nace , zaka na reporting
mana duk abunda takeyi sannan duk inda
zata je da fatan kagane? albashinka mai
tsoka ne yafi na wani chairman din local
govt ka amince?” mutuminne ya katse masa
tunaninsa da wannan batun, atake ya gyada
kai yace “na amince” nan yaci gaba da cewa
” ga kayan da zakana sawa ako yaushe baki,
in kaga wani abu da bai gamesheka ba ka
kira ka sanar damu” nan ya mika masa
wasu files komi ne akan Salma Tanko
ayadda ya gani har yana dariyan sunan
aransa yance cewa ji wani suna Taaannkoo,
haka dai ya karba ya duba sosai sannan
yaje gida yayi sallama da hajiyarsa ya koma
ya tattaro dan komatsansa domin anbashi
daki daya agidan salma a b.q inda zai na
zama dare-dare.
************
Alhaji Tanko ne ya shigo sanye da manyan
kaya ya dibi takardu da jakansa ya hada
kaya a karamin akwati duk tana kallonsa ba
tace komi ba, ita tsoro ma takeji kar ya afka
mata don tasan hali, sai da ya kammala tsaf
sannan yace ” na sako miki sabon P.A in
kika kuskura ki kayi rashin hankali zakiji jiki
domin zai sanar min” ta kalleshi ido narai
narai sannan tace ” haba mana, ina
matsayin matarka ta sunna amma kana
hadani da wani baligin namiji wai shi P.A ”
hannu yasa mata alamun ta dakata sannan
yace ” ba fa P.A din bane, gadinki zai nayi
saboda na mutunta ki ne a idon mutane
yasa nakirashi da haka” ya fice ya barta
tana zubar da hawaye, itakam bata ma san
makomar rayuwarta ba, aikuwa ko waye ne
haka zai kwashi wulakanci har sai ya gaji da
kansa ya tafi, doguwar riga ta sanya ta yafa
gyalen sannan ta sauko kasa don ganin
wani marar aikinyi aka kawo musu,
Yana zaune a babban falon sai kallon gidan
yake don tunda yake bai taba shiga gidan da
ya hadu masa irin wannan ba, gidan ya hadu
sai dai mai karatu yayi tunani da kansa,
tsaye cak ta tsaya da ta hango shi alokacin
yana danna wayarsa, jin masu aikin suna
gaisheta yasa ya dago kansa aikuwa caraf
akanta, gabansa tayi mummunan faduwa.
Kamar yadda ya fada haka ya cika alkawari
domin kuwa ran Asabar karfe goma na safe
ya daura ma Salma aure da Alh.Tanko,
dama yace kar ayi mata komi duk da haka
sai da Hajiya tayi sayayyanta acewarta yarta
baza’a mata gori ba.
Bayan daura aure wanda kowa yayi mamaki
ganin yadda aka tsallake su fatima da Amina
aka daurawa Salma aure ba tare da yin wani
bidi’a ba aka kaita gidanta dake asokoro,
gida na gani na fada yasha kayan duniya da
kayan alatu, bata tara wasu kawaye ba
domin agunta auren dole aka mata, tayi
niyyan taci kudinsa ne ta sallameshi Allah
ya kamata tayi ciki sannan babanta yaji
labari wanda gashi yanufi gun sarki yakai
kara an daura musu aure, kwata-kwata ta
tsani ganinsa duk da cewa bata da wani
tsayayyen saurayi kuma Alh.Tanko ba wani
muni yake dashi ba sai dai tsoho ne yakai
hamsin da biyar, bafulatanin yola ne futuk
irin bararoji dinnan, yaransa uku ne kacal
kuma babu karami,yar autarsa ce ma sa’an
salman, kudi kam ba’a magana wanda har
wasu suna cewa tabbas Barrister Jibrin kudi
yabi ya aura wa yarsa tsohon dan siyasa.
Duk da tsufansa bai tsufa a soyayya ba
domin kuwa lallabata yakeyi kamar zai
maidata cikinsa, ya saka mata masu aiki
agidan wanda ko tsinke sai taga dama ta
rike ko ta kawar akan hanya.
