Share this page
1 / 2
An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://thausanovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.thausanovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels ” Ya Jalal tun jiya nake kiranka kana gani ba ka dauka ba” ta fada a marairaice cikin damuwa, ya kalleta sannan ya sake murmushi ya saka hannunsa a aljihu idonsa kyar akanta ” ke dadina dake rashin hakuri, sai kace zan gudu nabar kasan, toh banda kati ne shiyasa ban kira ba” “kai Ya Jalal” ta fada cikin kokonton abunda ya fada, sannan ta karasa da cewa “kai dai baka yi niyyan kira ba” ta bude motan ta dauko wayansa dake caji sannan ta saka password din ta shiga tana bincikawa ko zata ga abunda take nema, daga karshe ta mayar ta ajiye sannan tace ” ga kati har dubu biyu aciki, ni dai baka kyauta min ba” ” to tuba nakeyi yar mama” ya fada sannan ya ciro hannunsa daga aljihun wandon nasa ya kama kanta yana mutsikawa da sauri tasa hannunta tacire nasa hannun tana turo baki ” yau naje nayi kitso zaka saka min ciwon kai” ” wani gutsirin gashin naki da ko nawa ya fishi yawa?” ya fada yana mata gwalo sannan ya juya ya shiga cikin gidan yayinda ta bishi da gudu domin bashi amsan maganansa ” wallahi ya Jalal baka fini gashi ba kai dai ka fini cikan kai” ko kulata baiyi ba har suka shiga cikin gidan , fannin mahaifiyarsa ya nufa tana biye dashi kaman kaza har sai da suka isa suka zauna agefenta tana lazimi akan sallaya. Jiranta sukayi har ta idar kafin ta juyo tana murmushi ” karan me ka kawo yau” ya sosa keya sannan yace ” yau bata yi gagara ba” ita dai Amina bakinta ta turo cikin shagwaba take cewa ” Mamy sai kace nine mai yin mugunta kinfi son Ya Jalal akaina wallahi”, Mamy tayi murmushi sannan tace ” tashi min a jiki kafin kiji min ciwo jiki duk tauri kinyi wanka yau kuwa?” ” ayya Mamy wanka na uku yau” “Hajiya rage ma yara mana,wankan ki daya” Jalal ya katseta ya hade girarsa sama hakan sai ya bata dariya tace ” kamanta yau ba ka leko gida ba? tun jiya rabonka da gida, irin kaima ka girma ka siya gida” hannunsa yasa ya jawo kunnenta ya murda tana kara,Mamy tasa hannu ta make shi “Sakemin kunnen yarinya, kullum ka shigo gidannan sai ka zalunceta” “Mamy kina ganin rashin kunyar da takeyi” mikewa yayi ya buga rigarsa yafita yana hararar Amina. Motarsa ya nufa ya kunna tare da yin horn, maigadinsu Idi yana bacci amma tsantsar yadda Jalal yake danna horn ba shiri ya farka ya bude masa,har ya fito ya leka tare da cewa ” Wataran sai na sace ka agun” Idi yayi dariya yana bada hakuri, gidan mai ya nufa domin saka mai a motarsa ganin ta kusa karewa, a nutse yabi layin ya kunna radio yana sauraren labarai da akeyi har wata mai bara tazo, tsohuwa ce sosai ta tsaya dai-dai window tana bara, duba motan yayi ko zai ga canji har yaci karo da dari biyar ya mika mata tare da cewa “Gashi baba” ta karba tana ta godiya sannan tace ” me sunanka?” Yayi murmushi kaman ba zai amsata ba can dai yace “Jalaludeen” “Masha Allah, duk wacce ka hadu da ita yau karka kulata, ko da ka kulata karka bari wani abu ya kara hada ku” ya kalleta tare da girgiza kai duk da cewa ya tsorata da kalamun nata, sannan yanufa inda ake zuba mai din