Labari*
*Queen Mermue*
*6*
"Zainab! Zainab! Zainab!"
"Lafiya Zahra?" Zainab ce ta tambaye ta cikin rudani da tunanin wani abu ya faru na tashin hankali.
"Mstww! Lafiya kalau mana, nifa matsala ta da ke kin cika tsoron bala'i."
"Ai tsoro wajibi ne, ji yadda kika shigo kina min wannan kiran 'yan farauta."
"Kada fa ki bata min rai Zainab." cikin daga murya ta yi maganar,
"Na zo miki da zance mai dadi, amma kina son bata min rai haba".
"Yi hakuri kawalliya romon jaba, ina jin ki wane irin albishir ne wannan?"
"Kalli nan"sabuwar wayarta ce ta mika mata ta na murmushi,
"Wayar wace wannan Zahra,Ina kika samu wannan babbar waya?" magana take, amma jikinta har kakkarwa yake burinta guda shi ne taji inda ta samo irin wannan babbar wayar.
"Ahmad ya bani" Ta faɗa tana wani fari da ido.
"Waye kuma Ahmad?" Ta faɗa cike da mamaki don ita dai bata san Zahra da wani Ahmad ba.
"Wannan kuma sai mun zauna sannan zaki sha labari"
"Mu shiga daki na matsu inji ina kika samo wannan wayar."
Labarin haduwar su da Ahmad ta ba ta har kiran da ya ma ta da yadda suka yi da Al'amin da Gwoggo. Jinjina kai kawai Zainab ke yi ta na mai mamaki irin wannan damar da Zahra ta samu amma ta na wasa da ita, in ita ce ai da tuni ta bada kai".
"Humm! Ban taba sanin baki da hankali ba sai yau Zahra, yanzu akan wannan dan talakawan kike kin d'an masu da shi?, sam bazai yuwu ba dole ne muyi amfani da wannan damar muci karen mu ba babbaka, kinga nidai shawarar da zan baki a matsayina na kawarki wadda ke sonki shine ki ba Ahmad dama ya zo ko don mu fantama mu wataya yarda muke so, don haka kada ki bar Ahmad."
Ajiyar zuciya ta dauke me nauyi hade da jan siririn tsaki ta ce,
"Hmmm! Ba wai bana son Ahmad ba ne, ke ma kinsa namiji me kudi da kyau ne mafarkina, amma soyayyar Al'amin daban ce a zuciyata shi zan aura amma kafin nan za muyi soyayya da Ahmad kamar dai yadda nake gani a littafai kuma fa Al'amin zai yi kudi na sosai haka nake ji a raina."
"Miye dalilin ki na fadar haka?" Zainab ta tambaya hade da kallon Zahra cike da mamaki.
Murmushi Zahra ta yi dake nuna tabbacin abinda zata fada,
"Haba! sai kace baki karanta litattafai bakya ganin yadda suke yin kudi daga baya, ai duk talaucin taurarin cikin littafi zaki ga dole suyi kudi kafin Littafin ya kare. To kamar haka ne kin dai san ni ma tauraruwa ce don ina da kyau na dai-dai gwargwado kuma yanzu idan zan dinga samun kuɗi a wurin Ahmad kinga zan kara da shafe-shafen nan da ake yi."
"Kai gaskiya kawata kanki naja, kin fimu gaskiya don haka dole muyi yadda muke so, yanzu dai kira Ahmad din mu gaisa gara yasan da zamana ko ya kika ce?"
"Haba ke ko ai sai na ja ajina, taya zan kira shi?, ai shi ya dace ya kira ni bamu yi dadewar da zan kira shi ba."
" Ehh to nan ma ki na da gaskiya,amma ina tsohuwar yawar ta ki ai sai a bani ni ma in shigo gari ko?"
"Mstww! Na ba