Tana sanya kaya adaidai lokacin da yashigo
dakin, bata damu ba balle taji kunya kamar
yadda sauran amare sukeyi basu saba da
cire kaya agaban mazansu ba amma
kasancewar bariki tayi kuma ta saba yasa
ko daya shigo bata juya ba, ya tayata cirewa
idonsa kur akanta har ta tsargu tace ” meye
ka zura min ido kaman zaka cinyeni?”
“don Allah kizo mu tafi honeymoon, na gaji
da kasannan ko ke kanki zaki huta ma” ta ce
” ba inda zanje , ba yanzu ba ka bari sai na
huta tukunna” duk da baisan dalilinta ba
amma yabarta ahaka, ji yakeyi kaman ya
cinyeta, akwai wani abu da yakeji agame da
ita , shi dai yasan yana sonta amma ba
zallan So ba, yakanji kaman ya mayar da ita
cikinsa , haka ya rinjayeta zuwa ibadansu na
ma’aurata.
Wata uku da aure Salma ta rame ta kode
sosai ,tana cikin tashin hankali wani abu da
yake damunta shine yadda Alh.Tanko ke
mata wasu abubuwa da bata ganewa, da
farko idan ya kwaso bukatarsa baya
sauraronta afka mata kawai yakeyi wanda ba
karamin jin jiki takeyi ba, domin akwai ranan
da tana kallo ya shigo tun daga falo ya
sallami ma’aikata sannan ya fara rage kayan
jikinsa, yayi kanta amma ta gwada masa
bata da niyya, yadda ya fusgeta ranshi
abace idonshi jawur ya wurgata kan gado a
daki sai da ya idda sannan yafita, taji ciwo
sosai domin yadda yasa mata karfi, akwai
randa ya gama biyan bukatunsa da safe da
rana sai gashi ya dawo ta danne ta yadda,
daredare ta shirya tsaf zata kwanta sai
gashi ya dawo alokacin duk jikinta radadi
yake rokonshi ta fara yi akan yayi hakuri
alokacin ya fara zaginta ” ba ke kika ce kina
sona ba? bayan na miki ciki ai da kin karbi
kudi kika zubar kika ware abunki amma kika
fada wa babanki saboda shima yana son
kudi ya kai kara na, toh na aureki kuma
shima na bashi kudin don haka dole ki biya
min bukata” tuni ta fara ja baya amma belt
ya cire ya mata duka sosai ya biya
bukatarsa, taji jiki kuma tayi kuka sosai
gashi Hajiyarta ta umurceta da rike sirrin
aurenta,tsananin kishi da yake mata ko
masu aiki yaga tana magana dasu , zai hau
mita da zaginta,ahankali tazo ta gane tana
da ciki, gashi ko yaushe yana makale da ita,
duk inda zaije ko wani gari zaije, ko yana
gun uwargidansa toh zaiyi ta sintiri a
tsakani,abunda bature yake kira Obsession,
ko yaushe yana makale ajikinta ko meeting
zai je wani gari da ita yake zuwa, ba ya
barinta,duk da wahalan da take sha bata
sanar masa ba sai wata rana yazo zai fita
kamshin turarensa ya hau kanta alokacin da
ya rungumeta, amai ta masa ajiki tuni ya
gano ciki ne
“Muje a zubar” ya fada cikin yanayin
maganansa kamar ta yan maye, ta zaro ido
sannan tace
“Dan halal din?”
“ae, zai katsemin jin dadi don haka dole ki
zubar”.