tunda layinsa yazo ana zuba masa yabar wurin, yana tunanin kalamun baiwar Allahn ta fada yayi yar dariya sannan ya nufi shago, yana so yasiya maganin sauro da kuma batir, shiganshi shagon ya gama diban abunda yakeso harda goran ruwa da na juice da ya diba, yazo layin biya anan ne gizo ke saka domin kuwa mai karban kudin sai hayaniya yake da wata duk da Jalal bai gane akan me ba yasan cewa akan kudi ne, ganin abun nasu yaki cinyewa har mai shagon na kokarin zaginta yasa Jalal yace ” lafiya meke faruwa?” juyowa tayi idonta yayi jajur kaman za tayi kuka “Bawan Allah ka bashi hakuri na zo nan nasiya kaya kuma sauri nakeyi na bashi ATM dina don yayi amfani da POS toh yakiyi inaga network ne amma yana so yace min barauniya dama sata nazo yi” Jalal ya kura mata ido, bata yi kama da ballagazan mace ba kokuma wacce zata ci kudi ko wacce zata yaudari wani ba, Abaya ne ajikinta ta rufe kanta duk da gilashin ciwon ido dake idonta tana da dan haske kadan ita ba fara ba sannan ba baka ba, ya ciro ATM dinshi sannan ya mikawa mai shagon ” gashi ka biya anawa, ka hada dukka” kallonsa tayi a tsorace sannan tace ” kayan dubu sha biyu na dauka, ka bari kawai zan jira idan an sami network” ya kalleta sannan yayi murmushi ” meye 12k babu damuwa” godiya ta farayi alokacin ya biya dukka ta hada kayan ta riko sai da ta saka a motanta sannan ta juyo ta sameshi yana shirin tafiya ” ka tsaya, zan karbi account numbanka don Allah na tura maka anjima ko gobe” ya kalleta yaga hakikan gaskiya take fada, ” ina ATM card dinki?” ta ciro ta miko mishi, “wayanki fa?” shima ta mika masa yayi dialling numbansa tayi ringing anasa yaga numban sannan ya duba sunanta a ATM card din “Salma Jibrin” ya fada ahankali sannan yayi saving numban, shima yayi saving nashi sunan sai ya mika mata dukka sannan yace ” na gode” baki abude ta tsaya kallonsa har yabar gurin, yana tafiya yana murmushi wanda shi kanshi bai san dalili ba, dole ne ma yakirata shikam ya samo matar aure, wayarsa ya dauka yakira Amina, ” meye kuma?” ” ke ajiye batun fushi, na samu matan aure” ” kafi shekara uku kana fads mun wannan kalmomin har yau ko budurwa baka dashi sai tarin kawayen banza” ” da gaske wallahi naga matan aure” yana gama fada ya kashe wayan dadi kasheshi shikam ya sami matan aure. toh jama’a dagaske ya sami matan auren? ko kuwa zamu bi maganan tsohuwa mai bara?. Gida ya isa cikin kwanciyan hankali yayi wanka ya bi lafiyan gado, wayarsa yaji tayi kara ya dauko ya duba,anan gabansa ta tsinke ta fadi daya tuna meya aikata, dubu sha biyun da ya cire dazu ba nashi bane na hajiyarsa ce, ya zaiyi da ita? tunda ta bashi kudin ne ya cikata asiyo napep abayar ana sana’a amma tsantsan ganin halin da take ciki baisan lokacin da ya cire ya bayar ba, harda cewa 12k ai ba komi bane. Gashi albashin shi ma dubu 60 ne a wata, tunanin duniya ya damesa a ranshi yana cewa akwai rikici.Wayan ya dauko yakira numban harta gama ta tsinke ba’a dauka ba hakan yasa yakara kira, wannan karon ta dauka cikin sassanyar murya tayi sallama, ya amsa sannan yace Jalal ne, tace ” nagane ai, kamanta nayi saving nima?” yayi murmushi alokacin ta masa godiya sosai tare da rokonshi ya turo mata account