Share this page
1 / 5
An dauko wannan littafi daga shafin https://thausanovels.com.ng ku ziyarci shafin na https://thausanovels.com.ng domin samun kayatattun littatafan hausa kama daga kan na yake yake dana soyayya Marubuci ko marubuciya zasu iya turo mana da littatafansu mu dora masu a shafinmu kyauta don masoyansu su rika Downloading a online, Sannan marubuta zasu iya turo mana da tarihin rahuwarsu da tarihin rubutunsu, dama sharhin littatafansu don masoyansu su gani kuma su karu da hakan Domin turo mana da littafi ko tarihin rayuwar marubuci ko marubuciya sai ayi mana magana ta whatssap da wannan nambar +2348140419490 A lura dakyau - kyauta muke saka littafi a shafinmu bama amsan ko sisin marubuci, duk wanda ya amshi kudinku da sunanmu babu ruwanmu, Alura dakyau - manazarta bama tura littafi ta private ku dena binmu private kuna neman mu tura maku littafi, duk mai bukatar littafi yaje website namu Alura da kyau - Littatfanmu suna fitowa cikin manhajoji uku ne PDF,TXT da DOC amman munfi amfani da PDF da TXT masu amfani da wayar android ko tablet ko computer zai fi kyau ku riga dauko PDF da DOC Masu amfani da kananan wayoyi java ko mara java TXT zakuna zaba don shine daidai wayarku This hausa novel was uploaded and downloaded from https://thausanovels.com.ng You can download more hausa novels there Also you can send us your novel to upload it in our website for your fans to download it online It is free we do not charge for uploading novel Also if you are an Author be it online or Non online you can send us your biography including your book summary,commentary and others via this number +2348140419490 its free we do not charge for our services Note that - we do not charge for our services we uploaded novels and posted biography free, any person that collect your money in our name is your fault do not blame us Note that - pls readers stop calling us and be asking us to send you a novels we are not sending novels through whatssap or private our novels is public at any day, any time you can visits our site and download it Note that - our ebooks came as PDF,TXT or DOC format but the popular format are PDF or TXT, those with android or tablet or pc we suggest you to download PDF or DOC those with java phone or non-java phone we recommend you to download TXT This Novel is downloaded from https://thausanovels.com.ng to download more hausa novels visits our site at www.thausanovels.com.ng For feedback and support Facebook : https://facebook.com/taskarnovels Twitter : https://twitter.com/taskarnovels Telegram : https://t.me/taskarnovels [10/24, 7:06 PM] ‪+234 701 117 6189‬: [12:00, 7/28/2016] Foulani Cerdiya😘 *AMEENA DA AMEENU* ®NWA ©FOULANI CERDIYA 1-10 *AZAMANIN MAN,AKW'AI MASU KI'DAN DAMUKE D'AUKOWA LOKACIN BIKUNKUNANMU SUNA NE BIKI NE, DA DAI MAKAMANTANSU AKW'AI WAD'ANSU MASU KI'DA D RAWA A GURIN BIKI WAD'ANDA SUN KASANCE YARAN DJ N* *SOMETIMES ZAKIGA MASU D'J SUNZO DA Y'AN MATA GURIN BIKI SUNAMUSU RAWA* *TA BURGEWA DAN KAWAI SU BASU ABIN HANNUNSU, DAGANAN WASU* *ZAKIGA SUN LALACE TARBIYYARSU TA TAB'ARB'ARE,* *HARMA KIGA BAASAMU DAMAR YIN AURE BA.