BENAXIR OMAR
Ganinshi da tayi ya mike yasa ta sauko
ahankali yayinda shi kuma yana kokarin
gaisheta duk da ido da ta tsura mishi tana ji
ajikinta kamar ta sanshi haka kawai kuma
take jin gabanta yana fadi, murmushi tayi
sannan ta amsa gaisuwar ” lafiya lao ya
aiki?” ya amsa da “lafiya kalao madam”
zama tayi yayinda tace ya zauna shima
sannan ta mika masa hannu ya miko mata
takardunsa , daya bayan daya ta dudduba
sannan ta mika masa “sannunka Jalal, na
tabbata anyi maka bayanin yadda aikin
yake” ya gyada kansa alokacin ta kare masa
kallo tsaf, ko babu komi zai iya zama gaban
mota, tunda taga yana da kyau dinshi, zata
iya zuwa dashi ko ina, musamman cikin
kawaye in tace mijinta babu wanda zai
musanta,
“dama akwai taron da zanje, don haka mu
tafi” haka suka bita a baya yayinda ta nufi
motar da za tashiga drivern ya bude motan
ta shiga gidan baya ta owners corner
yayinda Jalal ya shiga gaba sannan suka
tafi, har zuwa lokacin tsananin mamaki ne a
tattare dashi shin ta ganeshi kuwa? ko
kuma da gangan take nunawa bata sanshi
ba? ko ta manta dashi ne? bama wannan
bane tashin hankali, babban tashin hankalin
shine wai tayi aure, bayan alkawarin da ta
masa na cewa idan yasamo kudi zata
aureshi , ta yaudare shi kenan? ya zaiyi
kenan ko ya sami wannan kudin? wani
zuciyar kuma take ce masa ‘ idan banda kai
da neman magana, ina kai ina Salma? ai
asalinta matar manya ce shiyasa ma ta auri
daidai ita’ wata zuciyar kuwa tace ‘tace ko
tayi aure za ta iya aurenka, tace za ta kashe
wancan auren’ toh ko dai ta manta ma
dashi ne? gashi yana tsoro baisan ta inda
zai fara tanka mata ko ta sanshi ba.
Suna isa ta shiga meeting yayinda ya tsaya
da drivern yana jira ta fito alokacin ya
tambayeshi ” Madam yar wacce gari ce?”
yayi dariya don inyamuri ne sannan hausan
bai zauna ba sannan turancin ma babu kauri
yace “madame fah ni i think she dey for this
town, e don tey wey i dey work for dem
house, na d papa come carry me say mek i
dey watch him pikin, she no lyk the husband
sef” Jalal ya zura masa ido yana kokarin
gano kan maganan, nan dai ya kara
tambayansa ” tana da yara?”
” noo! she no get pikin, the marriege na only
one year sef”
nan ya gyada kai yana tunani inhar bata son
auren, akwai alamun zata iya aurensa ta
rabu da wancan indai yayi kudi shima, nan
dai ya samu ya lallaba dan inyamuri mai
surutu ya basa labarin yadda akayi auren da
yadda tayi cikin baban yasa ayi auren, da
yadda take takure agidan sannan Alhaji
Tanko baya zama bayan arizikin da ya ajiye
mata agidan.
Fitowarta yasa suka nutsu kowa ya daidaita
tsayuwarshi, alokacin ta shiga cikin motan
sannan suka nufi gida, shima sai da Alhaji
Tanko yakirashi awaya don ya kara jadadda
masa cewa duk abunda tayi ko duk inda taje
ya tabbata yakira ya sanar masa, Salma
kuwa duk tana tunanin hanyan da zata
kashe aurenta amma idan tayi tunanin yadda
makomar ta zai kasance idan ta kuskura ta
kashe aurenta sai taji jikinta yayi sanyi
domin kuwa akan maganan Barrister zai iya
tsame hannunsa a lamarinta, don haka dole
ta nemi wani hanya.