numbernsa saboda ta mayar mishi da kudin, yace mata bakomi shikam dubu sha biyu ai ba wani abu bane, nan dai suka gaggaisa yace yana son sanin ita wacece tace masa ta gama makaranta wannan shekaran a baze, nan yace mata shi yana aiki a federal secretariat wanda azahiri karya yakeyi, anan ta gwada masa akwai wani bappanta da yake gun har take tambayanshi ko ya sanshi? Ganin asirinshi zai tonu yasa dasauri ya kawar da labarin, suka yi sallama dai ya kashe wayar tasa. Washegari da yamma yakirata yace yanason ganinta, tace masa tana gida, sai da yaje gidansu yaci abinci ya koshi tas, Amina ta hau tsokanansa don yadda taga yayi kyau har wani kamshi yakeyi, tuni ya mammake kanta yabar gidan, biyoshi tayi “ina zakije?” “zan bika hiran” ta amsa mishi, duk da yayi mamakin yadda akayi tasan hira zaije amma ya danne yace “ba inda zakije” ficewa yayi yabarta agidan Jalal da Amina sune yara kadai agun iyayensu, mahaifinsu ya rasu hakan yasa Hajiyarsu Ladi ta dawo musu uba kuma uwa, tana aiki sannan gidansu na daga cikin gadonsu, Hajiyarsu na aiki a ministry of defence, komi ita take musu har ya gama jami’a da kale kala, university of abuja yayi, Jalal dai yana da tsayi sosai, yadda jikinsa ma ba’a gani tsayin ta boye, cikakken bahaushe yana da kyau dai dai gwargwado ba irin mahaukacin kyau ba amma yana da cika ido, abunda ke janye hankalin mutane akanshi shine idanunsa, kaman na mai jin bacci,yana da charisma da cute face, fuskanshi na yara gashi gashin kanshi akwance take luf luf hakan yasa mata ke binsa kaman zasu cinyeshi, tun a jami’a Allah yayishi mai farin jini, duk da ba abunda ya ajiye ko ya tara , tarin kawaye da yake dasu sai masha Allah, kasancewar su sukeson zama dashi yasa su suke kashe masa kudin, kowa tasan Jalal , gashi da son kwallo dan manchester ne, da ya kammala ya samu yayi bautan kasanshi a Benue nanma sai da Hajiya ladi tayi da gaske akan yan’matan da ya kwaso mata, irin mazannane masu bude cikinsu wa mata, zai nuna miki ya yarda dake sosai, har ki fara sonsa ma baki sani ba, sannan shi zai daukeni ne a matsayin kawa, hakan yasa mutane ke masa kallon babban mayaudari. Irin mazan da zasu iya bada rayuwarsu don su faranta miki amma su bawai suna sonki bane, gashi dai ba shekaru yakeda shi ba ,26 ne kacal , Hajiyarsa ta sana masa aiki a office dinsu duk da bawani matsayi yakeda sosai ba, ta sama mishi ne kafin tasamu mai kyau wanda zaiyi. kanwarsa Amina kuwa ajinta biyu itama tana gwagwalada, sun shaku sosai ga fahimtar juna a tsakaninsu. Salamatu Jibrin shine sunanta, itace ta uku acikin biyar daga yaran Barrister Jibrin, Wani Hamsheken dan siyasa wanda dasu ake damawa a mulkin nigeria, tsohon Hannu ne sosai sannan ga sarauta da yake dashi agarinsu. Salma irin yaran da suka taso cikin gata, babu kwaba babu tsawa, ba tasan babu ba sannan tarbiyar dai gashi ne ana fama, Ta kammala makaranta a baze tana zaman gida, shekarunta ashirin da uku a duniya. Mahaifiyarta Hajiya Abu mace ce kamila, fulani mai nutsuwa da hangen nesa dukkan iya kokarinta na ganin ta tarbiyantar da yaranta , burinta bai cika ba domin kuwa mijinta ya hanata sakat, da zaran yaga zata takurasu zai taka mata birki acewarsu