* *SABODA WANNAN SANA'A DA WASU Y'AN MATAN SUKA D'ORAWA KANSU, DUK KUWA INDA* *KIKAGA MUTUM NA RAWA GABAN MAZA DA MATA* *KINSAN BABU* *KUNYA A GURIN.* *ALLAH SA* *MUDACE AMEEN* Tafiya nake akan titi kamar yadda nasaba dan in samo muku labarai, aikuwa kw'atsam naci karo da wata nuts'atstsiyar yarinya cikin k'atoton hijab, daga gani makaranta zata ko kuma ta taso? oho nidai Foulani haka nayi ta mamaki, da jaka a rataye a kafad'arta, tafiya take cikin kw'anciyar hankali a natse. Madaidaiciya ce, daga kallon danayi mata daga baya, binta na cigaba dayi a baya har naga ta tsayar da me keke napep(adaidaita sahu) banji inda tace masa xataje ba amma naga ta sh'iga, nima da saurina na ts'ayar dawani nace yabimin bayan waccen matar, adai-dai gidan wani party naga ta sauka, tabiya d'an keke napep kud'insa ta fito,. mamaki na zaro ido ganin da hijab ne ajikinta yanzu kuma naganta tafito da mayafi, hmm dad'inta d'aya kayan jikinta ba matsatstsu bane, kuma mayafin bawani babba bane can, tayi rolling dash'i ta sh'ige. Kid'ane ke tash'i sosai,. Ta sh'iga ga matanan a zazzaune akan fararen kujeru, daga can kuma gamasu kid'a nan, yana tash'i wajen naga ta nufa, tayiwa wani magana yazoko har inda take, ahankali naji tana masa magana yace to ta sh'iga ta ajiye jakarta , aka ware kid'a tafito tafara dancing kamar baajikinta ba, aikuwa nan danan mutanen dake wajen suka dinga zuwa sunayi mata lik'i, kud'i kuwa se zubar mata ake saboda yadda ta iya rawar sosai, 6:00 ta kalli agogon hannunta, jakarta ta d'auko, wannan wanda naga tayiwa maganar sh'idi'nne ya biyota a baya, a d'an wani waje suka samu suka tsaya, kud'i ya ciro a aljihunsa ya mik'o mata yace"ga kudin ladar rawarki, "Ok nagode ta karba tana hucewa atake kuma wasu zafafan hawaye suka ziraro mata, a ranta tace"Allah kazama gatana ka fitardani daga rayuwar danake,. Tash'are hawayenta ta ts'aida wani me keke napep ya kaita har k'ofar wani madaidaicin gida, ta fito da hijab d'in d'azu ajikinta t bash'i kud'i ta sh'ige gida da saurinta. Da sallama ta sh'iga gidan, wata matace a zaune tana tsefewa wata yarinya kai, "Mama sannu da gida "yawwa y'ar kirki har kindawo "eh wlh Haleema ma tana gaish'eki gash'i tace ma abaki ta ciro kud'i ajakarta ta mik'a mata Mama ta karb'a tana irgawa, ta lissafa dubu biyar ne cif "duk ita tabaki wannan d'in Ameenah? "eh ita tabani ta fad'a tana sh'igewa d'aki. Yarinyar da akewa tsifarce ta juyo ta kalli Mama tace"Mama kinga sai ki biyamana kud'in makaranta nida Asleem "Insha Allahu Tasleem mugodewa Allah da yakaho mana kud'in nan dan dakinga gobe baki da zuwa makaranta. A d'aki kuwa Ameenah ce zaune tana ninke kayanta tasa asif ta fito dawata doguwar riga ta saka sannan tafita tayo alwala tayi sallah, bayan ta idar ta d'aga hannunta tana rok'on Allah ya kaho musu mafita a rayuwarsu, Allah ya fitar da'ita daga cikin