*****
Wasa-wasa sai gashi Jalal yayi wata uku
yana aiki a gidan, duk wani bayani akan
salma yana dashi sannan ya zama kusa da
ita sosai domin hatta abinci wataran ta kan
ce shi zai kawo mata, shi kuwa ya kan
sanar da Alhaji Tanko har ya samu ya
amince dashi sosai, sannan ya fahimci
halinta sosai, macece mai son dadi da kuma
son asani, rayuwarta na karya ne duk da
cewan tana da kudin da kuma abun gadaran
wato kyau, matsalarta daya ne! duk
tinkahonta da kuma yanga da gori da takeyi
wa kawayenta ta kan nutsu idan anzo
hidiman miji, Alhaji Tanko kowa yasan tsoho
ne shiyasa bata ma so asan shi mijinta
agurinta kauyenci ne hakan, duk lokacin da
bukatar namijin ya taso ta kan fizge tace
baya gari ne amma bata tashi gane amfanin
Jalal ba sai randa bata da lafiya kuma taje
asibiti, alokacin Alhaji tanko yayi wata uku
da barin kasan nurse ta bukaci tasan mijinta
atake ta nuna Jalal sannan tace “gashi can”
idonshi a zare yace ” nikuma madam?” ta
gyada kai alokacin nurse tace ya shiga ciki
aikuwa jikinsa a sanyaye yabita bayan ta
gama masa bayani suka fito zasu wuce
yadda take tafiya nurse din tace ” ka rike ta
mana kar ta fadi” ya juyo yana kame kame
atake ta damko shi ta rungumeshi wani yarrr
yaji ajikinsa hankalinsa ya tashi, tsigan
jikinsa duk ya tashi.
Ganin bai riketa kamar ya yadda ta riko shi
ba yasa ta kara damkesa har da sunkuyawa
wanda da sauri ba shiri ya rikota har suka
karasa motan, haka ya sakata aciki yaje
gaba drivern yaja suka tafi, isansu gida ma
langwabewa tayi taki fitowa ganin haka yasa
ya zagayo ya bude mata kofan dan bata
daman fitowa amma ganin baida niyyan
rikota yasa ta rikoshi ta rungume, jikinsa na
bari ya juya bayansa don yaga wa ke
kallonsu, anyi sa’a drivern ne kawai sauran
ma’aikatan suna ciki da sauri Jalal ya
dauketa cak ya kaita cikin gidan, sama ya
haura ya ajiyeta akan gadon alokacin har jan
numfashi take dan ita kadai take jin abunda
ke ranta,
” barin kira masu aikin ko akwai abunda kike
bukata” ya fada alokacin da yake shirin fita.
” a’a ka bari idan inason abu kai zaka min,
miko min wayata” kallon da ya mata yasa
ita kanta ta tsargu da kanta, sai dai yanayin
kwanciyan da tayi ya daga masa hankali,
jakanta ya miko mata sannan yace “gashi”
taciro wayanta sannan ta saka akunnenta ”
Aisha kin dawo ne? kizo gidana mana,
tambayi hajiya wallahi bani da lafiya kinji?”
can kuma sai ta ajiye wayan sannan tace ”
kanwata Aisha yar autarmu ce zata zo, zata
tayani zama suna hutun makaranta, ku barta
ta shigo” ya gyada kai sannan yayi hanyan
ficewa ta katse shi da “Kafin nan kaje min
capital hub ka duba min case din wayata
don Allah” ya gyada kai sannan yafice, mota
ya dauka yabar gidan.
**********
Tana tsaye agaban mai siyar da kayan
wayan, taje duba earpiece don ta nemi nata
ta rasa kuma bata iya zama babu earpiece
ba, suna kan ciniki Jalal ya shigo tare da
sallama, ta amsa duk da kanta yana kasa
sai da yaji gabansa ya fadi, ya zura mata
ido alokacin da ta dago tana magana da mai
shagon, kamanninta da Salma kaman carbon
copy, hatta muryarsu daya ne, banbanci
daya ya gani ita riga da wando ne ajikinta ta
rufe da kimono yayinda Salma bata fita da
irin wannan shigar, sannan Salma tafi
wannan duhu kadan, har ta gama cinikinta
idonsa akanta kafin ta juyo suka hada ido,
gabanta ne ya tsinke ya fadi dasauri ta
sunkuyar da kanta sannan ta fice, sai daya
bita da kallo sannan ya siya abunda zai siya
yafito. Motansa ya gani anyi parking ta baya
don haka sai ya shiga ya zauna yana horn
ko zai ga mai motan amma shiru, ya kai
awa biyu yana zaune yayi cikiya har ya gaji
hatta masu gadin gun sun tayashi cikiya,
suna neman mai motan don wrong parking
akayi gashi antare wa masu fita hanya, can
dai yaga tazo ta bude motan za tashiga
dasauri ya nufi kanta da fada ” ke wacce irin
mutum ce? daga gani ke learner ce, inba
haka ba meyasa zakiyi wrong parking kuma
kin shiga kasuwan kin zauna kamar gidanku”
wani harara da ta sakar masa sannan tace ”
sai meye? dukana zaka yi? Arrogant
Bastard!” wani kullin bakin ciki yaji aranshi
yafara zaginta yayinda ta dau motanta
tabarshi tsaye agun, masu gadin ma da yake
sunga macece ba wanda yabi ta ko ya
hanata, da bakin ciki ya nufi gida yayi horn.