yaransa bawanda zai takurasu, akullum takan ce masa “Alhaji ta ina zasuyi aure? ka ajiye yara mata har biyar agabanka sannan ka hana a kwabe su? wani namiji ne zai auri mace marar tarbiya?” ya kan yi murmushi yace “kowacce mace da mijinta, in kuma kika ga ba tayi aure ba to lokacinta ne baiyiba” Amma hakan bai hana Hajiya Abu tsayawa kan yaranta ba, da zaran taga zasuyi mummunan shiga tana hana su, ko sun siyo kayan yagawa takeyi ko ta kyautar hakan yasa duk basa jin dadi sai Abbansu yana gari, ko fita zasuyi wani party ko wani gu sai dai su saci hanya amma Hajiya Abu kam ta hana. Akwai Fatima, Hajara, Salamatu,Amina,sai Aisha yar autarsu, Fatima da Hajara har masters sunyi amma shiru babu mijin aure abunda Hajiya Abu take gudu, duk tabi ta damu don ma Allah yasa Barrister Jibrin na da kudi da dangi ba zasu barsu su huta da surutun sunki aure ba, Fatima shago ta bude na dinki tana desighninh kaya yayinda Hajara ta bude restaurant anan suke kashe lokutansu yayinda salma ta gama kenan tana jira ta tafi bautan kasa, Amina da Aisha kuma suna Baze basu kammala ba, Wannan dan gidan suna cike da son juna duk da sai dare suke haduwa acikin gida anan kowa zai baje kolin wahalan da yasha aranan. Salma ta shirya tsaf tana jiran Jalal domin yazo, dama ta sanar wa Hajiya Abu abunda ya hadasu da kuma dalilin zuwansa, acewarta zata masa godiya sosai. ******** Shigansa cikin gidan bakinsa bata rufu ba, domin kuwa tunda yake bai taba shiga lafiyayyar gida irin wannan ba, wayyo Duniya, Kudi suna inda suke, Mai gadin gidan ne ya masa jagora har lambun gidan nan ya nuna masa inda zai zauna tare da cewa ” ka jira anan small Madam na zuwa” . Ta fito zata wuce Hajiya Abu ta kalleta “Meye haka? Kaman ba yar musulma ba? Sau nawa zan fada miki cewa ki daina fita haka, idan baki kiyayeni ba zan dauki gyalenki gaba daya na kyautar ki fara saka hijab mu gani, yarinya kunne kaman na kashi” baki ta turo ta kalli jikinta, rigan pakistan ne da wando sai gyalen ta yafa a kafada tabar kanta a bude , haka kuwa ta koma ta sanyi doguwar abaya ta killace kanta sannan ta shige ta fice, aranta kaman ta fashe da kuka don bakin ciki ahaka har ta isa lambun tana neman murmushi don ta shimfida wa fuskanta. Yadda ya tsura mata ido yasa ta tsargu tare da cewa ” ko nayi laifi ne?” “inaaa! ai ke bakya laifi!” tayi murmushi shima yayi alokacin aka kawo masa drinks ya fara sha, har lokacin bai ce komi sai da ya kammala sannan ya gyra murya tare da cewa ” nazo da kokon bara ta ne, Allah yasa akalleni” idonta ta lumshe cikin nutsuwa tare da cewa ” inajinka” ” Ko zaki iya bani zuciyanki? ma’ana in aureki? ki zama uwar yayana?” tayi murmushi sannan tace “toh, aurena kake son yi?” cikin murmushi da farin ciki yace “sosaima” tayi murmushi tace “aure kaman kayi shi yafi komi sauki indai zaka siya min gida a Banana Island, sannan zaka siya min Bugatti Veyron” idonsa ya zaro domin har zai shake da juice din da ya sha tare da cewa ” Banana island gida fa agun least in samu na 418million naira, wannan motan kuwa kusan billion uku ce fa” Gyada kai tayi sannan tace “kwarai kuwa, in baza ka iya ba kuma ka kara wuta” ya sosa kansa yayi murmushi sannan yace ” kin