halin data jefa kanta na zuwa gidan biki tayi rawa dan kawai abata kud'i tasamu na taimakawa Mamanta domin.......... ~HOPE DA DAD'I INAJIRAN RA'AYINKU~ Maman triplet ce😘 [10/24, 7:06 PM] ‪+234 701 117 6189‬: *AMEENA DA AMEENU* ®NWA ©FOULANI CERDIYYA 10~40 Maraicin da suke ciki ya jaho musu haka, ga mats'anancin son Ameen datakeyi, wanda besan tanayi ba hasalima gani take kamar ya tsaneta, saboda k'azamar rayuwar data d'aukarwa kanta dan ta taimaki mahaifiyarta, Amma tana tunanin wannan zuwan datayi gidan party Insha Allah sh'ine zuwanta na 'karsh'e, badan komai ba sai dan ta samu soyayyar Ameen kamar yadda Haleema tash'a gaya mata takance da ita"Friendy kin d'auki rayuwa me wahala gash'i kin fad'a son Yah Ameen kina tunanin zai soki a haka ne? sh'awarata a gareki itace ki hak'ura da wannan yawace-yawacen gidan rawar. Hawaye ya k'ara zubowa a Fuskar Haleema wanda hakan yayi dai-dai da sh'igowar Tasleem k'aninta da gudu, yana zuwa ya fad'a jikinta yace"Aunty Sayyada sunan da suke kiranta dash'i a dalilin kasancewar sunan Mama ne akasa mata, sh'iyasa k'annen nata ke kiranta da Sayyada Wacece Ameenah(Sayyada))? Amina muhd Abdullahi sh'ine asalin sunanta y'ace wurin Alhaji Muhd yakasance d'a d'aya agurin iyayensa wato Alhaji Abdullahi d'an kasuwane na hak'ik'a inda yake ordern kaya daga waje yana turowa nigeria domin a sayar Alhamdulillah sana'ar ta karfesh'i dan nan danan yafara gini, ana haka ne Allah ya had'ash'i da Ameenah wato Mama Mama ta kasance itama y'ace d'aya a gurin iyayenta bayanta basu k'ara haihuwa ba Alhaji Muhd ya auri Mamanta har dai bayan auren nasu basu haihuba sai da suka d'an jima dayin Aure lokaci d'aya Allah ya basu haihuwar yarinya mace wato Ameenah Ameenah ta taso cikin kulawa daso da k'auna har makw'aftansu ma suna son Ameenah sakamakon yarinyar ky'akyky'awa ce data fara hankali kuma ta kasance nutsatstsiya ce bata da hayaniya bata da girman kai duk kuwa dacewar Alokacin Mahaifin nata me kud'i ne Bayan y'an sh'ekaru sunja har ansa Ameenah a makaranta ta boko da islamiyya, tunda suna primary take da wata k'awa me suna Haleemah'Haleema irin yaran nanne masu kok'ari a makaranta kamar dai Ameenah itama babu ruwanta hakan ce tasa suka saba da'ita kuma itace k'awarta har yanzu, Mama ta haifi yara biyu bayan Ameenah wato Asleem da Tasleem sune ma suka samata suna Sayyada wato Aunty Sayyada Mahaifinta ya rasu; bayan yayi jinya inda tacinye masa rabin dukiyar daya tara.Watarana da daddare bayan mutuwar Mahaifinsu Ameenah b'arayi suka sh'igo musu suka musu satar kaf abinda suke dash'i, kuma Alokacin ne Ameenah ta gama secondary school daganan rayuwa ta sauya musu,babban gidan dasuke cikima suka sayar dash'i dan asamu na cin abinci da biyawa yara makaranta, Ameenah tana zuwa islamiyyar dake bayan gidansu wacce itama Haleemah tana zuwa,. Bayan anyi hakane ta yanke sh'awar dayaya xata ringa taimakawa Mamanta? hardai wata rana taje bikin wata frnd d'inta taga wata tana rawa a gidan biki kuma ta