Babban mamakinsa shine ganin wannan
motan acikin gidansu, nan tunaninsa ya
kawo masa kammanin da sukeyi da Salma,
ko itace Aishan? lallaima, haka dai yashiga
har fanninta sannan ya buga kofan, daga ciki
aka basa daman shiga donhaka ya murda
kofan ya shiga kamar munafiki, hangota da
yayi yasa ya sunkuyar da kai gabansa na
fadi don kar amasa matsifa,
“chai Adda dama wannan pig din agidannan
yake?” mamaki ya ishi Salma sannan tace
“aina kika sanshi?”
“shine wanda nake gaya miki yanzu, zai
raina min hankali a capital hub”
“oh, shine Jalal da nake gaya miki na
aikeshi” wani harara Aishan ta saka mishi
alokacin da Salma tace masa
” ga kanwata Aisha, kayi hakuri da ita tana
da saurin fushi” ya gyada kai sannan yace ”
ina wuni small madam?”
” pig! am not small madam, i am madam ka
gane ko? gidan sisterna ne nan don haka i
have every right, ji yadda yaci gaye kaman
dan maigida ko maigida,kaje makaranta ma
kuwa?” ya gyada kansa don Allah yasani
zuciyarsa fashewa ce ba tayi agun ba, ji yar
karamar yarinya zata raina masa hankali
yana da degree dinshi amma ta mayar dashi
wani almajiri, Salma ce tayi murmushi
sannan tace ” degree fa gareshi” shi kam
ficewa yayi don bakin ciki yana zuwa daki ya
buga hannunsa a jikin bango da karfi ” wata
karamar yarinya zata raina min hankali,
what stupidity ne wannan” lallai za’ayi
zaman doya da manja, don zata bata masa
plans dinsa.
BABU RUWAN K’WAI DA ASKI
na
Benaxir Omar
*******
Fitowa tayi falon tana neman remote, zama
tayi sannan ta kwalawa mai aikin kira wacce
ta shigo a gigice, tun zuwanta gidan yau
kwana uku kenan har ta fita ran masu aikin
gidan, Aisha irin matannan ne masu raina
talaka, kyamar talaka da kuma ci wa talaka
fuska hakan yasa babu mai gigin shiga
hidimanta.
“Na saka zee world wa ya canja ya mayar
tashan yan kwallo?” yadda tayi tambayan ba
shiri mai aikin tace ” inaga oga jalal ne ”
“waya basa daman shigowa falonnan, ko
taba wani abu?” mai aikin sunkuyar da kai
kawai tayi ba tare da ta amsa ba a dai-dai
lokacin Jalal ya shigo. Wani kallo da ta
masa shi kanshi sai da ya tsargu sannan
tace masa ” waya ce kana taba abu a
falonnan , ku kauyawannan wallahi kuna da
dogon buri yanzu ina kai ina wannan falon?”
kallonta kawai yayi bai bata amsa ba ya
haura sama don Salma ce takirashi, tana
zaune akan kujerar dakinta tayi wanka tayi
kyau yayi sallama,
“rufe kofan” ta fada dai-dai lokacin da ya
shigo, ya juya a tsanake ya tura kofan
sannan ta kara da cewa ” da key” sai da ya
juyo ya kara kallonta duk da maganan bata
kwanta masa ba kafin yace “toh” sannan ya
rufe, kujera ya nema ya zauna tare da cewa
” gani, naji kina nema na”
“meyasa ka tsaneni? meye na rasa ajikina?!!
duk yadda nayi da kai baka damu dani ba!!!”