iya wasa wallahi, har kin tsoratani fa” daure fuska tayi sannan tace ” ba wasa a magana ta, nidai godiya nake son maka, amma bayan haka kar kayi tunanin akwai abunda zai hadani dakai” yayi jum idonsa ta kada tayi ja domin tunda yake ba’a taba masa wulakanci irin wannan ba, don ya matukar shan mamaki shi da yanmata suke binsa amma wai yau shi ake bawa doka , bazai bari yaji kunya ba don haka yace ” kimin alkawari idan na kawo miki wadannan zaki auren” ta kalleshi sannan tace ” ka kawo mana mu gani, zan aureka na maka alkawari” ya gyada kai sannan yace ” ko da kuwa kinyi aure dole ki kashe auren kizo ki auren” ta kalleshi sama da kasa ganin irin halin da yake ciki tayi murmushi sannan tace ” na maka alkawari, ina jiranka” aranta kuwa tasan bazai taba samun wannan kudin ba, da haka sukayi sallama suka rabu ahaka, gogan kuwa yasa aransa dole ne ma yayi kudi ya dawo aureta. ************ Barrister Jibirn ne a zube a fada ya kawo karar abokinsa gaban sarki, sannan babban dan siyasa dan takarar shugaban kasa cewa ” mai girma na kawo karan Alh. Tanko gurinka” sarkin ya kalleshi sannan cikin iko da mulki yayi numfashi alokacin da ya bashi daman fadan maganansa ” mai girma Alh. Tanko ya lalata min yarinya, Salma, shi yake fita da ita domin har ciki yayi mata, ya bata wa yarinya ta rayuwa” ayadda yake magana zaka gane tsantsan damuwan da yake ciki, anan sarkin ya masa umarni da ya tafi zai nemeshi, arananan ya kira Alh. Tanko awaya sannan yace masa” inaso gobe ka taho da waliyinka, sannan da sadaki zan daura maka aure” . Salma ce akwance akan gado, jikinta duk ya kumbura ga fashewa da jikinta yayi, Hajiya abu kuwa wanda mutuwa ne bata yiba don tsantsan bakin ciki da takaicin abunda yar tata ta janyo mata, ta shigo dakin tare da cewa ” zaki fito ne ko sai na hambareki” dasauri ta fito daga bargon domin tasan halin uwarta dama gashi ita ta farfasa mata jiki kafin ta sanar da ita wanda ya mata ciki, wanda fadan sai da ya kusa zautar da ita. Suka isa falon alokacin Barrister Jibrin yana zaune kana ganin fuskarshi kaga damuwa da tsantsan tashin hankali ” kishirya kuje asibiti a zubar da cikinnan” a sanyaye ta mike zata fice ,hajiya abu bata san lokacin da ta mike ta bita da sabon duka ba dakyar barrister Jibrin ya banbareta alokacin har wani haki takeyi tana jan numfashi “Haba alhaji!! duk iya kokarina na ganin na gyra tarbiyan yarannan amma kaga abun kunyan da salma ta jawo min, zata kasheni tun kafin lokacina! haba mana dan Allah” rarrashinta yayi alokacin ya dubi su fatima yace “dukkanku ku fito da mazaje, sati mai zuwa zan daura muku aure sannan idan baku kawo ba zan hadaku da abokaina ba, ba zaku tozarta ni agari ba” Kamar yadda ya fada haka ya cika alkawari domin kuwa ran Asabar karfe goma na safe ya daura ma Salma aure da Alh.Tanko, dama yace kar ayi mata komi duk da haka sai da Hajiya tayi sayayyanta acewarta yarta baza’a mata gori ba. Bayan daura aure wanda kowa yayi mamaki ganin yadda aka tsallake su fatima da Amina aka daurawa Salma aure ba tare da yin wani bidi’a ba aka kaita gidanta dake asokoro, gida na gani na fada yasha kayan duniya da kayan alatu, bata tara wasu kawaye ba domin agunta auren dole