fuskanci kud'i aka biyata sh'inefa taje tayiwa masu Dj mgana su kuma ganin ky'akyky'awa yasa sukayi saurin amince mata data dinga zuwa tana musu rawar sudinga biyanta, kullum ran asabar da lahadi zakiga Ameenah baa zuwa Islamiyya, Halema takan tambayeta" wai ke Friendy ina kike zuwa ran weekend ina monitoring d'inki saboda nash'a zuwa idan antash'i Mama tacemin kinje makaranta while ni bakizo ba, ki gayamin ina kike zuwa? kuka ne ya kufcewa Ameenah adalilin yaudarar Mamanta datakeyi, "Kiyi hak'uri Friendy wallahi ba inda nake zuwa, but.......sai kuma tayi sh'iru tarasa abin cewa"but what? tell me bekamata ki boyemin ba' nan dai Ameenah ta gaya mata abinda yake faruwa na zuwa gidan party tayi rawa a biyata. Salati Haleema tasa tace"talauci haukane Friendy? kinyi Kuskure, yanzu ni bazaki iya gayamin mats'alarki na? sh'in ni bazan iya taimakonki ba,? nandai Haleema tayi Fush'i da k'awartata hardai tayi mata alk'awarin baxata k'ara xuwa guri Party tayi rawa ba. anan nema Haleema take sanar mata bikin Yah Ameen saura sati d'aya,"yaush'e ya dawo ne Friendy, "ya dad'e da daho wa anyi anyi ya futo da mata yak'i to akw'ai wata y'ar k'awar Mumy shine aka had'asu duk da yace sh'i baya sonta ita kuma tana sonsa sosai, "Allah ya kaimu mush'a biki Ameenah ta fad'a tana faraa a fuskarta. Yau takama Friday taje wajen Dj khaleed tana tambayarsa koda wani party a week d'in nan? "Yes akw'ai wani zafaffen Party dazamuje wannan partyn nasan zamu samu kud'i, murmush'i tayi tace"ok yaush'ene "gobe ne "aina ne? ya fad'a mata sunan gurin "Allah ya kaimu ta fad'a tana juyawa tace "sai nazo a hanya tunani take ga bikin Yayan Haleema ya zatayi? data tuna jiya basu wani ci abinci ba yasa tace afili" sorry Friendy bayan ta koma gidane, Haleema tazo, lokacin Ameenah na d'aki tana gogewa su Asleem unifoam d'in school d'insu, Tasleem ce ta sh'igo tace"Aunty sayyada ga Aunty Haleema, da gudu ta fito tana fadin"oyoyo my Friendy, murmush'i mamatayi tace"saketa karki karyata, tayi dariya ta sh'ige d'aki itama ta bita, Haleema ta dubi Ameenah tace"ke gobe zaa fara bikin Yah Ameen, dummmm gaban Ameenah ya fad'i saboda bazata samu damar attending ba dalilin gobe zataje rawa kuma...... "ke ina miki magana, karb'i wannan, ash'obenki "woww yayi ky'au but Friendy ya....Haleema ta rufe mata baki tace"noh karkice komi kedai kizo, "ok alot of thanks Friendy harara ta galla mata tace"ke kika san thanks d'in ai suka tuntsire da dariya. Ameenah ce taketa sh'irin fita tayi kw'alliya harta gaji, tada yayin bikinta na less golden, dan daga wajan rawarta zata zarce gurin bikin su Haleema, duk da Haleeman tace ta ts'aya zata biyo ta d'aukets su tafi, itakuwa bata kaho komai ba ta yanke sh'awarar d'aukar wayar Mamanta ta tafi da ita in yaso in tafifo daga can saita kirata ta gaya mata wajen. "Cab Aminah ta fad'a ganin wajen partyn dabata ma tab'a zuwansa ba, gaskiya gurinfa yayi ky'au anyi decoration na k'ayatuwa tunda take zuwa party bata taba zuwa irin wannan