“hajiya da aure fa akanki, haramunne duk
wani alaka da zai shiga tsakaninmu”
“bawani kar kawo wannan hujjan, kai dai
tsantsan ka tsaneni baka sona dole ka fadi
haka, kasan sarai mijina baya zama, bama
haka ba ina zan kai wannan tsohon
najadun? bana sonsa, ko kawaye na ba
wacce ta sanshi, amma kaga kai abun
alfaharine, zan wadata ka da dukiya da duk
wani abu da kake son mallaka a duniyyan
nan in zaka bani kanka”.
Yadda ya tsaya nazarinta yaga tabbas da
gaske takeyi babu wasa a al’amarinta kafin
ya idar da tunaninsa kawai ya ganta a
gabansa tana kokarin kai masa hannu,
mikewa yayi da azama yana kokarin
kaucewa ganin yadda yakeyi yasa tace
“kwana daya dubu hamsin” wani harara ya
sakar mata ba shiri tace ” dari to” ya girgiza
kai sannan yace ” in zaki bada dari biyu toh”
da sauri ta gyada kai kafin ya yarda ta taba
shi, dakinta suka nufa dama tace kar kowa
ya dameta Aisha kuma tunda ta fara kallon
series dinta na india ba tasan meke faruwa
ba.
****
Tun jalal bai saba ba har ya saba da maitam
Salma, zata bukace shi kuma ta biyashi
sannu sannu ya fara tara dukiya mai dumbin
yawa, yayinda tsakaninsa da Aisha daga
hantara sai zagi duk da batasan meke
faruwa abayan idonta ba dama gashi ta cika
yawo, duk da tsanarsa da takeyi Jalal bai
taba tanka mata ba don kallon yarinya yake
mata mai fama da yarinta wanda hakan shi
yake kara tunzurata taji kaman ta kasheshi
babban abun da ke damunta shine yadda
taga Salma ke mutunta shi ko ince tsoronshi
domin idan ya fadi abu Salma bata taba
cewa a’a komi ya fada ya zauna ga kuma
wani kusanci da yadda da yake tsakaninsu
wanda har sai da ta fadawa Hajiyarsu ta
tsayar mata amma tace ai shi yasa shi yana
mata komi duk da haka tace “wannan
haramunne kina mace kina tare da wani kato
wanda ba muharraminki ba, sannan kice min
wai aiki yake miki haukan banza kawai”
yadda hajiya ta hau sosai dakyar ta kashe
wayanta ranan Salma ta saka Aisha agaba
da matsifa ba shiri ta tattara tabar gidan
acewarta zata je gun tailor.
***
Jalal ya fara cimma burinsa domin ba
karamin kudi yakeyi da Salma ba, komi
agidan yadawo Jalal yanzu kam sun daina
boye soyayyar da sukeyi wa juna, agaban
ma’aikata suke duk wani shiriritansu, amma
tsantsan tsoron Salma babu wanda yake iya
magana balle ma ina zasu ga maigidan su
sanar mishi.
Ta fito sanye da dogon riga, Jalal yana rike
da kugunta yayinda ta langwabe ta bayansa
cikin farin ciki sai ga Aisha da Amina (kawar
Aisha ce wanda makaranta ce ta hadasu )
sun shigo rike da ledodi ahannunsu, cak
suka tsaya, Jalal ya zaro ido ganin kanwarsa
jiki na bari ya sake jikin Salma yayinda
itama ta sake shi don ganin Aisha, salati
Amina ta ja tana cewa ” yaya jalal?! me
kakeyi anan? wannan ne aikin naka?”.
www.Benaxiromar.com
An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya
Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online,
Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan
Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490
A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu,
Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu
Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC
Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku
This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng
You can download more hausa novels there
Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online
It is free we do not charge for uploading novel
Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services
Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us
Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it
Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC
those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT
This Novel is downloaded from https://thausanovels.com.ng
to download more hausa novels visits our site at www.thausanovels.com.ng
For feedback and support
Facebook : https://facebook.com/taskarnovels
Twitter : https://twitter.com/taskarnovels
Telegram : https://t.me/taskarnovels