aka mata, tayi niyyan taci kudinsa ne ta sallameshi Allah ya kamata tayi ciki sannan babanta yaji labari wanda gashi yanufi gun sarki yakai kara an daura musu aure, kwata-kwata ta tsani ganinsa duk da cewa bata da wani tsayayyen saurayi kuma Alh.Tanko ba wani muni yake dashi ba sai dai tsoho ne yakai hamsin da biyar, bafulatanin yola ne futuk irin bararoji dinnan, yaransa uku ne kacal kuma babu karami,yar autarsa ce ma sa’an salman, kudi kam ba’a magana wanda har wasu suna cewa tabbas Barrister Jibrin kudi yabi ya aura wa yarsa tsohon dan siyasa. Duk da tsufansa bai tsufa a soyayya ba domin kuwa lallabata yakeyi kamar zai maidata cikinsa, ya saka mata masu aiki agidan wanda ko tsinke sai taga dama ta rike ko ta kawar akan hanya. Tana sanya kaya adaidai lokacin da yashigo dakin, bata damu ba balle taji kunya kamar yadda sauran amare sukeyi basu saba da cire kaya agaban mazansu ba amma kasancewar bariki tayi kuma ta saba yasa ko daya shigo bata juya ba, ya tayata cirewa idonsa kur akanta har ta tsargu tace ” meye ka zura min ido kaman zaka cinyeni?” “don Allah kizo mu tafi honeymoon, na gaji da kasannan ko ke kanki zaki huta ma” ta ce ” ba inda zanje , ba yanzu ba ka bari sai na huta tukunna” duk da baisan dalilinta ba amma yabarta ahaka, ji yakeyi kaman ya cinyeta, akwai wani abu da yakeji agame da ita , shi dai yasan yana sonta amma ba zallan So ba, yakanji kaman ya mayar da ita cikinsa , haka ya rinjayeta zuwa ibadansu na ma’aurata. Wata uku da aure Salma ta rame ta kode sosai ,tana cikin tashin hankali wani abu da yake damunta shine yadda Alh.Tanko ke mata wasu abubuwa da bata ganewa, da farko idan ya kwaso bukatarsa baya sauraronta afka mata kawai yakeyi wanda ba karamin jin jiki takeyi ba, domin akwai ranan da tana kallo ya shigo tun daga falo ya sallami ma’aikata sannan ya fara rage kayan jikinsa, yayi kanta amma ta gwada masa bata da niyya, yadda ya fusgeta ranshi abace idonshi jawur ya wurgata kan gado a daki sai da ya idda sannan yafita, taji ciwo sosai domin yadda yasa mata karfi, akwai randa ya gama biyan bukatunsa da safe da rana sai gashi ya dawo ta danne ta yadda, daredare ta shirya tsaf zata kwanta sai gashi ya dawo alokacin duk jikinta radadi yake rokonshi ta fara yi akan yayi hakuri alokacin ya fara zaginta ” ba ke kika ce kina sona ba? bayan na miki ciki ai da kin karbi kudi kika zubar kika ware abunki amma kika fada wa babanki saboda shima yana son kudi ya kai kara na, toh na aureki kuma shima na bashi kudin don haka dole ki biya min bukata” tuni ta fara ja baya amma belt ya cire ya mata duka sosai ya biya bukatarsa, taji jiki kuma tayi kuka sosai gashi Hajiyarta ta umurceta da rike sirrin aurenta,tsananin kishi da yake mata ko masu aiki yaga tana magana dasu , zai hau mita da zaginta,ahankali tazo ta gane tana da ciki, gashi ko yaushe yana makale da ita, duk inda zaije ko wani gari zaije, ko yana gun uwargidansa toh zaiyi ta sintiri a tsakani,abunda bature yake kira Obsession, ko yaushe yana makale ajikinta ko meeting zai je wani gari da ita yake zuwa, ba ya barinta,duk da wahalan da take sha bata sanar masa ba sai wata rana yazo zai fita kamshin turarensa ya hau kanta alokacin