ba, Mutane sai sh'igowa suke suma y'an gayu, sai dai tunda Ameenah ta sh'igo gurin gabanta keta fad'uwa ganin irin kayan dake jikinta, sh'ine na ragowar mutanen dake sh'igowa, *"Tash'in hankali*Ameenah ta fad'a a fili, bayan an zazzauna akan chairs dake wurin amarya da ango suka sh'igo aka bisu da tafi masu camera sai d'aukar photo suke, itadai jikinta yanata rawa gabanta nata fad'uwa, bayan anyi wasu jawabe -jawabe, aka ware Dj kid'a ya fara tash'i, babu yadda zatayi dolenta ta sh'iga tayi musu abinsu ,amma badan haka ba da bazata sh'igaba, tambayarta d'aya wai sh'in bikin nan nasu waye? itafa jikinta yana bata kodai bikinsu Haleema ne? "Nash'iga uku idan sh'ine hawa tayi kan stage tafara rawa normal, rawarta ta burge kowa da kowa, masu waya suka fara vedio, Ango Ameen sani muhd yaji gaba d'aya yarinyar ta burgesh'i, besan ta akai ya tsinci kansa da kallonta ba har ya tash'i yayi mata lik'i "woww handsome Ameenah ta fad'a a ranta dan yayi mata mugun ky'au inama mijintane, gaskiya ta burges'hi sai dai daya tuna rash'in kunya ce da fitsara yasata yin rawar sai yaji ta bash'i haushi zuwa yayi yasanarwa da masu magana cewar a daina d'aukar vedio, aiko aka sanar gab'a d'aya suka koma suna kallo amma sundena d'aukar vedion, "wannan familynmu ce? ko kuma yaya? tambayar dayakewa kansa kenan, kamar daga sama ta hango Haleema tana tahowa, Innalillshi wa'inna ilaihir rajiun, na sh'iga uku!!! can wata dabara ta fad'o mata ta sauko tana tafiya a hankali sh'ikuwa angon kallonta kawai yake taburgesh'i kuma ta bash'i haushi tana isa inda take ta rungumeta tace" nama rugaki zuwa, "Friendy kinyi bala'in ky'au "kema kinyi ky'au, Sh'ine kika taho, to aina kika san gurin? "uh....ai..hm kinga, tun kafin ta k'arasa fad'a Haleema tagane rawa tazoyi, tsaki tayi ta jaho hannunta suka hau kan stage d'in, ta rik'o hannunta ,suka fara rawa tare itada Haleeman, nanfa aja k'ara tagi raf rafrafraf, tasowa yayi ya musu lik'i yace ya kamata ku fita daga wajen rawar nan, yana fad'a ya kalli Ameenah data kulash'i ya harareta, a dai*dai lokacin k'arfe sh'idata nuna, aiko tayi dariya suka fita itada Haleema, Me dj ne ya taso yabiyota ya bata wasu uban kud'ad'e wanda bansan adadinsu ba, amma fa sunkai kudan dubu tal..bara dai inyi sh'iru kar ace na zuk'ata. Bayansu Ameena sun dawo daga dinner ne tazo kw'anciya bacci but baccin yak'i zuwa idonta , ta juya nan ta juya can tarasa mekeyi mata dad'i abu d'ayane ya ts'aya mata arai hararar da yayan Haleema yayi mata, murmush'i tasaki ita kad'ai, "dama zaka aureni *Ameenah da Ameen* what a mach!!! sai kuma ta tuna auren sa akeyi take taji fad'uwar gaba, tayaya ma za'ai ya aureta? yana da wannan matar? "ze aureki mana Ameenah kina fa da ky'au idan sh'i yakewa Ameenah fara ce amma ba k'al ba, doguwace dai-dai misali, k'irjinta cike yake fam, gata da hips , tana fa shape me 8 tana da fuska me ky'au wacce take d'auke da dara-daran idanuwa d'auke da zara-zaran bakin gash'in ido(eyelashes), gata dawani irin hanci me ky'au bawai dan yana da tsini ba, hancinta yayi ky'au a fuskarta, bakinta me ky'au d'an k'arami, gash'im giratta mara yawa y'ar siririya, gata maabociyar kw'alliya, idan tad'au makeup ke sekace khareena kapoor, idan tayi murmush'i dimples d'inta su lots'a, idan tana tafiya kese ki rantse tana sani take girgiza jikinta, amma ba haka bane, hasalima itabata so takeyi, woww takoina tayi. *Ameenah* Bayan sati d'aya, Ameenah na zaune ita kad'ai, tayi uban tagumi, ga lokacin islamiyya yayi, amma tana zaune tana sana'ar tata wato tunani, tarasa meyasa idan ta rufe idonta take ganin Ameen a ciki? bata san soba amma dase tace kosh'i ne? hawaye suka gangaro kan fuskarta, dai*dai nan Asleem ya sh'igo ,"Aunty me akayi miki? "bakomi Asleem i just need your prayer....... sallama tajiyo wacce kobaa gaya mataba tasan Friendy c, sh'igowa tayi da sallamarta, Ameenah ta goge fuskarta ta amsa, tun kafin Haleema ta zauna tace"mekuma akayi miki kike kuka? seko ta fad'a jikinta cikin kuka tace"i don't know Friendy tunani yamin yawa just pray for me pls, fad'amin abinda ke damunki? da ky'ar ta gaya mata komi, tana gama fad'a ta ky'al ky'ale da dariya tace" You feel in love, brother na , don't worry Friendy muyita addu'a dan kinsan sh'aamin Yah Ameen sai sh'i, but dole yasoki ai. Maman triplet😘 *Wanene *Ameen*?? sh'i irin mutanen nanne miskilai ga zafin kai, da nuna isa gash'i bayada yawan magana, sh'i i irin chocolate colour d'in nanne fatarsh'i very smooth yana da ts'ayi da zati, Fuskarsh'i d'auke take da dara-daran idanuwa hancinsa dogo, gawani saje daya kewaye Fuskarsa"Wow Ameen kenan wanda y'an mata suketa kaho masa hari Amma basa burgesh'i saboda sh'i har yanzu bega macen datayi masa ba dan sh'i ya kasance yana son mace me ilimin addini bawai dole sena boko ba, sannan yana son Mace nutsatssiya mai hankali da kamun kai wacce tasan mutuncin kanta. Yayi aure da matarsa khadeeja wacce ta kasance zab'in mumynsh'ice, dan sh'i bama yasonta , ko gado ne yadda sun had'aba, Khadeeja irin y'ayan masu kudin nanne wadanda basusan sunemu abu su rasa ba. Sedai abinda take buri da Ameen ya kw'anta da'ita gash'i sh'ikuma yak'i dan yace jikinsa bame arha bane, yana nan yayiwa macen datasan kanta , wacce bakowani karene yake kallon surarta ba ita ba irin macen dayake burin samu bace, yanason nutsatstsiya wacce zata bawa y'ayansh'i tarbiyya me ky'au ba ky'alekyalen abinda wasu mazan suke dubawa ba, yanason mace me dauriya bame raki ba wacce bazata iya d'aukarsh'i a sh'infid'a ba, dan sh'i d'in ingarmane, totally khadeeja batayi masa ba, ita sedai ky'au a fuska amma k'irjin a sh'afe yake, har garama hips d'innata ba laifi. ~Maman triplet~😘 [10/24, 7:06 PM] ‪+234 701 117 6189‬: *AMEENA DA AMEEN* ©FOULANI CERDIYA ®NWA 40~42 Abinda yafisa Ameena taji gaba d'aya rawar da takeyi tafita daga ranta sh'ine, Watarana taje gidan party, kamar yadda tasaba takansa kayanda ba matseta sukayi ba, tayi kw'alliya a fuskarta tunda dama itad'in sarkin kw'alliyace, bayan