da ya rungumeta, amai ta masa ajiki tuni ya gano ciki ne “Muje a zubar” ya fada cikin yanayin maganansa kamar ta yan maye, ta zaro ido sannan tace “Dan halal din?” “ae, zai katsemin jin dadi don haka dole ki zubar”. Ta kalleshi idonta a zare, dama gashi ya kumbura yayi manya, tamkar wacce take matsanancin jinya “kayi hakuri amma bazan iyaba” ji yayi kaman ya mareta don bakin ciki amma ya danne, fita yayi ya sami likitan yace masa ” ku zubar” likitan yayi mamaki sarai kasancewar shi yake lura da duk iyalansa don haka sai ya ce “kayi hakuri, me yasa za’a cire?” “na aureta don in moreta ne ba don na haihu ba, sannan in yara ne ai inada su, bana bukatan wasu” likitan yayi tsananin mamaki sannan yace ” ka mata magana, idan har ta amince me zai hana ayi mata?” ya kalleshi a kule sannan yace ” ko ba ta amince ba kuyi ahakan, ku danneta kuyi mata” “Alhaji, baza mu iya yi mata komi ba in bata amince ba, aiki ne wanda baza mu iya danne ta muyi mata ba” bai saurareshi ba ya fice , aikuwa sama da kasa salma tace bawanda ya isa ya danneta amata aikin da bata so, karshe haka suka tafi gida Alh yana ta sake- sake aransa akan yadda zai zubar da cikin ko ta karfi,lallabata yayi adaki ya lallabata har sai da ya cimma bukatarsa sannan ya bugi cikinta da karfi sai da ta zauce, ya kara bugeta, karan da ta saka sai da masu aikin suka nutsu kowa na fargaban meya faru kuma na tsoron lekawa kar ace abakin aikinsu, asibiti aka nufa da ita amma dai kam ciki ya zube, tayi kuka kaman zata mutu, gashi ya hana a sanar da iyayenta, Aranan tayi nadaman abubuwan da ta aikata lalle bariki baiyiba, mutumin da take ganin zai bata kudi yana biyan bukatarsa sannan za taje inda take so wanda aganinta wayewa ne amma ba daga nan ba, lallai Allah ba’a masa wayo ta dauka duk abunda za tayi da bariki zata zo ta auri wanda take so, taje yankee tayi rayuwan jin dadi, toh ga kudi ga komi amma babu kwanciyan hankali wannan matsifa da me yayi kama? yadawo aya ga mutanen baya agareta, ita kam tsoron lalata mahaifarta taji domin kuwa ta tuna da cikin da ta zubar na farko ko shekara abu baiyi ba ta kara zubar da wani. ******* Jalal ne rike da takardunsa yana zaune yana dan duba agogon dake hannunsa domin duba lokaci, wani dattijo ne ya shigo yakira Jalal din wanda ya bishi suka shiga office din tare suka zauna alokacin Jalal ya gaisheshi sannan mutumin yace ” mun duba takardunka yayi kyau sosai, mahaifiyarka tana da kima sosai a idona don haka zan nema maka aiki ko ba mai wahala ba wanda zaka na samun albashi mai tsoka, kai dai ka zamo mai rike sirrin maigidanmu Alhaji Tanko kaji ko?” Ayadda Jalal yake ji zai iya yin komi don ya samu aiki mai tsoka burinsa akullum shine ya tara kudin da zai auri salma ya biya mata bukatunta na gida da motan da takeso, duk da wani fanni na zuciyarsa na sanar masa cewa da kamar wuya amma ya kan janye wannan batun aransa don ya samu karfin gwiwa. “yanzu dai aikin kasa shine zaka zama P.A na amaryarsa yakamata ace mace akasa amma itace bataso matan da kansu suke barin aikin, don haka oga yace asa namiji yanzu don wancan karon dakyar aka kwace wata ahannunta don oga yace kar abari taje gidansu ita kuma ta

Chapter 1 of 2