tasa hijab d'in makaranta tafito, Mama ta tarar a ts'akar gidan, tayi mata sallama tace mata ta tafi islamiyya, anan Mama tayi mata nasiha da cewa"Ameenah ki kula da kanki, kar kiyadda ki biyewa rud'in rayuwa kiyi abinda duk inda kikaje zaa samiki albarka ayabeki,kar kiyi abinda zaayi Allah wadai dake". "To Mama nayi miki alk'awarin kare mutunci na,insha Allah daganan tasa k'afa ta fice, tana zuwa titi ta tari me keke napep(Adai-daita sahu) ya kaita gidan party, ta fito cikin tafiya ta k'asaita wacce dama asalin Ameenah a haka take, jikinta yakan d'anyi rawa kamar tana girgiza sh'i while ba haka bane. Gurin partyn ya had'u ga maza da matanan, sunata dancing anata rawar sh'oki. Tak'arasa gurin y'an uwanta y'an D'j tamusu magana suka gaisa, alokacin me magana yayi umarni da kowa yakoma gurinsa ya zauna zasu fara nasu programm d'in, wato Mace da namiji su fito suyi rawa kamar yadda akasaba a wajen D'j. Aka fito aka fara rawa, nanfa Ameenah ta fara zuba rawa iri iri ta 'iya, mutane akafiffito akayi mata lik'i . Ana cikin rawarne tasamu y'ar uwarta wato y'ar rawa itama ta sh'igo cikin fili, "Woww rawar nan sun iyata kugunsu kamar ya cire gash'i komi a tare sukeyi, ke kyace zama sukayi aka koyamusu amma ina babu d'aya ballantana k'anwar biyu. Agogone ya nuna kansa 6:00 tafito, tana fitowa aka mik'o mata kud'inta ta karb'a, _SHOKI AH SHOKI_ wak'ar data daki kunnenta, amma ta fuske tasakud'inta ajaka, wanda adai-dai lokacin ne y'anmata da samarin gurin suka tash'i suna taya iblis iblish'sh'i a kw'aso a kuma rufe ido d'aya, *WA'IYAZUBILLAH* _SHOKI AH_ tana kaiwa nan tafad'i ak'asa *TUIM* kallo sai yadawo kanta, da gudu mutanen gun sukayo gurin a dai-dai nan tace ga garinku ne . Wata gigitacciyar k'ara taji a lokacin da akace bata numfash'i, "Ni Ameenatu baiwar Allah, ubangiji na tuba kayafeni" Ameenah ta fad'a tare da saurin ficewa daga hall d'in, tana ta jimamin yanzu mofy ta rasu? agurin rawa,? yanzu taje tace da Allah me? "Yasalam har Ameenah ta dawo gida da jimamin abun aranta, sukuku tazama, Mama ta tambayeta ko lafiya? tace da ita bakomi Abinci ma ta kasa ci, balle wani abu ruwa, itadai istigfari take yi da salloli tana rok'on Allah ya yafemata. *Y'AN UWA MUGANE WANI ABU, ITA RAWA BA'ACE HARAM BACE, AMMAADINGA SANIN A'INDA ZAAYI,* *SABODA YANZU* *DUK BIKUN KUNAN DAMUKEYI ZAKIGA* *MATA DA MAZA AN HAD'U ANCUD'E* *ANA RAWA A GURI D'AYA*. *IDAN DA'ACE A IYA* *GURINE PERSONAL WANDA BA MAZA IYA ZALLAN* *MATANE TO BABU WANI ABU,* *AMMA IDAN KAJI ANCE ZAAYI BIKI BABU D'J* *SAI KIJI ANA* *FAD'IN AI BIKIN WANCE LAMI BA* *DAD'I WAI SABODA* *BAAYI D'J BA HMMMMM* *ESPECIALLY IDAN AKASA* _SHOKI_ *WLH MATA DA MAZANE ZAKIGA SUN CURE GURI D'AYA ANA KW'ASO SHOKI* *ALLAH SA MUDACE* ~Maman Triplet~ Ga ha'intar Mama datekeyi, tunda bata san aina take samo kud'inba tana dai cemata Haleema ce ta bata, da farko Mama fad'a tayi mata akan me Haleema zata na bata kud'i ita gaskiya bataso at the end dai wataran Mamynsu Haleema tazo ta kahomata kayan provision tayi mata godiya, to tundaga lokacin ne Maman take yarda da hakan. Haleema takan rufawa Ameenah asiri saboda sau tari tash'a zuwa taga Ameenah bata nan koda kuwa Mama tace ai Ameenan tatafi sai kiji tace" May be sab'ani mukeyi Mama bari inje makarantar" koda wasa bata tab'a nuna mata bata zuwa makaranta ba. Kuma koda Maman tayi mata godiya akan wani abu da Ameenan ta kaho tace inji Mamynsu Haleema bata tab'a nuna mata ba itance ta bayar ba, dan wani lokacin idan taje ta dawo kud'in da'aka bata takan sayo kayan Abinci da kayan dazaa nema ta kaho mata azuwan Mamyn Haleema ce ta bayar. Koda tafad'a mata cewar Ameen takeso Haleema tayi murna da farin ciki sai dai ta k'ara gargad'inta da dole ne ta sauya halinta, ta dawo Ameenarta data sauya kanta da wannan banzar rayuwar. Ta zuwa gidan biki yin rawa, hirarsu ta k'arshe da Haleema ranar dataje gidan party ta dawo tayi sallah tana addu'ar Allah ya kaho musu d'auki cikin rayuwarsu, Sallama tayi ta sh'igo suka gaisa da Mama, ananne Maman take mata godiyar kud'in data bayar akaho mata. Murmush'i kawai tayi tace"ai Mama yiwa kaine," "kish'iga tana ciki" "to Mama Haleema ta fad'a tana sh'igewa cikin d'akin. tunani take ita kad'ai ta tuno hararar da Ameen yayi mata a farkon ganinta dash'i face to face, dan bata tab'a ganinsa a fili ba sai a hoto, afili ma yafi ky'au....... "sannunki juliet sarkin soyayya kinwani kish'ingid'e da alama tunanin romieo n kike ko?" Haleema ta fad'a cike da zolaya "Eh yason ranki y'ar sa eyes?" "Wai hmmm wai wayaga kuma fa ko kundace wallahi," But Friendy kinsan Yah Ameen d'an uwana ne, dole tilas ki gy'ara halinki ki dena zuwa gidan rawar nan dan Allah badanni ba" "kina tunanin wani zai aureki ne idan yasan cewar kina zuwa gidan biki yin rawa? sam-sam baze yuhuba, bawai akan Yah Ameen ba, kinsan kowanne uba burinsa samawa y'ayansa uwa tagari? why not bazaki zama haka ba?, ko kinaso nan gaba y'ayanki su taso ace Uwarsu kafin tayi rawa y'ar D'j ce? bafa haka kike ba Friendy You have to change your bad behaviours, pls You know har baiko akaiwa Benazir an kusa bikin but da saurayin yaji tana yimawa y'an D'j rawa ya fasa aurenta? pls nd pls Friendy ki sauya. Tana kaiwa nan tayi sh'iru "Insha Allah bazan k'ara koda rawa a gidan biki ba har indai ba iya y'an uwana mata ne zalla ba." "Yawwa k'awas har naji dad'i, nagode da k'arba'ar sh'awarata da kikayi" "nice da godiya ai"Ameenah ta fad'a da faraa a fuskarta. "ina romieo na??" "Hahhhhhh yana gurin matarsa daga aure wata d'aya hartafara kaho k'ara, sh'i yace mafa ya gaji da ita, dan halinta be masa ba. Itama kuma Mamy ta gaji da kaho k'arar da Aunty khadeejan ke kahowa,. danfa rash'in kunya wai ta iya cewa Mamy wai betab'a kw'anciyar aure da ita ba Mamy taji haush'i ranar nan wallahi. Haleema ta k'arasa maganar da bacin rai "Allah yasa mudace Ameen, Ameena ta fad'a tana mik'ewa ta kahowa K'awarta ta abin sh'a. ~Maman triplet~😘 [10/24, 7:07 PM] ‪+234 701

Chapter 1 of 5